Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi maganar me sunan amma be ta6a bawa zancen muhimmaci ba se kuma gashi Abba da kansa yace a kira masa shi...



*Zarah Bint Yusuf (Mhiz Innocent)*✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*




Page_004_005



____Tun kafin ta k'arasa ta hango shi zaune yana kallan inda ta saba 6illowa ta wajen sassanyan murmurshi kwance akan fuskar sa, itama murmurshin ta maeda masa sannan ta k'araso ta zauna, ya sake yin wani murmurshin sannan yace yana mik'a mata wata leda

"Gashi.." d'an bud'e manyan idanun ta tayi kamar wata babba sannan ta kar6a, tun kafin ta bud'e tasan menene dan haka ta rik'o hannun sa ta rungume tana jin dad'i tace

"Wae siyowa kayi?" girgiza kae kawae yayi yana ta6e baki, bata kuma bi takan zancen ba suka cigaba da abinda ya kawo su wajen, suna yi tana shan mangoron ta, shi kuma yana kallan ta hakan na masa dad'i ko ba komae shima yau yayi mata wani abun da taji dad'i..

Seda aka tashi daga school d'in sannan Yah Sadeeq ya kama hannun Ayrah dake jiran sa a k'ofar ajin su

"Muje ki kae ni wajen Raj" ya fad'a har lokacin suna tafiya, babu musu ta gyad'a kae tana cigaba da wasan ta hannun ta cikin nasa a haka har suka k'arasa inda tasan zasu same shi, cikin sa'a kuwa se suka tadda shi a tsaye da alama shima ya gama abinda zeyi zeyi gaba ne, juyawar da zeyi se suka had'a ido da Yah Sadeeq, sosae k'irjin sa ya buga sanda yagan su suna cigaba da tahowa inda yake, kawae se ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya, sam idanun sa be sauka akan Ayrah da keta yi masa murmurshi ba, a hankali ya lumshe manyan idanun sa dae_dae lokacin da suka ida isowa dab dashi, Yah Sadeeq yace yana kallan sa

"Sannu.." d'aga ido yayi ya kalle shi se dae ya gaza cewa komae dan be san da wanne shi kuma yazo ba, se dae ga mamakin sa se yaji yace

"Abban mu na son ganin ka idan babu damuwa" idan babu damuwar daya ambata shi ya sanya ya d'an ji sanyi dan da farko har ya fara tunanin ko za'a raba shi ne da Ayrah, amma abinda be gane ba shine meye had'in sa da Abban nasu? Ko dae abinda zuciyar tasa ke harsashe ne kawae dae yayi amfani da kalmomi biyun nan dan kada ya saka masa shakku akan maganar?

"Zamu iya tafiya?" ya tsinto maganar Yah Sadeeq d'in

"Toh" ya furta cikin rashin sanin mafita

"Yau a gidan mu zaka kwana Raj?" Ayrah ta fad'a tana cigaba da tsalle tsallen ta, suna gaba yayin da Raj ke bayan su har suka k'arasa bakin Gate d'in ya cigaba da binsu zuwa wani waje ke6antacce kuma rufaffe wanda anan ne suka saba zama su jira Abban, Yah Sadeeq ya nemi waje ya zauna yayin da shi kuma ya tsaya a gefe tunani fall cikin ransa, Yah Sadeeq na zama Ayrah ta zame hannun ta zuwa wajen Raj ta fara masa surutu yayin da yau gaba d'aya yake jin sa a takure musamman da yake kusa da wata bak'uwar fuska, dan haka amsar sa ta zama bata wuce murmurshi da gyad'a kae, shi kam Yah Sadeeq bin su kawae yake da kallo yana mamakin yadda Ayrahn ta saba da shi cikin k'ank'anin lokaci, basu dad'e da zama ba Abba ya iso, ita ta fara yin gaba da gudu sanda ta hango Abban, Yah Sadeeq yabi bayan ta, seda ya kusa isa inda motar Abban take sannan ya tuna da Raj, ya juyo ya kalle shi yace

"Ka taho ga Abban namu nan yazo" binsa yayi a baya suka k'arasa har inda Abban yake, Yah Sadeeq ya bud'e front seat ya shiga yayin da Ayrah ta shiga baya, Abba yabi Raj da kallo dake tsaye a waje kafin ya maeda duban sa ga Yah Sadeeq yace

"Shine wannan?" jinjina kae yayi kafin yace

"Ehh Abba"

"Koma baya shi kuma ya shigo nan" Abba ya fad'a yana sake Kallan Raj, fitar yayi ya kalli Raj da Ayrah ke kalla tana fad'in

"Ka taho mu tafi" ya kalle ta yayi murmurshi sannan ya maeda duban sa kan Yah Sadeeq daya fito daga motar

"Ka shiga Abban na ciki"

"Tohm" ya amsa da hakan yana k'arasawa ya shiga gaban dake a bud'e ya zauna

"Barka da wannan lokaci" ya fad'a kansa a k'asa, cigaba da kallan kyakykyawan yaron Abba yayi wanda yake sa'an d'an sa Sadeeq, tun kafin ya kaega cewa yaron komae yaji wata nutsuwa tattare dashi amma duk seya watsar yace

"Barka dae..yaya sunan ka?" Abba ya fad'a yana gyara zaman sa a inda yake zaune, har lokacin be d'ago ba ya furta

"Suraj.."

"Kaee Raj dae.." Ayrah dake baya ta fad'a tana waro idanun ta, dukkan su murmurshi suka yi kafin Abba ya sake cewa

"Mahaefin ka fa?"

"Kabeeru" jinjina kae Abba yayi sannan yace

"Baka zuwa makaranta ne?" se a lokacin ya d'ago kae ya kalli Abban sannan ya maeda kan nasa k'asa yace

"Ehh" d'an shiru Abba yayi yana tunanin tambayar da zata fito daga bakin sa haka dae ya cije yace

"Suraj meyasa baka zuwa makaranta?"

"Abba Raj ne fa" Ayrah ta sake fad'a, girgiza kae Abba yayi da d'an murmurshi akan fuskar sa kafin yace

"Toh shikenan Raj" Yah Sadeeq dake gefen ta shima murmurshin yayi yana girgiza kae

"Abbu bashi da kud'in saka ni.."

"Shikenan kawae, idan nace zan saka ka zaka ji dad'i?" da sauri ya d'ago kae ya sake kallan Abban, ya lumshe idanun sa yana jin dad'i har besan sanda ya jinjina kae ba murmurshi na wanzuwa a kyakykyawar fuskar sa ba, Abba ma yayi murmurshi yace

"Ka fad'a wa Abban naka idan yana da lokaci ya same ni a gida akwae maganar da zamu yi.." amsawa yayi da

"Toh angode, Allah ya saka da alkhaeri"

"Ameen" Abba ya fad'a yana sake yabawa da hankalin yaron, be bar cikin motar ba seda Abban ya bashi number sa yace ya kaewa Abban nasa ya kira shi..

(_A gurguje zanyi wajen nan pls, saboda idan nace zan ja nan d'in da nisa gaskiya zamu dad'e ne bamu matsa gaba ba, so shys nayi deciding kawae nayi briefing wajen amma yadda zaku fahimta_)


... Sanda Raj ya jewa da Iyayen sa maganar Abban sosae suka yi mamaki, dan da farko ma daya fad'awa Ummeen sa cewar mutumin yace ze sanya shi a makaranta bata yarda ba k'aryatawa tayi kuma ta rufe shi da fad'a dan lokacin ma tun safe babu abinda suka ci kuma har zuwa lokacin Abbun nasa be dawo ba, dama shine me fafutuka ya fita yayi er buga buga ya samo musu abinda zasu ci amma takamaemae bashi da tsayayyiyar sana'a, shiyasa idan ya fita ma ya samo wani abun gaba d'aya suna amfani dashi ne wajen samun abinda zasu ci

"Toh hayaniyar me nake ji kuma da rana tsakar nan" maganar da taji daga tsakar gidan ne ya sanya ta dakatawa daga fad'an da take wa Raj, Malam Kabeeru ya k'araso hannun sa d'auke da wata leda, seta k'arasa ta kar6a tana fad'in

"Sannu da zuwa Abbu"

"Yawwah sannun ka dae" ya fad'a yana kallan Raj dake fad'in

"Abbu sannu da zuwa" amsa sannu da zuwan yayi kafin yaja kujera er tsuguno ya zauna a tsakar gidan yana sauke numfashi

"Meya faru ne kike ta fad'a tun daga soro nake jiyo muryar ki?"

"Gashi nan yaron nan yazo min da wani zance wae wani mutumi yace ze sanya shi makaranta wae kuma ya bashi number sa ka ganta ma yace wae kaema kaje yana neman ka" ta fad'a tana mik'a masa wata takadda dake d'auke da number Abban, kallan su su duka Abbu yayi cikin mamaki, se kuma ya tsaeda idanun sa akan Raj yace

"A'ina ya san ka?" d'an shiru kad'an yayi sannan yace bayan ya d'auke kae

"A makarantar da nake zuwa" jinjina kae Abbu yayi yana mamakin yadda d'an nasa kullum burin sa shine yayi karatu amma shi kam ya rasa yadda zeyi ya cika masa wannan burin nasa, shi kansa sa yana sa kud'i zeyi k'ok'ari wajen cikawa d'an nasa buri ne ta hanyar kae shi wata k'asar ma ba Nigeria ba yayi karatu

"Kuma ka tabbatar da gaske kake?" Abbu yayi k'arfin halin fad'in hakan duk da shi shaida ne akan d'an nasa duk da k'arancin shekaru irin nasa amma da wuya yayi k'arya a cikin lamarin sa

"Ehh Abba Allah kuwa da gaske nake"

"Ikon Allah" Abbu ya fad'a yana jinjina kae, Ummee tace

"Toh zaka je d'in?" kallan ta Abbu yayi kana yace

"Me ze hana, kika sani ko alkhaeri ke kiran mu?"

"Toh Allah yasa, bari na tashi na d'ora mana shinkafar can mu samu mu ci" Ummee ta fad'a tana mik'ewa.


Washe gari da wuri Abbu ya shirya tare shi da Raj, ya kira Abba da er k'aramar wayar sa yayi masa kwatancen gidan nasa sannan suka tafi gidan, daga gidan nasu akwae d'an nisa sosae dan haka suka d'an rage tafiyar a k'asa kafin suka tari adaedaeta ta k'arasa dasu da ragowar chanjin daya ragewa Abbu, a k'ofar gidan suka tsaya Abbu yayi wa Abba flashing a wayar sa saboda kud'in wayar sa daya k'are, ganin kiran nasa ya sanya Abba kawae ya fito dan ya fahimci yazo ne, suka gaesa cikin mutuntawa sannan kowannen su ya gabatar da kansa ga d'an uwan sa, tun a lokacin Abba yaji Abbun ya kwanta masa dan kana ganin sa kaga mutumin kirki gashi ko had'a idanu da Abban ya kasa yi, magana ta k'arshe data wakana a tsakanin su shine Abba yace bayan yaji yadda rayuwar su ke kasancewa, se yayi buga buga yake samu suci abinci, wani lokacin idan be samu komae ba haka zasu wuni da yunwa, shi gashi ba karatu yayi ba dududu iya secondary school ya tsaya, sana'a kuma ta k'i shi, shiyasa ma har lokaci be saka Raj a makaranta ba, saboda komae suka samu cikin su ne, kuma gashi Raj d'in ya tashi da k'aunar makaranta a ransa shi kuma be san yadda zeyi ya saka shi ba, dan idan yace ze saka shin zasu matuk'ar takura ne

"Allah sarki, kar ka damu In Sha Allah kamar an saka Suraj a makaranta ne an gama, maganar sana'a kuma dama inaso na bud'e wani shago ne a cikin satin nan, toh idan zaka iya seka dinga zuwa muna zama tare ina sallamar ka" daga inda Abbu ke zaune kan wata kujera ya zamo kamar ze tsugunna yace muryar sa na rawa

"Nagode sosae Alhaji, Allah ya saka da alkhaeri, ya biya buk'ata, yasa ka gama da duniya lafiya, nagode nagode sosae Alhaji"

"Ya isa haka, babu komae Allah ya taemake mu.." Abba ya fad'a yana rik'o Abban, seya mik'e ya koma ya zauna dae_dae lokacin da Abba ke fad'in

"In Sha Allah zuwa gobe se kazo mu fara shirye shirye.."

"Toh Alhaji babu damuwa" ya fad'a yana cigaba da kwararowa Abban addu'a cikin matuk'ar farin ciki da jin dad'i. Sanda ya koma gida ya fad'awa matar sa zancen tayi matuk'ar farin ciki, haka suka had'u suka dinga yiwa Abba addu'o'i kala kala. Shima Abban daya jewa Umma da maganar taji dad'i sosae ta kuma yi addu'ar Allah ya taemaka. Washe gari kuwa kamar yadda Abban ya fad'awa Abbu se gashi da wurwuri a gidan, daga nan babu 6ata lokaci suka tafi kasuwar zuwa shagon da aka bawa Abba hayar sa, dama ba tun yanzu yake da burin bud'e shago ba amma be bawa abin muhimmaci ba seda wannan abin ya faru dan haka kayan da yake d'an siya yana ajjewa su yayi amfani dasu ya zuba a cikin shagon, sannan yayi amfani da ragowar kud'in da yake dashi ya k'aro wasu kayan ya zuba zuwa lokacin da Allah ze hore ya zuba wasu masu yawa, duk da shagon yafi k'arfin kayan daya zuba a ciki amma haka yake jin sa cikin farin ciki mara misaltuwa, haka suka isa shagon Abba ya bud'e bayan sunyi addu'o'i sosae, tare suka zauna cikin shagon shi da Abbu, Abbu ke kula da harkokin kayan siyarwar yayin da Abba ke kula da harkar kud'i, cikin ikon Allah a ranar kawae sunyi ciniki sosae musamman daya kasance ranar farko ce se Abba yayi discount akan duk wani abu da mutum ze siya, hakan yasa mutane da dama suka dinga zuwa suna siyar kayayyakin, basu suka tashi ba se dab da maghrib sannan suka tashi, Abba ya d'auki kud'i masu d'an dama a cikin cinikin da suka yi ya bawa Abbu, Abbu yayi ta godiya ya tafi gida cikin farin ciki, yau beyi wahala ya nemo kud'in da zasu samu suci abinci ba yana zaune kawae cikin shago babu rana kuma gashi an bashi abinda ko buga bugar yayi baze samu ba, hakan yasa farin cikin nasa ya sake ri6anyuwa.

Tun daga wannan ranar ya kasance kullum Abba da Abbu zasu fita kasuwa da safe basa tashi se dab da maghrib, sosae Abba ya sanya idanu akan Abbu da al'amarin sa, cikin k'ank'anin lokaci Abba ya fahimci Abbu mutum ne me rik'on amana da kirki, babu 6ata lokaci ya shiga gwada shi lokacin da harkar ta bud'e dan yana so ne ya d'an dinga sakar masa abubuwa ba tare da wani tunani ba, sau da dama yasha gwada shi seya same shi da rik'on amana lamarin sa babu ha'inci a ciki, cikin ikon Allah da yaddar Allah sana'ar tasa ta samu kar6uwa a wajen mutane, sosae ake zuwa a siyi kayan da yake siyarwa saboda haka a hankali ya d'an fara sakarwa da Abba wasu abubuwa da dama saboda shima ya d'an samu sassauci. A 6angare guda kuwa ya sanya Raj a makarantar su Ayrah, an saka shi a Junior class saboda yanayin shekarun sa, ba laefi sun d'an fara sabo shi da Yah Sadeeq amma ba wani sosae ba, yayin da a tsakanin sa da Ayrah kuwa kullum wata sabuwar shak'uwa ke k'ara ninkuwa a tare dasu kamar wad'anda suka yi shekara da shekaru a tare, kamar kuma wad'anda suka fito ciki d'aya haka suke al'amuran su, kowanne najin d'an uwan sa a cikin ransa, a tsakanin su babu wanda ke son ganin d'aya yana cikin 6acin rae, sau da dama Umma kanyi mamaki na shak'uwar ta su amma idan ta tuna komae daga Allah ne seta dena mamakin, daga k'arshe ma gaba d'aya Raj ya dawo gidan su Ayrah da zama, idan Abba ya d'auko su daga makaranta seya wuce dasu dukkan su har Raj d'in gida, su tafi Islamiyya sannan idan suka dawo suci abinci kana Raj ya tafi gida, wata ran da k'yar yake tafiya d'in idan Ayrah ta saka rigimar seta bishi, da k'yar take hak'ura idan Umman dashi kansa Raj d'in suka rarrashe ta kana take hak'ura amma fa ta dinga nunk'ufurci kenan kamar wata babba, tayi ta bin kujera tana kwanciya kamar zata yi kuka, idan kuwa da rana ne ko a makaranta in dae basa cikin aji toh zaka same su ne kullum tare da juna, wata iriyar shak'uwa suka yi mara misaltuwa ko iyayen Raj d'in ma abin har mamaki yake basu, sunan Raj kuwa seda Ayrah ta lak'abawa kowa, daga zarar kace masa Suraj za tace ba Suraj ba Raj, kuma in zaka kwana kana fad'ar Suraj itama zata kwana tana gyara maka, dan haka yanzu en gidan su ma kwata kwata Raj d'in suke ce masa, Iyayen sa ne dae suke k'ok'arin ce masa Raj d'in ko dan Ayrahn musamman idan a gaban tane, shi kansa yanzun yafi jin dad'in Raj d'in kuma babban dalili daya kasance Ayrah ce ta saka masa sunan.



A cikin shekarar da taemakon Allah komae ya cigaba da bud'ewa Abba, seya kasance ma yanzun ya zuba atamfofi ne kala kala kuma masu yawa, sosae Abbu ke taemaka masa ta hanyoyi da dama, dan yanzun ya gama sakar masa komae, ko menene in dae shi da kansa ze iya yi toh fa ze iya d'ora Abbu akae saboda yadda yayi na'am dashi, haka suka cigaba da tafiyar da shagon su 2, sosae abubuwa da dama na Abban suka chanja ciki kuwa hadda cimar gidan sa da suturun da shi kansa da iyalan sa kan saka da kuma sauran abubuwa makaman tan wannan, shi kansa Abbu ba'a barshi a baya ba dan kuwa yanzun rayuwa suke cikin kwanciyar hankali babu yunwa babu komae, dan a lokacin ma seda ya nemi Abba ya sakar masa harkar makarantar Raj amma Abba yace a'ah tunda ya fara shi ze k'arasa In Sha Allah, beyi musu ba se k'ara godiya da yayi, godiyar da kusan kullum se yayi ta baya gajiya da ita.

_*MAFARI*_


... Da sallama Abba ya shigo gidan kamar koda yaushe hannun sa d'auke da ledar daya saba shigo da ita kusan kullum wanda hakan ma ya riga ya zame masa jiki, in dae ze dawo gidan toh In Sha Allah ze siyo wani abun ya tahowa da iyalin nasa shi, da gudu ta sauko daga kan kujerar ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in

"Abba Sannu da zuwa"

"Yawwah an baby.."

"Abba meka siyo min?" ta fad'a tana murmurshi, shima murmurshin yayi sannan yace

"Kar6i maza ki kaewa Umman ku, ina take?" seda ta sanya hannu ta kar6a sannan tace

"Tana kitchen" daga haka tayi hanyar kitchen d'in tana kiran sunan Umma, Raj dake zaune kan kujera ya sakko a hankali ya furta

"Abba sannu da zuwa"

"Yawwah sannun kadae" Abban ya fad'a yana wucewa d'akin sa... Seda ya samu yaci abinci a cikin parlourn sannan Umma ta gabatar masa da ruwa ya sha kana yace

"Dama akwae maganar dana ke so muyi" gyara zama Umma tayi kana ta kalli Ayrah dake shirin fita daga d'akin saboda Raj daya shigo yanzun kuma ya fita

"Ina kuma zaki je?" Umman ta fad'a, turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace

"Umma Raj zan bi"

"Ina ze je?"

"Wajen Yah Sadeeq.." ta fad'a tana kallan Umman, Abba ne yanzu kuma yace

"Toh shikenan, amma banda shiga ball ta maza ce" jinjina kae tayi tana murmurshi ta fice daga d'akin, Umma ta juyo da kanta wajen Abba tace

"Abban su ina jin ka" seda Abban ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Wato Alhaji Mato ne yazo min da wata shawara..toh yanzu dae so nake nayi shawarar dake inji me kikace, wato ba wani abu bane ya bani shawara ne wadda In Sha Allah akwae cigaba a cikin ta, cemin yayi meze hana tunda Allah yasa min albarka a wannan harkar na koma cikin kano ko da zama ko da sana'a, kin san kano cibiyar kasuwanci ce.." d'an shiru Umma tayi tana nazarin maganar Abban se kuma can tace

"Hakan ma yayi Abban su, me son cigaban ka ae me k'aunar ka ne, ni ina ganin kawae ka amince da shawarar tasa.."

"Toh shikenan amma batun zama fa? Acan d'in zamu zauna ko kuma dae in fara maganar ni kad'ae na tafi can sena dinga zuwa?" Abba ya fad'a yana Kallan Umma, murmurshi Umma tayi kana tace

"Abban su ni bana tunanin wannan mafita ce, ni a gani na gwara ka tsayar da hankalin ka kan abu guda d'aya, ba kae kana can mu muna nan ba hankalin ka ze rabu gida biyu, ni a gani na kawae muma mu tafi tare da kae.."

"Shikenan toh Allah ya taemake mu" Abba ya fad'a yana murmurshi. Be hak'ura haka ba seda ya nemi Abbu yayi shawara dashi, cikin ikon Allah kuma shima ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari, dan haka Abba ya sake jin nutsuwa a lamarin, saboda haka babu 6ata lokaci ya fara shirye shiryen tafiya kanon, ita kanta Umma ma ba'a barta a baya ba, shiri take yi na tafiyar ta su, dan haka babu 6ata lokaci Abban ya kusa gama komae, da yake Alhaji Mato yafi zama a kano ya saka shi ya nemar masa gida a cikin garin na Kano d'an madaedaeci haka me kyau, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen tambayar Abbu yadda za'ayi, ze bishi can garin kanon ne ko kuwa anan ze zauna se Abban ya dinga yi masa aeke, girgiza kae yayi a lokacin da Abban ke masa maganar yace

"Ayyah Abban Sadeeq, ya za'ayi in zauna anan kae kana can wani gari? In Sha Allah zan bika can d'in idan yaso sena dinga dawowa nan d'in wajen iyali na" Take Abba yayi na'am da maganar Abbun, dan haka yace

"Toh shikenan, Allah ya taemake mu"

"Ameen Ameen" Abbu ya fad'a..


Rana ku suka cigaba da tafiya babu tsayawa, har zuwa sanda Abba ya k'arasa abinda be gama ba, yanzu haka ya siyar da kayayyakin da yake siyarwa anan d'in ya had'e kud'ad'en nasa waje guda, be sanya su a banki ba saboda matsalar da account d'in sa ya samu, hakan ne yasa ya had'a su cikin wata jaka daban wadda yake ajje muhimman takardun sa masu matuk'ar amfani, duk wani abu da yasan yana da amfani a wajen sa ya had'e su duka cikin wannan jakar sannan ya had'a ragowar kayan sa cikin wata, haka zalika Umma ma tayi sallama da mak'ota en uwa da abokan arzik'i, ranar da zasu koma zuwa garin kano tazo...

Tun safe Umma ta gama shiryawa tsaff cikin atamfa riga da zani da hijab dogo, ta shirya Ayrah cikin doguwar rigar en kanti da baby hijab suka fito parlour, tun d'azu Ayrahn ke ta 6ata rae da alama k'iris take jira ta fashe da kuka dan haka Umman na kallan ta tak'i kula ta ballantana ma ta sakar mata kukan shagwa6ar ta ta, tana zaune kan kujerar ta kwantar da kanta akan wata leda dake d'auke da kaya, Yah Sadeeq ne ya shigo cikin d'akin idanun sa akan ta ya fara sauka, shima yana ganin ta yasan yau da rigima ta tashi

"Auta meya faru?" ya fad'a yana kallan ta, manyan idanun ta ta d'aga ta kalle shi amma ba tace komae ba, Umma dake kallan su tace k'asa k'asa

"Ka rabu da ita don Allah, kar kasa ta mana kuka kuma" yaji abinda Umman ta fad'a dan haka kawae seya koma kusa da Ayrahn ya zauna, seta maeda kanta ta kwantar akan cinyar sa tana cigaba da kallan k'ofa.. Basufi mintuna 2 da zama ba sega sallama daga k'ofar d'akin, Umma da Yah Sadeeq suka amsa sallamar, yana sanye cikin riga da wando na wani yadi me kyau kasancewar sa me tsafta ya sanya kayan nasa a goge suke tsaff tsaff yayi matuk'ar kyau, da gudu ta mik'e ta k'arasa bakin k'ofar da suke k'ok'arin shigowa ta rungume shi tana sakin dariya kamar ba itace yanzu zaune kamar zata yi kuka ba, shima dariyar yayi yana fad'in

"Oyoyo Ayrah" ta sake yin dariya kana tace

"Ina ta jiran ka, shine ba kazo ba" dukka en d'akin binsu suke da kallo, ya rik'o mata hannu zuwa cikin d'akin yace

"Gani fa nazo"

"Zo kaji" ta fad'a tana janyo shi k'asa, seya d'an yo k'asan, ta sake jan shi ya tsuguna a k'asan sannan ta kae bakin ta kunnen sa tace k'asa k'asa

"Jiya wata tace suna da mangoro a gidan su, zaka ciro min?" bud'e idanu yayi yana sake kallan en d'akin sannan ya mik'e ya sake kama hannun ta zuwa cikin d'akin, ita kuma ta tura d'an k'aramin bakin ta gaba, seda suka k'arasa ya zauna sannan ya gaeda Umma da suke gaesawa da Ummee sannan ya kalli Ayrah dake zaune dab dashi ta rik'o hannun sa kamar wanda ze gudu yace

"Toh zan raka ki yi murmurshi" se a lokacin ta saki fuskar ta tana jin dad'i har cikin ranta. Basu dad'e da zama ba Yah Sadeeq daya fita d'azun yazo yace Umma su fito, har lokacin hannun ta na cikin na Raj sanda suka fito d'in, Ummee ta kalli Abba tace

"Toh Alhaji mun gode Allah ya saka da alkhaeri, ya tsare ya bada sa'a"

"Ameen Ameen" Abba ya fad'a yana shirin d'aukar jakar da Yah Sadeeq ya fito da ita a hannun sa, Abbu yayi murmurshi yana kallan Abba yace

"Haba haba Alhaji ina wajen sannan zaka d'auki kaya?" shima Abban murmurshi yayi sannan yace

"A'ah toh ka bar Sadeeq ya d'auka.."

"Babu komae muje kawae" ya fad'a yana rik'e wata akwati kuma a hannun sa, Abba be sake cewa komae ba se kallan Ayrah da yayi wadda ta

Please Login or Register in order to submit comment