Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta, ya san da gasken take yi, wanda shi kuma gaskiya bai shirya wa hakan ba, in fact ma bai da lokacin kula wasu ƴan mata don ba sa gabanshi, shiyasa ya miƙe yana mayar da maganar nata wasa tare da cewa, "ai Hajiya da tun farko zancen sa kika ɗauko zai fi, don Ansar ya fi Ni bukatar Matar aure a wannan lokacin fiye dani, shi ne na Mata mai jaye-jaye, ina ga shi ne hanyar da za a bi a kimtsa shi da wannan rashin jin nasa, but ni ina na ga lokacin kula wasu mata ma?"
Ya ƙare maganar yana tafiya tare da bin hanyar da zai sada shi ɗakin sa; batare da ya sake sauraron ta ba duk da amsan da take ba shi tana ce mishi, "ya dawo basu gama maganar ba."
Da sauri ya shige ɗan corridorn da zai sada shi da ɗakin da yake kwana

Hakan ne yasa dole Hajiya tabar surutun nata tana girgiza kanta, tare da ƙoƙarin daukar littafin addu'o'in da take duba wa, a ranta tana fatan kawo ƙarshen tuzurancin Jikan nan nata, don ta fara gajiya da zaman sa babu aure, daga shi har ɗan uwansa, ga ƙanninsu nan Mata duk sun kawo kai, ita Naja'at wacce take bin Ansar har an tsayar da ranan aurenta nan da kafin ta gama final study ɗin ta, time ɗin zai ɗauki like a 1year ko da ɗan wasu watanni, dole ne a wannan karon ta hurawa Uwarsu wuta don ganin sun aurar da su gaba ɗaya ko za a yi tare dana Naja'at ne, don bata ga amfanin zaman su a haka ba.
*** *** *** *** ***

_____A washe gari aka sallame Ni daga asibiti, duk da har lokacin a birgice nake jikin nawa ya ƙi daɗi, domin har lokacin kuka nake yi ina roƙon Umma, "kar a bar ni na koma ƙauye, mutuwa zan yi in na koma, ba na son wani auren." Jikina ya rikice matuƙa; yayi zafi cike da azabar zazzaɓi, duk irin rarrashin da Umma take min tare da su Baba, amma sam ba na jin su,
Har Hajiya Ummee da kanta ta zaunar dani tana ta rarrashina tana sanar min, "ba can ƙauye za a kaini ba, wurin Yayana za a kaini wanda yake aure a nan, kuma suna da yaƙinin bazai taɓa cutar dani ba tunda ɗan uwana ne."
Sosai take bani baki da kwantar min da hankali,
Wadda Ni kuma sam na ƙi dena kukan da nake yi, musamman yanzu da na ji wanda aka aura min, ai nan sai na ƙara saka kuka mai dalili sabida na san bani da wani sauran gata yanzu, ban san Yaya Yunus ba ban kuma san ɗabi'un sa ba; tunda bai zauna damu ba dukka-dukka sanin da nayi masa sau biyu ne zuwa uku, bani da tabbacin zan samu kwanciyar hankali da salaman zuciya a gidansa, ina ganin tamkar rayuwata ta zo ƙarshe ne, gaba ɗaya hankalina ya kasa kwanciya bare in saurari rarrashin da suke min

Umma ta tasa Ni gaba hankalin ta a matukar tashe ta rasa abun yi, ta haƙura ne kawai don kalaman da Hajiya Ummee tayi mata, sannan ta haƙura ne kawai don bata da yanda zata yi, bata da wata hanyar da zata nema don ƙwato ƴarta, shiyasa ta haƙura ta ba wa zuciyarta hakuri ta miƙa komai zuwa ga Allah, ta san Allah shi zai tsare mata ɗiyarta tunda an rigada an gama cutar ta, sosai take ɓoye tashin hankalin ta musamman kasancewar Baba yana ƙara bata baki, tare kuma da ganin halin da nake ciki shiyasa take ta kwantar min da hankali tana faɗa min, "tana tare da Ni a koyaushe, ina nan anguwan ƙaya; ina low-cost? Tunda ina kusa dasu baza ta taɓa bari a cutar da Ni ba, da ikon Allah Allah zai jiɓanci lamarina."
Ta kuma ƙara kwantar min da hankali tana faɗa min, "gwara in koma wajen Yayana a nan birni, da in zauna a can ƙauye, ta san bazan taɓa shan wahala kamar yanda na sha a baya ba."

Amma kawai jin Umma nake yi, Ni kaɗai na san azaban da na sha a baya, Ni kaɗai nake iya tantance uƙuba da ƙuncin da ke cikin raina, walwalata ta tafi gaba ɗaya, bani da sauran wani farin ciki, hawayena masu zafi suna kwaranya min wanda ban san ranan tsayawar su ba, ba na son auren har cikin raina, ji nake yi tamkar zan mutu amma na kasa bayyana yadda nake ji,
Ina ji ina gani a washe gari su Baffa suka zo tafiya dani,
Har da kayana waɗanda Alh. Badamasi yayi min su cikin akwati biyu na aure, aka zuba a guda ɗaya aka cika su,
Daga Baffa sai Baba Haruna da Baba Mamuda, sai kuma Tukur ƙaramin ɗan Baba Iro wanda bai wuce sa'an Yaya Haula ba, shi ne wanda ya riƙe akwatin ma,
Ina ji ina gani ina kuka da hawaye da majina aka rabo Ni da Ummana da ƴan uwana aka tafi dani gidan Yaya Yunus, wanda babu irin rarrashin da Baffa bai yi min ba amma na kasa shiru, sai da Baba Mamuda ya daka min tsawa sannan na natsu har na bi su cikin tashin hankali, sai kukan zuci da nake yi jikina na rawa da tunanin abun da zan je in tarar a sabuwar rayuwar da zan yi; a gidan wanda aka ce shi ne Mijina.
***** ***** ***** *****

_____Yayinda tun sanda Baban Sasa ya sanar da Yunus auren da aka yi masa, ya koma gida cikin tsananin tashin hankali da tunanin bala'in da ke son kunno masa, ya san cewa Matarsa Sharhabila Mace ce mai tsananin kishi da tsananin ƙaunar da take mishi, haka shi kansa irin ƙaunar da yake mata ba ya tunanin zai iya haɗa ta da wata a duniyar nan, sai ga shi iyayensa sun shiga rayuwarsa sun yi masa karan tsaye suna son rusa mishi jin daɗin sa,
Iya ɓacin rai da tsananin takaicin Mahaifin nasa; yasa hankalin sa yayi mugun tashi, wanda nan take duk da bazai ce ga yarinyar da aka aura mishi ba; bai kuma san wacce yarinya bace tunda bai san yaran gidan ba, amma ya ji ya tsane ta matuƙa, yayinda sabida tunanin kar hankalin Matarsa ya tashi ya kasa sanar mata da abun da ke faruwa, domin ya dauki alkawarin bazai taɓa sanar mata da auren ba, ya shirya yarinyar ta zo gidan sa, but zata yi rayuwar ƙasƙanci wanda ya shirya mata ko don samun farin ciki a gidan sa, kuma daga ƙarshe idan ya samu yanda yake so ya sake ta ya mayar musu da ita kamar yanda suka aura mishi, tabbas zasu ga abun da zai aikata musu, don a yanda ya ɗauki fushi da tsananin ɓacin rai komai zai iya yi

A ranan da ya tabbatar zasu zo kawo ƴarinyar kamar yanda aka sanar masa, sai ya ɗauki Matarsa da ya'yansa suka wuce gidan surukan sa ya bar su a can suyi musu wuni, shi kuma ya dawo gida yana jiran zuwan su ransa a ɓace cike da tunanin abubuwan da zai aikata, don bazai yarda Sharhabila ta san da maganar auren ba, zai ɓoye mata iya tsawon lokutan da ya ɗiba wa yarinyar ta bar masa gida, dole zai ɓoye mata gaskiya a wannan gaɓar, dole zai yi mata ƙarya wanda bai taɓa yin mata ba.


_Hmm! Wasa Farin girki._
[23/07, 9:22 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 20*
_____Wannan ne karon farko da dukkanmu muka taɓa taka gidan Yaya Yunus, a cikin dangin mu babu wanda ya taɓa zuwa gidan, tun auren sa babu wanda ya je, saboda a lokacin da yayi auren Baban Sasa yana fushi dashi wanda ya hana kowa zuwa ya duba inda yake, daga baya kuma da aka yi sulhu har Baban Sasa ya sauko daga fushin da yake yi dashi, lokacin Sharhabila ta sake haihuwa na biyu a lokacin ne Baban Sasa ya yarje wa wasu su je su duba ta,
A lokacin sai aka zaɓi Inna Amarya da Matar Baffa Inna Uwa, sai kuma babban ƴar Baban Sasa wato Yayar Yunus ɗin; Hajja Jamma, su suka yi tattaki suka je suka duba jaririn, tun daga wannan lokacin ba a sake zuwa ba har wannan lokacin da yanzu zamu je, sabida a wancan lokacin basu samu karɓar arziki ba,
A cikin su Baffa babu wanda ma ya san gidan har sai da aka kira Yaya Yunus da kansa yayi musu kwatance aka kawo mu har ƙofan gida a keke napep

Dayake ya sanar da mai gadi, don haka yana ganin mu yayi mana jagora muka shiga ciki, ya nuna mana ta hanyar da ake bi, dukkan mu babu wanda bai yi mamakin girman gidan ba, yayinda su Baffa suka buɗe baki suna kallon ikon Allah cike da sha'awa da ƙauyanci,
Hatta Ni da nake tafe ina zubar da hawaye sai da na bi gidan da kallo ina mamakin inda muka shigo,
Bamu tsinke da lamarin ba sai da muka taka ƙafafuwan mu cikin babban falon su, wanda sanyi na AC da wani daddaɗan ƙamshi mai ni'ima ya kewaye mana hanci ya kutsa ciki, tuni mun saki ajiyar zuciya sabida wani irin daɗi da iskan da ke shigan mu yana ratsa mana kwanya,
Babu wanda bai nuna ƙauyanci a irin gidan ba, don Baba Mamuda ma kasa shiru yayi a fili ya furta, "ikon Allah!" Yana sake bin Falon da kallo duk mun kasa zama muna tsaye kamar gunki,
Kamar yanda mai gadin yayi mana jagora har ciki sannan ya fita ya rufo ƙofa

Muna a tsayen ko minti biyu bamu yi ba sai ga Yaya Yunus ya fito daga wani daki, yana sanye da doguwar rigan jallabiya baƙa wacce ta yi wa kyakkyawar farar fatarsa kyau, fuskarsa babu fara'a ko kusa, amma kuma fitowarsa ne yayi ƙoƙarin ƙaƙalo murmushin dole yana mana iso tare da cewa, "Baffa, ku zauna mana kun tsaya a tsaye."
Yayi furucin still yana bin mu da kallo ya ƙarisa karisowa cikin falon

"Au to! Ai Ni wlh mun yi tunanin mun yi ɓatan kai ne, don har shigowana nan ban yarda gidan ka bane sai da naga ka fito, ashe dai bamu ɓata ba?"
A cewar Baba Mamuda da ya sake magana yana mai zama a ƙasa

Dukkanmu sai muka bi ƙasan muka zauna kowa ya kasa zama a kan kujerar,
Yayinda nima tuni na raɓe a gefen Tukur ina sake bin Falon da kallo baki a sake, ban san ma sanda kukan nawa ya ɗauke ba don ganin aljannar duniya

Shima Yaya Yunus a ƙasan ya zauna yana mai gaishe su cikin girmamawa, yayinda sai a lokacin ne ya kalli inda nake, duk da ba ya kallon fuskata bazai iya shaida Ni ba, amma kallo ɗaya yayi min ya ɗauke kansa,
Bayan sun gama gaisawa sai ya miƙe ya je kawo musu ruwa yana kiran Tukur da, "kai zo ka daukar musu ruwan nan."
Tunda sai da ya kalle sa sannan yayi maganar kasancewar bai san sunan shi ba, a zahiri da yawa mutanen da ke gidan mu Yara-yara duk ba wai sanin mu ya cika yi ba, kasancewar mu da yawa kuma duk muna kama da juna, sannan bai cika zama sosai ba bare ya san wasu daga cikin ƴan uwa

Shi kuma Tukur dayake ya san dashi yake yi, da sauri ya miƙe jiki na rawa ya je gabansa ya kwaso ruwan faro da lemun kwali ya kawo gaban su Baba Haruna

Tahowa yayi Yaya Yunusan ya zauna yana cewa, "ku sha ruwa Baffa, Matar gidan ba ta nan shiyasa ku ka ji shiru."

Jinjina kansu suka yi, sannan suka ɗauki ruwan suka soma sha,
Ni kuwa ina raɓe kaina a ƙasa har yanzu na kasa kallon inda yake sabida halin da nake ciki, yanzu ma hankalina ya soma dawowa jikina inda tuni wasu sabbin hawayen sun soma tseren gudu daga kan fuskata

Baffa ne ya miƙo min kwali daya na lemun yace, "Madina amsa ki sha ke ma."

Ɗago kaina nayi da sauri na saka hannu na amsa tare da mayar da kaina ban ce komai ba, kuma bani da alamun shan, kamar na nitse haka nake ji na sabida tsaban rashin natsuwa duk a takure nake, jikina har lokacin rawa yake yi, ban san kuma wanne irin rayuwa zan yi a wannan gidan mai kama da Aljanna ba? Fargaba da tashin hankali da tsoro ya hana Ni sukuni

Su kuwa sai da suka gama shan ruwan; yayinda Yaya Yunus yake tambayar su mutanen gidan? Suka amsa mishi suna ce wa, "sun ce a gaishe ku."

Daga nan Baba Haruna ya soma magana yana nuna Ni tare da cewa, "to ga shi mun cika alƙawari mun kawo maka Madina har gida, saura kuma ka riƙe amana ku zauna lafiya, mun so mu samu Iyalin naka mu haɗa ku gaba ɗaya muyi muku nasiha da kuma danƙa muku amanar Madina, ita yarinya ce bata san komai a kan harkan rayuwarku ba, yana da kyau ku nutsar da ita ku tallafi rayuwarta ku kula da komai nata, barin kai Yunusa tunda ƙanwarka ce, na san baza ka wulaƙanta ta ko ka ci mata zarafi ba, duk abun da tayi ba daidai ba ka kwaɓe ta ka sanya ta a hanya."
Sannan ya juya gare Ni yana cewa, "ke kuma Madina, ga Mijinki nan kuma yayanki, ki yi duk abun da ya ce ku zauna lafiya ban da rashin kunya ko nuna rashin tarbiyya, mun san halin ki a yanda kike da kamun kai ki ci gaba da biyayya ban da musu da gardama, ki bi Matarsa sahu da ƙafa don ku zauna lafiya, kinga ke yarinya ce idan kika yi mata biyayya sai ta jawo ki a jiki ta nuna miki abun da yake dai-dai da wanda ba dai-dai ba. Allah yayi muku albarka gaba ɗaya, mu ba jima wa zamu yi ba yanzun nan zamu tafi tunda mun yi abun da ya kawo mu, ga kayanta nan mun zo mata dashi, kamar yanda Baban Sasa ya faɗa maka kayi mata duk abun da ya dace na game da haƙƙinta na aure, kayan lefe da sauran abubuwa na kayan ɗaki tunda itama Matarka ce."

Shi dai Yaya Yunus shiru yayi yana sauraron shi har sanda ya gama, sannan su Baffa suma suka sanya baki duk albarka suka sanya mana but babu wanda ya amsa, bai ma ɗago kansa ba har suka gama, sannan ya miƙe da nufin raka su tunda har sun tashi

Ni kuwa a nan take wani marayan kuka ya kufce min, na sanya hannu na rufe bakina ina kwantar da kaina a saman gwiwa na, ji nake yi tamkar na bi su amma babu hali, kuka nake yi sosai na ƙudundune kaina ina jin tamkar an kawo Ni inda babu kowa nawa, ko ya rayuwata zata kasance da Yayana wanda ban ma san waye shi ba? Ban san wanne irin zama zamu yi dashi ba?
Tsawan da na ji an daka min ne yasa na ɗago kaina a firgice ina sauke manyan idanuna da suka sauya kala zuwa ja, na zuba a kansa, take wani irin tsoro ya shige Ni sakamakon ganin yanayin fuskarsa da babu ɓurɓushin fara'a

Shi kuwa zare min ido yake yi yana sakar min wani bahagon kallo mai cike da tsantsan tsana da ƙyamar da yake min, hannunsa yasa a bakinsa tare da cewa, "shiii! Kar in sake jin wannan shegiyar muryan taki ta bayyana a falon nan, if not..."
Sai ya gyaɗa kansa yana mai sakar min harara tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa

Take na riƙe bakin nawa ina mai mayar da kaina ƙasa, wani irin tsoron sa yana kama Ni, ji nake yi tamkar in yi fitsari a wando tsaban yanda na firgice ina sauke numfashi a kai - a kai,
Shi kuwa wuce wa yayi bai sake bi ta kaina ba, don da alamu akwai ɓacin rai a tattare dashi, sai da ya ja dogon tsaki wanda ya ƙara ruɗa min ciki, sannan yabar wurin yana bugo ƙofan,
Amma duk da haka bai sa na ɗago kaina na sake kallon inda yake ba, kuma kukan nawa cak ya tsaya sai ruwan hawaye da nake zubar wa tuni ya jiƙa min koren hijabina, duk da AC da fankan da ke wainawa amma Ni gumi ne yake tsatstsafo min, gumin tsoro da tashin hankali gami da rasa madafa, abun da ya faru dani watannin baya su ne ke dawo min a ƙwaƙwalwa ta zuciyata na ƙara buga wa da ƙarfi, tsoro na ƙara ratsa Ni, shikenan na san na mutu yanzu, ba na son auren nan, ya xan yi da rayuwata? Shikenan zan iya mutuwa muddin irin abun da ya faru dani a baya ya sake faruwa dani a yanzu, bazan iya jure wa, "Wayyo Ummana ki zo ki cece Ni."
Abun da nake ta faɗa kenan ina ƙara tusa kaina a tsakankanin cinyoyina fuska cike da hawaye,
A haka na zauna tsawon lokaci ban san ma iya lokutan da na dauka ba, har jikina yayi tsami haka yake rawa kamar zan kife, amma na kasa motsawa tun sanda na shigar da kaina na ƙanƙame jikina,
Sai da na ji muryansa a kaina sannan na ɗago ina kallonsa a firgice, tuni na dauke ido daga kallonsa sabida ganin babu rahama a tattare da shi

Shi kuwa ji yake yi tamkar ya shaƙo Ni ya kashe Ni don baƙin ciki, wai a rasa wacce za a aura mishi sai wannan ƙanƙanuwar yarinyar ƙazama da ita gaja, a yanda ya ji ya raina Ni Ko ƴar aikin gidan sa ban kai matsayin ba, wai amma a Matsayin Matarsa nake, gaskiya Iyayensa sun cuce sa sun gama dashi, su rasa wacce zasu ba shi sai sauran wani banza da ya sake ta sannan za a aura mishi, mai zai yi da ita? Take zuciyarsa ta ƙara hassala ya sake daka min tsawa da faɗin, "ɗago kanki ban son muna-furci a nan, shashashan yarinya ƙazama."
Wani banzan kallo ya watsa min ganin na ɗago kai bisa umarnin sa, "bari in kafa miki sharuɗɗan da ba ki sani ba, ke ba ki kai matsayin Matar da zan iya zama da ita a gidana ba, su iyayenmu da suka aura min ke zasu gaji su zo su ɗauke ki kamar yanda suka kawo ki, so kar ki saka ran cewa Ni Yunus zan iya zama da jakar yarinya ƴar ƙauye kamar ki, kuma daga yau ki ɗauka ke ƴar aiki ce a gidan nan an kawo ki bauta ne, Matata idan ta dawo zan sanar mata da cewan na ɗauko ki kiyi mana aiki ne, idan kika sake maganar nan ta fito tasan cewa akwai aure a tsakanin mu..."
Sai ya girgiza kansa yana cizan laɓɓansa, murya a dake a kausashe ya ƙara da faɗin, "sai na karya ki wlh in har kika bari ta sani, domin baza ki zo ki gurɓata min farin cikin gidana ba, kina jina ko?"

Da sauri na ɗaga mishi kaina ina karkarwa kamar mazari,
Shi kuma ya ci gaba da jan min kunne sannan ya miƙe ya sake barina a wurin, take na saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ina jin wani irin sanyi yana mamaye min ilahirin zuciya, idan na fahimce sa zan zauna a gidan ne a matsayin ƴar aiki? Wannan kalman ba ƙaramin daɗi yayi min ba, don maimakon in shiga wani hali sai na ji daɗi a raina, fargabana da tashin hankalina nan take ya gushe sabida jin cewa bazai ɗauke Ni a matsayin Matar sa ba, baza muyi zaman aure ba, bazai yi min abun da Alh. Badamasi yayi min ba, tabbas na yarda, na yarda in dauwama ina musu bauta da in zauna a matsayin Matarsa, domin a yanzu ba na buƙatar hakan, a yanda nake jin na tsani aure na gummaci na zauna a haka ina musu bauta batare da ya ɗauke Ni a matsayin Mata ba, take kuwa na share hawayena sabida jin sanyi a raina, Allah ya amshi addu'a ta, bani da shan wahala kuma, zan yi rayuwata babu fargaba bare tsoron abin da zai same Ni, "na yarda wlh Yaya Yunus, zan kasance baiwarku in har baza ka kalle ni a matsayin Matarka ba, zan zauna a haka."
Nayi maganar a fili ina mai farin ciki a karon farko da na ji zuciyata ta rage nauyi, wani ƙululun abu da ya tsaya min a maƙoshi ya wuce zuruf tamkar an yaye min baƙin cikina,
Kaina na ɗaura a saman cinyana nayi shiru kamar ruwa ya cinye Ni, a raina ina tunanin yadda zamu kasance da kuma Matarsa? Yayinda tunanin ta ya faɗo min da halayyarta lokacin da ta zo bikinmu,
Ƙara na ji daga waje kamar ana jan wani abu amma ban san na mene ne ba, take na ɗago kaina ina zazzare ido, na yi shiru ina sake jin ƙaran kaɗan-kaɗan, sai kuma hayaniya da ya biyo baya kamar muryoyi.

[25/07, 6:53 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 21*
_____Ashe wannan ƙaran da na ji; ƙaran buɗe gate ne, Matarsa ta dawo a cikin motanta da Yaranta, Bayan sun fito ne yaran suke hayaniya suna gudu zasu shigo cikin gidan

Ina zaune a inda nake a takure ina rarraba ido da tunanin ƙaran abun da na ji, sai na ga an buɗe ƙofan. Take na mayar da kallona a kan Yaran nashi da suka shigo waɗanda na shaida fuskarsu, duk da sau ɗaya zan iya cewa na sansu

Babban shine Mubashir; wanda a ƙalla bazai fi 7years ba,
Sai ƙaramin Abubakar mai sunan Mahaifin Yaya Yunus; wato Baban Sasa, suna kiransa da Sadam, shekarun sa bai fi 5yrars ba,
Kayan su iri ɗaya ƴan kanti sun yi tocking an sanya musu facing cap, yaran kyawawa da su sai rashin jin tsiya

Tunda suka shigo suka hange Ni sai suka dakata da kiran sunan Dadyn nasu suna faman bi na da ido kamar sun samu TV

A lokacin ne Yaya Yunus ya fito fuskarsa cike da fara'a, da alamun ganin su ne ya sanya shi farin ciki, tafi yayi musu yana mai buɗe hannayen shi yace, "Hello My guys, Come and hug me."
Da gudu kuwa suka rugo a guje suka faɗa jikinsa, ya haɗa su ya rungume suna dariya

Ni kuwa kallonsu nake yi kamar idanuna zasu faɗo tsaban yanda na bi su da ido,
Muryan Matarsa wacce ta shigo yanzu ne ya ankarar da Ni, sai na juya ina bin ta da kallo, ta shigo tana rufe ƙofan batare da ita ta kula da Ni ba,
Fuskarta a yatsine ta juya tana kallonsu da faɗin, "shi ne ku ka tafi ku ka bar Ni da kayan nan ko? Ni zan ɗauko muku wato? Common ku zo ku amsa kar ku bar Ni da kaya a nan."


Nufo ta suka yi suna dariya, kowannen su ya amshi leda ɗaya daga hannunta na daga tsaraban da tayi musu,
Kana suka koma cikin falon suna tsalle-tsalle,
Sadam da ya nufi wurin Kujera sai lokacin ya sake ankare wa da Ni zaune kaina a ƙasa, sai ya buga ƙara yana cewa, "laa Mamy zo ki ga wata a nan a zaune."

A take gaba ɗayan su suka bi inda nake da kallo, har Yaya Yunus da shi sam ya manta da Ni a gidan ma,
Ko kafin yayi magana Sharhabila ta riga sa idanunta a zare take kallonsa da faɗin, "Husband, wace ce wannan kuma?"

Ɗan sauran fara'an fuskarsa tuni ya shanye shi, sai ya yatsina face yana cewa, "Let me explain to you but not now, let you rest

Please Login or Register in order to submit comment