Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya tsirga min, cak numfashina ta ɗauke gaba ɗaya nayi suman tsoro

Shi kuma a hakan bai sa ya dakatar da abun da yayi ninya ba, domin ko ɗigon tausayi babu shi a lamuransa a wannan lokacin, cikan burinsa kawai yake hangowa da kuma samun damar aiwatar da abun da ya zo yi,
Nan da nan ya janye min skirt ɗina ya fara aikata abin da yayi ninya, bayan ya shafe jikinsa da wannan maganin da ke fitar da manya-manyan tsutsotsi luƙa-luƙa, ga wani irin wari da yake yi sakamakon ƙara kwanakin da yayi a haka a rufe cikin kwalɓa, shi kansa tamkar zai yi amai a wannan lokacin sabida yanda warin ya addabe shi,
Yana ganin ya fara kusantana jini ya ɓalle, sai yayi saurin dakatawa yana ɗaukar abun zuba jinin nasa tsumma ya sharo jinin gaba ɗaya, shi kansa tsaban tsoro da halin da yake ciki bazai barsa ya ɗauki tsawon lokaci a tare dani ba, bare kuma zafin da yake ratsa shi in ya shiga ƙasana, don haka yana ganin jinin ya bayyana yayi sauri ya gama komai ya gyara wandonsa ya wuce ɗakinsa, ɗan jakan kayansa da ya gama shiryawa ya ɗauka ya fice a gidan da hanzari, don yasa a ransa daga nan kuma gaba yayi

Allah da ikonsa har ya fice Lantana bata dawo ba, sai da kamar mintuna shida suka wuce sannan ta dawo gidan ita kaɗai, don ta je gidan bata samu Jummai mai magani ba tayi nisan zango an kira ta a maƙota, kuma duk inda ta zagaya da ake sa ran za a same ta amma ta je bata same ta ba, shiyasa don kar ta bar Madina ita kaɗai, ga kuma lokacin tafiyar Mijinta yayi kar ya ji ta shiru,
Amma kuma dawowar ta sai ta tarar da abun da ya fi ƙarfin ta, tashin hankalin da ba a saka mishi rana,
Ta tarar da Madina a wannan mummunar yanayin jini ya ɓalle mata ita kuma bata numfashi ta mutu,
Kurma ihu tayi mai ƙara ta soma kururuwa ta fita cikin ɗakin,
Ɗakin Alhaji ta faɗa sai dai babu shi babu dalilinsa, kuma babu ɗan jakansa,
Kafin ma ta tabbatar da mai ke faruwa sai ga surukanta sun shigo da gudun su suna tambayar lafiya?
Don ihun nata ne ya jawo su don ganin mai ke faruwa,
Salati ta dinga yi tana cewa, "yarinyar mutane zata mutu a hannunmu, ku je ku gani ta mutu a ɗakina, na dawo na tarar da ita cikin wani hali jini ya ɓalle mata ta mutu, ga babu Alhaji ya gudu, innalillahi wa'inna ilaihi taji'un...! Mun shiga uku."

A guje suka ranta ana-kare zuwa ɗakin Lantanan, nan kuwa suka tarar da abun da ke faruwa suma sai suka saka salati, jikinsu na faman rawa gaba ɗaya sun ruɗe,
Ga kukan Lantana da take salati da kururuwa

Ɗaya daga cikin surukuwar ta tace, "ai zama bai ganmu ba wlh, a sanar da ƴan uwanta domin wannan bala'in ya fi ƙarfin mu, su zo su ɗauki yar su idan ba haka ba sai su ce mu muka kashe ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un! Ina zamu saka kanmu?"
A cewar Lantana hankalin ta a matuƙar tashe

A lokacin sai ga Jummai mai magani ta shigo gidan tana kwaɗa sallama

Jin muryanta yasa Lantana ta fita da sauri tana cewa, "Jummai don Allah ki zo ki yi ceton rai, yarinyar nan fa ta mutu ina gani domin jini ya tsinke mata, na dawo na tarar da ita ba ta nimfashi ban san mai ya same ta ba."

Da jin haka sai Jummai ta nufi ɗakin itama da sauri suka shige zuwa wurin Madina; wacce suke tunanin rai yayi halin sa.
*****


Alh. Badamasi kai tsaye daga nan wurin Bokansa ya nufa, bayan ya bayyana a gabansa ya zayyane masa cika aikin da yayi a yau

Boka ya bushe da dariya yace, "madalla aikin ka ya zo gargara, domin a wannan lokacin zaka ga cikan aikin ka da zaran ka sanya ƙafa kabar ƙauyen nan,ka tafi duk inda zaka je ko'ina kake son zama arzikin ka na can, babu haufi a ɗan ƙanƙanin lokaci zaka ga cikan burinka, abu biyu ya rage maka ka saki yarinyar saki uku, sannan wannan layan da zan baka; ka kasance da ita duk inda zaka je, babu kai babu talauci, zaka yi mamakin samun ɗaukakar ka."
Ya ƙare maganar yana dariya mai ƙara da amsa kuwa

Farin ciki kuwa ya cika Alh. Badamasi tsaban dad'i, domin har hankalin sa ya kwanta sabida jin aikin nasa ya zo ƙarshe, yanzu sai biyan buƙata, don haka ya amshi layan kamar yanda Bokan ya miƙa masa, ya sake cewa, "amma maganar da ka faɗa min cewa yarinyar babu ita babu aure, yanzu ya zan yi? Wanne taimako zaka bani Boka domin kar yarinyar tayi aure bani da labari?"

Idanunsa ya zare a kansa yana kallonsa da jajayen idanunsa masu ban tsoro, cikin amon muryansa yace, "ba auren ta bane matsalar ka, daga zaran da aka kusance ta ƙadarin aikin ka zai karye, sai dai a sake sabon aiki, kuma aikin dole da ita za a sake, domin ita ce ƙaddaran arzikin ka, dole sai ka sake auren ta sannan zaka sake samun wani arzikin. Tana da ƙashin arziki yarinyar; duk wanda ya aure ta sai ya tabbatar da hakan."

Jin haka hankalin Alh. Badamasi ya tashi ainun, domin babban aiki ne a gabansa, idan aikin sa ya ɓaci taya ya zai iya samo ta har ya aure ta? Shiyasa yace ma Bokan, "Boka babu wani hanya sai wannan dole? Bazan iya auren wata ba dole sai ita?"

Fuska ya ɗaure tamau yace, "ita ce ƙaddaran ka, ko baka ji mai nace maka bane? Dole da ita za a sake aiki, kuskurenka ka bari wani ya kusance ta."

Zufa ya sharce daga fuskarsa, hankalin sa ya ƙara tashi sosai yake duban Bokan, sai yace, "to Ranka ya daɗe ka taimaka kayi min aikin da babu wanda zai iya kusantan ta har abada, domin cikan burina na har abada, zan baka ko nawa ne ko me kake so a duniyar nan."

Dariya ya bushe dashi yana girgiza jikinsa tare da ware hannunsa, sai ya dube sa yace, "an gama da aikin ka, biyan buƙatarka zata biya babu ita babu wani mahalukin da zai kusance ta har abada, koda tayi aure dubu ne, don haka ka je kayi rayuwarka a duk inda kake so ka ɗauka buƙatarka ta biya, ka gaggauta zuwa ka cikasa aikin ka yanzu kar lokaci ya ƙure maka."
Daga haka Bokan ya sallame sa tare da ɓacewa ɓat a wurin

Don haka kai tsaye Alh. Badamasi jiki na rawa bayan ya koma cikin ƙauyen, sai ya samu wuri ya ɓoye Jakar kayansa sannan ya nufi kansa tsaye gidan su Madina,
A ƙofar gida ya tarar da Baba Iro da Nasir suna magana a tsakaninsu, a tsaye ma suke da alamun tsayuwar su kenan, shi Nasir yana riƙe da fatanya zai tafi gona shi ne Baba Iro yake tambayar sa a kan maganar takin da zasu je su siyo a birni,
A nan ya ƙariso wurin batare da yayi musu sallama ba fuskarsa babu walwala a turɓune

Ganinsa ne yasa Baba Iro ya faɗaɗa fara'an sa yana cewa, "ah ah! Alh. Badamasi kai ne tafe ashe?"

Yaya Nasiru gaishe sa yayi cikin girmamawa yana mai gyara fatanyan sa da ke maƙale a kafaɗa

Alh. Badamasi ya amsa har yanzu bai saki fuskarsa ba yake cewa, "dama magana ce ta kawo Ni."

"To fa, Allah yasa lafiya? To ko zamu zauna ne? Yaya Ali ma na cikin gida bari in sa a kira sa."

"A'a ba zancen da ya kawo Ni kenan ba, maganar da ke tafe dani idan ma na faɗa muku ya wadatar ai, a kan maganar ita wannan yarinyar ne da aka kaimin ita, to zancen gaskiya bazan iya zama da ita ba sabida ban zaci haka daga gare ta ba, an munafurce Ni an cuce Ni, maganar da nake muku yanzu bazan iya zama da ita ba, da naso in jure in danne in rufa mata asiri mu zauna a haka, amma na ga abun ba mai yiwuwa bane, shiyasa na yanke shawaran sanar muku domin in yanke hukuncina, sai dai kuyi haƙuri tunda kun cuce Ni tun farko baku faɗa min ita yarinyar ta san wani a waje ba kafin ku aura min ita, idan da kun faɗa min gaskiya zan iya hakura in zauna da ita, amma wannan ba maganar wasa bane tunda har na same ta ba cikakkiyar budurwa ba, a ce kamar yarinyar nan ta san Maza da yawa kafin tayi aure?"
Sai ya girgiza kansa yana mai nuna munin abun daga kan fuskarsa

Daga Baba Iro har Yaya Nasiru da yayi ninyar juya wa ya bar su suyi zancen nasu, jin abun da yake faɗa yasa shi dakata wa yana sauroron su, ashe mummunar labarin nan ne zasu ji wanda yasa gaba ɗayansu gabansu yayi mugun faɗuwa, tashin hankali ya bayyana a fuskokin su duk kansu sun kaɗu sun gaza yin magana koda jin zancen da ya gama fita daga bakin Alh. Badamasi, sai suka yi shiru suna bin sa da kallo cike da mamakin furucin sa, taya hakan zai faru yace an cuce sa Madina bata je masa a cikakkiyar budurwa ba? Wannan wanne irin mummunar sharri ne wanda hankali bazai ɗauka ba?

"Wai ka san kuwa mai kake faɗa Alh. Badamasi?" A cewar Baba Iro da yayi ƙarfin halin furta hakan cikin tsananin ruɗu da tashin hankalin sa da ya nuna a muryansa

"Ƙwarai kuwa na sani, ai shiyasa na zo na faɗa muku tun kafin abu yayi nisa, kar kuma ku ga laifina Ni bazan iya zama da ita ba, na sake ta saki uku ku je ku ɗauki yarinyar ku daga gidana."

"Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un!" Su dukkan su suka furta hakan suna mai zare idanunsu daga kallon Alhjin cikin tashin hankali mara misaltuwa,
Ko kafin suyi magana shi tuni ya juya yabar wurin da saurin sa,
Babu mai ƙarfin tsayar dashi daga cikin su sabida halin da suka shiga, jikinsu har rawa yake yi sai furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un suke yi

"Wai kuwa mafarki muke yi Nasiru ko da gaske ne abun da Alhaji ya faɗa? Wannan wanne irin mummunar bala'i ne yake tunkaro mu?"

Idanun Yaya Nasiru har sun soma kaɗa wa sabida tashin hankali, bai tsaya sauraron Baba Iro ba ya juya da sauri yayi cikin gidan hankalin sa a mugun tashe

Baba Iro ya bi bayansa yana ci gaba da salatin a fili, don yanayin da yake ciki yasa shi ruɗewan da bai san cewa da ƙarfi yake salatin ba.
[14/07, 1:23 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 14*
_____Babu inda Yaya Nasiru ya zarce sai sashin Baban Sasa,
Lokacin yana zaune bakin ƙofan ɗakin sa da buta a gaba zai yi alwalan sallan walha da ya saba yi, ya zauna tukunna yana aswaki before ya fara, sai ganin Nasiru yayi ya shigo sashin nasa kamar an jeho sa, har sai da ya ba shi tsoro ya ɗaga kai yana kallonsa tare da furta, "Subhanallah...! Nasiru, mene ne haka?"

"Baba, ba lafiya ba wlh, yanzun nan Alh. Badamasi ya zo Kofar gida ya tarar damu tare da Baba Iro...."
Nan ya kwashe komai ya sanar mishi

Tun kafin ma ya ƙarisa zancen shima Baba Iro ya shigo sashin har lokacin hankalin sa a mugun tashe yake

Shi kansa Baban Sasa yanda ya ruɗe tuni ya tashi a kan ƙafafunsa yana salati da sallallami, sai yace, "ina shi Badamasin yake?"

Baba Iro yace, "wlh ya tafi, inata yin masa magana amma bai kula Ni ba, mu yanzu ya zamu yi da wannan abun tashin hankalin? Abun da zai yi mana kenan? Sakayyar da zai yi mana kenan?"

Shiru Baban Sasa yayi, domin ransa yayi mugun ɓaci da abun da Alh. Badamasi yayi musu, in ban da sharri taya ya zai ce sun ɗauki yarinya a lalace sun ba shi? Abun da hankali ma bazai ɗauka ba ai dole sai dai wulaƙanta su zai yi

Baba Iro ya sake cewa, "wlh Yaya kawai wulaƙanci ne irin na masu kuɗi yau ya fado kanmu, amma ko ya ci amanar mu wannan mutumin, a ce da abun da zai saka mana kenan? Yanzu ya sakar mana yarinya kenan daga aure? Wannan wanne irin abun kunya ne ya jawo mana?"

Duban Nasiru Baban Sasa yayi, yace, "maza ka kira min Baffanku a sashin sa yanzu ya bar nan."

Yaya Nasiru ya amsa mishi da sauri yana yin gaba domin kiran Baffa

Ko kafin wani lokaci zancen ya soma yaɗuwa, tunda gaba ɗaya sauran iyayen Maza suka taru a sashin; Baba Iro yana maida musu da zance,
Babu wanda hankalin sa ya fi tashi barin Baffa, tunda dole shi zai fi su shiga tashin hankali kasancewar Abokinsa ne Alh. Badamasi ƙut da ƙut, kuma shi yayi masa hanyar da ya samu Madina ya aura, amma kuma tun ba a je ko'ina ba aure kwana biyu kacal; don bata cika na ukun ba ma, amma ya sakar musu ƴa, kuma ban da haka har da sharri, don haka tuni ya shuri takalma yabar gidan yana zage-zage da faɗin, "Ni Alh. Badamasi zai yi wa haka? Wlh tallahi baza mu ɗauki wannan wulaƙancin ba; ba zamu taɓa yarda ba, ko mene ne sai inda ƙarfin mu ya ƙare, bari in je in ji dalilin da zai wulaƙanta mana yarinya har da mata sharri."
Sai ya miƙa jiki ya tafi

Su Yaya Shamsu tuni sun mara masa baya sun bi shi, don suma ransu ya yi ƙololuwar ɓaci, bare akwai su da zuciya ƴan gidan, dukka Samarin gidan suka bi hanya zuwa gidan Alh. Badamasi


Amma koda suka je sun tarar da wani babban tashin hankalin ne da ya ɗaga musu hankali fiye da wanda suke ciki,
Don a lokacin an fiddo da Madina za a kawo ta gida, kasancewar Jummai mai magani tace, "baza ta taɓa ta ba har sai an mayar da ita gida."
Don a ganin su zuwa wannan lokacin Madina ta mutu tunda babu inda nata ke motsi, har lokacin kuma jini na zuban mata ta ƙasan ta, sai nannaɗo ta aka yi a zani kamar wata jaririya

Baffa yanda ya ruɗe kamar zai saka hannu a ka ya kurma ihu, take su Shamsu suka ɗauke ta suka wuce da ita gida,
Nan fa hankula ya ƙara tashi sabida ganin yanda Alh. Badamasi ya mayar musu da ƴa,
Ga shi su ba zuwa asibiti suka saba dashi ba, don ƙarshe sai dai aka kira Malam Bala na-Allah sabida Jummai ta kasa shawo kan matsalar; tunda ita tayi iya yin ta amma ta kasa

Matan gidan kowa jikinsa yayi sanyi sun yi jugum domin kowa yayi amanna Madina ta mutu, baza ta iya rayuwa ba a wannan halin da take ciki, Yaran gidan sai koke-koke suke yi,
Haka ma su Binta kuka kawai suke yi tunda duk suna sashin Baban Sasa inda aka ajiye Madinan a ɗakin Inna Lami,
Duk sun yi jugum suna jiran su ga abun da hali zai yi,
Su kansu su Baban Sasa suna nan cikin sasan sun kasa zaune sun kasa tsaye

Su Yaya Ahamdi tuni sun bazama neman Alh. Badamasi, don sun ce, "wlh sai sun kashe sa har lahira in har ƙanwarsu ta mutu, domin mutumin nan bai cancanci rayuwa ba, dabba ma ta fi shi tausayi a yanda ya wulakanta musu ƙanwa, sai sun kashe sa."
Haka suka fita gidan ana kiran su amma inaa sun ƙi tsaya wa sun tafi neman Alh. Badamasi

Basu san cewa shi tuni yabar garin ba, tunda ya san aika-aikan da yayi bazai taɓa zama ba

Yusuf ne ya je ya shafa wa Yaya Haula labarin har gida, ai babu shiri ta rugo aguje ta taho gidan nasu tun a hanya take kuka,
Koda ta zo ta tarar da Madina a wannan halin, domin duk yanda aka yi a hana ta shiga ɗakin taƙi sauraron mutane, tana kuka ta kutsa kai ciki tana kiran sunan ƴar uwanta, a lokacin da tayi ido biyu da ita sai ta yanke jiki ta faɗi, domin halin da ta ga ƴan gidan a ciki wanda zuciyarta ta bata shaidar ta rasa ƴar uwanta ne; tana ganin ta a kwance magashiyan ta zube a ƙasa a sume, dama ga ta da ƙaramin ciki, nan da nan jini ya ɓalle mata

Ai kuma sai tashin hankalin ya daɗu musu, ga Haula a ƙasa itama tana zubar da jinin,
Nan fa kowa ya fara salati itama aka kwashe ta su Inna Asabe suka ɗibo ruwa aka zuba mata,
Dayake akwai Jummai a wurin ita ta soma duba ta, tana musu bayani, "cikin da ke jikinta ne ya zube."
Sai da aka yi ta zuba mata ruwa sannan ta farfaɗo

Kuka sosai take yi tana kiran sunan ƴar uwanta tace, "a barta ta je ta ganta."
Amma haka aka riƙe ta ana bata baki,  but kwata-kwata ta kasa sauraron su, kuka take yi har da su majinu tana son miƙe wa amma jiri ya hana ta,
Inna Amarya ta kama ta tana cewa, "ki yi haƙuri mana Haula, ƴar uwanki bata mutu ba tana nan da ranta, yanzu haka ma ta fara motsi, idan ba ki kwantar da hankalin ki ba kuma kema kika shiga wani hali ya zamu yi umm? Wannan wanne irin bala'i ne?"

Baban Sasa ne yace, "Haulatu, zauna a nan kar ki tashi, kinga ke ma jikin naki babu dad'i, maza zauna bari a kawo miki maganin kema ki sha."
Sai ya dubi Jummai mai magani yace, "itama a haɗa mata maganin ta sha tunda ga abun da ya faru da ita."

Haula haɗa kai da gwiwa tayi ta dinga rera kuka gunun tausayi, kwata-kwata ba ta jin zafin ciwon da ke addabar ta, ta ƙanwarta gudan jininta take tunani, wanne irin azaba Madina take sha a wannan halin? "Allah Sarki! Ƴar ƙanwata, tun ba a je ko'ina ba Allah na jarabtar ki ta fannoni daban-daban, don Allah ku taimaka ku ceto min ƙanwata, ita kaɗai ta rage min, bazan iya rayuwa babu ita ba."
Haka take faɗa da ƙarfi tana ihu har da birgima, don abun yayi mata ciwo da yawa, baƙin cikin ta halin da Madina take ciki Allah kaɗai ya san azaban da take sha, idan ta tuna abun da Yusuf ya faɗa mata sai hankalinta ya ƙara tashi ainun, ta ɓarke da kuka tana kiran sunan Madina, sai ta yunƙura kamar zata tashi amma ta kasa sabida jirin da take gani a cikin idanuwanta, ga shi har lokacin su Inna Amarya suna riƙe da ita sun ƙi sakin ta, don halin da ta shiga hankalin su ya tashi tamkar mara hankali ko wacce aljanu suka shafa

Kai sun ga tashin hankali mutanen gidan nan a ɗan ƙanƙanin lokacin nan, bare yanda ake ta duba Madina duk wani taimako an bata amma har lokacin bata farfaɗo ba, sai dai daƙyar aka tsayar da jinin da ke zuba daga jikinta, mummunar fyaɗe yayi mata wanda hankalin su Baban Sasa ya fi na kowa tashi, musamman da Malam Bala yace musu, "sai dai yanda hali ya yiwu, amma gaskiya ya cuce ta, ya rigada ya ɓarka ta ya haɗa mata wurin kashi da fitsari, in so samu ne a ɗinke mata wurin."

La haula fisha'atillah! Ban san wanne irin bayani zan yi muku a kan halin da suka shiga ba, bare ga su mutanen karkara basu yarda da wani asibiti ba, kawai dai magungunan gargajiya suka sani, kasancewar Jummai mai magani tana yin ɗinki idan hakan ta faru, tunda ita kamar anguwar zoma ce amma na ƙauye, wasu abubuwan na asibiti duk ta sani, kuma ta saba ma mutane ɗinki in aka ɓarka su aka yi musu fyaɗe, sai ta samu igiyar buhu ta saka allura ta ɗinke mutum, cikin wannan azaban har Mace zata warke, idan da ƙaren kwana ta samu lafiya, idan kuma ya zo da akasi sai ta kamu da lalura kala-kala, haka za a yi ta banka mata magani har ta warke, wata kuma a haka zata zauna da ciwon a rasa mai ke damun ta, ko kuma ta zauna a ɓarke, shi wurin bai warke ba kuma bata samu lafiya ba na tsawon lokaci, shiyasa yawanci Matan karkaran kwata-kwata basu da galihu, rayuwa kawai suke yi a cikin duhun kai, ko da ganin su ka san cuta ta ci su har ta cinye, kuma Mazajen su ba sa kallonsu da daraja

Bayan an yi wa Madinan ɗinki ne lokacin Yaya Haula ta koma gida ta ari wayan Mijinta ta kira Ummansu, haka tana kuka ta sanar mata da abun da ke faruwa, tace, "Umma don Allah ki zo ki taimaka kar Madina ta mutu a nan, kin san babu mai kaita asibiti a duba ta, wlh a haka zata mutu har yanzu bata farfaɗo ba, ba ta ma iya motsa komai nata tana nan a yadda aka kawo ta, don Allah Umma ki zo ki cece ta kar ta mutu."

Kukan da take yi ya ƙara ɗaga wa Umma hankali, domin a lokacin da ta gama jin zancen itama fashe wa tayi da kuka sabida tsananin ruɗu da jin halin da ƴarta take ciki,
Ga shi a lokacin dare yayi sosai, babu yanda za a yi ta kama hanya ta zo ƙauyen nan a daren, tunda hanya babu kyau ba a cika bin hanyar da dare ba,
Yanda ta tashi hankalin ta ko barci a ranan ta gaza yi, kai ba ita kadai ba hatta su Hassana da Babansu basu runtsa ba, tunda a halin da Umma take ciki hankalin su suma yayi matuƙar tashi ainun, su Hassana sai kuka suke yi tausayin ƴar uwansu ya cika su


Da sassafe suka kama hanya zuwa ƙauyen, da ita da Baban su Hassana, su kuma su Hussaina suka zauna a gida, duk da sun so su bi su a tafi dasu su ga halin da Madinan take ciki, amma Baba yace, "baza su je ba, su zauna a gida har su dawo."
Haka suka tafi suka bar su suka nufi ƙauyen a cikin keke napep

Kafin karfe takwas sun isa cikin ƙauyen,
A lokacin da suka je har yanzu hankalin mutanen gidan a tashe yake, don a wannan lokacin suna sashin Matan Baban Sasa sun yi cirko-cirko,
Kasancewar a lokacin na farfaɗo ina ta yanka ihu da kururuwan azaba, bakina sai furta sunan Ummana nake yi, duk yanda suka so su samu kaina nayi shiru na ƙi, aka kira mai maganin domin ya duba Ni, amma abun ya cutura ihun azaba nake yi ina kiran sunan Ummanmu da Yaya Haula

Ga Yaya Haula a wurin ta riƙe ni itama tana ta kukan tana kiran sunana

Ana haka sai ga su Umma sun shigo sasan,
Ai da gudu Umma ta nufi hanyar ɗakin tunda ta ji muryan Madina daga can take fitowa, tun kafin ma mutanen su ankare da ita har ta shige itama tana kiran sunan Madinan, hankalin ta a mugun tashe,
Lokacin da ta isa inda ta hange ni kwance babu ko kaya a jikina, an ɗaure min ɗuwawu kamar an yi min nafkin sabida kar jini ya ɓata wurin gaba ɗaya, shine da aka yi min ɗinki sai aka toshe mini ɗuwawun da tsummokarai,
Yaya Haula tana zaune kusa da Ni ta ƙanƙame Ni muna kukan a tare,
Tsaban wahala duk na firgice na fita a hayyacina, kuma ba na gane kowa zafin ciwo ne yasa nake kiran sunayen mutanen gidan, wadda sunan Ummanmu ne ya fita a bakina

Kuka Umma ta fashe da shi ta saka salati, sai ta rungumo ni tana girgiza Ni hannunta a saman fuskata tana kiran suna na, "Madina, Madina, ki buɗe idanunki Ummanki ne, Madina Madina..."
Sai kiran suna na take yi tana kuka kashirɓan saboda tsananin ruɗewa, "shikenan, innalillahi wa'inna ilaihi taji'un... Kun kashe min ƴa kun cuce ta kun gama da ita, abun da na guda kenan tun farko, Madina yarinya ce amma tsaban mugunta ku ka nuna dole sai kun yi mata aure, kuma ku rasa wanda zaku bata sai wanda ya girmi Ubanta, a haife yayi jika da ita, wlh tallahi bazan yarda ba, idan ƴata ta mutu wlh sai nayi Shari'a da ku tunda kashe min ƴa zaku yi, bazan taɓa haƙura ba."
Maganar take yi tana kuka

Please Login or Register in order to submit comment