Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda zan yi, bazan iya tsira ba. A haka na kwana a cikin zullumi, ko in ce muka kwana dukkan mu, barci na ragagge ne a wannan ranan da nayi; cike da tsoro da zullumin zuwan goben.



_Labarin zai zo muku a duk sati sau uku a rana ne, every Juma'a; Saturday and Sunday, please babu ƙorafin hakan don Allah. Waɗanda suke son magana dani kai tsaye a WhatsApp zasu same Ni a kan wannan numban 07065334256. Nagode Masoyana._
[09/06, 5:55 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
   *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎

_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
   _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 2*
_____Washe gari Yaya Haula ta sanar da Mijinta saƙon Baban Sasa, ta CE mishi, "zata je ta sanar da Umman su." Shiyasa ya barta ta tafi kusan ƙarfe goma na safe, tafiyar awa ɗaya da rabi ne ya kaita cikin Zaria anguwan da Umman su take Aure

Dayake yau Asabar ne tana gida ita da yaranta, Mijinta ne kawai ya fita ƙwadugon sa da ya saba, ba wani me shi bane tunda kullum sai ya fita sannan zai samu wanda zasu ci a rana, shiyasa Umman namu take aikatau a wani gida da ke kusa da su, Matar tsohuwa ce sai jikokin ta da take zaune da su, shiyasa aka sama mata me aiki tana rage mata wasu abubuwa, to a nan ne su Umman mu suke samun na rufawa kansu asiri, ga Yaranta Hassana da Hussaina da ta haifa sun girma sosai, domin yanzu shekarun su kusan bakwai ne, tunda tun sanda Baban mu ya rasu ta koma ƙauyen su, sai tayi aure babu jimawa, to daga kan su Hassanan ne bata sake haihuwa ba duk da tayi ɓarin wasu ƴan biyun

Umman mu tayi mamakin ganin Yaya Haula da safen nan, shiyasa ko zama bata yi ba ta soma tambayar ta hankalin ta duk a tashe saboda gani take yi kamar babu lafiya, musamman yadda ta ga fuskar Yaya Haulan ta koma

Yaya Haula bata ce komai ba sai da ta zauna sannan ta gaishe ta, ƴan biyu ma suka gaishe ta; ta amsa su tana musu murmushi

Sai Umma ta cewa Hassana, "ta tashi ta ɗauko mata kofi ta zuba wa Yayar su koko."

Hakan yasa Hassanan ta miƙe ta je ta ɗauko ta kawo

Umma ta amsa ta zuba mata, ta tura mata da raguwar ƙosan da ke gabanta tace, "ga shi ki ci, sauko min takwaran tawa."

Babu musu ta kwanto goyon Ihsan ta miƙa mata, yarinyar sai Barci take yi tunda bata da aiki sai barci

Umma bayan ta amshe ta ta ɗaurata a jikinta tana kallon fuskarta, tare da kai hannu tana cire mata kwantsan da ke idanunta ɗaya; kana ta kalli Yaya Haula tana cewa, "kina mata amfani da maganin dana ba ki?"

"Eh Umma har ma ya ƙare, jikin nata da sauƙi yanzu ai." Ta bata amsa tana tura ƙosan a bakinta tare da korawa da kokon; tunda dama ba kari mai kyau tayi ba, Mijinta shima be dashi sai ya fita yake nemo wa, kullum a cikin ɗame-ɗame suke ga shi ita tana shayarwa, shiyasa yanzu ɗin ta shanye kokan tass tana siɗe baki

Sannan Umma ta kalle ta tana cewa, "ina jinki meke faruwa ne? Hankalina ya kasa kwanciya duk yanda aka yi ba lafiya ba?"

Ajiyan zuciya Yaya Haulan ta saki, kana damuwarta ta dawo sabo, a nan ta sanar da Umman duk abun da ke faruwa

Shiru Umma tayi sabida yanda maganar ta bige ta ainun; yayinda idan hankalin ta yayi dubu to ya tashi a wannan lokacin

"Ni Umma ba wai yin kaciyar bane yake damu na, Madina yarinya ce duk su Binta sun girme ta, ita ce ƙarama memakon su barta sai wata shekaran amma sun CE da ita za'a yi, Umma ki duba yanda na sha wahala a lokacin da aka yi min; idan har aka yiwa Madina yanzu bamu san wani hali zata shiga ba, don Allah Umma ki je ki roƙe su a dakata ko zuwa nan gaba sai ayi mata, Madina yarinya ce."

Umma tace, "to Haula ya zan yi wannan abun ya fi ƙarfi na, amma ban ji daɗi ba; ba ki ji yadda zuciyata take zafi ba hankalina duk ya tashi, wannan al'adan kwata-kwata be da tsari, da ace ina da fawan da zan ɗauko ɗiyata ta dawo hannu na da na jima da yi tunda na san dole zasu yi mata wannan kaciyar, sai dai na san baza su taɓa yarda ba, insha Allahu Allah bazai basu dama ba dole ne zan je in Yi musu magana tunda ina da haƙƙi a kanta." Sai ta kalli su Hassana da ke zaune suna ta shan kokan su tace, "ku tashi idan kun gama ku je gidan Asabe ku zauna, idan lokacin Islamiyar ku tayi sai ku wuce; Ni zan tafi anguwa."

"To Umma." Suka amsa mata suna miƙewa tunda sun gama abun da suke yi

Ita kuma sai ta miƙa wa Haula Ihsan ɗin ta miƙe tana cewa, "bari ta ƙarisa aikin ta." Da haka ta fice daga ɗakin

Itama Haulan miƙewa tayi ta shimfiɗa Ihsan ɗin sannan ta fita ta taya ta aikin, dama shara ne kawai da wanke-wanke, suna gamawa Umman ta saka kaya da hijabi suka fito gidan, sai a waya ta sanar da Mijin nata, kuma bae hana ta ba sai fatan alkhairi da yayi mata. Kai tsaye gidan da take aiki suka nufa sabida tana son ta faɗa musu, "baza ta samu shigowa yau ba." kar Matar ta ji ta shiru

Suna shiga kuwa suka cid da tsohuwar Matar a katafaren falon ta, duk da ta manyanta sosai amma kana kallon ta zaka san ƴar kwalliya ce, domin har yanzu gayu take yi babu ruwanta da tsufan da tayi, hannayen ta dukka sun sha jan lalli da aka yi mata hannu da ƙafa ya ɗauki farar fatanta sosai, sai sarƙa da awarwaro da ta zuba su na gwal sai walwali suke yi, duk da fuskarta babu kwalliya amma ta sha kwalli da Powder tayi kyau ainun, tana zaune a kan sofa tana kallon labarai a t.v, ta amsa musu sallaman cikin fara'an ta tana cewa, "yanzu nake tunanin lafiya ban ji ki ba? Shiyasa nake tunanin in aika a duba min ke."

Murmushi Umma tayi tana zama a ƙasa tare da cewa, "wlh kuwa Hajiya, baƙuwa nayi ƴata ta zo daga ƙauye, shi ne zamu je can saboda wata matsala, abun da yasa ban zo ba kenan kuma kar in tafi ban sanar miki ba shi ne na shigo. Ina kwana Hajiyam?" Ta ƙare maganar tana gaishe ta

"Lafiya lau, wlh babu komai, nima fita zan yi ai."

Haula wacce ta zuƙuna itama a ƙasa ta gaishe ta cikin girmamawa

Hajiya Ummee ta amsa mata cike da fara'a tana cewa, "yanzu Asiya wannan yarinyar ƴarki ce?"

"Eh wlh Hajiya, ita ce babban ƴata sai ƙanwarta."

"Masha Allah sannun ki, ya sunan ki?" Hajiya Ummee ta tambaya cikin fara'a tana kallon Haulan

Itama Murmushi tayi cikin girmamawa tace, "suna na Haula."

"Masha Allah! suna mai daɗi." Sai kuma ta kalli Umman tana cewa, "yanzu ki je kichen ki haɗo muku Breakfast sai ku ci kafin ku tafi."

"Wlh a'a Hajiya sauri muke yi, kuma mun ci abinci yanzu kafin mu fito."

A lokacin ne Ihsan ta tashi ta soma kuka

Hakan yasa cike da mamaki Hajiyan tace, "wai da goyo ne a bayan ta dama?"

"Eh, ɗiyarta ce." Umma ta bata amsa

"Ikon Allah! Ɗiyarta?" Inji Hajiyan tana sake cika da mamaki yayinda take kallon Haulan, "yanzu Asiya kina nufin yarinyar nan tana da aure ne?"

Murmushi Umma tayi tace, "eh Hajiya, ga ta nan har da ƴarta takwarata."

Hajiya Ummee ta cika da al'ajabin da ya kasa ɓoyuwa a kan kyakykyawar fauskarta, sai ta cewa Haulan, "ta sauko yarinyar ta bata." Hakan yasa ta sauko ta ta miƙa mata, sosai yarinyar ta bata sha'awa tana faɗin, "Masha Allah yarinya tubarakalla. Amma taya ya zaku yiwa yarinya kamar wannan aure Asiya? Wannan ai ganganci ne; kamar wannan fa?" Ta sake maganar tana nuna Haula da a yanzu ta koma ta zauna tana kallon Hajiyan cike da burgewa

Ita dai Umma murmushi kawai take yi bata ce komai ba

A lokacin ne wani kyakykyawar farin saurayi yayi sallama ya shigo cikin falon; yana riƙe da farar riga lab coat a hannun sa, yayinda idanuwansa suke sanye a cikin farin medical glass da ya haskaka mishi idanun suka ƙara yin kyau ainun, jikinsa sanye da ƙananan kaya riga da wando sun mishi kyau, kansa kuma babu hula sai kwantaccen gashin kansa me haɗe da yalwataccen sajen sa tare da ɗan guntun gemun sa, kana kallon sa zaka ga kamalan sa da kwarjinin sa a fuska

Duk amsa mishi sallaman suka yi, inda Hajiya Ummee take cewa, "Ah ah! Mashkur ka dawo ne kuma?"

Sai da ya samu wuri ya zauna kafin ya bata amsa yana cewa, "eh. Already na gama abun da na je yi." Daga nan sai ya mayar da hankalinsa a kan Umma yana gaishe ta

Ta amsa a cikin sakin fuska tana tambayar shi aikin nashi?

Yace, "alhmadulillah."

Itama Haula gaishe shi tayi

Sai ya ɗago yana kallonta, kana ya amsa ta a hankali yana ɗauke kai a kanta; ya mayar a kan yarinyar da ke hannun Hajiya Ummee, "yarinyar wace ce?" Ya tambaya yana ci gaba da tsira mata idanu

"Yarinyar Haula ce ɗiyar Asiya, ga ta nan zaune ai."

Hakan ne yasa ya sake ɗaga kai yana kallon Haulan; yayinda mamaki kwance a kan kamilalliyar fuskarsa na jin cewa wannan figaggiyar yarinyar; tsamurarriya; ita ce Maman jaririyar nan, ikon Allah! domin abin mamaki ya ba shi, saboda gani yake yi ai baza ta wuce shekaru 14 ba amma har da ɗiya? sai dai bai ce komai ba saboda shi ba mai yawan magana bane

Inda ita Hajiyan tace, "Mashkur akwai kuɗi a hannun ka; ka bani zan ba wa Asiya ne?"

"Eh akwai." Ya furta yana saka hannu cikin aljihun wandon sa tare da zaro kuɗin, bai ma san ko nawa bane ya miƙa mata

Itama sai ta amsa ta miƙawa Umma gaba ɗaya tana cewa, "to ga shi sai ku rage kuɗin mota, sauran sai ki ba wa Haula, Allah ya kiyaye hanya, nima fita zan yi kuma zamu kai yamma kafin mu dawo, sai Allah ya kaimu gobe sai ki zo; yau dai ki huta da aikin nan."

Sosai Umma tayi godiya, daga ita har Haula, sannan Hajiyan ta miƙa mata Ihsan ɗin ta goya ta, daga nan suka yi musu sallama suka fice.




             Kai tsaye keke napep suka yi drop ya nufi da su ƙauyen. Bayan sun kai suka wuce babban gidan su, koda suka shiga Yara suna hangen Umma suka soma mata Oyoyo suna cewa, "ga Umman su Madina, ga Umman su Madina."

A lokacin ina cikin ɗakin mu naji abun da suke faɗa, ai da gudu na fito domin gasgata abun da suke faɗa, ilai kuwa Ummata ne tare da Yaya Haula da suka shigo sasan a yanzu, da gudu na nufe ta ina kiran sunan ta, na rungume ta cikin tsantsan murna da farin cikin ganin ta; domin ba ƙaramin murna ne ya kama Ni ba sabida rabo na da ita tun bikin Yaya Haula

Murmushi ita kuma take yi tana shafa min kai tare da cewa, "kar ki ka dani mana Madina."

Ni kuwa sai dariya nake yi murna ta kasa ɓoyuwa a kan fuskata, nace, "Umma sannu da zuwa."

"Yauwa Madina." Umman ta amsa tana kuma mayar da hankalinta a kan Yaran da suke mata sannu, su ma tana amsa musu

A lokacin ne Inna Lami ta fito daga ɗaki tana ɗaura ɗankwali a kanta; tare da cewa, "wa nake ji kamar Asiya a gidan namu?"

"Ni ce wlh Yaya. Ina wuni?" Umma tafaɗa cikin yalwata fuskarta da fara'a sosai

"Lafiya lau, maraba da zuwa, ke Madina ɗauko mata tabarma mana kin barta a tsaye."

Da gudu na shiga ɗakin Inna Lamin na ɗauko tabarma, ta amsa ta shimfiɗa mata sannan Umma ta zauna itama ta zauna, a lokacin sauran Matan Baban Sasa suka fito su ma suna cewa, "Ah ah Asiya ce a gidann namu?"

"Wlh Ni ce."

Daga haka aka soma gaisawa cikin mutunta juna tunda an yi zaman lafiya tare, aka kawo wa Umma ruwa ta sha. Sun ɗan taɓa hira kaɗan ana ta raha daga nan ne ta miƙe ta wuce sauran sasan suma aka gaisa, sai ta wuce ita kaɗai sashin Baban Sasa, ta same shi yana kwance a falon shi, ya kishingiɗa yana fifita kasancewar babu wuta, ta shiga da sallama ya amsa mata yana miƙewa zaune tare da kallon ta

"Asiya ce?"

"Eh Yaya." Ta furta tana zama a ƙasan tare da gaishe shi cikin girmamawa

Ya amsa ta shima cikin kulawa yana tambayar ta iyalan nata?

"Alhamdulillah suna nan lafiya."

"To Haulatu har ta sanar miki da saƙon namu kenan?"

"Eh yau ta je gidana ta sanar min, shiyasa na taho sabida in roƙi alfarma."

Gyara zamansa yayi yana mayar da idanunsa a kanta tare da cewa, "to fa! Wanne alfarma kenan Asiya?"

Shiru ta ɗan yi ita kuma, kana kuma ta buɗe baki tare da cewa, "a kan maganar Madina ce da za'a yiwa kaciyar nan Yaya, Madina yarinya ce bata kai shekarun da ake yiwa sauran ba, shiyasa nace idan da hali a barta zuwa wata shekaran kamar yanda lokacin ne ta cika shekarun da za'a yi mata, don Allah a duba maganata Yaya."

Ɗan jimm. Baban Sasa yayi kana kuma yace, "mu ma mun yi wannan tunanin Asiya tun kafin kiyi, amma abun lura a nan dole ne fa za'a yiwa yarinyar nan al'adan nan tunda babu wanda zai tsallake ta, mu kuma muna ganin sauƙin hakan ne shiyasa muka yanke wannan shawaran, ba ki fi mu sanin me muke yi ba babu abun da zai samu Madina don wai bata kai shekarun sauran ba, ko a baya da muke gudanar da al'adar nan daga shekaru 5 ne zuwa 6, amma yanzu ita takai shekaru goma a lissafina, kinga kuwa tayi girman da itama za'a iya mata, duk a gidan nan babu kuma wani sa'anta da za'a haɗa su wata shekaran ayi musu, sauran duk Yara ne, to, a ganin mu da mu sake jira wata shekaran ayi mata da wasu tsirarun ƴan ƙauyen gwara a haɗa su gaba ɗaya ayi musu yanzu; tunda mun duba duk basu da yawa, Ni abun da yasa nace a sanar miki sabida ki sani ne kar a shiga haƙƙin ki a matsayin ki na Uwarta, amma ba shawaran ki muke so ba."

Umma da ke faman share hawaye tun soma maganar sa, kasa ɗagowa tayi da kanta sai da yace mata, "zata iya tafiya tunda shi ya gama magana." Sai ta ɗago tana roƙon shi cikin magiya tana sake jaddada mishi, "Madina yarinya ce a barta ta sake girma, tana gudun abun da zai biyo baya kar su kashe mata yarinya."

Ran Baban Sasa ya soma ɓaci, shiyasa ya buɗe baki a zafafe yace, "ke Asiya ba ma son maganar banza da hofi a nan, ita kanta farau ne da za ki ce wani abun zai same ta? Tun yaushe ake wannan al'adar babu wani abu da ya taɓa samun jama'a sai a kanta? Idan ba'a yi mata ba taya zata cika Mace a martaba ta a duniya? Ba na son zancen banza tun kafin raina ya ɓaci muyi rabuwar ɓatacciya ki ɓace min a gaba na." Sai ya ja dogon tsaki yana mayar da jiki ya sake kishingiɗa tare da kuma mitan cewa, "idan ba shirme ba; Ni ne za ki zo gabana kina gaya min abun da yakamata? ita ƴar uwanta da aka yi mata uban me ya same ta? Al'adan mu ne babu wanda ya isa ya hana ta."

Umma miƙewa tayi itama ranta a ɓace, sai dai ta kasa tsayar da hawayen nata sai kwaranya suke yi, sai da ta fita sannan ta share hawayen gudun kar a gani, amma ana kallonta za'a gane tayi kuka, baza ta iya tsayawa tana kallo a yiwa ɗiyarta kaciya ba, kamar Madina, wannan ai zalunci ne, ko a sanda aka yiwa Haula bata da yanda zata yi ne, bata ma san an yi ba sai daga baya, sannan bata manta wahalar da Haula ta sha ba a kan wannan kaciyar, Allah ne ya taƙaita wahala sai da tayi ta zuwar mata da magani tana bata daƙyar ta samu sauƙi, domin su sun ƙi kaita asibiti a duba ta sai jiƙe-jiƙe da ake bata, kuma sun hana ta ta ɗauke ta ta kaita tunda basu yarda da asibiti ba sai magungunan gargajiya, dole ta riƙa zuwa da maganin a ɓoye na asibiti tana bata har aka samu ta samu sauƙi, sai ga shi yanzu za'a kuma a kan Madina wacce bata kai shekarun su ba ma, wannan mugunta har ina? Baza ta iya tsayawa ta gani ba. Shiyasa tana shiga sashin su Inna Lami tace musu, "ita zata tafi."

"Ah ah baza ki bari ayi musu a gaban ki bane? Naji an ce Mutumin ne bai zo ba har yanzu." Cewar Inna Asabe da ta fito tsulum daga ɗaki jin abun da Umma take cewa

"A'a bazan zauna ba, tunda nayi abun da ya kawo Ni dole zan tafi, su kuma Allah ya basu lafiya Allah yasa ayi a Sa'a."

Tuni hawaye sun soma wanke min fuska saboda jin abun da Umma take faɗa, da sauri na miƙe daga kusa da Yaya Haula ina dire mata ɗiyarta, sai na nufi wajen da Umma ke tsaye na rungume ta ina me fashewa da kuka, cikin kukan nake cewa, "Umma kar ki tafi ki bar Ni don Allah, ba na so ayi min don Allah ki tafi dani."

Wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a kan fuskar Umma sabida tsantsan tausayi na, da sauri ta sa hannu ta share tana me kamo fuskata tare da cewa, "kiyi haƙuri Madina Allah shi ne zai kare ki, babu abin da zai faru da ke sai alkhairi, Ni zan tafi gida kinji?"

Kuka sosai nake yi a yanzu, ina cewa, "kar ta tafi." Na ƙanƙame ta sosai a jikina ina kuka har da su majinu, kuma na hana ta tafiya

Dole Yaya Haula ce ta taso itama tana kukan ta kama Ni, amma duk yadda ta so ta ɓanɓare Ni ta kasa

Su Inna Lami kuwa sun samu abun yi sai faɗa suke yi amma ko jin su ba na yi, Ni kuka na da tashin hankali na ya ishe Ni, ƙarshe Yayan mu Shamsu aka kira tunda shi ne a sasan, shi ya zo ya ɓanɓare Ni ya shiga dani ɗaki, ita kuma Umma tayi musu sallama ta fice ba tare da ta jira cewar su ba, haka Yaya Haula ta bi bayan ta domin suyi sallama sai share hawaye take yi

Mutanen gida kowa taɓe baki yayi ya ci gaba da aikin gaban shi domin su a wurin su ba tausayi na basu ba, su ma idan da hali baza su so a yiwa Yaran su ba amma an fi ƙarfin su basu da yanda zasu yi, duk yaran su na gidan aure sai da aka yi musu ba yau suka saba shiga baƙin ciki irin wannan ba, dole su danne kayan su tunda ko sun nuna a fili ƙarshe a kansu zai ƙare

Ni kuwa daƙyar Yaya Shamsu ya natsar da Ni sai da ya saka min hannu, tare da daka min tsawa yace, "idan ya sake jin kuka na zan ga abun da zai yi min."


Dole na gimtse baki har da riƙewa da hannu ina ta shashsheƙa, yayinda hawaye ke gudun tsere a idanu na amma babu halin fitar da kukana waje, idan ma na fitar abun da ya same Ni ni naso domin duk gidan nan babu mugu kamar Yaya Shamsu, shi a wurin shi ya kama yarinya yayi mata shegen duka na fitan hankali abu ne mae sauƙi, yawancin ƴan gidan namu haka suke sam-sam ba sa wasa Mazan. Ina nan a zaune aka soma kiran mu wai Mutumin da zai mana kaciyar ya iso, nan fa kuka na ya dawo sabo, ƙin fita nayi sai da aka zo aka ɗauke Ni, haka nake kuka ina bori baza ayi min ba, a lokacin da aka kai Ni zauren gidanmu har an yiwa Fatimah da Fa'iza sai tsandara ihu suke yi, saura su Luba da su ma kukan kawai suke yi, gaba ɗaya iyalan gidan mu Maza suna wajen, su Baffa da su Yaya Shamsu duk su ne masu kama mu

Nima fa sai na ruɗe kuka na ya ƙaru, amma sai aka ce a ɗaure min ƙafafu da hannaye tunda bazan tsaya ba sai bori nake yi. Hannayena suka soma ɗaurewa ta baya sai su ma ƙafafuna kamar wata akuya, aka rufe min idanu ya zamana ba na ganin komai sai kukana da na kasa denawa, dole shima aka ƙulle min baki saboda yanda nake yanka kuka kamar raina zai fita, a lokacin ne aka fito da bakin al'aurata da aka cire min skirt ɗin jiki na. Bayan wasu mintoci, sai na ji raɗaɗi, na yi kururuwa amma ba mai ji na, na yi ƙoƙarin fincike ƙafata amma sai na ji wani ƙarfe ya rirriƙe ƙafafuna, babu wani abun rage raɗaɗi sai wani ganye, ina jin sanda aka manna min shi a jiki na, daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sabida azaban da yayi min yawa, a tunani na raina ya gama ficewa a cikin jikina.
   
[10/06, 12:16 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎

_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





              *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 3*
_____Haƙiƙa ban taɓa fuskantar azaba irin makamanciyar wannan da na sha ba, ban yi tunanin a duniya akwai irin wannan uƙuban ba, tabbas sun gana min azaba ba kaɗan ba, tunda na sume ban sake sanin inda kaina yake ba har aka gamawa kowa kaciyar, yayinda aka ɗauke Ni aka kai Ni ɗaki Ni da sauran ƴan uwana waɗanda ko wacce ɗakin Mahaifiyarta aka kaita domin ta kula da ita, Ni kuwa babu kowa a tare da Ni sai Yaya Haula da take zuwa gida take dawowa, tayi kuka ba kaɗan ba, ta shiga tashin hankali matsananciya ganin har yanzu ban farfaɗo ba, duk da kuwa zuba min ruwa da akai tayi, amma sai Baban Sasa yace, "a bar Ni zan farfaɗo ne, babu abun da zai same Ni." Daga nan ne aka tafi aka bar Ni, Yaya Haula da ta gaji da jiran farkawa na itama sai ta koma gida, tunda tana da aiyuka duk bata yi ba, dole ta koma gida ta soma aikace-aikace tare da ɗaura girkin dare tunda a lokacin goshin magriba ya gabato, bayan ta gama ne ta sake dawowa gidan amma har a lokacin ban farka ba, da abincin da ta dafa ta riƙo min ta kawo min, sai dai hankalin ta ya sake tashi sabida ganin babu numfashina har yanzu, ga shi kuma jinin da ke fita daga ƙasa na bai dena fita ba, dole ta fita tana kuka ta je ta samo ganyen da aka yi mana amfani dashi wajen Inna Lami, ta shigo dashi ta sake duba min ƙasana ta ga yanda yake zubar da jini, sai ta cire wancan ganyen ta sanya min sabo, kana ta buga tagumi tana ta hawaye yayinda idanuwanta suna a kaina

A lokacin ne Baban Sasa ya aiko yana tambayar, "har yanzu ban farka ba?"

Yayinda ɗan aiken ya koma ya sanar mishi da halin da nake ciki. To tun suna ɗaukar abun da wasa amma har dare ya soma tsalawa ban farka ba, abun ya soma damun su Baffa, haka aka kira mae maganin gargajiya ya sake duba Ni, ga shi na kowa jinin ya tsaya amma ban dani, jinina sai zuba yake yi haka na sake yin fari a lokaci ɗaya tamkar bani da rai, lokaci ɗaya na zabge

Please Login or Register in order to submit comment