Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nasir ya kira sa yana faɗa masa."

Duk hiran da suke yi ina wurin na zauna kamar babu Ni, kaina a ƙasa ina jujjuya yatsuna gabana sai faɗuwa yake yi sabida irin kallon da nake jin a jikina kamar yana min, ko na ɗago ido sai na ga yana bi na da ido hakan ne yasa duk na tsargu na bi na daburce, take kuma hankalina ya koma kan rigan jikina, ganin bani da hijabi sai kunya kuma ta cika Ni,
Nayi saurin mike wa zan bar wajen,
Amma sai Umma ta tsayar dani tace min, "yanzu ita zata tafi."

Ban ji dad'i ba amma bani da yadda zan yi bare in tsayar da ita, ga Yaya Yunus ma a wurin shiyasa na ɓoye ƙwallan da ya cika min ido,
Har bakin ƙofa na raka ta sannan na dawo nayi cikin ɗakina da sauri na shige,
Dama na gama komai shiyasa fargaban ganin Yaya Yunusan yana gidan; sai nayi saurin rufe ƙofan ɗakina don hankalina zai fi kwanciya a haka,
Amma ko kafin in rufe sai ganinsa nayi ya dakatar dani ta hanyar sanya hannu, yana kallona yace, "me za ki yi kike rufe ƙofa?"

A daburce na bi sa da ido, murya na rawa nace masa, "ba..bbu."

Tura ƙofan yayi ya shiga ya mayar ya kulle yana wani shan ƙamshi kamar ba shi ba

Ni kuwa zallan tsoro da firgita yasa na soma sakin fitsari a wando nan take; ina mai kama cikina da ya fara murɗa min,
Ganin yana soma dumfaro Ni, sai na soma ja da baya ina yarfe hannu cikin tsananin tashin hankali da rawan bakin da ban san sanda maganar ta kufce min ba, nace....



_Juma'at Mubarakh ƴan uwa masoyana. Ina muku fatan alkhairi.😘 Ina jin daɗin yanda kuke nuna soyayyarku ga wannan littafin. Love 😍 you fan's._
[12/08, 9:27 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 30*
_____"Wayyo...! Don girman Allah kayi haƙuri kar kayi min zan mutu, don Allah ka taimake Ni ka cece Ni kayi min rai."

Fuska ya ɗaure sabida ganin gaba ɗaya na fita a hayyacina ina masa magiya, hannunsa yasa a bakinsa yace, "shiii! Kar in sake jin maganar ki ta fito, idan ba haka ba sai na farfasa miki bakin, ko kin ga na taɓa wasa da ke ne?"

Da sauri na soma girgiza masa kai ina mai matse jikina tare da ci gaba da ja da baya, idanuna tuni sun soma fitar da ruwan hawaye,
Wurina ya nufa ya damƙoni, na saki wani uban ihun da na kusa kurumce masa kunne,
Ganin yanda na firgice ina masa ihu kamar zan tsaga mishi kunne, take ya liƙe min bakin yana daka min tsawa da faɗin, "Allah idan ba ki yi min shiru ba; abun da zan miki sai kin sha mamaki na, kina da hankali kuwa? Ko kin manta Ni mijinki ne kike min wannan ihun da hauka? Ko don kinga ban zane miki jiki bane kike son raina Ni? Idan kika kuma ihu sai na miki abun da ba ki tunani."
A hankali ya ja Ni zuwa saman gadon ya zaunar dani yana cewa, "kuma ki yi motsi ki ga yanda zan yi da ke."
Ya Harare ni yana wuce wa wurin glop da ke kunne hasken ɗakin yayi fau, take ya kashe nan da nan ɗakin ya rage haske sai iya hasken ranan da ke ɓillowa ta window

A wannan lokacin bani da zaɓi sama da yin abun da Yaya Yunus ya zo min dashi, ina ji ina gani babu bakin kuka sabida a yanda ya ruɗa min ciki ya hana Ni kataɓus; sai ruwan hawaye da nake zubar wa a haka ya cire min kaya ya soma yin abun da na kasa fahimtar komai; sabida tsananin ruɗu da firgitan da nake ciki, gaba ɗaya na matse jikina na ƙudundune ina sauraron yanda yake wasa da sassan jikina tamkar zai haɗiye Ni ya mayar dani ciki, a yau na ga tashin hankali ƙiri-ƙiri, tsoro ya hana Ni bayyana halin da nake ciki, kamar sokuwa haka na zama sai yanda yayi dani gudun saɓa mishi daga barazanar da yake min, sai kukan zuci da nake yi na rufe idanuna gam ina jiran kuma wanne irin azaba yau zan karɓa? Sosai yake wasa dani cikin zaucen hankali wanda yasa gaba ɗaya zafi da rashin sabo yasa na fice a hayyacina,
Tun ina tunanin zan iya jure wa amma inaa; kuka sosai nake yi ina mishi magiyan, "ya ƙyale Ni."
Amma sam ba ya ji na tamkar ina ƙara tunzura shi ne

Sam Yaya Yunus bai yi ninyar yin min komai ba, sabida halin da nake ciki na cutan sanyi, yana gudun ya samu, amma yayi wasa dani son ransa har sai da gaba ɗaya ya gama fitar dani a hayyacina, sai da ya samu natsuwa son ransa sannan ya manne Ni a jikinsa yana hura min iska a kunne,
Take kuwa na kawo numfashi mai ƙarfi yayinda idanuna suna rufe gam hawaye masu zafi suna kwaranya daga gefen kunnena, sam ban sake motsa wa ba tamkar wata matacciya, wadda kawai numfashi ne ke tabbatar mishi da ina da rai,
Ya jima rungume dani kamar zai mayar dani ciki; sabida irin gamsuwar da yake samu da wani irin daɗi da ke fizgarsa, can kuma ya soma sakar min sumba a baki, ya bani umarnin buɗe idanu in kalle sa,
Sam na kasa sabida wani irin kunya da ke ɗawainiya da Ni tamkar zan nutse a ƙasa in mutu, na kasa yin abun da yace min sai ma fashe wa da kuka da nayi ina rawan baki, jikina gaba ɗaya ya ƙara yin zafi kamar an jona Ni a heater,
Wanda hakan ba ƙaramin taimaka masa yayi ba wajen sanya shi jin dad'i ya ƙara lafe wa a jikina kamar bazai bar Ni in shaƙi numfashi ba, a hankali ya sanya hannunsa a saman gashina da ke ɗaure babu gitso bare gyara,
Cikin bazatan muryansa na ji yana cewa, "shiii! Madina ki dena wannan shashsheƙan kukan haka, kinga jikinki har ya soma ɗaukan zafi, kar zazzaɓi ya kama ki."
Sai ya ja numfashi yana ƙara liƙe Ni a jikinsa, yayinda ya saka hannunsa a saman ƙirjina yana matsa wa a hankali tare da ci gaba da faɗin, "kinga dai Ni Mijinki ne, shiyasa na zo amsar haƙƙina a wurin ki, kar ki sake jin tsorona daga yau, domin abun da zai riƙa kasancewa da Ni da ke kenan daga yanzu, babu abun da zan miki kawai zan riƙa zuwa ina samun natsuwa ne a wurin ki, idan kuma kika ce baza ki kwantar da hankalinki ba har kika yi abun da Matata ta san halin da muke ciki, hmm za ki ga mai zan miki, don haka ki dena min wannan kukan kar in ƙara ganin kina jin tsorona, haƙƙinki zan sauke miki kina jina?"
Da sauri na gyaɗa mishi kaina ina mai matse bakina sabida kukan da ya taho min, cike da tsoro nake sauraron zantukan sa da sam ba na gane wa sabida halin firgici, amma bani da yanda zan yi ina ji ina gani ya gama duk abun da zai yi sannan ya saka Ni a gaba muka shiga toilet ya sanya Ni sai da muka yi wanka tare,
Ya so ɗaura Ni a kan hanyar da na kasa yin masa biyayya, dole ya ƙyale Ni sabida kar ya ci gaba da ruɗa Ni, amma ya san cewa a hankali zai cire min tsoron nan nawa dole sai na riƙa masa abun da yake so,
Haka ya fice ya bar Ni a ɗakin; ya bar Ni da tarin baƙin ciki da kunya, don gani nake yi abun tamkar a mafarki na kasa yarda da abubuwan da suke faruwa, kuka kawai nake yi sabida sam babu wani jin dad'i da sha'awar da nake ji illa azaba da raɗaɗin gama murɗa min ƙirji da yayi, na sha kuka har na godewa Allah,
Daga ƙarshe na takure a ɗaki ko fita na gaza yi sabida zazzaɓin da ya kama Ni a nan take, yayinda fargaban maganganun sa yasa Ni sam na gaza kwantar da hankalina, yanzu shikenan haka zan ƙare cikin wannan wahalar da Yaya Yunus yake son bijiro min dashi? Ni kam bazan iya jure wa ba, amma bani da yadda zan yi tunda haka ƙaddarana ta zo min, dole in masa biyayya tunda shi Mijina ne, ina jin tsoronsa matuƙa da bazan iya saɓa mishi ba,
Kuma na kasa cire tsoron da ya rigada ya shige Ni yayi tasiri a zuciyata; wanda a koyaushe a fargaba da zullumi nake ciki sabida tun daga ranan Yaya Yunus ya soma takura min da zuwa ɗakina,
A kowanne dare sai ya zo wurina yayi abun da yake so dani ya bar Ni cikin kuka da baƙin cikin abun da yake min,
Tabbas ba na jin daɗin duk abubuwan da yake min, da da yanda zan yi in hana sa da nayi tuni, sai dai dole Ni ƴar kallo ne bani da yadda zan yi, amma zuciyata sam ba ta karɓan duk wani abubuwan da yake min, kuma ga tilasta Ni da yake yi nima ina masa abun da zai ji dad'i dole, tun ina kuka da magiya ya kyale Ni amma sam ya ƙi saurarona, duk abun da zai yi min shi kaɗai yake kiɗansa yake rawansa sabida Ni bani da wannan sha'awar da zan ji komai a jikina, illa ma azaba da yake barina dashi in kwana kuka da ƙunci,
A wurin sa kuwa daɗin da yake ji ne yasa kullum ba ya ɗaga min ƙafa, ba ƙaramin gamsuwa yake samu da irin baiwar da Allah ya bani ba, har Allah - Allah yake yi ya zo waje na ya soma matsa Ni yana samun natsuwa,
Da wannan yanayin ne lokaci ɗaya na soma zabge wa, maimakon jikina da ya murmure na ɗan yi jiki, sai kuma tuni na zabge sabida zullumi da tsoron da na saka wa raina, ga zazzaɓin da nake fama dashi in har zai zo yayi min wannan abun to dole sai na kwana cikin zazzaɓi, ya zamana ma wani lokacin har sai nayi amai in ya fita yabar Ni in ta kuka ina amai da ƙaƙarin zubar da abun da yake saka Ni sha dole, sabida ba ƙaramin ƙyanƙyamin abun da yake min nake yi ba, sai dai ba yanda zan yi

Sam Sharhabila bata taɓa fahimtar halin da muke ciki ba, har kusan watanni biyu sun shuɗe muna a wannan yanayin,
A wannan lokacin na soma gane tabbas ina cikin wani hali sabida kumburin da cikina ya soma yi, tare da motsin da nake yawan ji a jikina, kuma sai yanzu ne na soma ciwuka kala-kala a tafe nake kawai amma sam ba na jin daɗin jikina, dauriya ce wacce na azawa kaina batare da na san lokacin da na zama Jaruman ba, tabbas Ni mai rauni ce amma a yanzu na zama jaruman da ya zama dole in kasance haka, domin a irin bautan da nake yi wa Aunty Sharhabila sam ba ta tausaya min a rayuwa, ban isa na huta ko na zauna don ina ciwo ba, ya zamar min dole ne sai nayi ko ina tafe ina kuka ne, ga fitinan Mijinta da ya zame min maye yana ƙuntata ma rayuwata, yana sanya Ni abun da har yanzu na gaza saba wa, a yanzu ma na dena kukan fili sai na zuciya tunda babu mai rarrashina bare tausaya min, na san Ni a haka rayuwata zata ƙare har abada, babu jin dad'i bare farin ciki, tabbas na koyi abubuwa da dama a wannan rayuwar tawa da nayi da mutanen nan, kuma a yanzu na soma wayon da yasa na fara saba wa da komai na rayuwa, wata rayuwa na farin ciki ko jin dadi duk na ajiye shi a gefe, kawai ina fuskantar yadda rayuwata zata kasance a nan gaba ne; duk idan Aunty Sharhabila ta gane abubuwan da ke faruwa, na san kashe Ni zata yi, baza ta taɓa bari na da rai ba

Inda shi Yaya Yunus yana cikin farin ciki a wannan lokacin, domin kasancewarsa dani ba ƙaramin taimaka masa yake yi ba, har ma yanzu ya fi samun gamsuwa dani fiye da ya kasance da Matarsa, domin romance ɗin da yake yi dani ya fi mishi jin daɗi shiyasa koyaushe yake nane dani; duk tsawon dare bazai sarara min ba, yanzu ma ko kusa ba ya damuwa da halin da Sharhabila take nuna masa, tunda ko ta ba shi hakkinsa ko kar ta ba shi ya samu wurin lafe wa,
Ana haka wani kwangila nasu da ya taɓa saka hannun jari akai da jima wa, sai ga shi wannan karon an neme su zuwa Kano, kwana ɗaya ya je yayi ya dawo duk a kan shirye-shiryen kayan nasu da zai shigo a wannan makon,
To gaskiya ba ƙaramin arziki suka samu ba don shi kansa ya rasa inda zai saka kansa don farin ciki, tunda tuni sun cire rai da wannan harkan, kasancewar dashi da Abokinsa Doctor Bilal suke zuba hannun jarin nasu, kuma tare suke komai don ko Sharhabila bai taɓa sanar mata da zancen ba, amma sai ga shi wannan karon komai ya buɗe musu Allah ya fito musu da kayansu har sun sami riba fiye da tunanin su,
Lokaci guda kuwa ya siya wani ƙaton gida a nan GRA sabon gari, sabida yayi hakan ne don ya huce gorin da Sharhabila tayi masa, ba wai don ba shi da kuɗin siya bane tun farko, amma yanzu da ya fara ganin gori dole ne ya nemi gidan ya siya, hawa biyu ne mai kyau sai ɗan gyare-gyare da ya fara yi, kuma har wannan lokacin bai taɓa sanar mata ba yana bari sai ya kammala komai sannan ya sanar mata

Ana haka jikina ya ci ƙarfina, tafiyan da nake yi a daddafe da ciwo ya soma kwantar da Ni har ba na iya yin aikin da na saba yi, jikina ya soma nauyi duk da ina cikin zullumi da ƙuncin da na kasa gane kaina, na rasa wanda zan iya bayyana masa cutan da ke damuna, Ni dai na san akwai cuta a jikina, Ni bazan taɓa gane ciki ne a jikina ba sabida ban san shi ba, ban san alamomin sa ba, kuma dayake Allah yaso ya ɓoye abun sa babu wanda ya gane ina da ciki a duk cikin su, ko don cikin ba wani girma ne dashi ba, Ni da yake a jikina Ni kaɗai na fuskanci cikina ya kumbura, wanda ina ji a raina wata cutar ne a tattare dani, sau tari ina zama in ta taɓa cikin ina kuka da hawayena da tunanin waye zan faɗa ma wa?
Da ace Umma zata zo zan faɗa mata ko don ta nema min lafiya, kuma na gaza sanar da Yaya Yunus duk da akwai lokacin da ya taɓa min makamancin irin tambayar, yanayin yadda nake jin baƙin ciki da tsanarsa; sabida ƙuncin da yake ƙuntata min sam yanzu ba na ganin zan iya neman taimako a wurin sa, na fi son in mutu da in ci gaba da zama dashi, domin ban san wanne irin tsana Allah ya saka min nasa a ƙanƙanin lokaci ba, na san ba haka nake ji a baya a game dashi ba, amma yanzu komai nasa na tsana, daga shi har Alh. Badamasi ganin baƙin su nake yi, ina ganin su ne mutane mafi muni da suka ƙuntata min a rayuwa, a kansu na ji na tsani kowanne irin namiji da zai iya kusanto Ni in buɗe ido in gansa, ina jin Maza basu da imani bare tausayi a cikin ransu, sun rigada sun gama min illa a rayuwata bani da sauran walwala da ya rage min,
Ana wannan yanayin ya ɗauke Ni yakai Ni asibiti da jikina ya rikice sam ba na iya yin komai,
Dole ya ɗauke Ni zuwa asibiti wurin Abokinsa Doctor Bilal

Shi Bilal tunda ya kalle Ni yayi min zargin mai ciki ne, domin kasancewar sa likita ya ga alamun haka, duk da ba cikin ya gani ba kasancewar ina sanye da hijabi bai yi girman da zai fito ba,
Dariya kawai yayi yace, "Abokina kana sha'anin ka, wannan aiki haka?"

Sam Yaya Yunus bai gane mai yake nufi ba, amma ya san shaƙiyancin sa ne shiyasa yace masa, "shi fa ba wasa ya zo yi ba, kawai ya duba Ni ya rubuta min magani mu koma."

Dayake ina jin jiki a lokacin, dole aka saka min ruwa sabida a lokacin warin asibitin ya sani jikina ya sake rikicewa nan take; zuciyata ta tashi na dinga amai kamar zan amayar da hanjin cikina, nan da nan aka soma bani taimakon gaggawa wurin saka min ruwa sabida ganin jikina ya saki sosai sai kuka nake yi,
Daga ƙarshe ya sanya aka ɗibi jinina da fitsarina aka je aka yi min gwaji; wanda hasashen sa dama ciki ne shiyasa gwajin da yasa aka yi min kenan,
A lokacin ina kwance ina barci a office ɗin sa ban san inda kaina yake ba,
Bayan an kawo result ɗin da ya duba ya gani da gaske cikin ne dani, sai ya fashe da dariya yana cewa, "ashe dai hasashena gaskiya ne ka cika aiki Malam, kana wani ƙumbo kullum ka riƙa cika min baki, to wannan me nake gani Mata har da Ciki?"

Sam Yaya Yunus bai gane mai yake nufi ba, sabida bai taɓa tunanin wannan maganar ba kasancewar tun ranan farko bai taɓa kwatanta sake kusanta na ba, iyakansa romance abun da yake haɗa Ni dashi kenan, tunda a nan yake jin dadin sa, amma sai ga shi babu zato babu tsammani ya ji maganar da ya zo tarwatsa mishi farin ciki, hankalinsa a tashe yake cewa, "ban gane ba Doctor? Ciki wanne cikin kake nufi wai tana dashi? Kar ka raina min hankali fa?"

"Kar in raina maka hankali ko kar ka raina wa kanka hankali? Ciki fa da ka sani wanda ka danƙara mata shi nake nufi, don haka ga result nan ya nuna min ciki har na watanni biyar da satikai biyu."

Sosai a wannan lokacin Yaya Yunus ya sake rikicewa, sam ya kasa yarda don faɗi yake yi, "wlh ƙarya kake yi Doctor, yarinyar da na taɓa sanin ta sau ɗaya ko minti biyu ban yi ba a time ɗin; and lokacin babu wani daɗin da zan iya tsaya wa in ji sai azaban da na ji, shine zaka ce min ta samu ciki? To taya ya?"

"Yau na ga ikon Allah da mutumin nan? Shi dama idan Allah ya so ikonsa ai komai yana yi, mutane nawa ne suke samun ciki a First sex ɗin su har su haihu? Wannan ba hujja bane Yunus, Allah na yin yanda ya so, na ga dai wannan ƙanwarka ce kuma Matarka; to mene ne abun mamaki bare na tayar da jijiya tunda an ce tana da ciki? Kuma fa Ni da kai mun san ka kusance ta, Allah ne yayi ikonsa kawai ashe da rabon za a samu ɗa."

Hulansa ya cire yana fifita tare da sake cewa, "wai Dacta kana nufin dai da gaske cikin ne a jikinta? Kuma nawa?"
Sai ya girgiza kansa cike da tashin hankalin da yake ciki yace, "to ina zan kai cikin? Ai ban shirya haihuwa da ita ba, kai kanka ka san matsalata Matata bata san auren da ke tsakaninmu ba, kuma ka san halin ta akwai shegen kishi wlh a kan haka sai mu samu matsala, ban shirya rabuwa da farin cikin gidana ba, zubar da cikin nan za a yi."

"Ban gane ba? Kana cikin hankalin ka kuwa Yunus? A zubar da ciki kuma? Don me?"

Idanu ya tsare shi dashi tare da cewa, "sabida ba wannan ne a gabana ba Doctor, Ni ban shirya samun matsala a gidana ba, ban ga amfanin da cikin nan zai yi min ba tunda bata da wani amfani a gare Ni, Ni ba ina tare da ita bane don wani abu; sai domin ƙaddara da babu yanda zan yi iyayena sun liƙa min, zaman lafiyana da kuma zaman lafiyanta kawai a zubar da cikin nan."
Sai kuma ya ja tsaki yace, "mai zan yi da cikin ta?"

Baki kawai Doctor Bilal ya saki yana bin shi da kallo cike da al'ajabin maganarsa gami da mamaki, "wai Yunus da gaske kake yi zubar da cikin kake son yi?"


"I'm serious doctor, ka taimaka kawai ka zubar dashi tun yanzu Please, shi ne taimakon da zaka yi min."

"Lallai ka bani mamaki, a kan wata kuma sai ka jefa ƙanwarka a cikin matsala; idan kuma ta mutu fa? YUNUS ka dawo tunaninka ka san cewa wannan ƙanwarka ce jininka; why would you hurt her don kawai sabida tsoron Matarka ta san da zancen? Akwai aure fa a tsakaninku; meyasa zaka aikata haka? Tell me; ko dama ba ƙanwar naka bane babu aure a tsakaninku kake nuna wannan tsoron ba ka son Matarka ta sani? Wanne irin aure ne ma wannan? Kana ɓoye min wani abu Yunus, babu yanda za a yi tana Matarka kawai ka ce a zubar mata da ciki kana son cutar da ita".



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment