Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na fito dan tabbatarwa" ya fad'a yana mik'ewa sannan ya kalli Hameeda yace

"Yanzu Rk ze shigo, yace min yana waje"

"Ikon Allah! Amma kuma babu sanarwa irin wannan babban bak'o haka?"

"Ke dae bari naje na fara tabbatar da zuwan nasa" Yaseer ya fad'a yana ficewa daga d'akin. Kallan sa ta cigaba dayi da manyan idanun ta da suka yi rau rau sanda yake wayar, har zuwa sanda taga yana shirin ajje wayar, yana sane da kallan da take masa dan haka ya sake rik'e wayar sannan yace

"Ka taho min da takadda da biro" se a lokacin ta d'auke kan ta daga kallan sa tana sauke ajiyar zuciya, "gaba d'aya yau lokaci baya sauri" ta ayyana a ran ta. Suna nan zaune babu wanda ke cewa da d'an uwan sa uffan, se ga Yaseer ya bud'e gate d'in gidan ya fito, da murmushi ya k'araso bakin motar Rk d'in yana fad'in

"Ohh Rk ashe da gaske kake? Ban ta6a tunani ba wallahi" ya fad'a dae_dae sanda idanun sa suka sauka akan Ayrah dake zaune tana jira a mik'o mata takaddar ta ta wuce gidan su (lol), murmushi Rk yayi kana ya bud'e murfin motar ya fita ya kama hannun Yaseer suka gaesa

"Wacece wannan?" Yaseer ya fad'a yana kallan cikin motar sannan ya dawo da duban sa kan Rk, iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace

"Muje ciki zan maka bayani" sosae kan Yaseer ya kulle, shi dae yasan Rk d'in bashi da wata budurwa balle yace budurwar sa ce, kae abinda ma ya sani a yadda yasan Rk d'in baze ta6a d'aukar budurwar sa yaje da ita wani gidan ba, amma jin abinda ya fad'a ya sanya shi fad'in

"Ohk, let's get in" Yaseer ya fad'a yana yin gaba, komawa Rk yayi ya lek'a ta window d'in side d'in sa sannan yace yana kallan ta yadda idanun ta suka sake cika taff da hawaye, baya so yayi wani abun da zesa ta sake yin kukan dan haka ya karyar da murya yace a tsanake

"Kiyi hak'uri Madam, ya manta be fito da takaddar ba, kizo muje ciki in rubuta acan"

"Ka aeko a kawo min" ta fad'a tana d'auke kae

"Shikenan tunda baki shirya kar6a ba" ya fad'a yana mik'ewa ya fara takawa, babu shiri ta bud'e murfin motar ta fito tana sauke numfashi a jere a jere, murmushi ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, tana ganin ya shige cikin gidan itama ta saka k'afar ta

"Barka dae Madam" Yaseer ya fad'a yana kallan ta, kamar baza tace komae ba se kuma ta d'an saci kallan sa tace ciki ciki

"Ina wuni?" shi bema ji ta ba dan haka ya sake jerawa da Rk suka cigaba da tafiya se dae babu wanda ke cewa komae, ita kuma tana bayan su tana bin Rk d'in cike da sassarfa, a haka har suka k'arasa cikin parlourn

"Bismilllah The great Rk" Yaseer ya fad'a yana murmushi dan sosae yaji dad'in ganin Rk d'in, shima murmushin ya maeda masa sannan ya k'arasa cikin parlourn ya zauna kan had'ad'd'iyar kujerar dake cikin parlourn, tsayawa tayi kawae tana cigaba da kallan sa, so take kawae taga ya d'auki takadda amma bata gani ba dan haka ta cigaba da tsayuwar ta

"Madam ki shigo mana!" Yaseer ya fad'a yana kallan Ayrah

"Rabu da ita, bata buk'atar komawa gida ne" Rk ya fad'a yana d'an kallan ta ta gefen ido, a hankali ta cigaba ta takowa zuwa cikin d'akin har lokacin idanun ta na cike da k'wallar nan, seta nemi gefen wata kujera ta zauna tana cigaba da k'ik'k'ifta idanu, murmushi Yaseer yayi dan ya fahimci kuka take 6oyewa, toh wacece ita? Ya k'agu yaji menene had'in ta da Rk d'in, dae_dae lokacin Hameeda ta fito daga d'aki sanye cikin doguwar rigar atamfa da mayafi madaedaeci, ta k'araso cikin d'akin fuskar ta d'auke da murmushi tace

"Barkan ku da zuwa" ta fad'a tana neman kusa da Ayrah da bata ma kalle ta ba ta zauna

"Yawwah barka dae Madam, mun same ku lafiya?" Rk ya fad'a shima da d'an murmushin dake k'ara masa kyau akan fuskar sa

"Lafiya k'alau Alhamdulillah, da alama dae wannan ce sirikar tamu?" ta fad'a tana kallan Ayrahn, da kallan farko ta mata ta hango zallar kyan da take dashi, wani kallo Ayrah ta d'aga narkakkun idanun ta ta watsawa Hameeda, ita kan ta Hameedan seta gaza gane wane irin kallo ne wannan? Murmushin yak'e yayi dan baya so su sake 6allo masa wani aekin yace yana mik'ewa

"Amm Madam.. Pls ga sister nan zata d'an yi wanka ta shirya pls, zuwa anjima zan zo na d'auke ta" duka kallan sa suke yi cike da mamaki, Yaseer yayi k'arfin halin fad'in

"Bangane ba?" lumshe idanun sa yayi yana fesar da iska daga bakin sa sannan ya bud'e idanun nasa yana kallan Yaseer yace

"Plsss idan na dawo zamu yi maganar, Abbu na jira na" ya fad'a yana fara yin gaba, mik'ewa tayi itama dae_dae lokacin da hawayen da suka dad'e cikin idanun ta suka samu damar zubowa akan fuskar ta, lura da hakan ya sanya shi d'an dakatawa kana yace a hankali yana kallan ta

"Ki shirya, ina dawowa se mu wuce.." ya fad'a cikin taushi, ita dae ba tace komae ba se sake share hawayen da tayi yayin da shi kuma ya fice daga d'akin cike da fatan kada ta tubure masa, Yaseer da Hameeda suka kalli junan su cike da mamakin wannan abu, sauke numfashi Yaseer yayi kana yabi bayan Rk daya fita

"Malam nifa bangane abinda kake nufi ba, ya zaka tafi kuma ka barmu cikin duhu? Ka fara warware mana wacece waccan d'in kafin ka bar gidan nan" numfashi ya sake fesarwa daga bakin sa sannan yace

"Sorry Friend, zance ne me tsayi amma ina gamawa da Abbu nan zan dawo pls" yayi maganar sanda ya bud'e murfin driver seat

"Shikenan karka d'au lokaci pls"

"In Sha Allah" Rk ya fad'a yana shigewa cikin motar

"Ammm pls kada a barta taje ko'ina kamin na dawo" Rk ya fad'a yana kallan Yaseer, yanzu kam kan Yaseer ya sake kullewa da al'amarin abokin nasa, dan haka bece komae ba ya bishi da kallo kawae, shi kuma Rk tunda yasan Yaseer d'in yaji abinda ya fad'a d'in ya sanya shi jan motar, bin sa da kallo Yaseer ya sake yi har ya fice daga cikin layin sannan ya sauke ajiyar zuciya yana komawa cikin gidan, "lallae akwae wani abun" ya fad'a a k'asan ran sa.




... Kae tsaye gida ya wuce zuciyar sa cike da sak'e_sak'e kala_kala, ya k'arasa yayi parking motar sa sannan ya fita ya shige cikin gidan, parlourn Abbu ya wuce da sallama d'auke a bakin sa ya shiga, Abbun na zaune akan kujera yana shan lemo gefe guda kuma yana kallo cikin k'atuwar T.Vn dake manne a jikin bango, seda ya d'auki remote ya rage volume d'in T.Vn sannan ya amsa sallamar Rk daya k'arasa shigowa cikin d'akin, murmushi ne ya su6uce akan fuskar Abbu sanda Rk yace

"Barka da wannan lokacin Abbu"

"Barka dae likita ya kamata ka samu bacci haka nan" jinjina kae Rk yayi yana yin d'an murmushin kana yace

"In Sha Allah Abbu" gyara zama Abbu yayi daga inda yake zaune sannan yace bayan yayi gyaran murya

"Wato maganar da nake so nayi da kae ita kan ta tana buk'atar nutsuwa, dan haka da zarar ka gama samun baccin da baka samu ba seka fara shirye_shirye saboda rashin ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an dakatawa, duk da Rk be fahimci maganar Abbun ba amma hakan be sanya shi cewa komae ba, yayi shiru yana cigaba da saurarar Abbun dan yasan ze warware masa komae ne

"Dama magana ce akan auren ka da Muneerah da za'a gabatar dashi nan da sati d'aya"



Mhiz Innocent.....✍️




https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 034



___Seda ya d'au wajen minti 1 bece komae ba yana ta kokawa da zuciyar sa akan zafin da take masa kada kuma 6acin rae yasa ya furta abinda be dace ba sannan a hankali ya d'aga idanun sa da suka sauya kala ya kalli Abbu

"Abbu aure ka nemar min hadda tsaeda rana ba tare da sani na ba?" ya fad'a ba tare dama yana sanin abinda ke fita daga bakin sa ba saboda tsananin 6acin rae, da mamaki Abbu ya kalle shi na tsawon sakanni, sosae yayi mamakin jin abinda ke fitowa daga bakin Rk d'in amma seya sake gyara zama sannan yace har lokacin yana kallan sa

"Toh ko ban isa bane?" se a lokacin Rk ya tuna abinda ya fad'a d'in a hankali ya d'an lumshe idanun sa sannan ya bud'e a nutse kuma a hankali ya furta

"Abbu ka isa.." daga haka ya mik'e cike da sassarfa ya fice daga d'akin, bin sa da kallo Abbu yayi har zuwa lokacin daya gama ficewa daga d'akin sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana jinjina kae.


... A hankali ya nemi waje ya zauna akan gadon sa idanun sa a lumshe, a karo na barkatae ya sake fidda iska daga bakin sa, hannu ya kae ya dafe kan sa daya cigaba da sara masa, ya kae wajen minti 5 a hakan yana sauke numfashi a jere a jere saboda yanda zuciyar sa ke cigaba da tafasa sannan ya mik'e kamar me tunanin wani abun se kuma ya koma ya zauna, tabbas Abbu na neman sakawa zuciyar sa ta buga, ta yaya ze iya kallan wata matar a matsayin matar sa bayan Ayrah? Be san ta yaya hakan ze kasance ba, son da yakewa Ayrah yana da yawa baya tunanin ko da ya auri wata ze iya adalci a tsakanin ku, toh ta yaya ma ze auri wata? Koda be auri Ayrah ba baya tunanin ze iya auren wata matar ballantana kuma yanzun daya same ta, se dae ga Abbu na neman saka shi auren wata bayan ita, baya so kuma ya d'auki zunubi akan hakan, amma ta yaya ze kalli Abbun ya fad'a masa baya son Muneerah saboda yana da wata matar daya aura ba tare da sanin su ba? Hannun sa ya kae ya cusa cikin kwantacciyar sumar kan sa nan take kuwa ta hargitse seya koma ya kwanta kawae cikin rashin sanin abinyi.



... A 6angaren Ayrah kuwa sanda Rk ya fita daga cikin d'akin seta cigaba kawae da kallan k'ofar kamar me tunani

"Muje na kae ki d'akin koh?" Hameedah ta fad'a tana murmushi, kamar ta mata banza se kuma taga gwara kawae ayi komae a yanzu a gama a wuce wajen, dan haka se kawae tayi gaba ta fara tafiya a hankali, Hameedahn seta wuce ta ta k'arasa zuwa bakin wani d'aki tace tana kallan ta

"Ki shiga kiyi wankan zan kawo miki kaya seki saka" se a lokacin ta iya bud'e baki tace

"Toh" sannan ta shige cikin d'akin, madaedaecin d'aki ne me d'auke da gado, wardrobe da kuma toilet, bata tsaya tabi ta kan d'akin ba kawae ta fad'a toilet d'in, anan d'in ma ba wani dad'ewa tayi ba dan haka ko minti 15 ba tayi ba ta fito sanye da hijab d'in, se a lokacin ta tsaya tana k'arewa d'akin kallo kafin ta d'auke kan ta ta maeda shi zuwa k'ofar d'akin da aka turo, Hameedah ce ta shigo yanzu hannun ta d'auke da riga har da sabon hijab ta k'araso tana bin ta da murmushin dae, seda ta ajje kan gadon sannan tace

"Bari na kawo miki abinci" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa

"Na k'oshi ni" tayi maganar a cunkushe, kallan ta Hameedah tayi ganin yanda ta wani d'auke kae ya sanya ta girgiza kae kawae ta fice daga d'akin, seda ta fita sannan Ayrah ta d'auki doguwar rigar abayar ta zura kana ta d'ora hijab d'in akae sannan tayi sallah ta mik'e ta cigaba da tsayuwa tana jiran dawowar sa, tun tana tsayen har ta gaji da tsayawar seta nemi gefen gadon ta d'an zauna tana share k'walla, yanzu kam idan har ya k'ara awa 1 bezo ba zata tashi ta tafi gidan su ne, ita kuma takaddar ya rik'e ta karya bayar, se yayi ta zama da auren shi kad'ae, ita ba abinda ya dame ta.


... A kujerun da suke ajje a compound d'in gidan suke zaune kowanne kan kujera d'aya, kallan sa Yaseer yake sosae yana nazarin yanayin sa, daga d'azu zuwa yanzu se yake ganin kamar ya sake chanjawa

"Wae me yake faruwa ne Rk?" d'an murmushin yak'e Rk yayi sannan yace bayan ya yatsina fuskar sa

"Yaseer, ina cikin matsala fa"

"Matsala kuma? Wace iriyar matsala? Ko da yake da farko dae ya kamata koma wacece waccan yarinyar ka maeda ta gida tunda kaga dare na sake yi" kallan sa Rk yayi sannan ya d'auke kan sa bayan ya sauke ajiyar zuciya yace a nutse kamar babu abinda ke damunsa

"Mata ta ce!" cigaba da kallan sa Yaseer yayi yana so ya gano ko dae abokin nasa ya fara shan k'waya ne? A iya sanin sa abokin nasa baya shaye shaye amma se gashi yau yayi magana irin ta en shaye shaye, se kuma ya saka wata dariya kana yayi shiru yana cigaba da kallan sa

"Tsaya mana pls, ni fa wallahi ba maganar raenin hankali nake maka ba" murmushi Rk yayi yana kallan Yaseer dake magana da iya gaskiyar sa, seda ya d'an lumshe idanun sa kad'an sannan ya bud'e a lokaci guda kana yace

"Am serious fah, mata ta ce ta sunnah" yayi maganar yanzu ma a nutse

"Look Friend, don Allah joke apart.." yayi saurin katse shi, dan kuwa ya gaji da jin wannan tatsuniyar tasa, gyara zama Rk yayi sannan ya fara da

"Nima ba wasa nake ba Yaseer, auren ne ya kasance kamar shirin film, ni kuma nayi kasada nayi aure ba tare da izinin su Abbu ba" daga nan ya shiga labartawa Yaseer d'in yadda auren nasu ya kasance, har ya k'are labarin Yaseer bece dashi uffan ba kawae kallan sa yake cike da mamaki, shima kansa daya gama bada labarin be d'aga ido ya kalli Yaseer d'in ba, sun kae wajen minti 2 a haka kafin Yaseer ya sauke ajiyar zuciya yace

"Lallae Rk, aure ba tare da izinin su Abbu ba? Baka tunanin wannan wani babban kuskure ne ka aekata?"

"Ya zanyi Yaseer? Ina kallo wani ya aure ta a gaba na? Ko kuma na maeda ta gida su aura mata wani bani ba?" ya fad'a yana kallan Yaseer da har lokacin mamaki yak'i barin sa, cike da mamaki Yaseer yace

"A'ah na kasa gane duk wannan abin, meyasa iyayen ta zasu ce baza ka aure ta ba? Idan ma akwae wani dalilin ina ganin kamar Abbu ne zece baza ka aure ta ba saboda wannan dalilin koh?" ya k'are maganar da sigar tambaya, ta6e baki Rk yayi, shi kan sa a wannan wajen be san abinda zece ba, be san dalilin hakan ba, da farko kamar Ayrahn na bayan sa duk da yadda iyayen su kace baze aure ta ba, se kuma daga k'arshe gaba d'aya ta juya masa baya

"Amma meyasa ba zaka tambaye ta dalilin ta na juya maka baya ba?" Yaseer ya katse masa tunanin da yake yi kamar yasan abinda yake sak'awa a ransa, ajiye numfashi yayi kafin yace

"Tak'i bani wannan damar Yaseer, tun farko abinda naso inji kenan a lokacin ne kuma ta birkice min, yanzu kuma bani da k'warin gwuiwar tambayar ta dalilin hakan tunda ga abinda ya faru" jinjina kae Yaseer ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Rk d'in amma duk da haka yace

"Amma yaushe zaka sanar dasu Abbun?" seda ya d'aga ido ya kalli Yaseer d'in sannan yace bayan ya girgiza kae

"Ba yanzu ba Yaseer, maganar da nake maka aure na da Muneerah rana ita yau ne, me kake tunanin ze faru idan na fad'awa Abbu maganar nan?" ya k'are maganar yana d'an ajje numfashi, shima Yaseer sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace

"Hakane kuma" ya fad'a yana jinjina kae cike da tunani a zuciyar sa ko ze samowa Abokin nasa mafita.



... Tana zaune cikin d'akin a ranta tana k'iyasta adadin lokacin da take jira ya cika ta tashi ta fita daga d'akin, wani irin bacci me dad'i ke ta sakad'ar ta tun d'azun, se yakice shi take yi ta k'arfi da yaji amma se dad'a lumshe idanu take yi kamar wadda tasha kayan maye, ko cikakken minti 1 bata k'ara ba ta 6ingire kan gadon se bacci. Sosae Rk yaji dad'i lokacin da Hameedah ke sanar dashi Ayrahn bacci take yi, dan haka ya d'an samu relief, hatta maganin ta ma bebi takan a tashe ta tasha a daren ba, a cewar sa goben seta sha tunda dae yanzu ta samu bacci, ko ba komae ze d'an samu nutsuwar zuciya kafin goben daya san me raba shi da ita se Allah. A hankali ta shiga bud'e narkakkun idanun ta da suka mata nauyi, har ta gama bud'e su tarr cikin d'akin, da sauri ta mik'e zaune tana cigaba da kallan d'akin, kallan agogon dake manne a jikin bangon d'akin wanda ya harba k'arfe 6:00 tayi, seta sake kallan agogon kamar me k'aryata abinda ta gani, se dae ga mamakin ta hakan dae ya sake nuna mata, wannan wane irin bacci ne? Bata san sanda hawaye ya soma sintiri akan kuncin ta ba, ta mik'e da wani irin sauri ta dirga daga kan gadon, sabon brush d'in data gani akan gadon ta d'auka ta fad'a toilet d'in tayi alwala tayi brush sannan ta fito tayi sallah tana istigfari cikin ran ta, bata san wane irin nannauyan bacci ne haka ya d'auke ta cikin k'ank'anin lokaci irin wannan ba, seda ta idar da Sallahr sannan ta sake fad'awa toilet d'in tayi wanka kana ta shirya yanzu ma cikin abayar data gani akan gadon ta maeda hijab d'in jikin ta ba tare data shafa komae akan fuskar ta ba ko ta shafa wani abu me kama da mae ba ta k'arasa ta ta6a k'ofar d'akin, cikin sa'a kuwa se taji ta a bud'e, sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta k'arasa fitowa daga cikin d'akin, ba tare data kalli ko'ina ba kawae tayi hanyar fita daga cikin d'akin, daga inda yake zaune kan dinning shi da Yaseer ya mik'e da sauri dan tunda ta fito yake ankare da ita, bece da ita komae ba kawae ya k'arasa a nutse zuwa gaban ta, dakatawa tayi da sauri ganin yanda ya tsaya d'in dab da ita, Yaseer dake zaune shima ya mik'e ya bar parlourn gaba d'aya, se a lokacin ya d'aga hannayen sa ya sak'ale su a k'irjin sa sannan ya zuba mata idanun sa gaba d'aya, k'ok'arin komawa gefe ta soma yi ba tare data kalle shi ba har lokacin fuskar ta a had'e

"Ina zaki je?" ya fad'a a nutse har lokacin idanun sa na kan ta, bata dae kalle shin ba se d'aga kae da tayi kawae ta kalli gefen sa sannan ta sake had'e fuska tace k'irjin ta na d'an bugawa saboda yadda ya tsare ta da idanun sa

"Gidan mu zan tafi!" ta fad'a lokacin da wasu ruwan hawaye suka taru a cikin idanun ta, cike da fatan kada ya kawo wata maganar dake nuni da k'in zuwan ta

"Gidan ku kuma?" ya tambaya yana d'an d'age girar sa guda d'aya yana cigaba da bin ta da wani irin kallo saboda yadda yaga ta masa wani shahararren kyau kamar ba cikin tashin hankali take ba, ba tace komae ba tunda tasan ae yaji abinda ta fad'a d'in dan haka ta sake k'ok'arin tafiya

"Toh ya zakiyi da aure na kuma da yake kan ki?"

"Zan fad'awa Abba na abinda ya faru, nasan zasu warware auren gaba d'aya.." ta fad'a har lokacin fuskar ta a had'e, murmushi ya saki daga inda yake tsaye sannan ya d'an lumshe idanun sa kad'an kana yace

"Ohk je ki.." bata sake cewa komae ba ta sauke ajiyar zuciya sannan tabi gefen sa ta fice daga d'akin, bin ta yayi da kallo yana mamakin ta, sosae yake mamakin ta musamman idan ya tuna yanda suka fara soyayyar su hankali kwance amma rana d'aya ta sauya kamar ba ita ba, be ta6a tunanin zata ta6a juya masa baya ba, ya d'auka zata taya shi fafutuka ne da kuma nemo hanyar da zesa iyayen su su amince da auren su, se yanzu yaji inama kafin ta fita ya tambaye ta dalilin sauyawar ta? Koda yake yana da 80% sure cewar maganar iyayen ta kawae tabi yasa ta chanja masa, yasan tana k'aunar sa fiye da zaton sa, amma kuma soyayyar iyayen ta ta danne tashi, amma meyasa tun farko bata chanja ba se daga baya? Meyasa haka? Shi kad'ae yake tunanin sa kuma yasan babu me amsa masa dan haka kawae ya sauke hannayen sa sannan ya fita daga cikin d'akin, yana hango ta sanda ta fita zuwa k'ofar gidan, seda ta fita d'in sannan ya k'arasa ya hau motar sa ya jata shima ya fice daga gidan, a nutse kuma cike da takatsantsan yake bin ta a baya, baya so ta fahimci bin ta yake dan haka yake bin ta a hankali, itama a hankali take tafiya kamar wadda k'wae ya fashewa a ciki, se dae hakan na da nasaba ne da jikin ta da har lokacin take ji be koma mata dae_dae ba, a haka har ta fita titi ta tsaya tana kallan motocin da suke wucewa, se a lokacin ta tuna babu ko sisi a tare da ita, amma koma menene gwara taje gidan idan yaso seta kar6a ta bawa me Napep d'in, dan haka babu 6ata lokaci ta shiga tsare adaedaeta, daga cikin layin ya dakata da motar tasa yana ganin ta har zuwa sanda wata k'atuwar mota me kyau ta dawo da baya tayi parking a gaban Ayrah, d'an runtse idanun sa yayi yana jiran ganin abinda ze faru next, dae_dae lokacin da mutumin cikin motar ke k'ok'arin fitowa ita kuma ta gama fad'awa me Napep d'in data tara inda zata je, babu 6ata lokaci ta fad'a ciki dae_dae lokacin da mutumin ya gama fitowa daga cikin motar, wani banzan kallo Rk yabi shi da shi yana jin yanda zuciyar sa ta fara tafasa lokaci d'aya, tana shiga kuma me Napep d'in yaja, mutumin na shirin yin magana yaga yaja adaedaetar sa

"Kashhh!" ya furta yana bin adaedaetar da kallo sanda suka wuce shi, se a lokacin Rk yaja motar sa ya fito daga cikin layin har lokacin yana d'an kallan mutumin yaga ko zeyi wani abun bayan nan, se dae yaga beyi ko k'ok'arin bin su ba, se a lokacin ya d'an ji sanyi sannan ya cigaba da bin ta, yana cikin driving d'in wayar sa ta soma ringing, kamar baze kalli me kiran ba se kuma ya kalla

"Muneerah" shine abinda ya bayyana akan screen d'in wayar, runtse idanun sa yayi zuciyar sa na cigaba da wani irin zafi, kawae seya kae hannun sa ya kashe wayar gaba d'aya sannan ya jefa ta kan kujerar me zaman banza ya cigaba da driving d'in sa yana jin yadda ran sa ke kuma 6aci. Har cikin layin su ya shigar da ita seda suka kusa kaewa k'ofar gidan su sannan tace

"Ya isa" babu 6ata lokaci ya tsaya ta sauka, se kuma ta d'an yi shiru tana tunanin yadda zata shaeda masa seta shiga gida ta kar6o kud'i, a ranta tana fatan Allah yasa me mutunci ne, ganin dae babu wata mafita ya sanya ta fad'in

"Bari na kar6o kud'in don Allah.." kallan ta yayi sannan yace

"Toh shikenan amma kiyi sauri don Allah" sauke ajiyar zuciya tayi kana a hankali ta juya, a hankali ta sauke idanun ta akan gidan nasu, se ta shiga kallan sa kamar yau ta fara ganin sa, a hankali ta lumshe idanun ta sannan ta taka k'afar ta cikin soron gidan nasu tana jin yadda bugun zuciyar ta ya k'aru lokaci guda..


Mhiz Innocent..... ✍️




https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 035



___A hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin gidan har zuwa sanda ta k'arasa cikin tsakar gidan, Abba da Yah Sadeeq suna zaune a tsakar gidan, yayin da Umma ke fitowa daga cikin kitchen hannun ta d'auke da tea flask ta k'araso ta ajje a gaban su Abba

"Sannu da k'ok'ari" Abba ya fad'a, seta d'an yi murmurshi sannan ta fara k'ok'arin mik'ewa, dae_dae lokacin data d'ago d'in yayi dae_dae da lokacin da Ayrah ta

Please Login or Register in order to submit comment