Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sulɓi kalan ruwan goro, yanayin rigan sai ya ƙara zamar dani ƴar karama, musamman abun da ya faru daga jiya zuwa yau har wani rama na sake yi, duk na zurzurma nayi zuru-zuru dani sabida tashin hankali, sai idanuna da suka yi jawur suka kumbura suntum, koda ganina ka san babu kuzari da jin daɗi a tattare da Ni, ga tsoron da ya bayyana a tattare dani cike nake da firgici da tunanin koyaushe Yaya Yunus zai dawo ɗakin, dalilin da yasa nan da nan na fita nayi dukka abun da yace, na haɗa shayin na sha da biredi don dole, na kuma sha maganin daƙyar cike da tashin zuciya, duk da rayuwar da nayi a baya da ciwon da nayi yasa na soma saba wa da magunguna, haka na haɗiye dole kamar zan yi amai,
Sai da na jima a zaune ina ƙwannafi ina mayar da nimfarfashi kafin na tashi a daddafe na soma ayyukan gidan, ba wai don zan iya ba sai don tsoron abun da Aunty Sharhabila zata yi min, duk da nayi mamakin ganin bata zo ta hukunta Ni ba a kan rashin aikin da ban yi mata ba jiya,
A jigace nayi komai ina yi ina zubar da hawaye, sai da na gama sannan na koma na kwanta, dayake akwai gajiya nan da nan barci ya sure Ni

Wannan ne ya taimake Ni koda ta dawo ta ga nayi komai, shiyasa bata neme Ni ba bare ta san halin da nake ciki, sai daga baya ne ta ƙwalla min kira a dai-dai lokacin da na farka ina kwance na gaza tashi; nayi shiru ina tunanin rayuwa, yayinda ruwan hawaye ke zuba min masu zafi ina share wa da bayan hannuna, ƙunci da yanayin da nake ciki yasa na rasa abun da ke min dad'i, rayuwar da na shiga a baya ya taɓa Ni matuƙa wanda ba na tunanin dawowan sa, ina mai cike da tsoro da firgicin koma wa wahalar da ya faru da Ni baya, shiyasa a yanzu na gaza samun natsuwa bare in kwantar da hankalina, gani nake yi a koyaushe Yaya Yunus zai gallaza min kamar yanda Alh. Badamasi yayi min, a wannan lokacin tabbas zan iya mutuwa bazan taɓa rayuwa ba,
Ina wannan halin na ji kiran Aunty Sharhabila, tuni na miƙe zumbur jiki na rawa na fita ina amsa wa

Tun daga nesa take bi na da kallo sabida ganin yadda nake tafiya ƙafafu a rarrabe kamar ƴar kaciya, baki sake take bi na da ido kafin tace, "keee! Wannan wanne irin iskanci ne haka kamar wata Agwagwa?"

A daidai lokacin Yaya Yunus ya fito daga ɗaki sabida ba ya wurin yana ɗaki yana shiryawa bai rigada ya fito ba, su kuma suna a kan daining ita da Yaran suna cin abinci, jin abun da take furta wa ne yayi saurin duban wurin da nake, a yanda ya ga ina tafiya sai da shima gabansa ya yanke ya faɗi sabida tunanin sa tsab Sharhabila zata iya gane mene ne,
Ganin yanda na daburce ina shirin yin magana, sai yayi saurin riga Ni da faɗin, "ba na faɗa miki abun da ya faru ba jiya? Maybe garin fita da gudun da tayi ne ta faɗi don shine sanadin da na kira Doctor Bilal ya duba ta, ina tunanin bata warke bane."

Taɓe baki tayi batare da ta damu ba bare ta gane a halin da yayi maganar, sai tace, "ki zo ki kwashe Bags ɗin yaran nan da suka watsar kikai ɗakinsu, ki jira su; su gama cin abinci ki yi musu wanka ki canza musu kaya."

Da sauri na amsa mata ina ƙoƙarin karisa wa wajen kujerun inda suka watsar da takardun su da Jaka, har da takalma, a hankali nake tafiyar sabida yadda nake jin azaba na huro min, amma haka nan na shanye nayi ƙoƙarin yin abun da ta saka Ni cikin dauriya da ɓoye raunina, yayinda idanuna tuni sun cika da hawaye,
Da gudu Sadam ya biyo NI yana kiran suna na tare da cewa, "jiya bai ganni ba? ya tambayi Mamynsu tace mishi nabar gidan."
Ni dai ban kula sa ba haka nayi gaba zuwa ɗakin gudun yin laifi,
Shima ya take min baya; Mamynsa tana kiran sa amma sam ya ƙi dawowa,
A haka muka shiga ɗakin tare sai surutu yake yi min, yawanci duk a kan shirmen sa ne, amma yau halin da nake ciki na gaza kula sa illa ma share hawaye da nake yi a ɓoye gudun kar ya gani,
Shiyasa koda na gama jera musu kayan sai na kwashe kayan makarantar su na nufi dashi cikin bayin zan wanke musu, a bokiti na zuba sannan na kira sa na fara mishi wankan, na sauya mishi kaya sannan ya fita a ɗakin yana kiran sunan Mubashir don shima ya zo a yi masa wankan,
Ko kafin ya zo har na fara wanke kayan,
Bayan ya zo sai shima nayi masa wankan sannan na ƙarisa musu wankin, sai da na ƙara kimtsa ɗakin sannan na fice na kwashe kwanukan da suka gama cin abincin, dayake a lokacin sun rigada sun gama, Yaya Yunus ne kawai yake zaune a falo yana cin nasa hankalin sa yana a kan kallo,
Nima a kitchen na ci nawa sannan nayi wanke-wanke na koma daki tunda babu sauran aiki,
Sau tari wani lokacin sau ɗaya nake girka abinci, sabida ba koyaushe suke cin abu mai nauyi da dare ba, sai dai su sha tea su kwanta, wani lokacin kuma sai tace, "in girka da yawa in zuba a kula in ajiye musu na dare."
Shiyasa aikin yake min sauƙi; sai dai idan ta so mugunta ne zata ƙirƙiro wani abun ta saka Ni dole in yi

Tun wannan abun da ya faru dani da Yaya Yunus bai sake zuwa inda nake ba, tunda ya bani umarnin shan magani kullum sai nake sha gudun saɓa masa bare yayi min hukuncin da yace, haƙiƙa ina matuƙar tsorace dashi a ɗan wannan kwanakin, domin a kullum a fargaba nake kwana nake tashi, sai dai kuma ganin bai sake kula Ni ba sai hankalina ya soma kwanciya har na soma tunanin babu abun da zai ƙara min, amma da zaran na ji muryansa nake lafe wa in ɓoye ba na son zuwa inda yake,
Na fahimci ba sa shiri sosai da Sharhabila don wani lokacin har hayaniyar su nake ji, na rasa mai ke haɗa su, sai dai kawai idan fushin ta ya tashi to Ni ce a wahale don a kaina take ƙare wa, a yanda take zagina da aibata Ni tana min gori, ina gane cewan ta gaji dani ne, kuma tana son in bar gidan amma alamu ya nuna Mijinta ya ƙi bari, shine abun da ke yawan haɗa su

Tabbas ba don son da yake mata ba da tuni ya ci mata mutunci, sabida yanda take son nuna mishi danginsa ba komai bane a wurin ta, ta rantse, "idan har yana son su zauna lafiya sai ya mayar dani ƙauyen mu, don ta gaji da ganina a gidan."
Ya rasa yanda zai yi da ita da fitinan ta,
A haka suke yau faɗa gobe zaman lafiya,
Wannan yanayin ne yasa shaf ya manta da Doctor Bilal yace masa, "ya kawo Ni asibiti a fara duba Ni a ɗaura Ni a magani kan cutan sanyin da ke damuna."
Sai da shi da kansa Doctorn ya kira sa yace mishi, "ya ji shiru fa har yanzu bai kawo Ni ba? Ko ya fi son ya kwasa ne tunda dole zamu riƙa mu'amala?"
Dayake yayi ta mishi shaƙiyanci ne shiyasa yace mishi, "bazai kawo Ni ba."
Shima kuma Doctor Bilal sai naci yake mishi yana cewa, "wlh in bai zo ba zai zo har gida ya duba Ni, sannan ya faɗa ma Matarsa abun da ke faruwa."
Ya san halin Abokinsa shiyasa dole ya yarda ya je da kansa yace, "ya haɗa masa magungunan tunda ba dole sai ya kawo Ni ba, idan kuma ya matsa wlh zasu ɓata tunda babu dole a ciki, ba ya son ya shiga tsakaninsa da Matarsa."

Bilal dai dariya ya dinga masa yana cewa, "kai dai ka sani, nan da lokaci kaɗan zaka zo neman shawara a wurina, mu zuba mu gani na san fa irin ku, yarinyar da ka raina ta zo ta tsole maka ido a nan gaba, wlh ka dena cika baki, kai baka godewa Allah ba ma don Allah ya kashe ya baka?"

Yaya Yunus uffan bai ce masa ba har ya gama maganganun sa ya ɗauki magungunan da ya haɗa masa ya fice yana cewa, "ai sai kayi banza, duk ranan da na sake ta zan faɗa maka sai ka lallaɓa ka je can ka aure ta".*****

Kai tsaye gida ya wuce da maganin bai koma office ba, sabida lokacin tashi bai yi ba,
Shiyasa yayi amfani da wannan damar ya dawo gida ya bani maganin, ya kuma kafa min sharuɗan sha kullum,
A yanayin yadda nake ciki babu bakin tambaya, kawai umarnin sa nake bi kamar yanda yake saka Ni dole ina shan maganin da ban san na mene ne ba, amma zuciyata tana tunanin ko don halin da ya saka Ni ne yake nema min magani? Duk da a yanzu na warke garau har tafiyana ta dawo dai-dai, sai dai yawan tunani da nake yi da koke-koken kewan su Umma, shine dalilin da yasa koyaushe da zazzaɓi a jikina, ga ciwon kai da ya zame min jiki kullum dashi nake kwana nake tashi, tsoron sa da ya dasa min ne yasa ba na iya masa musu bare in saɓa mishi daga umarnin da yake bani,
Haka na amshi maganin na dinga sha batare da na san na mene ne ba,
Sai dai tunda na fara sha tabbas na soma ganin canji wanda yasa Ni ban gane komai ba, a tunanina irin ciwon da nayi a baya ne ya dawo min, sabida yadda Yaya Haula ta taɓa min bayani, kasancewar idan na zuƙuna a bayi ina tsarki sai in riƙa ganin Ruwa yana fita mai kamar warin ƙwai, tabbas na tuna maganganun Yaya Haula dole cutan nan ne da a tunanina ya rabu dani; shine ya sake dawo min, sai dai kuma a nan bani da wannan gatan, bani da wanda zan iya faɗa ma lalura na, tabbas a tsorace nake domin na sha kuka ganin halin da nake ciki, har Allah - Allah nake yi Umma ta sake dawowa in sanar mata da halin da nake ciki,
Duk da na san zai yi wuya in ganta nan kusa saboda a yanzu bata fi wata ɗaya da zuwan ta ba, kuma tana jima wa bata zo ba yanzu tunda hankalinta a kwance yake; tana ganina cikin ƙoshin lafiya wanda ta ga canji sosai a jikina, bata san cewa da irin wahalan da nake sha ba, don dai kawai sauyin yanayin wurin zama ba kamar ƙauye ba a nan

Ko kafin in shanye wannan maganin sai ga Yaya Yunus ya sake kawo min makamancin wancan, a ranan ma haka ya dawo gida ya kawo min sabida ba ya son Sharhabila ta zargi wani abu, tunda ya san fitinan ta. domin sai da yayi min gargaɗin ɓoye wa ina sha a ɓoye,
Lokacin ina kichen ina tsaka da aiki na ji diran Motansa, sai da na firgita sabida a tunanina ko Aunty Sharhabila ce ta fara dawowa ban kammala musu abinci ba, amma kuma ai na san lokacin dawowansu bai yi ba,
Shiyasa lokaci ɗaya na soma ruɗe wa,
Shiru nayi ina maƙe a kitchen din ina jiran in ga wanda zai shigo, sai na ji ana buga ƙofan, shaf na manta na rufe dole sai na buɗe, da guduna na nufi bakin ƙofan na buɗe ina sauke idona a kan Yaya Yunus da ke tsaye riƙe da ledan maganin,
Ai nan nayi saurin ja da baya jikina na ƴar kerma a daburce na soma mishi sannu da zuwa

Shi kuwa baki sake yake bi na da ido sabida ganina da yayi babu hijabin da nake yawan saka wa wani lokacin, don yanzu kwanan nan abun da na tsira yi kenan sabida ganin kamar halittar jikina ya soma canza wa, abun ya soma bani tsoro a cikin wata ɗaya jikina ya soma canza wa, abun da bani dashi sai ga su sun soma fitowa, nan da nan ƙirjina suka soma haɓɓasa wa kamar ana hura balo-balo, da kuwa ko ƙirgan dangi babu kamar allon mayu, kunya yasa na soma ɗan saka hijabi ko kuma in sa kayan da na san yayi min yawa,
Amma yau kuma ina sanye da wata ƙaramar riga ne ƴar kanti da wandonta burgujeje, dayake rigan mai taushi ne sai ta lafe a jikina ta fitar min da ƴan twagwaye na da suka soma bunƙasa gunun sha'awa

Shi Yaya Yunus gani yake yi har wani kutuɓur-ɓur nayi, na ƙara girma a gabansa, kamar ba Ni ba, abun ya matuƙar ba shi mamakin da yasa ya gaza dena kallona idanunsa a zare yana yawo da su a jikina; yana ganin ikon Allah da al'ajabin sauyawa ta kamar almara, don shi gani yake yi ma kamar har wani kyau na ƙara na ƙara haske tarr a ido gunun sha'awa... Tabb! Babbar magana.🤔
[11/08, 4:22 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*




*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 29*
_____Ganin kallon da yake min ne yasa na tsure; tuni hanjin cikina ya kaɗa nan da nan na ƙarisa tsure wa sabida gani nake yi kamar kallon tuhuma yake min, tuni na sauke kaina ƙasa ina rawan jikin da na saba kamar na ga dodo

Shi kuwa daƙyar ya iya ɗauke kansa a ɗan tagwayen nawa da suka tsole mishi ido, ya soma ƙoƙarin dawowa daidai tare da ɓoye mamakin sauyawan nawa, nan take ya taɓe baki a zuciyarsa yana cewa, "lallai yarinyar nan ta soma girma kenan? Kamar ba ita ba."
Janye guntun tunanin nasa yayi yana miƙo min ledan yace, "ga maganin ki, ki haɗa da sauran in bai ƙare ba ki ci gaba da sha, ina fata dai ba asaran kuɗina kike min ba? Kina sha kuwa?",
A yanda ya ƙare maganar ne take na ɗago kai da rawan baki na amsa mishi,
Sai ya jinjina kansa ya juya ya tafi bayan da na amsa ledan, bai sake tunanin sake kallona ba amma har yanzu a ransa yana mamakin mugun sauyawan nawa kamar wata almara, "ko dama haka girman Macen yake ne?"
Tunanin da ya tsaya masa a rai kenan babu mai iya amsa mishi


Ni kuwa ganin ya tafi ba ƙaramin sanyi na ji a raina ba, tuni na mayar da ƙofan ina sauke ajiyar zuciya na tsananin firgitan da ke tattare da Ni, ko kusa ban yi tunanin yanayin jikina ba bare in kawo wani zargin, ɗaki kawai na nufa na ajiye maganin ina mai tunanin, "to wannan wanne irin magani ne ba ya kare wa? Meyasa yake ci gaba da kawo min bayan Ni tuni na warke?"
Jikina ne yayi sanyi sabida tunanin da ina da daman da zan iya faɗa masa matsalata fa? Da ace wannan maganin zai zame min maganin lalura ta da nake fama dashi kullum nake cikin damuwar ciwon, duk da a yanzu ba kamar da ba irin farin ruwan da nake zubar wa, da ƙaiƙaiyin da ke damuna, yanzu da sauƙi -sauƙi,
Ni kuma sam ban gane cewan maganin da nake sha bane yake sake bayyanar min da shi yana fitar dashi a jikina.****

Ashe wannan sauyawan nawa ba komai bane a kan gaba, domin a cikin watanni biyun da suka shuɗe Ni kaina na soma tsorata da yanayin jikin nawa, sabida yadda gaba ɗaya komai nawa ya fashe tamkar ana bani yis ina sha, nayi wani irin girma nayi tsawo kamar ba Ni ce ƴar tsamurarriyan nan ba da wahala tasa na tsamure, amma yanzu kuma sai jikin nawa ya fashe girman ya zo min a ɗan ƙanƙanin lokaci, Ni kaina bazan iya cewa ga dalilin sauyawan nawa ba, amma tabbas ina jin alamomin da dole zan fahimci akwai abun da ke damuna, amma sai dai rashin wayau da rashin tunani bazan taɓa iya cinkan ko mene ne ba, amma tabbas duk wanda ya kalle Ni da idon basira ya san cewa tamkar shigan ciki ne ya mayar da Ni haka, jikina ya sauya nan take na murmure na ƙara haske; ƙirjina nan da nan suka haɓake suka yi fam wanda kunya yasa tuni na dena zama haka nan babu Hijabi, sabida yadda Sharhabila ta soma saka min ido don ita kanta girman nawa ya soma bata tsoro, ba komai ya zo mata a rai ba sai Mijinta sabida ganin yanda na girma na mallaki komai na ɗiya Macen da za a iya kalla, duk wanda ya kalle Ni ba ƙaramin sha'awa zan ba shi ba sabida yadda na koma,
Hankalinta ya soma tashi ne sabida tunanin abun da ka je ya dawo sakamakon sauyawa na haka, ko kusa bata taɓa yi min kallon ciki ne a jikina ba tunda ta san bani da aure kuma ba na fita ko'ina, kuma ta san Mijinta bazai taɓa nema na ba shiyasa ko kusa tunaninta bai kai can ba

Wanda shima tunda ya soma kula da yanayin sauyin nawa tunaninsa ya soma sauya wa, da farko ya ɗauke kai a kaina sabida bazan burge sa har ya iya sake kai kansa gare Ni ba, shima wancan tsautsayi ne don bai manta wahalar da ya sha ba, amma kuma sai me; yanda na ƙara canzawan nan sabida ganina da ya sake yi babu Hijabi, ya ga irin girman da nayi da sha'awan da halittana ta ba shi shiyasa tunanina ya gaza fita a ransa, ya danne tsawon lokaci amma abun ya faskara, don tsab yake tunanin yanda zai mirza Ni a hannunsa in ya riƙe Ni, tsananin bukatana ya ƙi barin zuciyarsa, shiyasa a sace yake kallona yanzu, ada ba ya lura dani tunda ba na gabansa, amma yanzu ko gibta wa nayi idanunsa yana kaina, ko akwai Hijabi ko babu haka zai ta bina da kallo kamar maye, yana tunanin yanda zai yi ya koma gare Ni batare da Sharhabila ta fahimta ba, don ya gama yanke hukuncin dole zai je wurina tunda ai Ni Matarsa ce, bazai zauna sha'awata da kwaɗayin da yake min ya illata sa ba, abu ɗaya ne ya san cewa bazai iya ba in har bai tabbatar na samu lafiya ba, shiyasa yayi tunanin ci gaba da amso min maganin zuwa gobe tunda tun kawo min na biyu bai sake kawo min ba

Ita Sharhabila a tunaninta hankalin Yaya Yunus ba ya kaina ne bai taɓa damuwa dani ba bare in burge shi daga yanayin sauya wa ta, shiyasa hankalin ta ya ɗan soma kwanciya sabida ganin ba na gabansa, amma jefi-jefi takan tayar mishi da zancen, "gaskiya ta gaji da zama da ni, don ya ci a ce yanzu ya mayar da ni gida an sake min wani auren, don bazai yiwu ta ci gaba da ciyar da wata ƙatuwar banza ba."

Bata san cewa jin ta kawai yake yi ba amma ba ya tunanin zai mayar da Ni a wannan gaɓar, don haka sai ya ci gaba da bata baki yana cewa, "ta ɗan jira zuwa wani lokaci da kansa zai ɗauke Ni ya mayar da Ni, tunda har yanzu ban wani jima ba dukka-dukka shekarata ɗaya ne fa."
Da haka zai ta kwantar mata da hankali har ta haƙura,
Da ninyar idan aka jima bai tayar da maganar ba zata sake tayar masa da ɓalli, don tana jin tsoro da zamana a gidan tunda ta san ba Uwa ɗaya Uba ɗaya muke da shi ba, musamman ma ƙawayenta da suke zuga ta tun sanda suke ganina a gidan, suna bata shawaran, "gwara ta kore Ni ta nemi tsohuwa zai fi, don idan aka tashi shammatan ta baza ta ji da dad'i ba."

Basu san cewa tuni an gama da wannan babin ba

Ni kuwa sam ban san halin da suke ciki ba, kawai rayuwata nake yi babu tunanin akwai ranan da Yaya Yunus zai sake bijiro min da makamancin abun da yayi min a baya,
Har da tsoron shi ne yasa nake ƙara ɓoye jikina; amma ban san cewa yana hankalce dani ba, dama kawai yake jira

Ana haka a washe gari da suka fita aiki sai ga Umma ta zo,
Ba ƙaramin farin cikin ganinta nayi ba don ban taɓa zaton ganinta a wannan lokacin ba,
Haka na rungume ta ina farin cikin da rabon da nayi sa tun wancan zuwan nata, yanzu kuwa kusan watanni uku da satikai kenan baya,
Haka nayi ta farin ciki na rasa inda zan tsoma kaina don murna

Ita kanta sauyin da ta ga nayi ba ƙaramin mamaki ya bata ba, wanda tuni a hasashe da kuma hangen nesan ta na matsayin uWa tabbas ta gane ciki ne tattare dani, dole ciki ne a jikina sabida tana ganin sauyin nawa alamun na mai ciki ne, tayi farin ciki matuƙa sosai, lallai ta sake yarda ɗiyarta tana zaune lafiya tunda ga shi har da rabon ciki,
Dama rashin haɗuwar da take yi da Sharhabila shiyasa har yanzu bata gane irin zaman da nake yi a gidan ba, kasancewar tun zuwan farko basu sake haɗuwa ba, har ta zo ta tafi kuwa

Ni kaina na san cewa irin kallon da Umma take min akwai abun da ke faruwa, shiyasa nahau tambayarta har ina ce mata, "har yanzu Yaya Haula bata sake zuwa ta duba Ni ba."

Tana murmushi tace, "ai ba yanzu ba kuwa sabida har da albishir na zo in faɗa miki ma, kwanakin baya Nafisa da Binta sun haihu har sun yi arba'in ma ina tunani, itama Haula ta haihu yau kwana biyar, dalilin da yasa na zo a wannan lokacin ma don in sanar miki ne."

Cikin farin ciki nace, "Umma don Allah da gaske yaya Haula itama ta sake haihuwa?"

"Kwarai kuwa, ta sake haihuwar Mace, dama fama da ciki take yi shiyasa kika ga bata sake zuwa ba, Ni na hana ta tunda ta so zuwa."

Wani irin dad'i ne ya ratsa Ni wanda har sai da hawaye suka tarun min a ido, cikin raunin murya nace, "Umma don Allah ina son in je in ganta, tunda na zo gidan nan ban taɓa fita ba, babu wanda ya zo wurina sai ke, don Allah Umma ina son in je in ga Yaya Haula da abun da ta haifa, nayi matuƙar kewarta."

Hannuna ta riƙe tana cewa, "to meye na kukan? Idan kin tambayi Mijinki yabar ki ai bazan hana ki zuwa ba, ko shi zai kaiki ai, don haka yana dawowa Sai ki faɗa masa ko zai bar ki, amma ina fatan kuna zaune lafiya babu wata matsalar ko?"

Shiru nayi ina mai sunkuyar da kaina na kasa cewa komai, don na san ko giyan wake na sha bazan iya tunkaran Yaya Yunus da wannan maganar ba, mutumin da nake jin tsoransa nake shakkar sa taya ya zan iya faɗa masa har in roƙe sa ya bar Ni zuwa ƙauye? Sabida Umma bata san irin zaman da nake yi na rashin galihu bane shiyasa take furta hakan,
Amma koda ta tambaye Ni sabida sauyin yanayina na kasa faɗa mata komai, to mai zan ce? Ni kaina jikin nawa ya zame min abun kallo ne,
Sai kuma ta koma bani shawarwarin da na kasa fahimtar inda ta dosa,
Bata fito tayi min bayanin abin da take hasashe a kaina ba, amma kuma ta zauna tana ta min maganganun da Ni kaina jinta kawai nake yi

Ana haka sai ga Yaya Yunus ya dawo gidan, abun ya bani mamaki tunda lokacin ƙarfe sha biyu ne na rana

Zuwan nan ne yasa suka hadu da Umma, har suka gaisa cikin mutunci,
Yace, "Umma ashe ke ce a gidan namu? Tun yaushe kika zo?"

Tana murmushi tace, "wlh kuwa, ai ban wani jima da zuwa ba, kuma ina ta zuwa amma muna samun saɓani sai dai tace min kuna wurin aiki."

"Haka ne Umma."

Da haka dai suka ɗan taɓa hira a tsakaninsu har tana faɗa mishi haihuwar Yaya Haula,
Sai yace mata, "ai duk ya ji labari tunda

Please Login or Register in order to submit comment