Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi wani irin firiricewa sabida jinina da ke ƙarewa, amma su basu san da haka ba, basu kaiNi asibiti ba tunda ba sa kai Yaran su asibiti, kula dani kawai ake yi ana min maganin gargajiya sai toshe min gaba ake yi da wasu abubuwa duk don jinin nawa ya tsaya, daƙyar aka samu ya tsaya

A ranan Yaya Haula sai a gidan mu ta kwana domin hankalin ta ya ƙi kwanciya, kuka take tayi dole Mijinta yace, "ta je ta kwana dani tunda hankalin ta bae kwanta ba."

Sai goshin asuba na farfaɗo, sai dai ba na iya gani sai dishi-dishi, hakan yasa na saki kuka a hankali wadda muryata gaba ɗaya ta dishe ba a jin kukan nawa sai hawaye da ke zubar min sosai

Ganin na farka da gudu Yaya Haula ta fita ta sanar da jama'ar gidan,
Nan da nan sai ga su sun shigo har da su Baban Sasa sai sannu ake min, nan aka ce, "a ɗaga Ni a bani maganin da aka ajiye min domin jiran farkawa na."

Sai dai babu inda nawa ke motsi duk yanda aka yi da ni haka nake bi, har yanzu ba na ganin Mutanen da ke cikin ɗakin sai maganganun su da ba na ganewa, yayinda bakina sunan Umma kawai yake furtawa sai dai babu mae ji na, da haka ina jin yanda ake ta ɗura min maganin a baki sai dai kawai in buɗe baki in amsa ana riƙe dani, daƙyar nake iya haɗiyewa shiyasa duk yake zuba a ƙasa, daga ƙarshe aka bani abinci sannan aka kwantar da Ni, raɗaɗin da nake ji a jikina bazai taɓa iya misaltuwa ba, haƙiƙa nayi tunanin mutuwa zan yi sabida azaban da nake sha, gani da raina amma ba na sanin abun da ke faruwa, ba na iya magana sannan ba na iya gani, sai dai jin murya, a koyaushe ina iya jiyo muryan Yaya Haula da kukanta da yadda take rarrashina, amma ko na buɗe baki da ninyar kiran sunan ta in yi magana domin in faɗa mata irin tsananin zafin da nake ji a ƙasana; ba na iyawa, harshe na ba ya furtawa, sai dai in ta hawaye wanda ke nuni da tsananin azaban da nake sha

Yaya Haula ta kasa jirgawa ko nan da can ne tana nan tare da Ni, lokaci bayan lokaci tana min sannu

Amma Ni idanuna a rufe suke still hawaye suna sauka a kan kuncina, ko na buɗe ido ba na iya ganin ta, ko nayi yunƙurin yin magana ba a ji na, shiyasa tunda na kwanta a haka ban sake motsawa ba, sai dai azaban da ke ratsa Ni ji nake yi kamar mutuwata ta zo ta same Ni, ko kaɗan ba na buƙatar ci gaba da rayuwa, a yanda nake ji gwara in mutu in huta da irin baƙar azabar da ke ratsa min can cikin jikina. A haka barci ya ɗauke Ni ba tare da na sake sanin me ke faruwa ba

A yanda nake saukar da numfashi da ƙarfi ina shashsheƙa hakan ya tabbatarwa da Yaya Haula barci ne ya sure Ni, sai a lokacin ta saki ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya tana saka hannu ta shafo kaina har zuwa dogon gashi na da yake baƙinƙirin ba shi da cika sosai, ko kaɗan ba shi da yawa tamkar kan yarinya, sai dai ina da yalwan gashin saje wanda ya saukar min har wajen kumatu na, koda na rufe kaina da ɗankwali dole zaka fuskanci cewa ina da yalwan gashi domin ba ya rufuwa; koda hula na sanya kuwa, abun da ke ƙarawa ƴar tsukakken fuskata kyau kenan, tabbas bamu da bambanci da Yaya Haula domin kamannin mu ɗaya ne zarr, itama haka take da sajen nan domin ita har ta fi Ni yawan gashin kai, sai dai kawai bambancin mu Ni na fi ta hasken fata ne sannan kuma ina da lotsatstsen gemu, ƙasan gemu na yana lotsawa musamman idan nayi murmushi, dai-dai gwargwado Allah ya bamu kyau tunda duk mun biyo Mahaifinmu ne, kuma haka ƴan gidan mu gaba daya suke da kyawu, ɗaiɗaiku ne basu da haske a duk faɗin gidan mu, Kakannin mu duk Fulani ne makiyaya, Asali Kakan mu shi ya soma kafa ƙauyen nan wanda har ga shi yanzu tayi rassa ta ko ina, don ma wai wasu suna tashi su koma cikin birni ne sabida kidnappers da suka addabe mu a shekarun baya, sai da aka tashi tsaye da addu'o'i sannan aka samu salama, wanda ina ji a wajen iyayen mu an kafe Garin ne shiyasa aka samu sauƙi ba sa shigowa, ko sun zo kusa da ƙauyen sai dai su kewaye su wuce baza su taɓa shiga ba

Yaya Haula ta jima a ɗakin kafin ta tashi ta fita, ta yiwa Mutanen gidan sallama sannan ta wuce gida, sai a nan ta samu tayi ɗan aikace-aikacen ta wanda dama Matar Yayan Mijinta duk tayi mata wasu abubuwan, kasancewar suna zaune lafiya ana mutunci sosai tare, duk da ita wancan Matar har da yaranta guda biyu da ta haifa, kuma ta girmi Yaya Haula sosai domin ba yarinya bace, ko kaɗan ba ta ƙyashin Yaya Haula tana janta a jiki sosai, kafin Yaya Haula ta saki jiki a gidan Mijinta Rabi'u duk ita ta koya mata wasu abubuwan, ita take sanya ta a hanya shiyasa Yaya Haula bata sha wahala sosai ba, ga shi uwar mijin su Mace ce me kirki duk tana nuna musu ƙauna kamar ƴaƴan cikin ta, kasancewar bata da Yara mata sai su biyun kaɗai da ta haifa Maza, shiyasa take kulawa da Matan su tunda su kaɗai gare ta, Yaranta suna sonta sosai suna mata duk abun da take so duk da Allah be hore musu ba sosai, shiyasa itama take yin iya ƙoƙarin ta wajen ganin sun ji daɗin zama da ita basu yi kuka da ita ba.

To yau da gobe a haka nake ta jinyan jiki na, tun ba na sanin abun da ke faruwa azaba tayi min yawa, har dai yanzu na soma gane wasu abubuwa, duk da ciwo sosai nayi a cikin sati biyu kacal baza kaso sake kallo na ba idan kayi min duba ɗaya, na rame sosai na fita a cikin hayyaci na, memakon inyi baƙi sai na kwanɗe kamar wacce babu jini a jikinta, to hakan ne amma babu wanda zai taimaka min sai dai ayi ta ɗura min saiwowi shi ne magani na, Yaya Haula ita ke min komai sai wasu daga cikin Ƙannin mu da ake sakawa suna min wasu abubuwan idan babu ita, kasancewar yanda ciwon ya ci ya cini shiyasa su Baban Sasa suke tausayi na sosai, hakan yasa suke bani kulawa dai-dai gwargwado duk da ba wani abun suke min ba, amma suna zuwa akai-akai suna duba Ni sannan su suka sa Matansu su riƙa kula da Ni, duk da babu wanda ke min wani abu domin su kansu ba ta Ni suke yi ba, dama-dama Inna Lami tunda ita ce dama mariƙiya ta, kafin wani yayi min abu ita zata yi min, sauran yaran duk sun warke amma ban dani, kullum cikin tashin hankali nake da koke-koke shiyasa jiki na a koyaushe yake sake rikicewa, ba Ni da aikin yi sai tunanin Ummata ina zuba idanun ganin ta zo, amma sai ga shi har an yi wata ɗaya da min kaciya babu ita babu dalilin ta, tun ina saka rai har na ɗebe tsammanin zuwan ta, tabbas baza ta zo ɗin ba duk da a koyaushe ƙorafi na a kan Yaya Haula, "meyasa Umman mu bata zo ta duba Ni ba?.. don Allah ta kira min ita in ji muryan ta, ko kuma ta je can ta faɗa mata halin da nake ciki."

Yaya Haula takan riƙe min hannu tayi ta bani haƙuri tana faɗin, "Mijin ta bazai barta ta je a nan kusa ba tunda bata jima da zuwa ba, sannan akwai kuɗin mota tafiyan bazai yiwu mata a ƙasa ba tunda basu dashi, wayanta har yanzu ba'a gyara ba shiyasa baza ta iya kira min ita ba, amma in kwantar da hankalina zata zo."

Kullum zancen nata kenan, "zata zo." Amma shiru har yanzu, na san Yaya Haula tana min wayau ne domin in kwantar da hankali na, duk da ina da ƙarancin shekaru amma Allah ya zuba min wayau ba kaɗan ba, na fahimce ta ƙwarai kuma na cire rai da zuwan Umman mu, baza ta taɓa zuwa ba tunda dama ba zuwan take yi ba sai idan wani abu babba ya faru, itama kanta tana fama da kanta shiyasa ba kasafai take zuwa ba sabida halin rayuwa. Shiyasa tun daga ranan na cire komai a raina na fuskanci yanda Allah zai mayar min da rayuwata a nan gaba, nayi ta jinya na tsawon watanni biyu ban warke ba; wanda har hakan ya soma ba wa wasu haushi kasancewar kullum ina ɗaki ba na fita, duk wani aikace-aikace da nake yi a gidan sai dai Matan suyi ko su saka yaran su, ga shi shegen ƙyuya ne da Yaran Ni kaɗai ce ake saka Ni abu a daɗin rai, kuma inyi me kyau babu guna-guni bare ɓata fuska tunda na saba, sun ji daban da wannan ciwon da nayi, shiyasa kowa ya fara jin haushi na tunda na ƙi tashi in taimaka musu kamar yanda na saba, Ni suke tula ma aikin komai Ni ce jakar gidan, tun ban gama warware wa ba tafiya ma daƙyar nake yi domin ba na tashi tsaye sosai, a haka aka soma saka Ni aikin sai dai bani da yanda zan yi haka na koma musu Bauta, abubuwan da suke saka Ni wahalhalun yayi min yawa tunda ba daɗin jikin nawa nake ji ba, hakan yasa kullum a tafe nake ina ciwo kuma babu me tausaya min, na sake fita hayyaci na duk na tsamure, sai idanu a waje kamar zasu faɗo sabida yanda suka zazzago, kasancewar Masha Allah Ina da idanduna, har kuma a lokacin ba na tafiya yanda yakamata, ba na miƙewa tsaye sosai saboda yanayin sauyin da na samu a tare da Ni, tun daga lokacin na san na sanja sosai, ada ni sai in daɗe ban yi ciwo ba amma yanzu tunda al'amarin nan ya faru ba na yin sati ban kwanta jinya ba, ga shi kullum na shiga bayi bayan na gama uzuri na sai inga abu zare-zare yana bi na me kama da jini, ban taɓa damuwa da hakan ba tunda ban taɓa sanarwa kowa ba, ko Yaya Haula ne, ga shegen ƙaiƙayi da yanzu nake fama dashi, kullum bani da aiki sai susa ina kartan jiki na, haka na ci gaba da wannan rayuwan tunda ban taɓa sanin matsala bane bare in sanar da wani, har na saba ma yanzu

A hankali a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya kamar yanda ta saba, ga shi yanzu har mun yi kusan watanni goma da yin mana kaciya, mun manta ma da an yi mana, sai yanzu aka tashi da zancen auren mu gadan-gadan, haka Baban Sasa ya tara jama'ar gidan domin a sanar mana da hukuncin da suka yanke

Jiki na yayi sanyi a lokacin gaba ɗaya na rasa sukuni na sabida ban san wanda za'a haɗa Ni dashi ba, kwata-kwata a raina ba na buƙatar wani aure a rayuwata, Ni da so samu ne a bar Ni in ci gaba da zama a haka, Ni kaina ina mamakin kaina sabida ko ada Ina da samari waɗanda suke so na ƴan cikin ƙauyen, tunda tun muna yara muna sanin soyayya; kasancewar samarin karkara akwai saurin girma, kuma mu ba komai bane don ƙaramin Yaro ya fara samartaka, duk da ban taɓa kula su ba domin ko sun tsayar dani guduwa nake yi sabida kunya, amma kuma yanayin da nake ji a wancan lokacin ya sha bamban da yanzu, ada ina farin ciki idan naji wani ya nuna yana so na, amma yanzu daga Mazan har soyayyar ba na sha'awa, ba na jin bege a tare da Ni, babu shauƙi ko kusa a tattare da Ni

Duk iyalan gidan mu har waɗanda suka yi aure Matan a nan kusa sun zo, su Yaya Haula duk suna nan tare dasu aka zauna zaman taron

A nan Baban Sasa ya soma jawabi kamar yanda suka yanke hukunci, kowanne lokaci su ne masu zaɓa ma Yaran gidan Abokan rayuwa Mazan mu da Matan mu, Binta da Fa'iza su ne aka haɗa su aure da Yayyunmu na gidan, Ni kuma da su Nafisa gaba ɗayan mu ƴan anguwa aka haɗa mu da su, yawancin su daga masu Mata biyu sai me Mata ɗaya, sai dai Ni nawa bayan Matar da yake dashi tsoho ne, domin Mutumin abokin Baffa ne ya girmi Babana kenan, shi ya ganni yace yana so shi ne ya sanar da Baffa, shi kuma Baffa ya zo ya faɗama Baban Sasa, bae Yi la'akari da cewa Mutumin babban Mutum bane yayi jika dani amma nan take ya amince; wanda su kansu gaba ɗaya murna suke yi kasancewar Alh. Badamasi yana ɗaya daga cikin masu arzikin ƙauyen, Matar shi ɗaya kuma ita duk ta haifa mishi yaran shi guda bakwai da ya haifa, har wasu sun yi aure da jikokin sa, sai Ni yanzu da ake shirin haɗa Ni dashi

Su kansu Matan gidan sun girgiza da jin wanda za'a haɗa Ni dashi ɗin, duk da a cikin mazajen sauran duk babu sa'annin shi, babban Mutum amma shi ne za'a haɗa Ni aure dashi, wasu kuma a cikin su baƙin ciki da hassada sai da ya cika musu zuciya sabida gani suke yi nayi goshi zan auri me arziƙi, har suna jin dama Ƴaƴan su ne ba Ni ba

Sun shirya auren nan da sati uku masu zuwa, bayan shekara ɗaya kuma za'a kai ko wacce ɗakin auren ta tunda yawanci hakan ake yi, idan aka ɗaura aure daga baya ake yin shagali, lokacin sauran sun cika shekaru 13 kenan, Ni kuma ina da 12

Daga Ni har Yaya Haula kuwa; hawaye ne kawai yake zirya a kan fuskokin mu, sai dai bamu bari kowa ya fuskanta ba kasancewar yawan da aka yi a wajen, ita tana kukan tausayina ne; nima haka, tare da kukan baƙin cikin wannan rashin gata da za'a yi min, kamar Ni yarinyata a haɗa Ni da wanda ya girmi Mahaifina? Ina zan kai wannan tsohon me ruɓaɓɓen baki? Shiyasa Allah-Allah nake yi in fita in saki kukan da yake cin raina, ana sallaman mu kuwa na fice fit nayi bayan gidan inda babu wanda zai iya gani na; babu wanda zai iya ji na, a nan na saki wani kuka mae tsananin ƙarfi wanda ke fita mun tun daga can ƙasar zuciyata, har wani ɗauke numfashi nake yi sabida azaban maƙaƙin da nake ji a maƙogwaro na, wani abu ne ya tsaya min a wurin kuma ya ƙi wucewa, sai kokawa nake yi da hannuna a maƙogwaro na kamar raina zai fita, inda nake kuka sosai har ba na iya ganin abun da ke wajen, ji nake yi kamar in kwanta in mutu sabida baƙin cikin da nake ji a lokacin yana sake ratsa min zuciya, sai dai babu hali, bani da ikon da zan bijirewa zaɓin su domin ba kaina farau ba, kuma ba'a taɓa yin hakan ba, gidan mu akwai biyayya, ba a ja da maganar Baban Sasa, sannan Mata basu da wani galihu da zasu ɗaga murya har aji koken su, na tabbata da yanzu za'a san mae nake yiwa kuka bazan sha a gidan nan ba, za'a yi min dukan tsiya ne musamman idan suka ga zan zubar musu da mutunci, idan aka yanke magana ɗaya ba a yin ta biyu haka tsarin gidan yake, ko ince haka na taso naga ana yi.
[11/06, 10:03 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎

_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
  _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 4*
 _____Tafiyar da naji kamar za'a zo wurin ne yasa nayi saurin saka hannu biyu ina share hawayen nawa, tare da ɗaura kaina a saman cinyoyina sabida in ɓoye halin da nake ciki, yayinda gabana ke tsananin bugawa da ƙarfi na tsananin tsoro, sai dai kuma muryan Yaya Haula naji a kusa dani tana kiran suna na, da sauri na ɗago kai ina kallon ta a firgice,
Sai dai itama ɗin nan da nan ta ruɗe sabida ganin yanda idanuwana suka koma, ta tsorata da ganin yanayi na shiyasa da sauri ta kamo Ni jikinta tana shafa min fuska tare da tambaya na abun da ya same Ni? Muryanta na nuni da tsantsan damuwar da take ciki,
Kuka na ƙara saka mata sabida tuƙuƙin da ke ci na, ɗazu ma nayi bare yanzu dana samu me rarrashina, nan na ƙara ƙanƙame ta ina kuka sosai kamar raina zai fita

Sai itama ta saki kukan tana cewa, "don Allah ki rufa min Asiri ki dena kukan nan haka kar wani ya zo ya ganmu, Madina kinji kiyi haƙuri ki dena kuka ki ɗauki ƙaddaran ki a haka; haka Allah ya so babu yanda zamu iya, idan kika sanya wa zuciyarki dangana komai zai wuce."

Cikin kuka sosai na ɗago idanuwana ina kallon ta, cike da shashsheƙa muryata bata fita sosai domin ita kanta ba ta fahimtar abun da nake cewa, daƙyar nake iya faɗin, "Yaya... don Allah... ki taimaka min ki ce ba na son shi..  bazan iya auran sa ba... ki ce ma Umma tazo ta tafi dani Ni ba na son aure yanzu..." Dole nayi shiru sabida kukan da ya ci ƙarfi na

Yaya Haula ta kasa magana illa kama Ni da tayi tana ta ƙoƙarin share min hawaye na, sai dai kuma wasu ne suke gudun tsere, ina jikinta na lafe ina ta sakin ajiyan zuciya da shashsheƙa, muryata ma bata fita sosai sabida yanda kukan ya shaƙe min murya. Haƙuri kawai take bani a yanzu ɗin amma na dena sauraron ta ma, nayi nisa cikin wata duniyar da yanda rayuwata zata kasance, daƙyar ta samu ta rarrashe Ni ta share min hawaye, sai dai ana kallo na an san nayi kuka sabida yanda idanun nawa suka sake fitowa waje suka yi gulu-gulu suka canza kala gaba ɗaya, jan hannuna tayi muka fita gidan batare da ta bari an kula da yanayin fuskar nawa ba, gidan ta muka wuce ta shigar dani cikin ɗakin ta tana ta rarrashina, a haka barci ya ɗauke Ni ban sake yin magana ba. Sai a lokacin ta saki ajiyan zuciya tana sharce hawayen ta daga kan fuskarta, fuskata ta tsirawa idanu tana kallon yanda nake ta faman ajiyan zuciya akai-akai ina shashsheƙa, sai ta saka hannu a saman goshi na tana shafawa tare da lumshe idanu ta sake buɗewa a kaina, sai kuma can ta sauke numfashi tana buga tagumi, haƙiƙa tana tausayina matuƙa sabida kasancewata ƙaramar yarinya, idan da ace tana da damar da zata hana auren nan babu yanda za'a yi ta bari ayi min aure, domin ba komai bane a cikin auren sai wahalhalu; ita kanta abinda ta fuskanta kenan, duk abun da ya faru a rayuwarta ba komai bane a kaina, ta fi jin tausayi na a kanta, sai dai kuma babu yanda zata yi bata da hanyar da zata tsiratar dani, dole haƙuri zata ci gaba da bani da sannu wata rana komai zai wuce, haka take fata a koda yaushe


Ta ƙi tashi na har kusan magriba sanda Mijinta Rabi'u zai dawo, sannan ne ta tashe Ni tace min, "in je in Yi sallah sai in dawo in ci abinci."

Kuka na saka mata ina faɗa mata, "kaina na min ciwo zan mutu." Sosai nake kuka sabida yanda nake ji a jikina kamar ana sassara Ni, babu inda ba ya min ciwo a cikin jiki na

Duk Yaya Haula ta gama ruɗewa ta rasa inda zata sani

Matar Yayan Mijinta ne ta shigo mae suna Hadiza tana tambayar ta abun da ke faruwa?

A nan ne take sanar mata halin da nake ciki

Riƙo Ni tayi cike da tausayi na tana mun sannu, kana kuma ta kalli Yaya Haulan tana cewa, "ai kuwa naga kamar Mama tana da maganin ciwon kai, ki je ki amso mata ki bata don Allah, kinji jikinta yanda yayi zafi kuwa?" Sai kuma ta koma taɓa min jikin ko ta ina tana min sannu

Yaya Haula miƙewa tayi har tana sharce hawayen da suka zubo mata, jiki na rawa ta fita ta wuce ɗakin Mama, sai ga ta sun dawo da ita da Maman. Nan Yaya Haula ta ɗauko ruwa ta bani tace, "in sha."

Haka na ƙoƙarta na sha ina ci gaba da kukan nawa sosai, ga tsananin sara min da kaina ke yi har jujjuya kan nake yi tsaban azaba, ba na jin ma sannun da suke min, haka na maƙale a jikin Yaya Haula ina ta kukan ina ce mata, "zan mutu kaina."

Duk cirko-cirko suka yi suna kallo na cike da tsantsan tausayi da ya nuna a kan fuskokin su

Hadiza ta ɗibo min abinci tace, "in CI sabida maganin da na sha."

Dole Yaya Haula ta amsa tana bani a baki don na kasa amsa

Mama kuma ta fita ta ƙaro min wani maganin, bayan ta jiƙa ta haɗo min ta kawo a bani


A lokacin Rabi'u da Ahmad sun shigo, suka zo suka tarar da su a wannan halin duk sun yi cirko-cirko suna tausaya min, su ma tambayar halin da ake ciki suka yi. Nan Ahmad yace, "bari ya je ya amso min magani tunda akwai kuɗi a jikin sa." Dayake sosai na basu tausayi

Haka sukai ta kula dani har bayan sallan isha'i ina wani hali ciwon ya ƙi lafawa, takamaime bazan ce ga inda yake min ciwo ba sabida ko ina nawa azaban ciwo yake min

Ƙarshe dai dole Rabi'u ya je gidan mu ya sanar da halin da nake ciki. Dalilin da yasa na kwana a gidan su Yaya Haula kenan tunda har barci ya ɗauke Ni, shiyasa ba'a tashe Ni ba na kwana a gidan, kuma Baffa yace, "a bar Ni a wurin ta tunda zata fi kula dani".



             Washe gari da tsananin ciwon na tashi babu sauƙi ko kaɗan a tattare dani, jikina ya rikice ko haɗa haƙori ba na iya yi tsaban karkarwan da suke yi, daga waje zaka iya jin ƙaran su, zazzaɓi ne mai zafin gaske ya kama ni da ya haddasa min ciwon kai mai tsanani, ko buɗe idanu ba na iya yi sabida yanda azaba da zafi suka rufar min, ga su sun yi wani irin jajir don ji nake yi kamar zasu fito, kukan ma na kasa yi domin babu ƙarfin yi, hawaye kawai suke silalowa daga rufaffun idanuna

Yaya Haula kuka wi-wi take yi sabida yanda ta ga jikin nawa ya koma, duk wani taimako an yi min amma babu sauƙi, jikinta na rawa ta tashi ta wuce gidanmu, tana zuwa Falon Baban sasa ta zarce, ta je ta same shi kamar yanda ɗabi'ar sa ne yana nan a kishingiɗe yana jin rediyo, ko kuma yana duba littafan addini, dayake yanzu ba ya zuwa aikin komai sai dai idan lokacin gona yayi an girbe amfanin gona a zo a tsibire mishi. Baban sasa ya fi kowa kuɗi a gidan sabida yana da gonaki da yawa, har ara wa ƴan uwanshi yake yi suyi amfani dashi, kuma babu ruwan shi da aiki sai dai ya samo masu haya suyi mishi, ko kuma Yaran gidan su taru suyi mishi, iyakan shi ya je ya duba gonakin ya zazzagaya, yana zaune a gida kodayaushe sai idan ya nishaɗu ya fita ya ga gari ko ya je zaga gonaki, ko kuma ayi mishi shimfiɗa a ƙofar gida

Da kukan Yaya Haula da ya ratsa mishi kunne yasa shi miƙewa zaune ya gyara zaman shi, yana kallonta har ta zo ta duƙa a gaban shi, yace da ita, "lafiya Haulatu? Mene ne ya faru?"

Cikin kuka idanuwanta na fitar da ruwan hawaye sosai take cewa, "Baban sasa Madina ce, Madina zata mutu, don Allah ku cecen min ƙanwata ita

Please Login or Register in order to submit comment