Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farar fatar sa da hannun sa kana yace cikin sake karantar yanayin kyakykyawar ta sa


"Idan kin amince zamu iya yin hakan a rubuce saboda ki tabbatar da abinda na fad'a gaskiya ne, wato dae ina nufin zamu yi auren yarjejeniyar yini d'aya ne!!" ya fad'a dan cikin ran sa ya shiryawa kowanne irin k'alubale daze biyo bayan auren ta da yayi, baya jin ko d'arr akan abinda ya aekata d'in ko da zasu dawwama ne cikin auren sirri hakan ba damuwar sa bace, dan kuwa daya rasa ta gwara ya jurewa kowanne kalar abu daze tunkaro shi komae zafin sa kuwa...


End of ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER ONE)

In Sha Allah zamu d'ora da ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER TWO) nan da kwana 2 idan na huta, shima FREE ne duk dan jin dad'in ku 🤗😍

Dan neman qarin bayani se a tuntu6e ni ta 08124818273



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 031



___Manyan fararen idanun ta da colour d'in su ya sauya ta d'aga ta zube su a kan sa sanda yake maganar, ta cigaba da saurarar sa tana nazarin kowacce kalma da yake fad'a, sosae k'irjin ta ke mata wani irin suya yana zafi, seta shiga jera ajiyar zuciya kafin ta durk'ushe a wajen tana sakin wani marayan kuka na rashin sanin abinyi, a hankali kukan da take yake fita idanun ta a lumshe haka zalika zuciyar ta na cigaba da zafi, daga inda yake ya runtse idanun sa yana jin kukan nata har cikin jikin sa, seya sauke wata ajiyar zuciya yana d'auke kae daga inda take durk'ushe, ya zama dole ya koyi wofantar da al'amuran ta ko dan saboda wannan kasadar da yake neman aekatawa, idan ba haka ba tabbas ze koma shine me laefin ba wasu ba, duk da yadda kukan nata ke ratsa shi hakan be hana shi sake kicin kicin da fuskar sa ba, ba zaka ta6a gane menene a cikin zuciyar sa ba yadda kyakykyawar fuskar sa take babu annuri se ka d'auka haka ne a cikin ran sa ma, hannayen sa ya d'auka duka ya sak'ale su a k'irjin sa kafin ya d'an lumshe idanun sa kana ya bud'e su yace a hankali

"Kuka bashi da amfani, ina ga gwara ki mik'e mu ida wannan aekin" ya d'an yi shiru bayan ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da fad'in

"Wannan mutumin ya d'auko ki ne dan a d'aura muku aure dashi na dindindin, shiyasa ni kuma zan k'wace ki daga tarkon sa da kike k'ok'arin fad'awa..." da ya kae k'arshen maganar seya sake dakatawa yana cigaba da nazarin ta, sanda ta dena kukan se sheshshek'a da take yi kan ta har lokacin na kan gwuiwar ta, se a lokacin ta saka hannun ta ta share hawayen da suka k'i tsayawa da zuba a fuskar ta tace cikin raunanniyar murya

"Idan da gaske taemako na zaka yi toh ka kira min Abba na, ko kuma ka maeda ni gidan mu saboda bana son ganin ka" tsayawa yayi ya cigaba da kallan ta yanda take maganar bilhak'k'i da gaskiyar ta, shi har yanzu idan tana wani abun mamaki take bashi, meyasa ta fishi d'aukar zafi haka? Meyasa duk da abinda Abban ta yayi wa Abbun sa besa ya guje ta ba se ita? Meyasa take abu kamar da mak'iyin ta take tare? Meyasa ta chanja lokaci d'aya? Lumshe idanun sa yayi yana hana yanda ran sa ke neman 6aci tasiri, sosae zuciyar sa ke masa zafi na maganganun ta amma ya daure ya sake runtse idanun sa na tsawon sakanni sannan ya bud'e su a kan ta sanda suka yi wani ja kamar wanda abu ya zubar wa cikin ido, seya maeda kallan sa kan ta sannan yace sanda bugun zuciyar sa ke cigaba da k'aruwa

"Wannan shine abinda kike so na miki? Ki sani ba zaki ta6a barin garin nan babu aure akan ki ba, ko dae ki bari ki auri wancan mutumin ko kuma ki amince da aure na na Contract, The choice is yours.." yayi maganar yana lumshe idanun sa kafin ya d'ora da fad'in

"Idan kuma kina tunanin abinda kike tunani shine mafita.. well.. se kije ki samu wad'anda suka sato ki dan a d'aura miki aure da d'aya daga cikin su kice su baki waya ki kira Abban ki..." ya k'are maganar da wani irin murmushin takaeci daya fice daga gefen bakin sa, daga haka ya juya yana shirin ficewa daga soron, bata san sanda ta mik'e da wani irin sauri ba se kawae tsintar hannun sa yayi cikin nata, ya dakata lokaci d'aya yana lumshe idanun sa lokaci d'aya kuma yana jin yanda jikin sa ya amsa, se kuma ta sake shi kafin kamar zata fashe da kuka ta furta

"Na amince!!" ta fad'a dae_dae lokacin da wani kuka me sauti ya k'wace mata, seda ya sake runtse idanun sa kafin ya juyo inda take, ya sanya hannun sa cikin aljihu ya fiddo da wata takadda da biro sannan ya mik'a mata ba tare daya dubi kukan da take yi kamar ran ta ze fita ba

"Ki saka hannu!" ya fad'a yana mik'a mata, kamar ba zata d'ago ba se kuma a hankali ta fara rage sautin kukan nata sannan ta sanya hannu ta kar6a, sosae bugun zuciyar ta ke k'aruwa ta kar6i takaddar daya mik'a mata, tsayawa tayi kawae tana kallan takaddar kamar me karatu ko me nazarin abinda ke cikin takaddar, hawayen da yak'i tsayawa a idanun ta se sauka yake akan takaddar, wajen minti 1 tayi a hakan da dae ta fahimci bata da wata mafita se kawae ta d'aga biron ta d'ora shi kan takaddar, duk da yadda hannun ta ke rawa hakan be sata dakatawa ba se da tayi signature sannan ta jefar da takaddar daga hannun ta tana runtse idanun ta, bata jira ta sake jin komae daga bakin sa ba ta mik'e ta fara takawa a hankali saboda jirin dake d'ibar ta, hakan ne ya sanya ta yin layi kamar wadda tayi maye, bin bayan ta yayi da kallo sanda ta 6acewa ganin sa daga inda yake yana jiyo sheshshek'ar kukan ta, ya kae minti d'aya a hakan kamar wanda aka sassak'a sannan ya lumshe idanun sa ya saka hannu ya d'auki takaddar kana ya fice daga soron. Kae tsaye cikin motar sa ya koma ya jinginar da kan sa akan kujerar daya kwantar da ita, idanun sa a lumshe zuciyar sa na harbawa da k'arfin gaske, hannun sa dake d'auke da takaddar ya rufe ta a cikin hannun nasa kamar wanda ze yaga takaddar, se kuma ya bud'e hannun yana sauke numfashi a hankali, wayar sa dake ajje kan kujera ce tayi ringing, se a lokacin ya bud'e lumsassun idanun sa ya d'ora akan wayar

"Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seya maeda idanun sa kawae ya rufe yana cigaba da sauke numfashi akae akae, be d'aga wayar ba har ta gaji dan kan ta ta dena ringing d'in sannan ya janyo ta ya kashe ta gaba d'aya, gaba d'aya zuciyar sa a dame take yanzu haka, ya rasa ma meya kamata yayi, baya tunanin koya d'aga wayar ma ze iya cewa wani abun, dan haka k'in d'agawar kawae shine mafita.



... B'angaren Ayrah kuwa a tsakar d'akin ta zube tana sakin wani gigitaccen kuka me tsuma zuciyar me sauraro, zuciyar ta gaba d'aya a cunkushe take, ta rasa abinda zatayi, ta rasa tunanin daya kamata tayi, abinda ta sani kawae shine yanda zuciyar ta ke bugawa kamar zata faso k'irjin ta ta fito, ta kae fiye da minti 30 tana kukan sannan ta fara sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma tana neman kan wani d'an madaedaecin gado dake cikin d'akin ta d'ora kan ta akae cikin rashin sanin abinyi.


... "Yalla6ae kayi hak'uri ka zauna mu samo mafita" Muttala ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya kasa zama, idanun nan nasa sun sake ja kamar garwashi, haka zalika bak'ar fuskar sa ta sake had'ewa cikin rashin walwala

"Waye shi? Wanene uban shi? Me yake tak'ama dashi? Ya akayi yasan da plan d'in mu? Ya akayi ya biyo mu cikin garin nan?" shine abinda Alhaji Maton ya fad'a a zafafe

"Ka kwantar da hankalin ka Yalla6ae, zuwa gobe zan bincika maka waye shi" wani banzan kallo Alhaji Mato ya watsawa Muttala kafin yace

"Muna da wannan lokacin? Tambayar ka nake muna dashi?" ya k'are maganar yana kallan sa, shiru Muttala yayi yana sake tunanin wata mafitar, hakan ya sake bawa Alhaji Mato damar yin shiru shima yana nazarin abinda ya kamata yayi kafin goben

"Ya shiga gona ta, bazan k'yale shi ba wallahi, yana so yayi wasa dani, ba zeji da dad'i ba, Muttala asan yadda za'ayi a gama mun dashi kafin goben, shi kad'ae ne matsala ta a yanzun.." Alhaji Mato ya k'are maganar yana kallan Muttala

"An gama ranka ya dad'e"






.... Washe_gari da safe wajen k'arfe 8 tana zaune kan dadduma kamar maraeniyar data rasa uwa da uba, manyan idanun nan nata sun sake yin zuru zuru, ga yunwar da take ji amma saboda tashin hankalin da take ji ta kasa kae koda ruwa ne cikin bakin ta, haka nan kawae take zaune, ita ba Azumi ba ita ba cin abinci ba, idan ka gan ta seta baka tausayi musamman yadda har lokacin hawaye be bar zuba akan kuncin ta ba duk da yadda ta dena kukan amma hakan be hana hawayen zuba ba, ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciya, k'wak'walwa da gangar jikin ta, tana nan zaune gaba d'aya bata a hayyacin ta kamar wadda ta zare, ta tsaya ta k'urawa waje d'aya idanu se kuma hawayen dake sauka akan fuskar ta. Babu dad'ewa aka turo k'ofar d'akin, bata damu dame shigowar ba dan ita wannan sam ba damuwar ta bace, wadda ta shigo ta k'arasa ta ajiye abincin data shigo dashi, duk da ganin abincin data kawo jiya duk suna ajiye bata ce komae ba ta fice daga d'akin tunda dae ta gama aekin ta.


.... Wajen k'arfe 1pm aka sake shigowa d'akin, har lokacin dae tana zaune a wajen yanzu kam ko hawayen ma sun gaji da zuba, tayi shiru kawae tana jiran taga yadda Allah zeyi da ita, yanzu wata matar ce ta shigo daban ta kalle ta sannan tace

"Baba na kira!" sam bata ji ta ba dan kuwa bata tare da ita, hankalin ta da tunanin ta gaba d'aya suna ta wani wajen ne, ganin da matar tayi kamar bata tare da ita ne ya sanya ta k'arasawa gaban Ayrah ta tsuguna sannan tace

"Baba na kiran ki" firgigit ta lumshe idanun ta sannan ta bud'e da sauri lokaci d'aya kuma k'irjin ta na bugawa, seta kalli matar dan har lokacin bata san aenahin abinda ta fad'a d'in ba, seda ta sake maemaetawa sannan kawae ta mik'e tana gyara zaman hijab d'in ta kan doguwar rigar da aka bata ta saka wadda take over size dan kuwa yawo take a cikin ta, lumshe idanun ta tayi bayan ta mik'e d'in sanda taji wani irin jiri na neman kada ta, a hankali ta kama kan ta tana sake rufe idanun ta, a haka dae suka cigaba da tafiya ba dan tana gane inda suke zuwa d'in ba. Cikin wani d'aki me madaedaecin kyau, ehh zamu iya kiran sa madaedaeci musamman idan muka yi duba da gidajen cikin k'auyen, dan kuwa wannan d'in shimfid'e yake da manyan tabarmi masu kyau, da kuma wata k'aramar kujera wadda Me gari ke zaune a kae, sam bata san wad'anda ke cikin d'akin ba dan idanun ta da kan su suke lumshewa ga kan ta daya cigaba da sarawa, Me gari yayi gyaran murya sannan ya fara magana a nutse

"Kin yanke hukuncin wanda kika za6a a matsayin mijin ki?" ya jefawa Ayrah tambayar, seda matar nan ta d'an ta6a ta dae_dae lokacin da kan ta ya sake sarawa, a hankali ta sanya k'aramin red lips d'in ta na k'asa cikin bakin ta ta cija tana jin yadda ya bushe musamman saboda ruwan daya dad'e be shiga cikin bakin ba, d'aga ido Alhaji Mato yayi ya kalli inda Ayrah ke zaune, be ta6a tunanin tun yanzu Me gari ze kira su yayi tambayar k'arshe ba, gashi yayi sake saurayin na nan be kae gayi masa komae ba, meya kamata yayi a yanzu?

"Ranka ya dad'e ina ganin kawae a bani ita zan maeda ta gidan su!" Alhaji Mato ya fad'a yana kallan Me gari, d'aga kyawawan idanun sa Rk yayi ya sauke su kan Alhaji Mato, kafin a hankali ya saki wani miskilin murmushi, dama seda yayi tunanin hakan zata kasance, shiyasa ya maza yayi wa tufkar hanci, girgiza kae Me gari yayi yana tuna maganar da suka yi da Rk, lallae shima yayi wannan tunanin, ze iya yiwuwa Alhaji Maton be yadda da wannan hukuncin ba ya d'auki Ayrah su tafi wani wajen a d'aura musu aure

"Kace kuma ba anan garin iyayen ta suke ba?" cikin in'ina Alhaji Mato yace cike da danasanin abinda ya fad'a d'in

"Ehh.. Ehh.. Ranka ya dad'e" jinjina kae Me gari yayi kana yace a nutse

"Yanzu ba matar ka bace, shima ba matar sa bace saboda haka baze yiwu a had'a ku ku tafi a haka ba, dan haka kamar yanda muka saba, zan d'aura mata aure da wanda ta za6a, shi seya d'auke ta su koma gidan... Kae sake gwada layin nan muji" Me gari ya k'arasa maganar yana kallan wani dake gefen sa, seya fiddo da waya daga cikin aljihun sa ya sake danna wata number ya kira, kira wajen 3 number daya kira bata shiga ba, ya kalli Me gari yace

"Yalla6ae kamar jiyan dae yau ma bata shiga" ya fad'a cike da ladabi, gyaran murya Me gari yayi sannan yace

"Babu matsala, zamu yi abinda ya dace.. Cikin su biyun wa kika za6a?" Me gari ya k'are maganar yana kallan Ayrah

"Raj!" ta furta ba tare data kalli kowa ba, ba kuma tare data bud'e idanun ta ba, har kuma lokacin hannun ta na dafe da kan ta ne daya cigaba da sara mata, daga inda yake ya lumshe idanun sa yana cigaba da kallan inda take kan ta a k'asa haka zalika idanun ta a rufe

"Toh madallah, idan an idar da Sallahr azahar ni da kae na zan d'aura auren nan, Allah yasa albarka" Me gari ya fad'a, huci Alhaji Mato ke fitarwa daga bakin sa zuciyar sa na cigaba da tafarfasa, shi kad'ae yasan abinda ze yiwa Rk, dan ya riga yaci alwashin baze ta6a barin sa yaci bulus ba, baze ta6a k'yale shi ba, baze ta6a rangwanta masa ba. Matar nan ce dae ta kamata ta mata jagora zuwa cikin gidan, a lokacin kawae zubewa tayi akan gadon, daga kukan har hawayen yanzu babu ko d'aya dake fita, kawae ta cigaba da kwanciyar ne cikin rashin sanin abinyi, kuma cikin rashin sanin mafita, se a lokacin ta tsaya tayi tunani, shin wanene wannan mutumin? Meyasa ya sato ta daga gidan su? Meyasa yake son auren ta bayan ita ko sanin sa bata yi ba? Meyasa ya rabo ta da gidan su? Meyasa beje ya nemi auren ta wajen Abban ta ba kamar yanda Addini ya tanadar? Meyasa yake son neman auren ta ta wannan sigar? So take ta tabbatarwa da kan ta amincewa auren Rk da tayi ba kuskure bane amma hakan ya citira, kawae ji take kamar ta tafka wani babban kuskure ne auren sa data amince zata yi, nan take kuma wani tunanin ya fad'o mata

"Auren kwangila ne ae, kwangilar ma ta yini d'aya, daga zarar ya sawwak'e miki babu wanda ze san kin aure shi, taemakon ki yayi ba komae ba..." abinda zuciyar ta keta sak'a mata kenan amma har yanzu ta kasa yafewa kan ta, musamman idan ta tuna Abban ta, ta tuna irin amincewar da yayi wa su Raj amma suka ci amanar sa, ta tuna yanda yace ba zata auri Rk d'in ba amma yanzu idan suka ji labarin ta aure shi na yini d'aya fa?

"In har kin so baza suji labarin ba" abinda ta sake sak'awa kenan a cikin ran ta, se kawae ta lumshe idanun ta tana sake dafe kan ta da dukkan hannayen ta.






... Har aka idar da Sallah yana cikin masallaci, ya kasa motsawa ko nan da can ne, idanun sa a lumshe suke tunani barkatae na yawo cikin k'wak'walwar sa, tun jiyan nan daya kashe wayar sa be sake kunnawa ba dan baya son a kira shi ko kad'an. K'arfe 2:25 mutanen dake cikin masallacin suka shaeda d'aurin auren RAJ KABEER da AYRAH IBRAHEEM KHALEEL akan sadaki mafi k'ank'anta wato mafi alkhaeri..




Mhiz Innocent.....✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 032


___Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa ilahirin jikin sa lokacin da yaji zancen d'aurin auren, a hankali ya lumshe idanun sa, se dae ga mamakin sa sosae bugun zuciyar sa ya k'aru, seya dakata yana tuna kasadar da yayi da kuma k'alubalen da yasan dole seya tunkaro shi, amma tunda dae ya gama da wannan koma wanne k'alubale ne yana ganin me sauk'i ne, a hankali kuma se yaji wani rauni na son shigar sa, cikin sakannin da basu gaza 2 ba ya bud'e manyan idanun sa da hakan yasa zaka iya fahimtar yadda yanayin fuskar sa take, sosae annuri ke fita daga kyakykyawar fuskar sa, seya fesar da iska daga bakin sa sannan ya cigaba da kar6ar hannun mutane dake mik'a masa suna gaesawa, wasu da gasken dan taya murna ne suke mik'a masa hannun su gaesa yayin da wasu suna so ne kawae su gaesa da shi d'in saboda yadda yake, d'an birni, had'ad'd'e kuma kyakykyawa, kwata kwata baya lura da yanayin mutum kawae ze mik'a tattausan hannun sa ne su gaesa duk da ba kallan fuskar mutanen yake ba.



... Ayrah na cikin gida sam bata san abinda ke faruwa ba, ita gaba d'aya tana jin komae ne kamar a mafarki ko kuma wani wasan film, dan haka ta gaza amincewa kan ta wannan abinda yake faruwa gaskiya ne, a yanda tafi d'auka wani mummunan mafarki ne take yi wanda yake nuni da tana neman bijirewa maganar Abban ta, dan haka take fatan tayi maza ta farka daga baccin, se dae me? Har yanzun tak'i farkawa, tun tana cigaba da yadda mafarkin ne har tazo ta fara tunanin shin ko gasken ne? Duk abinda ke faruwa a yanzun da gaske ne? Ba ita ta tashi daga kwancen da take ba seda taji ana kiran sallah, a hankali ta fara k'ok'arin mik'ewa se dae jirin daya kwashe ta ta sanya ta saurin komawa ta kwanta tana sakin wani kuka, ita kad'ae tasan abinda take ji a jikin ta, ita kad'ae tasan yanda take jin kan ta da gangar jikin ta, gaba d'aya jin kan ta take yi ya mata wani gingirin kamar ba'a jikin ta yake ba, ga jikin ta da gaba d'aya ta rasa gane a wane yanayi ma zata saka shi, ta kae wajen minti 1 a kwancen seda jirin ya d'an yi sauk'i sannan ta mik'e duk da yanda take kallan abinci da ruwa a ajiye hakan be sanya tabi ta kan su ba, kae tsaye ta fice daga cikin d'akin zuwa ban d'akin dake kusa da d'akin da take ciki, alwala kawae tayi ta dawo cikin d'akin ta tada sallah.



... "Toh kae Allah ya baku zaman lafiya, Alhaji Mato kuma Allah ya baka hak'uri, dama kasan ance ba komae ne idan aka rasa ake kuma samun sa ba, Allah ya musanya maka da wadda ta fi ta" Me gari ya fad'a yana kallan su su duka

"Ameen ranka ya dad'e, Allah ya k'ara girma" Rk ya fad'a ba tare daya d'aga ido ya kalli Alhaji Mato dake jifan sa da wani kallo na gargad'i da kallan nan irin na zaka sani, Alhaji Mato be iya cewa komae ba saboda yasan idan ya bud'e baki komae ka iya fitowa daga bakin sa, k'ila ma yayi maganar da zata iya tona masa asiri a cikin k'auyen, dan haka yaga shirun nasa yafi masa alkhaeri

"Ayi mata magana ta fito se ku tafi koh?" Me gari ya fad'a yana kallan Rk, jinjina kae Rk yayi lokaci d'aya yana lumshe idanun sa se kuma ya bud'e bakin sa a nutse ya furta

"Ehh" babu 6ata lokaci Me gari ya aeka wani daga cikin yaran sa zuwa cikin gidan cewar a fito da Ayrah.


... Lokacin da matar nan ta sake shigowa cikin d'akin da k'yar take iya bud'e narkakkun idanun ta da suke wani lumshewa da kan su kamar er maye, sanyi sosae take ji a jikin ta wanda hakan ya sanya ta takurewa cikin hijab d'in ta tana jin kamar k'asusuwan ta zasu tsage, ciwon da kan ta yake yi kuwa se abinda yayi gaba, gaba d'aya jikin ta yayi wani irin tsami

"Ki taso zaku tafi" maganar da taji matar tayi ya sanya tilas ta bud'e lumsassun idanun ta ta jefa su kan matar da take gani biyu biyu, ta d'auka ma ba taji abinda tace ba dan haka ta sake maemaetawa a karo na biyu, a hankali ta zura k'afar ta daga kan gadon da take, tilas ta sake runtse idanun ta saboda yadda taji kamar ginin gidan gaba d'aya ze fad'o a kan ta, bata so ma wasu su fahimci bata da lafiyar ballantana ace za'a d'aga tafiyar tasu, burin ta d'aya kawae ta bud'e idanun ta ta gan ta cikin gidan su, gata ga Umman ta, ga Abban ta ga kuma Yah Sadeeq d'in ta, seda matar tayi gaba sannan ta mik'e tabi bayan ta a nutse tana tafiya tana dafa bango saboda kada ta fad'i, sosae tayi da gaske dan kada ta zube kafin ta isa wajen, cike da k'arfin hali ta cigaba da takawa har zuwa wajen Me garin. Bin ta yayi da kallo sanda ta zube a k'asa idanun ta a lumshe, daga yanayin yadda ta zauna d'in kawae zaka fahimci ba'a lafiyar ta take ba

"Toh yanzu dae zamu damk'aki hannun mijin ki, Allah ya bada zaman lafiya" shine abinda ta tsinto Me garin na fad'a, ta sake lumshe idanun ta a karo na barkatae tana jin wani irin yanayi, kenan da gaske an d'aura mata aure da Raj? da Me gari yasan tashin hankalin da take ciki tabbas da baze ambaci Rk a matsayin mijin ta ba, daga lokacin da aka fad'i hakan tana sake jin kan ta ne dumu_dumu a mae laefi, wadda ta bijirewa umarnin iyayen ta, se dae tasan wannan d'in bame yiwuwa bane, kwangila ce suka k'ulla tsakanin ta da Rk d'in kuma nan da anjima zata k'are, dan haka wannan d'in kamar wani wasan kwaekwayo ne aka gabatar dashi cikin k'auyen. Sosae Rk yayi wa Me gari godiya sannan ya mik'e yana kallan er rigimar tasa, be san yanda zasu k'arke ba, be san kuma meze faru anan gaba ba

"A'ah ba dae tafiya ba?" Me gari ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya mik'e shima, dan so yake ya fara yin gaba kafin Rk ya riga shi, dan kuwa tun kafin ya isa gida yake so ya gama dashi, se dae da alama Me garin na son jik'a masa aeki

"Ehh.. A'ah.." Alhajin Maton ya fad'a cikin inda inda yana komawa ya zauna

"Yawwah koda naji, ae ka zauna muyi hira koh?" bece komae ba dan a yadda yake ji ze iya sussurfawa Me garin zagi ne

"Allah ya tsare" Me gari ya sake bin Rk da addu'ar sanda ya k'arasa dab da ita, ya rasa yanda zeyi ya mata magana, mik'ewar da tayi ne ya sanya shi d'an lumshe idanun sa sannan yayi gaba yayinda ta bishi a baya hannun ta rik'e da kan ta da har lokacin be bar sara mata ba, hannu ya saka ya bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza, zata iya cewa ta fishi k'aguwa su bar k'auyen nan ko dan a warware wannan auren wasan sannan ta tafi gidan su, uwa uba kuma ga yadda take ji a yanzun koda wane lokaci zata iya zubewa idan bata nemi wajen zama ba, dan haka babu musu ta shige cikin motar ta kwantar da kan ta tana sakin wata ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma kan ta na sake juya mata ta fara ganin ko ina na juya mata, sam be lura da yanayin da take ciki ba ya koma

Please Login or Register in order to submit comment