Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen, acan ya hango shi tsaye wajen me siyar da mango yana ta zuba shi da me mangoron, seya samu kansa da jan tsaki gami da furta

"Yaseer!!" ya fad'a yana shirin d'auke kansa idanun sa suka sauka akan fuskar ta sanda wani sassanya kuma kyakykyawan murmushi yake tashi akan fuskar ta wanda ya matuk'ar k'awata kuma ya sake fito da aenahin kyawun ta, cikin en sekonnin da basu wuce 2 ba yaji yanayin bugun zuciyar sa ya sauya wanda har be san sanda ya rintse idanun sa ba yana sanya hannun sa saetin zuciyar sa, seya maeda kansa jikin kujera yana sake lumshe idanun sa kafin a hankali ya fesar da wata iska daga bakin sa

"What happen to me?" he asked him self still dae idanun sa suna a lumshe haka zalika hannun sa dafe da k'irjin sa, yafi minti 2 a haka kafin bugun numfashin sa ya fara komawa dae_dae, dae_dae lokacin kuma da Yaseer ya bud'e murfin motar ya shigo, da mamaki ya kalli Rk da har lokacin be bud'e idanun sa ba yace

"Rk.. Lafiya?" se a lokacin ya shiga bud'e idanun sa dake d'auke da dogayen bak'in gashin idanu masu matuk'ar kyau sannan ya sauke su kan Yaseer yace muryar sa a d'an ciki

"Babu komae.."

"Sure?" seya jinjina masa kae kawae yana sake lumshe ido, shi kansa ba zece ga dalilin da yasa yaji bugun zuciyar sa ya chanja tafarar d'aya ba

"Ohk.." Yaseer ya fad'a yana kunna motar ya fara driving, seda suka yi nisa da fara tafiyar sannan Yaseer ya kalli Rk kana ya maeda duban sa kan titi yace

"Ina tunanin gobe zan koma Kano fa.."

"Saboda?" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalle shi

"Madam ta matsa wallahi, ni kuma bansan 6acin ran ta, so dole na koma a goben gaskiya" murmushi Rk yayi wanda ya sake fito da aenahin kyansa kana yace bayan yaja k'aramin tsaki

"Idan ba kayi haka ba ae bazan gane kae ne ba"

"Me kuma nayi?" Yaseer ya fad'a yana dariya, shiru Rk ya masa dan yasan dama da biyu yayi maganar

"Mutumi na kae ma ka daure kayi auren nan wallahi.." kafin ya kae ga k'arasawa Rk yace

"Bismilllahi.., pls wae kae baka gajiya da zancen nan ne? Ka dae san bazan k'ara shekarun da nayi a baya ba tare da nayi aure ba koh?"

"Yawwah mutumi na yanzu kace dae na fara shiri kenan?" Yaseer ya fad'a duk da yayi mamakin jin zancen Rk d'in

"Kamar haka kake so na fad'a koh? Toh ae gashi nan na fad'a maka" Rk yayi maganar cikin basarwa, tsaki Yaseer ya ja yana fad'in k'asa_k'asa

"Ae seka yi ta zama" duk da ya ji shi amma bece masa komae ba ya cigaba da danna wayar sa..


.... Da sallama ya shiga cikin parlourn, Mummy dake zaune kan kujera ta taso tana fad'in

"Sannu da zuwa likita, ka dawo lafiya?" murmushi yayi kana yace

"Lafiya k'alau Mummy, Daddy fa?"

"Be shigo ba tukunnah" seya jinjina kae kawae, can ya jiyo Mummyn na fad'in

"Ka dad'e da shigowa ne?" d'an ta6e baki yayi kana yace bayan ya girgiza kae

"Nop, ban wuce 1 hour ba.."

"Ohk bari Muneerat ta kawo maka abinci yanzun nan" seya d'an yi shiru kad'an, baya son Mummyn ta dinga had'a harkar sa da yarinyar ballantana har suyi tunanin wani abun, se dae 'ya 'ya ce, ko yaya ya nuna baya son hakan yasan ba zata ji dad'i ba, so ko dan kulawar Mummyn a gare shi ya sanya ya dinga d'auke kae akan wasu abubuwan, dan haka bece komae ba ya wuce dinning area, ya ja kujera ya zauna bayan ya ciro wayar sa daga cikin aljihu ya fara dannawa. Wajen mintuna 10 da zaman nasa, wata madaedaeciyar budurwa er kimanin shekaru 22 ta fito daga cikin kitchen sanye cikin riga da skirt na atamfa wanda suka yi cif cif a jikin ta, se dae kasancewar haka take a tsaye yasa kayan basu wani mata kyau ba sun dae yi mata cas cas kamar a jikin ta aka d'inka, daga fuska babu laefi tana da nata kyan dae_dae misali, bak'a ce se dae ba can ba, amma saboda man da take shafawa yasa fuskar ta ta ta fito tayi haske sosae kuma take wani irin shek'i, sannan kuma doguwa ce babu laefi, kan ta babu d'an kwali se wata hula data saka ta zame ta har wajen rabin kan ta, wanda ya fito da kusan rabin kitson attach d'in dake kan ta, a hankali ta k'arasa ta ajje cooler data d'auko sannan ta koma ta kwaso ragowar kana ta dawo taja kujera ta zauna tana kallan sa cike da matsananciyar k'aunar sa tace

"Sannu da zuwa Yaya na" se a lokacin ma shi yasan da wanzuwar ta a wajen, ya d'an d'aga kan sa ya kalle ta da kyawawan manyan idanun sa sannan ya d'auke, seta lumshe idanun ta tana jin idanun nasa kamar wani abu ne a cikin su wanda ya sanya bata iya jure kallan cikin k'wayar idanun sa, sosae taji dad'in yadda ya kalle tan, kafin ta dawo daga wannan kuma taji yace

"Yawwah barka.." seta sake yin murmushi tana janyo plate ta fara serving nasa, Mummy da fitowar ta kenan daga d'aki ta kalli Muneerat dake zuba masa abinci cikin plate da gasken gaske, seta girgiza kae a ranta tana raya "Lallae soyayya me chanja mutum" dan kuwa tasan halin k'wuiwa irin na d'iyar ta ta, bata aekin komae cikin gida, koda abinci ne kuwa se dae a kawo mata idan an kawo kuma a zuba mata, ina ganin da da dama ma cewa zata yi a bata a baki. Plate d'in ta tura gaban sa sanda ta gama zuba komae a muhallin sa sannan ta koma kan kujerar tana fad'in

"Bismilllah Yaya na" seya ajje wayar sa a gefen sa, sannan yaja plate d'in a hankali yace

"Thank u" wani irin farr tayi da idanu tana jin dad'i mara misaltuwa, ko ba komae tasan tayi abin kirki tunda gashi wanda tayi dan shi d'in har godiya ya mata, zata so ace kuma wannan kwalliyar ma ya kalla yace tayi kyau da tafi kowa farin ciki, se dae tasan kafin ma ya kalle tan abu ne me wuya ballantana yace tayi kyau, wayar sa daya ajje tabi da kallo sanda ta kawo wani haske, tana jin kamar ta janyo wayar ta duba wani abu amma se dae ba zata iya ba musamman daya kasance idanun sa na wajen, se kawae ta cigaba da kallan had'ad'd'iyar wallpaper wayar tasa dake d'auke da tambarin "A" wanda ita har yanzu tayi tunanin ta fad'ad'a k'wak'walwar ta amma ta gaza gane abinda yake nufi da hakan

"Uhmm Yaya na ya d'alibae?" tayi k'arfin halin fad'in hakan dan katse shirun daya wanzu a wajen na wasu mintuna dan tasan ko da zata shekara ba tace komae ba, shi shirun baze dame shi ba balle yace wani abun, d'an ta6e baki yayi gami da yamutsa fuska ta d'auka ma ba zece komae ba se kuma taji yace

"Alhamdulillah, baza kiyi karatu bane?" yayi maganar sanda ya ajje spoon cikin plate d'in, bata bawa maganar daya fad'a muhimmaci ba seta kalli abincin daya keci da kallo sannan ta kalle shi sanda yake k'ok'arin mik'ewa tace

"Wae har ka gama?" ta fad'a itama bayan ta mik'e tsaye cikin maraeraece fuska, sake yamutsa fuska yayi kana yace

"Ehh, dama ba yunwa nake ji ba, kije kiyi karatun ki" ya fad'a yana d'aukar wayar sa, seta bishi da kallo sanda yake wucewa har ya fice daga d'akin, komawa tayi ta zauna tana jin yadda wasu k'walla suka tarar mata a ido, dae_dae lokacin Mummy ta k'araso taja kujera ta zauna tana kallan ta tace

"Muneerah meya faru?" seta d'ago idanun ta ta kalli Mummyn sannan tace

"Mummy kinga fa abinda yaci, kamar dan ina wajen ne fa yak'i ci da yawa fa"

"Ke waye ya fad'a miki haka Muneerah?" Mummy ta fad'a tana kallan ta, seta sake maraeraece fuska sannan tace kamar zata sanya kuka

"Toh Mummy se yaushe ne zamu saba, har yanzu kullum jiya i yau" ajiyar zuciya Mummy ta sauke sannan tace

"Uhmm Muneerah gajen hak'uri ne dake, idan ma kun saba idan ma baku saba ba aure ne dae kin san za'a yi shi koh? Ko kuwa kin ta6a ganin Daddyn ki yayi magana 2? Sun riga sun gama magana saboda haka ki kwantar da hankalin ki, ko ba yanzu ba zaku saba nan gaba" hannu Muneerah ta saka ta sake share k'wallar idanun ta sannan tace

"Da gaske Mummy?" ta fad'a kamar zata yi kuka, murmushi Mummy tayi tana jan Muneerah jikin ta tace

"K'warae kuwa Munee.." se a lokacin Muneerahn tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye ta, ji take kamar taje tace wa Daddyn nata idan za'a saka musu rana kada a saka da yawa, kae ita da zata iya ma da kanta za taje wajen Abban Rk d'in tayi masa maganar kar a saka ranar da yawa.


... Yana fitowa compound d'in gidan motar Daddy ta shigo gidan, seya k'arasa zuwa parking space d'in zuwa wajen motar, ya sanya hannu ya bud'e murfin motar inda Daddy ke zaune, Daddy ya fito yana murmushi yace

"Ka dawo kenan Doctor?" murmushi Rk yayi kana yace

"Ehh Daddy, barka da dawowa"

"Yawwah" ya fad'a sanda yake mik'a masa brief case d'in hannun sa, hannu 2 Rk ya saka ya kar6a kana suka fara takawa zuwa d'akin Daddyn

"Ya karatu ya kuma d'alibae?" Daddyn ya fad'a har lokacin suna tafiya

"Alhamdulillah Daddy" Rk ya fad'a

"Toh Allah ya taemaka"

"Ameen" ya fad'a sannan suka cigaba da tafiya, seda suka shiga parlour sannan Rk ya ajje brief case d'in hannun sa kan kujera kana ya sake fad'in

"Sannu da dawowa Daddy"

"Yawwah.." Daddy ya fad'a yana sake jin k'aunar Rk d'in a ransa, d'aya daga cikin halayen daya sanya yake son aura masa Muneerah shine tarbiyyar sa, sosae hakan ke k'ara masa k'aemi wajen son cika wannan burin nasu shi da d'an uwan sa

"Bari na wuce.." Rk ya fad'a

"Tohm shikenan, idan da akwae wata matsalar seka sanar dani" Daddy ya fad'a yana bin Rk da kallo sanda yake ficewa daga cikin d'akin.


.. Fitowar su kenan daga Capteria, su 3 ne a wannan karon, rana ta farko kenan data fara bin su Capteria saboda k'aryar su data musu yawa, ita kuwa ba er kowan kowa ba idan tace zata biye musu d'an kud'in da take dashi seta k'arar dashi a kwanaki k'alilan, dan haka take kama kan ta sosae, daga ita se Jidda se Ruks ne yanzun, tana sanye cikin abaya maroon colour da mayafin ta data yafa shi bayan ta saka wata kyakykyawar hula saboda kada sumar ta ta fito. Sun zo zasu gifta ta wajen wasu jerin reading chairs Jidda tace

"Ko mu d'an zauna mu huta ne?" da sauri Ayrah ta girgiza kae sannan tace

"A'ah ni kam na gaji" dan har ga Allah ta gaji so take ta zauna ta huta, idan da dama ma ta kwanta

"Haka dae, Allah kuwa Ayrah kin fiya lalaci" Jidda ta fad'a tana kallan ta bayan ta jefa mata harara, murgud'a d'an k'aramin bakin ta tayi ba tare da tace komae ba, Ruks tace

"Gaskiya dae kam, ya kamata mu huta" ganin su dae hutawar zasu yi ya sanya ta ta6e baki sannan tace

"Ni dae na tafi.." ta fad'a tana yin gaba, suka bita da kallo sannan suka nemi waje suka zauna. A hankali take tafiya zuciyar ta fall cike da tunanin Umman ta, sosae take jin kewar ta musamman a kwanakin nan duk da kullum se sunyi waya, amma ta k'agu ta gan ta

"Raj!!" taji an ambata daga bayan ta, wanda kiran sunan ya gama fita ne da bugun zuciyar ta, take a lokaci guda taji bugun zuciyar ta ya sauya, suna ne da zata iya kiran sa da extra ordinary one, sannan kuma tun daga wancan lokacin bata sake jin me irin sunan ba ballantana tayi tsammanin ko suna ne yazo d'aya, "ko dae shine?" ta tambayi kan ta, wannan tambayar data yiwa kanta ya sanya har bata san lokacin data juya da wani irin sauri ba tana wuwwulga kyawawan idanun ta cikin harabar makarantar, dae_dae lokacin data hango wani ya k'arasa shigewa cikin wata hamshak'iyar mota, cikin sakannin da basu wuce 5 ba motar ta bar wajen, ji tayi kamar sun tafi da duk wani kuzari da numfashin ta, ta lumshe idanun ta tana jan numfashin ta a nutse ko zata samu ya dawo dae_dae

"Raj!" yanda aka fad'i sunan ya sake dawo mata cikin kwanyar ta, seta sake bud'e idanun ta tana fatan ace taga Raj d'in ta a gaban ta, toh koma dae kunnen ta ne ke mata gizo?.....


Mhiz Innocent....... ✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 017_018



___A hankali ta sauke numfashi tana sake lumshe idanun ta, ganin da tayi ta tsaya ne akan hanya ya sanya ta jan k'afafun ta ta fara takawa zuwa Hostel, da k'yar ta iya k'arasawa cikin d'akin saboda yadda jikin ta yayi wani irin mugun sanyi haka zalika k'irjin ta ya mata wani irin nauyi. Ajiye littafin hannun ta tayi sannan ta haye kan gadon ta taja pillow ta kwanta tana lumshe idanun ta

"Raj!" ta sake fad'a akan la66an ta, cikin lokaci k'ank'ani rayuwar su ta baya ta fara dawo mata cikin kwanya kamar wadda ake haskawa, wata irin kewa ta musamman ta shiga ratsa ta, tana jin ina ma ace ta gan shi, ina ma ta sake ganin shi a rayuwar ta ko da sau d'aya ne, ko ina ya shiga? Ina yake? Meyasa bata sakr ganin sa tun wancan lokacin ba? Se yanzu ta tsaya tayi wa kan ta wad'annan tambayoyin wanda ada k'uruciya bata bar ta tayi ba, tabbas Raj d'in wani mutum ne na musamman a rayuwar ta wanda bata tunanin har abada zata ta6a mantawa da shi, koda kuwa bata sake ganin sa ba a kafatanin rayuwar ta, ko idan ta gan shi zata gane shi? Tana zaune a haka kamar me shirya film duk wani abu daya faru a rayuwar su tana k'ok'arin tuna su, duk da wasu abubuwan da dama ta manta saboda yanayin shekarun ta a wancan lokacin har zuwa sanda Bahijja ta shigo cikin d'akin, ta kalle ta yadda take juyi daga wannan 6angaren gadon zuwa wani 6angaren

"Lafiya kuwa Ayrah?" seta bud'e ido da sauri yadda ta tsorata dan sam bata san da shigowar Bahijjan ba kawae maganar ta taji, ganin ta ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Ehh.. Yanzu kika shigo?"

"Ehh yanzun nan" Bahijja ta fad'a tana zame mayafin jikin ta, Ayrah ta koma ta kwanta dan sosae take jin dad'in tunanin da take yi.




*** *** ***

.. Littafin ta ta d'auka ta sake karantawa sannan ta rufe, Ruks dake kusa da ita tace

"Wae Ayrah gaba d'aya littafin kike k'ok'arin karancewa ne? Test ce fa ba exam ba" ta fad'a dan tun jiya data farka cikin dare taga Ayrahn na ta karatu, shiru Ayrahn ta mata har seda ta gama zuba littafan ta cikin jaka sannan tace kamar bata son yin maganar

"Ae dae na gama" jinjina kae Ruks tayi sannan tace

"Gaskiyane, sannu da k'ok'ari, ni kam dae ina kusa da ke"

"Toh" Ayrah ta furta dan ita sam bata da k'yashi a rayuwar ta, bata k'i duk abinda ta karanta kema ta baki ki rubuta ba, se dae abin nata har da rashin wayo da ga6un ta, dan kuwa zata iya bud'e miki paper ta kiyi copying ba abinda ya dame ta, Bahijja dake saka takalmi tace

"Wallahi dama ni topic d'in daya gama mana last week kawae na karanta, couz ina da tabbacin a cikin sa zeyi tambaya" dariya Jidda tayi sanda take k'ok'arin ficewa daga d'akin tace

"Ashe duk gwara ni ma, cha66.." tayi maganar tana ficewa daga d'akin, suma duk se suka rankaya suka fice daga cikin d'akin zuwa class. Sanda suka je 8 ba tayi ba dan haka sun riga shi zuwa, seda suka je da wajen mintuna 5 sannan yazo, tunda suka shiga ajin ta d'auko littafin ta ta cigaba da dubawa, Ruks da Bahijja sune a gefe da gefen ta yayin da Jidda ke kusa da Ruks, tun ranar data fahimci su zaman baya kamar a jikin su yake seta k'yale su kawae ita take zaman ta a gaba, se dae wani lokacin ne se suma su zauna a gaban, musamman kuma idan za'ayi test se duk su dawo gaban ko dan ta taemaka musu saboda yadda suka fahimci yanda kwanyar ta ke ja. Cikin takun nutsuwa yayi parking motar sa a bakin ajin, a hankali ya saka hannu ya zare bluetooth d'in dake kunnen sa ya ajje shi kan d'aya kujerar sannan ya cigaba da danna wayar sa, seda 8:00 ta buga sannan ya bud'e k'ofar ya fito bayan ya d'auki wasu books dake a back seat, sanye cikin k'ananan kaya kamar koda yaushe, kayan dake matuk'ar yi masa kyau, su sake fito da zalla kuma aenahin kyan sa, cikin nutsuwa ya cigaba da takawa zuwa ajin, kafin ya shiga wad'anda zuwan su kenan suka yi wani irin sauri suka shige ajin dan kada ya riga su shiga, yana shiga kuwa gaba d'aya en ajin suka nutsu

"Wow! Kamar ko yaushe dae" taji Ruks dake gefen ta ta fad'a, shiru tayi dan tasan da wanda take, ita kuwa haka kawae take gujewa kallan inda yake, saboda yadda kallan nasa ke yawan haefar mata da fad'uwar gaban data rasa dalilin sa, ita har yanzu dukan su mamaki suke bata idan ta kalli yadda dukkan su suke crushing akan abu d'aya, kuma a gaban juna zasu zauna suna kod'a shi kowacce ta kawo nata point d'in, seta ta6e baki kawae a ranta tana ayyana

"Meya shafeni ni?" kafin a fara test d'in abinda be yiwa su Bahijja dad'i ba shine yadda ya tarwatsa kan en ajin ta hanyar bawa monitorn su umarni, cikin lokaci k'ank'ani kowannen su aka tarwatsa shi zuwa wani wajen, sannan ya bada minti 20 kawae kowa yayi submitting test d'in sa duk da uban tambayar da yayi musu, duk da tambayar guda 2 ce amma idan baka nutsu ka fahimce ta ba yanzun nan zaka yi kwa6a, saboda haka daga wajen mutane da dama basu wani tsaya sunyi nazari ba kawae suka shiga amsa ta, se kuma wani 6angaren da suka tsaya suka yi nazari sosae akae, cikin su ne hadda Ayrah a ciki wadda seda ta shafe wajen minti 5 tana nazarin questions d'in kafin tayi bismilllah ta fara rubutu cikin k'warewa

"Time taken" ya furta a nutse bayan cika mintuna 20 d'in daya bayar, mik'ewa Monitorn nasu yayi yabi kowa ya kar6a paper sa, wasu duk suka baada yayin da wasu k'alilan basu bayar ba saboda basu gama ba, Monitorn bebi ta kansu ba ya had'a paper hannun sa yabi bayan Rk daya fice daga cikin ajin har zuwa motar sa, ya bud'e ya shige motar sannan Monitorn ya ajje masa papers d'in a front seat, dae_dae sanda yake tada motar su 3 suka fito, Ayrah se wata er ajin tasu Fateema, sannan wani su kad'ae ne basu bayar ba, Monitor ya kalle su sannan ya kalli Rk yace a hankali

"Sir.. Pls wad'anda basu bayar ba!" da mamaki Rk ya kalle shi kamar ba zece komae ba se kuma yace

"Saboda raeni?" da sauri ya girgiza kae lokaci d'aya yana furta

"No sir, ina sauri ne ban kar6i ta sun ba saboda kada dukan mu mu rasa, Sorry sir"

"Leave them, next tym zasu yi saurin baka.." yayi maganar sanda yake maeda kan sa kan driving d'in daze soma

"Pls Sir, ayi musu hak'uri ba dan halin su ba" yayi d'an shiru sannan yace bayan ya fesar da iska daga bakin sa

"Su wakilta mutum d'aya a kae min office" ya fad'a yana yin gaba

"Thank u so much Sir" Monitorn ya fad'a yana mik'ewa tsaye zuwa bakin class d'in, daga inda take ta runtse idanun ta tana ganin kamar tun yanzu tayi failing course d'in tunda gashi ta rasa C.A, tana shirin komawa cikin ajin hannun ta akan fuskar ta tana ji kamar ta fashe da kuka ta jiyo muryar Monitorn nasu na fad'in

"Ayrah.." seta dakata lokaci d'aya tana juyowa, ya kalli yanda fararen idanun ta suka sauya kala sannan yace bayan yayi murmurshi

"Doctor yace a cikin wad'anda ba kuyi submitting Paper ku ba ku wakilta mutum d'aya ya kae masa" lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin dad'i na ratsa ta, seta kalli Fatima dake gefen ta itama rik'e da tata Paper a hannun ta tace tana kallan namijin da shima be bada ba, bata san sunan sa ba dan ita harkar matan ajin nasu ma bata kowa take shiga ba ballantana ta mazan ajin nasu

"Gashi zaka kae masa?" ta k'are maganar tana kallan sa, Monitor ya kalle ta yace

"kin san yadda za'ayi? Ki kar6i Paper su ki had'a ki kae masa" da mamaki ta kalle shi jin furucin sa kafin tace komae ya sake jinjina kae, da sauri ta girgiza kae sannan tace da sauri tun kafin ma ya sake cewa komae

"A'ah ba zan iya ba.." tayi maganar da dukkan gaskiyar ta, dan a yadda take ji koda za'a ce sun rasa exam ne ba C.A ba ba zata iya zuwa wajen mutumin ba, cikin maraeraecewa Fateema tace

"Don Allah Ayrah kije ki kae kin ji?"

"Toh ke waya hana ki zuwa?" ta fad'i abinda take sak'awa cikin ran ta, kafin duk suce komae ta sake fad'in

"Babu inda zan je ni" tayi maganar kamar zata saka kuka, hannu Monitor ya saka ya kar6i takaddun hannun su duka har ta Ayrah sannan yace

"Zo muje mu kae masa" tunda taga ya kar6a se kawae ta bishi a baya kamar wata doluwa, a haka har suka k'arasa Office d'in Rk, seya kalle ta bayan sun dakata daga tafiyar yace

"Kinga abinda yasa nace ki kae masa da kan ki, su Fateema sun fiya kaud'i, kuma kin san halin doctor.. kada suzo su janyo muku shiyasa nace ke kije, yanzu dae kije ki kae kada lokaci ya k'ure yace baze kar6a ba" hannu ta sanya ta kar6a fuskar ta a cunkushe, sannan ta runtse idanu tana karanto addu'ar da duk tazo bakin ta kana ta fara takawa zuwa bakin Office d'in, da sallama d'auke akan la66an ta ta shiga cikin Office d'in, ba tare data kalli kowa ba ta zube akan k'afafun ta, wani irin sassanyan k'amshi ke tashi cikin Office d'in, wanda ya had'e da k'amshin turaren sa da kuma shi kan sa na Office d'in ga kuma sanyin A.C hakan ba k'aramin k'arawa yanayin Office d'in dad'in shak'a yayi ba. Da mamaki Muneerah dake zaune kan kujera ta kalle ta, seta saka hannu ta zame k'aramin glass d'in dake fuskar ta ta cigaba da kallan ta

"Malama menene zaki shigowa mutane waje without even taking excuse?" taji maganar daga gefen ta, idan kujerar da Muneerahn ke kae ta d'ago ta kalle ta toh Ayrah ma ta kalle ta, seta d'aga kae a hankali ta kalli inda yake zaune kan kujera yayi shiru hannayen sa rik'e da ha6ar sa kamar me tunani

"Sir.." karo na farko kenan data ta6a yi masa magana, ita bata so ma hakan ta faru ba, so tayi har ta gama makarantar wata magana ba zata ta6a had'a ta da shi ba, idanun sa masu kaefi ya d'aga ya kalli Muneerah dake sake fad'in cikin kufula

"Kamar dake nake koh?" lumshe idanun ta Ayrah tayi ba tare data juya ta kalli Muneerah ba tace

"Sir test d'in mu na kawo.." tayi maganar tana mik'ewa daga zaunen da take ta ajje masa kan bench d'in dake gaban sa, jin bece komae bane ya sanya ta mik'ewa tana jin k'irjin ta na bugawa lokaci d'aya kuma tana fatan Allah yasa kada yace wani abun, ya kar6a kenan

"Don't ever try dis mistake again.." ta jiyo daddad'ar muryar sa yana fad'in hakan kuma a hankali kamar wanda akawa dole, ba tare data kalle shi ba ballantana bugun zuciyar ta ya k'aru tace

"In Sha Allah" tana shirin fita

Please Login or Register in order to submit comment