Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanya ta tunanin tabbas shi da Yah Sadeeq suka zo dan haka da sauri ta kalli Jidda tace

"Mu dae mun tafi" ta fad'a tana Allah Allah Jidda ta amsa ta fice daga d'akin

"Ba zaki tsaya kiyi sallama dasu Ruks ba?" 6ata fuska tayi sannan tace bayan ta girgiza kae

"A'ah ki fad'a musu na tafi ni dae, se an dawo hutu bye.." ta fad'a tana ficewa daga d'akin

"Toh Allah ya kaemu" shine abinda Jidda ta fad'a tana bin Ayrah da kallo sanda ta fice daga d'akin cikin d'oki kae seka rantse tafi shekara ba taga Abban ba. Sosae taji dad'in ganin Abban dan murna gaba d'aya ta kasa dena murmushi se dae tayi mamakin rashin ganin Yah Sadeeq tare da Abban, dan haka ta kasa shiru seda tace

"Abba Yah Sadeeq fa?"

"Yah Sadeeq na gida, kin san yanayin aekin su hutu yake shiyasa.." se tayi murmushi, a yanzu da taga Abba se d'okin nata kuma ya koma na son ganin Yah Sadeeq da Umma, suna tafiya a hanya suna hira sosae cike da farin ciki da kewar juna, Abban ya zage yana jan d'iyar ta sa da hira, se dae da yake basu kad'ae ne a cikin motar ba ya sanya yawanci hirar tasu bata wuce akan karatu.




... Da wani sauri Bahijja ta turo k'ofar d'akin hannun ta d'auke da wayar Abeeda, Abeeda da Ruks suka biyo bayan ta, idanun ta a warwaje ta furta

"Ina Ayrah take?" tayi maganar cikin d'aga murya, da mamaki Jidda ke kallan ta yadda take a wani birkice kamar mahaukaciya tace

"Meya faru?"

"Ke dae ina take kawae?"

"Yanzun nan aka zo aka d'auke ta" Jidda ta fad'a sannan ta d'ora da

"Pls meya faru?" komawa Bahijja tayi ta zauna, tana tuna yau da taga Ayrah a cikin d'akin nan babu abinda ze hana ta shak'e ta ko zata ji sauk'in abinda take ji a cikin zuciyar ta, kar6ar wayar hannun ta Ruks tayi sannan ta mik'awa Jidda tace

"Kalla ki gani" hannu Jidda ta saka ta kar6i wayar sannan ta shiga kallan hoton sannu a hankali, tana kae hannun ta tana zooming, ta kae wajen minti 1 tana kallan hoton sannan ta d'ago ta kalle su cike da mamaki akan fuskar ta

"Kenan abinda Abeeda ta fad'a gaskiya ne?" tayi tambayar tana kallan su su duka, kamar wata k'adangaruwa Bahijja ta shiga girgiza kae tana jin kamar ta rusa ihu

"Shegiyar yarinya ta cuce mu, dama seda nayi tunanin kyawun ta ze iya rud'ar shi, ashe mu bamu sani ba ma sun dad'e suna soyayyar su amma shegiyar yarinya seta dinga nuna kamar ma tsanar sa tayi, bamu sani ba ashe wawaye sakarkaru ta maeda mu, k'aramar yarinya tayi wasa da tunanin mu kenan?" ajiyar zuciya Jidda ta sauke kana tace

"Lallae kam, ni kae na abin ya bani mamaki wallahi, yaushe muna zaune har hakan ta faru bamu sani ba? Ya akayi hakan?" tayi maganar cike da mamakin dae, girgiza kae Ruks tayi kafin tace

"Wallahi ku bari kawae, ni dan mamaki ma na rasa wane tunani ya kamata nayi" Abeeda tace

"Ahh toh, ni kae na nasan amanar ku akaci shiyasa naga bazan k'yale ba gwara na sanar daku"

"Aekuwa wallahi za taci uwar ta yarinyar nan" Bahijja ta fad'a dan tana ganin kamar duk tafi su takaeci da abinda Ayrahn ta aekata musu, ta shammace su, tayi wasa da hankalin su, ta kuma nuna musu yawan shekaru ba shine wayo ba.


.. Da sallama ya shiga d'akin yana sanye cikin wasu k'ananan kaya masu kyau da taushi, kan sa d'auke da facing cap data matuk'ar k'awata shigar sa ya fito yayi kyau abin sa, cikin sa'a seya samu Mummy har ma da Daddy a d'akin, ba k'aramin dad'in ganin hakan yayi ba, dan haka ya k'arasa ya zauna k'asan Carpet yace

"Barkan ku da warhaka"

"Barka kadae" suka had'a baki wajen fad'in hakan

"Daddy dama inaso ne na shaeda maka yau zan koma Kano"

"Kano kuma Likita? Wani abu ne ya faru?" seya girgiza kae kawae yana d'an lumshe idanun sa kad'an bece komae ba har zuwa sanda Mummy tace

"Haba kae kuwa Raj, gaggawar ta me ce?"

"A'ah Mummy.." shine abinda kawae ya fad'a, Daddy yace

"Ko dae akwae abinda zaka yi ne acan d'in?" tambayar Daddyn ta matuk'ar yi masa dad'i dan haka da sauri ya furta

"Ehh Daddy, akwae wani abu me muhimmanci da zan gabatar acan d'in.."

"Toh shikenan babu damuwa, akwae maganar ma dama da zaku yi da Abbun naka.." be bawa zancen muhimmanci ba dan haka kawae abinda yace shine

"Tohm"

"Allah yayi maka albarka kaji Doctor, Allah kuma ya sanya albarka" shine abinda Mummy tace

"Ameen" kawae yace duk da ita kan ta be gane akan maganar da take magana ba, ya dae fi tunanin itama taji labarin ajiye aekin da zeyi ne yasa take magana fatan alkhaeri, seya mik'e hannun sa d'aya cikin aljihun sa yace bayan yayi murmushi

"Daddy bari naje na sake shiryawa"

"Toh Raj, seka fito" daga haka ya fice daga d'akin.



.. Ko jakar ta bata iya d'auka ba ta fad'a cikin gidan nasu da gudu tana kwad'a sallama da siririyar muryar ta, wani sanyi Umma taji ya ratsa ta jin muryar shalelen er tata, kafin ma ta kae ga k'arasowa Umman ta fito daga cikin d'akin ta, aekuwa tana shigowa ba tayi wata wata ba ta fad'a jikin Umman tana sakin dariya lokaci d'aya tana furta

"Nayi kewar ki sosae Umma ta" murmushi Umma tayi ita kan ta tasan tayi kewar d'iyar ta ta sosae, dan haka itana ta rungume ta tana fad'in

"Yanzu ae gani gaki koh?" seta jinjina kae har lokacin tana jikin Umma, sun kae wajen minti 1 a haka sannan Ayrah ta saki Umma tana fad'in

"Umma ina Yah Sadeeq?"

"Yana d'aki bacci yake" Umma ta fad'a tana kallan d'iyar ta ta

"Umma wallahi yanzu Yah Sadeeq ya zama malalaci, kullum cikin bacci" ta fad'a lokacin data shiga d'akin nasa, seta hange shi kwance kan gadon idanun sa a rufe ya lullu6e rabin jikin sa da bargo, se tayi murmushi tana jin dad'in ganin sa sannan ta k'arasa ciki tana fad'in

"Yah Sadeeq ka tashi, na dawo" kamar daga sama ya jiyo muryar lilin ta sa, dan haka a hankali ya bud'e idanun sa se kuwa ya sauke su a kan ta, murmushi suka sakarwa junan su sannan Yah Sadeeq yace

"Yanzu kuka shigo?"

"Ehh Yah Sadeeq nayi kewar ka wallahi" ta fad'a tana 6ata fuska, dariya yayi yana jin dad'in ganin k'anwar ta sa dan shi kan sa yayi kewar ta irin sosae d'in nan

"Nayi kewar rigimar nan taki Auta" ya fad'a har lokacin yana murmushi

"Kae Yah Sadeeq rigima kuma?" ta fad'a har lokacin dae tana 6ata fuska gami da tura baki

"Toh shikenan dae ya hanya?" ya fad'a yana k'ok'arin tashi zaune, shi kan sa baya so ta gane karaya ce a k'afar sa dan ya riga yasan halin ta yanzun nan zata fishi shiga damuwa, se akayi sa'a ma tace

"Yah Sadeeq kayi baccin toh, idan ka tashi se muyi hirar" ta fad'a tana kallan sa, seya koma ya kwanta ba dan yana tunanin ze iya baccin ba sannan yace

"Toh shikenan Auta.."

"Yawwah Yah Sadeeq" ta fad'a tana ficewa daga d'akin tana fad'in

"Umma kin ga lalacin Yah Sadeeq d'in koh? Ya sake komawa baccin" ta fad'a tana k'arasawa tsakar gidan, dae_dae lokacin da Umma take fad'in

"Za dae a tantance malalacin" turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace

"Kae Umma" dariya Umma tayi tana fad'in

"Toh shikenan, ina Abban?"

"Aou" ta fad'a bayan ta kae hannun ta kan bakin ta sannan tace

"Allah sarki Umma k'anwar Zaenab ce ta rasu shine ya tafi za'a kae ta"

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun, ashe ta rasu? Toh Allah ya ji k'an ta, ashe ba mazauniya bace" Umma ta fad'a tana tuna yarinyar data rasun wadda ba tafi wata 5 da haehuwa ba, k'arasowa Ayrah tayi ta zauna kan tabarmar da Umma ta shimfid'a, seda Umma ta zauna sannan ta d'ora kan ta akan cinyar Umman tace

"Umma nazo muku da wani albishir, amma bazan fad'a ba se Abba ya dawo"

"Wane albishir ne wannan?"

"A'ah Umma se Abba da ya dawo" Ayrahn ta fad'a tana sake gyara kwanciyar ta kan cinyar Umma

"Toh shikenan, ya exam ya karatun?"

"Umma komae Alhamdulillah fa" ta fad'a tana murmushi, daga haka suka cigaba da hira, Umma nata jin labaran da Ayrahn ke ta bata, wani tayi dariya wani ta girgiza kae cike da ganin wautar Ayrahn, se dae lokaci lokaci ta kan yi shiru ta saki murmushi me k'ayatarwa idan ta tuna Rk, Umman na lura da ita amma har lokacin tak'i fad'awa Umma komae game da albishir d'in da tace zata yi musu, dan haka itama ta mata shiru kawae tana cigaba da saurarar hirar da take mata.



... A 6angaren Rk kuwa dab da maghrib ya isa gidan nasu cikin motar sa, k'atuwar harabar gida dake d'auke da manya manyan motoci a gefe guda, shuke shuke da sauran abubuwa na burgewa, kae tsaye parking lot d'in ya wuce da motar sa yayi parking nata dae_dae lokacin da wani ya k'araso da sauri yana fad'in

"Barka da dawowa yalla6ae" ya fad'a yana duk'awa

"Barka, a shigar min da kaya ciki" shine abinda Rk ya fad'a yana wucewa cikin tafiyar nan tasa ta nutsuwa hannun sa d'aya cikin aljihun sa, tafiya me tsayi ce yayi kafin ta sada shi da aenahin inda d'aku nan masu gidan yake, yayi murmushi sanda ya ganshi a k'ofar Parlourn Ummeen sa, babu 6ata lokaci ya sanya k'afar sa cikin k'aton hamshak'in Parlourn da sallama, Ummee na zaune kan kujera hannun ta d'auke da remote tana shirin chanja channel yayi sallama, seta ajje remote d'in akan kujera tana kallan sa sanda wani k'awataccen murmushi ya su6uce a fuskar ta tace tana k'arasawa inda yake

"Oyoyo Oyoyo.." k'arasawa yayi inda take yayi hugging nata sannan ya zauna a k'asan kujerar yace cikin girmamawa

"Ummee barka da wannan lokacin"

"Barka dae ya hanya?"

"Hanya Alhamdulillah" ya fad'a dae_dae sanda aka k'walla kiran Sallah a masallacin su dake jikin gidan nasu, se yayi saurin mik'ewa yana fad'in

"Ummee bari naje"

"Toh Raj seka dawo" ta fad'a tana bin sa da kallo har lokacin da murmushi kan fuskar ta. A harabar gidan suka yi kaci6us da Abbu dake sanye cikin wata dakakkiyar bluen shadda d'inkin babbar riga data matuk'ar yi masa kwarjini

"Welcome my Son" Abbu ya fad'a yana bud'a hannun sa, Rk ya k'arasa yayi hugging mahaefin nasa sannan yace

"Barka da wannan lokacin Abbu"

"Barka dae Raj, ka dawo ashe? Mu wuce masallaci dae tukunna" babu 6ata lokaci suka wuce masallacin dake jikin gidan su, ana Sallahr Isha'i Rk ya koma gida saboda yadda yake so ya watsa ruwa a jikin sa yayin da ya bar Abbun a masallaci.



Cigaban nan wajen yana page 1, yanzu haka mun ji TUSHEN LABARIN MU dan haka zamu d'ora ne da CIGABAN LABARI....



... "Shin yanzu kin san wanene Raj d'in da kike magana a kan sa? Waye mahaefin sa? Meya aekatawa rayuwar ku? Mahaefin ku ya amince masa ya bashi amanar da be ta6a bawa wani ba amma daga k'arshe ya wulak'antashi ya tozarta shi yayi wancakali da duk wannan amanar, mahaefin ki ya d'auko shi daga rana ya sanya shi a inuwa amma daya tashi dame ya saka mishi? Seya d'auki mahaefin ki ya jefa shi cikin ranar shi kuma ya cigaba da rayuwar sa ba tare da tunanin halin da zamu iya shiga mu dukan mu ba, Yanzu haka Sadeeq na kwance ne a d'aki sakamakon karayar daya samu ana buk'atar a masa aeki amma babu kud'in aekin, mahaefin Raj ya cuci Abban ku, ya raba shi da dukiyar sa, takaddun sa masu muhimmanci, uwa uba kuma shine silar shigar mu cikin kowanne hali, silar abinda ya aekatawa mahaefin ku ne ya janyo masa hawan jini, ya cuce mu mu kan mu akan son zuciyar sa, ta yaya zan miki wannan bayanin a wancan lokacin ki fahimta? Ina k'wak'walwar ki take ta k'arfin fahimtar wannan zancen?" Umma ta k'arashe maganar tana kallan Ayrah da tunda ta fara maganar ba tace komae ba, idanun ta gaba d'aya Umma suke kalla har lokacin tana cigaba da tuno maganar Umman cikin kunnuwan ta wanda take jin su kamar amsa kuwwa suke mata a kunnen ta, dan kuwa duk da Umman tayi shiru hakan be hana ta cigaba da jiyo sautin muryar Umman a kunnen ta ba, kunnen nata ya mata wani duumm kamar wadda ta kurumce banda sautin muryar Umman babu abinda take ji har yanzun, bata ma sani ba ko Umman ta cigaba da fad'a mata magana ko tayi shiru ne ita dae bata sani ba, abinda kawae ta sani maganganun nan da suka sanya ta cikin sani irin shock da kuma hutun da k'wak'walwar ta ta tafi na wucin gadi su kad'ae keta dawo mata, jikin ta wani irin rawa yake yi kamar me jin sanyi, duk da idanun ta ba'a rufe suke ba amma se take so ta sake bud'e su tarr ko dan ta cigaba da kallan Umman da yanzun take ganin ta dishi dishi, gaba d'aya ta kasa koda bud'e bakin ta ne ballantana ta furta wani abun, koda yake idan ta bud'e d'in ma menene za tace??



Mhiz Innocent......✍️


https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 027_028



___Ganin da Umma tayi har lokacin Ayrah ta gaza furta komae ya sanya ta sanya hannu ta share idanun ta itama da k'wallar ta gama tarar mata, kawae seta juya a hankali ta fice daga d'akin dan ta bar Ayrahn ta dawo daga shock d'in data shiga, ta san dole abin ya ta6a ta aenun, bata ta6a zata ba ba kuma ta ta6a tsammani ba se gashi rana tsaka taji dalilin rabuwar Abba da Abbun Raj. Ko d'aga ido ta kalli Umman ta kasa yi sanda Umman ta fice daga d'akin, ita bama ta lura ta fita ba dan kuwa har zuwa lokacin ta kasa gasgata duk maganganun nan da Umma take fad'a ba mafarki bane "Abbun Raj fa" shine abinda ta dinga maemaetawa a cikin ran ta tana so ta hasaso fuskar sa amma ta kasa dan shekarun nada yawa, ga kuma yanayin shekarun ta a lokacin, amma tabbas idan har bata manta ba mutumin ya zo wa Abban ta a matsayin mutumin kirki, bata san menene ya had'a su ba se gashi yau Umma ta bankad'a mata komae taji dalilin Abba na cewa ba zata auri Raj ba, tabbas in dae kuwa haka ne dalilin Abban yana da gaskiya, a hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin zafi a cikin zuciyar ta, sosae zuciyar ta ke zafi wanda har ta numfashin ta seda ya koma fita da zafi, se a lokacin taji wani kuka ya taho mata, bata hana fitowar kukan ba se kawae ta jefar da jikin ta kan gadon ta fashe da wani irin kuka, a hankali take dukan kan ta akan pillown kan gadon tana jin wata iriyar nadama da danasani na lullu6e ta, kunyar abinda ta fad'awa Abba d'azu na sake k'arawa yanayin da take ciki k'aemi, wani irin kuka take wanda ke fitowa daga can k'asan ran ta, kukan nadama, kukan danasani, kukan rashin sanin mafita, a yau d'aya taji tayi danasanin sanin Rk a rayuwar ta, meyasa ma ta san shi? Meyasa tayi silar zuwan sa wajen Abba? Meyasa ta zamo silar da Abba ya janyo mahaefin sa cikin jikin sa? Yanzu kenan itace silar komae? Itace ta janyo komae? Meyasa tayi hakan? Gani take kamar komae ya faru itace me laefi tunda ita ta kawo Rk d'in

"Nice silar komae!" ta fad'a sanda take sake sakin wani kukan me cin rae

"Tabbas nice sila, dan da ban san Raj ba Abba baze ta6a sanin Abbun sa ba, ni na janyo Abba ya jawo Abbu a jikin sa har me faruwa ta faru, nayi danasanin sanin ka a rayuwa ta Raj!" ta k'arashe maganar tana cigaba da kukan da har muryar ta ta fara dashewa, yau mamaki na neman kashe ta, wae Abbu ne ya cuci Abba, Abbu ne sanadiyyar tarwatsewar farin cikin su, Abbu ne sanadiyyar saka damuwa a zukatan iyayen ta, Abbu ne sanadiyyar abubuwa da dama da suka faru a rayuwar su, shi kam yanzu menene zece musu su yafe masa? A hankali ta sake komawa ta kwanta har lokacin ta kasa tsaeda kukan da take, haka zalika zafin da zuciyar ta yake yak'i raguwa sema k'aruwa da yake yi, ta rasa yadda za tayi, ji take dama zata iya janyo abinda ya faru ada ta goge komae akan alak'ar ta da Rk, da kuma ana iya tariyo baya data hana kan ta had'uwa da Rk, Yah Sadeeq ne ya fad'o mata, se taji wata sabuwar k'walla ta zubo mata, ta sanya hannu ta d'auke ta lokaci d'aya tana lumshe idanun ta, bata da k'arfin da zata iya tashi yanzu haka taje ta duba jikin sa, amma ita kad'ae tasan abinda take ji a cikin jiki rae da kuma zuciyar ta.


... "Don Allah Alhaji kayi hak'uri ka bari ko zuwa gobe ne, kaga ko hutawa ba kayi ba" Muttala ya fad'a yana kallan Alhajin daya fito daga d'akin sa cikin wata bugaggiyar shadda d'inkin babbar riga, juyawa yayi ya kalli Muttala sannan yace har lokacin be tsaya ba

"Wallahi bazan iya hak'ura se gobe ba, gwara ma ka k'yale ni kawae" yayi maganar sanda ya isa motar sa, ya bud'e ya shiga sannan ya kalli Muttala yace

"Zaka raka ni ne ko kuma in nemi wani?" seya girgiza kae sannan ya k'arasa ya bud'e wajen me zaman banza ya shiga ya kalle shi cike da girmamawa yace

"Yalla6ae daka bari dae ko zuwa goben ne kada su fahimci wani abun!" wani kallo Alhajin ya jefa masa se kuma yayi murmushi wanda ya sake k'ank'antar da jajayen idanun sa

"Tunda kaga zan yi driving da kae na kasan abu ne me muhimmanci, na kasa jurewa gwara naje ko nan sati 1 ne a d'aura mana aure idan yaso seta cigaba da karatun a cikin gida na" jin maganar da Alhajin ya fad'a ne ya sanya Muttala jinjina kae kawae, bece komae ba har zuwa sanda Alhajin ya tayar da motar sa suka fice daga gidan. A k'ofar gidan yayi parking motar ta sa, sannan ya kashe ta ya kalli Muttala da tunda suka fara tafiya har yanzu be sake cewa komae ba yace

"Yi mana sallama da shi pls" seya kalli Alhajin sannan yace bayan ya girgiza kae

"A'ah fa Yalla6ae kada ka manta sirikin ka ne, ina ganin gwara ka fito ko kan dakalin can ne seka zauna" Muttala ya fad'a yana nuna wani dakali dake a k'ofar gidan dake kusa da nasu Ayrah, shiru Alhajin yayi kamar ba zece komae ba se kuma can yace

"Toh yanzu kae dae je ka" yayi maganar yana sanya hannun sa ya bud'e k'ofar, kusan a tare suka fito, Alhajin ya kalli wajen yana yamutsa fuska sannan ya zauna yayin da Muttala ya tsaya k'ofar gidan ya k'wala sallama, daga can cikin gidan Abba ya amsa yana mik'ewa ya zura takalmin sa ya fito daga d'akin nasa, k'arasowa yayi yana kallan Muttala ganin da yayi be shaida fuskar ba, se dae ya mik'a masa hannu suka gaesa sannan yace da d'an murmushi kan fuskar sa duk da yanayin da yake ciki a yau d'in na damuwa

"Se dae ban shaeda fuskar ba" murmushi shima Muttalan yayi sannan yace

"Ehh dama baka sanni ba gaskiya, ga can wanda yazo wajen ka akan wata magana me muhimmanci" yayi maganar yana nuna Alhajin dake zaune kan dakalin yana kallan wani wajen, saboda k'arancin hasken dake a wajen ya sanya Abba be iya hangar fuskar sa ba, seya dawo da duban sa ga Muttala yace

"Toh ikon Allah" ya fad'a yana yin gaba zuwa wajen da Alhajin ke zaune, dae_dae lokacin da Abban ke dab da k'arasawa wajen Alhajin haske ya kawo a wani k'wan lantarki dake k'ofar gidan dake kallan nasu, hakan ne ya bawa Abba damar ganin fuskar mutumin da akace shi ke son magana dashi, cikin son sake tabbatarwa ya sake bud'e idanun sa dan ganin da gaske fuskar da yake gani ita d'in ce ko kuwa dae? Shi kan sa Alhajin kallan Abba yake with shock all over his face, se yaji gaba d'aya jikin sa ya d'auki wani mahaukacin rawa, ya had'iyi wani yawu da k'yar sannan yace bayan ya mik'a masa hannu

"Kae ne mahaefin Ayrah?" Alhajin ya fad'a yana kallan Abba, a ran sa yana tuna cikakken sunan Ayrahn, tabbas da gaske shine mahaefin ta, amma dae gwara ya tabbatar ta hanyar ji daga bakin Abban, da mamaki Abba ke kallan sa jin maganar da yayi, meya kawo zancen Ayrah a tsakanin su kuma?

"Meya kawo ka k'ofar gida na?" Abba ya fad'a yana kallan sa fuskar sa a d'inke tsaff, jikin sa ya sake wani sanyi wata zufa na karyo masa yace bayan yayi k'asa da muryar sa

"Kayi hak'uri mu zauna sena maka bayani, wallahi ba tashin hankali ne ya kawo ni wajen ka ba"

"Alhaji Mato!" Abba ya fad'a cikin er d'aga murya, a ran sa Abba na sak'a lallae duk abinda Alhaji Maton yazo da shi me girma ne

"Bani da lokacin 6atawa, idan ba kada abin fad'a na shige gida" Wani yawun Alhaji Mato ya sake had'iyewa shi kan sa yana tunanin ta ina ma ze fara sanarwa da Abban son er sa yake? So na aure, ganin dae da gaske Abban yake idan bece wani abu ba ze iya tafiya ya k'yale shi ya sanya shi fad'in

"Wallahi abin alkhaeri ne ya kawo ni, d'iyar ka na gani kuma ina son ta da aure shine kawae abinda ya kawo ni, kuma kada ka damu wancan lokacin akasi aka samu na fad'i magana saboda 6acin rae amma zan dawo maka da kud'in daka biya ni, kuma zan baka sana'ar da zaka dinga yi kana.... "


"Dakata Alhaji Mato" Abba ya fad'a bayan ya d'aga masa hannu, zuciyar sa na wani irin zafi da jin kalaman Alhaji Maton na son zuciya

"Kada na sake ganin k'afar ka a k'ofar gidan nan, kud'i kuma har abada na riga na biya ka kuma bazan ta6a kar6a ba, saboda haka kada ka sake tunanin zan d'auki 'ya ta in baka ita bayan na san wanene kae, ka cire wannan ma a cikin ran ka" daga haka Abba ya juya yana jin wani jiri jiri na d'ibar sa kamar ze fad'i, da kallo Alhaji Mato ya bishi zuciyar sa na wani irin tafasa, lallae yau ya kuma yadda Abban matsiyaci ne, be san me ake kira da arzik'i ba, har yanzu dae yana zaune cikin duhun kae, har abada ma baya tunanin Abban nada rabon arzik'i a rayuwar sa, tunda gashi yanzu arzik'in ya biyo shi har gida amma ya saka k'afa yayi fatali dashi saboda wani banzan ra'ayin sa na rik'au. Seda Abba ya shiga gida sannan Muttala ya kalli Alhaji Mato cikin mamaki yace

"Yalla6ae wae dama ka san shi ne?"

"Bar shashasha me k'ashin tsiya, arzik'i na kiran sa yana guduwa, wani k'aramin abu ne ya ta6a shiga tsakanin mu amma da yake zuciya ce dashi irin ta kafirae ya kasa mantawa, toh se yayi tayi ae, ba dae er sa bace na gani ina so kuma sena aure ta, dan kuwa ban ta6a ganin abu inaso ban same shi ba, kuma baza a fara akan ta er talakawa ma da ita ba, ko da amincewar sa ko babu wallahi sena aure ta.. Wuce muje.." ya fad'a yana huci sanda ya k'arasa ya bud'e motar sa ya shige, Muttala ma ya shiga, Alhaji Mato yaja motar da wani irin gudu kamar ze tashi sama.

.. Akan la66an sa kawae Abba yayi sallamar dan baya jin ze iya d'aga murya sosae saboda yadda yake jin jikin sa, da kallo Umma ta bishi dashi sanda yake shigowa cikin d'akin, seta mik'e da sauri cikin mamakin yadda taga yanayin nasa ya sake chanjawa fiye da d'azun

"Abban su" shine abinda ta iya furtawa tana cigaba da kallan sa, Abba ya nemi waje ya zauna amma har lokacin bece komae ba, fita Umma tayi ta d'ebo ruwa me sanyi cikin randa sannan ta koma d'akin ta

Please Login or Register in order to submit comment