Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fad'a yana d'aga masa hannu idanun sa akan sa cike da zallahr 6acin rae

"Aou aou toh hakane abin, wato har yanzu kae ka kasa gane Annabi ya faku koh?, toh cigaba da zama da ita, ina ga ba zaka fahimci abinda nake fad'a maka ba se ranar da kayan sakawa ma ya gagare ka sakawa.." Abba ya runtse idanun sa zafin zuciyar da yanzun ya zame masa jiki se k'aruwa yake yi, a nutse ya mik'e tsaye sannan cikin kaurin murya ya furta

"Kana buk'atar kud'in ka ne ko kuwa?"

"A'ah se kuma in k'i buk'ata, ina jiran kud'i na a cikin satin nan kawae" Alhaji Mato ya fad'a shima yana mik'ewa ya bar wajen, da kallo Abba ya bishi yana mamakin wannan banzan hali irin na Alhaji Maton, shikenan kuma a matsayin ka na bawa musulmi Allah baze jarabce ka ba? Da wannan tunanin ya koma gida yana sak'a da warwarar yadda ze biya Alhaji Maton kud'in sa. Sanda ya koma gidan bayan yaci abinci Umma ta tambaye shi yadda suka yi da Alhaji Maton, duk se yaji tausayin ta ya kama shi yadda wani ke ik'rarin duk dalilin tane abubuwa ke faruwa dashi, abinda shi kuma baze ta6a yadda ba kenan, dan kuwa shi musulmi ne daya yadda da k'addara me kyau da kuma mara kyau, gyara zama yayi yana kallan ta

"Kada ki damu, zan san yadda zanyi in biya shi kud'in sa.." cike da mamaki Umma tace

"Aou yace se an biya shi?"

"K'warae kuwa" Abba ya fad'a

"Ikon Allah.." Umma ta fad'a tana girgiza kae... Abba beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'akko motar sa ya siyar da ita ba, saboda matsalolin da take dasu yasa ba tayi wani daraja ba gata kuma dama ba babbar mota bace, seya d'auki kud'in Alhaji Mato ya bashi sannan ya rik'e ragowar a hannun sa dan amfanin yau da gobe, abinda ya tsaya masa a rae yanzun kawae shine yadda zeyi ya samu sana'a ko dan ya sanya 'ya'yan nasa a makaranta, abinda ya k'ara masa k'aemi ma akan saka su a makarantar shine.. Rannan suna zaune a cikin parlourn dukan su suna kallan Al jazeera inda Abba ke kallan labarae, Ayrah na zaune gefen Abban itama tana kallan T.Vn kamar me fuskantar abinda ake nunawa a ciki, daga k'arshe a cikin labaran aka nuno wasu d'alibae da Uniform d'in su, se kuwa tayi zumbur ta tashi zaune tana kallan Abba tace

"Abba mun dena zuwa makaranta?" kallan ta Abba yayi cikin mamakin jin furucin ta, se yayi murmushi sannan yace yana shafa doguwar sumar kanta dake a bud'e

"A'ah za'a sanya ku mana"

"Abba yaushe?" ta sake tambayar sa, seya d'an yi shiru kana yace

"Nan bada dad'ewa ba Uhmm?"

"Hadda Raj koh?" ta fad'a tana murmurshi, zancen kenan dan kullum idan ba tayi maganar Raj ba toh ba Ayrahn bace

"Ehh" Abba ya fad'a yana maeda duban sa kan T.V.



.... Sosae Umma ta takurawa Abba akan zuwa asibiti saboda rashin baccin da yake samu, shima kansa rashin baccin na damun sa dan haka a wannan karon da tazo masa da k'orafi be musa mata ba ya shirya ya tafi asibitin, gwajin hawan jini aka fara masa, kuma tashin farko su kaga yanda jinin sa ya hau, sosae suka bashi shawarwari akan hakan da kuma magunguna, hakan ba k'aramin kuma tayar masa da hankali yayi ba, amma gudun kada hankalin Umma ya tashi yasa be sanar da ita ba, kawae yace mata an gwada shi amma basu fad'a masa aenahin abinda ke damun sa ba se result d'in ya fito, haka ta yadda da abinda ya fad'a mata d'in, yayin da shi kuma ya cigaba da shan magungunan sa ba tare daya bari Umman ta sani ba. A lokacin ne ya cigaba da fama da rashin bacci da kuma tunanin daya zame masa jiki, se kuma bugun zuciya da shima baya rabo dashi, haka wataran ze kwana a zaune, se dae da yake baya bari lokacin ya tafi masa a banza se hakan yake sakawa baya wani damuwa sosae, dan kuwa k'arin lokacin karatun Qur'an ya samu, idan dae ya fahimci bacci baze zo masa ba seya fito tsakar gidan nasu ya shimfid'a dadduma yayi ta karatu har zuwa asuba, ranar da kuma ya samu baccin se yayi baccin sosae, sau da dama Umma kan farka ta same shi yana karatu, dalilin kenan daya sanya bata damu da rashin baccin nasa ba, saboda ta riga data saba da ganin sa cikin dare yana tashi karatu, se dae tasan ya k'ara lokacin karatun, amma duk da haka bata kawo rashin samun bacci ne ya sanya shi k'ara lokacin karatun ba, tafi ta'allak'a hakan da yanayin rayuwa kawae.. Sanda Umman ta gano ciwon dake tattare da Abban ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, dan har kuka seda tayi, Abba ya fesar da iska daga bakin sa yana kallan ta yace

"Kiyi hak'uri kiyi shiru, kada kisa nima nawa hankalin ya tashi mana"

"Amma Abban su meyasa ka 6oye min?"

"Toh yanzu ba gashi kin sani ba?" ya fad'a yana kallan ta, seta share hawayen fuskar ta sannan tace

"Duk da kullum cikin yi maka addu'a nake, amma ko ba komae zan dage da maka addu'a akan ciwon koh?"

"Toh shikenan nayi laefi amin afuwa" ya fad'a yana kallan ta da tattausan murmushi akan fuskar sa, itama murmurshin tayi duk da yadda can k'asan zuciyar ta ke cunkushe da tausayin Abban.



.. Sosae Abba ya dage wajen neman sana'ar da zata rufa musu asiri, se dae har zuwa lokacin be samu ba, gaba d'aya yanzu burin sa be wuce na yadda ze samu ya sanya Yah Sadeeq da Ayrah a makaranta ba dan haka idan ya tashi tun safe ya fita baya dawowa se dare amma har zuwa lokacin be samu ba.



.. "Abba wae ana sallama da kae" Yah Sadeeq ya fad'a yana Kallan Abba dake zaune

"Inji wa?" Abban ya fad'a yana kallan sa, girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace

"Abba bansan shi ba.."

"Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana mik'ewa, ya kalli Umma da itama kallan sa take yace

"Bari naje.."

"A dawo lafiya" ta fad'a sanda yake barin tsakar gidan zuwa waje.. Murmushi yayi sanda yaga mak'ocin sane wanda suke yawan had'uwa a masallaci, seya mik'a masa hannu suka gaesa sannan mutumin yace

"Wato dama magana ce akan wani aeki, yasa nace bari na maka magana idan zaka iya toh seka fara ko ranar litinin ne.." sosae annurin fuskar Abba ya k'aru yace

"Ina jin ka wane irin aeki ne?"

"Aekin Company ne haka amma ba wani aekin wahala bane sosae, idan ka amince zaka iya se muje ka gani" sosae Abba yaji dad'in wannan abu dan haka cikin farin ciki yace

"Toh nagode nagode sosae, Allah ya saka da alkhaeri.."

"Ameen Ameen" mutumin ya fad'a. Abba na komawa gida ya sanar da Umma abin alkhaerin daya same su, sosae Umman ma taji dad'i dan haka babu 6ata lokaci Abba ya gabatar da isthikara, kafin ya fara zuwa aekin kuwa sosae yaji ya kwanta masa, har ya k'agu ma ya fara aekin.. Ranar litinin kuwa Abba ya fara aekin, kuma a ranar aka fad'a masa albashin sa, duk da kud'in basu taka kara sun karya ba amma shi a wajen sa da iyalin sa sosae suka ji dad'i, suka kuma godewa Allah.. Babu 6ata lokaci k'arshen wata nayi Abba ya sanya su Ayrah a makarantar gwamnati d'an nesa da gidan su, yayi amfani da kud'in ya siya musu duk wasu kaya na buk'ata da yasan zasu buk'ace su, farin ciki a wajen Ayrah kamar zata yi mene, dan sosae tayi missing School, yadda suka samu background me kyau ya sanya yanzun abin bezo musu da wahala ba, duk da yanayi na chanji da yake tsakanin government school da private school, dan haka suka cigaba da karatun su.. Kud'in Abban gaba d'aya yake k'arewa a wajen hidimar makaranta, kud'in mota da kuma kud'in cefane dan haka akwae wani mutum da yake siyar da kayan abinci a wajen sa yake kar6ar bashin abinci duk k'arshen wata, wani watan kuma seya bashi kud'in sa ya sake kar6ar wasu, haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa. Tun daga wancan lokacin Abba be sake bi takan Alhaji Mato ba dan ya riga yasan babu abinda ze saka ya sake bashi wani abun ko kuma jari, dan haka kwata kwata ma bebi ta kansa ba, ya fita harkar sa kamar yadda shima ya fita tasa. A 6angaren Ayrah kuwa zuwa lokacin tun tana zancen Raj har ta gaji ta dena yi, dan tun iyayen na biye mata har suka zo suka dena kula ta idan tayi zancen nasa, basu san me zasu ce mata akan Raj d'in ba dan kuwa a lokacin shekarun ta sunyi kad'an ta fahimci irin abinda Abbun yayi wa Abba.


.. Kwanaki nata tafiya, haka watanni ma suna ta shud'ewa suka had'u suka bada shekaru, izuwa lokacin sosae hidimomi suka taru suka k'ara yiwa Abba yawa, ga kuma kullum yadda tsadar abubuwa ke k'aruwa amma kuma albashin sa kamar na da ne, ba'a k'ara musu ba ballantana su samu sauk'in yadda abubuwa ke ta tashi, k'arshen wata ne a lokacin sanda aka musu albashi, dama kuma kafin zuwan albashin ya riga ya kashe su da bashi, kae tsaye seda ya fara zuwa kasuwa ya siyowa su Ayrah sabbin Uniform, a yadda yaso ma har da jaka da takalma ze siya musu saboda yadda nasun suka tsufa amma kuma yasan idan yayi hakan zasu takura ne matuk'a, dan haka kawae daga Uniform d'in ya baro kasuwar, daga nan ya wuce ya biya wad'anda ke binsa bashi wanda bashi da yawa, ya zama na saura kud'in daya san na cefane ne kawae dana kud'in motar su Ayrahn. Wajen da yaje na k'arshe shine wajen wanda yake kar6ar kayan abinci a wajen sa, ya k'arasa da sallama yana neman waje ya zauna, amsa masa sallamar mutumin yayi sannan Abba ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara, seya sanya hannu cikin aljihu ya d'akko kud'in daya ware wanda ze bashi, ya mik'a masa yace

"Gashi.." kar6a mutumin yayi yana karkad'e hannun sa da fulawa ta 6ata, ya k'irga sannan ya kalli Abba

"Wani abun za'a baka da kud'in ne?" girgiza kae Abba yayi cikin sarewa da yadda yaga mutumin kamar wanda ze bashi kayan kyauta yace

"A'ah kayi hak'uri don Allah, kasan lamarin ne se a hankali, ka rik'e wannan, a bani kayan kamar yadda aka saba bani idan yaso se a d'ora akan wad'ancan" tun kafin ya kae k'arshen maganar mutumin ya fara girgiza kae, yana gamawa yace

"A'ah wallahi bazan iya ba, kae ma kayi hak'uri, duk lokacin daka gama biyan bashin se kazo mu san yadda za'ayi, shine kawae alfarmar da zan iya maka" Abba ya runtse idanun sa yana jin gaba d'aya jikin sa babu dad'i, dama daga yadda yaga yanayin mutumin yasan ba lallae ya yadda da abinda yazo masa dashi d'in ba, dan haka ya mik'e yace a hankali

"Toh nagode, zan kawo maka cikon kud'in In Allah ya yadda.." Abba ya fad'a yana yin gaba, mutumin ya bishi da kallo yace bayan yaja tsaki

"Ayi mutum kullum cikin neman alfarma yake, na tsani irin haka wallahi" ya fad'a yana d'aura wani mae a cikin leda..


... Da sallama Abba ya shiga gidan, Ayrah ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in

"Abba sannu da zuwa"

"Yawwah sannu Auta" ya fad'a yana sakar mata ledar hannun sa daya shigo da ita, tana shirin juyawa yace

"Ina d'an kwalin kuma?"

"Abba tsifa Umma ke min, yanzun na cire shi" ta fad'a tana d'an murmushi gami da shafa kanta

"Toh ayi maza a gama tsifar a rufe kan" Abba ya fad'a sanda yake kallan Umma dake masa sannu da zuwa, Ayrah ta k'araso ta ajje ledar hannun ta, sannan ta tafi da d'ayar kitchen dan ko Abban be fad'a ba tasan tsarabar tace, er madaedaeciyar roba ta d'akko ta zuba mangoron nata a ciki sannan taje ta wanke shi kana ta dawo cikin parlourn dae_dae lokacin da Abba ke fad'in

"Lafiya kuwa Sadeeq ke bacci da yamman nan?"

"Wallahi kuwa Abban su kamar zazza6i ne a jikin sa d'azun"

"Toh Subhanallahi Allah ya sawwak'e... Ga rama can ki kwad'a mana ita muci yanzun, kafin dare kuma mu san yadda za'ayi.." babu musu Umma ta mik'e ta fita daga d'akin zuwa kitchen ta gyara ramar tass ta kwad'a ta sannan ta kawowa Abba tasa kana ta zubo musu ita da Ayrah har ma da Yah Sadeeq, kallan Ayrah dake ta shan mangoron ta hankali kwance tayi ta girgiza kae tana murmushi tace

"Tashi Sadeeq ya tashi haka nan yaci abinci.." da "toh" ta amsa sannan ta mik'e ta fita bayan ta wanke hannun ta ta dawo cikin d'akin, hannun ta ta saka a hankali tace

"Yah Sadeeq, Yah Sadeeq.." a hankali ya shiga bud'e idanun sa da suka masa nauyi saboda wani azababben ciwon kae daya rik'e masa kae, kallan sa su duka suka yi sanda yake k'ok'arin tashi zaune kan kujerar, Yah Sadeeq ba gwanin raki bane dan haka kana ganin sa kasan da gaske rashin lafiya ce ta kama shi

"Yah Sadeeq baka da lafiya?" Ayrah ta fad'a tana kallan sa da idanun ta da suka yi rau rau, seya jinjina kae kawae yana lumshe idanun sa

"Kayi wanka se kazo kaci abinci ko zaka ji d'adin jikin ka" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq, seya mik'e a hankali ya fita daga d'akin hannun sa dafe da k'irjin sa ya wuce toilet d'in yayi wanka sannan ya fito.. Tare suka ci ramar cikin kwano d'aya, yana ci Umma na lura da yadda yake ta 6ata rae alamar kawae ci yake babu taste a bakin sa, wani iri da yaji a k'irjin sa ya sanya shi d'aukar ruwan da Ayrah ta kawo yanzu ta ajiye ya kafa bakin sa ya fara sha, se dae kafin ya ida shan ruwan wani irin amae ya taso masa, dan haka babu 6ata lokaci kuma cikin hanzari ya jefar da cup d'in yayi waje, aekuwa ya dinga kwara aman kamar ransa ze fita, dukkan su biyo shi suka yi wajen cike da tausayawa babu ma Ayrah data fara matse k'walla saboda tausayin d'an uwan nata

"Sannu" suka dinga jefa masa sanda Umma ta taemaka masa ya tashi ta k'arasa dashi zuwa parlourn nata, Abba ya kalle ta yace

"Ina ga ki shirya kawae mu wuce asibiti.." Yah Sadeeq dafe da k'irjin sa yace yana d'an girgiza kansa dan shi kad'ae yasan yadda yake ji a cikin jikin sa

"Abba bacci nake ji, a bari na tashi tukunna se muje don Allah"

"Abba don Allah a barshi yayi bacci" Ayrah dake rik'e da hannun Yah Sadeeq ta fad'a, jinjina kae Abba yayi kana yace

"Shikenan, kayi baccin.." babu musu Yah Sadeeq ya koma ya kwanta yana lumshe idanun sa k'irjin sa na bugawa da k'arfin gaske, cikin en mintuna kad'an wani nannauyan bacci yayi awon gaba dashi, duk da kuma baccin daya d'auke shi hakan be sanya ya d'auke hannun sa dake kan k'irjin sa ba, ita kuma Ayrah na zaune gefen sa har lokacin hannun sa cikin nata tana jin tausayin d'an uwan nata rabin jikin ta.........


Mhiz Innocent.... ✍️




https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 009_010



___Sosae jikin Yah Sadeeq yayi tsanani a daren ta yadda dole seda suka mik'a shi asibiti, da kud'ad'en da suka ragewa Abba a hannu dasu yayi amfani wajen bada kud'in gwaje gwaje da sauran abubuwan da ba za'a rasa ba, tashin farko aka tabbatar da Yah Sadeeq d'in na d'auke da chronic ulcer ne, ga kuma matsananincin zazza6in daya sake rufe shi a ranar, dan haka asibitin suka rik'e shi ya kwana acan d'in, magunguna sosae aka had'a masa wad'anda suka janyo k'arewar kud'in daya rage a hannun Abba tass, sosae Yah Sadeeq d'in yaji jiki ya rame dama ba wani jiki gare shi ba, kamar wanda ya shekara a kwance, seda yayi sati 1 sannan aka sallame shi, zuwa lokacin kam tuni Abba ya fara tunanin mafitar daze samar musu wadda zasu dinga samun abincin da zasu dinga ci da sauran kayan amfani na yau da kullum. Sanda suka dawo gidan ma seya zama na basu da komae na dangane da abinci, dan haka Abba beyi k'asa a gwuiwa ba ya nemi bashi a wajen ogan su na company kuma cikin ikon Allah ya bashi, da wannan kud'in suka yi amfani har zuwa k'arshen wata, sedae fa a cikin watan dama Ayrah ce kad'ae ke zuwa makaranta saboda Yah Sadeeq har lokacin be gama warkewa ba, itama kuma babu kud'in da za'a dinga bata na mota dan haka Abba da kansa ke raka Ayrahn har makaranta a k'afa sannan ya wuce company shi kuma. A cikin wannan d'an tsukun ne Ayrah tayi k'awa Zaenab a makarantar bokon nasu, wadda take cikin unguwar su d'an nesa kad'an da gidan su, sosae suka k'ulla k'awance wanda har hakan ya janyo Abba yasan mahaefin ta ya zamana suna gaesawa sosae kamar abokae, sanda Baban Zaenab d'in ya fahimci yadda Ayrahn ke zuwa makaranta a k'afa se be cewa Abba komae ba washe gari kawae yazo k'ofar gidan su Ayrahn ya d'auke ta da yake yana da babur wanda a shi yake d'aukar Zaenab ya kae ta makaranta, sosae Abba yaji dad'in hakan ya yiwa Baban Zaenab d'in godiya. Tun daga ranar ya kasance kullum Baban Zaenab d'in ke zuwa ya d'auki Ayrah su wuce makaranta tare.. Sanda Yah Sadeeq ya warke bayan doguwar rashin lafiyar da yayi Abba da kansa yaje wajen Baban Zaenab d'in ya sake masa godiya sannan ya fad'a masa zancen warkewar Yah Sadeeq d'in kuma shine ze cigaba da tafiya da Ayrah makaranta, dan zuwa lokacin abubuwa sun d'an yiwa Abba kyau ba kamar da ba, da farko Baban Zaenab d'in ya nuna k'in amincewar sa akan hakan, ya nuna ze cigaba da kae Ayrah tare da Zaenab makaranta, se da Abba ya ganar dashi sosae kafin ya hak'ura... Haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa wataran su samu suci abinci wataran kuma se dae suyi hak'uri, ko kuma su samu suci abincin sau 2 a rana, harkokin yau da kullum kuma wasu se dae ayi hak'uri, idan kuma abu ya zama dole toh Abba kanyi iya k'ok'arin sa wajen samar da abun...



_BAYAN WASU SHEKARU_

__A cikin shekarun da suka shud'e sosae abubuwa suka cigaba da faruwa, ta 6angaren su Ayrah dae babu wani chanji dan kuwa har zuwa lokacin Abba aekin Companyn nan yake yi, yayin da Yah Sadeeq ya gama Secondary School har da shekara 3 da wani abun ma amma saboda yanayin rayuwa yasa har lokacin be cigaba ba, se dae wani lokacin ya kan bi Abba Company ya d'an taemaka masa da wasu auyukan..


.. Shigowar ta gidan kenan da sallama sanye cikin Uniform riga da wando blue da kuma hijab me d'an girma fari, k'afar ta tana saye cikin wani takalmi sau ciki bak'i me d'an madaedaecin kyau, matashiyar budurwa er kimanin shekaru 15, fara k'all da ita, zuwa lokacin data fara zama budurwa sosae kyawun ta ya k'ara fitowa sosae, haka zalika hasken fatar ta ya k'aru, Umma dake zaune cikin d'aki tana cigaba da sak'ar wata hula da yanzun take yi tana d'an samun kud'i, ta amsa sallamar Ayrahn, k'arasawa Ayrah tayi zuwa cikin d'akin sannan ta zube akan ledar tsakar d'akin hannun ta kan k'afar ta tana k'ok'arin cire takalmin k'afar ta tace bayan ta d'an tura k'aramin bakin ta gaba

"Washh Allah na" ta fad'a tana cigaba da cire takalmin ta, Umma da take kallan ta ta girgiza kae tace

"Sannu malalaciya" dae_dae lokacin data gama cire takalmin ta juyo tana kallan Umma seta sake maraeraece fuska tana fad'in

"Allah kuwa Umma na gaji da gaske" ta fad'a tana d'ora kanta akan cinyar Umman, ajjiye sak'ar hannun ta Umma tayi sannan tace bayan ta d'ora hannun ta akan Ayrah

"Qualifying d'in ta fito?" seta tashi da sauri wani murmushi na k'wacewa akan kyakykyawar fuskar ta, ta saka hannu ta janyo jakar ta data ajje a gefe sannan ta bud'e ta d'akko wata farar takadda ta mik'awa Umma har lokacin murmurshi be bar kan fuskar ta ba

"Umma naci.." ta fad'a dae_dae lokacin da Umman ta kar6i takaddar, ta karanta sannan ta d'ago tana kallan Ayrahn itama da murmushi kan fuskar ta tana jin wani irin dad'i mara misaltuwa

"Alhamdulillah, Alhamdulillah" shine abinda Umman ke fad'a har cikin ranta tana jin dad'i

"Umma nayi k'ok'ari koh? Abba ya dawo yaji abin farin ciki, dama Yah Sadeeq yace ze siya min waya idan naci" murmushi Umma tayi tana kallan Ayrahn sannan tace

"Sosae ma kuwa Auta, kinyi k'ok'ari, Allah ya k'ara miki baseerah"

"Ameen Umma na" ta fad'a tana maeda kan ta ta d'ora akan cinyar Umman

"Toh a tashi ayi Sallah koh?" seta jinjina kae tana tashi zaune ta cire Hijab d'in jikin ta sannan ta zame k'aramin d'an kwalin da yake kanta wanda hakan ya bawa dogon bak'in kwantaccen gashin ta damar zubowa akan kafad'ar ta kasancewar ko Ribbon bata saka ta d'aure shi ba, duk da bata saka komae a kan ta wanda ya danganci relaxer hakan be hana gashin ta kwanciya kamar ta saka masa wani abun ba

"Je kiyi wanka kizo na miki kitso.." Umma ta fad'a tana kallan ta, seta 6ata fuska kamar me shirin yin kuka, k'uruciyar ta na bayyana sosae tace

"Don Allah Umma bana so.." ta fad'a tana maeda d'an kwalin kanta ta d'aure, seya kasance gashin nata ya d'an lek'o ta baya, mik'ewa tayi hannun ta d'auke da takalmin ta data cire dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ya shigo cikin gidan da sallama, dukkan su suka amsa masa sallamar sanda ya k'araso cikin tsakar gidan, matashi ne kyakykyawa shima kamar er uwar sa, sedae bashi da wani jiki dan zamu iya kiran sa da siriri, da sauri Ayrah ta koma cikin d'akin ta d'akko takaddar nan sannan ta kalli Yah Sadeeq daya ida shigowa cikin d'akin tace tun kafin ya kae ga zama

"Yah Sadeeq albishirin ka?" seya kalle ta yana murmushi kana yace

"Goro fari tass" seta maedo da hannun ta data 6oye a bayan ta tace

"Naci qualifying" ta fad'a tana mik'a masa takaddar, cikin farin ciki ya sanya hannun sa ya kar6a seda ya karanta sannan ya maeda duban sa kanta har lokacin yana murmushi yace

"Dat's my lily, kinyi k'ok'ari sosae" ya fad'a yana dan jan kumatun ta, murmushi tayi kana tace

"Yah Sadeeq alk'awarin mu.."

"Ohh kinga har na manta kuwa" ya fad'a yana fiddo ido, seta d'an tura bakin ta kad'an sannan tace

"Kae Yah Sadeeq.." dariya yayi yana d'an satar kallan Umma kana ya maeda duban sa kanta yace

"Kada ki damu, ina d'aukar albashi zan siya miki Uhmm?" (shima yanzu ya samu aeki a wani company inda yake zuwa yayi aekin a biya shi k'arshen wata) er k'ara kad'an ta saki tana rungume Yah Sadeeq d'in cikin farin ciki tace

"Nagode sosae Yah Sadeeq.." Umma dake gefen su tace tana kallan su

"Gwara ma ka chanja wani abun ba dae waya ba, du du du ma yaushe ta dena shashanci balle kuma a d'auki waya a bata?" d'agowa tayi tana kallan Umma idanun ta sun cika taff da hawaye tace

"Allah kuwa Umma na girma fa"

"Toh in gani a k'asa" Umman ta fad'a tana mik'ewa ta fice daga d'akin, seta sanya hannu tana goge hawayen idanun ta, Yah Sadeeq yayi murmushi yana kallan ta yace

"Kiyi shiru zan taushi Umma ta bari na siya miki er k'aramar waya ki dinga yin game, amma fa se kin min alk'awari.."

"Ehh wallahi na yadda nayi" ta fad'a tana d'aga yatsan ta d'aya, dariya ta bashi dan haka seda yayi dariyar kana yace

"Ohk toh yanzu yaushe zaku fara Neco?"

"Aou na manta" ta fad'a tana dafe bakin ta kana ta ta6e bakin se kuma tace tana kallan Umma data dawo cikin d'akin

"Umma wae kuma kinji se mun biya wani kud'in kafin mu fara Necon" da mamaki dukkan su suke kallan ta, Yah Sadeeq yace

"Wane kud'in kenan?" seta k'ara ta6e baki kafin tace

"Nima bansani ba"

"Yanzu kuma naga kin ci exam d'in ae.." Umma ta fad'a tana kallan ta

"Ehh Umma haka dae suka ce"

"Toh Allah ya kyauta" Umma ta fad'a tana jinjina kae... Lokacin da Abba ya dawo yaji labarin Ayrahn taci exam

Please Login or Register in order to submit comment