Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigo cikin gidan kuma idanun ta suka fara sauka akan Umma, da gudu ta k'arasa bata yi wata wata ba ta rungume ta tana fashewa da wani kuka me tsuma zuciyar me sauraro, lumshe idanu Umma tayi sanda Ayrahn ta rungume ta, lokaci d'aya taji zuciyar ta ta wani irin karyewa, babu 6ata lokaci itama ta rungume d'iyar ta ta, tana hana kan ta yin kuka kada su had'u su zama su biyu, Abba da Yah Sadeeq kallan su kawae suke yi babu wanda ya iya cewa komae har zuwa sanda Ayrah ta gaji da kukan ta soma durk'ushewa akan k'afafun ta, rik'o ta Umma tayi kafin ta kae k'asan se suka k'arasa zubewa a k'asan, a hankali taja sheshshek'ar kuka sannan tace

"Umma!!" kallan ta Umma tayi kamar me son gano gaskiyar al'amari daga cikin idanun Ayrahn, idan ta tuna yanda Ayrahn ta fice daga gidan ba tare da izinin su ba se taji kamar ta sake ta ta tashi tayi tafiyar ta, amma kuma ta rasa dalilin da yasa ta kasa aekata hakan, bata amsa kiran da Ayrahn ta mata ba har zuwa sanda Ayrahn ta kalli Abba da har lokacin kallan ta yake tace

"Abba na!"

"Daga ina kike?" shine abinda ya fara fitowa daga bakin Abba yana tsare ta da idanu, seda ta d'an lumshe idanu nan take k'irjin ta ya soma bugawa idan ta tuna abinda ze fito daga bakin na ta, ba tare da tunanin komae ba ba kuma tare da tsayawa dogon nazari ba ta furta

"Abba ban san daga inda zan fara ba Umma wani cukurkudad'd'en al'amari ne Umma" ta k'arasa maganar tana kallan Umma, dukkan su zuba mata ido suka yi suna kallan ta musamman Yah Sadeeq dake karanto zallar gaskiya a tattare da k'anwar ta sa amma duk da haka bece komae ba, ganin da tayi duk suna kallan ta ya sanya ta cigaba da fad'in

"Umma yanzu haka an d'aura mana aure da Raj fa!" ta k'arasa fad'a tana jin wani zafi da ciwo a cikin zuciyar ta musamman yanzu data tuna a gaban Abba ne kuma laefin da aka yiwa Abba ne ya sanya yace ba zata aure shi ba, da wani irin sauri Umma ta saki Ayrah dake jikin ta sannan ta soma matsawa gefe har lokacin idanun ta akan Ayrahn k'irjin ta kuma still yana bugawa da k'arfin daya wuce na d'azu, Abba da Yah Sadeeq suma duka kallan ta suke yi kafin Abba ya girgiza kae yana d'auke kae wani murmushin takaeci me ciwo na su6uce masa, shi kan sa ji yake daze iya kuka da yayi koda abinda yake ji cikin zuciyar sa ze ragu, ya d'auki sakanni masu yawa a hakan sannan ya juyo yana cigaba da kallan Ayrahn dake share hawayen fuskar ta

"Ashe zargin da muke gaskiya ne Ayrah? Bama iya za6ar namiji ki kayi akan mu ba? Kin je kin auri abinda zuciyar ki ke so acan wani wajen? Bama iya guduwa kika yi ba Ayrah? Hadda aure ku kayi? Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" Abba ya fad'a yana sauke numfashi saboda yadda k'irjin sa ya masa wani irin nauyi sannan a hankali ya zame a wajen ya kwanta ko zeji sauk'in abinda yake ji, se a lokacin hawayen da suka taru a cikin idanun Umma suka zubo cike da takaeci ta furta

"Ayrah kin cuce mu kin cuci kan ki, kin wulak'anta mu kin wulak'anta kan ki, kin tozarta mu kin tozarta kan ki tunda har kika iya d'aukar jiki kika bi saurayi kuka tafi wani wajen aka d'aura muku aure saboda iyayen ki sun ce basa son shi, meyasa kika yi haka Ayrah?" Umma ta k'arasa fad'a wasu zafafan hawaye suna zuba akan fuskar ta, Yah Sadeeq dake gefe kawae kallan su yake yi su duka musamman Ayrah da yaga ta rikice daga kallan daya mata tun farkon lokacin da Abba ya fara magana, a hankali ta shiga girgiza kae k'irjin ta na wani irin bugawa idanun ta da suka cika taff da hawaye har wani dishi_dishi suke gani, cikin kuka ta kalli Umma tana girgiza kae tace

"Umma ku yafe min don Allah, Umma nayi nadamar zuwa na duniya, ni banza ce kuma shashasha Umma, Umma ku tsaya inyi muku bayanin abinda ya faru don Allah.. wallahi.." d'aga mata hannu Abba yayi daga inda yake kwance dafe da saetin zuciyar sa yace

"Ki tashi ki fita a gidan nan, bana son na sake ganin ki cikin gidan nan, kin za6i d'a namiji akan mu saboda haka kije duniya ce ae.." sake fashewa da kuka tayi a cikin ranta tana maemaeta kalmar "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shin me yake shirin faruwa ne? A cikin su babu wanda ze tsaya ya saurare ta tayi musu cikakken bayani

"Umma bani da laefi" ta fad'a cikin kuka, ba tare da Umma ta kalle ta ba tana jin wani iri cikin ranta, tana jin danasanin haehuwar 'ya irin ta, data san idan tazo duniya zata bijirewa umarnin su ta aekata wannan mummunan abun da har su mutu ba za'a bar yin gulmar su da hakan ba da tun farko tayi addu'ar Allah yasa cikin ya zube

"Ki tashi ki fita a gidan nan bana son sake ganin ki, idan kuma na sake ganin k'afar ki cikin gidan nan sena tsine miki.." Umman ta k'arasa fad'a tana gyarawa Abba kwanciya lokaci guda kuma tana goge hawayen da suka k'i tsayawa da zuba akan fuskar ta, runtse idanun ta tayi hawaye sunk'i dena zuba daga idanun ta

"Allah ka d'au raena na huta da wannan bala'in.." ta fad'a tana jin yadda ilahirin jikin ta ke rawa kamar mazari, kallan ta Umma ta sake yi tana shirin cewa wani abun seta mik'e da sauri, bata so Umman ta sake furta wata kalma mara dad'i a kan ta dan haka ta mik'e duk da yanda take jin jiri na d'ibar ta amma haka ta tashi bata ko ganin gaban ta ta fito daga cikin gidan..Tafiya kawae take yi ba tare da tana sanin inda take jefa k'afafun ta ba, hawaye ne ke ta sintiri akan kuncin ta, Raj ya cuce ta, ya cuci rayuwar ta, ya yaudare ta da kalaman bakin sa daga k'arshe ya raba ta da iyayen ta, ya sanya bata da wani 'yanci ta koma k'ark'ashin sa akan wani son zuciya nasa, meyasa dangin su duka suka kasance masu son zuciya? Meyasa Raj zeyi mata haka? tunda take bata ta6a tunanin soyayya na komawa k'iyayya ba, sedae yau gata dumu dumu cikin matsananciyar k'iyayyar Raj wadda bata san adadin ta ba, wadda ke ruruwa yanzun a cikin zuciyar ta saboda abinda ya aekata mata, bata jin a yanzu a fad'in duniyar nan akwae wanda ta tsana kamar shi, dan kuwa duk mutumin daze raba ta da iyayen ta mak'iyin ta ne, kamar daga sama ta jiyo muryar sa daga gefen ta

"Muje ki huta da kae na zan zo na musu bayani" ya fad'a a nutse, wani banzan kallo ta d'aga fusatattun idanun ta ta watsa masa tana jin yadda zuciyar ta ke cigaba da mata zafi, bata jin a yanzu zata iya masa magana, ko da kuma ta bud'e baki da niyyar yin magana to tasan kalaman da zasu fita daga bakin ta masu zafi ne zuwa ga wanda za'a fad'awa, dan haka ta cigaba da tafiya ba tare data d'auki wani mataki akan hawayen dake ta zuba daga idanun ta ba, ya san yanzu ran ta a 6ace yake kuma ko ze mutu baza ta kula shi ba ballantana ta shiga motar sa, dan haka ya kalli gefe da gefe sannan ya k'arasa a nutse zuwa inda take babu 6ata lokaci ya sanya hannun sa ya d'auke ta dukan ta, duka k'arfin ta ta saka tana k'ok'arin k'wace jikin ta dan ta sauka daga jikin sa amma ina yak'i bata damar hakan, sema k'arasawa da yayi ya bud'e front seat ya jefa ta ya kulle sannan ya koma mazaunin driver ya shiga shima ya kulle side d'in sa, hannun ta ta saka dan bud'e murfin k'ofar amma ta ji shi a rufe dan haka ta sanya hannun ta ta fara turawa nan ma ta kasa, kawae seta koma jikin kujerar tana fashewa da wani marayan kuka, daga inda yake ya d'an runtse idanun sa kukan nata na ratsa shi, amma a yadda yaga k'wayar idanun ta cike suke da fusatattun abubuwa ya sanya shi yi mata shiru ta cigaba da rera kukan ta kamar ran ta ze fita.


... Wajen minti 1 bayan ta fita babu wanda ya sake cewa komae, Yah Sadeeq ya lumshe idanun sa sannan ya fara magana a nutse

"Abba, Umma kada 6acin rae yasa ku man ta wacece Ayrah, Abba kada 6acin rae yasa ku aebata d'iyar da kuka haefa, Abba ina ji a jiki na akwae wani 6oyayyen al'amari dake faruwa wanda da zamu bawa Ayrah dama zata fad'e shi, amma Abba bamu bata ba, mun k'i bata wannan damar data nema, Abba Ayrah bata da wayo ko bud'ewar idon da zesa ta bi saurayi!" tashi zaune Abba yayi har lokacin hannun sa na d'ore akan k'irjin sa yace bayan ya girgiza kae

"Shin baka ji abinda ta fad'a bane Sadeeq? Tun ina k'ok'arin k'arya ta abinda muke zargi yau Ayrah da kan ta tazo ta tabbatar mana harda k'arin wani abun ma" Abban ya k'arasa fad'a yana kallan Yah Sadeeq

"Umma, Abba Ayrah ce fa, Umma Ayrah ce fa, kuna tunanin zata iya zuwa can wani waje tayi aure da wanda bakwa so? Ayrahn da kullum cikin son farin cikin ku take Umma?" shiru dukan su suka yi cikin nazarin abinda Yah Sadeeq d'in ya fad'a, kamar babu wanda ze tanka a cikin su se kuma Umma tace

"Ya akayi hakan ta faru kenan Sadeeq? Me kake so ka ce mana? Dukan mu ba'a son ran mu muke zargin Ayrah ba Sadeeq, babu yadda zamu yi ne, mu iyaye ne ta yaya zamu aebata d'iyar mu? Abinda take fad'a yanzu ya zama dole mu shiga rud'ani, ta bar gida bayan maganar hana ta auren yaron nan, yanzu kuma ta dawo tace tana d'auke da auren sa, Sadeeq ya kake so muyi?" seda yaja ajiyar zuciya sannan yace

"Umma, Abba don Allah mu bari naje na kira Ayrah tazo ta mana bayani, inaji a jiki na akwae wani abun.." ya fad'a har cikin ran sa yana jin abinda ya fad'a d'in, shiru na wajen minti 2 ya wanzu a wajen kowanne da abinda yake sak'awa a ran sa, se dae dukan su sun gamsu da zancen d'an nasu, a gefe guda kuma dukan su sun so su fahimci kamar sun yi laefi, k'in tsayawa suji abinda ze fito daga bakin Ayrahn, yanke mata hukunci tun kafin su san aenahin abinda ya faru, koma menene ya faru 6acin rae ne

"Je ka kira min d'iya ta!" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq lokaci guda kuma tana jin yadda wani nauyi dake k'irjin ta ya d'an ragu, seta saka hannu ta goge hawayen fuskar ta dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ya saki murmushi kana ya mik'e yana kallan Abba yace a hankali

"Abba in kira ta?" seda Abba ya runtse idanun sa sannan ya bud'e kawae ya jinjina kae, cike da farin ciki ya sanya k'afa ya fice daga cikin gidan yana d'an d'ingishi dan har lokacin k'afar ta sa bata ida warkewa ba.


... Dae_dae lokacin daya fito titi yayi dae_dae da lokacin daya hango Ayrahn cikin motar Rk, yana k'ok'arin k'arasawa wajen motar Rk ya tashi motar ya bar wajen, se yayi sauri ya tsaeda Napep ya sanar dashi yabi masa motar Rk d'in, babu musu me Napep d'in ya bi shi, dae_dae wani waje motar Rk d'in ta dakata wanda yafi kama da Hotel, Yah Sadeeq ya sauka ya biya me Napep d'in kud'in sa sannan ya cigaba da tafiya zuwa wajen motar. Saukowa Rk yayi daga driver seat ya zagaya zuwa wajen me zaman banza ya bud'e k'ofar yana kallan yanda take a cure waje d'aya, yanzu ta dena kukan se dae ita kad'ae tasan abinda take sak'awa a cikin zuciyar ta

"Don Allah ki fito!" ya fad'a cikin rarrashi, idan motar da take ciki ta d'aga kae ta kalle shi toh itama ta kalle shi

"Ayrah!" Yah Sadeeq ya fad'a sanda ya k'araso dab da motar, da wani irin sauri ta d'aga kan ta ba tare data shirya ba, nan take idanun ta suka sauka akan Yah Sadeeq, seda ta d'an lumshe idanun ta sannan ta bud'e dan tabbatar da Yah Sadeeq d'in ne ba gizo yake mata ba sannan ta sauko daga cikin motar a million ta k'arasa ta fad'a jikin Yah Sadeeq d'in tana sakin wani irin kuka, a hanzarce ya d'aga kan sa ya kalli wanda ta rungume d'in, ko wani be masa bayani ba ya fahimci wanene shi, amma me kuma ya kawo shi nan d'in? Shima Yah Sadeeq d'in rungume ta yayi yana jin yanda take kuka sosae, tana shirin fara magana duk dae cikin kukan yace

"Ya isa! Ki bari mu zauna, ina buk'atar jin gaskiyar al'amari, bana son k'arya Ayrah.." kamar wata k'adangaruwa ta shiga jinjina kae har lokacin tak'i sakin sa, d'aga idanun sa yayi ya kalli Rk da har lokacin yake tsaye se dae basu yake kalla ba yace

"Raj?" se a lokacin ya juyo ya kalle shi cike da mamakin yadda ya kama sunan sa, seya jinjina kae yana lumshe idanun sa, d'an murmushi kad'an Yah Sadeeq yayi kana ya furta

"Sad..."

"Sadeeq!" Rk ya k'arasa sunan yana nuna Yah Sadeeq

"Ehh" shine abinda Yah Sadeeq ya furta sannan ya d'ago Ayrah dake jikin sa ya rik'e hannayen ta kana yace

"Ina son magana da kae idan babu damuwa"

"Why not?" Rk ga fad'a bayan ya d'aga kafad'a

"Mu k'arasa can.." Rk ya fad'a yana nuna wani d'an madaedaecin waje dake d'auke da wasu kujeru masu kyau, babu wanda ya sake cewa komae cikin su Rk na gaba yayin da Yah Sadeeq ke a bayan sa suka cigaba da tafiya zuwa wajen, ita dae Ayrah babu abinda tace ta cigaba da rik'e hannun yayan ta dan tana ji kamar idan ta sake shi zata bud'e ido taga baya nan, a haka suka k'arasa wajen, Rk ne ya fara neman waje ya zauna sannan Yah Sadeeq ya zauna, ita dae Ayrah ko zaman ma kasawa tayi seda Yah Sadeeq ya kalle ta yace a hankali

"Ki zauna kin ji?" kamar bata san da wata halittar a wajen ba taja kujera ta zauna har lokacin idanun ta na kan Yah Sadeeq, shiru Rk yayi kawae yana jiran jin abinda Yah Sadeeq d'in zece, kamar ya sani kuwa seya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta

"Menene gaskiyar barin Ayrah gida don Allah? Menene gaskiyar auren ka da tace tana d'auke da shi a kan ta?" shiru ya d'an yi yana nazarin tambayar Yah Sadeeq d'in, kamar ba zece komae ba se kuma ya d'an lumshe manyan idanun sa sannan ya bud'e yana tunanin tsayin adadin maganar da zeyi, amma ya zama dole yayi ko dan hakan ze wanke Ayrah daga wajen iyayen ta, sannan kuma su yafe mata koda ze samu kan ta ta dawo asalin Ayrahn sa, a hankali ya shiga labartawa Yah Sadeeq abinda ya faru, duk wani abu daya sani seda ya fad'a masa, yana kaewa k'arshe yayi shiru yana d'an aje numfashi kad'an, shiru Yah Sadeeq yayi tun lokacin da Rk d'in ya fara bashi labari, mamaki, tsoro gami da al'ajabin wannan al'amari yak'i barin sa, ya rasa ma me zece kwata kwata, ya rasa ma wane tunani ya kamata yayi, abin ya bashi tsoro da mamaki aenun, a hankali ya dubi inda Ayrah take zaune duk tayi wani iri da ita kamar ba Ayrah ta asali ba, se yaji wani matsananincin tausayin ta ya mamaye shi, Allah sarki baewar Allah, ashe dae Ayrahn er halak ce, ta haefu cikin Umma da Abba, tana k'aunar farin cikin Abban ta dana Umman ta haka zalika kuma tana k'in abinda basa so, tunda gashi nan duk irin yawan k'aunar da take wa Raj daga ji iyayen ta basa son shi itama ta sauya masa

"Amma pls ko zan iya sanin dalilin Abba na cewa bazan auri Ayrah ba?" tambayar data katsewa Yah Sadeeq tunani kenan, seya d'aga ido ya kalli Rk sannan ya girgiza kae yana kallan sa har lokacin yace

"Kada ka nuna kamar wani baka sani ba mana!" iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace

"Wallahi ban sani ba!" ya fad'a dan ya cire duk wani kokwanto dake tattare da Yah Sadeeq d'in, shiru Yah Sadeeq yayi na en wasu sakanni, sam bega amfanin 6oyewar ba gwara ma ya fad'a masa ya sani d'in kada ya zaci haka kurum za'a hana shi auren ta ne bayan tana son shi yana son ta

"Mahaefin ka.." Yah Sadeeq ya fad'a masa duk abinda ya faru kamar yadda ya sani, tun daga lokacin da suka zo hawa mota da kuma sanda suka dawo Kano, daskarewa Rk yayi akan kujerar da yake zaune yana cigaba da kallan Yah Sadeeq kamar wani sak'ago ko kuma wani mara wayo, anya kuwa Yah Sadeeq d'in yasan abinda ke fitowa daga cikin bakin sa? Shin me yake k'ok'arin cewa Abbun sa ya aekata? Anya kuwa ba ya fad'i hakan bane dan ya kawar dashi daga kan k'anwar tasa ba? A hankali ya shiga tariyo abinda Abbu ya fad'a masa da kuma wannan maganar da Yah Sadeeq d'in ke fad'a masa, seya shiga had'a su waje d'aya yaga ko iri d'aya ce, shin zasu zauna a mizani d'aya? Se dae ina, kwata kwata ba iri d'aya bace, sam babu ma ta inda suka had'u ko kad'an, toh kenan me yake faruwa??



Mhiz Innocent.....✍️

https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 036


___Ya d'auki wajen mintina 2 a haka, zuciyar sa a matuk'ar cunkushe, gaba d'aya ya rasa meke masa dad'i, duka tunanin sa ya tafi ne wajen tunanin menene gaskiyar abinda yake fitowa daga bakin Yah Sadeeq, shin me ya kamata ya amince da shi? Maganar Abbun sa ko kuma maganar Yah Sadeeq d'in? Iska me zafi ya fesar daga cikin bakin sa lokaci d'aya yana lumshe idanun sa, har lokacin kuma yana jin yanda zuciyar sa ke ta azalzalar sa

"Yah Sadeeq ka tashi muje wajen su Abba" shine abinda Ayrah ta fad'a tana d'an jan hannun Yah Sadeeq d'in, kallan ta yayi sannan yace a nutse

"Ina zuwa, yanzun zamu tafi.." ya k'are maganar yana maeda duban sa kan Rk da har lokacin ya gaza furta ko kalma d'aya, shi dae Yah Sadeeq abinda be fahimta ba shine..tsananin mamakin abinda Abbun nasa ya aekata ne ya sanya shi kasa furta komae ko kuma maganar ce tazo masa a bazata

"Are u ohk?" Yah Sadeeq ya tambaya yana kallan yanda har lokacin idanun sa ke a lumshe, se a lokacin ya shiga bud'e manyan idanun sa a nutse wad'anda lokaci d'aya colour d'in su ya chanja, akan Yah Sadeeq d'in ya sauke su se dae har lokacin bece ko uffan ba in ban da jinjina kae kawae da yayi

"Can i just go with her pls?" Yah Sadeeq ya fad'a har lokacin yana kallan Rk, a nutse ya d'aga kan sa ya kalli Ayrah dake zaune gefen Yah Sadeeq kamar bata san da zaman sa a wajen ba, dan kuwa har cikin ran ta tana ji in dae har Abba da Umma basu yafe mata ba ba zata ta6a yafewa Rk ba

"Yeah" ya furta a hankali kamar wanda akawa dole, daga haka ya mik'e ba tare daya sake cewa komae ba ya fara barin wajen zuwa wajen motar sa, bin sa da kallo Yah Sadeeq yayi sanda yake barin wajen, gaba d'aya yanayin sa ya chanja cikin k'ank'anin lokaci wanda har hakan seda ya bawa Yah Sadeeq d'in mamaki, se dae hakan kad'ae ya isa ya nuna masa halin su ze iya kasancewa mabanbanta ne da shi da mahaefin sa.

"Auta.." Yah Sadeeq ya fad'a yana kallan ta da murmushi saman fuskar sa, dan so yake ya d'an kawar mata da wata damuwar kamin su k'arasa gida, aekuwa yaci nasara dan kuwa seda tayi murmushin itama kafin ta sanya hannun ta akan fuskar ta ta goge hawayen fuskar ta still dae tana cigaba da murmushin

"Tashi mu tafi.." ya fad'a bayan ya mik'e, babu musu ta mik'e suka bar wajen zuwa titi, suka samu abin hawa. A 6angaren Rk kuwa a nutse ya k'arasa wajen motar sa ya bud'e ya fad'a ciki, babu 6ata lokaci ya tayar da motar, sam gudu ba d'abi'ar sa bace amma yau seya tsinci kan sa da yin gudun sosae dan so yake ya samu nutsuwar da ze zauna yayi tunani akan wannan maganar, a haka har ya k'arasa gida. A compound d'in gidan yayi parking motar ta sa, ya sauka ya soma takawa zuwa part d'in sa, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin sanya mukulli dan bud'ewa ya jiyo muryar Ummee na fad'in

"Yanzu kake dawowa ne?" seya d'an dakata kad'an sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Ummeen kana yace

"Ehh.." kawae dan a yadda yake jin sa baya jin ze iya doguwar magana haka nan, kallan sa Ummee ta cigaba da yi tana nazarin yanayin sa

"Kana lafiya kuwa?" Ummeen ta tambaya, nan ma da "Ehh" kawae ya amsa yana k'arasa saka key d'in ya bud'e ya tura kan sa cikin d'akin, bin sa da kallo Ummee tayi, se kuma ta juya itama da nufin shiga cikin d'akin nasa se kuma ta dakata ta girgiza kae kamin ta wuce part d'in ta.

.. A hankali ya kwanta kan kujerar d'akin, sannan ya d'auki hannun sa d'aya ya d'ora a kan sa dake cigaba da masa ciwo, idanun sa a lumshe suke yana sake tuna maganganun Yah Sadeeq, be san dalilin da yasa ya kasa k'arya ta Yah Sadeeq d'in ba a lokacin da yake fad'a masa ga abinda mahaefin sa yayi, ya rasa dalilin hakan, haka kawae yake ganin babu abinda ze sa Yah Sadeeq d'in ya zauna ya d'irka k'arya akan mahaefin sa kuma yazo yana fad'a masa, abu ne me kamar wuya hakan ya faru, amma kuma ta yaya zeyi gaggawar amincewa ba tare da wata hujja ba? Duk da yana buk'atar bincike ko da akan takaddun Abba ne da Yah Sadeeq d'in yace Abbu ya tafi har dasu, amma kuma akwae abubuwa da dama da ke ta masa dirar mikiya cikin k'wak'walwar sa, tunda Abbu ya fita da niyyar raka Abba Kano, dawowar sa gida cikin gaggawa suka bar garin, tun daga lokacin be sake ganin Ayrah ko wani daga cikin dangin su ba, ko kuma wani abu daya shafe su ba, kenan me hakan ke nufi? Lokaci guda bugun numfashin sa ya k'aru, baya fatan ace haka d'in ne dan idan hakan ya tabbata gaskiya ne be san da wane ido ze kalli Ayrah da shi kan sa Abba ba, mutum me hallaci a gare shi, mutum me kirki da dattako, wanda tun a lokacin ba wani k'arfi gare shi ba amma saboda wadatar zuci da kuma tausayi irin na sa ya taemaka masa, be tsaya iya nan ba ya taemakawa Abbun sa amma ace abinda Abbun sa yayi kenan? Ya zama dole ya bincika.


.. Babu wanda yace uffan a cikin su sanda Yah Sadeeq d'in ya gama bada labarin, Ayrah na taya shi har lokacin tana share k'walla a idanun ta, Abba gaba d'aya bashi da abin cewa shiyasa ma yayi shiru yayin da Umma kuma mamaki gami da takaeci sune suka taru suka mata yawa yasa ta kasa cewa komae, a hankali ta shiga goge hawayen dake ta saukowa daga kan fuskar ta tana girgiza kae, se yanzu ta sake gane kuskuren da suka aekata na yankewa Ayrahn hukunci ba tare da sun yi bincike ba, hannu Umma ta mik'awa Ayrah bayan ta d'aga fuskar ta ta kalle ta, sannan ta mata alama da ta taho da kan ta, babu 6ata lokaci Ayrah ta k'arasa da sauri ta fad'a jikin Umman tana sakin wani irin kuka, itama Umma bata hana kan ta kukan ba ta rungume d'iyar ta ta sosae tana jin yadda ilahirin jikin Ayrahn ke rawa

"Kiyi hak'uri Ayrah, don Allah ki yafe min, nice na fara d'arsawa Abban ku zargin guduwa kikayi daga gidan

Please Login or Register in order to submit comment