Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

insha Allahu kafin lokacin komai yayi settling baza ta taɓa gane komai ba,
Ya ɗauki like a two to three minutes a wurin, before ya wuce ɗakin da nake kwance ya bar Ni a sume har lokacin,
Inda nake ya nufa yana kallon fuskata da har lokacin akwai danshin ruwa da hawaye da majinu sun daɓalɓala min fuska,
Toilet ɗin ɗakin ya shiga ya ɗibo ruwa a ɗan wani cup da ya gani a ciki, sai ya zo ya dinga shafa min a fuska don dai in farka

Kamar shuɗewar minti ɗaya sai numfashina ya dawo jikina, sai dai ban buɗe idona ba sai wani irin kuka da na saka har numfashina yana shaƙe wa, sunan Umma da Haula nake kokarin kira ina faɗin, "su taimaka min zan mutu, zai kashe Ni."
Sambatun da nake yi sam ba ya fahimtar mai nake cewa, sai yayi saurin kamo Ni sabida ganin ina jijjiga numfashina na sama da ƙasa,
Rungume ni yayi tsam a jikinsa, wanda gaba ɗaya yanayin da yake ciki na rikice wa jikinsa shima rawa yake yi, a hankali yake furta min saitin kunnena, "shiii Madina, ki yi shiru haka nan don Allah, na bari... na bari wlh bazan sake ba, ki taimaka ki yi hakuri ki dena wannan kukan, babu abun da zai faru da ke."

Tabbas na soma gane abun da ke faruwa yanzu, amma tsoro ya hana Ni motsa wa, tunda na fahimci muryan Yaya Yunus nake ji a kunnena, kamar a jikinsa nake an matse ni gam, Sai kawai na ɗauke numfashi nayi tsit sabida halin ruɗu da firgitan da nake ciki, zuciyata na harba wa kamar zata faso ta fito daga ƙoƙon zuciyata, na runtse idanuna cike da jin azaban da ke suka na tamkar zan mutu, jikina na rawa; haka ma bakina karkarwa yake yi lokaci guda yanayina ya sauya sabida fahimtar da nayi Yaya Yunus ne a tattare dani, tsoron da ke tare da Ni nan da nan ya haifar min da wani irin zazzaɓi mai mugun zafi, tuni na gama fice wa a hayyacina idanuna sun rufe fuskata ta jiƙe sharkaf haka gaban gashin kaina duk gumi ya tsatstsafo min


Wannan halin ba ƙaramin ruɗa Yaya Yunus yayi ba, shi kansa zuciyarsa wani irin buga wa take yi ya rasa inda zai tsoma kansa, ga dai Ni a jikinsa yana ta faman girgiza Ni amma ba na motsi sai numfarfashi da nake yi bakina na karkarwa; alamun zazzaɓin yayi min mugun kamu,
Saurin ajiye Ni yayi yana ɗaukan wayansa ya sake dannawa Doctor Bilal kira,
Ko kafin yayi magana shi Bilal ɗin ya riga sa yana cewa, "gani nan yanzu a bakin gate, bari in yi parking in shigo."
Wani numfashi mai sanyi ya sauke before ya kashe wayan batare da yayi magana ba, sai ya fice cikin ɗakin zuwa falo yana jiran Doctorn

Babu jima wa kuwa sai ga shi yayi sallama ya shigo

Da sauri Yaya Yunus ya nufe sa yana cewa, "Please Dacta mu je don Allah ka ga wannan yarinyar, jikinta gaba ɗaya a rikice yake ban san me ya same ta ba, hankalina gaba ɗaya ya tashi."

Doctor Bilal da nan da nan yayi tunanin ko yarinyar da ya kawo mishi ne, shiyasa bai tsawaita magana ba yace, "mu je, but mai ya same ta?"
Bin bayan Yaya Yunus yayi; shi kuma yana mishi bayani har sanda suka shiga cikin ɗakin,
Kai tsaye wurina suka nufa, yayinda doctorn yake bi na da kallo yana kallon yanda nake ta jijjiga kamar wacce ranta zai fita,
Shi kansa ya ɗan shiga confused, tare da tambayarsa, "anya ba Aljanu take dashi ba yarinyar nan?"
Sai ya kama hannuna ya taɓa ya koma yana Gwale min ido yana duba wa

Yaya Yunus ba ya son wata matsala ta faru, shiyasa kai tsaye yayi masa bayanin abun da ya haifar min da matsalar tun farko

Da mamaki Doctor Bilal yake kallonsa baki sake, a rikice kuma yace, "kuma ka ce min ƙanwarka ce? Taya ya wannan al'amarin ya faru Yunus? I don't understand what you said?"

"Hmm Dacta baza ka gane ba, but zan yi maka explain daga baya, amma zaman da ka ga tana yi a gidan nan akwai aurena a kanta, kawai na ɓoye ne wanda ko Sharhabila ban sanar mata da ainihin wace ce ita a gare Ni ba."

"What!" Yayi maganar baki a hangame yana bin sa da ido kamar wani sabon halitta, domin ya kasa ma wata magana sabida mamakin wai Matarsa ce

"Don Allah doctor ka duba ta, yanzu ba wannan ce a gabana ba, yarinyar zubar da jini fa take yi har yanzu."
Yayi maganar yana mai ɗago Ni tare da ƙoƙarin nuna mishi jinin da nake zubar wa

Shi kuma sai ya gyaɗa kansa yana cewa, "to fa; Allah yasa dai ba raping ɗin ta kayi ba, wannan ƙaramar yarinyar haka da jibgege irin ka ai dole komai ma zai faru wlh."
Ya ƙare maganar da ƴar dariya sabida yayi don tsokana ne

Shi kuma sai ya ja mishi tsaki yana cewa, "wannan fa ba maganar wasa bace, ka duba ta Please doctor kafin Sharhabila ta dawo ta gane mai muke ciki."

Dole Doctor ya shanye maganar da ke ransa ya soma ƙoƙarin duba lafiyata,
A gaban Yaya Yunus yake yin komai tunda ya kasa jirga wa ko nan da can ne, sai da ya gama duba Ni tsab wanda har sai da numfashina ya dawo jikina,
Sai yayi min wata allura nan take kuma na fara barci cikin wani yanayi,
Shi kuma sai ya kalli Yunusan yace, "but ban ga ka ji mata ciwo ba ai; amma na yi mamakin wannan jinin da take fitarwa?"

Cike da damuwa yace, "Yes Ni kaina abun da ke rikita Ni kenan, cus Ni Ko two minutes wlh ban yi ba nabar jikinta sabida azaban da ke ratsa Ni."

"Azaba? Yi min bayani yanda zan gane cus akwai abun da nake hasashe dama musamman wannan ruwan da na gani yana fita kuma."
A cewar doctor Bilal ɗin yana bin sa da ido

Nan Yaya Yunus ya bayyanar masa da halin da ya shiga tun a sanda ya kusance Ni, da raɗaɗin da ya ji batare da ya aiwatar da komai ba

"Gaskiya ina tunanin akwai cutan nan a jikinta na sanyi, ina tunanin yayi mata mugun kamu wanda yasa wurin ya bushe har ka iya jin zafi haka, dama hakan na faruwa, idan mace bata da ni'ima wurin a bushe yake, da zaran namiji ya kusance ta daga shi har ita baza su ji dadin sex ɗin ba, and both ɗin su zasu sha wahala, wasu ma yakan haifar musu da fitan jini cus wurin a bushe yake, hakan na faruwa gaskiya, ita kanta halin da take ciki na ga alamun da tsoro ne na rashin sabo, sai kuma wannan azaban da zata sha, since shi ne na farko shiyasa ko?"
Ya ƙare maganar da sigan tambaya don ya ji mai zai ce

But sai Yaya Yunus ya gyaɗa masa kai don bazai iya ce masa yarinyar ta taɓa aure ba, kuma bai da tabbacin ma an taɓa kusantan ta baya ga shi yanzu, haka kawai ya ji yana son ɓoye masa, cike da damuwa yake cewa, "kenan nima zan iya kwasa tunda ga abun da ya faru?"

"Eh too.. ba lallai ba, ka san Mace ita ce ta fi saurin kwasan cuta nan take, amma namiji gaskiya abun da wahala, sai dai kawai ka nema mata magani ko za a dace sabida gudun gaba; tunda ka ce da aure a tsakaninku, but don Allah yanzu ka bani labarin yanda aka yi ta zama Matarka ina Abokinka bani da labari, ka saka Ni a tunani wlh na kasa yarda, in fact ma har Matarka bata sani ba, to ya hakan ta faru?"

Dole Yaya Yunus ya zayyane masa komai na cewan iyayensa ne suka ɗaura mishi aure da ita, shi kuma da aka kawo ta sai ya nuna wa Matarsa cewan ƴar aiki ce, bata taɓa sani ba har kawo iyanzu

Dariya ne ya suɓuce wa Bilal, yace, "lallai akwai kallon daru duk sanda Sharhabila ta san cewa wannan yarinyar Matarka ce, kutt." Sai ya riƙe baki yana bin sa da kallo tare da murmushi a face ɗin sa

Shi kuma jan tsaki yayi yace, "babu magungunan da za a rubuta mata?"

"Akwai zan rubuta mata, inyaso sai ka bayar a siyo, zazzaɓin zai sauka ma da zaran ta farka insha Allahu, sai dai ka kula da ita don tana bukatar kulawa, kuma yakamata ka zo da ita asibiti a duba lafiyarta sabida a ɗaura ta a kan maganin cutan nan da take fama dashi, domin mugun ciwo ne mai shegen naci musamman in ba a kula da ita ba, and zai hana ka rawan gaban hantsinka Malam, kaii! Gaskiya na taya ka murna, ka samu tsuntsu daga sama gasashshe Alaji."
Sai ya fashe da dariya yace, "oh! Ashe shiyasa kake min wani jan ido kwanakin baya ashe da dalili? sai yanzu na kula kishi ne."

"Bilal ba na son wannan wasan don Allah, in ban da ƙaddara ba abun da zai sa in kawo kaina wajen wannan yarinyar, sai ka ce ban da tausayi? ji be ta ƙwaila ba abun da take dashi sai kawai in rasa wajen wacce zan je sai ita? Ai abun da kunya."

"Ohohh! Amma meyasa zuciyarka ta baka shawaran ka je wurin ta a yanzu after ka san cewa ƙwailan ce? Kai Malam wlh irin su kabar raina su zaka sha mamaki in ta ƙara wayau, haka halittarsu take ka ganta nan ƴar firit sai ta baka mamaki da zaran ta fara nuna kayan ni'imarta a fili."

Mike wa Yaya Yunus yayi yana cewa, "don Allah mu je falo mu ƙarisa magana don ba na son ci gaba da biye maka, amma ka dena min irin wannan abun don wlh ba abun da zan yi da wannan halittar, hakan ma baza ta sake faruwa ba an yi na farko da ƙarshe, wannan ma ƙaddara ce, Kodayake maybe ta silan hakan in taimaka mata tunda na ga alamun lalura ne da ita, amma ko giyan wake na sha bazan sake bibiyan ta in kwashi lalura ba."

Ba ƙaramin dariya Doctor Bilal yake masa ba,
Amma shi ko kula sa bai yi ba,
Sai tsokanarsa yake yi a haka suka fita falo yana sake ce masa, "ban da dai cika baki, ai ƙaddaran da ya kawo sa wurin ta yau ya nemi buƙata; ita ƙaddaran zata sake haɗa su wajen game zuciyarsu ya ji in ba ita ba; sai rijiya...."
A haka dai yayi ta mishi shaƙiyanci har yabar gidan

Shi kuma Yaya Yunus ya fita ya aiki mai gadi siyo mishi maganin da aka rubuta,
Koda ya dawo a falo ya tarar da shi,
amsan maganin yayi yakai ɗakin da nake kwance wanda har lokacin barci nake yi,
Ajiye wa kawai yayi ya fita yana rufo min ƙofan,
Sanan ya koma falo yana tunanin abun da zai ce ma Sharhabila in ta dawo,
Ƙarshe a wurin ya ɓata lokaci ya kasa koma wa wurin aiki, ana kiran sallah ya je yayi ya dawo ya ci gaba da zama, ya rasa mai ke mishi daɗi don yanda yake ta ƙullawa da kwance wa


Ana haka kuwa sai ga Sharhabila ta dawo gidan, ita kaɗai ta shigo gidan tunda bata kwaso yaran a makaranta ba, dama shi yake kwaso su yau kuma kansa yayi zafi ya manta shaf yana zaune a gida,
Sai da ma ya ji shigowar motanta gabansa ya soma buga wa yana fatan kar ta gane komai a kan yarinyar; kar asirin sa ya tonu.
[08/08, 5:36 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 28*
_____Koda ta shigo Falon; ta tarar da shi zaune, bata ce mishi komai ba ta wucewar ta zuwa nata ɗakin,
Shima sai bai kula ta ba ya ci gaba da zama yana saƙawa da kwance wa ta yanda al'amarin zai tafi masa yanda yake so yarinyar baza ta tona mishi asiri ba

Wanka Sharhabila ta soma yi sannan ta kimtsa jikinta cikin kaya masu sauƙi na shan iska, kasancewar ta sha aiki hankalin ta gaba daya ya tafi wurin zuwa cin abinci, ko kusa bata damu da rashin ganin Yaransu ba; sabida ta san tunda ga Dadynsu a gida dole ya ɗauko su,
Sai ta fita Falon tana wuce wa wurin dainng batare da ta kalli inda Yaya Yunus yake zaune ba, sai ma shan ƙamshi take yi don kar ya ga fuskar yin mata magana

Wanda shi yana zaune ne ya kasa tashi don fargaba, shima yana son tashi ya ɗauko Yaran tunda ya ga bata taho da su ba, amma bazai iya fita ba kar wani abun ya faru batare da yayi mata bayanin shirin da ya yake ƙullawa ba

Kamar kuwa ya sani ne, don lokacin da ta isa wurin daining ta ga babu abinci; wani ashar ta liliya tana mai juya wa da kwaɗa kiran sunan Madinan, yayinda ta nufi hanyar kitchen don a tunaninta bata gama girkin bane har yanzu da ta dawo

Yaya Yunus da sauri yace, "Madina bata da lafiya ne, tana can ɗakinta a kwance."

Juya wa tayi tana kallonsa, sai kuma tace, "don bata da lafiya sai ta ƙi mana girki? Kana nufin bata yi komai ba kenan?"

"Eh, sabida nima kaina kirana aka yi mai gadi yace min in zo babu lafiya ya ganta tana ihu ta fita waje; daƙyar ya riƙe ta ma har na dawo gidan, yanzu haka ma sai da na kira Likita ya duba ta har yanzu bata san inda kanta yake ba."

Wani kallo ta watsa mishi tana juya wa ta nufi ɗakin don ta tabbatar, sai da ta je ta ganni a wani mawuyacin hali sannan ta juya ta dawo tana cewa, "to wlh baza ta saɓu ba, sai dai ka ɗauke ta ka mayar da ita ƙauyen su tunda Ni dai bazan yi jinyarta ba, wa ya sani ma Aljanu ne da ita zata zo tana mana hauka a nan? Ka mayar da ita don bazan zauna ina aiki ba sai dai a nema min wata; tunda bata da amfani ita."

Tashi yayi yana bin ta da kallo tare da cewa, "babu inda zata je already na faɗa miki hakan, ita ƙanwata ce idan ke baza ki iya jinyarta ba Ni zan iya."
Daga haka ya juya ya shiga ɗakinsa bai ƙara tanka ta ba, a ransa yana godiya ga Allah da har ya samu Sharhabila bata yi wani zargi ba, saura kuma farkawan yarinyar yake jira, Allah yasa kar ta ɓallo masa wani abun, yana fatan ta tashi lafiya ba wani shedan da zai nuna ya neme ta, don yana tsoron fitinan Sharhabila.
Mukullin motansa ya ɗauka ya fita zuwa ɗauko Yaran su

Ita kuma Sharhabila tuni ta shiga kitchen tana ƙwafa ranta duk a ɓace, sai bala'i take yi tana zage-zage ita kaɗai, a cewar ta; "ta ɗaga mata ƙafa ne na yau kawai, idan har baza tayi aikin ta ba gwara ya mayar da ita ta samo wata, don ita bazai yiwu tana zuwa aiki ta shawo wahala sannan ta zo ta fara aikin gida ba, baza ta iya ba."
Indomie ta girka tunda shi ne mai sauƙi, ta zazzage guda uku ita da yara ta girka musu,
Ko kafin Yaya Yunus ya dawo har ta gama ma.*****

Yayinda Ni kuwa tun wannan barcin da ya sure Ni ban san inda kaina yake ba. Sai da kusan ƙarfe biyar tayi sannan na farka a wani mawuyacin hali, duk da babu inda ke min wani ciwo illa ƙasana da har yanzu nake jin kamar ana watsa min barkono, a lokacin da na tashi na ganni a wannan halin kuka kawai na saka zuciyata na harba wa tare da tashin hankalin abun da ya same Ni, musamman tuna abun da ya faru hankalina ya gaza kwanciya kuka nake yi sosai ina kwance na kasa tashi, shikenan abun da nake gudu ya faru; shima Yaya Yunus mugu ne bai tausaya min a matsayina na ƙanwarsa ba, maiyasa ba na iya kasancewa da farin ciki na ɗan wani lokaci sai wani bala'in ya faru da Ni? Tabbas ba na iya jin zan iya ci gaba da zama a gidan nan; domin wani irin matsanancin tsoron Yaya Yunus ne yake shiga na ina jin kamar zai sake shigowa ya afka min, kallonsa nake yi tamkar Alh. Badamasi sabida abun da yayi min shima,
sosai na ƙudundune ina ta sharɓan kuka wanda tuni ya haifar min da wani matsanancin ciwon kai, hankalina a tashe yake ba na jin zan iya taɓuka komai,
A haka har aka yi kiran sallan magriba ina wannan halin babu wanda ya leƙo ni, Sai da na gaji don kaina sannan na daure na cije na miƙe, daƙyar nake iya taka ƙafana saboda azaban zafi, hakan ne yasa na ƙara fashe wa da wani sabon kukan ina jin tamkar jiri zai kwasar dani sabida rashin ƙarfin jiki da yunwa, a haka cikin wahala da ciwo na shiga bayi na sake fitsarin da ya matse ni tun ɗazu, amma fargaba ya hana Ni miƙe wa bare in yi, bazan iya yin sallah ba a halin da nake ciki don ba na iya tsayuwa sabida jiri, babu inda ke min daɗi a jikina yunwa kamar zan mutu, haka na lallaɓa na koma saman gadon nayi shiru ina ci gaba da matsan hawaye,
A wannan halin na zauna har can dare ina jiran kowa ya kwanta sannan in je in duba sauran abinci in ci,
Sai dai me; koda can dare yayi na fita a daddafe na duba saman table babu komai, hankalina ya tashi matuƙa; nan na saki wani marayan kuka ina mai kifa kaina a saman teburin na ci gaba da rera wani sabon kukan da ya ciwo Ni, ya zan yi da raina; waye sai tallafa min?
Wani irin kakkarwa jikina yake yi kamar zan mutu tsaban yunwa, cikina ya murɗe ga ciwon da ke tattare dani har yanzu ji nake yi kamar ana suka na a can ƙasana, kukan da nake yi nan da nan ya sake haifar min da wani sabon zazzaɓin jikina yayi wani irin zafi kaina sai sara wa yake yi,
Daƙyar na iya janye jikina na ci gaba da tafiya zuwa ɗakina ina yi ina share hawaye,
A hankali na ƙarisa ciki ina tafiya daƙyar a cikin ɗingishi,
Motsi na ji a bayana wanda yasa na juya a firgice, take nayi arba da Yaya Yunus wanda ya biyo bayana sabida ya hango Ni wurin daining, shiyasa ya biyo bayana sabida ya fahimci abun da na je nema,
Ko kafin in saki ihun da na so kurma masa tuni ya toshe min baki ya matse ni gam a jikinsa,
Cikin sauri yace, "shiii! Idan kika yi min ihu wlh sai na mare ki."
Yanda ya ga ina sauke numfashin tsoro a firgice kamar raina zai fice, hakan ne yasa yayi saurin cire hannun nasa a bakina yana cewa, "maza mu je ciki ki zauna."

Wani irin kakkarwa jikina yake yi don na sadakar wani abun ya zo ya kuma yi min, ga tarin tsoron sa da ya mamaye Ni tamkar na ga wani dodo haka jikina yake kerma gunun tausayi, tuni na nufi ƙuryan ɗakin domin bin umarnin sa har kamar zan hantsala, irin saurin da nake yi ne yasa na fashe da kuka sabida zafin da yake ratsa Ni, ko ƙarisa wa wurin gadon ban yi ba na zube a ƙasa ina cure wa wuri ɗaya zuciyata kamar zata faso ƙirji, kallon inda yake nayi a firgice ina ja baya har sai da na ganni a ƙarshen ƙafan gadon, amma yanda na ruɗe sabida ganin yana tunkaro inda nake sai na ƙara tsure wa da tsoro, take na ƙara volume ɗin kukana bakina na rawa nace, "don Allah kar kayi min komai zan mutu, ka cece Ni kar ka taɓa Ni."

Shi kansa ba ya gane abun da nake faɗa, amma ya kula da yanda na firgice na kiɗime ina shirin sume masa, hakan ne yasa ya ɗan daka min tsawa yana cewa, "yi min shiru da Allah can, uban mai zan nema a wajen ki? Ko kina tunanin zan sake miki wani abun ne kike wannan karkarwan? Saura kuma in ƙara jin koken ki yana fita sai na zane ki a wannan daren, shiruu.."
Ya ƙare maganar da wani irin sauri a dake,
Wanda take yasa na shanye sauran kukan har ina kame baki don ruɗu, idanuna da suka kaɗa suka yi luhu-luhu suka fita a hayyacin su; a zazzare suke a kanshi kamar zasu faɗo; sai fitar da ruwan hawaye nake yi masu tsananin zafi

"Ban son shirme ki kama kanki, abun da ya faru ki ɗauka ƙaddara ne don ba ki da matsayin da zan iya haɗa jiki da ke, sannan gargaɗi zan yi miki idan kika bari Sharhabila ta san da wannan zancen... Uhmm."
Sai ya ja numfashi a ƙarshe yana karkaɗa kansa ya ƙara da faɗin, "ki kuka da abun da zan miki."
Juya wa yayi yabar ɗakin

Wani irin kuka ne ya ƙwace min mai tsananin raɗaɗi da ciwo, take na ƙara cure jikina wuri ɗaya na dunƙule kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka mai cin rai, zuciyata sai zafi take min kamar zata faso yayinda take tsintsinke wa tana wani irin buga wa da ƙarfi,
Kukan nake yi sosai wanda nan take na sake jin maganarsa a kaina, take na shanye kukan ina ɗago kai a firgice na kalle sa sabida jin motsin dawowan sa

Kofin hannunsa da ke cike da shayi, tare da biredi ya ajiye min yace, "ɗauka ki shanye yanzu."

Da sauri jiki na rawa na bi umarnin sa, ga tarin tsoron sa da ke ƙara mamaye Ni wanda yasa na kasa masa musu na dauka na soma sha kamar zan yi amai, duk iya jin yunwa na amma tsoro yasa na kasa natsuwa na ci a hankali, haka nayi ta tura wa tunda yana kaina a wurin a tsaye,
Sai kuma daga baya ya ɗauko ledan maganin da ban san dashi ba ya duba ya ɓalla ya bani, yace, "in kora."
Haka na amsa babu musu jiki na kerma nayi duk abun da yace,
Sai da ya ga na gama sannan ya bani sauran yace, "kullum in riƙa sha da safe da dare har sai na shanye, saura kuma in saɓa umarnin sa."
Daga haka yabar ɗakin yabar Ni a wannan halin ina kuka da tunanin Ummana da Yaya Haula,
Sosai nayi kuka a wannan daren wanda yasa jikina ya sake yin zafi zauu, ko runtsa wa na kasa yi sabida ciwo da damuwan abun da ya faru,
A haka safe yayi na kasa tashi a wurin,
Babu wanda ya leƙo ni har suka bar gidan,
Don Sharhabila ko bi ta kaina bata yi ba ta shirya yaranta tayi musu breakfast suka bar gidan,
Shima daga baya Yaya Yunus yayi shirinsa sannan ya taho don ya duba halin da nake ciki,
Shigowansa shi ya tayar dani yana cewa, "in tashi in yi wanka in haɗa tea in sha yanzu, sannan in sha maganina, idan ya kuma dawowa ya ganni a naɗe sai ya saɓa min. Sannan idan ba ki dena wannan koke-koken na muna-furci ba sai na saɓa miki, in ban da shirme yau aka saba miki abun ne da za ki riƙa min raki a gida? Kafin Ni sai da aka yi miki aure amma kin zo kina min shegantaka a gida."
Ya ja tsaki cike da haushina yabar ɗakin, don haka kawai yake jin haushina sabida ya san ba shi kaɗai na taɓa aura ba, amma kuma na zauna ina mishi raki da koke-koke, ya san ai dole Mijin da na aura ya taɓa sani na, duk da dai bai da tabbacin hakan kasancewar yanda ya ji ya shige Ni daƙyar, amma wani ɓangare na zuciyarsa sai ya ji yana mai jin haushin dole sauran wani aka kawo mishi gida, bazai taɓa yiwuwa a ce bai taɓa Ni ba,
Kasancewar shi bai da masaniyar abun da ya faru dani da dalilin rabuwa na da Alh. Badamasi

Tun kafin ya fita ma, jiki na ɓari na tashi na shiga bayi nayi wankan da yace, na saka wata ƴar kanti mai

Please Login or Register in order to submit comment