Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mazaunin driver yana sauke ajiyar zuciya, seda ya kalli inda take zaune sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya d'auke kae yana jan motar ya fara tafiya..



.... A d'aya 6angaren kuwa a ranar da Ayrahn ta bar gidan gaba d'aya cikin su babu wanda ya rintsa, Yah Sadeeq zuciyar sa sosae take masa zafi idan ya tuna halin kafiya irin na k'anwar tasa data kasa barin d'a namiji duk da yadda Abba yace ba zata aure shi ba, ta 6angaren Umma kuwa kwana tayi tana kuka a ranar, ta kasa sakewa, koda tayi k'ok'arin tunanin ba hakan ne dalilin rashin ganin d'iyar ta ta ba se kuma ta kasa samun hujjar da zata rik'a akan hakan, koda tayi tunanin d'iyar ta ta bata da bud'ewar ido ko wayon da zata bi saurayi ta gudu se kuma ta tsaya ta tuna tasirin soyayya, musamman yadda Ayrahn ke k'aunar Raj d'in, da yadda taga rikicewar ta a jiya da Abba ke fad'a mata ba zata aure shi ba seta sake jin jikin ta yayi wani mugun sanyi, dan haka tayi kukan ta ta godewa Allah sannan tayi shiru, 6angaren Abba kuwa ranar da bugun zuciya ya kwana, wanda hakan ke alamta masa tashin ciwon sa, haka dae ya dinga daurewa baya so 6acin rae ya sanya yayi wa d'iyar tasa fata mara kyau.




... Washe_gari da safe Umma ta fito ta shiga kitchen dan ta samu ta sarrafa musu wani abun da zasu ci a matsayin abun karin, ta dad'e a kitchen d'in tana nazari se kuma ta fito kae tsaye ta wuce d'akin Abba, tana shirin shiga Abban ya fito seta dakata lokacin da shima ya dakata yana kallan yadda idanun ta suka yi ja da alama jiya kwana tayi tana kuka

"Har yanzu kukan kike yi?" Abba ya tambaya yana cigaba da kallan ta, hannu Umma ta kae fuskar ta ta d'auke hawayen daya zuba, tun jiya take k'ok'arin cire damuwar daga cikin ran ta amma ta kasa, ta kasa mantawa, ko dae_dae da minti d'aya zuciyar ta ta kasa sukuni da wannan al'amari

"Aou cigaba kuma zaki yi?" seta girgiza kae sannan tace bayan ta runtse idanun ta ta bud'e

"Abban su bansan ina yin kukan ba, ko da nayi k'ok'arin mantawa hakan yana gagara ne a cikin zuciya ta, Abban su har yanzu na kasa amincewa ba mafarki nake yi ba" jinjina kae Abba ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Umman, shi kan sa jiya be rintsa ba ya zauna ne kawae se sak'e sak'e yake yi

"Kiyi hak'uri ki dena kukan haka nan kin ji?" ya fad'a yana kallan ta

"In Sha Allah, zan yi k'ok'ari naga hakan ta kasance.." Umma ta fad'a tana sake goge idanun ta.



... Driving yake a nutse kamar koda yaushe, jefi jefi yana juyawa yana duban inda take a takure cikin hijab ko k'wak'wk'waran motsi ba tayi, bece mata komae ba dan baya so ya tado da rigima tun yanzun dan haka ya mata shiru a ran sa yana tunanin mafita. Tafiya me tsayi suka yi kafin suka fara shiga garin Kano, zuwa lokacin kam mamaki take bashi ganin har lokacin bata motsa ba, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa sannan yaja motar ya gangara gefen titi ya kashe ta ya d'an jinginar da kan sa akan steering na tsawon sakanni kana ya d'ago kan nasa ya dubi inda take, seda ya lumshe idanun sa kafin a hankali yace

"Ayrah!!" beji ta amsa masa ba ko kuma ta d'ago har bayan wajen minti 1 sannan a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in nata ya d'an yi tapping nata, nan ma dae ba tayi motsi ba, seya ware manyan idanun sa akan ta sannan ya kae hannun sa a nutse gaba d'aya ya rik'o ta, se kuwa tayo baya zuwa jikin sa, k'irjin sa ya wani irin buga lokaci guda yana mamakin yadda yaji jikin ta yayi wani irin zafi daya wuce na k'a'ida, idanun sa akan kyakykyawar fuskar ta da tayi fayau kamar wadda tayi wata da watanni tana rashin lafiya, idanun ta a rufe suke, dogayen zara zaran eye lashes d'in ta sun kwanta sunyi luff akan idanun ta, a hankali ya sake bud'e bakin sa se dae yanzu a cunkushe ya furta

"Ayrah!!" nan ma dae ba tace komae ba, runtse idanun sa yayi yana jin wani abu me kama da tsoro na shigar sa

"Meya same ta?" ya tambayi kan sa, seya kae kunnen sa saetin dogon hancin ta da yayi ja kamar me mura, cikin lokaci k'ank'ani hucin numfashin da take fitarwa me zafi da kuma hucin zafin dake jikin ta ya sauka akan fuskar sa, seya sake lumshe idanun sa yana d'an tsayar da numfashin sa har lokacin cike da tsoro, cikin ikon Allah yaji numfashi kad'an na fita, be san sanda ya saki wata ajiyar zuciya ba sannan ya maeda ta kan kujerar ya kwantar kana ya tashi motar da gudun gaske ya wuce asibiti, sam gaba d'aya ma ya manta, haka zalika beyi tunanin komae ba ya wuce asibitin sa. Parking d'in motar sa yayi har lokacin bugun zuciyar sa be koma dae_dae ba, ya fito daga cikin motar cike da sassarfa wanda komae abin ka baka isa ka gane a yanayin da yake ciki ba, dan kuwa fuskar nan haka take babu yabo babu fallasa amma cikin zuciyar sa shi kad'ae yasan abinda yake ji, bud'e inda take kwance yayi beyi wata wata ba ya d'auke ta gaba d'ayan ta a hannun sa, sam be lura da kallan da en cikin asibitin ke bin sa dashi ba, yama manta abinda ya aekata haka ya wuce da ita cikin Office d'in sa, duk wad'anda ke kallan sa mamaki ne ya kamasu yadda suka ga Doctor Rk d'in da kan sa ya d'akko wata mace a hannun sa, nan take aka fara gulmammaki cikin asibitin, seda ya tsaya ya kar6i spare key d'in Office d'in sa dake ajje sannan ya wuce ya bud'e ya shiga har lokacin tana rik'e a hannun sa ya kwantar da ita kan gado.


.. Hannun ta har rawa yake yi ta d'auki wayar ta ta nemo number Abbu ta kira, babu jimawa Abbu ya amsa wayar

"Yalla6ae Doctor Rk ya shigo yanzun nan" daga inda Abbu yake ya saki ajiyar zuciya yana jin dad'i har cikin ran sa dan kuwa tun d'azun yake kiran layin Rk d'in amma se ace masa a kashe yake

"Ohk ina nan zuwa nan da 10 minutes" shine kawae abinda Abbu ya fad'a yana katse wayar sannan ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa asibitin.



.. Kamar wanda aka jefo haka Abbu ya fad'o cikin asibitin, dae_dae lokacin da Rk ya fito daga cikin Office d'in sa, Abbu ya sake sauke ajiyar zuciya ganin d'an nasa, seya k'arasa kafin yace

"Raj!" muryar wanda yaji ne ta sanya k'irjin sa ya d'an buga sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Abbun dake k'arasowa inda yake

"Ina ka shiga ne haka? Kasa hankalin mu duka ya tashi?" d'an yatsine fuska yayi lokaci guda kuma yana kae hannun sa kan sa sannan yace

"Amm... Abbu ina so ne nayi settling abubuwa da dama, bana buk'atar takura ne yasa na kashe waya ta, ina fatan dae ban yi laefi ba?" ya k'arasa maganar yana kallan Abbun

"Ohk tohm muje cikin Office d'in akwae maganar gaggawa da nake so muyi" be san sanda yayi gaba ba yana tarewa Abbu k'ofar shiga Office d'in ba sannan yayi wani murmushin yak'e yace

"Abbu pls.."

"Shikenan, kayi k'ok'arin gamawa, koma dae baka gama ba ka tabbatar ka dawo gida dan akwae muhimmiyar maganar da zamu yi bamu da ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an nazarin d'an nasa, ganin yanda idanun sa suka d'an tasa kamar wanda baya samun bacci, se kuma daya tuna yanzu yake fad'a masa aeki ne ya rik'e shi sannan ya d'an ji dama dama

"In Sha Allah" shine abinda Rk ya fad'a yana d'an kaucewa kallan da Abbun ke masa, dan gani yake kamar yana kallan k'wayar idanun sa ze karanto rashin gaskiyar dake tattare da shi


"Allah ya yadda" Abbu ya fad'a yana juyawa daga wajen, se a lokacin Rk ya saki ajiyar zuciya yana lumshe idanun sa, se yanzu ya gane shirmen daya aekata na zuwa da ita asibitin nan, me ya shiga kan sa ya kawo ta nan d'in? Hannu ya saka ya bud'e Office d'in ya shiga sannan ya kulle, idanun sa akan ta lokacin da idanun ta ke a rufe tana sauke numfashi a wahalce, daga yanayin yanda ta 6ata rae kawae zaka fahimci ba dad'in baccin take ji ba, ga kuma yanda ta d'an tura red lips d'in ta gaba kamar me shirin yin kuka, seya samu kan sa da lumshe idanu na tsawon second 10 sannan ya bud'e ya k'arasa bakin gadon bayan yaja wata kujera ya zauna, duk da yanda take sake had'e jikin ta waje d'aya hakan be hana gumi tsatstsafowa daga fuskar ta ba, ya sake sauke idanun sa kan fuskar ta sannan ya maeda kan jikin ta da har lokacin ke d'auke da hijab, a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in, kamar me tunanin wani abun ya dakata da hannun sa a sak'ale, ya kae wajen second 30 a hakan sannan ya k'arasar da hannun nasa zuwa kan hijab d'in nata ya fara janye shi sama, be sake shi seda yazo dab da fuskar ta, se a lokacin kuma ya fara tunanin yanda ze cire shi daga wajen fuskar ta dan baya so ya tashe ta dan kuwa be shiryawa abinda ze fad'a mata ba, be kuma shiryawa rigimar ta ba, a hankali ya d'an mik'e tsaye sannan ya rank'wafa ya kae hannun sa k'asan kan ta da nufin d'ago kan nata, dae_dae lokacin data bud'e idanun ta da suka mata nauyi, se rumfar mutum kawae ta gani a kan ta, duk da yanda kan ta ke cigaba da mata ciwo hakan be hana ta sake ware idanun ta ba, duk da bata fahimci menene ba amma ta tsorata matuk'a dan haka bata san sanda ta mik'e zaune ba tana sakin k'ara, lumshe idanun sa yayi yana jin k'arar ta ta har cikin jikin sa, sanda ya ida bud'e idanun sa se nata idanun suka sauka cikin nasa, cikin wata rud'ewar ta saki k'ara tana yin baya gami da sake jan hijab d'in ta ta lullu6e kafatanin jikin ta tana sakin kuka kamar wadda aka daka, lokaci d'aya kuma jikin ta na cigaba da rawa, runtse idanun sa yayi saboda yadda yaji kan sa ya sara da k'arar da tayi har sau biyu, ya d'an dafe kan sa sannan ya bud'e idanun sa ya sauke su a kan ta lokacin da take cigaba da mak'urewa a jikin bango hannun ta rik'e da hijab d'in ta kamar zata maeda shi cikin ta, cikin karyayyiyar murya me had'e da kuka ta furta

"Ina takadda ta? Meyasa baka maeda ni gidan mu ba?" tayi maganar sanda wasu hawaye masu d'umi suka samu damar zubowa akan kuncin ta, idanun sa yayi saurin janyewa daga cikin nata narkakkun idanun dake zubar da hawaye kamar an kunna famfo haka kuma sun cika taff da hawaye duk da wad'anda ke zuba, baya so tun yanzu raunin ta yaci galaba a kan sa dan haka ya d'an runtse idanun sa sannan ya bud'e su, ya d'auke su ya aza su a kan ta sanda ta cigaba da mutsu mutsu akan gadon tana cigaba da kukan ta

"Me kike ci na baka na zuba Madam? Ae har yanzu yinin be k'are ba!" ya fad'a yana sakin wani miskilin murmushi..




Mhiz Innocent.....✍️





https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 033


___Ganin da yayi tana cigaba da bin sa da kallan tuhuma lokaci guda kuma tana sake kwa6e fuskar alamar koda yaushe zata iya sakin kuka ya sanya shi sake lumshe idanun sa sannan a hankali ya d'aga hannun sa dake d'auke da wani had'ad'd'en agogo ya juya mata dashi dan ta gani, bin hannun tayi da kallo dan fahimtar abinda yake nufi da hakan

"Duba lokaci" ya fad'a har lokacin be d'auke hannun nasa ba, se ta sake bin hannun nasa da kallo sannan ta d'an runtse idanun ta dan har lokacin ganin ta be koma dae_dae ba, k'uri ta yiwa agogon kamar me k'irga sakannin da suke wucewa, ganin da yayi ta janye idanun ta daga kallan agogon ya tabbatar masa data gani, be sake cewa komae ba ya fice daga Office d'in, seda ya kulle k'ofar sannan ya tafi, bin sa tayi da kallo sanda ya fice d'in sannan ta dawo da kan ta kan gadon da sake kwantawa, ta k'agu ta koma gida, bata san nan d'in ina ne ba da babu shakka da kan ta zata koma gida. Wajen mintuna 20 se gashi ya turo k'ofar Office d'in ya shigo hannun sa d'auke da leda, se tayi sauri ta tashi dan tasan yanzu kam may be ya shigo mata da takaddar tane ta wuce gidan su, ganin yadda take shirin sakkowa daga kan gadon ne ya sanya shi fad'in

"Kici abinci ki sha magani, sannan ki koma gidan" ya fad'a yana ajje ledar akan gadon ba tare daya kalle ta ba haka zalika fuskar sa a had'e, ji tayi kamar ta fasa ihu, ita gaba d'aya bata ta wani abinci bare akae ga magani, dan haka ta d'auke kae kamar ba taji ba, d'an d'aga kae yayi ya saci kallan ta yadda take ta wani cic cin magani ita a lallae dole bata ji shi ba ya sanya wani murmushin gefen baki ya su6uce masa se kuma ya sake had'e fuskar sa sannan yace

"Well, se kiyi ta zama anan d'in, ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana ta6e baki gami da soma tafiya kamar ze bar Office d'in, se kuwa ta fashe da kukan tana sakkowa daga kan gadon gaba d'aya cikin kukan ta furta

"Don girman Allah kayi hak'uri, bazan iya cin abinci ba, ka maeda ni gidan mu ko ka bani kud'in mota na tafi.." tayi maganar tana saka hannun ta kan fuskar ta tana goge hawayen dake ta sintiri akan kuncin ta, dakatawa yayi daga inda yake ba tare daya juyo ba har wajen second 20, seda kukan nata ya fara raguwa sannan ya juyo a nutse ta fara takawa zuwa cikin d'akin, har ga Allah ya gaji da jin kukan nan nata, d'aga masa hankali yake yi, kuma babu damar rarrashi kada yaje ta koma zargin sa ko ta hasaso wani abun nan gaba, dan haka yanzu ma be kalle ta ba yaja wata kujera sannan ya janyo abincin ya d'ora akan kujerar kana yace

"Ba zaki koma gida a haka ba, dan haka ki tsaya kici abincin kawae" yayi maganar lokacin daya ida bud'e abincin, ya ajje cokali a gefe sannan yaja gefe ya tsaya yana fiddo da wayar sa daga aljihu ya shiga dannawa, seda ta gama sheshshek'ar ta ran ta na cigaba da suya, tasan taemakon ta yayi amma kuma ita bata buk'atar wani abinci dan gaba d'aya hankalin ta da nutsuwar ta sun tafi gida ne, amma kuma daga yadda yayi maganar tasan idan ba taci abincin ba ba mayar da ita zeyi ba dan haka ta k'arasa ta zauna kan gadon kana taja kujerar, ruwa ta fara d'auka ta 6alle murfin robar ta kae bakin ta, se yanzu ta tuna rabon ta da shan ruwa har ta man ta, wata irin k'ishirwa ta taso mata dan haka bata sauke robar ba seda ta shanye shi tass, sannan ta ajje tana sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma jikin ta na d'aukar rawa, lumshe idanu tayi dan gaba d'aya bakin ta babu taste amma yaza tayi? Janyo abincin tayi a hankali ta fara kaewa bakin ta tana 6ata rae, spoon na farko data fara kaewa sega hawaye sharr akan fuskar ta, haka dae ta cigaba da ci lokaci d'aya tana kae d'ayan hannun ta tana d'auke hawayen, daga inda yake yake d'an satar kallan ta gaba d'aya wani tausayin ta yazo ya lullu6e shi, seya maeda wayar cikin aljihu sannan ya k'arasa cikin Office d'in ya fara wani abun, ita sam bata lura dashi ba seda yazo dab da ita hannun sa d'auke da allura, beyi tunanin ta lura da ita ba seda yaga tayi sauri ta koma kan gadon manyan idanun ta da suka yi ja sun sake cika taff da hawaye

"Idan kana k'aunar Allah kada kamin allura, naci abincin fa, ka k'yale ni don Allah" ta k'arasa fad'a tana sakin kukan gaba d'aya, lumshe idanu yayi na tsawon sakanni kafin ya bud'e su still dae a kan ta, a hankali ya shiga takawa zuwa bakin gadon, ita kuma tana cigaba da komawa baya tana girgiza kae gami dayin kukan ta kamar wadda aka riga aka yiwa allurar

"Oh god" ya furta sanda ya dakata yana d'an murza goshin sa

"Wannan wace irin yarinya ce?" ya furta a k'asan ran sa kafin ya sake maeda duban sa kan ta har lokacin dae ba tayi shirun ba

"Ina yi miki allurar zan maeda ki gida bayan na baki takaddar ki" yayi maganar a nutse kuma cikin lallashi, ita sam ba fahimtar sa take ba wannan allurar kad'ae data gani ta gama rikita ta dan kuwa zata iya cewa tunda take da girman ta ba'a ta6a mata allura ba, ganin da yayi zata cigaba da 6ata masa lokaci ne ya sanya shi tamke fuskar sa sannan ya hau kan gadon ya zauna kana ya sanya tattausan hannun sa yana k'ok'arin rik'o ta, wani sabon kukan ta sake fashewa dashi tana cigaba da komawa baya, hannu biyu ya saka ya janyo ta gaba d'ayan ta cikin jikin sa, duk da yanda take cigaba da k'ok'arin k'wacewa tana kukan ta hakan be hana shi zagaye ta da d'ayan hannun sa ba sannan ya fara k'ok'arin zame hijab d'in jikin ta, lokaci d'aya bugun zuciyar sa ya k'aru, wani irin kasala na saukar masa, d'an lumshe idanun sa yayi kafin ya bud'e har lokacin yana jin yanda take cigaba da kici kicin k'wace kan ta, be bi ta kan ta ba kawae ya saka hannun nasa ya zame hijab d'in zuwa kan kafad'ar ta, sannan babu 6ata lokaci yayi mata allurar, k'ara ta saka sanda taji tsinin allurar ya shige ta bata san sanda ta ruk'unk'ume shi ba lokaci d'aya gaba d'aya jikin ta ya wani saki, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya saki sanda ta ruk'unk'ume shin, idanun sa a lumshe ya sake rik'e ta gam yana sauke taggwan ajiyar zuciya, sun kae wajen minti 1 a hakan har lokacin tana kuka a hankali, se a lokacin ta fara tuna a'ina take kuma a jikin wa take, da sauri ta saka hannun ta ta ture shi sannan ta tashi da sauri k'irjin ta na bugawa, se a lokacin ya bud'e idanun sa da suka sake lumshewa ba tare daya kalle ta ba ya mik'e ya k'arasa ya jefar da allurar cikin dustbin sannan ya juyo ya d'an kalle ta k'asa k'asa

"Tashi mu tafi" tun d'azun bata kalle shi ba se yanzu da taji yayi maganar nan da saurin da bata san tana dashi ba ta diro daga kan gadon duk da har yanzun tana d'an jin jiri amma tama manta da hakan, murmushin da tun kafin tasan wanene Abbun Raj rabon ta dayi ya su6uce akan fuskar ta lokaci d'aya kuma tana sake goge fuskar ta, wannan d'an murmushin da tayi seda yasa ya d'an ji sanyi har cikin ran sa, ganin tana k'ok'arin riga shi fita ma ya sanya shi fad'in

"Je ki wanke fuskar ki" yayi maganar yana tattara abinda ze fita dasu daga cikin asibitin dan so yake ya chanja mata asibiti idan bata samu sauk'i ba, kamar zata yi musu se kuma kawae ta juya ta fad'a inda taga yayi mata kama da toilet, babu jimawa ta fito tana sake sharce ruwan dake kan fuskar ta, ba tace komae ba haka zalika shima bece komae ba yayi gaba ita kuma tabi bayan sa, seda ya kulle Office d'in sannan ya cigaba da tafiya a nutse, ita kuma tana bin bayan sa, duk haka kurum take jin ta a wani irin takure, d'an jiri jirin da take ji ya sanya tafiyar ta ta ta sake zama very slow, se kuma idan taga ya mata nisa sannan ta saka iya k'arfin ta ta kusa cimmasa, yadda ake d'an satar kallan su ne ya sanya shi sake tattaro girar sama data k'asa ya had'e su waje d'aya, dan haka yawanci mutane se suka shiga hayyacin su, seda ya tsaya a pharmacy ya kar6ar mata magunguna har lokacin tana bayan sa kamar wata munafuka se bin wajen take yi da kallo har zuwa sanda suka fita harabar asibitin, yana shirin bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza kamar wanda aka tsikara kuma seya fasa, ya sake kicin kicin da rae dan abinda yake k'ok'arin aekatawa yanzun yasan wata rigimar ce ze kuma 6allowa, seya zagaya ya shiga driver seat ya zauna, ganin da tayi bece da ita komae ba ya sanya itama ta sake had'e ta ta fuskar kana ta bud'e ta shiga, babu 6ata lokaci yaja motar ya fice daga asibitin, sanda suka hau titin seta samu kan ta da juyawa tana k'arewa titin kallo, in dae har ba tayi mistake ba nan titin Kano ne, bata san sanda ta saki wani murmushi me sauti ba tana ji kamar ta tashi ta taka rawa, duk da yadda yaji tayi murmushin hakan be sanya shi kallan ta ba sema sake tsuke face da yayi, haka ya cigaba da tafiya tana cigaba da bin titin da kallo, ita dae ba taga yayi hanyar unguwar su ba, tun tana k'ok'arin yin shiru taga iya gudun ruwan sa har taji zuciyar ta na son karaya ta kalle shi yadda yake driving a nutse sannan ta d'auke kae tana 6ata fuska itama

"Bafa nan ne unguwar mu ba mu" tayi maganar murya a cunkushe, yadda tayi maganar ne ya sanya shi yin murmushin dabe shirya ba, gudun kada ta gan shi ya sanya shi saurin sake had'e fuska, kamar ba zece komae ba se kuma can bayan ya gama jan ajin sa yace

"A haka zaki koma musu gidan kamar korarriya? So kike hankalin su ya sake tashi fiye da da? Zamu je kiyi wanka ne ki chanja kaya sannan na maeda ki gidan" yayi maganar cikin tsare gida shima tasa muryar a cunkushe

"Toh ina ruwan ka?" ta fad'a bayan ta jefa masa harara, daga inda take tana ji kamar ta tashi ta rufe shi da duka, yace taemakon ta zeyi, ya taemake tan to kuma ina ruwan sa da yadda zata koma gida? Meye nasa a ciki? D'aga kafad'a yayi yana ta6e baki sannan yace

"Babu ruwa na, amma ni dae bazan kae ki gida a haka ba" kallan jikin ta ta shiga yi, dan ita dae bata ga abinda tayi ba da yake nema ya fad'a mata magana ba dan haka ta sake kufula tace

"Toh ka ajje ni in tafi da kae na mana, bana buk'atar taemakon ka a karo na biyu" ta fad'a tana jin yanda zuciyar ta ke mata zafi, be kula ta ba haka kuma be kalle ta ba hakan ya sake fusata ta, se kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya tana runtse idanu, yasan yanzu zata soma kukan nan nata da bata gajiya dashi dan haka yana karya kwanar wani layi yace a nutse

"Shikenan muje na rubuta takaddar ki tafi" jin abinda ya fad'a d'in ne ya sanya ta kalli inda suka shigo sannan taja doguwar ajiyar zuciya tana hana kukan daya taho mata fitowa, a k'ofar wani gida ya tsaya da motar tasa sannan ya dakata ya d'auki wayar sa ya danno number Yaseer ya kira, bata dad'e tana ringing ba Yaseer ya d'aga

"Kana gida ne?" Rk ya fad'a

"Ehh.. Na dawo" Yaseer ya fad'a daga inda yake zaune kusa da matar sa Hameeda

"Toh gani k'ofar gidan ka" dariya Yaseer yayi gami da fad'in

"Haba mana Mr man, ae ba seka zolaye ni ba, nasan ba ta6a zuwa zaka yi ba" d'an murmushi kad'an Rk yayi sannan yace

"Toh ka fito ka tabbatar mana, hope dae Madam na nan?" da mamaki Yaseer ya kalli Hameeda sannan yace

"Yeah, amma dae fari dae bari

Please Login or Register in order to submit comment