Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

and we will talk."

Idanu ta mayar kaina, ta sake tsare Ni da kallo cike da zallan mamaki, don fuskata tana nuna mata kamar ta taɓa ganin fuskar, kuma duk yanda aka yi Ni ƴar uwansa ne sabida ta ga kamannin Yaya Yunus a tattare da Ni, hakan ne yasa nan da nan ta sauya fuska tana cewa, "No, now I want you to tell me who she is, why she came here?"

Hannunsa ya zuba a aljihun rigansa, cike da rashin damuwa yana ci gaba da yatsina fuska yace, "ɗazu aka kawo min ita daga ƙauye, cus na ga kina neman mai aiki since wancan tayi aure, kuma aiki yayi miki yawa, that's the reason da na yanke hukuncin kawai bari in ɗauko wata a ƙauye ta zauna da mu."

"Husband, amma meyasa baka nemi shawarata ba? A kan me zaka dauko min ƴar ƙauye ka kawo min ita gida na? Idan nace ina buƙatar ƴar aiki i told you irin wannan nace nake so?"
Sai kuma ta sake kallona tamkar tana nazari, kana tace, "I know wannan yarinyar har da ita muka je auren ta kwanaki? Ya aka yi kuma ta zo nan?"
Kallon da take mishi na tuhuma, shine dalilin da yasa ya taho inda take tare da kama hannunta, cikin sanyin murya yace, "Calm down mana Wifey, meyasa kike ɗaga murya a kan ɗan wannan abun? Zauna please sai in miki bayani?"
Ya kamo hannunta har zuwa saman Kujera before ya ci gaba da faɗin, "auren ta ya mutu ne ashe, kuma ranan da na je gida na ganta sai nayi tunanin kawai a bani ita in zo miki da ita, ko aikace-aikace sai ta taya ki, so ban dauko ta bane shine na saka aka kawo min ita. I forgot to tell you, but please be patient and please don't be angry."
Kwaɓe fuska tayi tace, "amma husband, ka san da cewa ba na son irin waɗannan ƙauyawan? And ka san da cewa a masu aikina sai na zaɓa na darje kuma ƴan birni nake so don ba na son ƙazanta, meyasa zaka dauko min ƙazama daga wancan banzan kauyen ka kawo min ita nan? Ni fa ba na buƙatar ta wlh don bata da wurin zama a nan."
A kalaman ta sai da ya ji ransa ya sosu jin yanda take zagin ƙauyen su, ko ta manta shima daga can ya fito ne? Amma sai ya sake tausasa murya musamman akwai yaransu a wurin yana sake bata hakuri, tare da ce mata, "yayi hakan ne kawai don faranta mata, ya san yarinyar zata iya duk aikin da ta sanya ta batare da wahala ba, kuma idan ba ta son ƙazanta zata iya gyara ta duk yanda take son ta zama, amma ta barta a nan tunda already ya rigada ya dauko ta, bai san mai zai ce wa iyayensa ba kuma idan ya mayar da ita."

Kwata-kwata Sharhabila ba abun da take hangowa kenan ba, domin a kallo ɗaya da tayi min sai ta ji ranta bai kwanta da Ni ba, kasancewar ta mai shegen kishin tsiya, don me zai dauko Ni ya kawo Ni gidansa bayan ya san komai zai iya faruwa? Bare ƴar uwanshi ce akwai aure a tsakaninmu wata rana labarin zai iya sauya wa, musamman yadda ta ganni kyakkyawa kalansa ina samun gyara zan sauya, ita dai kwata-kwata bata yarda ba don haka ta nuna mishi sam a'a

Ya san cewa kishin ta ne ya motsa, don haka ya ci gaba da lallaɓa ta yana cewa, "ta ba shi ɗan wasu lokuta before ya mayar da Ni, amma ban da yanzu, kuma abun da take tunani bazai taɓa kasancewa ba, ya rasa wacce zai kula sai Ni ƴar ƙauye? Ai ta san ya fi ƙarfina."
Daga nan fa ya ci gaba da muzanta Ni a gabanta yana faɗan duk maganar da ta zo bakin sa don dai ya sake kwantar mata da hankali


A gabana ina jin su duk abun da suke faɗa, kaina a ƙasa ina jin kamar in fashe da kuka, zuciyata ta cika da ƙunci da baƙin cikin yanda yake ci min mutunci yana zagina duk a kan Matarsa, har yana cewa, "mai zai yi da sauran Maza? Ta kwantar da hankalinta ko a kafa aka ɗaura mishi Ni sai ya kwance."
Idanuna na lumshe ina mai jin wasu hawaye masu zafin gaske suna zubo min, Ni kuma a haka zan ƙare kenan bani da madafa da farin ciki?
Ina ji ina gani ana zagina ana ci min mutunci da aibata Ni, amma bani da yanda zan yi, ko giyan wake na sha ai Yaya Yunus ya fi ƙarfina; nesa ba kusa ba, wutsiyan raƙumi tayi nesa da ƙasa.
Daga ƙarshe ina jin sanda suka bar wurin gaba ɗaya amma hakan bai sa na ɗago kaina ba, idanuna suna kullen har yanzu na ɗaura kaina a ƙafafuna tamkar babu numfashi a tattare da Ni, rayuwar duniya kawai nake tunani, da kuma yanda zan rayu a cikin wannan gidan.
Sai ga Sharhabilan ta fito tana daka min tsawa,
Take na ɗago kai ina kallonta da rinannun idanuna masu cike da rauni da zallan tausayi

Wani kallon sama da ƙasa tayi min tana jan dogon tsaki, tana riƙe da hannun Sadam da ke biye da ita, sai ta zauna a kan Kujera ta ɗaura kafa daya kan ɗaya tana cewa, "daga yau ba zaman hutu ya kawo ki ba, tunda already kin san abun da yasa aka kawo ki nan, so da sannu zan kafa miki sharuɗɗana da yakamata ki sansu kuma babu gindaye wa, zan fara horar da ke a kan abubuwan da nake so; don kaf aikin gidan nan ke za ki riƙa yi komai da komai, abu na gaba ba na son ƙazanta, sannan kibar ganin Husband Yayanki ne; ba na son in sake ganin koda magana ta sake haɗa ku dashi, duk abun da kike son sani Ni za ki faɗa ma wa, ko gaisuwa ba na son ya haɗa ku, kina jina?"
Ta ƙare maganar tana mai daka min tsawa,
Take kuwa na amsa ta jikina na rawa kamar mazari,
Sai ta ja dogon tsaki tana mai yatsina fuska, ta kalli Sadam tace, "ɗaga ni mu je in nuna mata masaukin ta."
Sai ta miƙe rike da hannun Yaron, batare da ta kalle Ni ba tace, "biyo NI."

Kasancewar na gane dani take yi, shiyasa na tashi na bi bayanta jiki na rawa,
Har mun fara tafiya ta juya tana kafa min ido, sai tace, "uban wa kika bar wa wancan kayan; baza ki ɗauko ki taho dashi ba?"
Waiga wa nayi na hangi akwatin kayana a wurin, take na juya na bi umarnin ta na ɗauko kayan na bi bayanta har lokacin jikina rawa yake yi

Wani ɗaki takaini ɗan dai-dai, gado ne kawai a ciki da wurin ajiye kaya, sai bayi wurin kewaya wa,
Ta nuna min tace, "nan ne zan riƙa kwana."
Sannan tabar ɗakin ta tafi ta bar Ni a tsaye,
Bata sake bi ta kaina ba har na gaji da tsayuwa; na zauna ina ta tunani tare da kallon dakin da aka bani mai kyau a ido,
Har dare yayi basu sake bi ta kaina ba ina nan zaune na rasa madafa tunda ban san me zan yi ba, ga shi ina son shiga bayi sannan ina son yin sallan da suka wuce Ni, amma ban san inda zan je in yi ba, bayin da ke cikin ɗakin ban san mene ne ba bare in duba, tunda na zauna ko jirga wa na kasa yi,
Har dare ya tsala ban sake jin wani motsi ba, tun ina gyangyaɗi ina matse ƙafafuna sabida fitsarin da ya matse ni, har dai barci ya sure Ni a haka cikin wani yanayi ina zaune a yadda nake

Sai washe gari Sharhabila ta dawo dakin ta tayar da Ni, tana bi na da mugun kallo cike da ƙyama tace, "shegiya an samu wurin banza har da hangame baki ana barci, dalla tashi ki shiga wancan ƙofan ki yi wanka ki canza kayan jikinki; ki zo ki same Ni ina jiran ki, saura ki ɓata min lokaci ki ga yanda zan yi da ke."
Ta ja tsaki ta fice a ɗakin cikin tafiyan ƙasaita

Ni kuma jiki na rawa na miƙe na nufi ƙofan da ta nuna min, ina buɗe wa na fahimci bayi ne duk da babu komai a ciki sai famfo da sabulan wanka, sai bokiti, hakan ne yasa da sauri na duƙa na saki fitsarin da ya cika min mara fam yana shirin fitowa, ban tsaya ɓata lokaci ba tunda ta sanar min tana jira na, kasancewar na san famfo tunda akwai a ƙauyen mu, na san ruwa yake fitar wa shiyasa na ɗauki bokitin na tara na zuba ruwan, ruwan sanyi ne amma a haka nan nayi wankan tunda bani da yanda zan yi, dole abun da na gani da shi zan yi amfani,
Take kuwa wani sanyi ya ratsa min jiki tsaban azaban sanyin ruwan, duk da na saba wanka da ruwan sanyi amma sai da jikina ya soma karkarwa, tunda damuna ne akwai sanyi a gari sosai na ji sanyi na ratsa Ni,
Cikin sauri na gama na fita na bude kayana na ɗauko wata doguwar riga ƴar kanti sabuwa fil na sanya, farar riga ce mai igiya a baya, saman rigan wuyan V ne an yi masa aiki da baƙin zare da kore, rigan ba ƙaramin kyau tayi min ba nan da nan ta sake fito da yarinta ta, ban tsaya wani ɓata lokaci ba na nemo hula na saka a kaina, ko bi ta kallon kayan ban yi ba tunda duk sababbi ne wadanda Alh. Badamasi yayi min na aure, ban taɓa ganin kayan ba koda aka nuna a gidan mu, Ni kaina a yanzu na tsorata nayi mamakin ganin yawan kayan, amma hankalina ba ya wurin ban tsaya duba wa ba na fice da sauri,
Hanyar da na ga ta biyo dani jiya nan na bi, sai gani a falon inda take zaune ita kaɗai,
Da alamun babu kowa sai ita,
Yaya Yunus tare da yaransa ya wuce da su school

Tana gani na ta haɗe fuska tana jan tsaki,
Ni kuma na zube a ƙasa ina gaishe ta amma kamar bada ita nake yi ba, sai da ta sha ƙamshin ta son ranta sannan ta miƙe ta nufi wurin Dinnig, abinci ta zuba min a wani plate sannan ta kawo min gabana, ta bani umarnin, "in cinye shi yanzu."
Daga haka tabar wurin ta shige ɗakinta

Dama da yunwa na kwana hanjin cikina sai kaɗa wa suke yi, take yawuna ya tsinke sabida ganin soyayyen dankalin Hausa cikin plate ɗin, nan da nan na saka hannu na dinga ɗauka ina tusa wa a baki kamar zan haɗiye plate din, yanayin cin da nake mishi take na shaƙe ya cika min maƙogwaro ga babu ruwa,
Da sauri na miƙe ganin zan mutu na koma ɗakin da ta kaini jiya da gudu, a can na shiga bayi na sha ruwa a famfon sannan na samu damar koma wa na ƙarisa cinye dankalin har ina lanɗe baki, kwata-kwata bai ishe Ni ba amma babu damar ƙara wa, ga shegen daɗi da yayi min a baki har kunnuwa na motsa wa suke yi,
Na jima a nan zaune kafin ta dawo ta iza ƙeyana ta kaini wani waje, wanda a bayaninta na gane kitchen ne

Duk abubuwan da yakamata in sani sai da ta zauna tayi min bayanin komai, daga ƙarshe ta sanya Ni na taya ta girki ina yin duk abun da ta sanya Ni ina shan zagin ta, don wani lokacin har marina take yi,
Ko kafin mu gama aikin sai da nayi kuka duk ta kumbura min fuska da hannunta,
Kuma bata bar Ni a haka ba; ta saka Ni a gaba na wanke mata duk abun da muka ɓata,
Sannan ta saka Ni shara na share falon na goge duk tana nuna min yanda zan yi, tana jan min kunne, "saura in kuskure kar in koya da kyau, wlh sai ta ɗumama min jiki, duk kuskure ɗaya da zan yi mata kamar na rasa abinci a gidan ne."

Tabbas ban san cewa matar nan muguwa ba ce sai yau da na tsinci kaina a hannunta, lallai yau na tabbatar da cewan na faɗa wata sabuwar rayuwa mai wuyan fice wa, babu tausayi babu imani ga mutanen gidan, sai dai kuma bani da halin bijire musu duk abun da suka sanya Ni dole in yi,
Daga ranan sai na zama tamkar Jaka babu kalan wahalan da ba na sha a hannun Sharhabila, ga shi abu kaɗan sai duka,
A cikin kwana uku cur ta koya min duk abun da yakamata in sani, abinci ne kawai ba ta sakar min dukka amma tana koya min tare muke komai, ina kuskure wa ko ban fahimci wani abun ba sai ta tafka min mari, nan da nan lokaci ɗaya fuskata ta sauya kamanni har wani tara jini fuskar tayi, abun ka da farar mace tuni fuskar tayi jawur sabida tsaban wahala,
Komai na gidan yanzu Ni nake yi, hatta kula da yaransu ya dawo hannuna, Ni nake saka musu kaya na cire musu sannan na wanke, duk in zasu sauya kaya Ni za a kira in canza musu, wanka ma sai yazamana Ni nake musu,
Lokaci ɗaya yaran sai suka saba dani har magana suna min tunda sun ga ina lallaɓa su ina musu duk abun da suke so; Ni kuwa gudun kuskure ne.
Sai ya zamana ko wani abun suka samo in har na ci ne sai su kawo su bani su ce in ci, tun ina ƙin amsa musamman Sadam yayi ta kuka wai, "ya bani abu na ƙi amsa."
Hakan ne yasa nake amsa ina ci bani da yadda zan yi, amma cike da tsoro nake kar Sharhabila ta gane ina cinye mata abun Yaranta

Ai kuwa kamar na san zan sha wahala ne in ta gane, ranan da Sadam ya kawo min ayaba yace, "ga shi Dadyn mu ya siyo ya bamu, kema ki ci wannan."
Har na amsa na ɓare ina ci,
Sai ga Sharhabila ta shigo ɗakin Yaran, tunda a nan nake ina gyara musu ɗakin,
Tana ganina ta daka min tsawa tana cewa, "shegiya muna-fuka dama abun da kike yi kenan, idan na basu abu ki ƙwace ki cinye?"

Baki na buɗe da ninyar yin magana har na fara rantsuwa; amma marin da ta sauke min a kuncina tuni na saka ƙara na kama kumatun ina ihu sabida azaban zafin marin, sauran ayaban da ke bakina dole suka zubo waje tsaban wahalar da ya tunkaro Ni,
Hakan bai yi mata ba sai da ta haɗa da duka tana zagina tare da jan min kunne ta murɗe

Sadam kuwa kuka ya saka yana mai riƙe hannunta da cewan, "Mamy ni na bata fa ta ci, Mamy ki sake ta haka nan Ni nace ta ci."

Wani kallo ta watsa mishi tace, "kai ka bata don Ubanka an ce ka bata ne?"
Sai ta zare mishi ido tace, "idan ka sake ɗauko wani abu ka bata wlh sai na saɓa maka Sadam, ɓace dalla ka bani waje."

Yaron sai ya fita yana kuka har da ƙara volume

Ita kuma ta sake Ni tana cewa, "saura ki zauna ki ɓata lokaci a nan kar ki zo ki ƙarisa min sauran aikin ba, ki kuma gyara musu ɗakin da kyau ko tsinke ba na son gani, ki fito da kayansu ki wanke musu kar ki soma ki saka a inji, da hannu nake so."

Jiki na rawa na amsa mata babu damar sakin kukan da ya taho min,
Sai da na ga ta fita sannan na fashe da wani marayan kuka har da shashsheƙa, ban tsaya ɓata lokaci ba na ci gaba da kimtsa musu ɗakin zuciyata kamar zata fashe don azaban marin da tayi min, har ƙara taɓa wurin nake yi ina mai ci gaba da zubar da hawaye,
Sai da na gama sannan na fita zuwa falon,
Babu kowa sai Yaya Yunus da ke zaune daga shi sai singlet yana shan juice a cup, hannunsa ɗaya kuma riƙe da waya,
Kaina na sunkuyar a ƙasa da ninyar wuce wa, don ban manta gargaɗin da Matarsa take yawan min a kansa ba na dena kallonsa,
Har na kusa isa kitchen na ji muryansa yana cewa, "Kee! Zo nan".
[28/07, 9:33 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 550
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 22*
_____Da sauri na isa inda yake ina mai zube wa a ƙasa jikina na rawa; sabida ganin hakan bai taɓa faruwa dani bane, a tunanina laifi nayi mishi tunda bai taɓa kira na haka ba

Shi kuwa bai ɗago kansa daga duba wayan da yake yi ba, sai ma muskuta zamansa da yayi yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, tamkar ya manta dani kuma can yace, "kira min mai gadi."

"To." Na amsa mishi da sauri ina miƙe wa na fita, sai a lokacin na saki numfashi mai sanyin daɗi ina nufan bakin gate ɗin,
Bayan na kira sa muka dawo a tare zuwa cikin gidan,
Har ƙasa na duƙa nace mishi, "na kira shi."

Bai bi ta kaina ba ya ɗago yana duban mai gadin tare da amsa gaisuwar sa, sai yace, "zaka je ka siyo mana kayan shayi ne."
Sai kuma ya koma kwaɗa kiran Matar shi, "Wifey... Wifey.."

"Na'am, Husband, ina zuwa."

Sum-sum na tashi na miƙe sabida fahimtar aikina ya ƙare a wurin, yayinda na nufi kitchen ina fara tsabtace shi kamar koyaushe kafin a fara amfani dashi

Sharhabila ta fito ta zauna a gefen sa saman hannun Kujeran, tare da cewa, "gani Husband."

"Me da me kika ce ya ƙare? ga mai gadi nan zai siyo kawai, don ba na jin fita." Ya ƙare maganar da ɗaukar kudin da ke ajiye gefen sa yana miƙa mata

Amsa tayi sannan ta kalli mai gadin tana lissafa mishi kayan tea da zai siyo musu,
Bayan ta sallame shi sai ta miƙe ta nufi kitchen, tana shiga ta bi Ni da kallon ƙasƙanci tana ƙin amsa gaisuwa na,
Wadda nayi mata har ina duƙa wa har ƙasa, duk da in da sabo ya ci a ce na saba, don koyaushe in na gaishe ta bata da lokacin ma da zata kula Ni balle ta amsa min, sai dai ta jefa min harara ko kuma ta zage Ni ranƙwashi ya biyo baya, ko kuma duka da tsawa, babu irin hantarar da ba ta min, sam bata da zuciya mai kyau, bata da imani kwata-kwata a zamana da ita na gama fahimtar haka,
Yanzu ma tsaki ta ja tana cewa, "ki yi sauri ki gama don baza ki bar mu da yinwa ba, ki fere arish ɗin nan sannan ki haɗa da ƙwai guda goma, ki tafasa ruwan zafi ki zuba a flaks ki kawo kan Dinnig, saura ki bari in sake dawowa ba ki yi da jiki ba."
Ta ƙare maganar tana juya wa ta fice batare da ta sake bi ta kaina ba

Yayinda na saki numfashin tsoro sabida ganin ta fita salin-alin bata duke Ni ba, da sauri cikin kazar-kazar ɗina na soma gudanar da aikin, tunda aiki ba baƙon abu bane a wurina, nayi na gidan mu ma mai tarin wahala bare wannan da nake ganin tamkar ba komai bane a kan wancan, don haka cikin ƙanƙanin lokaci na gama abun da ke gabana don kar ta sake dawowa ta tarar dani, sabida na san hakan bazai min daɗi ba,
Lokacin da na fita falon har lokacin Yaya Yunus ne zaune yanzu daga shi sai yaran; suna zaune a saman shimfiɗaɗɗen kafet sun saka littafi a gaba suna Home work, kasancewar yau weekend ne shiyasa dukkan su suna gida,
Yaran sai surutu suke yi suna tambayar Dadyn su abun da basu gane ba

Da sauri Sadam ya miƙe zai biyo NI sabida hango Ni da yayi,
Amma sai Sharhabila ta kira sa sabida fitowar ta kenan ta hango sa, ta kwaɗa masa kira tana hararan shi da cewan, "dawo ka ƙarisa aikin ka Sadam, ina zaka je?"

Tura baki yayi yana dawowa da baya-baya, sai kuma ya juya da gudu zuwa wurin littafin sa yana cewa, "Mamy zan taya ta ne."

Hannunsa ta ja ta ƙarisa zaunar dashi tana cewa, "No kar ka sake zuwa inda take, ita ƴar aiki ne ba na son ina ganin ku tare kana ji na?"

Kallonta yayi kamar zai yi kuka, sai yace, "Mamy amma ina sonta Allah, nima zan riƙa koyon aikin ne ina miki."

Sanin halin sa da shegen surutu in ta biye masa, shiyasa ta janye littafan nasu tace, "Oya, tashi mu je kuyi breakfast, sai ku dawo in taya ku Home work din."
Sai da suka tashi suka bar wurin sannan ta kalli Yaya Yunus tana cewa, "Husband mu je mu karya, ina son fita wurin Dady don ya kira ni a kan aikin da zan fara."

Sai lokacin ya ɗago ya dube ta, fuskarsa ya ɗan sanja before yace, "Wifey I don't like this job of yours, ba na son ki sha wahala Please ki bar wannan aikin sabida Ni ban ga amfanin sa ba."

Ɗan waro ido tayi kansa, sai kuma tace, "Ni kuwa na ga amfanin sa Husband, ai dama nace maka ina samun ƴar aiki zan koma bakin aikina, so Ni ba na son zaman nan gwara kawai in riƙa fita ina shan iska, kuma Dady ma ya sake min magana ai ka ga bazan watsa mishi ƙasa a ido ba."

Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya juya kansa yace, "ok mu je mu karya."
Tare suka miƙe zuwa kan daining ɗin, Sharhabila na ci gaba da mishi zancen

Yayinda Ni kuma tunda na jera musu komai tuni na bar wajen na koma kitchen, sai da na sake gyara ko'ina sannan na fito na koma masaukina, ina jiran su gama in je in kwaso komai in wanke, abun da suka rage kuma shine nawa, don bani da rabo a gidan har sai sun ci abinci sun rage sannan nake da damar ci, a haka ta gargaɗe Ni kuma ina bin umarnin ta ba na gindaye wa, sabida ba kaɗan ba ina matuƙar tsoron Matar nan, muguwa ce; komai na san zata iya min in har ta kama Ni da wani laifi, shiyasa koda ƙaramin kuskure ne ba na gigin aikata wa,
Zama nayi na haɗa kai da gwiwa ina tsumayen kiranta, yayinda kewan Ummana da Yaya Haula ya cika min zuciya, su ne kaɗai masoyana a rayuwa; waɗanda nake tuna su a koyaushe kuma nake jin kewarsu fiye da komai, don tuni hawaye sun soma zubo min, nayi saurin sanya hannu na kwashe ina tunanin meyasa Ummana bata zo ta ganni ba? Ga shi yau kusan sati Uku kenan babu ita, bayan tayi min alƙawarin zuwa babu jima wa zata zo ta duba Ni, amma shiru, ko dai ta manta dani ne? Kullum tunanin su yana maƙale a zuciyata, kuka sosai na sha har sai da na ji kaina ya soma sara min, sannan na dakata ina sauke ajiyar zuciya batare da na ɗago kaina daga saman gwiwowi na ba.
***** ***** ***** *****

Yayinda kamar yanda nake tunanin Ummana; haka itama tana can a cikin damuwar halin da nake ciki, tun tafiyana hankalin ta ya gaza kwanciya kawai ƙarfin hali take yi, kuma abun da yasa bata zo ba har yanzu sabida bata da kuɗin transport, sannan bata san gidan Yaya Yunus ɗin ba, dole sai ta kira Haula ta tambayar mata Baffa, shiyasa take jiran sai nayi kamar wata ɗaya sannan ta je ta duba Ni, shima ta daure ne kawai takai zuciya nesa tana danne damuwarta, don ma Hajiya Ummee tana ƙara bata baki tana tausanta tunda ta gane halin da take ciki na damuwa

Shiyasa yau da ta zo aiki gidan, bayan sun gaisa da Hajiya Ummeen, har ta miƙe zata wuce ta fara aikace-aikacen ta, sai tace mata, "Asiya dawo muyi magana mana. Wai kuwa yaushe ne kika yanke zuwa duba Madina? Ai yakamata a ce kin duba ta zuwa yanzu tunda na ga har yanzu kina cikin damuwa, kin kasa sakin ranki."

Cikin sanyin murya Umma ta kalle ta tare da cewa,

Please Login or Register in order to submit comment