Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koda yaushe, tunda suka shiga motar Ayrah keta basu labarin abinda ya faru a makaranta, Abba nata biye mata, yayin da wani lokacin Yah Sadeeq ya amsa mata wani lokacin yayi shiru har zuwa sanda suka isa gida, Abba ya sauke su a inda ya saba sauke su sannan ya wuce da motar tasa zuwa inda ya saba ajiye ta.. Sun riga shi shiga gida, da gudu Ayrah ta shige gidan tana k'walawa Umma kira, Umma dake kitchen ta fito tana kallan su tace

"Sannun ku da zuwa yaran kirki" Yah Sadeeq ne ya amsa da

"Yawwah Umma" yana cire jakar bayan sa, kallan sa Umma tayi sannan tace

"Zaka fara cin abinci ne ko seka yi wanka?"

"A'ah Umma bari nayi wankan, ina so ne nayi muraja'a kafin muje Islamiyya"

"Ohk tohm" ta fad'a tana maeda duban ta kan Ayrah dake rik'e da hannayen ta

"Umma kinsan me?" ta fad'a tana ware manyan idanun ta, murmushi Umma tayi sannan tace

"A'ah sekin fad'a.." seta ta6e baki kamar wata babba sannan tace

"Umma wani yaro a makarantar mu kullum sena ganshi idan Uncle ya shigo yana lek'e ta window"

"Shi ba d'an makarantar bane?" Umma ta fad'a tana kallan sa

"Ehh Umma" Ayrahn ta fad'a kawae ba dan tana da tabbacin abinda ta fad'a ba

"Ke banda sharri.." Yah Sadeeq dake shirin mik'ewa ya fad'a

"Allah kuwa da wasa nake.." ta fad'a dan ita a hausar ta idan tace da wasa take toh tana nufin da gaske take, idan kuma tace da gaske take toh tana nufin da wasa take, ta fad'a tana d'an rufe idanun ta hannun ta a saetin bakin ta

"Lallae.." Yah Sadeeq ya fad'a yana mik'ewa da dariya akan fuskar sa na wannan hausar ta Ayrah

"Toh yanzu dae muje na shirya ki ku wuce makaranta.." Umma ta fad'a dan tasan shirmen Ayrahn, Umman da kanta ta mata wanka ta sanya mata kayan Islamiyyar sannan suka fito suka ci abinci kana suka wuce Islamiyyar.. Washe gari ma hakan ce ta kasance koda suka je makarantar seda taga wannan yaron yana lek'e ta taga har zuwa sanda Abba yazo ya d'auke su, tunda suka shiga motar Yah Sadeeq ya fahimci akwae matsala dangane da mahaefin nasu saboda gaba d'aya yanayin sa ya chanja, amma ita kuwa Ayrah yarinta besa ta fahimci hakan ba ta cigaba da hirar data saba musu, inda Abban ke iya k'ok'arin sa wajen biye mata.. Tunda suka shiga gidan ya kasa mik'ewa ya tafi d'aki yayi wanka, dan haka sallah kawae yayi ya cigaba da zama cikin d'akin har zuwa sanda Abban ya shigo da sallama zuwa cikin d'akin, shi da Umma suka amsa sallamar tasa suna binsa da kallo, haka kawae k'irjin Umma ya buga da ganin yanayin Abban da bata saba gani a tattare dashi ba, amma se ba tace komae ba ta barshi ya zauna tace a hankali

"Sannu da zuwa Abban su.."

"Yawwah" ya fad'a ba tare daya kalle ta ba

"Abba sannu da zuwa" Yah Sadeeq ya fad'a yana kallan Abban, mik'ewa Umma tayi da niyyar samo masa ko d'an ruwa ne wanda ze sanyaya masa zuciya, amma se taji yace

"Dawo ki zauna kiji abinda ya same mu kuma.." babu musu ta dawo ta zauna tana jin k'irjin ta na cigaba bugawa, ganin kamar zaman nasa beyi bane ya sanya shi mik'ewa tunda duk alama ta nuna iyayen nasa magana zasuyi

"Sadeeq dawo ka zauna.." Abba ya fad'a yana kallan Yah Sadeeq, komawa yayi daga niyyar tashin da yake yi, Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Wato ina chanjin dana fad'a miki anyi na principles da sauran manyan masu muk'ami?" Umma ta lumshe idanun ta sannan tace

"Ehh.."

"Toh tsautsayi ya biyo ta kanmu, an sallame mu..wae zasu kawo wasu sababbi.." Abba ya fad'a yana jin ciwon hakan har cikin ransa

"Innalillahi wa inna ilaehi rajiun.." Umma ta fad'a tana jin wani iri, lokaci guda kuma tana kallan Abban cike da tausayawa

"Abba me kuka yi musu?" Yah Sadeeq ya fad'a fuskar sa cike da alhini, d'an murmushi Abban ya saki me cin rae kafin yace

"Kada ka damu Sadeeq In Sha Allah ae Allah ba azzalimin bawan sa bane, da sannu duk wani me mugunta a fad'in duniyar nan ze girbe abinda ya shuka.." Abba ya fad'a kafin ya maeda duban sa kan Umma da har lokacin ta kasa furta komae bayan salatin da tayi

"Ina ganin lokacin hak'ura da aekin gwamnati yayi, tunda nayi har sau 2 Allah beyi zan d'ore ba.." da sauri Umma ta d'ago ta kalle shi tace

"Toh Abban su idan ka hak'ura ya za'ayi kenan?" murmushi me ciwo yayi sannan yace

"Kinga dae aekin Bank d'in nan seda na sakankance suka zo suka dakatar damu, yanzu ga wannan ma, bana so na sake neman wani shima na sakankance kuma azo a samu matsala, yaran nan karatu suke yi, muma akwae buk'atun mu na yau da kullum, saboda haka.." seya d'an dakata kad'an kafin ya d'ora da fad'in

"Ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, maganar wannan shagon In Sha Allah zan maeda hankali a kanta, Allah ya saka mana" Abba ya fad'a yana mik'ewa, dukkan su suka bi Abban da kallo cike da tausayawa, dan Abban wani mutum ne wanda kafin ka ganshi cikin 6acin rae se an dad'e, se an matuk'ar kaeshi bango sannan hakan kan bayyana akan fuskar sa, Umma ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"In Sha Allah se Allah ya sakawa me gaskiya.." ta fad'a itama tana tashi, Yah Sadeeq ya amsa da

"Ameen Umma.." dae_dae lokacin da Ayrah ta fito daga d'aki kamar koda yaushe da d'an gudun ta

"Umma ba'a min wankan ba fa" ta fad'a tana ta6e baki, Umma tace bayan ta d'an yi murmushi

"Gani nan, dama yanzu can zance muje.." ta fad'a tana kama hannun Ayrahn zuwa d'aki..


.... Duk da abin nan daya faru hakan be hana Abba d'aukar 'ya'yan nasa yakae makaranta ba, sedae har lokacin bashi da walwala dan gaba d'aya hankalin sa na kan abinda ze cigaba dayi dan cigaba da kula da harkokin iyalin sa, ga rashin bacci daya samu a jiyan hakan ya k'arawa yanayin nasa rashin armashi, bayan ya sallame su suka masa a dawo lafiya sannan ya tashi motar sa, Yah Sadeeq ya kalli Abban nasu dan shi kanshi jiya kafin ya kwanta da Abban nasu ya kwana, duk da k'ananun shekaru irin nasa wanda ba zasu wuce 12 ba yana da hankali da nutsuwa, shiyasa wani lokacin Abban ke d'aukar sa kamar d'an shekara 20 dan ko shawara zeyi da Umma yana barin Yah Sadeeq d'in ya zauna a wajen suyi shawarar tare

"Abba Allah ya bada sa'a, ya tsare, Allah ya kiyaye hanya.." ya fad'a kamar yadda suka sabawa Abban addu'a idan ze fita, murmushi Abba yayi kana yace

"Ameen Sadeeq, Allah ya baku sa'a kaji, ka cigaba da taya ni da addu'a.."

"Toh Abba.." Yah Sadeeq d'in ya fad'a yana wucewa...


... Sanda aka fito break bayan sun gama cin abincin kamar yadda suka saba, se suka fito zuwa harabar makarantar, ta kalli inda ta saba ganin sa kamar koda yaushe yana zaune yanzun idanun sa kan wata takadda yana kalla, a hankali ta fara takawa zuwa inda yake zaunen idanun ta a kansa

"Ayrah..er carafke fa muma yau zamu yi" wata k'awar ta da itama ba zata wuce sa'ar ta ba ta fad'a da maganar ta me cike da tsamin baki, bata ma jita ba dan gaba d'aya hankalin ta yayi kansa, har zuwa sanda wata a cikin k'awayen nata ta dafa ta tana fad'in

"A'ah ki taho enter zamu yi" ta fad'a tana dariya, hannu Ayrah ta saka ta zame hannun k'awar ta ta dake kan kafad'ar ta sannan tace

"Ke ni ba zanyi ba.." daga haka tayi gaba, su kuma yaran duk basu bi ta kanta ba suka cigaba da wasan su, seda ta isa inda yake d'in sannan ta tsaya tana cigaba da kallan sa da kuma kayan dake jikin sa, a k'alla zeyi shekaru 12 ne, fari ne sosae kyakykyawa ajin farko, me manyan idanu da dogon hanci, ga wata bak'ar suma dake kwance akansa sedae daga gani kasan bata samun yadda take so dan haka ta d'an cukurkud'e kad'an, kayan jikin sa ma haka kana ganin su kasan sunji jiki amma da alama shi duk wad'annan basu dame shi ba dan kuwa har lokacin idanun sa na kan takaddar hannun sa ne

"Kae!!" Ayrah ta fad'a tana kallan sa, da sauri ya d'aga manyan idanun sa ya sauke su akan Ayrahn, bece komae ba seya maeda kansa kan takaddar sa

"Kae!!" ta sake fad'a a karo na, d'an lumshe idanun sa yayi sannan ya ninke takaddar a hannun sa ya mik'e, yana k'ok'arin barin wajen Ayrah tace

"Kawo na koya maka.." seya d'an dakata kad'an kafin ya juyo yana kallan ta, hannu ta mik'a ta kar6i takaddar hannun sa tana kallan abinda ke ciki, ta karanta da karatun data iya sannan ta kalle shi yadda shima ita d'in yake kalla, seta saka dariya kawae hadda toshe baki kamar wata babba, dama fuskar tasa babu annuri yanzu kuma da yaga tana masa dariya seya sake tsuke ta ya sanya hannu ya kar6i takaddar hannun ta ya juya da nufin barin wajen, hannun ta ta saka ta rik'o nasa hannun, manyan idanun ta sun cika da k'walla tace

"Yi hak'uri, gani nayi kae babba ne fa.." ta fad'a abinda take ganin shine ya dace ta fad'a

"Allah kuwa idan kana so zan fad'awa Yah Sadeeq ya dinga kowa maka karatu.." seya juyo gaba d'ayan sa yana kallan ta lokaci d'aya murmushi na su6ucewa akan fuskar sa yace

"Da gaske?" karo na farko kenan da yayi magana, seta jinjina kae kawae tana d'an murmushi...


Ku sani wannan book d'in ina yin sa ne based on experience, zan iya cewa wani abun ma true ne wlh nake had'a muku dashi duk dan labarin ya k'ara armashi kuma ku fahimci sak'on da nake son isarwa, Allah yasa mu dace..


*ZARAH BINT YUSUF (Mhiz Innocent)*✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page_003



___"Ke Ayrah!!" Yah Sadeeq ya fad'a yana k'arasowa wajen, dukkan su suka d'aga kae suka kalli inda yake, bata motsa daga inda take ba sedae ta cigaba da kallan sa har ya k'araso wajen, ya kalli inda yaron nan ke tsaye na tsawon sakanni sannan ya maeda kan Ayrah, kama hannun ta yayi ba tare da yace komae ba suka bar wajen, yayin da shi kuma ya bisu da ido har suka bar wajen, seda suka isa bakin ajin su sannan ya tsaya ya kalle ta fuskar sa a had'e yace

"Meya kae ki can?" rau rau tayi da idanun ta, tana ta6e d'an k'aramin bakin ta kamar zata yi kuka

"Ba nace miki ba'a wasa da maza ba?" jinjina kae kawae tayi, yace

"Bari na sake ganin ki da wani!" ya fad'a yana sake had'e rae dan ta fahimci da gasken yake

"Ya hak'uri Yah Sadeeq.." ta fad'a tana share k'wallar idanun ta, seya d'an yi murmushi kana yace

"Yawwah..toh maza ki koma aji.." daga haka ta shige class d'in su shima ya tafi nasu ajin.


.. Washe gari ma haka ta sake ganin yaron nan yana lek'e ta window, koda aka fita break seta ajjiye basket d'in ta a cikin ajin sannan ta fita zuwa inda ta ganshi a bayan ajin nasu yau sa6anin da da yake zama a gaban ajin nasu, yana zaune yau ma kamar jiyan yana karanta wata takadda dake hannun sa, seta k'arasa ta zauna tace

"Wae kae ba'a saka a makaranta ba?" tayi maganar cike da sakarci, da sauri ya juyo yana kallan ta dan besan da zuwan ta wajen ba maganar ta kawae yaji, ganin ta ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan ya jinjina kae

"Kawo na koya maka toh" ta fad'a tana kallan sa, seya lumshe manyan idanun sa sannan ya mik'a mata takaddar hannun nasa, ta kalla abinda ke cikin takaddar, abinda aka koya musu yau ne seta dinga fad'a masa yadda ta fahimci aekin, shi kuma yana biye mata yana jin abinda take koya masan, kasancewar k'wak'walwar tasu ba d'aya bace kuma karatun su Ayrahn na yara ne yasa cikin k'ank'anin lokaci tana masa yake ganewa, tunda ta fara bece komae ba yayi shiru yana saurarar ta yana kallan ta yadda take maganar duk da ba wani iya magana tayi ba amma yana ganewa, wani abun ne dae sedae idan ta fad'a ya gyara da kanshi, idan ya fahimci bata san yadda zata fad'a ya gane ba, tana ji an kad'a k'ararrawa alamar an koma break seta yarda takaddar hannun ta ta mik'e tana waro idanun ta

"Na tafi.." ta fad'a tana shirin wucewa yace

"Nagode..ya sunan ki?" seta juyo ta zuba masa manyan idanun ta sannan tace bayan tayi murmushi

"Ayrah.." ta fad'a tana juyawa, kamar wadda ta tuno wani abun seta juyo da sauri tace

"Kae fa?" murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sannan yace

"Suraj..."

"Suraj!!" ta maemaeta sunan a la66an ta sannan ta wuce ba tare da ta sake cewa komae ba ta koma ajin su.


... Abba na sauke su a inda ya saba sauke su se suka tafi gida, kamar kullum da sallama suka shiga gidan nasu, Umma na zaune kan dadduma da alama sallah ta idar, tayi musu sannu da zuwa tana rik'e Ayrah data rungume ta

"Tashi ki kae basket d'in kitchen.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah

"Umma akwae abinci a ciki fa" da mamaki Umma ta kalle ta kana tace

"Baki cinye ba?" girgiza kae Ayrah tayi tace

"A'ah banci ba fa" mik'ewa Umma tayi rik'e da Ayrahn a hannun ta tace bayan ta zauna

"Baki da lafiya ne ko a k'oshe kike?"

"Ehh" Ayrahn ta fad'a tana cire hannun ta daga cikin na Umma ta wuce d'aki, Umma ta bita da kallo tana girgiza kae sannan ta dawo dashi ga Sadeeq dake tsaye tace

"Meya hana ta cin abincin?" girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace

"Wallahi Umma bansani ba, kuma amma banga alamar rashin lafiya a tattare da ita ba ballantana ace koh?"

"Ehh hakane, may be ko yau a k'oshe take, ko kuma kana so ka koya mata halin ka" Umma ta fad'a tana kallan sa, murmushi Sadeeq yayi yana wucewa d'aki..

... Suna zaune a parlourn suna cin abinci, ita a d'an k'aramin plate d'in data saba cin abinci a ciki wanda indae ba'a ciki aka zuba mata ba bata ta6a cin abincin, yayin da Yah Sadeeq ke zaune kan kujera shi kuma yana rubutu a littafi, ita kuma Umma tana zaune kusa da Ayrahn itama tana cin nata abincin a plate, kallo suke a er madaedaeciyar Tvn su, tashar MBC bollywood suke kalla inda suke nuna film d'in Mujhse Dosti Karoge, sosae Ayrah ke kallan duk da ba wani fahimta take ba, daga film d'in hausan har na Indian kawae tana zama ne idanun ta duka akan Tvn amma in za'a tsare ta a tambaye ta ba ganewa take ba

"Raj.." taji an fad'a a cikin film d'in, seta sake kallan cikin Tvn sosae, shiru tayi tana tuna sunan wannan d'in nan daya fad'a mata

"Suraj.. Raj.." ta fad'a a fili tana saka hannun ta a kumatun ta kamar me tunani

"Ayrah.." Umma ta fad'a tana kallan ta, seta kalli Umman kafin Umman ta sake cewa komae tace

"Umma irin sunan wani d'an ajin mu.."

"Wanne?" Umma ta fad'a tana kallan ta

"Raj.."

"Anya kuwa?" Umma ta fad'a tana kallan ta, jinjina kae tayi kana tace

"Allah kuwa Umma, shima sunan sa Raj"

"Toh yayi, k'arasa cin abincin ki" babu musu ta cigaba da cin abincin ta tana yi tana kallan Tvn.



... "Monitor jeka taho min da yaron can.." Uncle Abdoul ya fad'a yana kallan Monitorn ajin su Ayrah, tashi yayi ya fita daga ajin, ya zagaya inda Uncle d'in yake nuna masa, yana zaune gaba d'aya ya gama muzanta haka kuma ya tsorata, yana ganin shikenan daga yau korar sa za'ayi a hana shi shigowa makarantar gaba d'aya, be ta6a tunanin za'a iya ganin sa ba dan yadda yake takatsantsan akan kar wanda ya ganshi, se gashi yau malami da kansa ya ganshi, ya d'an runtse idanu kad'an yana jin kwata kwata babu dad'i

"Wae kazo inji Uncle" maganar data sanya shi saurin bud'e idanun sa kenan yana kallan yaron da yazo kiran sa, k'irjin sa na bugawa haka ya mik'e yana jin kamar ya gudu amma beyi hakan ba yabi bayan sa har zuwa cikin ajin, a k'ofar ajin ya tsaya ya kasa yin gaba ko baya har zuwa sanda monitorn ya wuce wajen zaman sa ya zauna

"K'araso ciki" Uncle d'in ya fad'a yana kallan Suraj, ya kasa d'aga ido gaba d'aya ya kalli cikin ajin dan yasan idanun kowa na kansa ne

"Me yake kawo ka nan?" Uncle Abdoul ya tambaya, kasa cewa komae yayi dan baya jin ze iya fad'in wani abun

"Wani abun kake siyarwa?" k'arya bata daga cikin halayen sa amma yau yana ganin gwara yayi tan, dan haka kawae ya jinjina kae

"Toh kada ka sake zuwa nan wajen siyar da abu saboda kana d'aukewa wasu hankali, ka tafi can harabar makaranta ka dinga siyarwa.. Ina kayan siyarwar taka?"

"Toh.. Suna waje.." ya fad'a a hankali

"Tashi kaje toh.." Uncle ya fad'a, da sauri ya mik'e cike da sassarfa ya fice daga ajin, binsa tayi da kallo dan tunda ya shigo take kallan sa har zuwa sanda ya fita d'in.. Ana fita break kuwa ta zagaya inda ya saba zama, yana zaune se dae sa6anin yadda take ganin sa da takadda a hannun sa yanzu ya d'ora kansa akan cinyar sa ne, ta k'arasa ta zauna sannan tace a hankali

"Raj.." maganar da yaji ya sanya shi d'aga idanun sa ya kalle ta, seya maeda kansa kawae yayi shiru

"Toh na dena kula ka" ta fad'a tana tura d'an k'aramin bakin ta gaba kuma tana shirin mik'ewa, da sauri ya juyo yana kallan ta se tace

"Toh me aka maka?" ta fad'a har ranta tana jin ba dad'i na yanayin data ganshi, seya sake d'agowa ya kalli idanun ta da suka yi rau rau kamar za tayi kuka, da sauri ya girgiza kae kafin yace a nutse

"Ance kar na sake lek'awa cikin ajin.."

"Ya hak'uri" ta fad'a kamar me shirin yin kuka, bece komae ba illah kallan ta kawae da yake yi, ta rufe idanun ta sannan ta bud'e tace

"Kawae ka dena lek'awa zan dinga koya maka komae kaga ni babba ce" ta fad'a tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace

"Tohm nagode.."

"Ae ni babba ce koh?" ta fad'a tana kallan sa, ya sake yin murmushi sannan yace

"Ehh sosae ma"

"Yeah" ta fad'a tana dariya har da rufe fuskar ta.

Tun daga ranar ya kasance kullum taje makaranta idan aka fita break bata cin komae sedae ta tafi wajen Raj ta zauna ta koya masa duk abinda aka koya musu, kuma In Sha Allah kullum ta koma gida se tayi wa Umma zancen Raj, babu ranar banza da za'a tashi a kwanta Umma ba taji maganar Raj a bakin Ayrah ba. Yau ma kamar kullum yana zaune yana jiran ta dan yanzu yama dena lek'e ya hak'ura gaba d'aya, yafi ganewa idan tazo d'in kawae ta koya masa

"Raj.." yaji ta fad'a daga inda yake zaune, se yayi murmushi ya juya yana kallan ta dan ba tun yau ba yake fad'a mata sunan sa Suraj ba Raj ba amma ita ta kasa chanjawa kullum da Raj take kiran sa, dan haka yanzun har ya hak'ura ya dena tuna mata idan ta kira shi da Raj d'in kawae amsawa yake yi, tazo ta zauna da littafin ta a hannu, d'ayan hannun nata d'auke da mangoro guda d'aya irin babban nan, ta shiga koya masa abinda aka koya musun, tana yi tana shan mangoron ta cikin nishad'i, yana lura da yadda take sha wani lokacin har da lumshe ido amma yarinta besa ko bismilllah tayi masa ba

"Kina san mangoro ne?" yayi maganar yana kallan ta, da sauri ta d'aga kae ta kalle shi sannan ta jinjina kae tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace

"Zan dinga tsinko miki a wata bishiya"

"Don Allah?" ta fad'a tana kallan sa

"Ehh" yace, sannan suka cigaba da karatun su..


... "Wae Ayrah me yake damun ki ne? Kullum kika fita da abinci sedae ki dawo dashi babu abinda aka ta6a a cikin sa?" Umma ta fad'a tana tsare Ayrah da idanun ta, ba tace komae ba se tura bakin ta da tayi hawaye na taruwa a manyan k'wayar idanun ta

"Umma shi fa baya zuwa makaranta, shine nake koya masa" tayi maganar tana kallan Umma

"Waye?" Umma ta fad'a da mamaki

"Raj!" Ayrah ta fad'a kae tsaye

"Oh god" Umma tace tana dafe goshin ta, wae wanene Raj d'in nan ne? Kullum garin Allah se Ayrahn tayi zancen sa

"Kikace d'an ajin ku ne kuma?" girgiza kae Ayrah tayi sannan tace

"Allah kuwa Umma da gaske nake" murmushi Umma tayi kad'an sannan tace

"Toh me yake kawo shi makarantar?" Shiru tayi da alama bata fahimci tambayar Umman ba, sema cewa da tayi

"Umma shi nake koyawa karatu fa in an fita break" da mamaki Umma ke kallan Ayrahn, tace har lokacin tana kallan ta

"Yaro ne?" girgiza kae tayi tana ta6e baki kana tace

"A'ah babba ne." ta fad'a tana kae hannun ta sama kamar me auna tsayin wani

"Babba kamar wa?" Umma ta fad'a

"Kamar Yah Sadeeq" d'an sauke ajiyar zuciya Umma tayi dae_dae lokacin da Abba yayi sallama cikin d'akin, da gudu Ayrah ta tafi ta rungume Abban tana fad'in

"Abba sannu da zuwa" hannu ya saka ya d'aga ta sama sannan yace

"Yawwah an baby" ya fad'a yana sauke ta sannan yaja hannun ta zuwa cikin d'akin suka zauna

"Sannu da zuwa Abban su" Umma ta fad'a tana kallan Abba, kallan ta Abba yayi yana karantar yanayin ta cikin kulawa yace

"Wani abu ya faru ne?" girgiza kae tayi sannan tace

"A'ah kawae dae Ayrah ce.."

"Me Ayrahn tayi?" Abba ya fad'a yana gyara zaman sa, ajiyar zuciya Umma ta sauke tana bin Ayrah da kallo wadda tayi cikin d'aki da gudu

"Kamar kasan sunan Raj a bakin Ayrah koh?" d'an shiru Abba yayi sannan yace

"Ehh k'warae, kamar d'an ajin su koh?" girgiza kae Umma tayi sannan tace

"Bana tunanin d'an ajin su ne, a yadda take bani labari kuma na fahimta, kamar ba'a makarantar yake ba, ina nufin baya zuwa makaranta, kuma yana son karatu shiyasa yake zuwa yana lek'e a ajin su.."

"Lek'e kuma?"

"Wallahi kuwa Abban su, nima abin ya bani mamaki"

"Ikon Allah.." Abba ya fad'a yana jinjina kae

"Shikenan In Sha Allah zan binciki al'amarin, idan da akwae halin taemakawa sena taemaka masa" murmushi Umma tayi kana tace

"Allah ya saka da alkhaeri Abban su, ya k'ara bud'i.." ire iren halayen Abban dake sake birgeta kenan, duk da shima ba wani k'arfin hali yake dashi ba amma yana iya k'ok'arin sa wajen ganin ya taemakawa wanda ke k'asan sa kuma mabuk'aci, shima murmushin Abba yayi sannan yace

"Albishirin ki.."

"Goro.." Umma ta fad'a tana gyara zama

"Alhaji mato ya yadda ze bani hayar shagon nan, idan yaso a hankali sena dinga biyan sa.."

"Kae Masha Allah, Alhamdulillah Allah mun gode maka" Umma ta fad'a fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi

"Toh amma ina tunanin Sadeeq yayi k'ank'anta da wanda ze dinga taemaka min, koma ba haka ba inaso dukkan su su samu karatu me zurfi.." Abba ya fad'a yana zurfafa tunani cikin k'wak'walwar sa, murmushi Umma tayi sannan tace

"Ae Abban su wannan me sauk'i ne In Allah ya yadda, tunda aka samu wannan"

"Hakane kuma.." Abba ya fad'a yana kallan Yah Sadeeq daya fito daga cikin d'aki sanye cikin Uniform d'in Islamiyya, ya k'araso ya zauna yana kallan Abban yace

"Abba sannu da zuwa"

"Yawwah Sadeeq..za'a tafi makarantar ne?"

"Ehh Abba"

"Toh Allah ya kiyaye" Abba ya fad'a, Sadeeq ya amsa da

"Ameen, Umma na tafi.." ya kae k'arshen maganar yana kallan Umma, itama addu'ar ta masa sannan ya fara k'ok'arin fita, yana dab da fita d'in Abba yace

"Afff, Sadeeq..!" juyowa yayi yana amsa kiran Abban sannan ya dawo, Abba yace

"Gobe idan kaje makaranta akwae wani yaro... Kikace sunan sa?" ya k'arasa maganar yana kallan Umma

"Raj.. Haka dae tace min sunan sa"

"Ikon Allah.." Abba ya fad'a yana maeda duban sa kan Yah Sadeeq yace

"Kaji sunan sa Raj, anan makarantar ku yake, ita Ayrah ta sanshi, seta nuna maka shi kazo min dashi idan an tashi"

"Toh Abba.." Yah Sadeeq ya fad'a yana ficewa daga d'akin, a ransa yana tuna sunan, kusan kullum se Ayrah

Please Login or Register in order to submit comment