Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwata kwata basu samu traffic jam ba, mamaki ya sake kama shi ganin se tafiya suke yi kamar baza su dena ba, har lokacin kuma bugun da zuciyar sa take be ragu ba, haka ya cigaba da bin su zuwa lokacin da yaga sun fara barin gari suna shiga cikin wani waje daya fi masa kama da k'auye, mamaki ya sake kama shi amma da yake baya so su gane akwae wanda ke bin su seya dakata har zuwa sanda suka masa nisa sannan ya cigaba da bin su a nutse yana yi yana lumshe idanun sa saboda yadda yake jin jikin sa ya masa wani iri ga yadda bugun zuciyar sa ke ta k'aruwa. Dae-dae wani madaedaecin gida ya hango su sun yi parking d'in motar su, ze iya cewa tunda suka shigo k'auyen bega gida me kyan sa ba dan kuwa duk gidajen k'asa ne yayin da wannan d'in ya kasance ginin bulo ne, Muttala ya fita ya bud'e k'ofar gidan da mukullin hannun sa sannan ya dawo ya tashi motar zuwa cikin gidan kana ya saka mukulli jikin gate d'in sannan ya sauke ajiyar zuciya

"Da alama mun tsira fa" ya fad'a yana fesar da iska daga bakin sa, mutumin da shima ya fito daga cikin motar yace

"Wallahi kuwa, kayi maza ka kira mana Alhaji ka sanar dashi mun gama aekin mu" murmushi Muttala yayi kana ya fito da wayar sa ya lalubo number Alhaji Mato, tun kafin Alhaji Mato yace komae Muttala yace

"Yalla6ae albishirin ka?" daga inda Alhaji Mato yake ya saki wani murmushin jin dad'i yana shafa tumbin sa, ko Muttalan be fad'a ba yasan sun yi nasara, amma saboda ya sake tabbatar wa ya sanya shi fad'in

"Goro.."

"Mun gama aekin mu, yanzu haka gamu a cikin gidan yalla6ae"

"Weldone, ku jira ni yanzu zan taho.." Alhaji Mato ya fad'a yana jin wani irin dad'i na ratsa shi, yasan tabbas yau d'in Ayrah zata kwana ne a matsayin matar sa, baya shakkar wannan tunda dae an riga da an samo masa ita.





.... A 6angaren Ummee kuwa ganin har bayan wajen awa d'aya Ayrahn bata fito ba seta mik'e ta sake komawa d'akin nata, gwara ta rarrashe tan kawae ko zata samu ta saki ran ta ta cigaba da harkokin ta, a hankali ta yaye labulen d'akin idanun ta kan gadon data san akae zata sami Ayrahn, se dae ga mamakin ta babu kowa kan gadon babu ma alamar akwae mutum cikin d'akin, sauke labulen tayi a ran ta tana ayyana babu mamaki tana cikin toilet, se kuma kwanyar ta ta tuna mata ae yanzun ta fito daga ban d'akin, dan saboda ta tabbatar da gasken bata cikin band'akin ya sanya ta k'arasa toilet d'in, k'ofar sa a bud'e take amma duk da haka seda ta shiga ta duba bata ga kowa ba, k'irjin ta ya buga tana tuna yadda suka rabu da Ayrahn jiya, kada dae halin en yau zata nuna musu? Kada dae ace d'iyar ta ta ta chanja hali bata sani ba? Kada dae ace d'iyar ta ta ta za6i d'a namiji akan su? Tsara hakan cikin ran ta yasa ta sake jin jikin ta yayi mugun sanyi, a hankali taja k'afafun ta zuwa d'akin Abba, Abba ya kalle ta da mamaki ganin yanayin ta yace a hankali

"Lafiya kuwa Ruk'ayyah?"

"Bana tunanin haka" Umma ta fad'a tana jin wasu zafafan k'walla na zubo mata

"Subhanallahi, meya faru?" Umma bata tabbatar ba dan haka a ran ta taji gwara ta bari ta sake tabbatarwa ko fita tayi ta siyo wani abun dan haka seta furta

"Babu komae"

"Ya zaki ce babu komae kuma? Bayan kin fita lafiya, yanzu kuma kin dawo kina kuka?"

"Babu komae" ta sake fad'a tana cigaba da share k'wallar dake ta zubar mata. Wasa_wasa se gashi Ayrah har wajen azahar babu ita babu labarin ta zuwa lokacin tuni Umma ta gama na'am da abinda take zargi

"Ina yarinyar nan ne? Ko har yanzu baccin take?" Abba ya fad'a yana kallan Umma, kawae seta fashe da kuka tana jin wani iri a cikin zuciyar ta, a yau d'aya tana jin kamar tayi danasanin haehuwar Ayrah amma ta kasa, amma duk da haka yarinyar ta shammace ta, ta shammace ta aenun, bata ta6a tunanin hakan daga gare ta ba

"Abban su yarinyar nan ina tunanin ta gudu da wancan yaron, ashe shiyasa ta kasa ce min komae tunda taji abinda ya faru, ashe tace kya yi kya gama bazan rabu da shi ba, Abban su yarinyar nan ta bani mamaki" dafe saetin zuciyar sa Abba yayi yadda yaji ya wani irin buga, seya shiga tari, saboda tsananin tashin hankali babu wanda ya iya kula shi, seda Yah Sadeeq ya dawo daga shocking d'in da maganar Umman ta shigar dashi sannan ya d'auki ruwan gaban sa ya mik'awa Abba, kar6a Abba yayi ya sha kana ya koma sauke ajiyar zuciya, kafin ya d'ago ya kalli Umma da har lokacin take share hawaye a fuskar ta

"Waye ya fad'a miki hakan?"

"Tun d'azu na neme ta na rasa cikin gidan nan Abban su, ko ka ta6a ganin Ayrah ta fita babu izinin wani a cikin mu? Abban su yau nayi nadama.."

"Ya isa haka Ruk'ayyah" Abba ya fad'a yana d'aga mata hannu

"Bar ta taje, in dae bijirewa umarnin iyaye ne taje gata ga duniyar, kada muyi mata baki saboda ni uba ne ke kuma uwa ce kada ya kama ta, amma ni kae na yau Ayrah ta wulak'antani a rayuwa.." kallan su kawae Yah Sadeeq yake yi ya kasa cewa komae, ya kasa koda bud'e bakin sa ne ya furta wani abu, dan maganar ta shige shi, bashi da bakin da ze iya k'arya ta wannan maganar ko kuma ya musa, toh idan ya musa d'in mene hujjar sa ta yin hakan? Meze kawo a matsayin hujjar sa? Amma meyasa Ayrah zata yi haka? Meyasa zata za6i d'a namiji akan iyayen su? Iyayen da suka d'auke ta tun ciki har tazo duniya suna d'awaeniya da ita har kawo yanzun basu gaji ba? Duk wani tunanin su akan ta ne, duk wani burin su akan ta, meyasa zata saka musu ta hanyar za6ar wanda ta had'u dashi rana tsaka a rayuwar ta? Ta fifita d'a namiji akan su??.



... Yana cikin motar har lokacin idanun sa na kan gidan yana tunanin yadda zeyi ya shiga cikin gidan, idan ya tuna maza ne har biyu suka d'auki Ayrahn suka shigar da ita cikin gida se yaji wani sabon tuk'uk'i da kuma wani zafi na cigaba da azalzalar sa cikin zuciya, seya bud'e murfin motar a hankali ya zuro k'afar sa dake cikin wani had'ad'd'en takalmi hannun sa akan goshin sa yana d'an murzawa, daga ganin mutanen da suka d'auke ta kasan sanya su akayi, kuma gidan da suka kawo ta babu alamar akwae mutum a ciki, kenan idan haka ne ogan nasu ze zo kuma ze nemi a bud'e masa k'ofar dan shiga gidan

"Exactly" ya fad'a yana sake bud'e idanun sa, seda ya fesar da wata zazzafar iska daga bakin sa sannan ya cigaba da zama cikin motar har lokacin gaba d'aya hankalin sa na kan gidan gefe guda kuma yana jiran yaga ta inda wani ze 6ullo.


... Zubewa yayi a gaban me garin yana d'aga hannun sa alamar girmamawa

"Allah ya taemake ka yalla6ae" wani matashi da zeyi 25 years ya fad'a kan sa a k'asa, me garin bece komae ba ya cigaba da kallan Mubarak yana jiran jin abinda ze fad'a

"Yalla6ae acan gidan Alhaji Mato naga wasu bak'in fuska sun shiga gidan, ban ta6a ganin su ba kuma naga kamar basu da gaskiya" Mubarak ya fad'a har lokacin kan sa na a k'asa, seda me gari ya d'an numfasa sannan yace

"Gidan Alhaji Mato?" Me gari ya fad'a, Mubarak ya sake jinjina kae kana yace

"K'warae kuwa yalla6ae nima nayi mamaki" d'an shiru Me garin yayi sannan yace

"Aje a zo min dasu" ya fad'a a nutse

"An gama ranka ya dad'e" Mubarak ya fad'a yana mik'ewa ya bar wajen.


... Suna zaune a tsakar gidan Muttala ya kalli wanda suke tare yace

"Kodae mu fito da ita, kada zafi ya mata illah"

"A'ah mu k'yale ta, mu dae ba aekin da aka saka mu ba kenan? Ina ruwan mu? Gwara kawae mu jira yazo shi yasan yadda za'ayi da ita" jinjina kae Muttala yayi kana yace

"Hakane kuma" babu wanda ya k'ara cewa komae a cikin su har zuwa sanda suka ji ana knocking k'ofar, da mamaki dukan su suka yi shiru suna saurarar knocking d'in sa ake dan tabbatarwa

"Wallahi da gaske k'wank'wasawa akeyi, waye kenan?"

"Ko dae Alhajin ne ya iso?" mutumin ya tambaya yana kallan Muttala, girgiza kae Muttala yayi kafin yace

"No bana tunanin haka gaskiya, idan shine ae akwae mukulli a hannun sa" Muttala yayi maganar yana mik'ewa a hankali ya k'arasa dab da gate d'in sannan yace

"Wanene?" Mubarak ne yace

"Daga gidan Me gari ne, me gidan yana nan?" se Muttala ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"A'ah be iso ba tukun"

"Toh Me gari na neman ku" Mubarak ya sake fad'a, kallan juna Muttala suka yi shida mutumin nan sannan Muttala ya d'aga kafad'a kafin a hankali ya furta

"Babu wata matsala fa" jin abinda ya fad'a ne ya sanya mutumin k'arasawa ya bud'e gate d'in sannan suka fara k'ok'arin fitowa daga cikin gidan

"Ku kad'ae ne a cikin gidan?" Mubarak ya sake tambaya, mutumin nan na shirin cewa "Ehh" Muttala ya girgiza kae da sauri kana yace

"A'ah akwae matar Oga amma bacci take"

"A taso ta itama ta fito, Me gari ke neman ku ku duka" had'iye yawu Muttala yayi kana ya koma cikin gidan ya k'arasa ya bud'e motar cikin tunanin yadda za'ayi ta farka saboda abinda suka shak'a mata, cikin sa'a seya hango wani ruwa wanda d'azun ya sha ya ajje ragowar, da sauri ya janyo kana ya bud'e ya fara zuba mata a fuska, seda ya kusa juye mata ruwan sannan ta fara bud'e dara daran idanun ta da suka sake komawa ciki saboda wahala, a hankali ta dinga bud'e su har ta gama ware su tarr cikin motar, idanun ta suka sauka akan Muttala, da sauri ta mik'e ta fara komawa baya tana shirin sakin k'ara Muttala ya girgiza mata kae da sauri yana d'ora hannun sa akan bakin sa sannan yace a hankali ganin yadda ta gama rikicewa gaba d'aya

"Kada kice komae, kiyi shiru taemakon ki zan yi" yayi maganar har lokacin yana kallan ta, cigaba da girgiza kae tayi hannun ta d'ore akan bakin ta hawaye se sintiri suke akan fuskar ta

"Ki dena kukan taemakon ki zan yi fa" ya sake fad'a ganin kamar bata ji abinda ya fad'a da farko ba

"Kiyi shiru kada ki nuna a tsorace kike kin ji, ko me kuma za'a ce miki kada kice komae, komae kika ji an fad'a ke dae ki bisu a haka" ya fad'a a nutse dan gudun kada ta tona musu asiri a gaban jama'a, haka kawae taji tayi na'am da zancen mutumin dan haka seta jinjina kae sannan yace

"Fito muje" babu musu ta sanya k'afa ta fito se dae har lokacin k'irjin ta be bar bugawa ba haka zalika tana mamakin ko nan d'in ina ne? Waye ya kawo ta? Yaushe suka zo? Ya akayi suka zo nan d'in? Su waye su? Meyasa suka kawo ta nan d'in? Amma koma dae menene tunda wannan mutumin ze taemaka mata bari ta zubawa sarautar Allah ido, seta sake bud'e idanun ta tana kallan gidan sanda Muttala ke fad'in

"Yawwah ga ta" Mubarak ya kalle ta sannan yace

"Toh ku wuce muje" babu musu duka suka fito daga gidan sannan suka kulle, tafiya take a hankali kamar wata mara laka tana cigaba da kallan garin da be mata kama da birni ba, ji take kamar ta saka kuka amma idan ta tuna abinda mutumin ya fad'a seta d'an lumshe idanun ta ta had'iye hawayen. Tunda suka fito idanun sa ke kan su, seya saki wata k'atuwar ajiyar sanda ya hange ta ta fito daga cikin gidan tana tafiya cikin k'oshin lafiya

"Thank god" ya fad'a yana fitowa daga cikin motar gaba d'aya, seda suka kusa zuwa gidan Me garin yana hango su sannan yabi bayan su cike da tunanin inda zasu je d'in. A inda Me gari ya saba zama suka isa sannan dukkan su suka tsaya, Mubarak ya kalle su yace

"Ku zauna dukan ku" Ayrah ta d'aga kae a hankali ta kalli Muttala seya jinjina mata kae irin kamar nufin sa babu wanda ya gan shi, bata iya zama ba seda taga shi kan sa Muttalan ya zauna sannan ta raku6e waje d'aya kamar munafuka tana matse k'walla, zubewa Mubarak yayi a wajen sannan yace kan sa a k'asa

"Yalla6ae gasu nan" kallan su Me gari yayi su duka, ita kuwa Ayrah gaba d'aya jikin ta rawa kawae yake yi har yanzu ta kasa gane mak'asudin zuwan ta wajen, dan kuwa sam ta kasa tuna yadda akayi tazo nan wajen, gyaran murya Me gari yayi sannan ya fara magana a nutse

"Meya kawo ku gidan nan? Ina Alhaji Mato?" dae_dae lokacin wayar Muttala ta fara ringing, seya fiddo ta daga cikin aljihun sa, ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae a hankali ya saci kallan Me gari sannan ya maeda kan sa kan wayar kawae ya d'aga, ban ji me akace daga can 6angaren ba na dae ji Muttalan yace

"Muna wajen Me gari dukan mu" se kuma yayi shiru can kuma yace

"Toh seka k'araso" Muttala ya fad'a yana katse wayar sannan ya kalli Me gari yace

"Yalla6ae yanzu ma Alhaji Maton ze zo da kan sa"

"Ahh toh Masha Allah" Me gari ya fad'a yana gyara zaman sa. Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna har zuwa lokacin da Alhaji Mato ya k'araso wajen da sallama cikin shadda kamar ko da yaushe me babbar riga, tumbin nan nasa kullum kamar k'ara ha6aka yake yi ya samu waje ya zauna abin sa, haka jajayen idanun sa ma sun k'ara wani ja kamar me ciwon ido, ya zube gaban Me gari da fara'a akan fuskar sa

"Barka da wannan lokaci Ranka ya dad'e yalla6ae" ya fad'a yana d'aga hannun sa alamar girmamawa

"Barka dae Alaji Mato, ashe ma kana kan hanya, kasan mutane ba abin yadda bane shiyasa na saka amin bincike, amma tunda ga ka kazo seka d'auki bak'in ka ku koma" gyara zama Alhaji Mato yayi yana satar kallan sahibar tasa da yaga ta k'ara masa kyau yace

"Wato yalla6ae dama wajen ka nazo gaskiya"

"Toh Ikon Allah, Allah yasa dae lafiya" Me gari ya fad'a shima yana gyara zaman sa, seda Alhaji Mato yaja numfashi sannan ya sake gyara zaman sa yana tunanin ta inda ze fara

"Yalla6ae wannan da kake gani mata ta ce, tsautsayi yasa na sake ta kuma ban maeda ta ba har ta gama idda, shine nake so a maeda mana auren mu yalla6ae dan nasan aekin ka ne wannan d'in" d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune tana jin maganar da Alhaji Mato yake yi ba dan tana fahimtar sa ba, ko kuma ta fahimci akan ta ake magana ba

"Ikon Allah" shine abinda Me gari ya fad'a kawae sannan ya sake yin gyaran murya yace

"yanzu a take kake nufi?" da sauri Alhaji Mato ya sake yin wani murmushin kafin yace

"Ehh Ranka ya dad'e yalla6ae"

"Allah ya gafarta malam ni ne nake neman auren ta yanzu, kuma muna son junan mu" dukkan su suka d'aga kae suna kallan me maganar cike da mamaki, da wani irin sauri ta d'aga kae ta kalli me maganar dan ta tabbatar wa da kan ta abinda take tunani, ita gaba d'aya kan ta ya kulle, har tana so ta dena gane komae, magana ake tayi gashi dae a gaban ta amma bata ganewa, bata fahimta, bata fuskan ta, ji take kamar dukan su wani yare suke yi, shin akan wa suke magana? Akan wata mace suke magana? Cigaba tayi da kallan sa sanda yake neman waje ya zauna yana lumshe idanun sa saboda gudun da bugun zuciyar sa keyi wanda ya wuce misali, ba k'in biyan kud'in shekara ba baya tunanin ko da abinda yafi hakane ya shiga tsakanin Abbu da Abba ze iya bari Ayrah ta auri wanin sa, wanin ma a gaban sa, Abba yace baze auri er sa ba se gashi wani ya d'auko ta wata uwa duniya dan a d'aura musu aure, toh meyasa baze yiwa kan sa wannan fad'an har yayi winning ba? Ko me zeyi se yayi yadda yayi aka d'aura musu aure a garin nan ba da wannan k'aton mutumin ba dashi za'a d'aura, tun da yasan ko d'aukar ta yayi ya maeda ta gidan su daga nashi iyayen har nasa ba amincewa zasu yi da auren junan su ba, dan haka ze zage damtse yasan yadda zasu yi suyi auren sirri in dae hakan ce mafita, ya ceci zuciyar sa sannan ya ceci Ayrah daga hannun wannan mugun mutumin

"Malam daga ina kae kuma?" Me gari ta fad'a yana kallan Rk, ajiye numfashi Rk yayi sannan yace har lokacin be kalli kowa ba

"Soyayya muke yi da ita, kuma bazan iya bar wa wani ita ba" yayi maganar a nutse kae ba zaka ta6a cewa tsara zancen yayi ba, bin sa da kallo Alhaji Mato yake yi dae_dae lokacin da Rk ya d'aga kan sa ya watsa masa wani banzan kallo me nuni da abubuwa da dama, da sauri Alhaji Mato ya d'auke kan sa yana jin tabbas idan yace wani abun asirin sa ka iya tonuwa mutuncin sa ya zube a banza, dole yayi tunanin mafita, d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune kamar wadda aka kafe ta yace

"Toh ke kin ji? Shin kina da ta cewa?" se a lokacin Ayrah ta d'aga kae ta kalli Me gari tana jin zuciyar ta kamar zata tarwatse, kwata kwata ta kasa bud'e bakin ta ballantana tace wani abu, toh ta bud'e d'in ma tace mene? Gaba d'aya ta kasa fahimtar wannan wasan kwaekwayon da suke gabatarwa a gaban ta, a hankali ta shiga tuna maganar Muttala se kawae ta shiga girgiza kae kamar wata kad'angaruwa, sauke numfashi Me gari yayi sannan ya kalli Alhaji Mato da kuma Rk yace

"Ina ganin dukan ku ku tashi ku tafi, zan rik'e ta a hannu na zuwa gobe kafin a kira magabatan ta, gobe bayan an sakko daga masallaci ni da kae na zan d'aura mata aure da wanda ta za6a a matsayin wanda take so!" dukan su kallan Me garin suke yi, Alhaji Mato yana ji kamar ya tashi ya rufe Rk da duka, idanun nan nasa suka k'ara yin jawur, ta 6angaren Rk kuwa gaba d'aya tunanin sa ya tafi yadda zeyi ya shawo kan Ayrahn ta amince da auren sa cikin garin nan. Kamar wata kurma doluwa kuma bebiya haka take bin wadda akace ta mata jagora zuwa cikin gidan Me garin, har lokacin ta kasa amincewa ba wasan kwaekwayo akeyi ba, a haka har suka k'arasa cikin wani madaedaecin d'aki seda ta zauna sannan wadda ta kawo tan ta fice daga d'akin.


... A zaune take kamar wata munafuka cure waje d'aya, kuka kawae take yi cikin rashin sanin abin yi, wannan mutumin kawae take jira yazo ya mayar da ita gida amma har yanzun shiru, ta rasa gane dalilin ta na zuwa k'auyen nan, abinda ya sake jefa ta cikin wani mad'aukakin mamaki shine ganin Rk da tayi, shin ko dae mafarki take yi ne bata sani ba? Tabbas ma babu mamaki mafarkin take yi dan kuwa wannan dae yafi kama da mafarkin. Tana nan zaune bata umm bata umm umm tunda kuma ta zauna ta kasa koda kae ruwa bakin ta ne ballantana akae ga cin abincin da aka dinga dire mata, ita bata ta su take yi ba, abinda kawae take buk'ata yanzu shine ta samu waya ta kira Abban ta ko Yah Sadeeq amma har yanzu bata ga wanda zata iya samun waya a wajen sa ba

"Ki zo ana neman ki" wata mata ta fad'a tana kallan ta, da mamaki ta d'aga kae ta kalle ta sannan cikin k'arfin hali ta furta

"Don Allah zan iya samun waya a wajen ki?" da mamaki matar ta kalle ta cike da mamakin yadda taji tayi magana dan kuwa ta d'auka bebiya ce, se kawae ta girgiza kae tana cigaba da kallan kyawun Ayrahn da duk da yadda take a firgice hakan be hana shi fitowa ba

"Muje koh?" matar ta fad'a tana cigaba da kallan ta, se kawae ta mik'e cikin rashin sanin abinyi tabi bayan matar kamar rak'umi da akala, a soron gidan suka tsaya sannan matar ta kalli Rk dake tsaye jikin bangon soron idanun sa a lumshe kamar me bacci

"Don Allah kada ku dad'e, kaga dae da yadda akayi na barka ka shigo gidan nan, da Baba ma ya sani baze bari ba wallahi"

"Nagode" ya fad'a yana bin ta da kallo sanda ta koma cikin gidan, wanda Ayrah ta gani ne ya sanya tayi kicin kicin da fuskar ta tana shirin komawa ciki yace a nutse

"Batu ne akan auren ki da za'a gabatar gobe" kamar wadda aka tsaeda ta seta dakata tana jin bugun zuciyar ta na k'aruwa, murmushi yayi ganin yaci nasara tunda gashi har ta tsaya, kafin yace komae ta juyo tana kallan sa murya a raunane tace

"Bana buk'atar taemakon ka, ban ce ka maeda ni gida ba dan bana buk'atar hakan daga gare ka, abinda nake so kawae shine ka bani aron wayar ka zan kira Abba na na sanar dashi inda nake zezo ya d'auke ni" kallan ta ya cigaba dayi yana jin muryar ta ta dake fita a raunane har cikin kwanyar sa, wani irin tausayin ta mara misaltuwa na ratsa shi amma yasan abinda zeyi, ya furta

"Kada kiyi wannan kuskuren, kada ki sake ki kira Abban ki, dan kuwa babu wanda ze yadda dake akan ba guduwa kika yi da kan ki ba, shawara d'aya ni kae na ba dan wani abun zan taemake ki ba se dan kasancewar ki er uwa ta musulma" ya d'an tsagaeta yana jin wani irin ciwo a cikin zuciyar sa wanda har hakan seda ya bayyana a cikin muryar sa da kuma kan fuskar sa sannan ya cigaba da fad'in

"Taemako d'aya zan miki shine zan kar6i auren ki a matsayin wadda muke soyayya, sannan a bani ke na tafi da ke zuwa Kano, tun kafin ma mu shiga cikin Kanon zan sawwak'e miki seki tafi gidan ku, kin ga babu wanda ze ji labarin auren idan bake kika fad'a ba.."

"Ya ishe ni haka malam, babu ruwan ka da rayuwa ta, na fad'a maka ka fita a rayuwa ta ni da iyaye na, ka bar ni zan auri koma wanene tunda ba zaka bani wayar ta ka bana buk'atar wani taemakon" ta fad'a sanda wasu kyawawan hawaye suka shiga zarya akan kuncin ta, runtse idanun sa yayi daga inda yake tsaye, baya tunanin kome zata yi a yanzu kam ze bata wayar sa tayi kira da ita, bama shi ba koda wani yaga ze bata wayar tayi kira toh ze san yadda zeyi ya hana wannan abin faruwa, kenan a 6ata masa budget? Kae ina hakan baze ta6a faruwa ba


"Kina tunanin mutumin daze aure kin ze sake ki kafin ya maeda ki gida? Yana son ki fa, idan da baya son ki baze kawo ki wata uwa duniya a d'aura muku aure ba, ni kuwa fa? Yanzu babu ko d'igon son ki a cikin zuciya ta, dan haka kawae zan aure ki ne dan na taemaka miki ki fita daga hannun wannan mutumin, muna barin k'auyen nan kuma zan rubuta miki takaddar ki da sharad'in ba zaki sake neman inda nake ba" ya k'arasa maganar yana kafe ta da idanun sa masu kyau da kwarjini

"Waye ze ne me ka? Tirrr!" ta fad'a tana sake tuna halin mahaefin sa, so take ta tambaye shi toh shi meya kawo shi nan d'in? Amma tasan idan tayi tambayar ze iya tunanin wani abun dan haka tayi shiru tana cigaba da kallan wani wajen, jin da yayi bata sake cewa komae akan zancen sa ba hakan ya alamta masa zata iya amincewa kenan da maganar tasa, lallae ya sake yadda Ayrahn har yanzu yarinya ce, seya saki wani shu'umin murmushi yana shafa bak'in sumar dake shimfid'e akan

Please Login or Register in order to submit comment