Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

data tuna da ita ta janyo ta nemo number Yah Sadeeq ta danna kira, bugu 1_2 ya d'aga dan lokacin be kae ga yin bacci ba

"Yah Sadeeq.." tayi maganar tana fashewa da wani marayan kuka a hankali, daga can 6angaren Yah Sadeeq ya girgiza kae yana murmushi dan yasan wannan kukan nata bana komae bane sena shagwa6ar data zame mata jiki

"Auta rigima" ya fad'a yana murmushi, dae_dae sannan wayar Jidda tayi k'ara, taja tsaki daga inda take kwance tana amsa wayar ba tare da tasan me kiran ba, daga can 6angaren akace

"Jidda don Allah kimin snapping aekin nan zanyi copying kafin gobe.."

"Don Allah kiyi hak'uri Abeedah, ki koma kije kiyi bacci ko dan gobe ki samu shiga class d'in" banji me akace daga can 6angaren ba amma naji Jidda tayi dariya tace

"Doctor RK fa.." daga inda Ayrah ke kwance ta d'an lumshe idanun ta tana jin yadda ta gaji da jin sunan da suke ta ambata tun d'azu, sunan da kusan duk hirar da suke tun d'azu a kansa ne suke yin ta, seta gyara kwanciyar ta ta kawae duk da tasan yau dae ba zata iya baccin ba...




_*Yanzu wasan ze soma*_🥲


Mhiz Innocent.....✍️





https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 013_014



___Washe_gari tun asuba ta tashi tayi wanka ta gabatar da sallah sannan ta cigaba da zama kan carpet d'in da tayi Sallahr akae tana addu'a, bata dad'e da zama ba su Jidda ma suka farka kusan a tare, Jidda ce ta fara shigewa toilet yayin da Ruks da Bahijja suka tsaya a bakin toilet d'in kowacce na jira Jidda ta fito itama ta shiga. Tana nan zaune haka suka dinga sauri suna shiryawa kafin wajen k'arfe 7:30 dukkan su suka gama shiryawa kusan duk cikin dogayen riguna da k'ananan mayafae, Bahijja dake saka boot a k'afar ta tace

"Kin gama shiryawa ne, ko har yanzu addu'ar ce ba'a gama ba?" tayi maganar tana kallan Ayrah, seta girgiza kae kafin tace

"A'ah ku jira ni yanzu zan shirya"

"Ayrah mun yi gaba, kiyi sauri ki shirya ki taho kafin 8 tayi" Ruks ta fad'a sanda take d'aukar jakar ta, jinjina kae kawae tayi ba tare da ta sake cewa komae ba, ta bisu da kallo sanda suke ficewa daga d'akin. A hankali ta mik'e ta sake fad'awa toilet ta wanko fuskar ta sannan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa kana ta saka hijab, ta d'auki sabuwar jakar da Yah Sadeeq ya siya mata wadda ta zuba littafan ta a ciki ta fito daga d'akin. A hankali take takawa a cikin filin makarantar cikin nutsuwar ta, duk da babu abinda ta shafa akan fuskar ta amma tayi kyau sosae, bayan ta d'auke da jakar goyo yayin da ta rungume wasu text books guda 2 wanda suma duk Yah Sadeeq ne ya siya mata saboda ta samu sauk'in karatu. Tun kafin ta k'arasa inda ze sada ta da ajin nasu taji shiru kamar babu mutane cikin ajin, har seda ta fara tantamar anya kuwa ba tayi 6atan kae ba?, dab da zata isa wajen ajin sassanya kuma daddad'ar muryar sa ce ta fara dakar mata kunnen ta, ba'a iya jiyo abinda yake fad'a d'in amma tana iya jiyo sautin yadda nutsatstsiyar muryar tasa ke fita, haka kurum taji k'irjin ta ya buga da wani irin k'arfi har seda ta dakata daga inda take tafe na wasu en mintuna kafin ta lumshe manyan idanun ta kana ta bud'e su tana mamakin yadda bugun zuciyar ta ya sauya cikin k'ank'anin lokaci. Da sallama akan la66an ta ta sanya k'afa cikin ajin nasu ba tare data kalli kowa ba, dan bata jin zata iya kallan kafatanin en ajin dan tasan duk idanun su na kanta ne

"Hey!" nutsatstsiya, sanyayyiya kuma daddad'ar muryar sa me dad'in saurara ta daki dodon kunnen ta, a take kuma a lokaci guda k'afar ta ta d'auki rawa wanda har yanzun ta kasa gane dalilin wannan rawar da jikin nata ke yi

"Ko dae da ita ake?" ta tambayi kan ta, gudun kada taje tayi laefi ya sanya ta dakatawa daga inda take, a hankali kuma ta shiga juyowa zuwa inda yake tsaye sannan ta d'aga raunannun idanun ta ta aza su inda ta tabbatar yana tsaye, ba ita yake kalla ba idanun sa na kan wani littafi dake gaban sa ne, kyakykyawa ajin farko, fari me kyakykyawan jiki kuma cikin kyakykyawar shiga, sanye yake cikin wasu riga da wando da suka dace da k'irar jikin sa, a saman kayan kuma suit ce itama me kyau, kansa babu komae se kwantacciyar bak'ar suma da tasha gyara na musamman, kamar yadda take a gyare haka kyakykyawan bak'in sajen sa ma yake a gyare kuma a kwance wanda hakan ba k'aramin k'arawa kyakykyawar fuskar sa kyau yayi ba, ganin da tayi ba ita yake kalla ba dan ita kanta bata ganin fuskar sa se gefen fuskar ta sa, seta d'an lumshe idanun ta kafin a hankali ta fara k'ok'arin juyawa

"Hey, go out!" ya sake fad'a har lokacin be kalle ta ba, kawae se tayi shahada ta tabbatar da ita yake, har lokacin bata kalli kowa ba taja k'afafun ta ta fice daga ajin. Kae tsaye hostel ta koma har lokacin tana tuna sautin muryar sa a cikin kwanyar ta sannan kuma tana hana k'wallar data tarar mata a idanu zubowa, tana shiga ta ajjiye jakar ta ta haye kan gadon ta jinginar da kanta a jikin gado, iska ta fesar daga cikin bakin ta tana d'an jan numfashi kafin ta sanya hannu ta goge hawayen da suka fara sakkowa akan fuskar ta, a hankali ta cigaba da jan sheshshek'a tana jin wani irin zafi wanda da farko bata ji shi ba se yanzun, ta tsani yarfi, ta tsani dizgi, se gashi her first day in University wani yayi embarrassing na ta a baenar nasi, d'an mitsitsin bakin ta ta murgud'a kamar wani na kallan ta sannan tace akan la66an ta

"Bashi da kirki". Tafi awa 1 a cikin hostel d'in seda ta kitanci lokacin da tasan ya fita sannan ta mik'e ta fita zuwa ajin nasu, cikin sa'a kuwa babu kowa cikin ajin a lokacin, se students kawae da kowa ke harkar gaban sa, koda ta shiga cikin ajin duk seta ji ta a takure musamman da taji a jikin ta idanun mutane da dama na yawo ne a kan ta, se take ganin kamar kowa kallan ta yake da wadda aka kora d'azu, duk se ta ji tana neman sark'ewa a tafiyar da take, gaba d'aya ma ta rasa inda za taje ta zauna, tsintsiyar hannun ta taji an kama se ta juya da sauri ta d'aga idanun ta ta kalli wadda ta rik'e mata hannun, Jidda ce, seta sauke ajiyar zuciya hadda lumshe idanun ta tana bud'ewa lokaci guda

"Muje ki zauna" Jiddan ta fad'a tana cigaba da jan ta zuwa cikin ajin, babu musu kuwa kamar wata doluwa ta bita cike da sassarfa, wani dake zaune kan wani bench yace yana kallan Jidda

"Hajiya Jidda an samu wata kenan?" seta juya ta watsa masa harara sannan tace

"Shishshigi ba kwarjini" dariya yayi hadda dukan bench yace bayan ta wuce wajen

"Yoh shishshigi kuma ya kae wanda kika yi?" ita dae bama taji shi ba suka k'arasa inda suke zaune sannan tace tana Kallan Ayrah

"Yawwah ki zauna, nan ne kusan permanent seat namu dan tunda muka zo anan muke zama" murmushin yak'e Ayrah tayi dan har ga Allah wajen be mata ba, dan kuwa a baya ne bench d'in nasu yake, se dae ta nemi waje ta zauna kawae.


Basu suka koma hostel ba a ranar se wajen k'arfe 6, dan haka suna komawa Ayrah ce ta fara fad'awa toilet tayi wanka dan sosae ta gaji tana fitowa ta zira doguwar riga mara nauyi ta maeda hijab d'in ta tayi sallah kana ta nemi waje ta zauna still dae da hijab d'in , dan haka kawae tunda tazo d'in tafi jin ta comfortable idan ta saka hijab d'in.

"Toh mu dae kinga had'a girkin mu muke, kawae kowaccen mu zata kawo abincin tane duk abinda muke so se mu dafa muci, kema ayi hakan dake?" Ruks ce me maganar tana kallan Ayrah, seda ta d'an yi jimm, saboda haka kawae taji basu wani kwanta mata can ba musamman daya kasance hirar su gaba d'aya rabin ta ta samari ce, tun jiyan kuma da tazo ba taji wata a cikin su tayi maganar karatu ba, amma kuma suna da kirki yadda suka tarbetan kawae ma ya mata dad'i dan haka se tace

"Tohm.."

"Ohk guys..me zamu dafa?" Ruks ta fad'a tana kallan su su duka, ta6e baki Jidda tayi kana tace

"Kawae mu dafa indomie, dan ni yunwa nake ji"

"Nima dae kam" Bahijja ta fad'a itama, mik'ewa Ruks tayi ta nufi inda kayan abincin nasu ke ajiye cikin d'an k'ank'anin lokaci ta d'ora musu Indomien, sanda take zuba Maggi a ciki ne ta jiyo muryar Jidda na fad'in

"Ke ni tun d'azu nake so mu tattauna akan shigar Doctor RK ta yau, amma wannan Abeedar ta mana k'erere, don Allah befi wancan satin kyau ba?" ajiye maggin hannun ta Ruks tayi sannan ta juyo tana rik'e ha6a kana tace tana murmushi

"Umhum wallahi ke kam ki bari kawae.., shi fa kowacce shiga yayi naga alama kyau take masa, wallahi guy d'in ya had'u iya had'uwa" ta fad'a tana jan baki kamar wadda taci abu me yaji, daga nan fa hirar tasu ta soma, maganar tasan nan dae da kullum ita suke yau ma dae ta san suke, da alama basa gajiya da hirar tasa kamar wani abinci

"Wae Bahijja meye haka naji kinyi shiru?" Jidda ta fad'a tana jefa mata harara, seta yamutse fuska kana tace

"Ke kam ki bari kawae, kae na ke ciwo" itama tayi maganar tana yamutse ta ta fuskar

"Toh Allah ya sawwak'e.. Ayrah ki sauko muci abinci" Ruks ta fad'a tana kallan Ayrah dake kwance kamar me bacci, se a lokacin ta tashi dan daga inda take zaune tun d'azu ji take kamar ta tashi ta musu duka, tana jin kamar tace musu sun ishe ta da maganar wannan mugun mutumin, haka dae ta mik'e ta sauko suka ci abincin.



...... Washe_gari k'arfe 7:40 dukan su suka gama shiryawa har da Ayrah, yau ma cikin hijab d'in dae ta shirya kamar jiyan, suka fito tare suna tafiya su Jidda na hira yayin da ita dae tayi shiru kawae, a dae_dae inda ze sada su da ajin nasu dukkan su suka ji wata murya na fad'in

"Ayrah Ibraheem Khaleel.." kusan a tare dukan su suka juya, se duk suka tsaya suna kallan mutumin daya kira sunan nata kafin suka kalli Ayrah, itama da kallan rashin sani take bin sa dan tunda take bata ta6a ganin fuskar ba

"Sak'o aka bani na kawo miki.." yayi maganar yana kallan ta

"Sak'o kuma? Ni ban sanka ba" ta fad'a cike da sakarcin nan nata, se yayi murmushi kana yace

"Ehh Hajiya, dama nasan baki sanni ba ae amma daga makarantar ku ne aka turo ni" seta d'an samu relief amma duk da haka tace

"Toh mene?"

"K'awa ta zo mu tafi 8 ta kusa, kuma kin san yau yana da first period a farko" Ruks ta fad'a tana jan hannun Ayrah, seta d'an maraeraece fuska sannan tace

"Uhmm daga makaranta ne fa.."

"Kinsan yadda za'ayi? Mu bari muyi gaba ke kuma kiyi sauri kiji abinda ze fad'a, but u should make sure dat kin shigo class before 8" seta jinjina kae tana bin su da kallo sanda suke wucewa ajin kana ita kuma ta dawo da duban ta inda mutumin yake, kafin tace komae yace

"Kayan abinci ne dana sakawa Hajiya akace mu kawo miki daga makaranta" seta tsaya ta cigaba da kallan sa kamar me tunani se kuma tace

"Kaya kuma?" yace

"Ehh.."

"A'ah Abba ya siya min" ta fad'a tana girgiza kae, seya sake yin murmushi kafin yace

"Ehh wannan ae daban yake Hajiya, kuma kinga daga makaranta ne" seta d'an yi jimm kafin tace

"Toh zan kira Yah Sadeeq na fad'a masa tukunna" mutumin ya sauke ajiyar zuciya yana mamakin wannan yarinya haka amma gudun kada ya takura ta shinshino wani abun ya sanya shi fad'in

"Toh kira shi"

"Ae ba yanzu ba.." tayi maganar cikin turo baki duk da bata san tayi hakan ba

"Meyasa?"

"Sauri nake" ta fad'a tana gyara tsayuwar ta, seya fesar da iska daga bakin sa kafin yace

"Toh shikenan, bari na jira ki" ba tace komae ba ta juya zuwa ajin nasu, dae_dae lokacin da wani d'alibi yayi sauri ya shige cikin ajin, seta ji dad'i hakan na nufin 8 ba tayi ba kenan, dan haka da confidence d'in ta ta sanya k'afa cikin ajin, tayi wajen taku 5 a cikin ajin tana jin dad'in yadda yau ta samu class d'in, se dae ga mamakin ta seta jiyo kamilalliyar muryar sa na fad'in

"Go out.." seta ta6e baki a ranta tana sak'a may be tana shigowa k'arfe 8 d'in ta cika, gashi nan har ze kori wata ko wani, dan haka ta cigaba da tafiya har zuwa sanda ta samu waje ta zauna tana lumshe idanun ta kana ta bud'e, abinda ya bata mamaki yadda taga kusan idon kowa na cikin ajin akan ta yake, seta sake kallan wani 6angaren taga still dae ita suke kalla, a hankali tabi jikin ta da kallo zuciyar ta na bugawa tana fatan ba wani abun ne ta manta bata saka ba, ta kalli jikin ta hijab d'in ta gashi nan har kusan k'asa, ita kanta kawae dae ta duba d'in ne amma tasan da akwae abinda beyi ba a jikin ta su Jidda zasu fad'a mata, inda taga kuma sun maeda hankali suna kalla itama ta d'aga raunannun idanun ta da suka cika taff da k'walla saboda wannan kallan da suke mata duk ya rikita ta, a hankali idanun ta suka sauka akan kamilalliya kuma nutsatsiyar fuskar sa me cike da wani irin zati, da kwarjini na musamman har bata san sanda ta d'auke idanun ta da sauri ba tana dafe k'irjin ta daya wani irin buga a lokaci guda

"Kurma ce?" yayi maganar kamar baya so kuma ba tare daya kalli en ajin ba

"Dake fa yake.. Ki tashi ki fita kin makara.." wata dake kusa da ita ta ankarar da ita, seta d'aga kae cikin rashin fahimta ta kalle shi dae_dae sanda shima ya d'ago nasa firgitattun idanun da suka ida rikita ta, ta sake jin zuciyar ta ta buga da k'arfin da yafi na d'azu, a hankali ya janye nasa idanun fuskar sa ba yabo ba fallasa ya sake fad'in

"Fita!" yanzun kam ta tabbatar da ita yake, dan haka jiki a matuk'ar sanyaye taja k'afafun ta ta fice daga cikin ajin, tana jin yadda idanun en ajin suka mata chaaa aka wanda har hakan ya jawo tafiyar ta ta sake chanjawa tana tafiya tana wani rangaji kamar er maye, tun kafin ta ida fitowa daga cikin ajin wani kuka ya k'wace mata, dan haka ita tama manta da wannan mutumin dake jiran ta kawae ta wuce Hostel, akan gadon ta ta zube tana fashewa da kuka, ta san mutumin be santa ba bata san shi ba ba dan haka ba se tace tsanar ta yayi shiyasa yake korar ta kullum, ban da haka meyasa wani ya shiga kafin ita be kore shi ba se ita, wayar ta data ajiye akan gadon dama bata tafi da ita class ba ce ta fara ringing seta janyo wayar ta d'aga tana k'ok'arin tsayar da kukan

"Subhanallahi Auta meya faru? Har yanzu baki dena kukan ba?" Yah Sadeeq ya fad'a, seta sake hasaso fuskar Rk cikin idanun ta kana ta harari iska tana murgud'a baki sannan tace

"Toh ba wani malami bane, Yah Sadeeq wallahi mugu ne kuma.."

"Kae Subhanallahi, Ayrah bakya so karatun naki yayi albarka?"

"Toh Yah Sadeeq sau biyu fa yana hana ni shiga aji wae na makara" murmushi Yah Sadeeq yayi daga inda yake kafin yace

"Toh kiyi hak'uri, kuma kada na sake ji kince bashi da kirki, daga yanzu ki dinga shiryawa da wuri kina tafiya class kin ji?" seta d'aga kae kamar yana kallan ta sannan tace

"Ehh"

"Dats my sister.." ya fad'a yana murmushi, seda Yah Sadeeq ya ajje wayar sannan tace bayan ta sake tuna fuskar Rk

"Mugu kawae.."




K'arfe 3 suka fito daga lectures d'in, Jidda, Ruks Bahijja har ma da Ayrah suka fito daga class d'in dan komawa Hostel, suna cikin tafiya kafin su k'arasa Hostel d'in Bahijja ta kalle su tace

"Ku wuce pls yanzu zanje na dawo"

"Ina zaki je?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, seta d'an yamutse fuska kafin tace

"Yanzun zan dawo pls, akwae sak'on da zan kar6a wajen wata cousin sister d'i ta data fara zuwa school d'in nan"

"Ohk" suka fad'a kusan a tare, suka cigaba da tafiya yayin da ita kuma Bahijja ta juya.. A hankali take takawa zuwa wajen, seta kalli gefe da gefe ganin babu idon wad'anda ke kanta yasa ta wuce wajen, seta dakata a bakin k'ofar office d'in nasa sannan ta kalli wani wanda ke tsaye a wajen tace

"Pls Doctor na ciki?"

"Yeah.." ya fad'a yana kallan ta

"Pls taemaka kamin iso mana" ta fad'a tana maraeraece fuska, seya d'aga kafad'a yana wucewa ciki, wajen minti 2 se gashi ya fito yace

"Ki shiga.." murmushi Bahijja tayi cikin jin dad'i kana tace

"Nagode sosae.." ta fad'a tana zame takalmin k'afar ta ta shige cikin office d'in, dae_dae lokacin Rk yana tsaye gefen kujerar office d'in, da sallama ta shiga ba tare daya kalle ta ba yace

"Come in" seta lumshe idanu tana jin yadda muryar tasa ke k'ara dad'i, ta k'arasa ta zube a k'asa tana fad'in

"Sir barka da rana.." kamar be ji ba seda ya nemi waje ya zauna ya bud'e wani littafi sannan yace

"Barka..how can i help u?" yayi maganar a had'e

"Sir.. Pls zuwa nayi na rok'i alfarma"

"Umhum.." yayi maganar har lokacin yana kallan littafin hannun sa, sosae taji dad'in yadda ya amsa matan, dan haka seta gyara zama tace

"Sir dama Mama na ce tace a cikin malamae na samu wanda ze d'an dinga taemaka min da abinda bangane ba, shine.. Shine nace bari nazo na kar6i koda contact naka ne, idan ina da buk'atar taemako sena kira ka.." a hankali ya ajje littafin dake hannun sa ya d'aga kyawawan idanun sa ya zube su kan Bahijja, be san sanda ya basu fuska da har irin wannan raenin ze shiga tsakanin su ba, seya kwantar da kansa akan kujera hannayen sa duka biyun ya sark'e su cikin juna kana ya sanya su a ha6ar sa yana d'an juya kujerar daya ke kae, jin shiru ya sanya ta fad'in ba tare data d'ago ta kalle shi ba, dan tasan idan tace zata kalle shin wannan kwarjinin nasa da idanun nan nasa zasu sanya ta kasa fad'ar abinda tayi niyyar fad'a, koma gaba d'aya ta manta abinda zata fad'a d'in

"Shine dama abinda ya.."

"U shut up bloody fool.." ya fad'a cikin er d'aga murya yana sake watsa mata idanun sa, tuni ta rikice ta d'ago kamar zata yi kuka dan gaba d'aya ya gama rikita ta da wannan razananniyar muryar tasa, bata jira ya sake cewa komae ba ta mik'e jiki na rawa ta fice daga Office d'in, dogon tsaki yaja yana jin wani irin 6acin rae na taso masa, a hankali ya lumshe idanun sa yana sake kwantar da kansa kan kujerar..


Seda ta tsaya ta saeta kan ta sannan ta tura k'ofar d'akin nasu, dukan su suka kalle ta cikin mamakin ganin ta kamar a birkice kuma a firgice

"Bahijja lafiya?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, se tayi wani yak'e kafin ta nemi waje ta zauna tace

"Lafiya mana me kika gani?"

"A'ah babu komae" Ruks ta fad'a tana d'an ta6e baki

"Dama ke muke jira muna tattaunawa ne akan yadda zamu tunkari Doctor Rk da k'udirin mu, idan yaso seya za6i d'aya duk wadda ya za6a kuma ragowar se suyi hak'uri.." a hankali ta zuro k'afafun ta daga kan gadon da take kae ta kalle su su duka sannan tace

"Sam banga amfanin mutum mara kirki ba, wanda be san darajar d'an adam ba, ku kamar ma bakwa ganin abinda yake min" Ayrah ta fad'a dan yau sun gama kae ta bango, kullum cikin zancen sa suke amma sau 2 yana mata d'iban albarka basu ta6a nuna sun gani ba ko sun sani, dukkan su suka kalle ta yadda tayi maganar da alama abin na mata ciwo a rae, Jidda ta dafa cinyar Ayrah tace

"K'awa ta mutumin nan fa in dae kabi k'a'idar sa toh zaka zauna lafiya, though dae he is not friendly but he is nice wallahi, baya son hayaniya kamar yadda bashi da hayaniya, daga zarar kin san halin sa fa shikenan babu wata matsala da zata sake faruwa tsakanin ku" ta6e baki Ayrah tayi dan ita dae ba taga inda za'a yabi mutumin ba, kuma ma meye had'in ta dashi da har zata tsaya sanin halin sa? Banda ma dae ita za tayi missing da wallahi ba zata sake zuwa ajin nasa ba in dae tasan shine ze d'auke su, kawae seta mik'e ta shige toilet, Jidda ta dawo da duban ta kan su Ruks tace

"Yawwah ya kuke ganin za'ayi?" Bahijja ta ta6e baki

"Nifa bana tunanin ze za6i wata a cikin mu wallahi, ina ganin kawae mu hak'ura mu bar abin a ran mu" tayi maganar tana fatan duk su hak'ura d'in su bar ta ita tayi yak'in ta ita kad'ae, shek'ek'e duka suka kalle ta kafin Ruks tayi k'arfin halin fad'in

"Kee.. Akwae mummuna ne a cikin mu? Ko kuma dae ke kin sare, idan kin sare ne just tell us kinga yanzu yak'in ya rage tsakani na da Jidda" Bahijja ta ta6e baki kawae ba tare da tace komae ba, Jidda tace

"Idan baki janye ba toh zamu ware rana ne muje duk cikin dabara mu isar da sirrin dake zuciyoyin mu" da sauri Bahijja ta kalle su, kallan nan irin na baku da hankali wanda bata san tayi musu shi d'in ba seda taga suna bin ta da kallan tuhuma sannan tayi k'ok'arin saeta kan ta.....


Mhiz Innocent.....✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 015_016



___"Bahijja!" Ruks ta fad'a tana sake kallan ta sosae, seta gyara zaman ta sannan tace bayan ta saki wani murmurshin yak'e

"Na'am, ehh haka ya kamata muyi kam.." daga haka basu sake cewa komae ba suka yi shiru se dae kowa da abinda yake sak'awa a cikin ransa. A hankali ta k'arasa bakin gadon ta chanja hijab d'in jikin ta da wani sannan ta kalle su su duka tace har lokacin fuskar ta ba yabo ba fallasa

"Zan d'an je na dawo" ta fad'a tana shirin ficewa daga d'akin, mik'ewa Jidda tayi tace bayan ta d'auki mayafin ta

"Muje na raka ki.." kamar tace ta barshi se kuma taga kamar hakan be dace ba dan haka seta dakata ta jira Jiddan har ta k'araso inda take suka fita tare. Ba laefi yanzu suna tafiyar suna d'an ta6a hira, hirar da se Jidda ta d'auko ta sannan Ayrah kan amsa mata har zuwa sanda Jiddan tace

"Ina zamu je wae?"

"Mango zan siyo.." harara Jidda ta jefa mata sannan tace

"Amma shine baki fad'a min ba, toh ae mun wuce wajen masu siyarwar"

"Aou mantawa nayi" ta fad'a tana dariya gami da sanya hannun ta akan bakin ta, daga haka suka juya Jidda ta kae su wajen da masu saeda fruits suke sosae, kae tsaye wajen me mango d'in suka je, Ayrah ta fad'a masa adadin data ke so, shi kuma ya fara zuba mata cikin leda. A hankali wata bak'ar had'ad'd'iyar mota ta gangara ta tsaya kusa da me siyar da mangon, su biyu ne cikin motar Rk zaune a wajen me zaman banza yana danna waya, yayin da Yaseer ke driving, kallan sa yayi sanda yaga yayi parking motar a wani waje daban, da mamaki yace

"A'ah meye haka?" Yaseer yace

"Fruit zan d'an siya, sun min kyau gaskiya.."

"Oh god, ji wani kuma" Rk ya fad'a yana watsa masa harara, Yaseer yace

"5 min pls.." ya fad'a sanda yake bud'e motar yana kuma d'aga hannun sa, Rk bece komae ba se d'aga kafad'a da yayi gami da ta6e baki lokaci d'aya yana maeda kansa kan wayar sa, wajen minti 2 da fitar Yaseer d'in, a hankali ya d'aga manyan idanun sa ya kalli

Please Login or Register in order to submit comment