Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwantar da kanta a hannun Raj yace

"Toh taho koh?" mak'ale kafad'a tayi tana sake cuno baki gami da sake rik'e hannun Raj, Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace cikin rarrashi bayan ya matsa dab da ita ya kamo d'ayan hannun ta

"Ki taho mu tafi kinji, zamu dawo ae"

"A'ah" ta sake fad'a tana kuma mak'ale kafad'a, Umma dake gefe ta d'an lumshe idanun ta kad'an ta bud'e kana ta matsa kusa da Ayrahn tace

"Taho kinji, ae zaki dinga zuwa Uhmm?" girgiza kae ta shiga yi sosae k'wallar data dad'e a idanun ta ta shiga sakkowa babu k'ak'k'autawa, shi kam Raj gaba d'aya ma ya kasa kallan ta dan zuciyar sa ta riga ta dad'e da gama karyewa, Yah Sadeeq ne ya k'araso a hankali ya rik'o hannun Ayrahn dake cigaba da girgiza kae yace cikin rarrashi

"Ki taho mana kinji" ya fad'a yana janyo ta, a hankali hannun nata dake rik'e da nasa ya shiga zamowa daga sama zuwa k'asa har zuwa sanda ya zama tafin hannun su ne kawae cikin na juna, Raj ya rik'e hannun nata sosae yana kallan k'wayar idanun ta dake cigaba da zubar da hawaye, Yah Sadeeq be kalle su ba ya jata ya d'auke ta kawae a hannun sa, abinda ya sanya hannun su rabuwa dana juna kenan kuma dae_dae lokacin da Ayrah ta saki kuka me k'arfin gaske cikin kukan tana fad'in

"Yah Sadeeq Raj, Yah Sadeeq Raj" be bi ta kanta ba se kwantar da kan nata da yayi a kan kafad'ar sa amma tak'i kwanciya ta cigaba da kukan ta kamar ranta ze fita, a haka yayi gaba. Lumshe idanun sa yayi sanda Ummeen sa ta d'ora hannun ta akan kafad'ar sa, yana jin wasu k'walla na tarar masa a cikin idanun sa, Ummee tace

"Kada kayi kuka fa" kamar ma zuga shi tayi se kuwa hawayen suka cigaba da zuba yana saka hannu yana goge su, Umma data mik'e tace

"Toh bari mu tafi"

"Allah ya tsare Hajiya.." Inji Ummee

"Ameen" Umma ta fad'a tana yin gaba...

Tunda suke tafiya kukan take yi tana cigaba da ambatar sunan Raj, se rarrashin ta Yah Sadeeq keyi amma tayi kamar bata san yana yi ba, ta cigaba da rera kukan ta tana yi tana sauke ajiyar zuciya, seda suka kusa isa tasha sannan bacci yayi awon gaba da ita a kafad'ar Yah Sadeeq... Motar da zata kaesu Kano direct ita suka samu tana shirin tashi mutane 2 kawae ake jira ta tashi, ganin su Abba ya sanya su dakatawa kwandasta ya kalli Abba yana tambayar inda zeje, Abban ya fad'a masa sannan ya bud'e musu motar, Umma ce ta fara shiga sannan Yah Sadeeq daya zauna a maleji, kana Abba ya kalli wajen da yayi ragowa sannan ya kalli Abbu dake tsaye rik'e da kayan Abban yace bayan ya kalli kwandastan

"Ae mu 2 ne kuma naga saura wajen mutum 1" kwandastan ya kalli Abba kana yace

"Shawara idan zaka d'auka ku raba motar, idan yaso wasu su tafi yanzu wasu kuma idan wata za taje kanon seta d'auke su" Take Abba yayi na'am da shawarar ya kalli Abbu yace

"Ko mu barsu su tafi, mu kuma ma taho?" Abbu yace

"Alhaji kar a samu matsala tunda kaga basu ta6a zuwa kano ba se wannan karon.."

"Hakane kuma" Abba ya fad'a yana tunanin mafita

"Meze hana kuyi gaba ni sena taho daga baya?" Abbu ya katsewa Abban tunanin da yake, Abba ya d'aga kae ya kalle shi kana yace

"Babu matsala?"

"A'ah babu matsala" Abbu ya fad'a yana murmurshi, mik'a hannu Abba yayi da niyyar kar6ar kayan hannun Abbu, kwandastan yace

"Yalla6ae cikin wajen nan wallahi babu wajen da zaka ajiye jakar nan, ko a jikin ka zaka rik'e zaka takura ne kuma ka takurawa mutane" Abba baya son dogon zance dan haka yace

"Bud'e min bayan motar na saka to"

"Ae da mutane a ciki" sauke numfashi Abba yayi yana tunanin meya kamata yayi yanzun, seya tsinto muryar Abbu na fad'in

"Toh Alhaji kona taho maka dasu?" kallan Abbun Abba yayi sannan yayi murmurshi yace

"Toh shikenan, yanzu zaka jira zuwan wata ne?"

"Ehh In Sha Allah Alhaji, Allah ya tsare.." Abbu ya fad'a

"Ameen Ameen, Allah ya tsare dukkan mu"

"Alhaji lokaci fa na tafiya" kwandastan ya fad'a yana kallan Abba, kallan Abbu Abba ya sake yi sannan yayi murmurshi ya koma ya shiga cikin motar sannan kwandastan ma ya shiga, Abbu ya sake yi musu addu'a sanda drivern motar ke k'ok'arin tashin ta, be bar inda yake tsaye ba seda motar tasu ta tashi. Tafiyar awanni suka yi suka isa garin na Kano zuwa lokacin Ayrah ta tashi daga bacci ta cigaba da kukan ta, tayi kukan harta gaji ta hak'ura se ajiyar zuciya da take ta saukewa daga k'arshe wani baccin ya sake d'auke ta a jikin Yah Sadeeq dan shi kad'ae ne ze iya rik'e ta saboda yadda su Umman suke a matse a inda suke zaune, se a lokacin Abba yayi dana sanin k'in tahowa da motar sa, daya sani ya kae ta gyara saboda matsalolin da take bashi a kwanakin nan, ganin tafiyar tasu me nisa ce ya sanya be taho da ita ba ko dan gudun matsala.... Sanda suka isa Kanon kae tsaye gidan da Alhaji Maton ya nemar musu suka isa, su Umma ne suka fara shigewa cikin gidan ita da Yah Sadeeq yayin da Abba ya tsaya ya lalubo wayar sa dan tuntu6ar Abbu yaji ko shima ya taho d'in dan yana ganin kamar wannan d'in nauyin sa, yana so kuma ya sanar dashi idan be samu motar ba ya bari se gobe kada yamma tayi masa a hanya, kiran farko da yayi ta shiga ta soma ringing, se dae har kiran ya katse ba'a d'auka ba, hakan ne yasa Abban ya sake kiran layin se dae ga mamakin sa se suke fad'a masa wayar tana a kashe ne, ya riga ya yaddarwa zuciyar sa matsalar network ne tunda a yanzu yayi kira na farko ta shiga yanzu kuma a kashe dan haka ya sake trying number sedae abinda yanzu kuma take fad'a masa shine kwata kwata ma ba zata shiga ba.......


*Zarah Bint Yusuf (Mhiz Innocent)*







https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page_006


___Sosae tsoro ya kama Abba, a ransa yana fatan ba wani abin ne ya faru ba

"Lafiya kuwa Abban su?" Umma da fitowar ta kenan ta fad'a tana kallan Abban da damuwa ta gama bayyana akan fuskar sa, kallan ta yayi sannan yace

"Na kira layin Kabeeru ne da farko ta shiga yanzu kuma ta dena shiga" Abban ya fad'a

"Ae Ina tunanin yanzu yana cikin mota ne, babu mamaki ko shiyasa kaji wayar a kashe" d'an murmushi kad'an Abba yayi sannan yace

"Babu shakka ma haka ne" itama murmushin ta maeda masa sannan tace

"Ya kamata muje ciki koh?" Babu musu yabi bayan Umman da tayi gaba zuwa cikin gidan daya kasance madaedaeci, gida ne haka me k'ofa da d'aku na 4 a cikin sa, 1 parlour wanda ya kasance shine na Umma sannan d'akin gado shi kuma shine na Abba, sannan ragowar d'aku nan da suka kasance madaedaeta su kuma Yah Sadeeq da Ayrah kowannen su ya d'auki d'aya, se kitchen da ban d'aki, babu laefi gidan yayi kyau duk da ba wani girma gare shi ba amma an masa k'yale k'yale wanda suka k'awata shi. Kae tsaye cikin d'akin Abban suka nufa wanda shima yake d'auke da d'an madaedaecin ban d'aki a cikin sa, Umma ce ta taemaka masa yayi wanka kafin ya fito su d'an zazzagaya gidan, kukan Ayrah data jiyo daga parlourn nata ne ya sanya ta fad'in

"Ya ilahy"

"Toh rigimatu ta farka kenan" Abba ya fad'a yana murmushi, mik'ewa Umma tayi ta fita daga d'akin dae_dae lokacin da Yah Sadeeq shima yake shirin shiga d'akin, ganin Umma ya sanya shi fad'in

"Alhamdulillah, Umma gwara ki rarrashi abar ki" ya fad'a yana juyawa yayin da Umma ta shige cikin d'akin, k'arasawa Umma tayi ta zauna inda Ayrah ke zaune ta kamo ta cikin jikin ta tace

"Kiyi hak'uri kiyi shiru kinji Auta"

"Umma Raj" Ayrahn ta fad'a tana kallan Umma da jajayen idanun ta, lumshe idanu Umma tayi a ranta tana cigaba da mamakin irin wannan shak'uwa tace

"Shikenan za'a kira Abban sa ya kawo miki shi kinji?" seta cigaba da kallon Umman kamar me nazari se kuma tace

"Umma ze zo?" murmurshi Umma tayi kana tace

"Ehh ze zo"

"Kuma in be zo ba na dena kula shi" ta fad'a cike da sakarci tana ta6e baki, girgiza kae Umma tayi

"Toh shikenan, kukan ya isa haka Uhmm?" ta fad'a tana kuma shafa bayan ta, cigaba tayi da sheshshek'ar ta har zuwa sanda ta gaji tayi shiru a jikin Umman... Wajen k'arfe 7pm na daren ranar Umma ta shiga d'akin Abba, seta tarar dashi zaune kan gadon, a hankali ta k'arasa ta zauna tana kallan sa tace cikin nutsuwa

"Abban su lafiya kuwa?" d'an gyara zama yayi sannan yace

"Haka nan kawae nake jin kamar ba lafiya ba, ina tunanin zan koma in bincika dan har yanzu layin sa baya shiga, kuma yaci ace yanzun dae ya iso cikin garin nan" cikin kwantar da murya kuma dan ta k'ara bawa Abban k'warin gwuiwa ya sanya ta fad'in

"In Sha Allah yana lafiya, lafiyar ce kuma ta 6oye shi.."

"Allah yasa" Abba ya fad'a.



Tun Abba na kiran layin Abbu har ya gaji ya hak'ura ya cigaba da addu'ar Allah yasa Abbun yana lafiya, duk kuma yabi ya takurawa kansa yana ganin kamar duk abinda ya samu Abbun shine sila, haka dae Umma ta dinga bashi baki akan ya kwantar da hankalin sa amma har zuwa dare babu kiran Abbu.. Washe gari Abba ya kasa sukuni dan haka tunda yayi sallahr Asuba ya shirya cikin wani yadi me kyau ya kalli Umma dake kallan sa

"Har yanzu hankali na ya kasa kwanciya Ruk'ayya, gwara naje na duba da kae na" jinjina kae Umma tayi dan itama yanzun ta fara d'an shiga cikin tsoro gwara Abban ya duba ko lafiyar ce ta 6oye Abbu, amma dan ta sake kwantar masa da hankali tunda tafiya zeyi ya sanya ta fad'in

"Hakan ma yayi Abban su, Allah ya tsare hanya..amma yadda nake ta tunani dae babu mamaki motar da zata zo zuwa Kano ne be samu ba shiyasa ya bari se yau ina ga" murmurshi Abba yayi kafin yace

"Toh banda abun Kabeeru ae ya kira ni ya fad'a min ko dan kada hankalin mu ya tashi dukan mu"

"Hakane Abban su, In Sha Allah lafiyar ce ma"

"I hope so" Abba ya fad'a sanda yake d'aura agogon hannun sa. Sanda ya fito daga d'akin yayi dae dae da lokacin da Ayrah ke fad'in daga toilet d'in tsakar gida

"Umma na gama" k'arasawa Umma tayi zuwa cikin toilet d'in ta yiwa Ayrahn tsarkin fitsarin da tayi sannan suka fito tare, da gudu ta isa wajen Abba tace hannun ta rik'e da nashi

"Abba don Allah zan bi ka" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace

"Tohm shikenan bari naje na dawo zan taho miki da tsaraba" d'aga idanun ta tayi ta kalli Abban tana murmurshi tace

"Abba ni kad'ae ni da Raj zaka siyowa banda Yah Sadeeq koh?" shima murmurshin yayi sannan yace

"Ehh.." seta saki Abban tana shirin shiga d'aki tace

"Abba ada lafiya" kallan Umma yayi bayan ya amsa addu'ar Ayrahn yace

"Ina tunanin zan d'akko Raj in had'a su da Sadeeq su cigaba da karatun su anan ko ya kika gani?" jinjina kae Umma tayi cikin na'am da zancen Abban sannan tace tana murmurshi

"Hakan yayi Abban su, Allah ya k'ara taemaka maka, in dae hakan yayi maka nima ya min"

"Toh gaskiya hakan ya min, ina tunanin zamu dawo ne tare da Raj yau d'in nan"

"Toh Allah ya tsare" Umma ta fad'a.... K'arfe 2 Abba ya sauka a unguwar su Raj bayan ya sake trying number Abbu a kashe, ya sauka daga adaedaetar data kawo shi dan be kae ga d'akko motar sa ba, da k'afar sa ya k'arasa cikin layin cikin nutsuwa, tun daga nesa yake hango gidan kamar da kwad'o a jiki, amma be gasgata hakan ba seda ya k'arasa bakin gidan ya tsaya, kwad'on ne kuwa a jiki, mamaki ya sake kamashi kawae ya tsaya cikin rashin sanin abinyi, ya kae wajen minti 5 tsaye a wajen lokacin ya sake gwada kiran number Abbu har kusan sau 5, sega wani mak'ocin su Abbun yazo wucewa, ya kalli Abba dake kallan wayar sa yace

"Salamu Alaekum" ya fad'a yana mik'awa Abba hannu, d'agowa Abba yayi yana kallan mutumin seya mik'a masa hannu suka yi musabaha sannan mutumin yace

"Malam Kabeeru kake nema ne?" murmurshi Abba yayi yana jin In Sha Allah mutumin yasan inda yake sannan yace

"Wallahi kuwa, tun jiya nake gwada kiran layin sa amma ban same shi ba, gashi kuma nazo gidan a kulle"

"Ikon Allah" mutumin ya fad'a yana jinjina kae, jin abinda ya fad'a ne ya sanya Abba sake kallan sa sanda yake fad'in

"Aekuwa da alama kunyi sa6ani dan kuwa jiya jiyan nan kafin azahar nazo na same shi suna had'a kaya shi da matar tasa a cikin wata mota, har nake tambayar sa dalilin tafiyar tasa haka babu sanarwa shine yake shaeda min tafiyar gaggawa ce ta kama shi da iyalan nasa shiyasa basu sanarwa da kowa ba amma muyi hak'uri zasu bar garin ne gaba d'aya" da sauri Abba ya sake kallan mutumin yana mamakin jin abinda ke fitowa daga bakin mutumin, cikin watsi da kuma kokawa da abinda ya fara zuwar masa k'wak'walwa da zuciya yace

"Anya kuwa? Magana nake fa akan Kabeeru.."

"Shi dae Malam Kabeeru baban Suraj, ni kae na nayi mamakin tafiyar tasu kamar wad'anda ake kora, babu wanda suka yi sallama da su se wad'anda suka gansu sanda suke k'ok'arin barin layin nan, kuma har yanzu maganar da nake maka bamu san takamaemae dalilin barin su garin nan ba"

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shine kawae abinda Abba ke maemaetawa a cikin zuciyar sa, yayin da mutumin ya kalle shi cikin mamakin ganin yadda Abban yayi shiru bece komae ba amma gaba d'aya yanayin sa ya nuna yana cikin tashin hankali, d'an baya kad'an Abban yayi zuciyar sa na wani irin bugawa da k'arfin gaske

"Subhanallahi" mutumin ya fad'a yana rik'o Abban, da sauri Abba ya nemi waje ya zauna dan yadda yaji kansa na wani irin juya masa ga wani jiri da lokaci d'aya ya nemi ya kayar dashi

"Lafiya dae koh?" mutumin ya fad'a yana nazarin yanayin Abban, cikin k'arfin hali Abba ya furta

"Lafiya k'alau, Nagode"

"Babu damuwa" mutumin ya fad'a yana yin gaba. Seda Abba ya k'ara wajen minti 20 a wajen sannan ya mik'e zuciyar sa a cunkushe, yama rasa meya kamata yayi tunani, anya kuwa da gaske Kabeerun guduwa yayi masa da kud'i da takaddun sa masu muhimmaci? Anya kuwa ya kamata ya yadda da wannan maganar? Yana so ta k'aryata hakan se dae kuma duk wasu alamu dake nuna Abbun guduwa yayi sun bayyana

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" ya sake maemaetawa sanda ya ida fitowa titi, sam bashi da k'arfin gwuiwar yin tuk'i dan haka bebi takan fire service da yake ajje motar sa ba ya tari mota wadda zata kae shi tasha ya hau motar Kano.. Ko a cikin motar ma gaba d'aya zuciya da k'wak'walwar sa sun kasa sukuni, so yake ya gane cewa mafarki ya yi ba gaskiya bane ace Kabeeru wae ya gudar masa da dukiyar daya dad'e yana tarawa wata da watanni, takaddun karatun sa daya dad'e yana yi shekara da shekaru, anya kuwa ba'a chanja Kabeerun ba, Kabeeru mutum me kirki mutunci da kawaeci, rik'on amanar da shine ya zamo abinda ya birge Abban har ya koma yana masa kallan d'an uwa, kamar d'an uwan da suka fito ciki d'aya, yana ganin kamar ya samu wanda ze iya kular masa da dukiya koda baya wajen, wanda ze rik'e masa amana ko da a bayan idanun sa ne, se dae kashh ashe be sani ba duk wannan a banza ne, ashe Abbun ya yaudare shi ne da halayen bogi, yayi amfani da yaddar daya bashi ya yanke shi son ransa, ashe tun farko akwae k'udurin da yake son cikawa shiyasa ya kwantar da kae, ya nuna kamar shi na Allah ne

"Meyasa zaka min haka Kabeeru?" Abba ya fad'a a fili yana dafe da k'irjin sa da har lokacin yake jin ya masa wani irin nauyi.


... Bin Abban tayi da kallo sanda ya shigo cikin gidan, a hankali ta bud'e baki ta amsa sallamar sa da taji yayi ta a hankali, seta mik'e tana goge hannayen ta daga cikin ruwan d'aurayar wanke wanke ta k'araso tana kallan sa tace

"Sannu da zuwa Abban su"

"Yawwah.." ya fad'a yana yin gaba, haka nan kawae taji zuciyar ta ta buga, seta lumshe idanun ta a ranta tana fatan Allah yasa ba wani mummunan abun ne ya faru ba, a hankali ta yaye labulen d'akin ta shiga da sallama seta nemi gefen gadon ta zauna tana cigaba da kallan sa tace

"Ko na had'a maka ruwan wanka ne?" girgiza kae Abba yayi kafin yace

"A'ah" cike da damuwa ta furta

"Abban su lafiya dae koh?" Abba ya runtse idanun sa yana jin zafin abinda ze fito daga bakin sa

"Kabeeru.." tun kafin Umma taji k'arshen maganar ta dafe k'irjin ta dan ita ta d'auka ko wani abun ne ya samu Kabeerun, se dae sa6anin abinda tayi tsammani se taji Abban yace

"Kabeeru yaci amana ta, ya tattara kayan sa ya gudu da kud'ad'en nan da kuma takaddu na.." runtse idanun ta Umma tayi a ranta tana fatan ta bud'e idanu taga ba gaskiya bane abinda take ji a kunnuwan ta ko kuma ya kasance mafarki ne take yi, se dae har zuwa sanda ta bud'e idanun ta se taga Abban a yadda ta barshi

"Anya kuwa Abban su?" ta fad'a cikin k'arfin gwuiwa, murmurshin takaeci Abba yayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo kana yace

"Tabbas haka ne, ban dawo gidan nan ba seda na bincika, har unguwar su naje aka tabbatar min a jiyan shima ya bar garin shi da iyalin sa"

"Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun" Umma ta shiga nanatawa tana kallan Abban tana jin da wani ne ya fad'a mata wannan zancen har abada ba zata ta6a yarda ba

"Abban su.. Abbun Raj fa kake magana, mutumin da kullum zancen sa a bakin ka baya wuce na alkhaeri kirkin sa da kuma rik'on amanar sa, koda sau d'aya ban ta6a jin ka fad'i aebun sa ba, se dae gashi yau ina jin wata magana mara dad'i akansa tana fitowa daga bakin ka, Abban su kana nufin duka kud'ad'en nan ya gudu dasu don Allah.."

"Toh ina suke Ruk'ayya? ae yanzu kinga irin sakayyar da yayi min na d'aukar amana ta da nayi na bashi koh?" wani numfashi me zafi Umma taja ta fesar sannan ta sake yin salati, daga nan kuma tayi shiru ta kasa cewa komae, dan kwata kwata ma bata san me za tace ba, mamakin ta d'aya yadda Abban da kansa yake fad'in Abbu ya gudu da kud'in sa, abin kamar almara, gaba d'aya k'wak'walwar ta ta tafi can tana mata bitar alak'ar Abban da kuma Abbu....


Sanda Yah Sadeeq yaji zancen nan seda yayi kuka sosae cikin tausayin Abban nasa, yana tuna irin gwagwarmayar da Abban yasha kafin ya samu wannan damar amma lokaci d'aya wani yazo yayi masa awon gaba da komae nasa, ya kuma yi alawadae da hali irin na Abbu, ya kalli Umma dake zaune ta jinginar da kanta kan kujera kamar me tunani

"Umma bansan meyasa ba ni gaba d'aya daga shi Raj d'in har mahaefin sa ba suyi min ba Umma, Umma mutumin nan ya cuci Abba ya cuce mu, Allah ya isar mana wallahi" kallan sa Umma tayi, bata jin komae idan ta tattauna magana da Yah Sadeeq d'in dan k'ananun shekarun sa basu hana shi hankali ba, idan yayi wani abun kamar wani babban mutum tace

"Bama seka fad'a ba Sadeeq, sakayya kam se Allah yayi mana ita, shi kuma yaje ya gani idan haram wata abace" dae_dae lokacin da Ayrah ta shigo d'akin ta k'arasa ta kwanta akan cinyar Umma kamar zata fashe da kuka ta furta

"Umma Raj.." Yah Sadeeq dake zaune kujerar kusa da Umma ne ya janyo ta da k'arfi cikin fad'a yace

"Wallahi idan kika sake mana maganar Raj a cikin gidan nan sena miki duka kinji na fad'a miki" ya fad'a yana d'aga hannu kamar ze mare ta, kuka ta fashe dashi kamar wadda ya ida dukan nata, Umma ta kae hannu ta rik'o ta ta d'auke ta zuwa kan cinyar ta ta kwantar sannan ta kalli Yah Sadeeq tace

"Ita me ta sani? Wannan fad'an babu abinda ze janyo se rigimar ta kasan hali dae"

"Umma ba duk itace ta janyo ba, da bata san Raj d'in bama ta yaya Abba ze had'u da baban sa ballantana har ya cuce shi" Umma na cigaba da rarrashin Ayrah tace a nutse

"Ya zamu yi da k'addara Sadeeq?"


... Sau wajen 3 Umman na farkawa daga baccin da babu dad'i cikin sa se tarin damuwa da tunanun nuka tana ganin Abban zaune babu alamar zeyi bacci, se daga k'arshe dae ta kasa shiru tace

"Kayi hak'uri Abban su don Allah kayi bacci, kada damuwa ta maka yawa.." Abba ya lumshe idanun sa, baya tunanin ko awa nawa zeyi zae iya yin wani bacci, amma dan ya kwantar mata da hankali ya sanya shi fad'in yana gyara zaman sa

"Toh shikenan, yanzu zan kwanta kiyi baccin ki.."


... Wasa wasa wajen kwana 3 kenan Abban baya samun yin bacci, shi kansa besan dalili ba dan ko yayi niyyar yin baccin baya samu yazo masa, se dae kawae ya kwanta yayi ta tunani, zuwa lokacin tunani ya zama kamar wani mahad'in rayuwar sa ne dan kuwa in dae ze zauna toh fa zeyi tunanin nan ne, har kuma zuwa lokacin mamaki yak'i sakar shi, ga Kabeerun da kullum da shi yake kwana yake tashi, duk da guduwa da kud'in da Abbu yayi ya masa zafi amma be kae zafin yadda ya d'auki duk wata yadda tasa ya dank'awa Abbun ba amma daga k'arshe yaci amanar sa, ya yaudare shi, gefe guda kuma tunanin halin da zasu shiga a yanzun yake, yana ganin kamar rayuwa na gab da juya musu baya, babu sana'a, babu takaddar da ze iya zuwa ya nemi aeki, ga kud'in da Alhaji mato yake bin sa, duka tunanin sa yafi karkata nan 6arin ne

"Allah ka bani ikon cinye wad'annan jarabobin" Abban ya fad'a akan la66an sa, yana jin wani irin rauni a tattare dashi....




https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 007_008


___Washe gari wajen k'arfe 8 na safe Abba na zaune cikin parlourn yana yin iya bakin k'ok'arin sa dan kada iyalan nasa su fahimci damuwar da yake ciki se ga kiran Alhaji Mato a wayar sa, ya kalli wayar na tsawon sakanni sannan ya d'aga ya kara ta a kunnen sa, daga can 6angaren Alhaji Mato yace

"Haji Ibraheem na jika shiru kwana 2 yasa nace bari na ta6o ka" d'an numfashi kad'an Abba ya sauke sannan yace

"Wallahi kuwa, nima ina ta k'ok'arin kiran ka se kuma na sha'afa, dama zuwa anjima nake so nazo wajen naka, ina so ka sake min kwantance"

"Toh toh Madallah.." Alhaji Maton ya fad'a yana d'orawa da yiwa Abban kwatance, Umma ta kalle shi sanda ya gama wayar tace a nutse

"Yanzu ya za'ayi da shi kenan?" seda Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Zan fad'a masa gaskiya ne, idan ya yadda da k'addara shikenan idan kuma be amince ba yace sena biya shi kud'in sa se nasan yadda za'ayi.."

"Toh Allah Ubangiji yasa ma shima ya kar6i wannan k'addarar"

"Ameen" Abba ya fad'a ba dan yana da tabbacin hakan ba, dan shi sheda ne akan son kud'i irin na Alhaji Maton.



.. Shiru Alhaji Maton yayi har Abba ya gama masa bayanin abinda ya faru, se yayi murmushi yana girgiza kae kana ya d'aga kae ya kalli Abba yace

"Haji Khaleel ni fa gani nake ko menene ya faru kae ka jawa kanka, ba sau d'aya ba ba sau biyu ba na fad'a maka na kuma baka shawara ka rabu da matar ka, farar k'afa gare ta, an kore ka daga banki, kazo ka fara teaching an dakatar da kae ka fara kasuwanci wani ya gudu da kud'in wannan kad'ae be ishe ka ka gane.."

"Malam ya ishe ni haka!" Abba

Please Login or Register in order to submit comment