Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da babu duk ɗaya ne a wurin ta, Madina ita ta zuƙuna ta haife ta; babu mahalukin da ya isa ya jirga da ita a gidan nan, ko me za a yi sai dai a yi wlh basu isa ba."
Haka take kuka tana sambatun nan ranta a mugun ɓace

Daga Ni har su Hussaina kukan muke yi muma, muna cikin daki tare ta rufe mu, ga shi babu Baba a gidan fitan sa kenan, Ni kuwa yanda jikina ke rawa na rasa abun da ke min dad'i, kuka nake yi bil hakki da gaskiya ina ganin shikenan kuma rayuwata zata sake koma wa gidan jiya, shikenan farin ciki zai sake ƙwaurace min, tsananin tsoron da nake ciki da kuma tashin hankalin abun da su Baba Sama'ila suka faɗa; nan da nan wani sabon zazzaɓi ya rufar min, har ba na iya kallon abun da ke cikin ɗakin, kuka nake yi sosai gaba ɗaya na haɗa zufa kashirɓan,
Ga ƴan biyu waɗanda suke rarrashina sun rungume Ni suna kiran sunana, amma sam ba na jinsu, Ni kaina ƙanƙame su nayi ina faman kuka da sambatun, "don Allah kar a tafi dani, Ni ba na son auren, Umma ki taimaka min kar su mayar dani ƙauye, ba na so, mutuwa zan yi."
Daga nan numfashina ya soma sama da ƙasa tun daga lokacin ban sake sanin mai ke faruwa ba,
Sai farfaɗo wa nayi na ganni a gadon asibiti ana yi min fifita,
Daga ni sai Umma a ɗakin a lokacin, tunda na bude ido na ganta sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma rai, zuciyata ta cinkushe ina ƙoƙarin yin magana amma inaa na kasa, bakina a buɗe ina kiran sunan Umman amma babu mai ji sabida yanda na kasa sarrafa harshen nawa

Ita kuma tuni ta kamo Ni zuwa jikinta tana hawayen baƙin ciki, cikin raunin murya take rarrashina da faɗin, "ki dena kukan nan kinji Madina? Gani a tare da ke babu abun da zai same ki, ki yi shiru haka nan kinga ba lafiya kika cika ba."

Daƙyar na iya janyo kalaman nawa da suka maƙale a maƙoshina, cikin wani zafin zuciya wanda ke tafiya da bugun numfashina mai ƙarfi kamar raina zai fice, numfashina gaba ɗaya ya sarƙe amma hakan bai sa na gaza yin shiru da son furta abun da ke raina ba, idanuna gaba ɗaya sun kumbura sun yi jazur sun canza launi, daƙyar nace mata, "Umma, aure suka yi min? Umma zasu.. tafi dani...?"
Ban ƙarisa maganar ba sabida yadda nayi luu na tafi alamun na sake sume wa

Kuka Umma ta fasa tana girgiza Ni cikin tsananin tashin hankali da ruɗewa, take ta miƙe da gudunta ta fita cikin ɗakin zuwa Office ɗin Mashkur

A tare suka dawo cikin ɗakin yana kallon halin da nake ciki, shi kansa a cikin damuwa yake duba da abun da ya faru dani, wani irin tausayina ne yake ji zuciyarsa tayi ƙunci da halin da nake ciki, tabbas ya tausaya min, kamar wannan yarinyar a ce tana fuskantar wannan rayuwar; wanda ko babba ne bazai iya jurewa ba? Yana ganin akwai matsala idan na ci gaba da kasancewa a haka tunda damuwar da ke tattare da Ni ya soma haifar min da babban matsala, babu buƙatar in ci gaba da kasancewa a haka in har ana son rayuwata, dole sai na fitar da damuwa a tattare da Ni, domin idan irin wannan na faruwa da ƙananun Yara kama ta; rayuwar su tana zama in a difficult situation; Wanda hakan na shafan rayuwarsu su tashi a cikin mental issues, ko kuma ciwon damuwa ko ciwon zuciya, daga ƙarshe ma su rasa hankalin su, tunda tun kafin ma su san meye rayuwa; wasu matsaloli masu girma sun addabe su, zasu tashi cikin ƙunci wanda zai hana su samun damar fuskantar meye rayuwar ita kanta.
Tabbas dole ne yayi iya yin sa domin taimakawa yarinyar nan, babu wani doka da ta amince a yi wa yarinya auren dole ko a tauye mata haƙƙinta.
Tunda yayi save na numfashina ya tabbatar da babu wani matsalar kuma, kawai halin tsorata ne da kuma rudin da nake ciki, wanda dole sai ana buƙatar samun hutun ƙwaƙwalwata, dalilin da yasa yayi min allura kenan sannan ya koma bama Umma haƙuri, kasancewar har lokacin kuka take yi,
"Ki yi haƙuri Umma, Ni a ganina in har ana so a ceci Madina daga faɗa wa ƙuncin rayuwa; da kuma ƙwato mata haƙƙinta dole ne sai mun saka hukuma a cikin zancen, tunda ba ta son auren bai kamata a yi mata ba, a wancan ta sha wahala amma tsaban rashin imani yanzu kuma su sake mata wani auren? Wasu irin mutane ne waɗannan? Ai koda suna da hakki a kanta but babu wata doka da ta basu damar tauye ta har haka. Don haka ki kwantar da hankalinki babu mai iya amsar ta, ko meye zamu yi don ƙwato mata haƙƙinta, ki zauna a wurin ta har zuwa nan ta farka, Allah zai bata lafiya, idan ta farka sai a yi gaggawar kira na Please?"

Cikin hawaye Umman ta soma mishi godiya har sai da ya dakatar da ita,
Fita yayi a ɗakin sabida a ganinsa ba ya bukatar godiyan su, aikin sa kawai yake yi, tunda Allah ya haɗa su dole ne su taimaka musu,
Lallai dole ya kira Hajiya Ummee ya sanar mata halin da ake ciki, idan basu taimaka ma yarinyar nan ba za a ɓata mata rayuwa na har abada ne, wannan ai zalunci ne, sun cutar da ita da yawa.
***



_____Baban Sasa kuwa ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba ganin sun dawo babu Madina, da kuma yanda suka yi da Umma da suka sanar mishi, yace, "shikenan zai nuna mata iyakan ta kuwa, lallai in bata bada Madina ta dawo gida ba wlh sai tayi nadamar sanin su, bata isa ta wulaƙanta su ba, ba hukuma ba ko waye zata kai ƙara wajen su shi ya san matakin da zai ɗauka a kan duk wanda ke da hannu a kan maganar."

Baffa da ransa bai dad'i ba da duk abubuwan da ke faruwa, domin ya ɗauki alkawarin bazai yarda a sake wulaƙanta wa Madina rayuwa ba, yanzu kuwa dole ne ya shawo kan Baban Sasa domin sassauta wa a kan lamuran, abun farin cikin ma da kasancewar Madina Yunus take aure, yana ganin wannan dama ce ta same shi domin ganin Rayuwarta ta inganta, tunda Yunus a birni yake da zama dole ne ya shawo kan Baban Sasa a danƙa Madina a can gidan da yake zaune, ba wai zamanta a ƙauye ba,
Wannan dalilin ne yace wa Baban Sasa, "don Allah idan da hali shi akwai alfarman da yake so ya nema wa Madina, na tabbata idan Asiya ta ji inda ƴarta zata zauna baza ta yi jayayya ba, Ni da kaina zan je in fahimtar da ita wanda aka ɗaura wa ɗiyarta, da kuma inda zata zauna, maimakon da ka ce Madina zata zauna a gidan nan nashi da ke ƙauye, mai zai hana Yaya ta zauna a can birnin kusa da shi Yunusan zai fi, na tabbata Asiya baza ta ƙi ba, sannan maganar nan fa har da hukuma za a sako, ka san halin su babu abun da baza su iya ba, ka bani dama in je birnin in fahimtar da ita, tunda babu wani gata da ya wuce auren Madinan, sannan ma ba a nan zata zauna ba na tabbata in ta fahimce mu komai zai daidaita."

"Kana nufin in janye maganar kawo Madina nan ƙauye ta zauna kusa da mu? Kar ka manta nayi hakan ne fa domin nima ɗana ya dawo kusa dani hankalinsa ya karkato wajen mu."

Baffa gyara zamansa yayi yace, "ƙwarai kuwa Yaya, ai tunda aka yi auren nan dole ne Yunusa hankalin sa ya karkato kanmu, ba wai dole sai Madina ta zauna a nan ba, abun da zamu yi kawai don kwantar da hankalin Asiya shine Madinan ta soma zama a can birnin, na tabbata nan gaba da kansa Yunusa zai iya dawowa da ita nan don ya riƙa leƙo mu, amma ba wai mu ɗauki zafi ba, domin a can akwai waɗanda suke taimaka mata kuma ga dukkan alamu manyan mutane ne, ai na san ka ga Matar da suka taho ƙauye tare da ita?"

Shiru Baban Sasa yayi duk da har lokacin bai saki fuskarsa ba, cike take da fushi da tsantsan ɓacin ran da ke cikin ta; wanda alamun bai yarda da maganar Baffa ba har yanzu, don gani yake yi kamar Asiya ta ci galaba a kansu ne, har kamar Asiya zasu zauna sai abin da ta so zasu yi? Bayan ƴar tasu ce ko'ina za a je,
Amma da Baffa ya ci gaba da ba shi baki yana sake fahimtar dashi gwara a bi hanyan lafiya a bi komai a sannu,
Wanda su kansu su Baba Iro da ke wurin daga ƙarshe suma sun goyi bayan maganar Baffa, sun kuma sake sanya baki wajen tausan Baban Sasa, sun ce, "ko ina Madina ta zauna ai dole tana ƙarƙashin ɗansu ne, kuma auren yana nan a kanta tunda bata bijire wa umarnin su ba, dama zaman auren shi suka fi so tayi, don haka ko'ina ta je wannan ba damuwar su bane in har tana tare da Yunusan, ba sai dole ta zauna a nan ƙauye ba."

Sai lokacin hankalin Baban Sasa ya kwanta har ya amince da Baffan ya je birnin ya fahimtar da Umman, idan ma bata yarda ba zai ɗauki mataki don dole,
Sannan daga nan sai ya ba Yaya Nasiru umanin kiran Yunus a yau ya zo ya same shi, ko me yake yi ya ajiye ya zo ya same shi,
Tunda shi bai san ma wainar da ake toya wa ba, bai san da auren da aka yi masa ba yana can hankalin sa kwance, kwatsam! Sai ya ji wannan kiran da dole aka tilasta masa biyo ƙauye da yammaci ya zo don jin ba'asi

Bayan ya iso a danƙareren Motansa; ƴan uwa da abokan arziki suka mamaye shi ana murnan ganin sa, daga ƙarshe suka shiga cikin gidan inda ya sauka a sashin iyayensa,
Matan gidan sai tururuwan zuwa gaishe shi suke yi kowa da ƴar abun tarban sa,
Babu abun da ya ci tunda bai saba cin abun ƙauyen ba, ko an mishi tayi bazai iya ci ba, in fact ma ko ruwa bai sha ba haka suka gama gaisawa har kowa ya watse aka ragu a sasan, ya rage daga Ƙanninsa su Yaya Nasiru su ke zaune da shi ana ɗan taɓa hiran yaushe gamo

Inna Lami kuma na kichen tana mishi girki tunda basu san da zuwan nashi ba, don haka nan da nan aka sanya yara suka siyo Taliyan Yara aka shiga girka mishi, tunda sun ga irin ciman su ne na gayu ta san bazai ƙi ci ba, kasancewar ko a kwanakin baya; irin sa tayi ta dafa wa Matarsa da Yaransa don sun ƙi cin komai sai shi

Yanzu ma da ko ruwa bai sha ba, sai Yaya Shamsu yace, "ko a siyo mishi ruwan leda ne ya sha tunda ya ƙi shan ruwan gidan?"

Murmushi kawai yayi ya girgiza kansa yana cewa, "bazai sha bane, idan ma zai sha akwai ruwa a cikin motansa zai ɗauka ya sha."

Tunda suka ji haka sai basu sake mishi tayi ba,
Babu jima wa kuma sai ga kiran Baban Sasa yace, "ya zo ya same shi."
Hakan ne yasa ya miƙe ya fita yabar su Yaya Ahamdi a nan wurin shi kuma ya wuce sashin Baban Sasa,
A lokacin shi kaɗai ne a zaune yana jiransa,
Sai da ya zauna suka gaisa ya tambaye sa iyalansa? Sannan yace mishi, "ka ci abinci bayan ka zo?"

"A'a Baba, ba na bukatar komai tunda ban daɗe da cin abinci ba."

Kansa ya jinjina yana mai sake tanƙwashe ƙafafunsa, yakai duba ga Yaya Yunusan da ya sauke kai ƙasa yana jiran ya ji abun da yasa aka kira sa da wannan yammacin bai shirya wa hakan ba, kiran sunansa da Baban Sasa yayi, shine dalilin ɗago kansa yana duban sa shima tare da amsa wa a cikin sanyin murya, don gaba ɗaya ya soma sarewa da wannan kiran, haka kawai yake jin ba alheri bane kiran nan, ta wani ɓangare na zuciyarsa buga wa take yi alamun akwai abun da zai same shi

Baban Sasa kuma gyaran murya ya sake yi yana cewa, "akwai hukuncin da muka yanke ne wanda ban nemi ra'ayin ka ba; duba da cewa na isa da kai sabida kai ɗana ne na cikina, a kaf cikin gidan nan babu wanda ban isa dashi ba, babu kuma wanda ba na iya yanke hukunci a cikin rayuwarsa kai tsaye batare da sun yi min jayayya ba, domin in nuna iko a kanka shiyasa na yanke wannan hukuncin kuma na kira ka in sanar maka, na san ka san Madina ƴar wurin Babanka Sule wanda ya rasu, tana ɗaya daga cikin Yaran da aka yi wa aure wancan zuwan da kayi nan ka halarci auren su, to maganar da nake maka yanzu haka auren ta ya mutu tun kwana biyu da aka kaita, na san ba lallai ka sani ba amma yanzu haka na mayar da auren a kanka, shekaran jiyan nan aka ɗaura maka aure da ita..."
Wani irin zabura da Yaya Yunus yayi shine ya dakatar da Baban Sasa daga maganar nasa, wanda ya bi shi da kallo fuska a turɓune yana son ya fahimci halin da yake ciki,
Shi kuma Yunus tsananin kiɗiman da yayi ne yasa shi shiga wani hali wanda nan take zufan tashin hankali ya soma keto mishi, har yanzu kyawawan idanunsa a zare a kan Baban Sasan yana son ya gaskata abun da yake faɗa masa,
"Ya na ganka a haka kamar baka yi farin ciki da abun da na faɗa maka bane? Wannan umarni ne kuma ba na neman shawaran kowa akai, a baya ka saɓa mana wanda mun so mu haɗa ka aure da Dije ƴar wurin Baffonku Abdullahi; amma ka bijire ka kawo ra'ayin kanka, in har ba wai ka gagare mu bane ina so daga yanzu ka shirya tarban Amaryan da muka yi maka a koyaushe, da zaran mun amso ta a wurin Mahaifiyarta zan sa a kawo ta har can inda kake zaune, don haka ya rage naka ka zauna da ita ko akasin hakan..."

Taran numfashin Baban Sasan yayi cikin tsananin tashin hankali da kiɗiman da yake ciki; tare da furta, "amma Baba Ni yaushe nace maka ina bukatar wani aure? In fact ma Ni da nake birni taya ya zaka ɗauki ƴar ƙauye ka ce zan iya rayuwa da ita?"
Sai ya soma girgiza kansa da ci gaba da faɗin, "impossible Baba! Ni rayuwata ta bambanta da naku wlh bazan iya zama da wata bayan Matata ba, sai dai ku canza wata shawaran..."

Tsawa Baban Sasa ya daka mishi wanda har jikinsa rawa yake yi tsaban yanda ɓacin rai ya nuna a kan fuskarsa, duk da dama a cikin ɓacin ran yake ga shi yanzu Yaya Yunus yana son ƙara masa, take ya nuna sa da yatsa yana cewa, "bazan zauna ina jayayya da kai ba, umarni ne wannan Yunusa, kuma ba a haife ka da har zaka zauna kana bijire wa abun da na gindaya ba, wlh ka ji na rantse maka idan baka yi abun da nace maka ba; to daga yau zan cire ka a kan zuri'ata; zan tsine maka albarka ka bi duniya a kan ƙin bin umarni na, shashasha mara hankali mara tunani, har Ni zan yi magana ka zauna kana faɗa min ra'ayin kanka? Ni ne Mahaifinka don haka ya zama dole ka zauna da Madina ko kana so ko ba ka so, zan gani idan ban isa da kai bane".



_Happy Juma'at Masoyana, enjoy your day, Allah ya bamu alkhairin da ke cikin ta._
[22/07, 9:49 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 19*
_____Shiru Hajiya Ummee tayi har sai da ta gama sauraron sa; kana tace, "Mashkur ina ga mun makaro a kan batun wannan yarinyar, kamata yayi a ce mun taimaka mata tun kafin wannan al'amarin ya shigo, amma a yanzu bani da wata fawan da zamu iya fito na fito da su, tunda na farko dai su ne Danginta; dangin Mahaifinta, waɗanda sun zama dole gare ta, dama taimako ne ya haɗa mu da Mahaifiyarta, amma yanzu tunda sun sake mata wani auren ina ga ko mataki zamu ɗauka baza mu samu wani ƙwarin gwiwar tunkaran su ba, a gabana Ɗan uwan Mahaifin yarinyar ya zo yana fahimtar da Umman nata, wanda Ni da ita mun ɗauki fushi matuƙa amma yayi ta bamu haƙuri har yana faɗa mana dalilin su na sake mata wani auren, ka san ƙauye komai su a al'ada suke ƙarewa, suna mayar da abu ƙarami babba ne, to a halin yanzu ɗan gidan aka ɗaura ma Madina wanda a bayanin shi Mutumin yace a nan cikin birnin ma yake da zama, can low-cost, ni a ganina ban ga abun tashin hankali ba a ciki yanzu, wanda ina kyautata zaton yarinyar nan Rayuwarta zata sauya Insha Allahu tunda ba daƙiƙi baƙauye suka ba auren ta ba, don haka na taushi Uwar ƙwarai kamar yanda na zauna muka fuskanci juna ta sanar min bayani a kan Yaron, don Ni a ganina zata fi jin dad'i ƴarta tana nan kusa da ita; da a ce an mayar da ita can ƙauyen tana auren wani baƙauye, bamu da abun yi tunda an rigada an sake mayar da auren ta da wani, kuma bazai yiwu mu mu zama silan mutuwar aurenta ba; yarinya ƙanƙanuwa kamar wannan a ce tayi aure har biyu babu ɗaya a ciki, ya kake ganin rayuwarta zata kasance a nan gaba? Hakurin dai shi ya fi tunda Allah ne ya ƙaddara mata hakan a Rayuwarta, ya halicce ta a cikin wasu irin mutane masu wuyan sha'ani, mu dai fatan mu kawai mu bi ta da addu'a mun yi iya yin mu, idan akwai abun taimako a nan gaba sai muyi mata, amma babu buƙatar dole sai mun shige gaba wajen ganin an raba auren nan."

Da kallo Mashkur yake bin ta dashi har zuwa ƙarshen dogon bayanin nan nata, ga dukkan alamu kyakkyawar fuskarsa ta nuna alamun rashin jin daɗin furucin ta, wanda har ya nuna a kan fuskarsa ya gaza ɓoyewa, domin har a zuciyarsa shi ya ɗauki Madina tamkar ƙanninsa waɗanda suka fito ciki ɗaya tare ne, abun da zai yi wa Naja'at da Khairiyya; haka zai iya yi wa Madina yarinyar da ta shiga ransa yake jin tsananin tausayin ta; bisa ga mummunan ƙaddaran da ta riske ta tun kafin ta san wace ce ita kanta? Haka kawai yake jinta har a cikin ransa, kuma yana burin ya taimaka mata, wannan zalunci ne da bai kamata su bari yana faruwa ba, don haka a cikin rashin jin dadin kalaman Kakar tasa yake cewa, "yanzu Hajiya, kina ganin ya dace mu bar waɗannan mutanen su cutar da yarinya karama Kamar wannan? Idan mun bar su fa mun so ne, akwai hanya da dama da zamu ƙwato mata haƙƙinta, babu ta hanyar da aka ce a yi wa yarinya auren dole, muna da kuɗin da zamu iya ɗaukaka mutanen nan ƙara ko ta ina. Ansar lauya ne, ko shi zai jagoranci al'amarin ta, bare na san ko Dady ya ji wannan zancen zai goya mana baya."
Sai ya ɓata fuska daga ƙarshen maganarsa yana mai sake yamutsa ƴar farar fuskarsa wadda har yanzu take nuna tsantsan rashin jin daɗin sa, "Hajiya don Allah mu duba wannan al'amarin, ina jin yarinyar nan kamar Khairiyya ko Naja'at ne, mutanen nan basu cancanci rangwami ba, koda sun kasance Iyayenta bai kamata su tauye mata haƙƙi ba, and sannan baya ga ita; sun cutar da Mahaifiyarta ma tunda suna nuna fifiko fiye da ita."

"Duk da haka Mashkur dole mu yi hakuri mu fauwala wa Allah; domin haka ƙaddaranta ta zo, baka gane bane; Ni ba na so mu kashe mata aure kamar wannan yarinyar ta sake zama Bazawara a karo na biyu, Mace ce ita, hakan zai shafi Rayuwarta, mutanen nan sun shammace mu sun rigada sun yi mata wani auren, kamar yanda na ba Mahaifiyarta haƙuri har ta iya saurarona; haka kaima zaka yi haƙuri Allah ya ga zuciyarmu, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi, kawai ka bar zancen nan."
Sai ta sauya akalar maganar batare da ta sake jin ra'ayin sa ba, "yanzu yaushe ne zaka sallami yarinyar tunda na ga alamun jikin da sauƙi?"

Sai da ya ɗauki good seconds kamar bazai ce komai ba; alamun abun har yanzu yana cin ransa, haka kawai bai san meyasa ya damu ba, amma yana ganin kawai sabida yanda tausayin yarinyar yake tasirantuwa a cikin ransa ne, but tunda haka tace dole ne ya cire komai a ransa since babu amfanin taimakon nata, daga haka ya furta da faɗin, "i think zuwa gobe zan iya sallamanta, na faɗa wa Mahaifiyarta ma."

"To Allah ya kaimu goben ya nuna mana aron kwana."

"Amin." Ya amsa yana janyo wayansa daga cikin aljihun wandon sa, ya mayar da hankali akai kamar bazai sake magana ba, sai kuma ya ɗago a bazata yana cewa, "Hajiya, Ni fa ina ga wannan weekend ɗin zan tafi Kaduna, kuma kinga yakamata in koma a kan course ɗin nan da nake son zuwa Abuja in yi, zan je mu tattauna da Dady."

Da wani yanayin kallo ta dube sa tana cewa, "wai dole ne sai ka ƙara karatun nan ne Likita? Ni fa ba na juren irin wannan karatun da ke tsamurar da ku; ku fake dashi ku ƙi yin aure, gaskiya i don't believe that, hankalina yanzu ba a kwance yake ba; na damu a kan zancen auren ku, still shiru kai baka ce komai ba, bare wancan ɗan ƙwal uban kar ma a yi labarin sa, sannan Farukh bai yi muku faɗan hakan ba duk da jan masa kunne da nayi but yayi biris shima bai ce komai ba, to ina ga wallahi lokaci yayi da zamu yi sadakar ku, don na gaji da ganin ku haka."

Bai san sanda murmushi ya suɓuce daga kyakkyawar fuskarsa ba, yayinda ya kawar da idonsa a kan kallon wayan nasa yana fuskantar ta sosai; cike da farin ciki da nishaɗin da nan take ya yalwata a kan fuskarsa, sai ya cije leɓe cike da shaƙiyanci irin wanda wani lokacin suke wasan Jika da Kaka yace, "Kai Hajiya Ummee, Ni fa na kula tsoron mutuwa kike yi batare da kin ga ƴaƴan mu ba, ko in ce ki taƙwarƙware batare da kin goya takwaranki a baya wacce zan fara miki ba, to kwantar da hankalinki tamkar kin yi filo da macizai ne suna saranki; very soon labari zai sauya don baza ki mutu batare da kin ga ƴan jikokin ki ba..."
Daƙuwan da take mishi shine yasa ya dakatar da maganar nasa yana dariya sosai, wanda ganin yanda ta taƙume fuskarta shi ne dalilin darawan nasa batare da ya shirya ba

"Lallai Farouk, yanzu na san irin zaman da zan yi da kai, amma da Uwarka zan yi don ita yakamata a ce na faɗa ma abun da kake min, ai ba Ni zaka yi wa takwara ba sai dai ka yi wa Uwanka, ka riƙe takwaran ba ita nake fatan samu ba, don Ni na wuce da sanin ta, don haka kar ma ka ɗauki maganata da wasa don a wannan karon zan tayar muku da ɓalli ne, maganar nan naka zuwa Abuja Insha Allahu tare da Mata zaka tafi don shi ne burina a yanzu, shima wancan uban shiriritan dawowa zai yi ya nema mata ko a dangi ne a haɗa ku gaba ɗaya a aurar, meye amfanin zaman ku haka muna da Yara kyawawa a dangi?"

Ya san halin Hajiya tunda ya ga ta sauya fuska tana maganar da haƙiƙanin gaskiyar

Please Login or Register in order to submit comment