Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"yanzu zasu koma in har bata dena kukan nan ba, tunda tana ɗaga musu hankali."
Hakan ne yasa dole ta shanye kukan nata har suka ɗan jima a asibitin sannan suka tafi, ko gidan Umma basu je ba suka wuce don a halin da suke ciki babu wanda zuciyarsa take mishi dad'i, tabbas sun tausaya min ba kaɗan ba, sun tafi da jimamin halin da nake ciki, suna ganin kamar bazan kai gobe ba sai wani ikon Allah, kowa yana min fatan samun lafiya a ransa; yayinda zuciyoyinsu a karye cike da sanyin jiki haka suka koma gida

Umma tun ranan da na farka ita take zama dani, tunda a halin da nake ciki dole sai tana kusa dani, don Ni kaina ba na barin ta jirga a jikinta nake kwance, dole sai tahau kan gadon ta riƙe Ni,
Baba ne kaɗai yake koma wa gida tunda shima kullum sai ya zo musamman in ya dawo daga sana'arsa, wani lokacin yana tahowa da su Hassana sai su duba Ni tunda su kansu a damuwa suke rayuwa, sai dai kasancewar yadda suke ɗaga hankalin su sai ya dena zuwa dasu sosai, sai idan an kwana biyu sannan suke zuwa

Ita kuma Hajiya Ummee ita ta ɗauki nauyin kawo mana abinci asibitin kullum, ko bata zo ba zata aiko driver dashi a kawo, itama sosai take kula damu don an zama ƴan uwa yanzu, tana jin mu tamkar ahalin ta, tana kallona tamkar jikarta, shiyasa ba ta gajiya da mana hidima

Shi kuma Mashkur dolen sa ya dena zuwa duba Ni koda ina barci ne, dole Dr. Jamila ce take min komai har lokacin da komai ya soma lafawa, tamkar komai bazai wuce ba haka rayuwar take tafiya, amma kuma yau da gobe tun ban saba da halin da nake ciki ba har na soma saba wa, musamman kasancewar akwai UmmanA a tattare dani, tunda tayi min alkawarin, "baza ta taɓa barina ba, zata zauna dani a koyaushe."
To yawan buɗe idanuna ina ganin ta a tare dani; shi ne yasa hankalina ya soma kwanciya har na fara ƙoƙarin saba wa da halin jinyar da nake ciki, ita take min komai ba ta bari Nurses suyi min, don da ita na fi yarda,
Tunda na ga Yaya Haula ta sake zuwa na ganta ido da ido; sai hankalina ya sake kwanciya ainun,
Sai dai ashe wahalar na gaba sabida har na soma jin sauƙi kuma aka sake min wani sabon aikin, gaskiya na sha wahalar da Ni kaina bazan iya misalta shi ba, tamkar an sake famo min asalin kyambon ciwon ne, ciwon ya sake dawowa sabo dal haka na sha jinya kamar bazan rayu ba, na sake sauya wa fiye da baya, na rame nayi baƙi a wannan lokacin ko abinci ba na iya ci sosai sai dai a bani ruwa-ruwa sau ɗaya a rana, hakan ne yasa na ƙara lalacewa gaba ɗaya halin jinya yasa na sauya kamanni, komai sai dai a yi min don na fi satikai ba na iya zama da ɗuwawu na

A takaice dai sai da na shafe watanni uku curr sannan na soma samun lafiya sosai, nayi jinya matuƙa; na sha wahalar rayuwa wanda ban taɓa tunanin zan rayu ba,
Duk wannan lokacin babu wanda ya sake tako kafansa daga gidan mu sai Baffa da suke zuwa akai-akai shi da Yaya Haula, su kaɗai ne suke zuwa duk cikin Iyayenmu, sai su Yaya Shamsu da suka zo sau ɗaya suma basu sake zuwa ba,
Ta hakan ne kaɗai suke samun labarina, tunda idan Baffa ya koma gida yana faɗa musu halin da nake ciki,
Ita kanta Haula sai lokacin ta samu natsuwa, sai lokacin ta kwantar da hankalinta tunda ina samun lafiya, ga shi komai ya soma wuce wa kamar ba a yi ba, ƙanwarta tilo ɗaya Allah ya bata lafiya kamar bata yi ciwo ba, sai fatan samun lafiyarta gaba ɗaya

Ganin jikin da sauƙi komai ya soma lafa wa, shiyasa Dr. Mashkur ya ci gaba da zuwa duba Ni, tunda gaskiya irin wahalar da na sha ba ƙaramin tausaya min yayi ba, matuƙa na shiga ransa da yawa wanda yake ganin bazai iya jure rashin zuwa ganina har ya ƙi kula dani ba,
Sai dai halin da nake nuna wa har yanzu bai sauya ba, tunda kwata-kwata ba na son tozali da wani namiji sai hankalina ya tashi fiye da tunanin su,
Umma ce ta zauna tayi min bayanin komai tana faɗa min, "shi ne Likitan da yake kula dani, in dena jin tsoransa shi ba mai cutar wa bane a gare Ni."
Yawan rarrashina da take yi da son fahimtar dani waye shi, shine har na soma saba wa da rage jin tsoron sa, amma duk sanda ya shigo sai hankalina ya tashi na kasa kallonsa har sai ya fita, duk abun da zai yi min bazan kula sa ba, kuma bazan kalle sa ba har jikina yayi ta rawa, sai ya fita nake samun natsuwar zuciya, domin wahalar da na sha a rayuwa a wajen Alhaji Badamasi bazan taɓa manta shi ba, ya cutar dani cutar da baza ta taɓa gushe wa daga zanen zuciyata ba, yayi min tabon da kowanne namiji na gani dole zan riƙa kallonsa da wannan yanayin, domin a wannan lokacin ba na fatan na sake koma wa ƙauyen mu, ina ji a jikina na baro sa har abada sai dai akai gawana can, domin bazan taɓa iya jurewa ba, a yanzu Ummana na fi buƙata a wurina, ita kaɗai nake son gani a tattare dani, zama kusa da ita ya fi min samun natsuwa, hankalina zai fi kwanciya, Maraichin da na kasance a ciki tsawon lokaci ina ƙulafucin uwa; a wannan lokacin zan samu, domin bazan taɓa bari a raba Ni da UmmanA ba, duk inda ta saka ƙafa dole sai na bi ta

Komai ya soma sauya wa tunda ga shi har ana tunanin bani sallama, tunda na warke garau sai abun da baza a rasa ba, tun aikin da aka yi min na biyu aka samu nasaran da na dena yoyon fitsari, yanzu haka raman da nayi ne kawai ban koma dai-dai ba, tunda har yanzu akwai damuwa a tattare dani, tunda hankalina bazai taɓa kwanciya ba in har ina tunanin ƙauyen mu da rayuwar da nayi a baya, duk da a yanzu Umma ta tabbatar min da cewan, "bazan taɓa koma wa can ba, a wajenta zan zauna tare da ƴan uwana su Hassana."
Sai dai hankalina har yanzu ba a kwance bane tunda na san waye Baban Sasa, in har bai amince ba na tabbata sai yasa an dauko Ni, hakan ne ke ƙara tayar min da hankali

Ana haka sai ga Yaya Haula ta sake dawowa ita kaɗai, wannan karon ko Ihsan bata taho da ita ba ta zo duba Ni, kuma kwana zata yi tunda da yammaci ta zo

Ai kuwa ba ƙaramin murna nayi ba, haka na rungume ta ina kiran sunanta kamar bakina zai tsage don farin ciki,
Wanda yanzu basu saba ganin hakan ba a gare Ni, sai dai a yau din ganin farin cikina ya fi musu komai har suna jin zuciyarsu ta sake sanyi ganin na saki jikina ina ta farin ciki da surutu, har ina tambayarta, "meyasa bata taho da Ihsan ba?"

Murmushi tayi itama tace min, "ai Ihsan ta girma sai ta zaɓi inda take son zuwa, tunda nace mata wajen ki zan zo, sai ta botsare wai baza ta je ba, ƙarshe ma guduwa tayi ta tafi wasanta."

Sai nace, "yanzu Yaya Haula da gaske ta ƙi zuwa ta duba Ni Ko? Shikenan nima zan dena kula ta tunda ba ta so na."

"Ki yi hakuri ƴar ƙanwata, kin santa da tsoron mota ba ta son ana hawa da ita mota shiyasa ba ta son zuwa, tace min wai kashe ta zata yi daƙyar fa muke zuwa ta dinga min kuka in muka biyo hanya zamu hau keke napep."

Umma ce tayi ƴar dariya tana cewa, "ina ruwan takwara ta, sai shegen tsoro kamar farar kura."
Sai ta miƙe kuma tana haɗa wasu daga cikin kayan da suke wurin, tace ma Haula, "ta kula dani bari ta je ta dawo."

Yaya Haula tace, "to Umma sai kin dawo."

Tana tafiya Ni kuma na kwantar da kaina a jikin Yaya Haulan ina ce mata, "Yaya don Allah ki ɗaure min wannan kan nawa, duk ya dame Ni sai ƙaiƙayi nake ji."

Hannu ta sa tana duba kan nawa tare da cewa, "wai kuwa ana wanke kan nan kuwa? Kinga yanda duk ya koma yayi datti da yawa, bari a wanke miki sai in miki kitso ko ƙwara huɗu ne."

Ita da kanta ta shiga bayin ta tara ruwa ta sake sauran ruwan zafin da muke dashi a Flaks, sai tayi min wanka da kanta ta wanke min kan nawa sosai,
Skirt din jikina na sako na fito a bayin ina rawan sanyi sai karkaɗa jikina nake yi ina rakin, "akwai sanyi a garin, da na sani ban bari an yi min wankan ba."
Dayake ita tana bayi bata kula Ni ba itama tana ɗauraye jikinta,
Ina zama a kan gadon na ƙanƙame jikina ina yarfe kaina,
Sai ga Dr. Mashkur ya shigo ciki da sallama,
Da sauri na ɗaga kai na kalle sa nan da nan turaren da yasa ya cika ɗakin,
Da alamun yanzu ya zo sabida yanda ya ɗauki wanka sai ƙamshi yake yi, yayi kyau cikin ƙananan kaya farare sol da siririn eye glasses da ya sanya, kyakkyawar kamilalliyar fuskarsa ta sake haske da kwarjini,
Dayake ina a tsorace ne nan da nan na miƙe da ninyar guduwa cikin bayin, ina zuwa bakin ƙofan sai ga Yaya Haula ta fito itama, nayi saurin ƙanƙame ta ina ɓoye wa a bayanta da sauri,
Ita kuma ganin halin da nake ciki har ta tsorata, don bata kula da Mashkur ba sai da yayi magana, hakan ne yasa ta gane dalilin guduwa na wanda shigowar sa ne yasa na firgita haka,
Hannuna ta riko tana wuto dani ciki tare da gaishe shi cikin girmamawa

Shi kuma sai bai shigo ciki ba ya tsaya a wurin yana kallon mu, fuskarsa yalwace da murmushi ya amsa mata, sai yace, "Haula ko?"

Cikin kunya Yaya Haula ta duƙar da kanta tana amsa mishi, don duk in ya ganta sai ya tambayi sunanta tunda yana yawan manta wa, wannan dai shine haɗuwar su na huɗu kenan amma bai wani riƙe sunan ta ba

Hannunsa ya saka a aljihu yana mai sake tambayarta, "ina Ihsan?"

"Tana gida na barta."

"Good." Ya furta yana ɗauke kai a kanta, ya sake kallona wanda ina manne a bayanta na ƙi motsa wa, shi dai har a zuciyarsa ba ƙaramin burge shi nake yi ba, yana ganin kyawun mu wanda har yanzu ba ƙaramin mamakin ƙanƙantar mu yake yi ba, a ganin sa kamar Yaya Haula wai har da auren ta da ƴa ita kanta tayi ƙanƙanta; bare Ni da yake ganina kamar ya ɗauke Ni ya riƙa jefa wa sama, bai san meyasa yake jin ya damu dani ba matuƙa, kuma halin da na shiga da abun da ya faru dani tun kallon farko da yayi min ya matuƙar sosa mishi rai, shi dai ya ɗauke mu tamkar ƙanninsa ne shiyasa yake jan mu a jikinsa,
Yana tsaye a wurin ya ƙi shigowa har lokacin, ganin shirun yayi yawa mun haɗe kai mun ƙi cewa komai, sai ya canza shirun da sake tambayarmu Umman namu?

Yaya Haula ce wannan karon ta sake ba shi amsa, a cewar ta, "yanzu Umman ta fita ta je ta dawo."

Shiru yayi sai kuma yace, "ok, idan ta dawo sai ki sanar da ita ina office."
Abun da ya furta kenan ya fita bayan ta amsa mishi

Yana fita tamkar an tsamo Ni a ƙaya, sai na sake numfashi mai ƙarfi wanda yasa Yaya Haula ta juya ta bi Ni da kallo,
"Wai lafiyarki Madina? Mene ne?"
Ɗan waro idanuna nayi wadanda suke a waje har yanzu sabida jinyar nan da nayi, sun yi zuru-zuru sun firfito sun ƙara haske sun yi narai-narai dasu na mara sa lafiya, fuskata a kwaɓe nace, "Yaya Ni ba na son ganin mutumin nan, tsoro yake bani."

"Tsoro kuma Madina? Likita ne fa bazai cutar da ke ba."

"Ni wlh ba na son sa, ba na son ina ganin kowanne namiji, gani nake yi kamar wancan mugun Mutumin ne."
Nayi furucin hawaye na fara zubo min nan da nan

Saurin kamo hannuna tayi ta dawo dani gabanta, sai ta soma rarrashina cike da tausayina tana cewa, "babu abun da zai kara faruwa da ke ƙanwata, wannan likita ne ki dena jin tsoron sa, shi taimakon ki yake yi idan kina jin tsoron mutane ki dena saka shi a ciki, ba ki ji mai Umma tace mana bane? Tace mu riƙa ce mishi Yaya Mashkur, kinga ai bazai cutar da mu ba, idan kina irin wannan tunanin za ki riƙa shiga damuwa mu kuma ki ɗaga mana hankali, maza ɗauko ledan kayan ki in zaɓa miki wanda za ki saka tukunna."

Da sauri na juya na ɗauko batare dana ce komai ba sabida yadda nake jin sanyi na ratsa Ni, don na ƙosa na saka kaya, ina ɗauko wa na bata sai na koma zame skirt din jikina na koma babu sauran kaya a jikina, na tsaya ina jiran ta har ta ciro wanda zan sa,
Wando ta soma bani na saka sannan na ɗago zan amshi doguwar rigan

A lokacin ne sai ga Mashkur ya sake shigowa cikin ɗakin,
Har razana nayi sabida ganin sa, sai nayi saurin koma wa gefen Yaya Haula ina ɓoye fuskata

Shi kuma sai ya bi Ni da kallo yana ɗan murmusawa, a wannan karon sai yace, "My sister meyasa kike tsorata ne idan kin ganni? I'm your brother; Stop being afraid, I have nothing to say to you."

Daga Ni har Yaya Haula bamu fahimci abun da yace ba daga ƙarshe, Ni dai tunda na duƙar da kaina ban sake cewa komai ba

Shi kuma sai yayi kamar bai damu ba illa bin mu da kallo da yake yi, cikin natsuwarsa tare da nuna kula wa yace, "ki gama saka mata kayan akwai gwajin da za a yi mata yanzu ki kawo ta Office ɗina."

Da sauri Yaya Haula tace mishi, "to." Tana amsan rigan tare da ƙoƙarin sanya min

Shi kuma sai ya fita batare da ya sake furta wata kalma ba, sosai ya sake ganin ƙanƙanta na wai kuma a hakan ne aka yi min aure, mamakinsa to wai meyasa ƙauye suke yi wa Yaransu aure tun basu balaga ba? Ji be dai wannan yarinyar ƙanƙanuwa da ita ko cika Mace bata yi ba amma har an yi mata aure? Dariya ce ta suɓuce masa sabida tunanin idan na haihu kuma ko da wanne Nonon zan shayar da Yarana oho? Tunda shi dai bai ga komai a ƙirjina ba balle a ce zan iya shayar da yaro in na haifa, "kai suma ƙauyawa da jaraba suke, Allah ya kyauta."
Ya furta a zuciya yana ƙarisa shiga cikin Office ɗin sa,
Wayansa a hannu yana latsa wa sabida kiran da yake son yi,
Wani number ya latsa wanda ya rubuta "My blood Brother"
Zama yayi a saman chair ɗin sa yana kara wayan a kunne, sai da aka yi peaking da jin saukar muryan da yake buƙatar ji, hakan ne yasa ya gyara zamansa cikin kamalansa da tausassan muryansa yake cewa, "ba ka jin magana Ansar, I told you to stop talking to me before salam, I don't like that, I will stop answering your calls tunda baza ka dena ba."

Daga can wata murya mai kama da nasa take furucin cikin ɓacin rai, duk da yana maganar ne da sanyin murya but sai da hakan ya nuna a kan voice ɗin sa,
Wanda hakan ne yasa Mashkur sauya akalar tambayar nasa da faɗin, "what's wrong with you? Wa ya taɓa min kai?"

Cikin yanayin maganarsa da Hausa ba ta fita sosai; kuma da yanayin fitan sautin muryan da sauri yake cewa, "wannan shegiyar yarinyar ce ta ɓata min rai, but forgot this issues, ina Hajiya na kira wayanta ba ta zuwa?"

Guntun tsaki Mashkur ya ja yana cewa, "kai baka da magana sai maganar wata ta ɓata maka rai ko? Ansar Why don't you leave this life? Idan aure kake so ka dawo gida mana a yi maka ka huta da wannan banzan rayuwar, ka san su Momy ransu yana ɓaci ko? They thought that now you have changed your behavior, but not so..."
Katse maganar yayi sabida ganin mu mun shigo cikin office ɗin, sai ya ƙara da faɗin, "zan kira ka ina da patients, ka kira numban ta i know network ne babu; ban jima da fitowa gidan ba."
Daga haka ya janye wayan a kunnen sa jin ya amsa mishi, sai ya ajiye yana kallonmu yanda ya ga na maƙale a bayan Yaya Haula ko leƙowa ba na yi,
Telephone na office ɗin ya ɗauka batare da yayi mana magana ba ya hau daddannawa zai yi kira.***




Duk wani abu da yakamata an yi min a ranan, wanda ya tabbatar da cewan babu wani abu da yayi saura a tattare dani, illa magunguna da aka bani sannan aka rubuta mana sallama,
Nayi farin ciki matuƙa; dukkanmu ma mun yi farin ciki tunda yau an sallame Ni zamu koma gida

Umma tana dawowa muka tattara kayanmu gaba ɗaya, Mashkur da kansa ya ɗauke mu ya mayar da mu gida a daren nan,
Tunda na ganni a gida sai hankalina ya sake kwanciya, wanda na tabbatar da cewan bani ba koma wa ƙauyen mu

A washe gari ma Yaya Haula kamar kar ta tafi haka take ji itama, amma kuma babu yadda zata yi tunda kwana ɗaya Mijinta ya bata, zuwa yamma ta wuce gida

Baffa shi ya kira ta ya tambaya jikin nawa? Tunda wannan karon bai je ba, kuma ya jima bai samu ya je ba kasancewar yanda damina ta shiga sosai suna aikin gona, bai samu ya zo ba,
A nan Haula take sanar mishi da sallaman da aka yi min

To wannan dalilin ne har su Baban Sasa suka san an sallame Ni,
Sai dai shi bai ce komai ba don kamar bazai yi magana ba, kowa ya zura ido ya ga matakin da zai ɗauka musamman da yace zai sake min aure

Ita kanta Yaya Haula fargaban ta shine Baban Sasa yace sai an dawo dani ƙauyen, amma jin shiru bai ce komai ba tunda ta san sun sani sai hankalinta ya soma kwanciya,
Ga shi har lokaci ya ja kusan ina kan rufa wata ɗaya a gida ban ji daga ƙauye an zo tafiya dani ba,
Shiyasa nima hankalina ya kwanta haka itama Ummana, tunda itama ba ƙaramin fargaba bane a ranta, ta san tabbas idan sun yi ninyar ɗauka ta dole ne sai sun ɗauke Ni, kasancewar sun fi ta iko a kaina, dole ko kotu aka je suna da damar amsa ta, musamman da na kai wannan munzalin tunda ba yarinya bace Ni,
Har mun yi tunanin ƙura ta lafa rayuwata ta soma sauya wa na saki raina da tunanin buɗe sabuwar rayuwa, ashe ba haka bane, babu wannan jin daɗin a rayuwata, Ni ba mai Sa'a bace da har zan iya tsallake wannan ƙaddaran tawa, ba a haifo ni a cikin jerin waɗanda zan yi rayuwa cikin farin ciki ba,
Mummunar labarin da ya kusan tarwatsa min rayuwata gaba ɗaya, wanda ya dawo dani cikin ƙuncin da nayi tunanin nayi bankwana dashi har gaban abada

Ashe Baban Sasa ya ɗaura min aure da ɗansa Yaya Yunus, wanda kowa yayi mamakin babban al'amarin, duba da wane ne Yaya Yunus a gidan mu, da kuma girman shi; ya wuce a haɗa shi aure da ƙwaila ƴar ƙauye irina,
Kowa ya kasa magana tsaban mamaki da al'ajabin wannan hukuncin da Baban Sasa ya yanke, yayi mugun yin musu bazata,
Wanda kuma ya yanke ne don ƙashin kansa, domin jefo tsuntsu biyu da dutse ɗaya, yayi hakan ne don ya nuna wa Umma cewan; su ke da iko da Ni fiye da ita a duniyar nan, kuma dole in dawo ƙarƙashin su in zauna,
Sannan yayi hakan ne domin ya samu damar dawo da ɗansa gare sa, duk da Yaya Yunus a matsayin ɗansu ne yake amma basu da iko a kansa, yayi musu rata da nisan da sun kasa tanƙwara shi, a koyaushe Baban Sasa yana zama da baƙin cikin rasa ɗansa da ya nuna ya fi karfinsu bare yayi musu biyayya, wanda sai su shafe tsawon lokaci basu sanya shi a ido ba, don haka a ganin sa idan ya haɗa auren sa dani dole ne ya riƙa ziyartan su akai-akai, sannan ma tunda yana da gidan sa da ya gina a ƙauyen, a nan zan zauna ko don dolen sa ya riƙa zuwa duba Ni, wannan hanyar ce kaɗai yake ganin zai bi domin Yaya Yunus ya dena nisa da gida, kuma wannan auren umarni ne ga dukkanmu; babu wanda ya isa ya tsere masa, zai yi fito na fito da duk wanda yace zai bijire a kan maganar

Allah Sarki! Ashe somun taɓi ne a kan ƙuncin rayuwar da na taɓa fuskanta, ashe ba a fara ba ma, yanzu ne sabon feji na daga cikin ƙalubalen rayuwata zata buɗe. Wayyo Ni Madina! Meyasa sai Ni rayuwa zata juya wa baya haka?.
*****

Abun da ke faruwa sam Alh. Badamasi bai sani ba, don tun tafiyar sa da kusan watanni uku ya aiko aka kwashe masa iyalansa kaf, waɗanda suka yi aure kawai ya bari tare da nasu iyalan, don suma yana da tarin gonaki ne a nan shiyasa ya bar musu su kula mishi dashi, tunda suka ga haka suka tabbatar da cewan Mahaifin nasu guduwa yayi a kan abun da ya aikata, mutanen gari ba wanda ya ji labari sai da Iyalansa suka tafi,
Yayinda shi kuma bai damu da wata *RAYUWAR MADINA* ba don ya san cewa Bokansa already yayi masa aiki a kanta, ya gama sakankance wa ita da aure har abada, koda tayi auren ma baza a taɓa jiƙa masa aikin sa ba tunda Already Boka yayi masa aiki a kan haka, don haka bai da wata damuwa, yanzu sai buɗi da yake samu har aiki ya soma ci; ya soma ganin albarkan abun.
[21/07, 8:33 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 550
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 18*
_____Da Yaya Manniru da Ya Ahmadi; sai Baba Sama'ila. Su suka zo tafiya dani a bisa umarnin Baban Sasa, da kuma sanar wa Umma aurena da aka ɗaura a jiya Alhamis

Tashin hankali! Umma fa hankalin ta yayi ƙololuwar tashi jin maganar da suka zo mata dashi, bama wai tafiya dani zasu yi ba, a'a an sake ɗaura mini wani sabon auren, lallai waɗannan mutanen basu so zaman lafiya ba, don Umma kuka ta saka tace, "wlh babu wanda ya isa ya tafi dani, ko uban waye ya ɗaura auren nan sai dai ya je ya kwance amma babu inda zan je baza ta bada Ni ba, idan kuma suka matsa mata sai dai takai su ƙara."

Duk yanda suka so su fahimtar da ita umarnin Baban Sasa ne; amma sam ta ƙi fahimta, dayake babu mai zafi a cikin su sosai, don Baba Sama'ila bai iya husuma ba, gwara Ya Ahmadi don shi so yayi ya tafi dani ta ƙarfi da yaji, yace, "sam baza su koma babu Ni ba dole sai sun tafi dani."

Umma kuma na kuka ta shigar da ni cikin daki ta rufe tace, "ta rantse sai dai in mutuwa tayi sannan zasu wuce dani, wannan ai zalunci ne, a kan me zasu mayar mata da ƴa wacce bata da galihu don kawai suna dangin Mahaifinta? nan tayi jinyan ta amma babu wanda ya bada ko sulen sa domin a nema mata magani, duk wata wahala da ta shiga su ne sila, sun kassara wa ƴarta rayuwa sannan hakan bai ishe su ba zasu zo su sake jefa ta a wani sabon bala'in, to wlh basu isa ba in har tana raye da auren da suka yi

Please Login or Register in order to submit comment