Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki riƙa faɗa min za ki ga na kawo miki kinji?"
Ya ƙare maganar da shafa kaina yana wani irin murmushi mai nuna tsantsan farin cikin sa da jin daɗin sakin jikina da nayi, alamun burinsa ya kusa cika nan bada jima wa ba,
Daga nan tafiya yayi Ni kuma na kwashe kayan na wuce,
Har na isa sashin mu babu wanda ya ganni sai da na koma sasan mu

Suna zaune su Inna Habibah a tsakar gidan na shigo da kayan,
Hakan ne yasa duk suka bi Ni da kallo,
Inda Inna amarya take cewa, "wai har ya tafi ne?"

Kai na gyaɗa mata tare da cewa, "eh ya wuce."

Inna Asabe tace, "kawo kayan mu gani, yau kuma tsaraban da yawa aka kawo mana kenan?"

Wurin ta na nufa ina miƙa mata ledojin,
Nan fa sai suka hau buɗe wa har da su Binta suna cewa, "kai! Wlh Madina ta fi mu more wa, ɗan dattijo sai mata hidima yake yi."

"Iyee! Lallai kam, abun na yi ne, kun gani fa har da kayan saka wa ya siyo mata."
A cewar Inna Asabe tana ɗaɗɗaga kayan, don ita har da hassada ma yake sanya wa take saka min ido

Lokacin ne Inna Lami ta fito daga kitchen itama ta samu wuri ta zauna a kujeran zuƙuno tana cewa, "oh! Shi kuma ko meye na yi mata sutura haka oho? Sai ka ce ya ganta a fatare?"

Inna Habibah tace, "to ban da abun ki Yaya, ai a fataren yake ganin ta, ba kya ganin kayan jikinta ne duk sun koɗe kullum a haka take zuwa masa, dole yayi tunanin bata da kayan ne, ai gwara ya siyo mata wlh, yana son ya ganta ɗas-ɗas."

Haka suka dinga duba kayan suna surutai, Inna Asabe tuni ta ɓarka ledan kayan zaƙin ta soma rabo sai ka ce nata, sai da ta raba wa kowa a wurin sannan ta miƙo min sauran tana cewa, "to ai dole kowa ya dangwali fa'ida, ba ga shi mun sha ba zamu mayar da yawun mu, suma kayan za a daukar wa Fatimah da Nafisa sai su saka."

Inna Lami tace, "a'a gaskiya ki bar mata abun ta, idan an basu su Fa'izan kuma fa? Sannan ma ya san kayan da ya siya mata in ya ga bata sanya ba zai iya tunanin mun hana ta ne, ki bata kayan ta kawai tunda mun sha wannan ya ishe mu."

Ni dai ina tsaye ina kallonsu bani da bakin cewa wani abu, yanda suka bani haka zan karɓa, farin ciki na ma yanda ta bani sauran da ɗan auki, zan iya sha har in ajiye wa Yaya Haula da Ihsan,
Tana bani kayan na wuce cikin ɗakin mu na zuba a cikin kayana na ɓoye ko ɗaya ban sha ba, sai idan Yaya Haula ta zo sannan zan raba in sha nawa


Su Fa'iza ne suka biyo bayana, suka zauna suna tsokanata wai, "sai na faɗa musu hiran da muke yi da Alhaji in ya kira Ni?".
[24/06, 8:23 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)``🙏

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 9*
_____Tun daga ranan akai-akai Alh. Badamasi yake zuwa wurina, duk idan zai zo sai ya kawo min tsaraba, bai taɓa zuwa hannu rabbana ba, shiyasa nima nan da nan na saki jikina dashi na saba dashi, har zama muke yi muyi ta hira don Ni tuni na dauke shi a matsayin mahaifi kamar yanda yake faɗa min koyaushe, duk da kasancewata ba wata mai hayaniya ba, amma ban san meyasa na saki jikina sosai da Alh. Badamasi ba, kuma dama a koyaushe Yaya Haula tana faɗa min, "na riƙa masa duk abun da yake so tunda shima yana son faranta min."
Tana nuna min cewa yana da muhimmanci a wurina saboda ta fi kowa jin daɗin yanda yake ɗaukar nauyina yana min komai na sha'anin gidan, ko kayan sallah yanzu shi yayi min, kayan da ko ƴan uwana basu samu kamar shi ba, shiyasa ake tayi dani a gidan, tun wasu suna ɓoye hassadar su a zuciya har sun fito suna nuna wa, amma basu da yanda zasu yi tunda baza su iya hana wa ba, sai dai suyi surutunsu su gaji

Ni har yanzu ban ma fahimci abun da yake kawo Alh. Badamasi wuri na ba; tunda har yanzu ban fahimci jagulanin da yake yi ba, wani lokacin dai ina mamaki idan ya fara shafa Ni yana yamutsa min ƙirjina da babu komai yana ɓashe baki, wai hakan shi a dad'i yake ji, amma Ni rashin wayon abun bai dame Ni ba, ba wai don ban san komai bane tunda mun karanta a makarantar allo ana mana karatu, kawai don gani nayi babu abun taɓawan ban taɓa kawowa da iskanci yake yi ba,
Shi kuwa dad'i yake ji idan ya zo yana jagula Ni yayi ta min hira yana ja na da surutu,
Babu ruwana kuwa na biye masa tun da na saki jikina mun saba, yanzu babu tsoron sa a raina bare tsoron auren sa,
Sai dai har yanzu ina nan ina fama da ƙaiƙayin gaba da na kasa faɗa ma kowa, abun sai gaba yake yi, Ni dai na san bani da lafiya yanda komai nawa ya sauya, in ta jin kumburi a saman marata, ga fitan farin ruwa mai wari da ya soma damuna, ko fitsari zan yi yanzu ba ya fita gaba ɗaya, na dinga sintiri kenan a bayi ina yin guntun fitsari, yanzu zan shiga anjima kuma sai in koma,
Hakan har ya soma jawo hankalin su Inna Lami kaina, don yawan shiga na bayin yasa suke yawan min faɗan, "wai uban mai ke kaini bayi kodayaushe? A rana sai in zagaya sau goma sai ka ce mai cuta?"
Tun suna min maganar dai har sun gaji sun sanya min idanu tunda ban fasa ba, da zaran na je nayi fitsarin ina dawowa zan sake jin marata ta cika kamar wani fitsarin ya taru, ga yawan soshe-soshe ba na iya haƙura ko a gaban waye haka zan ta soshe-soshen gabana

Dalilin da yasa Inna Lami tace, "abun nawa yayi yawa tana ga kamar sanyi ne ya kama Ni, dole a nema min magani kafin biki ya zo, don idan ba haka ba zan jawo musu matsala ne kawai."

Tun daga ranan aka soma banka min magungunan sanyi domin suna kyautata zaton ciwon sanyi ne ya kama Ni, kuma hakan ne tunda duk alamomin sa ya bayyana a tare da Ni, Ni ban san cutan ba; amma tunda na ga an soma bani magani na tabbatar da babban ciwo ne, don ita kanta Yaya Haula sai da ta zauna ta dinga min faɗa a kan rashin tsafta ko maimaita wando ɗaya,
Itama ta kawo min magungunan da take sha tace, "in haɗa in riƙa sha."
To kwana biyu abun yayi sauƙi tunda Ni kaina ina ƙoƙarin ɓoye soshe-soshen nan da nake yi, abun yana bani kunya, sosai nake daure wa abun na damuna wlh,
Daga an zauna sai a yi tayi dani sabida wannan ciwon da ya same Ni, babu wanda bai sani ba a gidan, sai ya zamana kuma kamar sun soma jin ƙyama na, ko bayi na shiga har gargaɗi su Inna Asabe suke yi wa su Fatima a kan, "kar su soma su zuƙuna a inda na zuƙuna, don zasu iya kwasa, wannan cutan ba abun so bane, itama Madinan Allah ya yaye mata."
Ko kayan sawa na babu mai taɓa min, daga an yi magana su ce, "kar su kamu da cutan sanyi."

Na soma shiga tashin hankali don da gaske mugun ciwo ne a tare da Ni, tunda ga shi na soma zama mujiya a gidan mu, komai a ce ina da cutan sanyi, abu kaɗan a soma maganar,
Shiyasa lokaci ɗaya na firgice bani da sana'a sai kuka,
Ganin abun yayi yawa sai na saci jiki na je na faɗa wa Yaya Haula halin da nake ciki

Ita kanta hankalinta ya tashi, amma sai ta soma rarrashina tana faɗa min, "ba mugun cuta bane kamar yanda kika ɗauka, kawai dai ana saurin kwasa ne a jikin Mutum shiyasa kika ga suna miki haka, kuma ai kina shan maganin ki da sannu za ki warke kar ki damu kowacce Mace tana dashi, na wasu ya fi na wasu ne."

Hankalina bai kwanta da maganar nata ba, taya ya zata ce min kowacce Mace tana dashi kuma ake guduna? Sai nace, "Yaya Haula to meyasa Ni kaɗai ce nake soshe-soshe ga shi har an soma guduna? Kenan kuma kuna dashi amma ba a gudun ku sai Ni?"

"Kinga Madina, baza ki gane irin wannan cutan ba koda nayi miki bayani, Ummanmu ta taɓa min bayanin kawai cuta ne da yawanci ƙazanta ne ke kawo ta sai kuma cushe-cushe da wasu Matan ke yi na maganin Mata, wasu kuma suna kwasa ne idan wasu suka yi fitsari a wuri suma suka yi a wurin, kin san nan ƙauye ne basu fahimci kalan cutan ba shiyasa suke miki haka, amma in kika bibiya duk ƴan gidan mu suna yi naki ne kawai ya fito fili, cutan kala-kala ne kowa da kalan nasa, ke naki kalan ta kenan amma in kika ci gaba da shan magani a hankali za ki warke, ko ba ki ga maganin da na kawo miki bane? To ai muma muna shan shi ne da Anti Hadiza, muna jiƙa wa muna sha ne tunda muma muna fama dashi, don haka ki dena damuwa kin ji ko?"

Kai na gyaɗa mata duk da har yanzu ban gamsu ba sabida ban gama gane abun da take nufi ba, amma na ji sanyi a raina kasancewar cutan ba Ni kaɗai ce da ita ba, ashe kowa yana dashi, sai dai na wani ya fi na wani ne kamar yanda Yaya Haula ta faɗa min, kuma na yarda cewa rashin shan magani da wuri ne ya jawo cutan tayi ƙarfi a jikina, tunda tun farko da na san haka ne da na soma jin alamomin ta; da na faɗa mata an nema min magani,
Shiyasa tun daga ranan na dage da shan magungunan da ake haɗa min ba na wasa da su,
Idan ya ƙare da kaina nake zuwa gidan Jummai mai magani in amso in jiƙa in ta sha,
A hankali kuma abun ya soma min sauƙi, ƙaiƙayin da nake fama dashi da ziryan shiga bayi ya rage sosai, kuma Ni kaina na canza iya gwargwado ina ɗan yin tsafta, tunda kusan kullum ina yin wanka ba kamar a baya ba; wanda sai in yi sati jikina bai ga ruwa ba,
sai lokacin hankalina ya kwanta na ci gaba da gudanar da rayuwata hankali kwance

A wannan lokacin ne aka soma shirye-shiryen bikin mu,
Tun ana kwana biyu ƴan uwa suka soma zuwa, yayyinmu da suke nesa da ƙauyen mu duk sun soma hallara,
Babban yarinyar Baban Sasa ta soma zuwa. Hajja Jamma, tare da zugan ƴaƴanta da ta kwaso, yanzu haka ta aurar da Yara uku biyu mata namiji ɗaya,
Ita ce ƴa ta farko a wurin Inna Lami, sai Yaya Yunus wanda yake bin ta, amma shi dayake ya daɗe bai yi aure ba sabida yawon cirani da ya tafi cikin birni can garin Lagos, ya daɗe a can yana yawon gararanba na neman kuɗi, daga bisani kuma ya dawo nan Zaria tunda neman kudin ya gagara a can,
A nan cikin Zaria ya samu wani uban gida da ya dauke sa aiki yana masa gadin gida, sanadin da yarinyar gidan ta gansa mai suna Sharhabila, tunda Yaya Yunus ya zo gidan ta ɗaura ido a kansa ta ji tana matuƙar ƙaunarsa, bare ta gansa kyakykyawa jinin Fulani fari tass, shiyasa ta soma shige masa tana nuna masa irin ƙaunar da take mishi,
Shi kuma Yaya Yunus gani yake yi ya tsinci dami a kala haka ya amince mata yana soyayya da ita, sun shaƙu sosai duk abun da take so shi yake so,
Sharhabila ita kaɗai ce wurin Iyayenta kuma suna ƙaunarta, koda ta nuna musu tana son Yaya Yunus basu musa mata ba, sai dai mahaifinta ya nuna masa, "dole sai ya tashi tsaye yayi karatu ya nemi aikin kansa sabida ya mallaki ƴarsa, don bazai bama mara ilmi da galihu ƴarsa ba, in ya shirya zai biya masa kudi ya ɗaura karatun sa."

Sanadin da Yaya Yunus ya koma karatu kenan, dama a lokacin ko primary bai yi ba, karatun allo kawai yayi, shi ne ya koma makaranta da taimakon mahaifin Sharhabila, kuma suka ci gaba da soyayyarsu babu wata matsala,
Dalilin da yasa Yaya Yunus ya jima bai yi aure ba kenan, don lokacin har Ƙaninsa Yaya Nasiru ya ajiye Mata da nasa ƴaƴan,
Yawanci Yaran Baban Sasa duk an aurar da su Maza da Mata, amma shi Yaya Yunus ya bi ra'ayin Mahaifin Sharhabila yana jiran har sai ya ba shi auren ƴarsa,
Tun abun yana damun su Baban Sasa don lokacin basu ɗauki karatu a bakin komai ba, hatta Mazan ba sa karatun boko a zamanin, amma sai ga shi Yaya Yunus ya fita zakka a cikin su, ya je birni yayi zaman sa a can yana karatu, sai ya jima ma kafin su ganshi a ƙauyen, lokaci ɗaya ya sauya musu zuwan ma sai ya ɗauki tsawon lokaci, har manta wa suke yi dashi, tun Baban Sasa yana ɗaukar fushi dashi har suka haƙura suka tsaya su ga iya gudun ruwan sa, ga shi sun yi masa Mata a ƙauyen amma ya buɗe musu ido yace, "bazai auri kowa ba sai Sharhabila, kawai suyi haƙuri."
Tun a nan suka san cewa Yaya Yunus ya canza ɗabi'u ba ya jin maganar su,
Haka suka fita harkanshi suka zura mishi ido tunda ya dena zuwa wurin su gaba ɗaya

A lokacin da ya gama secondary school ɗin sa, itama kuma Sharhabila ta gama karatun ta na NCE, sai lokacin Abbanta ya amince ya turo magabatan sa,
Haka Yaya Yunus ya dawo ya sanar da Iyayenmu,
Amma sai Baban Sasa yace, "in har shine bazai nema mishi auren yarinyar nan ba, don ba yanda za a yi kamar sa ya auri Mace irin wannan, wacce ta fi shi komai daga ƙarshe sai dai ta juya shi, in har bai bi zaɓin su ba baza su taɓa zuwa su nema mishi auren ta ba."
Duk yanda su Baffa suka so su tausasa Baban Sasa amma ya ƙeƙashe, yace, "bai yafe ma wanda ya shiga gaba ya nema masa auren yarinyar ba."

Shi kuma Yaya Yunus sai ya koma ya sanar da Abban Sharhabila, sabida ganin ƴarsa tana son Yaya Yunus shi kuma ya goya masa baya da kansa ya aura mishi ƴar shi, sannan ya ba shi gidan da zasu zauna a nan cikin Zaria, ya kuma nema mishi aiki a ƙarƙashin sa, sannan ya ba shi dama ya ci gaba da karatun sa,
Yanzu haka Yaya Yunus ya gama karatun sa na degree, shi kaɗai ne ya fita Zakka a danginmu, shi kaɗai ne yayi karatu ya zama ɗan birni,
Domin Ni kaina ada ban taɓa tunanin shi ɗan uwanmu bane, sai dai kawai kamanni da muke yi dashi wanda kana kallonsa ka san jinin mu ne,
An ja lokaci mai tsawo tun kafin a haife mu har muka girma bamu taɓa ganin sa ba,
Sai rasuwar Babanmu da ya zo gaisuwa tare da Matarsa da ya'yansa biyu dukka Maza da ya haifa,
Wannan zuwan ne yasa da yawa ƴaƴan gidan mu muka san Yaya Yunus,
Kuma ya zo da abun mamaki tunda a lokacin yayi kuɗi sosai, ga matarsa ƴar gayu da Yaransa sai zuwa kallonsu ake yi

Ya sha faɗa a lokacin don kusan tsine mishi Baban Sasa ya so yi a wannan zuwan,
An yi tashin hankali sosai ɗakyar aka shawo kan Baban Sasa ya yafe masa,
Sai da Yaya Yunus ɗin yayi ta ba shi hakuri sannan yayi masa alkwarin, "daga yanzu zai riƙa zuwa akai-akai yana duba su."
Don ma ya yarda da maganar sa har siyan fili yayi a cikin anguwan namu, babu nisa da gidan mu da filin nasa, yanzu haka har an gina masa gidan ginin zamani flat, tunda aka yi ginin sau ɗaya ya zo ya duba ya koma, basu taɓa zama a gidan ba amma duk an zuba komai na buƙata a gidan,
Sai wannan bikin namu da za a yi sai ga su sun dira, domin babu wanda yayi tunanin ganin su sai ga su tsalam,
Hajja Jamma ta zo da safe, sai ga su Yaya Yunus kuma da yamma,
Nan fa gida ya cika da murnan mutanen birni aka rasa inda za a saka su don tsaban farin cikin ganin su

Dukkan su a dakin Inna Lami suka sauka mutane sai tururuwan zuwa gaishe su suke yi,
Sai da aka natsa da jama'a sannan su Yaya Yunus suka wuce sashin Baban Sasa suka gaishe shi

Shi kansa yayi murnan ganin su baki har kunne, sai kallon jikokin nasa yake yi gunun sha'awa, ya rungume su yana shafa kawunan su yana musu tambayoyi?
Jima wa kaɗan kuma sauran iyayenmu Maza suka dinga shigowa ana gaisa wa,
Daga ƙarshe Yaya Yunus kaɗai ya zauna tare da yaran,
Ita kuma Sharhabila ta koma sashin mu

Duk da yanda Yaya Yunus ya ba kowa sha'awa a cikin dangi, dashi da ilayansa, amma hakan bai sa su Baban Sasa sun ji suna son Yaransu suyi karatun Boko ba, domin akwai gaba mai tsanani tsakanin su da karatun Boko, har yanzu kansu ya kasa wayewa a kan zuwan karatun zamanin, sun ƙi yarda dashi, suna ganin kamar hanya ce ta gurɓacewar ƴaƴan su, misali ga shi a kan Yaya Yunus, karatun ajami shi suka fi dogara dashi, sauyawan Yaya Yunus bai sa zuciyoyinsu ta sauko ba, kuma baza su taɓa yarda wani daga cikin Yaransu ya ƙara ƙetare maganar su kamar Yaya Yunus ba, daga kanshi babu ƙari, don shi kaɗai ne zai fita Zakka a cikin su, sabida ganin sa suke yi ya gagare su.
***

Har dare su Yaya Yunus suna gidan mu; tunda basu wuce sabon gidan su ba, duk da an share an gyara musu komai kasancewar yayi ƙura, su Yusuf aka sanya suka je suka gyara suka tsabtace,
Sai bayan sallan isha'i sannan suka wuce gidan nasu

Washe gari kuma sauran ƴan uwa suka ci gaba da zuwa gida sai ƙara bunƙasa yake yi,
Tun ranan farko da muka ga Matar Yaya Yunus bamu sake ganin ta ba har ranan bikin, domin ba ta zuwa sai dai Yaya Yunus ya zo da Yaran,
Sai a ranan bikin ne ta zo ta ci kwalliya sai ficchi take yi da iyayi, dama Matar akwai yanga, ga shi daga gani tana ƙyanƙyamin mu don ko magana wannan sai ta ga damar yi, duk wannan wulaƙancin amma haka zaka ga ƴan uwa suna ta shige mata, abun ka da ƴan ƙauye mutanen karkara basu saba ganin ƴar birni kamar ta ba,
tunda ta zo gidan yau ta shige cikin dakin Inna Lami ko fita ta ƙi yi, sai faman latsa babban wayanta take yi tana taunan chewing gum, duk wanda ya zo sai dai ya gaishe ta ita kuma ta amsa a gadarance, ga yaranta akwai shegen ƙyuya basu yarda da kowa ba,
To dama idan mutum yana da kuɗi ba a ganin laifin sa, gani suke yi don ita ƴar birni ce rayuwarta ta fita daban da nasu shiyasa halayyarta ma daban ne

A wannan lokacin mu kuwa muna can sashin Baba Sama'ila a can muke taronmu mu Amare, Kowa hankalin sa a kwance ban dani, na kasa kwantar da hankalina sabida yau ne ranan da zamu bar gidanmu mu je mu rayu a gidajen mu, shikenan an raba mu da ƴan uwanmu muma zamu je mu yi rayuwa a gidajen Mazajen mu, har kuka sai da nayi Yaya Haula ce kaɗai take rarrashina, abun ya haɗe min biyu sabida rashin ganin Ummanmu, shiyasa hankalina ya kasa kwanciya sai kuka nake yi ina cewa, "ta kira min Umma ta zo."

Amma har aka gama taron nan babu Umma ba labarin ta, tun Yaya Haula tana faɗa min, "zata zo zata zo."
Har na cire rai tunda ga shi har Magriba ta gabato za a tafi damu,
Har lokacin ban dena kuka ba haka aka wuce damu sashin Baban Sasa, a nan dukka aka yi mana faɗa sannan aka raba waɗanda zasu kaimu ɗakunan mu

Dama Binta da Fa'iza yayyinmu suka aura,
Fa'iza ita ta auri Yaya Ahmadi,
Ita kuma Binta ta auri Yaya Shamsu,
Kuma duk a gidan zasu zauna ɓarayin Samarin gidan, dama duk wanda zai yi aure in dai namiji ne a gidan yake yankan fili yayi auren sa tunda gidan babba ne, kowa yana da gadon sa a gidan, yanzu haka ƙofofi uku ne a gidanmu saboda girman gidan, ta asalin babban ƙofan gidan; ta nan ne sashin su Baban Sasa da su Baffa

Yaya Haula da Matar Yaya Nasir; da kuma Matar Baffonmu Abdullahi suka kaini gidan Alh. Badamasi,
Gidan madaidaici ne mai kyau, ya sha penti an gyara ko'ina kamar ba ƙauye ba,
Sashin Alh. Badamasi mu haɗu a falo ne, ga ɗakina ga ɗakin Matarsa haka gidan yake,
Sai kuma idan an zagaya ta baya a nan surakansa suke Yaransa biyu Maza da suka yi aure, amma ƙofan su daban ne; sai dai suna iya shigowa gidan tunda a haɗe yake,
Yara uku ya aurar, Mace ɗaya tana gaban kauyen mu a can tayi aure,
Sai sauran huɗun Yaran da yake dasu, Matasa ne sun girma domin babu sa'ana a ciki; sai Autar su Mace wacce yanzu bata fi shekaru takwas ba

Yau dai ga shi ina ji ina gani su Yaya Haula sun kawo Ni ɗakina sun tafi sun bar Ni, ina kuka da majinu amma babu damar bin su, tunda a ƙauyen abun kunya ne a ce Amarya ta gudo dakin Mijinta sabida tsoro, idan hakan ta faru ba ƙaramin wulaƙanta da muzanta take yi ba, kuma zai zama tarihi har ya'ya da jikoki sai ana yi da ita ana faɗan abun kunyar da tayi.
[25/06, 10:00 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎

_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 10*
_____An tafi an bar Ni cikin zallumi da tunanin abun da zai biyo baya, jikina sai rawa yake yi ina zaune a saman gadona nayi shiru cike da tsoro, babu wanda ya leƙo ɗakina tun tafiyan su Yaya Haula, tsoro da rashin sabo yasa na takura kaina wuri ɗaya, na rufe jikina gaba ɗaya da hijabina ina ta tunanuka a cikin raina, hawaye kaɗai suke iya zuba a fuskana don babu ƙarfin yin kukan bare in yi; sabida tashin hankali da tsoron da ke tattare dani,
Jimawa kaɗan sai na ji ana ƙoƙarin shigowa,
Hakan ne yasa na ƙara takurewa a can karshen gadon, ban iya ɗago kaina ba bare in san wane ne,
Sai da na ji muryan Alh. Badamasi sannan hankalina ya kwanta, duk da sai fama da faɗuwar gaba nake yi, zuciyata tana bugawa kamar zata faso ƙirjina, na san bazai wuce rashin sabo da kuma tsoro ba, ga kewan su Yaya Haula da nake ji tun ba a je ko'ina ba,
Hakan yasa hawayen da ke fita daga idanuwana suka ƙara yawan ɓulɓulowa,
Na kasa amsawa Alh. Badamasi da ke faman kirana; wanda ya ƙariso bakin gadon ga dukkan alamu yana mai cike da farin ciki, koda jin yanda sautin muryansa take fita cikin walwala da annashuwa

"Amaryata taso mana, ko kin yi barci ne?"
Ya sake yin maganar yana ƙoƙarin janye min hijabin da na rufe jikina dashi

Jikina sai faman rawa yake yi na ƙi na ɗago; illa ƙara rufe idona da nayi na kasa ƙwaƙƙwaran motsi

"Taso mana Madina, maza sauko a kan gadon ki zo ga tsire na siyo miki ki ci, sai ki kwanta kinji ko?"
Yayi maganar cikin lallami yana sake ɗaura hannunsa a kaina

Ni kuma sai lokacin nayi ƙoƙarin fito da kaina tare da buɗe fuskata ina kallonsa; a cikin hasken tocilan da ya ajiye a saman drowan gadon

Ganin nayi sharkaf da hawaye sai hankalinsa ya tashi, cike da rarrashi

Please Login or Register in order to submit comment