Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi shiru ya juya ya fice a ɗakin, domin a yanda ransa yake a ɓace bazai iya ƙara magana a kan abun da ya faɗa ba, ya saba idan zai je masallaci in har a gida ne yakan tasa yaran su tafi, amma yau ko bi ta kansu bai yi ba yabar gidan, yayinda zuciyarsa ke ƙuna da tafarfasa sabida gorin da Matarsa tayi masa, abun da bai saba faruwa bane sai a wannan lokacin, bai taɓa tunanin zata yi masa haka ba, har shi yau Sharhabila take kallon tsaban idanunsa tana masa gori a kan gida? Sabida shi ya ja wa kansa, a kan sonta; a kan soyayyarta yabar ahalin sa ya zo ya zauna da nata ahalin don dai ya faranta mata, a kan tsananin soyayyar da yake mata ya zama ba komai ba ya ƙasƙantar da kansa duk don ita, amma daga ƙarshe dole sai ta nuna masa ainihin wane ne shi, tabbas ta tuna masa shi ba komai bane; bai zama komai ba sai da taimakon Mahaifinta, Mahaifinta shi ya zamar da shi Mutum dole ta samu bakin masa gori, hmmm wanne baki kuma yake dashi yanzu da zai iya kare kansa?

Inda yabar Sharhabila cike da baƙin cikin kalamansa, yayinda ta kasa aiwatar da abun da tayi ninya don ba ƙaramin shakkar maganarsa tayi ba, sabida fushin sa ba abu bane mai kyau ba, in har yace zai yi tabbas zai yi ne, amma a yanda take matuƙar son Yunus baza ta so su rabu haka ba, sai dai wacce ta haɗa abun a kanta zata huce, wlh tallahi sai kowa ya san ranta ya ɓaci a gidan nan,
Ko bi ta kaina bata yi ba tabar dakin fuuu kamar zata kifa

Yayinda Ni kuma na sauke numfashin tsoro ina mai dafe ƙirjina wanda kamar zai fashe tsaban tsoron abun da zai biyo baya, sai kawai na duƙe a wurin na fashe da kuka sabida ban san wanne irin ƙaddara ce zata afka min ba, na san bazan sha ba tunda Matar gidan ta ɗauki wannan fushin, haka kawai zan shiga tsakanin su; a kaina ake wannan faɗan? Wayyo Allana na shiga uku na lalace! Ni Mace ce mara son fitina, haka kawai hankalina yayi matukar tashi kuka kawai nake yi kamar raina zai fita, wlh gwara in bar gidan da in zauna ina ganin Aunty Sharhabila a wannan yanayin na san bazan ji da daɗi ba,
Ko bi takan Sadam ban yi ba; wanda yake ta kiran suna na yana cewa, "in dena kukan." Shima ganin ina kukan ne yasa shi yin kukan sosai,
Shi kuwa Mubashir tuni ya bi bayan Mamynshi tunda shi bai cika shiga harka na ba, shi ɗan babu ruwansa ne,
Daga ƙarshe shima Sadam ɗin fita yayi a ɗakin yana kukan yana kiran sunan Dadyn su, zai je ya faɗa masa halin da nake ciki

Ni kuwa tsoro da firgicin abun da zai biyo baya yasa na kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi, ina zaune na sake takure kaina ina zubar da ruwan hawaye, ina tunanin abun da zai biyo baya kuma,
Amma shiru-shiru babu motsin mutanen gidan, da haka na miƙe na shiga bayi nayi wanka na sauya pad ɗin da aka bani a asibiti, sannan na zo na kwanta cikin ɗar-ɗar da tunanin Aunty Sharhabila zata iya zuwa ta rufe Ni da duka, tun ina jin tsoro da fargaba har dai barci ya zo ya tafi dani a wannan halin, batare da nayi tunanin neman abun da zan saka a cikina ba, don halin da nake ciki yasa ko yunwan ma ba na ji.
Da asuban fari na farka tunda dama na saba tashi a wannan lokacin, sam ban yi barci ishashshe ba sabida halin da nake ciki, ga yunwa da sai yanzu ne yake kartan min ciki kamar zan mutu, amma ban yi wata-wata ba na fita zuwa falo na soma gyara wa a wannan halin don dai kawai kar in kuma yin laifi, don na san laifi na nawa kuma sai dai kar in kuma, dayake akwai hasken glop shiyasa nan da nan na gyara tsab sannan na kwashe kulolin da ke saman daining na nufi dashi kitchen, tun abincin da nayi da rana ne wanda ko loma basu ci ba, sai ɗan kaɗan da aka tsakura ina tunanin yaran ne suka ci shi, sai kuma kofin tea da na ga an haɗa, shiyasa sai da na cika cikina da abincin jiyan sannan na koma yin wanke-wanken, ina jin kamar motsi a falon amma ban fita ba sabida zullumi

Ashe Yaya Yunus ne ya dawo daga masallaci, shima ya ji motsi a kitchen ɗin; wanda ya san cewa bazai wuce Ni ce ba, ɗaki ya wuce ya kwanta tunda rigima suke yi da Sharhabilan, jiya kwana suka yi suna faɗa wanda yayi zuciya ya koma ɗakin sa suka raba ɗaki,
Gari na washe wa ya tashi yayi wanka ya kimtsa zuwa wurin aikin sa,
A lokacin da ya fito nima tuni na gama musu breakfast har nayi Wa su Sadam wanka na shirya su,
Lokacin na koma ɗakina ina jiran jin kira daga Sharhabila, amma shiru bata kira Ni ba, ina ta tsumayen kiranta wanda na san bazai zamar min alkhairi ba, gabana sai bugun uku-uku yake yi, har dai na ji ƙaran Mota alamun sun fita,
Har zan fita kuma na sake jin motsi, ina leƙa wa na hangi Aunty Sharhabilan ne da alamun ita yanzu ta fito, tayi shirin ta na zuwa office wanda ta fita daga baya, a cikin motanta daban ta fice a gidan, abun da tun fara aikin nata tare suke fita da Yaya Yunus,
Ni dai tunda na ga ta fice na sauke ajiyar zuciya ina mai kama ƙirjina tsawon lokaci; a raina ina jin daɗin shan da nayi bata yi min komai ba,
Sai lokacin nayi wanka na shirya cikin doguwar riga baƙa, bayan na sanya pad ɗin da aka bani tare da wando, sannan na koma sauran ɗakunan su na gyara na kimtsa, har aikin da ta bani jiya wanda ban yi mata ba na gyaran sif ɗin ta, sai da yau na zauna na goge na mayar mata dasu tsab na shirya, sannan na je na ɗaura girki tunda yau bata bani abun dafa wa ba, kawai nayi gwanintan sake girka shinkafa da miya tunda akwai raguwar miyan jiya, yau nayi taka-tsan-tsan nayi shi lafiya babu wata matsala,
Sannan nakai musu falo na koma na gyara ɗakina, domin tun zama na a gidan nan na koya tsabta don dole, tunda idan ma nayi ƙazanta cin Ubana take yi Matar gidan, don haka nima na koya, ko don ƙirƙiran ma kaina aiki tunda ban saba zama haka nan ba, idan na gama musu nasu sai in koma in gyara nawa ɗakin, shiyasa kullum tsab dashi babu wata matsala, Ni kaina ma a yadda na sauya baza ka taɓa tunanin Ni ce wannan Madinan ta ƙauye ba;
bayan na gama gyara wa ne na tsaƙulo kayan da Ummana take kawo min, kayan girki, wasu waɗanda na san Aunty Sharhabila tana amfani dasu sai nakai kitchen na ajiye, waɗanda na san ba sa amfani dashi ban taɓa ganin sun yi amfani dashi ba tun zuwana gidan, kamar kayan miya, su; Kuka da kuɓewa, shiyasa sai na fita na zagaya ta bayan gidan na jefar da su, sannan na koma ciki.***

Ashe wasa farin girki ne daga nau'ikan azaban da Sharhabila ta tanadar min, dama na san cewa baza ta taɓa bari na nayi walwala da farin ciki a gidan nan ba, domin tun a ranan ta soma hukunta Ni a kan laifin da nayi mata, duk wani fushinta a kaina ta sauke, wani abun ma da gayya take yi domin Yaya Yunus ya tanka ta tunda a kan faɗan da suka yi ne, amma tayi tunanin zai iya hana ta dukana ko hukunta Ni; wanda ta shirya masa gadan-zare, don tsab ta yanke shawaran zuwa ta sanar da Dadynta, ta gilla mishi ƙaryan da sai ya gane bai da wayau, kuma dole a kore Ni a gidan, amma kamar ya san abun da ke zuciyarta ko uffan bai sake ce mata ba,
A gabanshi ta janyo Ni ta dinga kima daga kuskure kaɗan, duk tayi min ruɗu-ruɗu da fuska, amma bai ce mata komai ba, tunda ya ga alamun rigima take ji,
Kuma har a ransa sai da ya ji tausayina wanda bai taɓa jin irin sa ba, amma ko nuna wa a fuska bai yi ba,
Ni dai na ɗauke su gaba daya mugaye ne mara su imani, babu mai tausayina a cikin su, tunda shi kansa Yayan nawa yana gani tana min cin mutunci da ɗiban albarka bai ɓata cewa komai ba, nayi kuka a wannan lokacin har na gode wa Allah,
A tsakanin wannan ranakun ba ƙaramin wahalan ta na sha ba, idan zan samu sukuni sai idan tabar gidan zuwa wurin aiki, fuskata gaba ɗaya ta sauya kamanni sabida marukan da nake sha a wurinta, har tara jini idona na dama yayi, dayake abun ka da fara fuskata ta tasa sosai tayi jawur, domin kuskure kaɗan ko ban yi mata komai ba sai dai in ji ƙaran mari, tun ina jure wa amma inaa kuka sosai nake fashe mata dashi,
Kuma ta daka min tsawa tace, "in shiru don ubana."
Dole zan shanye in na koma daki in yi mai isana babu mai rarrashina tunda bani da yanda zan yi, a raina har na soma yanke hukuncin barin gidan, amma ina zan je? In na tuna akwai auren Yaya Yunus a kaina raina yana ɓaci ina shiga cikin wani hali mara misaltuwa, domin na san ko na tafi sai an dawo dani, bani da sauran wani gata kuma a rayuwa, na sallama wa farin ciki, dole a haka zan ƙare rayuwata, dalilin da yasa kawai na shanye duk wani cin kashi da ɗiban albarkan da take min, na san wata rana komai zai wuce, domin ina ji a jikina lokaci kaɗan ne ya rage min in mutu in bar musu duniyar, a yanda nake matuƙar bukatar mutuwata a wannan lokacin domin huta wa daga azabobin da nake fuskanta, tun ban san komai ba a rayuwa amma wahala ta sako Ni a gaba, daga wannan sai wancan, a ɗan ƙanƙanuwa ta har ina tunanin mutuwa a kan rayuwa, to mai ya fi min a yanzu? Sabida kamar a rayuwata munanan ƙaddara ce suke faruwa daga wannan sai wancan, wani abun tashin hankalin wanda ya ƙara tarwatsa min ɗan guntun farin cikina da nake iya rayuwa dashi, ina tunanin komai ya wuce na sallama ce wa zan yi zaman aure a gidan nan, sai sabon abu ya bijiro min,
Bayan sati ɗaya da kwanaki uku da faruwan faɗan su Yaya Yunus, ashe har lokacin basu shirya da Sharhabila ba, dayake shi mai sauƙin fushi ne bai yi kwanaki uku da faɗan ba ya sauko yana mata magana, amma ita sam ta ƙi karɓan sa, sai ma farfaɗan masa maganganu da take yi, tana ce masa, "in har bai kore Ni a gidan ba; shi da zaman lafiya har abada."
Ya san halin Sharhabila idan ta kama abu ba ta jin bari, amma sai ya share ta ya ci gaba da jawo ta a jiki sabida shi har ga Allah shi yake cutuwa da irin wannan faɗan nasu, domin bazai iya jure har wani lokaci suna ƙin haɗa shimfiɗa ba, duk rarrashin da ya yi wa Sharhabila domin ya samu su dawo dai-dai amma abun ya faskara, yayi-yayi amma abun ya faskara, wanda ya ja su da har sun shafe fiye da sati ɗaya ana abu ɗaya, yayi nacin har ya gaji,
Ga shi kuma hakurin sa ya gaza duk yanda ya bi da ita ta ƙi ba shi haɗin kai, kansa yayi zafi ya shiga wani hali mara misaltuwa, buƙata tayi masa yawa wanda ya ja har ba ya iya samun sukunin kansa,
Daga karshe sai da ya koma ya bata hakuri ya duƙa har ƙasa yana rarrashinta a wannan daren, daƙyar da siɗin goshi ya samu kanta sai dai ba a yanda yake so ba, don ƙiri-ƙiri ta ƙi ba shi haɗin kai sai dai yayi wasan sa da sassan jikinta ya gaji shi kaɗai yayi kiɗan sa yayi rawansa,
Wanda hakan ne yasa gaba ɗaya ya tashi a ranan babu wani sukuni tunda bai samu abun da yake so ba, kamar ma ya ƙara tsokano wa kansa ne, amma ya ya iya? Haka nan ya haƙura da safe suka shirya suka wuce wajen aiki, shi ya ɗauki Yaran ya sauke su a school ɗin su; tunda tun faɗan har yanzu a motanta take tafiya, ta dena bin sa,
A haka ya sauke yaran sannan ya wuce wurin aikin, amma sai dai gaba ɗaya ya kasa sukuni sabida wani irin tarin sha'awa da ya addabi maransa, cikin wannan yanayin ne ya tuno Ni a gida, lokaci guda tunanin aurensa da ke kaina ya faɗo masa, ba ƙaramin mugun dad'i ya ji ba a lokacin, domin yana ganin wannan babban hanya ce da zai iya yakice matsalarsa, tabbas wannan rana zan yi mishi amfani, ba dai nima Mace bace, kuma a hakan ai ake mana aure a ƙauye muke zama, ba ya tunanin zai iya jure wa ya haƙura ya kawar da kai a kaina batare da gusar da matsalarsa ba, don haka tuni ya zari mukullin mota yayi gida

A lokacin ina tsaka da gyara ɗakunan su ne, ina cikin ɗakin sa ina wanke toilet ya faɗo gidan,
Kansa tsaye inda ɗakina yake ya nufa yana wurwurga ido ya ga ta inda zan fito, amma koda ya shiga ya ga wayam babu kowa, a halin da yake ciki kwata-kwata babu natsuwa a tattare da shi, kawai burinsa ya hango abun harin sa, don har sai da ya leƙa toilet ɗin ɗakin bai ganni ba, sannan ya dawo da sauri ya nufi kichen, nan ma ya ga babu Ni sabida ko shiga ban yi ba, ina jiran in gama gyaran ne sai in ɗaura musu abinci,
Hanyar ɗakunan su ya nufa yana kwaɗa kiran suna na,
Ina cikin bayi kamar daga sama na ji ana kiran sunan nawa, wanda tuni na shaida muryansa, ai da gudun gaske na fita har jikina na rawa ina amsa mishi,
Lokacin har ya buɗe ƙofan ɗakin Sharhabila zai shiga; sai kuma ya ji muryata daga cikin ɗakin sa, da saurin sa ya juya ya shige muka kusa cin karo a bakin ƙofan, har sai da na buga kaina a ƙirjinsa,
Sai kawai na ji ya ƙanƙame Ni maimakon dukan da zan ji ya diran min, da sauri nayi ƙoƙarin ɗago kaina in dube shi don in tantance shi ɗin ne ko kuwa wani ne,
Amma ina ya hana hakan don tuni ya matse Ni a jikinsa yana mai sauke wani irin numfashi mai wuyan fassara,
Nan da nan kuwa jikina ya fara wani irin kerma na fitan hankali, dama ya lafiyar gwiwa bare tayi hauka, wani irin tsarga wa da cikina yayi na tsananin tsoron da ya shige Ni, take nayi saurin ƙwace jikina ina matsa wa da baya cikin wani irin yanayi ina zazzaro ido a kansa


Shi kuwa wani kallo yake min kamar wani maye ko Zakin da ya ga abincinsa a dawa, amma sabida ganin halin da na shiga sai ya ɗan sassauta yanayin sa murya a kasalance ya janyo hannuna; wanda har nayi ƙoƙarin juyawa in shige ƙuryan ɗakin sabida daburce wa,
Amma ya hana hakan, riƙo Ni sosai yayi yana bi na da kallo, sai kuma ya ɗan sassauta murya yace, "ina za ki je kuma? Kiran ki fa nake yi."

A daburce cikin rawan murya kamar ana kaɗa Ni nace, "dama zuwa zan yi."

Ba ƙaramin yanayi ya ji ba yau da ya ji saukar muryata a cikin kunnensa, ko don yana cikin wani hali ne oho, don yau sai ya ji kamar an sanya sweet a cikin muryan, yadda take shacking sai ta ƙara haifar mishi da wani irin shauƙi, ji yake yi bazai iya ɓata lokaci wajen fahimtar dani abun da yake muradi daga gare Ni ba, don haka tuni ya saki hannuna ya juya ya datse ƙofan har da murza mishi key,
Juyowan da zai yi tuni idanuna sun shige cikin nasa, haka kawai wani matsanancin tsoro ya rufar min; wanda rabon da in ji irin sa tun abun da Alh. Badamasi yayi min a baya,
Ai take na juya da sauri har ina ƙoƙarin kifa wa; nayi hanyar toilet zan shige zuciyata na wani irin tsinke wa gami da buga wa kamar zata fito,
Ko taku biyu ban yi ba; na ji an ɗaga Ni cakk ban tabbatar da abun da ke faruwa ba sai gani na nayi a saman gado. Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un!. Mafarkin da nake tunanin ya shuɗe a cikin babin rayuwata; mafarkin da ba na fatan dawowan sa cikin tarihin rayuwata, uƙuban da nake tsoron kamanta sake jin irin irinta a rayuwata, ita ce take tunkaro Ni a wannan gaɓan; waye zai cece Ni?.



_Kuna ganin Yayanta Yunus zai ci galaba a wannan sauyin ƙaddaran da zai sake faruwa da Madina? Ko kuwa aikin da Boka ya yi wa Alh. Badamasi bazai sake bada damar da wani zai iya sake kusantan ta ba na har abada?😨 Hmmm amsar na wuri na, ku ci gaba da bi na kawai domin ku sha labari. Tabbas *RAYUWAR MADINA!* akwai tarin ƙaddara da ƙalubale masu ban tausayi da ƙunan zuciya._
[06/08, 10:49 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 550
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 27*
_____A wannan gaɓar babu tausayi bare wani tunanin mai zai je ya dawo kan hukuncin da zuciyarsa ta yanke mishi a wannan ƙanƙanin lokacin, a halin da yake ciki bazai iya cewa ga abun da ke faruwa ba, amma yana jin zuciya na ɗibansa; sha'awa na rinjayar sa wanda shine dalilin da yasa ya neme Ni bai shirya ba, ko a mafarki shi kansa bai shirya wa hakan ba, amma ba shi da yanda zai yi tunda yana cikin matuƙar buƙata, ya san cewa ba abun da zai samu tunda kasancewar yadda yake ganina babu wani abun sha'awa da zai iya rinjayar sa zuwa gare Ni, amma kuma ƙaddara ce, bazai iya haƙura ba, don ji yake yi tamkar ana ƙara hura mishi wutan sha'awar dole sai ya kusance Ni,
A halin da nake ciki sam ba ya jin ihuna da kururuwa na, sai ya zamana tamkar a sama yake ji na, daga baya kuma ya dena ji, bai fahimci abun da ke faruwa ba, bai gane cewa zallan tsoro gami da rikitacciyar firgitan da nake ciki; tuni zuciyata tayi wani irin buga wa da nan take numfashina ya rabu da gangan jikina,
Amma sam bai sani ba, kawai abun da yake hango wa ya samu buƙatarsa, kai tsaye sai ya nufi abun da yake hari bayan da ya raba Ni da kayan jikina, shi kansa bazai ce ga abun da yake ji ba, kawai dai ya san ya jefa ƙwallonsa a raga daƙyar; wanda abun da yasa hakan kasancewar ɗinkin da aka yi min daƙyar ya nemo hanya ya shiga, sai dai kuma wani irin raɗaɗi da ya tsarga mishi lokaci guda ya saki wani ƙara,
Wanda yayi dai-dai da farkawata sakamakon makamancin raɗaɗin da na ji daga jikina, take na farfaɗo na yanka wata uban ƙaran nima; daga nan ban ƙara iya motsa kaina ba, ina a farke tabbas ina jin abun da ke faruwa, amma ina jin kamar ana tsira min wata allura mai shegen tsini da azaba, azaban da ke ratsa Ni yasa na gaza wata ƙwaƙƙwarwan motsi sai ruwan hawaye da ke zuba a fuskata, kuka nake son in yi da ƙarfi; amma kamar ba na duniyar, idanuna ne a bude amma hankalina da tunanina sun riga sun gushe gaba ɗaya, azaba da raɗaɗin da suke baƙunta na sun gusar dani daga gane komai a duniya

Wanda shi Yaya Yunus shi kansa daure wa ne yasa shi ci gaba da abun da yake yi, domin ji yake yi tamkar ya saka kansa a rijiya mai tsananin kwalabe masu hatsari, take a nan ya soma dawowa cikin hayyacinsa sabida sam ba daɗin abun da yake yi yake ji ba, sai ma wata wahala da take baƙuntansa wanda yake fitar da gurnani kamar zai mutu, tsananin bushewa da rashin ni'iman da ke jikina; ya haifar mishi da jin wannan azaban mai muni, wanda tuni jini ya ɓalle a jikina; ga kuma wani farin ruwa da ke biyo baya lokacin da ya gama janye jikinsa daga jikina, kawai mamakin abun da ya ji yake yi daga jikina, sam babu wani ni'ima da testing ɗin da zai iya cewa ya ji, sai ma bak'ar wahala da ya kwaso, ya rasa ma yanda zai yi sabida ganin yanda jinin gaba ɗaya ya ɓata min jiki kuma alamun fita yake yi har lokacin,
Take hankalin sa ya soma tashi don yana tunanin shi ne ya ɓallo wannan ruwan,
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Abun da ya iya furta wa kenan yana mai miƙe wa jiki a mace, ƙoƙarin mayar da kayansa ya soma yi yana tunanin yanda zai yi ya taimaka min,
Koda ya leƙa fuskata ya ganni a farke amma ba ya tunanin ina cikin hayyacina sam, don haka tuni ya sure Ni sabida tunanin a kowanne lokaci Matarsa zata iya dawowa ta tarar dashi a haka, Wayyo ya ja wa kansa, mai yayi haka?
Toilet ya shiga ya haɗa ruwa mai zafi sannan ya dawo ya nannaɗo Ni tamkar tsumma ya kaini ya saka Ni a cikin ruwan


Tsananin azaban da ya ƙara kunno min ne lokaci guda na dawo cikin hayyacina, wani irin kuka na saka ina mai yarfe hannuna idanuna tuni sun rufe tsaban wahala, kuka nake yi kamar zan shiɗe ina ƙoƙarin fita daga cikin ruwan,
Amma sai ya danne Ni yana mai kiran suna na tare da buga fuskata,
"Ke.. ke.. Madina, ke Madina buɗe idanunki, maza buɗe idanu."
Yadda muryansa ya daki ƙoƙon kunne na; tuni na dena sambatun da nake yi na bude idon a nan take na sauke a kansa, wani irin ƙara na saka sabida ganin sa a gabana take numfashina ya sake janye wa daga jikina, na tafi luuu da ninyar zillewa a cikin ruwan,
Saurin riƙe Ni yayi yana zuba salati hankalinsa a matukar tashe, tunanin sa kawai kar ya kashe musu yarinya sabida yana ganin zallan tsoro da firgitan da nake ciki,
Take yayi ƙoƙarin sauya ruwan sabida duk ya ɓaci da jini, ya sake sanya wani yana ta watsa min ruwa a fuska don in farfaɗo, amma inaa abun ya gagara,
Sai kawai ya ɗauko Ni ya fitar dani daga ɗakin yana mayar da ni inda nake kwana,
Da sauri ya koma ya ɗauko min kayana ya zo yayi ƙoƙarin saka min, ganin kamar na soma ɓata gadon da jinin wanda yake ganin bai tsaya ba har yanzu, sai kawai ya sake rikice wa gaba ɗaya jikinsa rawa yake yi, mike wa yayi ya lalubo wando ya saka min sannan ya mayar min da kayan nawa,
Sai ya koma ya fita ya je ya ɗauko wayansa ya kira Abokinsa Doctor Bilal, yana ɗauka bai tsaya wani biye masa wurin gaisuwa ba; tunda hankalin sa a matukar tashe yake, muryansa ma ta nuna halin da yake ciki, take yake ce masa, "don Allah ya zo gidansa yanzu babu lafiya, ya zo da hanzari zai duba patient."

Doctor Bilal yace, "subhanallah... To gani nan insha Allahu."
Abun da ya furta kenan bai tsaya jan zancen ba, don tunda ya ji haka ya san babu lafiyar ne

Shi kuma Yaya Yunus koda ya kashe wayan sai ya ɗauki rigansa ya mayar a jikinsa, dama wando kaɗai ya saka ɗazu, ya fito falo yana zirga-zirga ya rasa abun yi, wayansa ya duba ya ga agogo time ɗin karfe 11 ne, ya san akwai sauran lokaci before Sharhabila ta dawo, since 2 o'clock suke tashi daga wurin aiki,
Ya san

Please Login or Register in order to submit comment