Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'in sosae yayi farin ciki, duk da kud'in da akace zasu bayar a makarantar hakan be wani dame shi ba, tunda dae gwamnati ta biya kud'i masu yawan da dama yake tunanin idan Ayrahn bata ci ba ya zeyi ya same su, se gashi cikin ikon Allah ma taci exam d'in..



... Littafi ne a hannun ta na English tana duba wani aeki da yanzun malamin dake koyar dasu ya gama musu aekin ya fita, seta d'auki littafin tana d'an dubawa ko akwae abinda bata gane a ciki ba, k'awar ta Zaenab wadda suke kiran ta da zee ce ta ta6o ta tana fad'in

"Kefa er raenin hankali ce, hala baki ji abinda ake fad'a ba" seta d'aga kae tana kallan ta kana tace bayan ta d'an 6ata fuska

"Karatu fa nake, Allah kuwa banji abinda akace ba"

"Toh cewa akayi wad'anda suka ci Qualifying suje PC na neman su"

"PC kuma?" ta fad'a tana fiddo da manyan fararen idanun ta waje, sosae ta bawa Zee dariya dan haka tayi dariyar tana fad'in

"Matsoraciyar banza, toh meze mana?" seta sake maraeraece fuska sannan tace

"Allah kuwa ni dae tsoro nake ji"

"Toh ae dad'in ta bake kad'ae bace ba koh? Ki tashi mu tafi kina gani duk wad'anda suka ci d'in sun fita" Zaenab ta fad'a tana mik'ewa, itama Ayrahn mik'ewa tayi ta ajje littafin hannun ta kan bench d'in su sannan suka fito daga ajin zuwa office d'in Principal d'in su, suna tafiya jefi jefi suna d'an ta6a hira kasancewar akwae sabo me k'arfi a tsakanin su, dan kuwa unguwar su d'aya su biyun, kuma Islamiyya ma d'aya suke zuwa

"Ace yace dukkan mu mu wanke toilets" Zee ta fad'a tana satar kallan Ayrah, seta 6ata fuska gami da shagwa6e face tace

"Don Allah ki bari" ta fad'a tana ta6e baki.. Akan ta idanun sa suka fara sauka sanda yake sakkowa daga cikin wata bak'ar hamshak'iyar mota, bak'i ne sosae sannan kuma me jiki babu laefi, sanye cikin wata Ash d'in shadda wadda ta sake fiddo da bak'in sa sosae, hannun sa d'auke da irin wannan sandar girman yana sanya ta duk inda k'afar sa zata taka, a kallan farko zaka iya bashi shekaru 40 zuwa 45 amma idan ka masa kallo irin na sosae zaka fahimci kud'in daya gama wadatar sane ya 6oye aenahin shekarun sa dan kuwa ak'alla ze kae shekara 55, seya lumshe idanu yana jin wani irin maganad'iso na fuzgar sa zuwa ga yarinyar, yanayin yadda take magana a shagwa6e hakan ba k'aramin burge shi yayi ba, seya bita da idanu kamar wani maye sanda suke k'ok'arin shiga Office d'in principal, nan ma seda suka tsaya suka d'an yi magana kafin suka tu6e takalman su duka suka shige ciki, wani numfashi ya fesar me k'arfin gaske lokaci guda kuma yana saeta numfashin sa da yanayin fitar sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci

"Wacece wannan yarinyar?" ya fad'a sanda wani malami a cikin makarantar ya k'araso yana gaeda shi, amma shi sam be lura ba hankalin sa na kan Ayrah ne, da mamaki malamin ya kalli inda ya nuna da hannun sa yace yana kallan Alhajin

"Wa kenan yalla6ae?"

"Wata farar yarinya data shiga Office d'in nan yanzu ita da wata.."

"Ohk wae Ayrah Ibraheem Khaleel?"

"Ayrah!" ya ambata a fili, "kamar yadda sunan ke da dad'i haka mamallakiyar sunan ke da kyau" ya ayyana a ransa kafin a fili yace

"K'warae wacece ita?"

"D'aliba ce a makarantar nan.." malamin ya fad'a yana mamakin jin tambayoyin dake fitowa daga bakin Alhajin

"K'arin bayani.." Alhajin ya fad'a yana kafe Malamin nan da jajayen idanun sa da suka kasance na halitta, seda yaja numfashi kad'an sannan ya furta

"Hadda ita dae a cikin wad'anda suka ci qualifying, so yanzu akwae wani important issue ne yasa principal kiran su" ganin dae baze samu wani cikkaken information daga wajen sa ba ya sanya shi fad'in

"Ohk ya yanayin k'wakwalwar ta yake?" seda ya d'an yi shiru sannan yace yana murmushi

"Gifted, a cikin ajin su ita ke d'aukar first position koda yaushe"

"Thank u" Alhajin ya fad'a yana mik'awa Malamin hannu suka gaesa sannan yayi gaba, drivern Alhajin ne ya matso kusa dashi kansa a k'asa yace

"Yalla6ae kana buk'atar wani abu ne?"

"A'ah.." ya fad'a yana kallan wanda ya fito daga cikin motar yana maeda waya cikin aljihu, da alama waya ya gama yi a cikin motar, shima kamar Alhajin zasu yi shekaru kusan d'aya se dae banbancin kamanni, dae_dae lokacin da Ayrah ke fitowa daga cikin Office d'in se dae wannan karon ita kad'ae ce, Alhajin ya kalli abokin sa Alhaji Baba yace

"Wannan yarinyar ta min" bin Ayrah Alhaji Baba yayi da kallo kana ya dawo da duban sa kan Alhaji yace

"Wannan abar?" jinjina kae yayi yana cigaba da binta da kallo harta 6acewa ganin sa

"Wannan ae se dae ka raene ta yalla6ae.." Alhaji Baba ya fad'a yana kallan sa

"Babu damuwa zan raene tan, daga yanzu zuwa sanda zata gama Secondary School, zan kashe ko nawa ne a kanta nasan ka gane abinda nake nufi.." murmushi Alhaji Baba yayi kana yace

"Kana tunanin wannan yarinyar zata aure ka?"

"Meze hana? Ina da wani aebun da 'ya mace zata guje ni ne? Musamman ma irin wannan da take zuwa makarantar talakawa irin wannan?" Alhajin ya fad'a yana kallan Alhaji Baba

"Iyayen ta fa?"

"Me kud'i suke yi? Ina tunanin ka manta nace zan kashe ko nawa ne a kanta koh?" Alhaji ya katse shi da fad'in hakan

"A nemo min wace ce ita, su waye iyayen ta, menene burin su na rayuwa, dukka zan cika musu shi komae girman sa.." ya fad'a yana kallan drivern sa....





*_Doctor RK is coming...._*😌🌚



Mhiz Innocent.....✍️







https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd



*♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡*

*FREE BOOK*

*CHAPTER ONE*


✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨


Page 011_012




___"Sir mun binciko maka wacece ita" cewar wani d'an matashi daya shigo cikin wani hamshak'in parlour daya gaji da had'uwa, murmushi Alhajin yayi yana kallan sa sannan yace

"Good job Muttala, wacece ita? Menene burin nasu? Yaya iyayen ta suke?" gyara zama matashin saurayin da aka kira da Muttala yayi kana yace

"Kamar yadda muka tsammata talakawa ne futuk yalla6ae, kuma idan iyayen nata nada buri toh be wuce na d'iyar tasu tayi karatu ba"

"Sure? Kuma kana nufin ka bincika da kyau?" Alhajin ya fad'a

"Sosae kuwa ranka ya dad'e, idan da k'ari dae toh se dae ko a bawa baban nata jari, dan wallahi ranka ya dad'e da gani yana shan kebula" ya fad'a yana wani maraeraece fuska kamar wanda yaga wani abun mara dad'i, se kuma ya sake gyara zama yace

"Amma wani hanzari ba gudu ba yalla6ae, ina ga da zan iya bada shawara da nace kar ka fara tarar abin daka haka, a fara da ita yarinyar saboda gudun matsala" jinjina kae Alhajin yayi cike da gamsuwa da maganar Muttalan yace

"Hakane, yanzu abinda nake so, ayi duk abinda ya dace akan karatun yarinyar, kome take buk'ata zan samar mata shi, kada ayi sanya akan wannan al'amari kuma bana so a samu matsala"

"Babu damuwa Alhaji..". Muttala na fita daga d'akin kae tsaye makarantar su Ayrah ya wuce direct ya tafi wajen Principal ya sanar dashi sak'on Alhaji, sosae shi kansa Principal yayi mamakin jin wannan lamari amma tunda abin na manya ne seya dena ganin laefin sa, ya maeda hankali wajen sanar dasu abinda Ayrahn ke buk'ata daya danganci makaranta..



Da sallama ya shigo cikin gidan, duka suka amsa masa sanda yake k'arasowa cikin tsakar gidan da suke zaune, Ayrah dake kwance kan cinyar Umma tana kalmashe mata dogon gashin kan ta me santsi, Umman ta mik'e ta k'arasa wajen Abba kafin ya gama shigowa, ta masa sannu da zuwa sannan suka k'araso suka zauna a tsakar gidan

"Matso ina zaune na k'arasa miki kalbar.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah data d'auki mayafi ta yafa a kanta, seta kwa6e bakin ta sannan tace kamar za tayi kuka

"Don Allah Umma a bari haka nan" harara Umma ta jefa mata, Abba dake kallan su yayi murmushi sannan yace

"A'ah abar Auta ta huta haka nan, kinga ma nazo miki da wani albishir.." ya fad'a yana sanya hannun sa cikin aljihu ya d'auko kud'i sannan ya mik'a mata yace

"Ga kud'in nan sun samu" ya fad'a yana murmushi, hannu biyu Ayrah ta saka ta kar6a sannan tana murmushi ta kalli Umma kana ta maeda duban ta kan Abba tace

"Abba Albishirin ka.." Seya kalle su su duka kafin yace

"Albishir kuma? Ikon Allah... Toh goro.." yayi maganar duka a lokaci d'aya, Ayrahn ta cigaba da fad'in

"Abba PC da kansa yasa aka kira ni ya fad'a min wae an biya min kud'in ma saboda k'ok'ari na" ta k'arasa fad'a da k'ayataccen murmushi akan fuskar ta, shiru na wasu en sakanni kafin Abba yace

"Ikon Allah, toh Masha Allah Auta, Allah ya k'ara miki k'ok'ari Uhmm?"

"Ameen Abba" ta fad'a tana mik'a masa kud'in hannun ta, seya sanya hannu ya maeda kud'in cikin hannun ta sannan yace

"Ki rik'e su a wajen ki bana so na kashe, in case koda wata matsalar zata taso, duk da bama fata ma" seta mik'awa Umma kud'in tace tana Kallan Abba

"Allah ya k'ara arzik'i Abba.."


..... A cikin en tsukun su Ayrah suka zana NECO, sun shafe satittika suna gabatarwa, sosae Ayrah ta dage wajen yin karatu ko dan ta cika burin iyayen nata na son tayi karatu, a kwanakin sau da dama takan hana kanta bacci dan dae tayi karatun, har wani lokacin se Umma ta saka ta tayi bacci sannan take hak'ura da karatun tayi baccin..


.. Tun d'azu bacci ke ta barazanar d'aukar ta amma take ta basarwa dan jira take Abba ya dawo saboda tun d'azu ya fita a dalilin rasuwa da akayi a cikin layin nasu, bata k'ara minti 5 a zaune ba kuwa ta jiyo sallamar sa daga tsakar gida, seta tashi zaune tana janyo d'an kwalin ta daya sa6ule daga kanta ta yafa shi ta zubo dashi gaba sannan ta fito tsakar gidan

"Abba sannu da zuwa.." ta fad'a bayan ta nemi waje ta zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gida

"Yawwah Ayrah.." Abba ya fad'a yana kallan ta, seta cigaba da zama har zuwa sanda Umma ta fito daga kitchen d'auke da plate a hannun ta wanda ta yiwa Abba kwad'on salad a cikin sa

"Sannu" ya fad'a yana kallan ta da murmushi kan fuskar sa, Ayrah tace

"Abba.." yace

"Na'am" ya fad'a yana kallan ta yadda take lumshe manyan fararen idanun ta da alama bacci take ji

"Abba dama zuwa nayi na fad'a maka.." seya cigaba da kallan ta sannan yace jin tayi shiru

"Ina jin ki"

"Wae gobe idan Allah ya kaemu ance muje da wani d'an gidan mu za'a min registration na Jamb" sosae Abban ya cigaba da kallan Ayrah, I zuwa yanzu haka kawae yaji rashin yadda ya d'arsu a ransa, dan haka dole yayi wani abun

"Shima cewa suka yi zasu biya miki?" seta jinjina kae kawae

"K'arfe nawa?"

"Wae kafin k'arfe 2 dae.." seya jinjina kae shima kafin yace yana janyo plate d'in gaban sa

"Toh shikenan, Allah ya kaemu gobe inaso naje wajen principal d'in ku"

"Toh Abba seda safe.." ta fad'a tana mik'ewa, Umma ta bita da kallo sanda take shigewa d'akin ta bayan ta mata seda safe, seta dawo da kanta wajen Abba tace

"Amma gaskiya makarantar nan idan hakane suna da kirki, kuma hakan ba k'aramin k'arawa d'alibae k'warin gwuiwa zeyi ba"

"Sosae kuwa" Abba ya fad'a a ransa dae yana tunani ne.


Washe_gari Abba tare suka fita da Ayrah zuwa makarantar tasu, sanda suka shigo cikin makarantar da k'afar su suke takawa zuwa ciki, jefi jefi Abba kan d'an yi mata tambaya ita kuma ta amsa masa, har zuwa sanda suka k'arasa inda office d'in principal yake, a dae_dae lokacin da Alhaji ke fitowa daga cikin office d'in principal d'in nasu yayi dae_dae da lokacin da wayar Abba ta fara ringing, seya zaro ta daga cikin aljihu yana barin wajen zuwa baya dan amsa wayar saboda hayaniya, yana juyawar shi kuma Alhajin ya ida fitowa, a take idanun sa suka yi tozali da kyakykyawar fuskar ta sanda take tsaye a wajen tana jiran Abba ya dawo su shiga Office d'in tare, seya bita da wani mayattacen kallo da idanun nasa yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa saboda k'aunar yarinyar

"Yalla6ae.." wani dake gefen sa ya fad'a, se ya d'an yi firgigit ya juya yana kallan mutumin sannan ya rufe idanun sa ya bud'e kana ya saki murmushi yace a hankali

"Idan na ganta wallahi ina loosing control d'ina ne.." yayi maganar sanda suke barin wajen zuwa inda motocin su ke ajjiye, suna wucewar Abba kuma ya ida wayar sa ya k'araso yana kallan Ayrah yace

"Muje..".... Da sallama suka shiga Office d'in, principal dake zaune ya kalle su sannan yayi murmushi ganin Abba fad'i yake

"A'ah sannun ku da zuwa" ya fad'a kamar wanda yaga wani hamshak'in mutumin, shi kansa Abba seda abin ya d'an so bashi mamaki amma ya fuske ya nemi waje ya zauna yayin da Ayrah ta zauna a k'asa, seda suka gaesa sannan Abba yace

"Dama magana ce akan yarinyar nan" yayi maganar yana nuna Ayrah da kanta ke k'asa, sannan ya cigaba da fad'in

"Abubuwa da dama sun faru se dae ban samu damar zuwa wajen ku ba, toh shiyasa a wannan karon nace bari nazo naji daga bakin ku.. Naji yau ma ance wae za'a biya mata kud'in registration na Jamb?" murmushi Principal yayi kana yace bayan ya had'e hannayen sa cikin juna

"Ae wato Alhaji Ibraheem ka godewa Allah, Allah ya baka yarinya me hazak'a, saboda haka dan mun d'auki nauyin ta wannan ba komae bane, In Sha Allah ma zamu d'auki nauyin ta ne har ta gama karatu.." dukkan su se suka kalle shi suna jin wani irin farin ciki na ratsa ilahirin jikkunan su

"Toh Alhamdulillah, Masha Allah, muna godiya sosae Principal, Allah ya k'ara arzik'i" Inji Abba

"Ameen_Ameen.."




.... A kwanakin da suka biyo ne Ayrah suka zana jarabawar Jamb d'in, babu wani dad'ewa kuma result d'in ya fito, cikin ikon Allah kuma ta doko point dae_dae da course d'in data ke so dama kuma a Neco ma ta fito da 9 credit, dan haka komae yazo cikin sauk'i, wani malamin su ne ya shige mata gaba bayan fitowar result d'in nasu wanda shima Alhaji ne ya sanya shi yin hakan, sosae suka yi fafutuka wajen sama mata admission har Allah yasa ta samu Medicine a A.B.U Zaria. Ba k'aramin farin ciki Abba, Umma, Yah Sadeeq har ma ita kanta Ayrahn suka yi ba sanda suka ji an sama mata Admission d'in ta hanyar wannan malamin nasu, amma sanda duk suka ji a inda ta samu Admission d'in se duk jikin su yayi sanyi. Umma dake zaune kan tabarma ta kalli Abba dake fad'in

"Duk da naji dad'in wannan Admission d'in da aka samu, amma bana tunanin zan yadda Ayrah ta tafi har Zaria karatu, ina tunanin kawae a bashshi.." Yah Sadeeq da shima yake kusa da Abba yace

"Abba ni ina ganin kawae a batta d'in ta tafi, tunda duk da k'arancin shekarun Ayrah tana da hankali.." ya k'arasa maganar yana kallan Ayrah gami da sakar mata murmushi, itama murmushin ta saki tana jin dad'in wannan yabon na Yah Sadeeq duk da dae ita kanta ji take kamar ta hak'ura da makarantar, dan bata masan yadda rayuwar ta zata kasance acan wani waje babu Umman ta, ba Abban ta sannan kuma ba Yah Sadeeq d'in ta ba, Umma taja doguwar ajiyar zuciya sannan tace

"Abban su barin wannan Admission d'in kamar mun saka k'afa ne munyi fatali da damar mu, ina ganin meze hana tunda mun yadda da d'iyar mu, mu barta taje d'in idan yaso mu dinga binta da addu'a kuma mu dinga kae mata ziyara..?" shiru Abba yayi na wasu en dak'ik'u kana yace

"Zan sake tunani.." daga haka be sake cewa komae ba.. A cikin satin Abba ya amince da zuwa makarantar Ayrahn, dan haka daga shi har Yah Sadeeq suka tashi tsaye sosae wajen fara siya mata abubuwan da zata tafi dasu, duk da ba wasu kaya ne na azo a gani ba amma dae sun samu sun siya mata abubuwan da suka san zata buk'ata.. Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka gama komae, duk wasu abubuwa da suka kamata aka gama su daga 6angaren Abban har daga can 6angaren Alhaji..


..... Zubewa yayi a k'asan carpet kansa a k'asa yana jira Alhajin ya gama wayar da yake yi, seda ya shafe wajen rabin awa yana wayar da duk da ganin wani ya shigo besa ya katse ta ba

"Muttala ina jin ka" yayi maganar sanda yake aje wayar akan kujerar gefen sa

"Yalla6ae jibi ne tafiyar tasu fa" murmushi yayi kana yace

"Toh madallah, yanzu abinda za'ayi.. ga kud'i nan kaje duk inda ya dace ka siyo duk wani abu da kasan yarinya budurwa nada buk'ata idan zata je makarantar kwana.." ya fad'a yana ajje masa wasu uban kud'i a gaban sa

"Toh shikenan, amma bana tunanin a had'a da kayan lokacin da zasu tafi can makarantar, inaga gwara daga baya kayan su bita.." jinjina kae Alhajin yayi sannan yace

"Hakan ma yayi.." ya d'an dakata kana ya d'ora da

"Kana ganin idan naje wajen mahaefin ta a yanzu banyi gaggawa ba?" girgiza kae Muttala ya shiga yi ya d'an yi murmushi kana yace

"A'ah ranka ya dad'e ka bari tukunna, kada su fahimci dalilin hidimar ka tun yanzu, zefi kyau mubi komae daki_daki.."

"Gaskiya a haka ma nayi k'ok'ari wallahi, bari dae zan bar ta ta gabatar da first semester kawae zuwa lokacin zan je wajen baban nata" ya fad'a yana girgiza kae shima

"Toh hakan ma babu laefi" Inji Muttala..




.... Tana sanye cikin doguwar rigar atamfa da hijab kasancewar sa favourite nata, sosae kyakykyawar fuskar ta tayi fayau kamar mara lafiya, fararen manyan idanun ta sunyi ja, hannun ta cikin na Umma tana kallan ta da idanun nata da suka sake yin rau rau, Umma tayi murmushi dan tana so ne ta kwantar mata da hankali tace

"Ya isa haka shalele, kada ki 6ata fuskar nan taki yanzun nan mana Uhmm?" Umma ta fad'a tana sanya hannu ta d'auke k'wallar dake zuba akan kuncin ta

"Umma ta zanyi kewar ki" ta fad'a tana kwantawa a jikin Umman, hannu Umma ta saka ta rik'o ta bayan tayi murmushi tace

"Banda abin ki Ayrah ae ba dad'ewa zaki dinga yi ba, ko kin manta zaki dinga dawo mana hutu?" seta jinjina kae kawae

"Toh idan kin gama kukan seki taho mu tafi" Yah Sadeeq daya shigo ya fad'a, seta d'aga kae tana kallan sa gami da murgud'a mitsitsin bakin ta

"Iyeee.. Lallae ne yarinyar nan" Yah Sadeeq ya fad'a yana rik'e ha6a. Har k'ofar gida Umma ta rako su inda motar da zata kaesu Zarian take, seda taga tashin motar tasu sannan ta koma cikin gidan tana matse k'walla, dan kuwa tun tasowar Ayrahn baza tace ga ranar da suka ta6a rabuwa ba, dan tun tana yarinyar ta mayyar Umman ce, ko yadda da mutane ba wani sosae take ba ballantana ace taje ta kwana.


... "Ki maeda hankali kiyi karatu, sati d'ayan nan da aka wuce ki ki samu wata ta koya miki, banda yin k'awar da zaki zauna kina fad'a mata cikin ki duk da dae nasan halin ki amma dae gwara na tisa miki" Yah Sadeeq ya fad'a sanda suke tsaye a wani ke6antaccen waje, seta jinjina kae kawae dan bata tunanin zata iya magana, idan kuwa tace zatayi maganar toh tabbas kuka zata saka, Abba daya fahimci haka se yayi murmushi dan shi kansa har ya fara kewar Autar tasa, ya matsa kusa da ita yace

"Ayi karatu sosae koh?" nan ma dae seta jinjina kan tana kae hannun ta idanun ta ta goge hawayen daya sauko akan fuskar ta, hannu Yah Sadeeq ya sanya cikin aljihun sa ya zaro wata k'aramar waya yace yana kallan k'anwar tasa

"Yau dae ga alk'awarin mu.." seta kalli hannun nasa sannan ta kalle shi, bata san sanda murmushi ya su6uce a kyakykyawar fuskar ta ba, ta saka hannu ta kar6a cike da farin ciki kana ta d'an jujjuya ta sannan tace lokacin da wasu kyawawan hawaye suka samu damar zubowa akan kuncin ta

"Amma nagode sosae Yah Sadeeq, Allah ya k'ara arzik'i"

"Ameen" dukan su suka amsa da hakan cikin jin dad'in yadda ta d'an saki jiki.. seda suka d'an dad'e suna sallamar zuwa lokacin ta saki jiki suna ta d'an hira, se kuma daga baya tayi kukan ta ta godewa Allah, sannan su Abban suka tafi bayan sun kwantar mata da hankali...




... A hankali ta tura k'ofar d'akin hannun ta jaye da er trolley d'in ta da aka kar6o mata a wajen k'anwar Umma da itama zama ya dawo dasu cikin kano, dukkan su suka d'aga kae suka kalle ta sanda tayi sallama da kyakykyawar siririyar muryar ta data sake sirancewa saboda kukan da tayi, su 3 ne zaune a cikin d'akin, d'aya na daga gefe tana danna waya yayin da biyun ke zaune kusa da juna suna hira

"Wa'alaeki Assalam" suka amsa dukan su suna bin bak'uwar fuskar da suka gani da kallo

"Wow, tubarkallah Masha Allah" d'aya daga cikin su ta fad'a a ranta lokaci d'aya kuma tana mik'ewa tsaye ta k'arasa inda Ayrah take tace tana d'an yin murmushi

"Anan d'akin kike?" tayi maganar tana kallan idanun ta da suka yi ja alamar kuka tayi, seta k'ak'alo murmushi ta wanzar akan fuskar ta wanda kana gani kasan beje ko'ina ba tana jinjina kae

"U're highly welcome.." ta fad'a tana d'aukar bagcon data gani a gefen Ayrah tayi gaba, babu musu Ayrahn tabi bayan ta a hankali

"Ruks ki tashi me waje tazo fa" wadda ta kar6i jakar Ayrahn ta fad'a tana kallan wadda ke zaune kan gado tana danna waya, wadda aka kira da Ruks d'in ce ta mik'e tana kallan Ayrah itama tayi murmushi tace

"Barka da zuwa bak'uwa"

"Umhum" Ayrah ta fad'a kawae tana jefa mata kalar murmurshin data yiwa Jidda, seta k'arasa ta zauna akan gadon tana jin ta gaba d'aya a wani irin takure, musamman yadda taga su duk lokaci d'aya suna neman sakin jiki da ita, seda Jidda ta ajje mata kayan ta gefe guda sannan ta dawo ta zauna kusa dasu Ruks ta zauna, Bahijja da tun d'azun ba tace komae ba se kallan Ayrah da take tace

"Bak'uwa ya sunan ki?" a hankali ta bud'e bakin ta daya mata nauyi tace

"Ayrah.."

"Awwwn, sunan en gayu, suna me dad'i.." kusan a tare suka fad'i hakan, har seda hakan ya sanya ta tayi murmushi

"Toh barkan ki da zuwa" Bahijja ta fad'a... Suna nan zaune d'akin har bayan isha'i suna hirar su, hirar da kusan duk akan abu d'aya suke yin ta, ita dae tana zaune a gefe guda se dae ta bisu da ido kawae, so take ta ke6e ita kad'ae tayi kukan ta ko zata ji sauk'in kewar gida data fara damun ta tun yanzun.

"Ruks ki tashi ki d'ora mana ko Indomie ce pls, kinga bak'uwa ma ba taci komae ba" Jidda ta fad'a, Ruks ta kalli Ayrah tace

"Ayrah kina jin yunwa ne?" seta girgiza kae kawae tana yabawa da kulawar mutanen da bata ta6a ganin su ba se yau

"A'ah a k'oshe nake" ta fad'a tana kallan Ruks d'in

"Toh dae kin ji, mu duk bama jin yunwa muma, a bar shi kawae pls"

"Shikenan ae" Jidda ta fad'a

"Kuuu, kun san k'arfe nawa kuwa?" Bahijja ta fad'a tana d'an waro eyes d'in ta

"Wani abun ya faru?" Ruks da Jidda suka tambaya lokaci d'aya

"Ni kam seda safen ku wallahi, kwanciya zanyi ko dan na tashi da wuri, gobe fa Doctor RK ne a farko, ko kun manta abinda yayi last Monday?" ta k'arasa maganar tana hayewa kan gadon ta

"Nima kam seda safen ku" Ruks ta fad'a tana mik'ewa, harara Jidda ta jefa mata sannan tace

"Toh ni me zan zauna jira hajiya? Ayrah seda safe" tayi maganar itama tana hayewa gadon ta.. Bin su tayi da kallo su duka lokacin da d'akin yayi shiru, se taji tsoro ya fara shigar ta, dan haka taja jikin ta ta maeda shi kan gadon ta kwanta, ta lullu6e kafatanin jikin ta da hijab d'in ta wani sanyi na ratsa ta, a hankali ta lumshe idanun ta wasu hawaye masu d'umi na sakkowa akan fuskar ta, wayar

Please Login or Register in order to submit comment