Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan zancen Abba amma be san ta inda ze soma ba shi kan sa.



.... Washe_gari, fitowar sa kenan daga wanka wayar sa dake ajje kan gado tayi k'ara, seya k'arasa da mamakin me kiran nasa ganin asuba ce

"Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seda ya sake kallan agogon wayar dan sake tabbatar da lokacin da gaske ne ko dae shine yayi mistake, haka d'in ne dae dan haka kawae ya d'aga wayar yana karawa a kunnen sa

"Raj!"

"Na'am" ya fad'a muryar sa a d'an cunkushe

"Ina fatan kana sane da d'aurin auren ka yau d'in nan koh?" Abbu ya fad'a shima ran sa a 6ace kuma babu fara'a dan yadda ya fahimci Rk d'in akwae rashin daraja a al'amarin sa kwana biyun, shiru na wajen second 30 sannan yace

"Ehh.." daga haka Abbu ya katse wayar sa, gefen gadon ya nema ya zauna hannun sa dafe da kan sa yana jin yanda yake cigaba da sara masa, ga kuma bugu da k'irjin sa ke tayi kamar wanda yayi gudu, shi har yanzu ya rasa gane matsalar Abbu, Ummee, Daddy da kuma ita kan ta Muneerahn, shin ita bata da zuciya ne a k'irjin ta? Ya fad'a mata baya son ta baya son ta amma tak'i hak'ura, ya share ta ya share ta duk da haka tak'i hak'ura, toh ya suke so yayi da ran sa ne shi kam? Me zeyi da wata Muneerah a matsayin mata? Sam bata a gaban sa, kwata kwata yana ganin kamar za'a k'ware shi ne kuma itama a k'ware ta, amma tunda sun nace kuma sun dage bari ya bar su suyi auren duk abinda ya biyo baya kuma suyi kuka da kan su ba dae shi ba, tunda shi kam ya riga ya nuna musu baya ra'ayin ta ko kad'an.


.. A cikin garin Kano aka d'aura auren Raj Kabeer da kuma Muneerah Abubakar, wanda saboda Abbu shine waliyyin amarya shi ya nemi da akawo auren Kano, shi kuma mahaefin ta bek'i hakan ba ya kawo shi nan d'in, daga lokacin da aka d'aura aure aka nemi ango aka rasa dama kuma da k'yar yazo wajen, seda Abbu ya masa tass sannan yazo wajen dan da farko cewa yayi ba zeje ba. Kae tsaye gida ya wuce ya sauya jamfa da wandon dake jikin sa da k'ananan kaya, fuskar nan kamar wanda akawa albishir da mutuwa, ya had'e ta tsaff kamar ze rufe wanda ya masa magana da duka, babu 6ata lokaci ya hau motar sa yaja be tsaya ko ina ba se gidan su Ayrah, dan yanzun ita kad'ae yake son gani ko ze samu sassaucin abinda yake ji a cikin zuciyar sa, a k'ofar gidan ya dakata ya lalubo number Yah Sadeeq sa suka yi exchanging ya kira, bugu 1_2 ya d'aga, a dak'ile ya furta

"Pls.. Idan tana nan, ina waje zamu d'an gaesa ne.."

"Ohk" Yah Sadeeq ya amsa yana ajje wayar, sannan ya k'arasa cikin d'akin Ayrah dake zaune ita da Umma yace

"Umma Raj na k'ofar gida, wae zasu gaesa da Ayrah.." da sauri Ayrah ta d'aga kae ta kalli Yah Sadeeq se kuma ta sadda kan ta k'asa cike da kunya

"Tohm shikenan" Umma ta fad'a tana kallan Autar ta ta dake ta sussunne kae

"Toh tashi ki shirya ki je.."

"Kae Umma!" ta fad'a bayan ta d'ago kan ta ta kalli Umman, girgiza kae Umma tayi tana murmushi sannan ta mik'e tana fad'in

"Idan kin gama jin kunyar seki tashi ki je" daga haka ta fice daga d'akin, bin Umman tayi da kallo har ta gama ficewa daga d'akin sannan ta dawo da duban ta jikin mudubin d'akin nata ta kalli fuskar ta, babu komae akan fuskar ta ta, kuma itama bata buk'atar wani abun, se kwae ta mik'e ta ciro wani gogaggen hijab d'in ta a cikin wardrobe ta zura sannan ta fito tana kallan tsakar gidan nasu, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa sannan ta fice daga cikin gidan. Tunda ya hango ta yaji wani irin sanyi na ratsa shi, wannan bak'in cikin da yazo dashi ya shiga kwaranyewa yana yin nasa waje, be san sanda ya saki murmushi ba lokacin data dakata daga inda take tsaye ba, bud'e murfin motar yayi ya fita sannan ya k'arasa ya bud'e wajen me zaman banza kana yace yana kallan ta

"Bismillah gimbiya.." wata kunyar ce ta sake lullu6e ta dan haka da er sassarfa ta k'arasa ta shiga cikin motar, se da ta shiga sannan ya zagaya ya koma mazaunin driver har lokacin yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa musamman daya tsinci murmushi akan kyakykyawar fuskar ta daya dad'e be gani ba, koda ya shiga motar ma juyowa yayi gaba d'aya yana kallan ta kamar ze cinye ta, hannu ta kae taja hijab d'in jikin ta tana rufe fuska da shi sannan tace

"Kae don Allah!" wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace

"A'ah ki bar ni na kalla ni kam, kin san kuwa yanda na zak'u da ganin fuskar ki, nayi missing naki irin sosae d'in nan" ya fad'a yana ji kamar ya janyo ta ya rungume ta, se dae yasan halin abarsa dan haka ya d'an lumshe idanun sa dae_dae lokacin data d'ago kan ta

"Ina fatan an yafe min abinda na aekata, kae na bisa wuya na" ya fad'a yana d'an rank'wafar da kan sa, bin sa tayi da kallo sanda ya rank'wafar da kan nasa, dae_dae lokacin da idanun ta suka sauka kan wasu jerin gwanon invitation card dake ajje a waje guda, haka kawae taji sun d'auki hankalin ta saboda yanda taga kamar idanun ta sun hangi sunan da take da tabbacin babu me irin shi a yankin su, dan haka babu 6ata lokaci ta d'auki katin sannan ta sauke manyan kyawawan idanun ta kan katin ta shiga karantawa, katin gayyatar d'aurin auren Raj Kabeer ne da kuma Muneerah Abubakar, idan har bata manta ba ko kuma kamar yanda ta sani sunan sa ne wannan, take kuma a lokaci guda k'afafun ta suka fara rawa kamar wad'anda ake kad'asu, tun kuma lokacin data karanta sunan wata mace tare da sunan Rk taji kamar wani abu ya gifta ta wajen idanun ta ne dan haka bata sake ganin wani abu dake a cikin katin ba, k'irjin ta ya shiga bugawa da k'arfin gasken gaske hannun ta kuma dake d'auke da katin ya shiga rawa shima dan haka cikin k'ank'anin lokaci katin yayi nasa wajen saboda yanda hannun ta ya gaza rik'e shi, gaba d'aya kan ta ya kulle, k'wak'walwar ta ta toshe haka zalika idanun ta sun makance kunnuwan ta kuma sun kurumce, babu abinda take iya tunani da hangowa se sunan sa dake jikin katin tare da sunan wata mace...




Mhiz Innocent.....✍️



https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd


*CHAPTER TWO*

*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*



Page 038



___Jin da yayi shiru har lokacin ba tace komae ba ko tayi wani abun da zesa ya fahimci tana wajen ba ya sanya shi d'ago da kan sa a nutse ya sauke su a kan ta lokacin da jajayen idanun ta da k'walla ta gama cika su taff ke kan sa, abu kad'an ne ze sanya su zubowa, kallan sa kawae take yi kamar me son gano gaskiyar abinda ta gani a cikin katin nan daga cikin fuskar sa, da mamaki yake kallan ta ganin tana masa wani kallan tuhuma ga kuma kyawawan narkakkun idanun ta da suke cigaba da bin sa da kallo, a hankali ya kae hannun sa yana shirin rik'o ta lokaci guda kuma yake fad'i a nutse

"Meya faru?" ya fad'a cikin damuwa, dae_dae kuma lokacin daya ida kae hannun sa jikin ta, se a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta, ta kautar da jikin ta daga k'ok'arin rik'o ta daya ke yi, sannan cikin sake k'arya ta zuciyar ta da abinda ta gani tace

"Aure kayi?" ta k'are maganar lokacin da hawayen da suka taru a cikin idanun ta suka samu damar zubowa akan fuskar ta, runtse idanun sa yayi lokaci d'aya k'irjin sa ya d'an buga

"Ya akayi ta sani?" tambayar data fara zuwa masa a cikin kae kenan, kamar ta san me yake tunani seta saka hannu ta d'auko katin daya fad'i daga hannun ta d'azun duk da har lokacin jikin ta be bar rawa ba

"Wannan katin auren waye?" iska ya fesar daga bakin sa sannan ya dafe kan sa daya sara masa, a hankali ya sake d'aga idanun sa ya zuba su a kan ta sannan yace

"Ayrah pls ki tsaya zan miki bayani kin san.."

"Na auren waye?" ta sake katse masa maganar daya fara yi, dan haka kawae taji jikin ta ya sake yin sanyi, seda ya sake lumshe idanun sa sannan yace

"Nawa ne amma.." kukan data keta rik'ewa ne ya k'wace mata gaba d'aya, bata da k'arfin da zata iya ficewa ta shige gida tayi kukan ta dan haka ta d'ora kan ta akan cinyar ta ta shiga rera shi tana jin yanda wani irin takaeci, bak'in ciki da kuma k'unar zuci ke addabar ta

"Yah ilahee.." ya ambata akan la66an sa, shi kam yau yaga ta kan sa, hannun sa duka biyun ya saka ya janyo ta cikin jikin sa har zuwa lokacin kuma kukan take har da sheshshek'a, fuzge jikin ta ta shiga yi amma ya k'arasa shigar da ita sannan ya zagaye ta da duka hannayen nasa yana lumshe idanun sa, har lokacin bata hak'ura ba ta cigaba da k'ok'arin tashi lokaci d'aya kuma tana furta

"Ni ka sake ni, bana son ka, bana son ka" be san sanda murmushi ya k'wace masa ba yana girgiza kae, ban da abin Ayrah idan bata son shi mene na kishin sa haka? Sake rungume ta yayi tsam cikin jikin sa kamar ze maeda ta cikin sa, sannan ya d'ora kan sa akan ta dake kan k'irjin sa, da dae ta gaji da k'ok'arin tashin se kawae ta sake fashewa da wani kukan tana komawa jikin nasa gaba d'aya, hakan ne ya sake bashi damar rik'e ta sosae, be hana ta kukan ba dan yasan dole ne se tayi kukan musamman wannan abu data gan shi kawae daga sama, ta d'auki wajen minti 2 tana cigaba da rera kukan se kuma daga baya ta koma tayi lak'was tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya cike da jin haushin sa, se kuma a lokacin ta cigaba da kicin_kicin tashi, a wannan karon be hana ta tashin ba ya sake ta a hankali, kae tsaye ta ta6a k'ofar fita se ta ji ta a rufe, dan haka ba tare data kalle shi ba ta furta

"Ka bud'e min na fita" shiru yayi yana bin ta da kallo duk da baya iya hangen fuskar ta

"Don Allah ki tsaya ki saurare ni" kamar jira take seta juyo tana kallan sa, kafin ta fara magana fuskar nan ta ta tayi jajur haka zalika sassanyar muryar ta ta sake rusuna

"Babu abinda zaka fad'a min Raj, ka bud'e min na koma gidan mu, kaje kayi rayuwa da wadda kake so nima yanzu bana son ka.." ta fad'a tana jin wani irin zafi da bata ta6a jin sa ba cikin zuciyar ta, zazzafar iska ya fesar daga bakin sa kana ya d'an lumshe idanun sa yace

"Ayrah, wallahi Abbu ne ya aura min ita, akwae maganar auren dama tun kafin sake had'uwar mu, don Allah kiyi shiru ki dena wannan kukan wallahi yana nakasta min zuciya" hannu ta saka ta toshe kunnuwan ta, tana ji a ran ta kamar wad'annan d'in kalaman yaudara ne kawae yake fad'a mata, meyasa zeyi mata haka? Meyasa ta yadda dashi shi kuma yaci amanar ta? Meyasa ze had'a ta da wata bayan ita tunda take bata ta6a had'a shi da wani ba, tana cigaba da tare sabon kukan daya taho mata ta furta

"Ni ka bud'e min k'ofa na fita.." yanzu kam babu musu ya bud'e mata k'ofar, da sauri ta saka hannu ta bud'e murfin motar sannan ta fad'a cikin gidan nasu, a tsakar gida ta taradda Umma babu 6ata lokaci ta fad'a jikin Umman tana sake sakin wani sabon kukan

"Subhanallahi Ayrah.. Meya faru?" Umma ta fad'a tana rik'o Ayrahn dake cigaba da kuka kamar wadda akama mutuwa, bata iya cewa komae ba saboda yanda zuciyar ta ke cigaba da tafasa, haushi da kuma takaeci suna sake cika ta, seda ta gama kukan tsaf sannan ta d'ago tana kallan Umma da zuwa lokacin ta gama rud'ewa da yanda taga d'iyar ta ta na kuka haka

"Umma wae aure yaje yayi! Umma ya yaudare ni bansan yadda zanyi ba zuciya ta na dab da bugawa" ta fad'a tama manta Umman ta take fad'awa maganar, da mamaki Umma take kallan Ayrahn kafin cikin k'arfin hali ta furta

"Ay..." sallamar da Abba yayi cikin gidan itace ta katsewa Umma maganar da take k'ok'arin fad'a, seta d'aga kae ta kalli Abban, ga mamakin ta seta gan shi sun shigo tare da Rk, maganar sa da Ayrah ta jiyo ne ya sanya ta shirin mik'ewa a fusace tana shirin shigewa cikin d'aki Umma ta rik'o ta

"Ki tsaya tukunnah" ba dan taso ba haka ta zauna d'in har lokacin kan ta na kan cinyar Umma kuma har zuwa lokacin zafin da zuciyar ta ke mata be ragu ba, haka zalika ji take kamar tayi ta kukan kar ta dena, sam bata san kuma meya shigo dashi cikin gidan ba, me yake nufin zece mata ta yadda dashi?

"Ina jin ka Allah yasa lafiya" Abba ya fad'a bayan ya zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan, seda ya d'an yi shiru kad'an kana ya saci kallan inda Ayrah ke zaune sannan yace

"Abba dama akan maganar aure ne da nayi yau d'in nan, naso na yiwa Ayrah bayani se dae tak'i fahimta ta, Abbu be san da maganar aure na da ita ba shiyasa, kuma dama tun farko yana da burin aura min ita kasancewar er k'anin sa ce, se kuma yanzu Allah yayi za'a yi auren amma sam bani da laefi Abba" ya k'are maganar a maraeraece dan yana da tabbacin Ayrahn na jin sa, ajiye numfashi Abba yayi sannan yace

"Ikon Allah, dama namiji ba dan mace d'aya akayi shi ba, kuma hakan ya sake nuna min kae d'in yaro ne me biyayya, dan haka ka tashi kaje Allah yayi maka albarka.. Ke kuma Ayrah ki tashi ki bi mijin ki dan banga amfanin zaman naki cikin gida bayan da auren ki ba" ya k'are maganar yana kallan Ayrah, da sauri ta d'aga narkakkun idanun ta ta sauke su kan Abban da yayi magana, ita kan ta Umma tayi mamakin maganar Abban, amma shi kam da yayi maganar da alama ko a jikin sa

"Abban su.." Umma ta fad'a tana cigaba da kallan sa

"Babu damuwa, ta tashi ta bishi d'in" shine abinda Abban ya sake fad'a, ajiyar zuciya Umma ta sauke sannan ta kalli Ayrah dake girgiza kae kamar k'adangaruwa cikin kuka tace

"Abba don Allah ka bar ni a gidan nan kaaji" dama saboda hakan Abban yace tabi mijin ta, dan kuwa yasan idan ba yanzun ba nan gaba ma se gwagwarmayar tafi hakan dan haka ya kalle ta yace

"Babu komae kinji, ki tashi kije.. Zamu yi komae daga baya" ita sam ba fahimtar Abban take yi ba dan kuwa kishi ya riga ya gama rufe mata ido, duk kuwa da irin bayanin da yayi ita har yanzun bata gamsu ba, kawae ji take yi kamar yaudarar ta yayi. Umma ce ta mik'e ta fad'a cikin d'aki ta shiga had'awa Autar ta ta kayan da tasan zata yi amfani dasu ko kuma ta buk'ata kafin komae ya daedaeta sannan ta fito har ran ta tana jin babu dad'i, a yadda ta bar ta a tsakar gidan a haka ta same ta, zaune ta d'ora kan ta akan k'afar ta tana sheshshek'ar kuka, seda ta fito d'in sannan Abba ya kalli Rk

"Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka, In Sha Allah zan neme ka ko ta layin Sadeeq ne" sosae yaji dad'in abinda Abban yayi dan haka yace

"Nagode sosae Abba, Allah ya k'ara girma"

"Ameen" d'ago da fuskar Ayrah Umma tayi tana kallan yanda fuskar ta tayi kace_kace da hawaye, seta girgiza kae tana jin tun yanzu har kewa ta fara kama ta

"Kukan ya isa haka Ayrah, ki tashi kije zamu yi waya Uhmm?" Umma ta fad'a cikin rarrashi, tausayin Ayrahn na kamata yanda take yarinya da ita amma yanzu haka tana da kishiya wadda za'a kira da Amaryar mijin ta, d'aga ido tayi ta kalli Umma, tana shirin fara magana Umma ta girgiza kae tana murmushin yak'e

"Ya isa haka ki tashi ki je kin ji?" sam bata so wani 6acin ran ya sake shiga tsakanin ta da iyayen nata dan haka ta mik'e tana jin jiri na d'ibar ta

"Allah ya tsare Auta" shine abinda Abba ya fad'a sanda take shirin gifta inda yake zaune, bata iya amsawa ba dan ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciyar ta, shine ya d'auki kayan sannan yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya, suna fita kuwa Umma ta mik'e da sauri ta shige cikin d'aki saboda kukan da taji ya taho mata, bin ta da kallo Abba yayi sannan ya dawo da kallan sa tsakar gidan da murmushi kan fuskar sa gami da girgiza kae. A hankali take takawa kamar mara laka zuwa wajen motar tasa, shi ya saka hannu ya bud'e mata, yanzu kam babu musu ta shiga sannan ya zagaya driver seat ya shiga ya zauna, kallan ta yayi yanda yaga tana ta curewa waje d'aya kamar me jin sanyi lokaci d'aya kuma tana matsar k'walla, lumshe idanun sa yayi a ran sa yana sak'a gwara ya bar ta tayi kukan dan yasan kuka dole ne musamman gare ta data shak'u da iyayen ta haka, bugu da k'ari kuma ga wannan maganar da itama ta sake tada mata da hankali.


... A cikin wani k'ayataccen Hotel yayi parking, a nutse ya juya ya kalli inda take kwance kan kujerar tayi shiru kamar me tunani, haka kawae yaji wani tausayin ta ya lullu6e shi, ya lumshe idanu lokaci d'aya wani haushi na taso masa tunawar da yayi yanzu haka akwae auran wata a kan sa

"Ayrah!" ya fad'a a nutse kuma cikin tausashshiyar murya, a hankali ta bud'e lumsassun idanun ta ta watsa su a kan sa wanda har seda hakan ya sanya shi lumshe idanun sa, se kuma data ga hakan sannan tayi maza ya janye nata idanun tana iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta dena ganin laefin sa albarkacin maganar daya fad'awa Abba cewar bashi ita akayi amma har zuwa lokacin ta kasa, ta kuma k'i dena ganin laefin sa, se dae an samu ragin kaso me d'an yawa daga laefin sa data fara gani a farko.

"Ki goge idanun ki pls, zamu sauka.." ya fad'a yana mik'a mata handkerchief d'in hannun sa, kamar ba zata kar6a ba se kuma a hankali ta saka hannun ta ta kar6a kana ta goge hawayen da ba dan kan ta suke fitowa ba da kan su kawae suke fitowa. Seda suka k'ara wajen minti 2 a haka sannan ya fita ya bud'e mata k'ofa ta fito kana ya koma ya d'auki kayan ta sannan suka wuce, yana gaba tana bin sa a baya kamar wata mara laka saboda yanda tafiyar ta ta ta k'ara sanyi, be damu da hakan ba ya cigaba da tafiya har zuwa sanda ya gama komae ya kar6i mukulli sannan suka wuce cikin d'akin. Madaedaecin bedroom ne me d'auke da babban gado, wardrobe da kuma mirror da sauran abubuwa dae da aka san bedroom na d'auke da, a hankali ya saci kallan yanda ta tsaya daga k'ofar wajen kamar me tsoron wani abun, bece mata komae ba ya k'arasa ya ajje jakar hannun sa sannan ya dawo cikin d'akin, tana nan dae inda ya bar ta, ya kalle ta bayan ya karyar da kae yace

"Don Allah ki shigo ki zauna" ba tace komae ba kuma bata motsa daga inda take ba, a hankali ya sanya hannun sa d'aya saman goshin sa ya murza kana ya juya, wayar sa ya ajje kan k'aramar kujerar d'akin sannan ya soma takawa da niyyar juyawa, kamar jira wayar take ya ajiye ta ta soma ringing, kamar wadda aka tsikara ko kuma ake ja ta sauke idanun ta akan wayar

"Muneerah!" taga ya bayyana akan wayar, dama kukan be ishe ta ba dan haka nan take idanun ta suka sake tara k'walla, dawowa yayi da baya dae_dae lokacin da kiran ya katse, ya k'araso ya d'auki wayar yana kallan kiran waye? Ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae ya kalli Ayrah dake tsaye yanayin ta ya sake chanjawa daga d'azun, bata iya kallan fuskar sa ba se cigaba da rik'e kukan daya taho mata take yi, idan har bata man ta ba waccan d'in da aka d'aura musu aure ae sunan ta Muneerah, d'an runtse idanun sa yayi kafin ya ajje wayar inda ya d'auka sannan ya k'araso inda take beyi wata wata ba ya saka hannu ya d'aga ta gaba d'ayan ta ya d'auke ta kamar Baby, da sauri ta fara hantsilawa da niyyar sauka amma be sauke ta ba har seda ya k'arasa kan gado ya zauna sannan ya jata zuwa cikin jikin sa, kamar jira take yi kuwa ta saki kukan data kasa rik'ewa

"Oh god" ya fad'a yana lumshe idanun sa, meyasa ita kuka baya mata kad'an ne? Yana jin ta sanda take cigaba da kukan, shiru yayi yana cigaba da saurarar ta ko zata yi shiru, da yaga dae bata da niyyar yin shirun seya d'auki hannayen sa duka biyun ya d'ago kan ta dake kwance male_male akan k'irjin sa, ya gaji da jin kukan nan na ta, d'an mitsitsin bakin ta red colour kamar wanda aka sakawa jan baki yabi da kallo yanda take motsa shi, ya d'an sake lumshe idanun sa sannan babu 6ata lokaci ya kama bakin nata cikin bakin sa, lokaci d'aya kukan nata ya tsaya saboda yanda taji bak'on al'amarin da tunda take bata ta6a ji ba, cikin sauri ta bud'e idanun ta a razane k'irjin ta na bugawa jin kukan nata yak'i cigaba da fita, fahimtar abinda ke faruwa ya sanya ta soma janye bakin ta da k'arfi lokaci d'aya kuma tana k'ok'arin tashi daga jikin sa cike da tsoro, sam be kula ta ba sema sake rik'o ta da yayi gam cikin jikin sa ya shiga kissing nata a hankali cike da matsananciyar k'aunar ta, idanun sa a lumshe haka zalika yana sake cigaba da shigar da ita cikin jikin sa, kuma yana cigaba da kokawa da numfashin sa daya soma chanjawa, ya d'auki wajen minti 1 yana kissing nata zuwa lokacin jikin sa ya gama yin sanyi, wani bak'on al'amari ya soma ziyartar gangar jikin sa, yanda ya d'an sassauta rik'e bakin nata ne yasa tayi amfani da wannan damar ta k'wace lips d'in ta tana jin yadda k'irjin ta ya cigaba da bugawa, ajiyar zuciya ya sauke sanda ta cire bakin nata daga cikin nasa har lokacin idanun sa na a lumshe ne, hannu ta saka ta dafe bakin ta da kuma iya k'arfin ta ta soma k'ok'arin mik'ewa tana ajje numfashin dake alamta kuka take mara sauti, se kawae ya sake saka hannu ya jata cikin jikin sa ya mata wata kyakykyawar runguma, hannu ya saka ya soma zame hijab d'in jikin ta har lokacin kuma be sake ta ba kuma yak'i bata damar tashi, girgiza kae ta shiga yi kamin cikin k'arfin hali tace cikin raunatacciyar muryar ta

"Ni ka k'yale ni" ta fad'a kamar zata fashe da kuka, be kula ta ba kawae ya k'arasa zame hijab d'in gaba d'aya ya jefar gefe sannan a hankali ya shiga shafa bayan ta kamar yarinyar goye, shi kad'ae yasan yadda bugun zuciyar sa ya k'aru, kawae k'arfin hali yake yi yana jan numfashi a hankali, ga mamakin ta se taji kukan na neman tafiya inda ya fito, se dae bata ji zata iya d'aga ido ta kalle shi ba saboda kunyar abinda ya mata yanzun, shi ko kunya ma baya ji? Seta sake kae hannun ta bakin ta data ke ji kamar yanzu ne yake kissing d'in nata, dan haka ta d'an zabura kad'an kamar wadda aka daka tana shirin mik'ewa k'irjin ta na cigaba da bugawa

Please Login or Register in order to submit comment