Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hana Ni sai yace, "bari in sosa miki a hankali kar ki ji ma kanki ciwo, Ni zan fi ki iyawa." Yayi maganar cike da farin ciki yana kware min skirt ɗina, ya ɗaura hannusa a saman...

16/6/2023.
[17/06, 8:27 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎

_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._

           









______________ *EPISODE 6*
_____Hannunsa na riƙe ina sakin kuka a hankali. Ganin yanda duk na tsorata sai ya cire hannun; Ni kuma na ci gaba da sosawa sabida bazan iya jurewa ba, ƙoƙarin tashi nake yi amma ya ƙi saki na

Yace, "wai mene ne ya same ki a wurin kike wannan susan? Kar kiji ma kanki ciwo ki bari in sosa miki." Yayi maganar a cikin lallami

Ni kuma na ƙi yarda sabida tsaban tsoro duk na firgice, ga wurin kamar ana ƙara min ƙaiƙayi ya ƙi bari na in tashi bare in sosa yanda yakamata, sai kawai na fashe mishi da sabon kuka cikin rauni nace, "don Allah ka bar Ni in tashi yana min zafi."

"Haba Madina ki bari Ni in sosa miki, ba na son kina min gardama nace ko." Ya ƙare maganar yana cire hannuna a wurin; shi ya saka nashi, a hankali ya soma sosa min Ni kuma ina ci gaba da kuka, amma kasancewar ina jin daɗi sai ban hana shi ba sai kuka nake yi, ya sake cewa, "kiyi shiru kar wani yace wani abun nake miki, ba na son kukan ki."

Take na shanye kukan sai dai na kasa tsayar da hawayen

Hannu yasa ya ƙara ɗaga skirt ɗina yana shirin cire min wando tare da cewa, "bari muga mene ne a wurin yake saka ki jin ƙaiƙayi?"

Cikin rawan baki na kama hannunsa ina cewa, "a'a ka bari ba na so, kar ka cire min wando."

Kallona yayi yai dariya yace, "ashe kina da wayau? Ni fa Mijinki ne baza ki hana Ni abun da nayi ninya ba, ina lallaɓa ki ne idan ba haka ba zan sanar da baffanki tunda gardama kike son min a matsayina na Mijinki."

"Don Allah kayi haƙuri kar ka faɗa mishi." Nayi maganar a cikin tsoro da shashsheƙan kuka

Yace, "to yi shiru ya isa haka, ba na so kina kuka saboda ba kuka na zo saka ki ba, ki cire tsorona a ranki bazan cutar da ke ba zan kula da ke kinji ko?"

Kaina na gyaɗa mishi ina jan ajiyan zuciya

A hankali ya ci gaba da sosa min wurin ba tare da ya cire min wandon ba, sai da yayi sosai kafin yace, "ya isa haka?"

Da sauri na gyaɗa mishi kai sabida ba na son ya ci gaba da yi duk da har yanzu wurin bai dena min ƙaiƙayin ba, amma tsaban tsoro yasa na ɗaga mishi kaina

Murmushi yayi yana lakutan min hanci tare da cewa, "kin cika tsoro wlh, amma za ki saba dani ai. Yanzu tashi ki je amma ki share hawayen ki."

"To." Na amsa mishi da sauri jikina na rawa. Yana saki na kuwa na tashi zumbur zan tafi

Sai ya riƙe Ni yana min murmushi tare da cewa, "zan shiga birni gobe zan yi kwana biyu sabida kasuwanci na, me kike so in siyo miki a can?"

Shiru nayi na sunkuyar da kaina ban ce mishi komai ba

Sai ya sake murmusawa yace, "to share hawayen mana."

A hankali na sa ɗaya hannuna na share ina sake duƙar da kaina. Sai ya sakar min hannun na juya da sauri na fita, kamar an ciro Ni a ƙaya haka nake ji don ban tsaya a ko'ina ba sai a ɗakin mu. Haka nake ta numfarfashi sai kace wacce aka biyo

Inna Asabe da ta ga shigewa na; sai ga ta ta biyo NI ɗakin tana ɗaga labulen tare da cewa, "Madina har kin dawo ne?"

Kallonta nayi sai ban ce mata komai ba na sunkuyar da kaina; wata matsananciyar kunya ta kama Ni, domin gani nake yi kamar ta san abun da yayi min

"Oh! To Allah yasa dai ba gudowa kika yi ba, don yanzu daga zuwan ki har kin dawo, me yayi miki?" Tayi maganar don jin ƙwaƙwaf

Sai da gabana ya faɗi tsaban yadda nake a tsorace; amma sai nayi shiru da ita ina mirza yatsuna, na ƙi na ɗago kaina balle mu haɗa ido, wlh duk na tsargu

Inna Lami ta shigo sasan tana kiran sunan A'isha. Hakan ne yasa Inna Asabe ta juya ta saki labulen; ta wuce tana cewa, "ai yanzu aka kawo wuta sun tafi ɗakin Zainabu yin kallo, sai dai Madina ga ta nan ta dawo."

"Au har ta dawo ne?"

"Eh ga ta nan a ɗaki yanzu ta shigo, nima tambayar da nake mata kenan."

Inna Lami tace, "dama neman da nake yi ma Auta ruwa zata kai mishi, tunda ta dawo shikenan." Sai ta leƙo ɗakin tana kallona tace, "ya tafi ko?"

A hankali nace mata, "Eh." Ina ajiye gyalen da na gama ninke ma Nafisa

Ita kuma ta wuce bata sake cewa komai ba. Can kuma ta kwaɗa min kira tana cewa, "in ɗauko mata tsaki a ɗaki."

Dole na taso na fito na shiga ɗakin ta, na ɗauko nakai mata tana zaune a kichen. Kafin in kai ɗaki har Inna Habiba ta kira Ni ta sani aiki, dole na wuce nayi abun da ta sani, cike da dauriya haka nake yin komai domin tunda suka ga naji sauƙi kowa sai saka Ni aiki yake yi. Hakan ne yasa na ɗan manta da Alh. Badamasi na mayar da hankalina a kan abun da nake yi

Bayan su Binta sun dawo daga kallon da suka tafi ne; suka samu damar tambayana, tasa Ni a gaba suka yi sai tambayana abun da Alh. Badamasi yace min suke yi?

Ni dai nace musu, "babu komai, ya zo duba lafiyana ne." Daga haka ban ƙara ce musu komai ba

A nan ne Inna Asabe take cewa, "to komai bai ba ki ba haka ya bar ki?"

Nace mata, "eh."

Sai ta taɓe baki ta wuce tana surutai

Haka dai duk aka sa min ido sabida kiran nan da Alhaji Badamasi yayi min. Sai gulmace-gulmace ake yi ana surutai

Ni dai ban tanka su ba na shige ɗaki nayi banza da su. Duk wanda ya tambaye Ni kuma in amsa mishi iya abun da naga zan iya.

          Washe gari Yaya Haula bata zo ba. Sai na tambayi Inna Lami nace, "zan je gidanta."

Tace min, "bazan je ba tunda yanzu akwai aure a kanmu, babu inda zamu riƙa fita sai da dalili."

Haka babu yanda na iya na koma na ci gaba da ayyukan gidan wanda ya zama dole Ni zan yi in har ba rashin lafiya nake yi ba, duk da har yanzu ba sauƙi na ji ba amma ina lallaɓa wa ina yi, musamman yanda ƙaiƙayin gaba ya sako Ni a gaba duk na rasa yanda zan yi, abu kaɗan susa kamar wata mahaukaciya, ko kuma idan na je bayi in riƙa ganin jini na biyo fitsari na da wasu zare-zare, har yanzu na kasa sanarwa kowa haka na bar abun a raina, duk a tunanina jinin haila ne tunda an yi mana bayani lokacin da muke karatu, dayake ban taɓa yi ba amma yanzu da nake gani sai nake tunanin ko shi ne, shiyasa lokacin da aka yi kwana biyu naga ban ganshi ba sai nayi wanka na ci gaba da harkokina. Sai kuma can anjima da na shiga bayi na sake ganin ya dawo, duk a tunanina shi ne shiyasa na bari idan ya tsaya in sake yin wani wankan, amma kuma ya ƙi tsayawa duk idan na shiga bayi sai na ga jini yana zuba bayan na gama uzurina, tun abun yana damuna har dai na haƙura na bar komai a raina, wankan tsarkin ma na dena yi gaba ɗaya na ci gaba da rayuwata yanda Yakamata. Tun lokacin da Alh. Badamasi ya zo bai sake zuwa ba, duk da na zira idanu da fargaban dawowar shi kamar yanda yace min, amma jin shiru shiyasa na saki jikina na ci gaba da rayuwata, yanzu babu abun da ke damuwa sabida jikina ya warware sai ƙaiƙayin da nake fama dashi kawai, yanzu na rage jin tsoro da fargaba na auren domin har na manta cewa akwai aure a kaina, na koma kamar da abuna, ina shiga cikin ƴan uwana nayi wasa, idan aka sani aiki kuma nayi, bani da lokacin kaina ma bare wani abu ya dame Ni

A kai- akai Yaya Haula tana zuwa duba Ni, ganin na warware sosai walwalata ta dawo shiyasa ta ɗauke ƙafa itama hankalinta ya kwanta.     
***

           
_____Sati biyu curr sai ga Alh. Badamasi ya sake dawowa. Lokacin ina duƙe a makwararan ruwa ina yin wanke-wanke, sai sauri nake yi in gama sabida Inna Amarya tace min, "in Yi sauri in gama zata aike Ni." Murna nake yi sabida zan fita yau, don rabona da fita tun kafin aure na

Sai dai kuma zuwan Alh. Badamasi yasa ban samu wannan damar ba, Yusuf wanda yake kamar sa'anmu ɗan Inna Habiba, shi ne ya shigo ya sanar min, "in zo yana nan a Falon Baffa."

Jikina ne ya soma rawa komai na kasa ce mishi kuma na kasa tsayar da wanke-wanken

Inna Asabe ta leƙo daga ɗaki tace, "wai ba ke na ji kamar Yusuf yace ana kira ba? Zaman me kike yi to?"

Sum-sum na miƙe ina tsame hannuna tare da nufan cikin ɗakin mu

Ina jin Inna Asaben tana cewa, "shima sai kace maye, ko meye na kiran nata oho? Tunda ba'a kaita ba ai sai ya bari lokaci yayi a kai mishi ita, idan ma latse ta yake yi sai yayi mai sosan."

Inna Amarya ta kwashe da dariya dayake su kaɗai ne a sasan a lokacin, itama tace, "ai kuwa dai, ƙila za'a bar mana abun kunya ne don naga alaman kafin shekaran ma za'a haife mana a gida, Mutum tsoho sai shegen ƙunata, nan da su Binta suke auren yayyinsu ga su a gida amma basu taɓa kiran su ba, shi da yake ɗan anace ne kinga ya samu damar zuwa, Allah dai yasa a rabu lafiya mu kaita gidan batare da ya bunbura mata ciki ba."

Ni da nake ɗaki ina sauraron su, amma tsaban yanda duk na ruɗe ba na ma fahimtar abun da suke cewa, tunanin kawai abun da yau zai yi min nake yi, domin tsoron sa nake ji har ga Allah, Mutumin yayi min girma ga ƙaton ciki a gaba, ko kaɗan ban damu da yanda kayana suke a ɓace ba, duk da dama bana kirki bane doguwar riga ce duk ta koɗe, har da yagi a ƙasan rigan, haka na gyara hulan da ke kaina tare da ɗaukar gyalen Nafisa tunda Ni bani da mai kyau, na yafa na fito, suka bi Ni da kallo suna tuntsirewa da dariya

Inna Asabe tace, "a haka za ki je kina daka tsami? Ko turare ai kya shafa ya fi jin daɗin matsowa kusa da ke. Dalla zo ki amsa ki shafa." Ta furta hakan ganin na ƙi tsayawa ina shirin fita

Shiyasa na dawo na bi umarninta. Ɗauko min turaren Fatimah tayi wanda ta ajiye a ɗakinta ta miƙa min tace, "shafa kaɗan ki ban." Haka na amsa na shafa sannan na bata na fice da sauri

Sai dai koda na je Sasan Baffa; ganin Amaryan shi Inna Baraka sai duk kunya ta kama Ni

Ita kuma tace, "tun ɗazu Mutum ya zo kin shanya shi sai yanzu za ki zo? In CE Yusuf ɗin bai faɗa miki bane?"

"Ya faɗa min." Nayi maganar kaina a ƙasa don na kasa kallonta

Taɓe baki tayi tace, "zo ki ɗauki wannan ki kai mishi."

Ta miƙa min fura a kwanon sha, na ɗauka na shiga Falon batare da jinkiri ba tunda babu damar tsayawa tana wurin. Haka na shiga yau ma babu sallama duk a rikice nake kamar zan zubar da furan, na ajiye mishi a gabanshi kaina a ƙasa na zauna daga can gefe

Shi kuma yayi murmushi yana kallona yace, "Amaryata babu gaisuwa?"

Cikin rawan murya nace mishi, "ina wuni?"

"Lafiya lau, ke ma ya jikin naki?"

Na kasa amsawa illa matse hannuna da nake yi waɗanda nan da nan suka haɗa zufa, ba ma su kaɗai ba hatta Ni kaina ji nake yi zufan ya soma jiƙa min jiki, ga tsoro ga rashin sabo shiyasa nake jina a takure zafi ya ishe Ni

"To zo ki miƙo min furan in sha, kamar ba ki san yanda ake kula da Miji ba ko? Taso ki bani."

A hankali na matso na ɗauki furan tana tambal-tambal kamar zata zube sabida rawan da jikina yake yi, na miƙa masa batare dana kalle sa ba

Sai yasa hannu ya amsa tare da riƙe min hannuna

Hakan ne yasa na ɗago na kalle shi ina zare idanu, har na soma tara ruwan hawaye suna ƙoƙarin saukowa, kamar an jona Ni a shocking sabida yanda jikina yake yi a lokacin

Bai sake Ni ba, shi kuma sai ya ajiye furan ya ɗago Ni tare da ɗaura Ni a saman cinyansa daƙyar sabida yanda nake noƙewa ba na son zuwa. "Kin cika gardama Amaryata, ga shegen tsoro kamar farar kura, ki natsu ba komai zan yi miki ba, kinga Ni Mijinki ne don kin zauna a cinyana ba komai bane, ko ba ki san yanda Mata da Miji suke yi bane idan sun yi aure?" Ya ƙare maganar yana leƙa fuskata har yana goga min duƙunanan gemun sa

Wlh ji nayi kamar zan mutu tsaban yanda na firgice, wani abu ne ya tsirga min a ciki babu inda jikina ba ya rawa, sai kawai na fashe da kuka don na kasa jure wannan yanayin

Nan da nan ya ruɗe shima yana tambayana, "mene ne haka kuma? Meye na kuka? Kinga Yi shiru kinji ko? Yi shiru mana."
Ya dinga rarrashina amma kamar ba na ji, burina kawai in sauka daga jikinsa,
Da ya fahimci hakan sai ya ƙi saki na, ya soma tsorata Ni a kan, "zai sanar da Baffana tunda gudun sa nake yi, idan kuma ban yi shiru ba zai ce a ba shi Ni in tare tun yanzu bazai jira sai wani lokacin ba."

Dole nayi shiru don ya tsorata Ni ba kaɗan ba, gum nayi ina ta faman ajiyan zuciya

Yace, "yauwa ko ke fa Amaryata. Kinga duk abun da nayi miki kar ki soma ki faɗa ma kowa domin Ni mijinki ne, nima bazan sanar da Baffanki kina guduna ba, zan ce mishi kina min biyayya sosai, don haka daga yanzu zan riƙa zuwa ina duba ki duk idan ina gida, kuma zan siyo miki abun daɗi kinji?"

Kaina na gyaɗa mishi kuma ina sake jan ajiyan zuciya. Ina ganin yanda ya ɗauko bak'ar leda a kusa dashi ya buɗe min, ya ciro chocolate a ciki tare da buɗewa ya bani yace, "ga shi wannan naki ne, ki shanye, duk abun cikin nan naki ne nayo miki tsaraba, kuma duk idan zan zo zan riƙa siyo miki."
Tsoro ya hana Ni amsa, tunda na kalla na ɗauke kaina. Sai ya kamo hannuna ya saka min yace, "sha in gani." Da rawan hannu na soma sha gudun kar yace nayi mishi gardama, haka na dinga sha ban tsaya ba saboda daɗin da ya ratsa Ni, take a nan na lumƙume ina siɗe hannu

Yayi dariya yace, "akwai daɗi ko?"
     

Na gyaɗa mishi kai sabida tunda nake Ni dai ban taɓa shan irin wannan abun ba, ba ƙaramin daɗi yayi min ba, shiyasa yana ɓare min wani na amsa da sauri na soma sha, haka yayi ta bani sai da na sha guda huɗu kafin yace, "ya isa haka. Wannan sai ki je dashi ciki ki shanye sauran kar ace ban kawo miki tsaraba ba, kinga har da minti ma." Duk ya nuna min abun ciki

Ni kuma sai kallo nake yi na kasa cewa komai, yayinda nake ta faman lanɗe baki. Ina jin sanda ya kai hannunsa saman ƙirjina yana cewa, "duk kin ɓata kayan ki da madaran." Dayake ruwa-ruwa ne saboda daga gani ya sha rana shiyasa ya narke ya ɓata min kaya,
Shi kuma sai shafa min ƙirji yake yi a zuwan yana goge min kayana, yana ta lugui-guita min wurin tsaban iskanci ne a ransa,
Ni kuma ban fahimci komai ba tunda na san ko ƙirgan dangi ban fara ba, wurin kamar ƙirjin namiji ban ga abun da zai shafa a wurin ba, amma shi ya gani daɗi yake ji har matsawa yake yi tare da cire min gyalen yana cewa, "wannan rigan naki duk ta koɗe, tamkar ba Matar Alhaji ba, duk idan na koma Birni zan siyo miki kaya masu kyau ki riƙa saka wa, kina so ko?"

Na ɗaga mishi kai da sauri raina cikin murna

"Yauwa to bari in bar ki ki tafi, sai idan na sake dawowa kinji? Ɗauki ledan." Ya sauke Ni daga kan cinyansa yana miƙa min ledan, sannan ya shafa kaina yana murmusawa yace, "ai yanzu kin dena tsorona ko?"

Shiru nayi masa ina sunkuyar da kaina

Sai ya sake cewa, "ki ɗauke Ni tamkar baban ki kinji? Duk abun da kike so zan yi miki."

Wannan kalaman nasa shiyasa na ji tamkar bazai cutar da Ni ɗin ba, don dama kallon Baba nake mishi, amma tunda da kansa yace in kalle shi kamar Babana shiyasa naji daɗi, na gyaɗa mishi kai ina jin tsoron sa ya soma raguwa daga raina. Yana sallama na sai na fice da sauri riƙe da ledan na ɓoye shi a cikin gyalena.
[18/06, 12:12 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
     *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 7*
_____Ban haɗu da kowa ba sai da na shiga Sasanmu, ai kuwa su Fatimah suna zaune a tsakar gidan, dawowarsu kenan daga sasan su Luba sun je taya ta kalallaɓa, shi ne suke rigima wajen rabo, domin gaba ɗayansu suka dawo sasan an zo rabo ake rigima, wannan tace, "nata yayi kaɗan." Haka ma wannan, shi ne suka ce, "sam rabon bai yi ba baza su yarda ba." Dayake Nafisa ke raba wa

Ita kuma tace, "idan baza su amsa a haka ba to su bar shi."

Tsiya fa ya fara kaurewa a tsakanin su har suka fara sa'insa da Fa'iza

Inna Amarya na tsaye a kansu tana cewa, "to ku kawo in raba muku tunda rigima zaku yi, ke ma Binta zuba naki ayi sabon rabo." Ta ƙare maganar tana kallon Binta da har ta ɗauki nata ta soma ci

Haka nan ta zuba tana tura baki, sai kuma tace, "wlh in dai aka bani wanda bai kai haka ba bazan yarda ba, tunda Ni da Nafisa mun fi shan wahala, to me suka yi su Fa'izan da zata wani ce nata yayi kaɗan?"

"Nima haka na gani ai." A cewar Nafisan itama tana kumbura baki

"Ƴan wahala, a kan kalallaɓa duk ku bi ku ishi mutane, da kin bar su sun wuce can inda suka fito suyi rabon ba a nan ba, kuma wlh idan suka sake suka yi mana dambe Ahmadi zan kira ya ci ubansu." Inji Inna Asabe da ke zaune a cikin ɗakin ta a bakin ƙofa, ta ɗago labule tana musu faɗan hakan

Ana haka sai gani na shigo cikin sasan. Sai duk suka bi Ni da kallo kamar wacce suke neman wani abu daga jikina, a yanda suka kafe Ni da kallo shiyasa duk na tsargu na kasa ƙarisowa ciki

Inna Amarya tace, "ya tafi kenan?"

Sanin da Ni take yi shiyasa na gyaɗa mata kaina ina ƙoƙarin tahowa

Har zan shiga ɗaki Inna Asabe tayi saurin cewa, "zo nan me ya ba ki kike ɓoyewa?"

"Ba ɓoyewa nake yi ba Inna." Nayi maganar da sauri ina kallonta

"Zo nan mu gani."

Haka na isa wurinta, ta buɗe gyalen; ta amsa ledan tana leƙa wa

Itama sai Inna Amarya ta wuce wurin ta tana cewa, "oh yau kuma da tsaraba ya kawo mata? Mene ne a cikin ledan?"

Taɓe baki Inna Asabe tayi tana cewa, "oho ga dai yi nan kamar minti ne da wasu abubuwan ban gane ko mene ne ba, duba min ki gani." Ta miƙa mata chocolate guda ɗaya tare da sake zaro biscuits daga cikin ledan

Sai duk su Nafisa suka taso a inda suke suka taho wurin. Kowaccen su murna a kan fuskarta suna cewa, "wlh kayan daɗi ne na ƴan binni, wannan cakulate ne da biskit." Nan da nan dukkan su suka fito da kayan suna dudduba wa

"Ai kuwa baza ki ci ke kaɗai ba, mu ma bari mu raba mu dangwali fa'ida." Inna Asabe ta furta ta soma ɓare ɓawon, haka ta rarraba musu har Inna Amarya, aka ajiye wa Inna Lami da Inna Habiba da suka fita gidan; sun je barka a cikin anguwa

Guda ɗaya suka bani chocolate ɗin sai ƙaramin biscuit mara madara. Ni dai tunda na amsa na wuce dashi ɗaki na ɓoye, duk da ina son shan chocolate ɗin amma haka na haƙura sabida tunanin ajiyewa Ihsan ɗin Yaya Haula

Sai ga su Bintan sun shigo ɗakin sun tasa Ni gaba suna tambayana wai, "shi ya bani?"

Nace musu, "eh shi ya bani, yace a birni ya siyo min."

"Wlh kin more Madina, za ki ci dadi a gidan mutumin nan, Allah da Ni ke." Luba ta furta tana dafa min kafaɗa

Haka sukai ta santi suna taya Ni murnan samun Alh. Badamasi a matsayin Miji


Ni kuwa sai kallonsu nake yi nima ina jin dadi, ko ba komai na samu nima wanda zai riƙa bani wani abu a gidan, nima za'a riƙa siyan min duk abun da nake so. Sai murna nake yi a raina Allah-Allah nake yi Yaya Haula ta zo in bata labari. Ai kuwa zuwa gobe da yamma sai ga ta ta leƙo gidan. Tana zuwa na miƙa mata nace, "ta bama Ihsan."

"Waye ya ba ki wannan abun Madina?" Ta tambaye Ni cike da mamaki tana kallo

Ni kuma na sanar mata Alh. Badamasi ne, yanda ta ga ina murna sai itama ta ji daɗi a ranta,
Murmushi tayi tace, "ashe ya sake zuwa duba ki ne?"

Nace mata, "eh Yaya. Kuma yace zai riƙa kawo min duk idan ya je birni, kuma yace ma zai siyo min kayan sakawa na birni." Nayi maganar cikin yarinta da nuna tsantsan murna na a fili; sai washe baki nake yi

Sosai Yaya Haula ta ji daɗi a ranta sabida jin yanda Alh. Badamasi yake kula da ƙanwarta, da alamu ƙanwarta zata ji daɗi a gidan tunda ga shi ya nuna mata tun a gida kafin a kaita. Burinta dama ta samu kulawa kuma in Allah ya yarda Madina tayi dace da Mijin aure. Haka ta ɓare musu Chocolate da biscuit ɗin; ta bama Ihsan rabi sannan itama ta ɓalla, nima ta bani ɓallin tace, "in CI." Sabida ganin ina ta kallonta ina haɗiye yawu

Ai kuwa da sauri na amsa na lunƙuma a baki ina dariya, ƙasan gemuna ya lotsa sosai,
Itama dariyan tayi, dariyan farin ciki dukkan mu muke yi

Sai da aka kusa kiran magriba sannan tace, "zata tafi." Shi ne na raka ta har bakin ƙofan gida sannan ta tafi

Na dawo gida ina ta farin ciki, don wannan kyautar ya faranta min rai, har ji nake yi da ace gobe ma ya sake dawowa; abun ka da wauta irin nawa. A ɗan kwanakin walwalana ya dawo sabida dama duk sabida rashin sakin jiki ne dashi yasa Ni na tsangwami kaina, ga tsoro da fargaba, yanzu kuma duk babu haka na saki jikina na ci gaba da rayuwata tuni na manta da wani aure. Iyakan matsalata yanda nake fama da ƙaiƙayin gaba

Kusan kwana goma da zuwan Alh. Badamasi bai sake zuwa ba, ga shi mu kuma ba ma fita ko nan da can iyakan aikin gida da muke yi, ƙanninmu ne kawai suke tafiya Islamiyya da karatun allo na safe

A cikin ƴan kwanakin nan

Please Login or Register in order to submit comment