Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"a'a wlh Hajiya, ai Ni tuni na cire damuwar Madina a raina tunda haka Allah ya ƙaddaro mata, bani da yadda zan yi, dama wata rana dole zata yi auren ai, amma na bari ne zuwa tayi kamar wata sai in je in ganta."

"To Masha Allah, Allah ya kaimu lokacin, ai ina ga kwanaki suka rage, amma idan za ki tafi sai ki faɗa min in ba ki saƙo, yanzu ma bari in ɗauko miki kudi ki shiga kasuwa ki yi mata siyayyan abubuwan da kika san zai amfane ta, ina zuwa."
Sai ta mike zuwa ɗakin ta; ta je ta duba Jakarta 5k kaɗai ya rage a ciki, sai ta ɗauka ta fito zuwa ɗakin Mashkur tunda ta san yana ciki bai fita ba

Ilai kuwa yana kwance bai tashi ba, yana huce gajiyar aikin da ya sha jiya a asibiti, kusan kwana yayi a can don sai ƙarfe uku ya dawo, shiyasa yau yake huta wa duk da yana fita da weekend amma ba koyaushe ba, bare yanzu da yake son barin garin zuwa Abuja yin wani sabon course din, akwai ƙanin Hajiya Ummee; Uncle Hashim da ke zaune a can Soja ne, a gidan sa zai zauna yayi karatun nasa, remain 2 month yanzu ya tafi

Tura ƙofan tayi ta shiga tana kokarin ɗaura zanin ta da ke shirin kwance wa, yayinda bakin ta ɗauke da sallama ta ƙarisa shige wa,
A cikin ɗakin nasa ta baza idanu tana kallo, wanda ɗakin ya kasance nasu su biyu da suke zaune a gidan, shi da Ansar wanda sun fi zama wurin Kakar tasu Mahaifiyar Momyn su fiye da can gidan su Kaduna, sabida sun fi shaƙuwa da ita, sanadin zaman Mashkur a nan sabida yayi karatun sa na degree har matakin Masters a nan ABU ne, shiyasa yayi zaman sa,
Shi kuma Ansar kasancewar akwai ɗan uwansa a nan ne shiyasa shima yawanci in ya zo ƙasar a nan yake hutun sa ba ya zuwa gidan su, dayake shi yana can Riyadh yana kula da Companin Momynsa a matsayin Manager kuma lauya, still yana ci gaba da karatun sa, shi irin mutanen nan ne masu son jin dadi da more rayuwa, rayuwarsa ta fita daban da ƴan uwansa, shiyasa ya matsa wa Iyayensa tun lokacin da ya gama karatun sa na degree ya matsa zai koma can ya kula wa da Momynsu Companin ta, tunda yawancin dukiyarta suna can ne a Riyadh sai dai masu kula mata dashi, yanzu kusan five years kenan da komawarsa can sai dai ya zo Hutu idan ya ga dama,
Soyayyar da Hajiya Ummee take musu ne yasa suka dawo wurin ta suna zama sabida kulawar da take basu, wanda ya samo asali ne sabida ƙaunar da take yi wa Momynsu tunda ita kaɗai Allah ya bata, bare tayi rayuwa tsawon lokaci batare da suna tare da ƴarta ba, sai daga baya ta samu damar kasancewa da ita, shiyasa take matuƙar ƙaunarta da ƴaƴanta

Kan gadon ta nufa tana tashin sa sabida ganin sa da tayi kwance ya kifa ciki yana ta sharan barci, daga shi sai dogon wando da singlet a jikinsa, ya tusa kansa a ƙasan pillow har tana jin munsharin sa,
Duka ta buga mishi a kafansa a karo na biyu, tana cewa, "dalla tashi Kasa kamar wani mushe, ko dai sake maka wani daren za a yi? Farouk tashi mana, Farouk... Farouk..." Sai da ta kira sunansa kusan sau uku before ya motsa,
Tace, "amma Allah yayi maka nauyin barci wlh, ban taɓa ganin mutum irin ka ba."

Idanu ya buɗe yana kallonta, sai kuma ya mayar yana mai kwantar da kansa batare da yace mata komai ba yana sauraron surutun nata, ganin ta cika sa da faɗan yawan barcin nasa ne, cikin magagin barcin da bai ishe sa ba yake cewa, "Hajiya kin cika ƙorafi wlh, kina ganin fa ba na samun isasshen barci ne sai a wannan time ɗin, kuma yanzu na kwanta but kina min ƙorafi."

"To wani yace kar kayi barcin? Ko Ni na hana ka? Mutum kullum agogo baza ka sarara wa kanka ba kana hanyar asibiti koyaushe, ko lokacin kanka baka dashi, a haka zaka yi auren ma baka da lokacin yarinyar mutane, ai dole ka ƙi ƙaunar aure tunda aiki ka saka a gaba, ga karatu ka hana kanka sukuni."
Sai ta ja yatsun ƙafafunsa ganin tunda yayi maganar ya sake kifa kansa a pillow kamar ya koma wani barcin, "da Allah tashi ka bani aron dubu biyar inyaso sai ka koma barcin, ka kwana ma a haka Ni bai dame Ni ba, amma sallame Ni in tafi."

Ɗago kansa yayi yana bin ta da kallo fuskarsa a dame, da alamun ta takura masa ne shiyasa ya kumbura fuskar yana kallonta ya ƙi magana

"Tashi mana ina sauri ne, nabar Asiya tana jira na."

"Mai za ki yi da kuɗi kuma Hajiya?"
Yayi maganar yana mai ƙoƙarin tashi zaune da sanyin jiki, wanda barcin ne ya cire masa karsashin sa

Zama tayi gefen gadon tana ba shi amsa da faɗin, "Asiya zan ba, zata yi wa Madinanta siyayya sabida zata je duba ta, shiyasa nima zan bada nawa gudummawar."

Shiru yayi yana kallonta, kamar zai yi magana kuma sai ya miƙe bai ce komai ba, wurin wardrobe ɗin sa ya nufa tare da buɗe wa, sai da ya zaƙulo wani farin gajeren wando mai aljihu da zip a jikinsa, sannan ya zuge ya ciro kudi har 10k, ya dawo ya miƙa mata yana cewa, "nima ga nawa nan a haɗa a yi mata siyayyar."

Baki Hajiya ta washe cike da jin dadi, tare da furta, "ai kuwa ta gode, ka ga yanzu sai in kai mata duk wani abun bukata na ɗiya Mace sai ta siya mata, har kayan girki, Allah yasa dai mu ji alheri don wlh ina tausayin yarinyar nan, Allah yasa ta dace da gidan Miji na gari."

"Amin." ya furta yana mai bin hanyar toilet batare da ya koma barcin ba, don ya rigada ya ji barcin kuma ya gudu

Ita kuma Hajiya Ummee sai ta tashi ta fice ta koma falon, bata tarar da Umma ba don tuni ta wuce kitchen tana wanke-wanke, can ta nufa ta same ta ta miƙa mata kuɗin, "ga shi nan har dana Farouk ya bayar a ba ki, sai ki siyan mata duk abun da kika san zata buƙata."


Hannu biyu Umma ta sanya ta amsa cikin tsananin farin ciki tana yi mata godiya, saboda ta san karamcin Hajiya in har bata amsa ba baza ta ƙyale ta ba, shiyasa ta amsa cike da murna tana sake mata godiyar kamar zata duƙa mata tana mata addu'o'i

Hajiya Ummee tace, "Ameen Ameen, ai babu godiya a tsakaninmu Asiya, yi wa kai ne, kuma zaman tare ne dole mu taimaka wa juna bamu san amfanin da zamu yi wa juna a nan gaba ba, duk sanda kika je dai ki gaishe ta da kyau da kyau, Allah ya zaunar da su lafiya Allah yasa mu ji alkhairi."

Umma na murmushi ta amsa da Amin tana sake cewa, "insha Allahu zata ji, zan sanar mata."

"To Ni bari in koma ɗaki, don zan yi sallan walha ne da ban yi ba."

"To Hajiya, amma mai za a dafa ne?"

Ɗan yatsina fuskar tsufan ta tayi tana cewa, "duk abun da kika dafa Asiya yayi, amma ki yi dai abun da Farouku yake so ne tunda yana gida, da alamu bazai fita da wuri ba sabida yanzu ma haka barci ya tashi."

"To Hajiya."
Ta amsa mata tana ci gaba da ƙarisa wanke tukunyar da yanzu ta zo kansa

Ita kuma Hajiya ta fita ta koma ɗakinta don yin Sallah.***

Koda Umma ta tashi aikin a gidan, kai tsaye kasuwa ta wuce tayi duk siyayyar da ta san zan iya buƙata cike da farin ciki; sabida samun kuɗin nan da tayi, ta san bani da matsalar kayan saka wa tunda lokacin da su Baffa suka zo tafiya dani sai da suka yi mata bayanin kayan da zan tafi dashi, don haka abubuwan girki ta haɗa min duk abun da ta san zan bukata, musamman namu na ƙauye wanda ta san na saba da shi, sannan ta siyan min wasu ƴan robobi haka da zasu yi min amfani, a takaice dai sai da ta kashe dubu goma cif ta taho da raguwar dubu biyar, a ciki ta yanke zata yi kuɗin mota sai ta bani wasu daga ciki in riƙe a hannu zai yi min amfani

Kasancewar ta ga ta samu kuɗin mota, shiyasa tana koma wa gida ta sanar da Mijinta zuwa jibi zata je duba Ni, kuma a ranan ta kira Yaya Haula tace mata, "ta je ta samu Baffa ta tambaye shi gidan Yaya Yunus a yi mata kwatance."

Jin hakan yasa Yaya Haula tace mata, "itama zata je, don Allah ta bari idan ta zo sai su tafi tare, tana son ta je ta ga Ƙanwarta, itama hankalin ta duk a tashe yake tunda aka tafi dani tana cikin damuwa."

Umma tace, "ai babu damuwa, in har kin tambayi Mijin naki ya bar ki, to zuwa jibin sai ki zo da wuri mu wuce taren."

Cike da farin ciki Yaya Haula tace, "to Umma Nagode, bari in je yanzu in tambaya Baffan; tunda na san yanzu haka yana gida ya dawo aiki."

Daga haka suka yi sallama da nufin in Haula ta tambaya zata yi mata Flash sai ta kira.
*** *** *** ***

_____Sai da na daidaici sun gama sun tashi a wurin sannan na je na kwashe kayan gaba ɗaya, ina shiga kitchen ban fara ci ba na ji kiran Sharhabila tana kwaɗa min kira, jiki na rawa na isa Falon lokacin tana tsaye a bakin ƙofan dakin ta tana bi na da mugun kallon da ta saba koyaushe, da sauri na isa gefen ta ina duƙa wa tare da amsa mata ina cewa, "gani Anti."

Wani kallo ta watsa min cikin kakkausar murya take bani umarnin, "in yi maza in shiga in yi wa su Mabashir wanka, saura kuma in daɗe in ɓata mata lokaci har ita ta shirya ta fito."

Da sauri na amsa mata yayinda jikina na rawa na tashi na bar wurin, ba wai tsoro ne kaɗai ya sani rawan jiki ba; har da yunwa tunda ko karyawa ban yi ba, ga shi har sha biyun rana tayi, amma bani da ikon yin magana dole abun da ta sanya Ni zan je in yi,
Haka kuwa na shiga nayi musu wankan na shirya su bayan ta zo ta fitar min da kayan da zan saka musu,
Sai da na gama sannan ta kira Ni muka shiga kitchen, ta nuna min abun da zan girka kafin su dawo gidan, "saura kuma in yi mata kuskure sai na lahira ya fi Ni jin daɗi."
Ta ja min kunne tana murɗe wa wadda har sai da na fitar da ƙwallan azaba,
Haka ta ture Ni ta fice batare da ta sake bi ta kaina ba,
Ni kuma na ci gaba da aikin jiki a mace ko abinci na kasa ci, haka na ɗaura abincin gudun in yi laifi, yadda tace min haka nayi tunda jallop ɗin taliya Macaroni ta nuna min, a risho nake girkin kasancewar har yanzu bata taɓa bari na; na taɓa mata kayan wuta ba, sai dai ita ta kunna min, risho ɗin ne kawai take bani damar kunna wa in har ba ta wurin,
Ni ina kitchen ɗin ban san sun fita ba duk da na ji kamar ƙaran mota, amma ban fita ba sai da na gama girkin tsab, tuni na cinye sauran breakfast ɗin su tunda yunwa ta dame Ni, ina yi ina ci har na gama girkin sannan na zuba a Kula na kai saman daining, kasancewar na fahimci kamar babu kowa a cikin gidan hakan yasa na ɗan saki jikina, duk da a gajiye nake tiɓis ga barci da nake jin yana ƙoƙarin ɗauka na, ko sallah ban yi ba na kwanta a tsakar falon sabida jin iska na hura ni, kuma ganin babu kowa shiyasa na ƙi zuwa masaukina tunda nan ya fi iska da daɗin kwanciya, kun san ɗan ƙauye bai iya samun wuri ba, kawai na ɗare musu kan Kujera nan da nan daddaɗan barci ya sure Ni wanda na daɗe ban yi irin sa ba,
Daɗin barcin ne yasa ban san iya lokutan da na ɗauka ina sharan shi ba, ashe har Yaya Yunus ya dawo ya shigo Falon ya tarar da Ni baki a wangale a saman Kujeran su ina sharan barci kamar wata gawa.
[29/07, 2:50 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 23*
_____Yaya Yunus da ya shigo ya hange Ni kwance baki wangale ina sharan barci, mamaki ne ya cika sa sabida ganin yanda na shantake ina barcin kamar na samu gidana, wurina ya nufa ya saka hannu ya buga ƙafana da ƙarfi,
Wanda a nan take na farka ina zare ido a kansa, muna haɗa ido nayi saurin miƙe wa zaune har jikina ya fara rawa cike da tsoron abun da zai yi min, tuni na zamo ƙasa kaina a ƙasa ina mai ƙanƙame jikina sabida tunanin ko duka na zai yi,
Shi kuwa wani kallo ya watsa min yana jan dogon tsaki, murya a kausashe yace, "wato abun da aka bar ki kiyi kenan? Kin zo kin wani saki leɓe kina sharan barci hanci cike da majina; idan kika yi mana fitsari uban wa zai wanke iyee?"
Yanda ya ƙarisa maganar ne da sauri na girgiza kaina batare da na kalle sa ba, cike da tsoro da rawan baki nake cewa, "kayi hakuri don Allah bazan sake ba."
Tsaki ya kuma ja yana mai koma wa can wani kujeran ya zauna tare da cewa, "tashi dalla ki je ki zubo min abinci, shashashan yarinya, saura in ƙara ganin kin hau mana Kujera kina barci, sai na sabauta ki, ƙazamiya."
Ya ƙare maganar cike da ƙyama yana aika min da mugun kallo mai cike da tsana,
Sai kuma ya kuma jan tsaki yana bin hanyar da na bi da kallo tare da tunanin cutan da iyayensa suka yi masa, wai su rasa wacce zasu aura mishi sai wannan tatsitsiyar yarinyar da komai bata dashi, to ya aure ta ya auri mene kenan? Rainin hankali. Fuska ya sake ɗaure wa yana mai cira wayansa daga aljihun gaban rigan sa; tare da soma latsa wa, koda ya ji motsina bai ɗago ya kalle Ni ba har nabar wajen

Ni kuwa jikina na rawa nake komai kamar ana kaɗa Ni sabida tsoro kar in kuskuren da zai dake Ni, duk da har yanzu bai taɓa saka hannu ya taɓa Ni ba amma ina gudun yin musu laifi, don na san bazan ji da daɗi ba,
Kai tsaye ɗaki na koma sabida na san ban da abun yi a nan kuma,
Ashe har magriba ma ta kusa, sallan da ban yi ba na je nayi sannan na zauna a ɗaki,
Ina nan zaune na ji ƙaran buɗe gate, a tunanina ko Aunty Sharhabila ce ta dawo, shiyasa na fita amma babu kowa, fahimtar hakan na gane ƙila Yaya Yunus ne ya sake fita,
Shiyasa na koma ɗaki tunda na tabbatar babu abun da zan yi,
Sai can bayan isha'i na ji hayaniyar dawowarsu; daga shi har Yaran da Matarsa, ban fita ba tunda na san ba abun da zan yi musu, kuma kasancewar Aunty Sharhabila ba ta son gaisuwana shiyasa na san ko na je zagina zata yi, shiyasa nayi zamana har sanda zata kira Ni,
Ai kuwa babu jima wa sai ga shi ta aiko Mubashir ɗakin in zo in cire musu kaya in yi musu wanka,
Hakan ne yasa na fita zuwa ɗakin nasu, nayi musu wanka sannan na saka musu kayan barci, daga haka na koma ɗaki tunda na san ba wani sauran abun da zan yi,
Sai da na bari sun daidaici barin falon; wurin karfe sha ɗaya sannan na fito saɗab-saɗab na cinye sauran abincin su, daga nan na koma na kwanta, dayake yau na samu na runtsa nayi barcin rana, shiyasa barcin bai ɗauke Ni da wuri ba sai daga baya, asuban fari na tashi na fara aikin da na saba koyaushe wadda na zama musu ƴar aikin gidan bisa tilas; tunda bani da galihu bare in samu sassauci daga mutanen gidan.***

_____Ranan Monday daga Aunty Sharhabila har Yaya Yunus suka shirya zasu tafi wurin aiki,
Ni na yi wa su Sadam wanka na saka musu kayan makarantan su, bayan sun gama karyawa da zasu tafi Aunty Sharhabila ta ja min kunne sosai a kan gidanta da kulan mata da zan yi dashi, sannan ta faɗa min abun da zan girka musu, "zuwa ƙarfe biyu zasu dawo gidan in tabbatar na gama komai,"
Na amsa mata jiki na rawa har sanda suka tafi sannan na fara aikin, ba ƙaramin daɗi na ji ba da gane cewan aiki zata fara daga yanzu, ko banza na rage samun tsangwama daga wurin ta, yanzu zan riƙa kasancewa Ni kaɗai har sanda zasu dawo, wataƙil na samu rahama a wannan lokacin.
Sai da na gama aikin tsab sannan na samu wuri ƙasan Kujeran na zauna ina duban wurin Tv, duk da a kashe yake, basu bar min komai ba sai da suka kashe, amma na zauna ne in huta kafin in ɗaura musu abinci kamar yadda ta umarce Ni, ban ɗaura da wuri bane kar yayi sanyi sai da na daidaici sha ɗaya tayi sannan na shiga kitchen ɗin, kamar yanda a risho ta bani damar yin mata girkin haka na ɗaura na soma yi, duk da ba komai na iya ba na game daga cikin abincin su, taliya da Macaroni tare da shinkafa kawai na iya girka wa, sai suyan dankali da ta koya min tare da ƙwai, duk da dama na saba yin girki a gidanmu shiyasa hakan bai wani bani wahala ba, a cimanmu na ƙauye babu abun da ban iya ba kasancewar yadda aka hora Ni da aiki.***

A wannan lokacin ne su Umma suka ƙariso gidan, bayan sun buga ƙofa mai gadi ya fito ya same su, sai da suka gaisa sannan suka nuna mishi gidan suka zo wurin mai gidan, suka faɗa sunan shi,
Mai gadi yace musu, "mutanen gidan ba sa nan gaskiya, sai dai mutum ɗaya ina tunanin ƴar aikin gidan ne."


Hankalin su ya ɗan tashi don har fuskokinsu sun nuna alamun damuwa, Umma sai tace mishi, "don Allah ya barsu su shiga su jira su saboda baza su iya tafiya ba."

Mai gadin ya basu hakuri a kan, "bazai barsu su shiga ba," amma ganin yanda suka matsa sosai suna ta roƙon sa, har Umman take faɗa masa, "wurin ƴarta ta zo kuma Matar mai gidan ne."

Da mamaki mai gadin yake duban Umma, duk da bai san wace ce Mahaifiyar Sharhabila ba; amma ya tabbata wannan baza ta zama Ummanta ba, amma haka nan sai yace, "su shigo yayi musu jagora ciki."
Abun da yasa yayi haka kar yayi laifi ne tunda tace ita ce Mahaifiyar Matar gidan, tunda a tunaninsa Sharhabila ce; babu wanda ya san Madina matarsa ce,
Har ciki ya shigar da su, ya buga ƙofan yana jiran a bude musu

Ina kitchen ina aiki lokacin na ɗaura sanwan abincin kenan, sai na ji bugun ƙofa, dayake na rufe shiyasa sai na fita da sauri ƙirjina na buga wa don a tunanina masu gidan ne suka dawo; ga shi ban gama girkin da ta bani ba, hankalina ya soma tashi zuciyata tana buga wa da ƙarfi, cike da tsoron da ya zame min jiki yanzu na saka hannu na rawa na bude ƙofan, babu zato babu tsammani nayi arba da su Umma a bakin ƙofan; wani ihu na saka da ban san sanda ya fito daga bakina ba, cike da kerma cikin hanzari na faɗa jikin Umman cikin tsananin farin ciki da murnan ganin su

Mai gadi tunda ya ga haka sai ya juya sabida ganin yanda na tabaibaye Umma ina ihun murna, a ransa yayi tunanin ƙila ƴan uwana ne kenan, tunda ya ga na nuna na sansu shiyasa yabar wurin kawai

Yayinda Ni kuma tuni na ɗafe Umman na ƙi sakinta ina kiran sunanta bakina ya ƙi rufuwa, faɗan murnan da na ji a wannan lokacin bazai iya misaltuwa ba, don ban taɓa tunanin ganin su a wannan lokacin ba, musamman da na ƙilla ido na ga Yaya Haula tana dariya itama, dariyan farin ciki da ya bayyana a kan ƙaramar fuskarta irin nawa,
Take na saki Umma na koma na rungume ta sai na fashe da kuka tsaban farin ciki,
Itama kukan ne ya ciyo ta tana hawaye tana dariya tare da ƙanƙame Ni

Umma da ta ga haka sai tace, "kai Madinah! Wannan murna haka har da kuka? Kukan kuma na mene ne tunda gamu mun zo?"

Jikina na janye ina kallon Umman idanuna sharkaf da hawaye, yayinda cikin yanayin raunin da ganinsu ya sanya Ni nake cewa, "Umma ai kin yi min alƙawarin zuwa amma kika ƙi zuwa sai yanzu, ina ta jiran zuwan ki har na cire rai."

Murmushi tayi ta kama hannuna tare da cewa, "mai zai hana Ni zuwa Madina? Ai ban manta da ke ba, bazan taɓa manta wa da ke ba har abada kina raina, mu shiga ciki zamu fi gaisawa sosai, kinga ki share hawayen ko tunda gamu."

Hannuna ɗaya na sanya a saman fuskata ina mai share hawayen, inda muka shiga ciki gaba ɗaya muka zauna a saman Kujerun Falon, dukkansu sai kallon falon suke yi suna mamakin kyawun sa da alatun da ke ciki, musamman Yaya Haula wacce bata saba ganin irin sa ba, gwara ma Umma tunda tana aiki gidan Hajiya Ummee bata wani nuna kauyancin ta ba, amma tayi mamakin ganin gidan Yaya Yunus ɗin, tare da tunanin duk wannan daulan nasa ne kenan? A nan ƴarta take rayuwa?
Ita kanta Yaya Haula abun da take tunani Kenan, sai kawai tarin farin cikin ta ya yalwata tana ganin inda ƴar uwanta ta samu ci gaba,
Yayinda dukkansu kallona suke yi cike da burge wa don ba ƙaramin sauya musu nayi ba a wannan ƙanƙanin lokacin, baza ka taɓa tunanin Ni bace sabida fatar jikina ta ƙara haske da sheƙi, ainahin fatata ta sake fitowa sabida samun hutu da jin dadi, ga dai shi ba wani daɗi nake ji a gidan ba, amma yanayin sauyin wuri da kuma AC da ke ratsa Ni; shiyasa nan da nan jikina ya sauya, da alamun jikina bai da wuyan sauya wa ne don su mamakin ganin kyawuna suke yi, duk da sun ga ƴar raman da nayi a fuska kasancewar fuskar tawa bata ƙara komai ba, idanuna suna waje har yanzu sun sake fitowa ainun, har da ƙashin wuya, amma gani suke yi kamar na ƙara tsawo da girma kaɗan da kyawun fata,
Sun ji daɗin ganina a haka matuƙa,
Amma duk da haka Umma sai tambayana take yi yanayin zaman nawa tana ce min, "babu wata matsala ko?"

Ko kusa ban faɗa mata halin da nake ciki ba, duk da a lokacin ba wai na dena hawayen nawa bane sabida tsananin kewarsu da nake ji, a tsakiyar su na zauna na ƙanƙame su; su dukka kamar za a ƙwace min su

Umma da ke kallona ta shafa kaina cike da samun natsuwa kaso bakwai bisa goma na daga damuwar da ke damun ta, take ce min, "to mene ne na kukan wai Madina? Ko dai akwai abun da ke damun ki ne kin ɓoye min kin ƙi ki faɗa? Ko kuma Yayan naki yana miki wani abun ne baza ki iya sanar min ba?"

Da sauri na girgiza kaina ina mai cewa, "a'a Umma, babu abun da ake min, ina jin daɗin zamana, amma Umma kewarku nake yi, na san zaku tafi ku bar Ni."
Sai kawai wasu hawayen masu zafi suka sake wanke min fuska

Yaya Haula da ke dariya tace, "haba Madina, mene ne kuma na kuka tunda Allah ya kawo ki inda za ki huta? Ai nan ya fi wancan ƙauyen namu gwara zamanki a nan wlh, ba ki ga yanda kika

Please Login or Register in order to submit comment