Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da girgiza Ni, ita kanta bata san mai take furta wa ba sabida halin ruɗe wa,
Sai ta mike kuma zata fitar da ni ɗakin, ta rungume Ni a cikin jikinta zata fitar da ni

Baban Sasa yace, "Asiya, ki dawo hankalin ki mana, wannan abun da ya faru ƙaddara ne bamu da yanda zamu yi, duk da mun san zafin abun da aka yi mata ne kike faɗin haka amma dole ki yi hakuri ki ɗaura wa kanki dangana, ki ajiye ta ina za ki je da ita kuma kin san ana duba ta ne?"

Kallonsa tayi idanunta jawur fuskarta tayi jaɓe-jaɓe da hawaye, a fusace tace, "asibiti zan kaita mana, tunda na ga baku da alamar ceton ta kun barta a nan sai ta mutu tukunna, Ni kuma bazan barta a nan ba wlh tunda Ni ce uwarta."
Sai ta sake fashe wa da wani sabon kuka tana surutai, "iyee wannan wanne irin zalunci ne? Shikenan kun cuce ta kun gama da ita, wlh Allah ya isa bazan taɓa yafe wa ba..."

Tun kafin ta idasa maganar Baban Sasa ya daka mata tsawa, yace, "ke Asiya ki shiga taitayin ki, duk maganganun da kika yi bamu ce komai ba hakan bazai yiwu ki zauna kina gaya mana magana ba, har da Allah ya isa ki dubi tsaban idanunmu kina gaya mana wannan kalman don ba ki da mutunci? Don haka duk da kina mahaifiyarta babu inda za ki je da ita tunda mu bamu gaza ba, yanzu ma taimako ake bata kuma da ikon Allah yarinya zata warke ta tashi da ƙafafunta, ba ma son maganar banza bamu nemi taimakon ki ba, wannan yarinya dai in har muna da rai baza ki yi iko da ita ba tunda mu ne dolen ta, ki ajiye ta baza ki kaita asibiti ba babu inda za ki matsa da ita, bamu hana ki zuwa ki duba ta ba amma ba ki da wannan hurumin na daukar ta ki kaita wani wuri."

Umma tace, "wlh tallahi bazan ajiye ta ba, ai wannan zalunci ne, don me yarinya tana cikin wani hali amma baza ku kaita asibiti ba? Don kawai kuna rayuwa kamar jakuna baku san inda kanku ke muku ciwo ba sai a tauye wa ƴata hakkinta?"

Ran Baban Sasa ya ƙara ɓaci ainun, bama shi kaɗai ba hatta sauran sabida yanda Umma take kuka tana zagin su, ya sake daka mata tsawa yace, "wlh summa tallahi idan ba ki ajiye ta ba sai na wanka miki mari Asiya, ke ba ki isa ki zo nan kina mana rashin kunya ba, kuma daga yau tunda ba ki da mutunci ba ki san ragowan sa ba, zan nuna miki Madina mun fi ki iko da ita, daga yau nayi miki iyaka da ita har abada, kar ki ƙara tako ƙafanki ki zo inda take, ki ajiye ta kibar mana gida yanzu."

Wasa-wasa fa magana ta zama tsiya, domin furr Umma ta shafa wa idanunta toka tace, "wlh baza ta taɓa ajiye Madina a gidan nan ba, in har sun ga ta fita gidan nan to ƙafarta kafar ƴarta ne, idan kuma suka nemi su hana ta fita da ita hukuma zata kira musu."
Umma fa ta haukace musu sam ba ta jin maganar su, kuka take yi sosai ta ƙanƙame ni a jikinta ta ƙi ajiye ni, wadda ba na gane komai a wannan lokacin,
Ga Haula itama kukan take yi sabida tashin hankalin da ta ga yana faruwa

Baban su Hassana duk yanda ya so ya rarrashi Umma ta ajiye Ni amma furr ta ƙi sauraron sa, shi kansa haƙuri yake bama su Baban Sasa sabida yanda ransu yayi mugun ɓaci a sakamakon abun da Umma take musu,
Ya rantse ya maya Baban Sasa, "Umma bata isa ta tafi da Madina ba, kuma idan bata bar musu gida ba sai ya sa Yara sun yi waje da ita."

Tsiya fa sosai ake yi, maƙota sun taru; gida ya cika.
Baffa ne kaɗai ke nuna sassauci a wurin tunda yana ganin shi ya ja komai, shi ne silan komai, sannan duk abun da Umma take yi yana ganin a kan gaskiyar ta ne, ƴarta ce, tana da ƴancin yin duk abun da take so, shi ke tausan Baban Sasa yana ba shi hakuri yana cewa, "don Allah a bi komai a sannu kar a yanke ɗanyen hukunci, ya san Asiya halin da take ciki ne na ruɗu a game da halin da Madina take ciki; shiyasa ta aikata hakan."

But sam Baban Sasa bai saurare shi ba, abun da har yakai da ya yanka wa Umma mari, sabida yanda ta ƙwaƙume Ni ta ƙi barina sai ta fice da ni a gidan, sun yi sun yi ta sake Ni ta ƙi, faɗi take yi, "basu isa su ƙwace Ni ba ƴarta ce, sun yi kaɗan wlh."
Abun ya sosa wa Baban Sasa rai, kamar shi da girmansa yana faɗa Umma tana faɗa? Yanda take wulaƙanta su tana zagin su a gaban jama'a; shiyasa ya zuciya ya wanka mata mari cikin tsananin ɓacin rai da tafasasshen zuciya.
[15/07, 8:53 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
   *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎

_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A✍️*



          *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._


*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












______________ *EPISODE 15*
_____Har ya ɗaga hannu da ninyar sake kwaɗa mata wani marin,
Sai Baffa yayi saurin tare wa yana ba shi haƙuri,
Cikin zuciya Baban Sasa yace, "ita ɗin banza da zata zauna tana mana rashin kunya mu ƙyale ta? har yaushe Asiya tayi kaurin wuyan da zata zo gabanmu tana gaggaya mana magana? Mu sa'an yin ta ne ko kuwa raini ne zai shiga tsakanin mu take ganin takai matsayin da zata zo gabanmu muna faɗa tana faɗa?"

Kuka Umma ta fashe dashi ta buɗe baki da nufin yin magana,
Amma sai Baba ya dakatar da ita yace, "ta dakata da maganar haka, idan tana jin maganarsa ta sauke yarinyar su wuce su tafi, tunda zuwan su babu wani amfani."

Baban Sasa ya daka ma su Shamsu tsawa yace, "su amshi Madinan su mayar da ita ɗaki."

Sosai Umma take kuka a lokacin, tana ji tana gani aka ƙwace Madina a hannunta, wacce a lokacin bata san ma mai ke faruwa ba, ita kanta ba ta hayyacin ta sabida azaban ciwo, bata san wainar da ake toya wa,
Duk iyalan gidan sun zo wurin sun yi cirko-cirko hankulan su a tashe

Yaya Haula na gefe tana rusan kuka sabida ganin marin da aka yi wa Ummanta, ita kanta kamar zata shiɗe sabida irin kukan da take yi, zata baka tausayi sabida yadda ita kanta ta fita a hayyacin ta tayi firjan-jan, ga shi tana gani Baba ya ja hannun Umma suka bar gidan itama tana kukan sosai, sai dai babu damar bin su tunda a halin da ake ciki ta san tsab Baban Sasa zai sa a zane ta,
Shiyasa tuni ta toshe bakinta tayi cikin gidan tana ci gaba da rusan kukan gunun tausayi

Su kuwa su Umma koda suka fita ta tubure babu inda zata je sai da ƴarta, ƙarshe zama tayi dirshan a wurin tana ta kuka,
Har Yara sun soma tabaibaye su,
Baba yayi rarrashin duniya ta ƙi tashi

Ana haka sai ga Baffa ya fito, shi ya saka su Yusuf da su Muntari suka kaɗa Yaran, ya je har gaban Umman yana bata haƙuri zuciyarsa cike da tausayinta, shi kansa ba ya jin daɗin abun da ke faruwa domin komai ya ɗaura wa kansa laifin ne, zai fi so a ɗauki yarinyar nan a damƙa ta wajen mahaifiyarta ko itama za a yi mata adalci, idan ya so a kaita asibitin da Umman take buƙata, gaskiya an zalunce ta, amma kuma Baban Sasa babu wanda ya isa ya ƙetare maganarsa, idan ya gindaya magana ta zaunu babu canza mishi zance, ita kanta Umma yau don tana cikin ruɗu da tashin hankali ne shiyasa har take musayar yawu da shi,
Sosai Baffa yake bata haƙuri yana rarrashinta a kan, "tayi haƙuri ta tafi, inyaso ko mene ne zai ba Yayan nasu haƙuri, wannan maganar da ya gindaya a tsakanin su kar ta sake zuwa, zai ba shi haƙuri ya sassauta Insha Allahu zata riƙa zuwa babu mai raba ta da ƴarta."

Cikin kuka Umma tace, "ai ko baka bani haƙuri ba wlh bazan taɓa yarda ba sai na ɗauki mataki, sai an bani ƴata, hukuma zata raba mu duk yanda zan yi sai an bi min haƙƙina, ai wannan zalunci ne, idan kun fi ƙarfina baku fi ƙarfin hukuma ba, kun yi wa ƴata auren dole da wanda yayi sa'ar Ubanta; duk don kun fi ƙarfina kuma ku ne kuke da iko a kanta, amma ai Ni Uwa ce, maiyasa baza ku ji koke na ba? Maiyasa kuke son ku zalunce Ni? Ƙarshe kun ga abun da ya faru ƙarshe ga wulaƙancin da yayi mata sannan ya sake ta, shikenan ƙaramar yarinya kamar Madina fa; kun mayar da ita bazawara, bazawaran ƙarfi da ya ji, wlh kun cuce mu kun cuce mu, tsakani na da ku Allah ya isa baza mu taɓa yafe wa ba..."

Baba ya katse mata zancen ta yana cewa, "wai ke Asiya ba a faɗa miki magana ɗaya ki ji ne? Kina ganin wannan babban Mutum ya zo gabanki yana ba ki haƙuri amma kuma ƙara zaƙalƙale wa kike yi, ko kuwa an ce miki tada husuman shi zai kawo maslaha a tsakanin ku? Ai ga shi yanzu kin ɓata komai, idan ba ki tashi ba Ni zan tafi in bar ki tunda ban ga amfanin zuwana ba."
Ya juya ya tafi batare da ya jira jin cewar ta ba; yana mai jin haushin Umman da take wannan haukan

Baffa yana cewa, "a'a baza a yi haka ba, ka dawo ku tafi tare don Allah, mu haƙuri muke baku mun san laifin mu ne an cuce ta, ita uwa ce dole hankalin ta ya tashi."
Sai ya koma kuma wajen Umma yana ta bata haƙuri tare da cewa, "ta tashi ta bi Mijinta."

Bata ce masa komai ba haka ta miƙe ta bi hanya har lokacin tana matse hawaye, zuciyarta ɗaci take mata ji take yi tamkar tayi hauka sabida wannan fin ƙarfin da aka yi mata, waɗannan wanne irin dabbobin mutane ne? Ta tabbata ƙarshe ƴarta mutuwa zata yi a wahale, sun zalunce ta, da farko sun ƙuntata mata sun yi mata al'adan nan nasu na banza da hofi, abun ya zo da matsala tayi kamar baza ta rayu ba, sannan suka zo suka yi mata auren dole, gani take yi kamar ba sa son Madina ba sa tausayinta, ko Haula da suka yi mata aure ai Yaro suka bata, amma ita Madina fa, wanda ya fi ƙarfin ta suka aura mata, ƙarshe ga abun da ya faru,wannan wanne irin zalunce ne? Dukka-dukka nawa Madina take da har zata san wahalhalun rayuwar nan? Ita yarinya ce taya ya zata iya jure wa?

Har suka koma gida Umma ta kasa yin shiru, duk ban bakin da Baba ya ci gaba da bata tunda ya san a halin da take ciki, amma hakan ya gagara ta ƙi tayi shiru har suka koma gida a haka

Su Hassana suna ganin ta a wannan halin suma hankalin su ya sake tashi, nan suka zo suka tabaibaye ta suna tambayarta abun da ke faruwa?

Hussaina tace, "Umma, ko dai Aunty Madinan mu ta rasu ne? Don Allah ki faɗa mana halin da ake ciki?"

Baba da ke kallonsu yace, "bata mutu ba tana nan a raye ƴar uwan taku, amma Umman ku ta so ta taho da ita ne sun hana ta shiyasa hankalin ta ya tashi, ku dena damun ta da surutu kun ga a halin da take ciki."

Maganar da Baban yayi shine yasa dole suka sarara mata, suma suka yi zaune suka yi zugum suna sauraron kukan Umman

Shi kansa Baba zaman yayi ya buga tagumi ko ruwa ya kasa zuba wa a cikin sa,
Yanda ka san an yi mutuwa a gidan haka suka yi shiru sai sautin kukan Umma da ke tashi, babu abun da ke ɗaga mata hankali sai a halin da ta ga ƴarta, idan ta tuna sai kukan ta ya daɗu tana kiran sunan Madina tare da furta, "Allah zai saka miki wlh, insha Allahu Allah sai yayi miki sakayya, bani da abun da zan iya bi miki hakkin ki da sai inda ƙarfina ya ƙare, amma nakai kukana ga Allah; Allah shi zai raya min ke Madina, Allah ya yaye miki duk matsalolin ki, kina ƙaramar yarinya kina ganin uƙuban rayuwa kala-kala, don dai Allah ya haɗa ki da mutanen da dabbobi ma sun fi su, a yau ina dana-sanin haihuwar ku a can, na tabbata ko mahaifinku yana raye dole hakan ne zata faru da ku, nayi dana-sani..."

Baba yace, "Subhanallah... Asiya, ki dena irin waɗannan maganganun kar kuma ki zo ki saɓa wa Allah, Allan da ya halicce su a irin wurin nan shi yake son ganin su a haka, kuma shi ne mai raya wa shi zai rayar da su komin wahala, ba su kaɗai bane fa a ƙauyen kinga wahala ta kashe su ne? Don haka; haka Allah ya so ya tsara musu rayuwarsu a can, addu'ar ki kawai suke buƙata, Allah shi zai bata lafiya kuma ta rayu kamar ƴar uwanta, wahala ba ta kisa wata rana komai zai wuce wlh, don Allah ki cire wannan damuwar a ranki tun kafin wani sanadin ya same ki, kinji ko ki dena wannan kukan, bamu da ƙarfin da zamu amshi Madina tunda can ne tushen ta, ke Uwa ce kawai baza su taɓa ba ki ita ba."

Duban sa tayi tana sharce hawayen fuskarta, tace, "sabida Ni Uwa ce kenan bazan iya amsar ƴata ba? Ni Uwa ce kawai bani da hurumin da zan iya riƙe ƴata? Ai ɗiyata ce ita nima ina da hakki, kawai zalunci ne irin nasu kuma sun rigada sun cuce Ni wlh bazan taɓa yafe musu ba, in Allah ya yarda sai Allah yayi mana hisabi damu dasu, bazan taɓa yafe wa ba."
Sai ta kifa kanta a saman gwiwowin ta tana ci gaba da sharɓan kuka

Yayinda Hassana tuni ta manne mata itama tana kukan sabida kasancewar ta mai saurin kuka, duk hankalin su ya tashi sabida ganin halin da Ummansu take ciki

Ana haka wayan Umman ta soma ƙara,
Sai Hussaina ta tashi ta je ta ɗauko mata tana duba sunan, sai da ta kawo tace, "Umma ga wayanki, tun ɗazu Hajiya Ummee ta kira muka ce mata kin fita, yanzu ma kinga ita ta sake kira."

Umma ta kasa ɗagowa ta amshi wayan har sai da Baba ya sake mata magana; sannan ne ta ɗago ta saka hannunta ta amsa tana danna received call, cikin muryan kuka tayi sallama don ta manta a halin da take a time ɗin

Wanda hakan ne ya ɗaga wa Hajiya Ummee hankali; take cewa, "Asiya lafiya? Mai ke faruwa ne na ji kamar muryanki kina kuka? Mai ya faru?"

Cikin tsananin damuwa da ya bayyana a cikin muryanta take cewa, "babu komai Hajiya."

"Ban gane babu komai ba? Ga muryanki nan ta nuna alamun babu lafiya? Yau tunda na ji shiru nace ko lafiya? sabida na kira wayan ma ɗazu ba a ɗauka ba, shiyasa yanzu na sake kira tunda na san ba kya fashin zuwa, ki faɗa min me ke faruwa ko zan iya taimaka wa; Don Allah kar ki yi shiru ki ɓoye min halin da kuke ciki?"

Hakan ne yasa Umma ta zayyane mata komai tana kuka a wannan lokacin, don baƙin cikin kamar yanzu abun ke faruwa, abun yayi mata ciwo yana cin ta a rai, tana gani za a kashe mata ƴa bata da yanda zata yi

Salati Hajiya Ummee tayi ta kwararowa hankali a tashe, duk da bata san yarinyar ba amma tayi matuƙar tausaya mata, tace, "yanzu dama akwai irin mutanen nan har yanzu a duniya? Wannan wanne irin zalunci ne?"

Shiru Umma tayi tana sauraron ta tana ci gaba da kukan

Sai tace, "ki yi shiru haka nan don Allah kina ɗaga min hankali, Insha Allahu zan san abun yi a kan wannan matsalar naki, don dole ne sai an dauki mataki a kansu tunda dai ina da damar da zan iya taimaka miki, baza mu barta can ba bare su kassara mata rayuwa, ai ke Uwa ce; kina da damar da za ki nemi kula da ita, in har baza su bayar da ita a nema mata magani ba; to dole mu sako hukuma a ciki, Ni zan tsaya miki, in har kina da Ni baza ki yi kuka ba Asiya, zaman amana muke yi da ke don haka ki share hawayen ki, ba na son ki sake shiga wani tashin hankali a kan wannan matsalar, da ikon Allah ta zo ƙarshe sai inda ƙarfina ya ƙare wajen taimakon ki."
A nan ta ci gaba da tausan Umman cikin kwantar mata da hankali har ta samu natsuwa,
Inda Umman take ta mata godiya kamar zata duƙa mata don farin ciki,
Tace, "babu godiya tsakaninmu Asiya, kin cancanci fiye da haka ma, ki jira Ni yanzu ina nan zuwa, bari muyi maganar da Mashkur."
Daga nan suka yi sallama Umma ta cire wayan daga kunnen ta,
Baba kuma da ya kasa kunne yana sauraron su duk da bai jin mai Hajiya take faɗa, shiyasa yake tambayarta abun da suka tattauna?
Ita kuma ta soma zayyano mishi komai


While Hajiya Ummee dayake tana bedroom ɗin ta ne zaune, tana gama wayan sai ta miƙe ta fito babban falon ta; inda ta samu Mashkur zaune a saman two sitter, ya tasa Laptop a gaba yana latsa wa; yana tare da cup juice a saman Centre table din wanda yake kurɓa jefi-jefi,
Kiran sunan sa tayi tana isa inda yake,
Shi kuma sai ya ɗago kansa yana kallonta ya amsa mata,
Zama tayi kan three sitter da ke kusa da wanda yake zaune, inda take facing ɗin sa da cewan, "wani taimako zaka yi min Mashkur; a kan Asiya ce da abun da ke faruwa da ita, dama tunda na ji shiru na san ba lafiya ba, ashe ƴarta ce a ƙauye wani iftila'i ya faru da ita."

Zura mata idanu yayi har ta gama masa bayanin komai, cikin natsuwarsa yake cewa, "Hajiya ko dai wannan yarinyar da ta taɓa zuwa da ita nan?"

"No ba ita ba, ƙanwarta ne."

"Subhanallah..." Ya furta cikin nuna alhini, kana yace, "wai kina nufin ƙaramar yarinya again wacce bata kai wancan ba? Meyasa wasu mutanen basu da hankali ne? And auren dole kuma tsoho; sannan issues na raping on a little girl?"

"Wlh kuwa, ai wasu mutanen kamar dabbobi suke, wasu wurin har yanzu basu waye bane, kuma abun baƙin cikin yanda suke nuna ikon su a kan yarinyar fiye da Mahaifiyarta, duk da an san su ne danginta amma ai Uwa tana da hakkinta, abun da zai baka takaici yanda ta faɗa min rashin wayewar su har takai basu yarda da kai ƴaƴansu asibiti ba, to ka duba ka gani taya ya yarinyar nan zata samu lafiya har ta warke a kan wannan babbar matsalar da ta same ta? wai fa gaba ɗaya wajen fitsarin ta dana kashin ta ya haɗe."

"Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un!" Mashkur ya furta yana mai sanya hannunsa ɗaya a saman face ɗin sa, tsaban takaici ma yayi shiru ya gaza magana yana sauraron Hajiya Ummee da ke ci gaba da maganar nata, can kuma sai ya ɗago kansa yana duban ta da faɗin, "but Hajiya, an kama mutumin ne? Wanda yayi mata wannan aika-aikan? Don bai kamata a barsa ba, duk yanda aka yi ya gwada mata rashin imani da mugunta ne, kuma ya zalunci yarinyar nan dole ne hukuma ta ɗauki mataki a kansa da duk wanda suka yi wa yarinyar auren."

Hajiya Ummee tace, "ban san dai wannan ba tunda bata faɗa min ba, amma yanzu nake son in je gidan muyi maganar, domin dole a yau zamu je ƙauyen a taho da yarinyar nan, idan har basu bada ita ba sai mu haɗa su da hukuma."

"No Hajiya, tare da hukuma zaku je, baza a yi ma wasa da lamarin ba, Insha Allahu zan taimaka ki je gidan yanzu zan fita in taho da ƴan sanda; inyaso sai ku wuce gaba ɗaya a taho da ita, because I have patients today at two o'clock; da sai in bi ku mu tafi tare, but in dai da matsala ku sake kira na don har Human rights sai sun shiga zancen Insha Allahu, da zaran an wuto da ita a kawo ta asibitin mu ina can har dare, zan tanadi duk abun da ya dace da ita."

Ba ƙaramin dad'i Hajiya Ummee ta ji ba, don haka ta tashi tace mishi, "bari ta je ta saka hijab yanzu sai ta wuce, daga can kawai zasu wuce ƙauyen ne."

Shima sai Mashkur ɗin ya tashi yana rufe Laptop ɗin sa, tare da ɗaukar wayansa ya tsaya a wurin yana latsa wa, hannunsa ɗaya cikin aljihu har ya lalubo numban wani abokinsa, can kuma ya kara a kunnensa before ya wuce hanyar ɗakin sa yana making call ɗin.
***

After Mashkur ya taho da ƴan sandan sai suka wuce gidan Umma,
Drivern Hajiya Ummee zai kaisu tare da Umman, sai motan ƴan sandan guda ɗaya da aka basu,
Don haka babu ɓata lokaci suka wuce ƙauyen,
Umma ta nuna musu hanya har suka sauka a ƙofar gidan,
Bayan sun sauko suka shiga gaba ɗaya har cikin gidan tare da POLICE

Kwatsam! Sai su Baban Sasa suka ga ƴan sanda a gidan wanda hakan ya ɗaga musu hankali matuƙa, musamman da suka fahimci tare da Umma suka zo wanda ya tabbatar musu da cewan ƙaran su takai a wurin hukuma,
Ran su Baban Sasa yayi mugun ɓaci ganin wannan wulaƙanci da tozarci da Umma take son musu, tunda ƴan sandan sun ce, "dole sai sun tafi da wasu daga cikin su don su je su amsa tambayoyin su a kan ƙaran su da aka kai, kuma dole su bada yarinyar ko kuma su ga abun da zai faru."
To dayake abun ya zo da sauƙi kasancewar suna jin tsoron hukuma kuma sun san mutuncin su ne zai zube idan har suka ja da maganar basu yi abun da suke so ba,
Shiyasa Baban Sasa yace, "su ɗauki yarinyar su tafi da ita, amma su babu wanda zai je ya bi su zuwa birni, yarinya ce dai ga ta nan sun bada ita su kaita duk inda zasu kaita, kuma idan har su ne dangin Mahaifinta wlh sai Umma ta ga abun da zai biyo baya, kar tayi tunanin ta haɗa su da hukuma ta ci galaba a kansu, zasu nuna mata su suke da iko da Madina."

Umma kuwa bata bi takan zancen su ba ko kadan, don bata damu ba tunda aka bata damar ɗaukar Madina, don haka ta nufi ɗakin da aka ajiye ta suka shiga har da Hajiya Ummee

Mutanen gida dai sun zaman musu abun kallo don nasu ido ne, suna ganin ikon Allan abun da ke faruwa da ɗanyen hukuncin da Umma ta ɗauka, don kawai a kan ƴarta, har da kawo musu wasu mutane gida,
Sai tsegumi ya tashi har da masu yaɗa wa Umman magana a fili,
But ita bata bi takansu ba suka ɗauki Madina zuwa waje ita da wata ƴar sanda guda ɗaya

Kamar tsumma haka aka naɗo Madinan, har yanzu ko riga babu a jikinta; bata san ma a halin da take ciki ba, don izuwa yanzu tunda ta sume kasancewar jinin da ke zuban mata ya ci gaba da zuba, sun rasa ma yanda zasu yi da ita, wanda tuni Malam Bala mai magani ya je samo wasu saiwoyin magunguna zai haɗa mata

Haula tana gidan ta a lokacin tunda fitan ta kenan ta je gida ta ɗauki ƴarta Ihsan, shiyasa bata san mai ke faruwa ba har aka ɗauki Madina aka tafi da ita, sai da ta dawo ne ta tarar da babban tashin hankalin da aka bari a gidan, sai zagin Mahaifiyarta ake yi a gabanta ana ta cece-kuce su Baban Sasa sai fitina suke yi, don sai a lokacin ne suka samu bakin magana tunda hukuman sun tafi, ransu ya ɓaci matuƙa kuma

Please Login or Register in order to submit comment