Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kenan min..."

Shi kansa jikinsa yay sanyi sosai, sai yace, "tana gidan naki ne har yanzu?"

Gyaɗa kanta tayi tana sharce hawayen da gefen gyalen ta

Shi kuma sai ya miƙe tare da cewa, "ta biyo shi."

Fita suka yi tsakar gidan yana kwaɗa wa Shamsu kira, sai kuma ya shiga sasan shi sabida jin babu motsin yara, "Lami... Lami."

"Na'am Malam." Inna Lami ta fito da sauri daga kichen wajen ɗaura musu karin kumallo tana amsa kiran nashi

"Babu Yaran nan ne a gidan?" Yayi maganar yana kallonta

"Eh Malam babu kowa wlh, duk sun tafi aiki, ƙananun kuma sun shiga makarantar safe ba'a tashi ba. Lafiya mene ne?" Ta ƙare maganar tana kallon Haula da ke kuka

Yace, "jikin Madina ne ya ƙi daɗi, Haulatu ta zo ta faɗa min jikin ya tsananta, sai ku je da ita a dawo da ita nan a kira mai magani."

Inna Lami ta amsa mishi tana yin ɗakinta da sauri


While sauran matan nashi duk sun fito kasancewar sun ji mai ke faruwa, sai suka yi Allah ya kyauta kawai

Baban sasa kuma ya koma cikin Falon shi ya zauna bayan ya bar musu sallahun, "idan sun dawo a kira shi."

Inna Lami barin ma Inna Amarya aikin nata tayi; tunda koko zata dama kuma har ruwan ya tausa, sai tabar mata suka tafi da Haula gidan su. Suna zuwa kuwa suka ganni a wannan halin, su Mama da Hadiza suna tsaye cirko-cirko, Rabi'u kuma ya fita da Ihsan saboda kukan da take yi duk ta cika gidan, sai ya fita da ita don ya rarrashe ta

Nan Inna Lami ta soma min sannu cike da tausayi na tana cewa, "ɗago ta Haula mu tafi, Allah ya ba ki lafiya, sannu."

Haka suka kama Ni suka fitar da Ni zuwa gidan mu, ana zuwa aka kaiNi ɗakin Inna Lami sannan aka kira Baban sasa, duk yawanci matan gidan sun zo sun cika sasan ana min sannu da jiki, wasu kuma ƙwaƙwaf ya kawo su saboda hayaniyar da ya cika sasan

A lokacin yaran gidan sun dawo daga makarantar allon da suka fita tun asuba, hakan ne yasa Baban sasa ya aiki ɗaya daga cikin su don kiran mai magani. A ɗakin Inna Lamin ya zauna yana kallona tare da min sannu

Ni kuma duk na fita a hayyacina ban san me suke cewa ba, an lulluɓe Ni sabida sanyin da nake ji,
Yaya Haula na gefena tana faman share hawaye

Babu jimawa Jummai mai magani ta shigo gidan, lokacin duk an watse sai su Inna Asabe da ke tsakar gidan a zaune. Su suka amsa mata sallaman nata suka gaisa sannan ta shigo cikin ɗakin, ta gaishe da Baban sasa, Yaya Haula ma ta gaishe ta. A nan ta fara duba Ni tana gwagwgwale min idanuwa har ta gama abubuwan da zata yi, sannan ta ba da saiwowi ta ce a jiƙa min, ta faɗa duk yanda za'a sha sannan tayi musu sallama ta tafi

Haka aka dinga jiƙa min magungunan ko abinci ba na iya ci, sai an bani a baki, Yaya Haula tana zaune gefe na ita take min komai


Sai da su Baffa suka dawo ne suna ta shigowa gaishe Ni; lokacin ma barcin wahala ya fizge Ni

Ban farka ba sai can wajen ƙarfe biyar da rabi, duk da haka babu abun da ya sauya daga tsanantawar da jikin nawa yayi. Nan ma Yaya Haula ta bani abinci a baki sannan ta bani maganin nawa, duk jikinta yayi sanyi matuƙa musamman da ta ga jikin nawa har yanzu babu sauƙi

Shiyasa Inna Lami ta dafa ruwan wanka tace, "ta zo tayi min wankan."

Haka Yaya Haula ta taimaka min ta cire min kayana tare da ɗaura min zani, ta riƙe Ni muka je bayi ta cuɗa Ni, ina ta kuka saboda sanyin da nake ji, har muka gama aka dawo dani ɗaki na sake rufe jikina gaba ɗaya na kwanta, daƙyar Yaya Haula ta lallaɓa Ni na tashi sai ta saka min kaya, ta ɗaura kaina a jikinta tana ta rarrashina

Shiru nayi ina jinta sabida bazan iya magana ba, idanuna suna a rufe sai hawaye nake zubar wa ina sake shigewa jikinta sabida yanda nake jin sanyi na ƙara shiga cikin ƙashina

Duk Yaya Haula ta rasa me ke mata daɗi, kamar zata yi kuka tsaban yanda take jin tausayina yana ƙara shiganta, hannunta ta sanya tana share min hawaye yayinda itama ƙwallan ne suka cika mata ido, cike da tsantsan damuwa take cewa, "sannu Madina kinji? Don Allah ki dena kukan nan kiyi haƙuri insha Allahu za ki samu lafiya."

Cikin rawan jiki tare da sakin hucin zafi mai haɗe da sarƙewar numfashi, daƙyar nake iya furta, "Yaya zan mutu, mutuwa zan yi ki kira min Ummana don Allah."

"Baza ki mutu ba ƙanwata, ke kaɗai ke gare Ni insha Allahu za ki samu lafiya." Haka Yaya Haula take furtawa cikin hawaye tana riƙe da Ni jikinta sai rawa yake yi

Inna Lami ne ta shigo ɗakin ta ganmu a haka, sai tace, "ha a, ya haka kuma Haula? Kin tasa ta gaba kina hawaye to da wanne zata ji? Idan baza ki rarrashe ta ba ai bai kamata ki zauna kina saka ta kuka ba." Sai ta ja tsaki tana cewa, "maza tashi ki je kichen idan Nafisa ta gama dama mata kunun sai ki ɗauko a bata."

Hakan ne yasa Yaya Haula ta ajiye kaina a saman katifan tana tashi da sauri ta fita, zuwa tayi ta ɗauko ta dawo dashi

Inna Lami tace, "tashi maza ki sha kunun nan da zafi zai taimaka miki a ciki, tashe ta ki bata kar yayi sanyi, saura kuma in dawo inga kin tasa ta gaba kuna ci gaba da kukan kinji ko?" Ta ƙare maganar tana hararan Yaya Haula

Ita kuma ta amsa mata da, "to." Tana ajiye kofin kunun tare da taimaka min na tashi, a haka ba na son sha ta bani tana lallaɓa Ni har na sha kaɗan na ƙara rafke wa. Sai dare Yaya Haula ta koma gida, ƙarshe kawo mata Ihsan aka yi tun rana tunda tana ta kukan yunwa. Kwata-kwata Yaya Haula bata so tafiya ta bar Ni ba, sabida sosai take jin tsoron yanda ta ga jikin nawa yake a rikice, gani take yi kamar in ta jirga za'a aiko mata na mutu ne, shiyasa duk ta damu, tana komawa gida bayan sun kwanta take ce ma Rabi'u, "don Allah ya gyara mata wayanta saboda tana buƙatar sanar da Ummansu halin da nake ciki, gwara ta zo ta duba Ni kar na mutu."

Yanda ta damu ne shiyasa yace, "tayi haƙuri insha Allahu zuwa gobe ko jibi akwai kuɗin da yake saka ran samu, zai je har birni ya gyara mata." Daga ƙarshe yayi ta rarrashinta sabida ganin hankalinta duk ba a kwance ba, daƙyar ya samu tayi barci a ranan sabida yanda duk ta damu ta ƙi kwanciya

Zan iya cewa ko runtsawa ban yi ba a wannan ranan sabida azaban ciwo, Ni kaina nayi tunanin mutuwa zan yi, haka na kwana a cikin mawuyacin hali gaba ɗaya na cire rai da rayuwa, ba abun da nake yi sai kuka da kiran Ummana, kukan ne yasa jikin nawa ya daɗa rikicewa sosai, ga kuma tunanin auren nan da ya tsaya min a rai ba kaɗan ba, ko numfashin kirki ba na iya yi, tamkar bazan rayu ba domin Ni kaina na cire rai da tsammanin zan kai safe, ciwo na ya ɗaga wa kowa hankali domin maimakon a samu sauƙi sai abun gaba yake yi, haka nake fizga da karkarwa sabida yanda zazzaɓin yayi min mugun kamu, ko haɗiye yawu ba na yi sabida yanda wuyana ya riƙe maƙogwaro na zafi, abinci ba na iya ci sai kuka. A cikin kwana biyu kacal na canza kamanni na koma kamar ƴar tsana tsaban yanda na tsamure, kullum nema min magani ake yi amma kamar ciwon daɗa ƙaruwa yake yi

A wannan yanayin na ci gaba da rayuwa cikin bak'ar wahala, a haka har aka shafe sati ina cikin wannan halin, duk wucewar rana ɗaya ƙara tashin hankali nake shiga saboda tunanin aure na, jikina har yayi sauki amma tunda naga an shiga satin da ya kasance za'a yi mana aure sai kuma na ƙara rikicewa

Wasu daga cikin matan gidan cewa suke yi, "duk saboda auren nan ne nake yin ciwo, yanzu haka ba na so ne, don sun ga alamu a tattare da Ni so nake yi in bijirewa auren."

Haka fa aka yi ta yaɗa maganganu har yakai kunnen su Baban sasa, amma babu wanda ya damu da maganar, sai ma jan musu kunne da Baban sasa yayi yace, "kar ya ƙara jin wannan zancen, idan ba haka ba zai saɓa musu, don aure babu fashi sai an yi shi, ba'a haifi yarinyar da zata bijire musu ba".
         
[16/06, 6:32 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._










______________ *EPISODE 5*
_____Kamar yanda aka sanya rana ba'a canza ba, a ranan Asabar aka ɗaura auren mu, duk da babu taron biki amma hakan bai hana zuwan yayyinmu gidan ba, an cika gidan kamar ana biki

Ni kuwa ina daki na ƙule jikin ya ƙi daɗi har yanzu, duk wanda ya zo sai ya shigo ya gaishe Ni duk da hakan bai hana su gulmace-gulmace ba. Ni dai ina kwance ina ta kukan fili dana zuci, sai dai babu wanda ya fuskanci hakan domin ana shigowa nake rufe fuskana, na sha kuka ranan duk da zafin ciwon da ke jikina ban saurara wa kaina ba

Yaya Haula ce kaɗai ta san halin da nake ciki, itama da ta gaji da rarrashina faɗa tayi ta min tana cewa, "sai kace a kaina farau duk na bi na tsangwami kaina? Na fi son ciwo ya kashe Ni ne bazan saurara wa kaina ba? idan har ban dena kukan ba to bazan sake ganin ta a gidan ba tunda ban san ciwon kaina ba."

Hakan ne yasa na shanye kukan nawa sai shashsheƙa da nake yi ina faman ajiyan zuciya. Ina ji ina gani ƴan uwa sai hira suke yi a waje amma Ni ina ɗaki ko tashi ba na iya yi, wani lokacin ne ma Nafisa ke zuwa ta taya Ni zama idan babu Yaya Haula, amma Ni kwata-kwata hankalina ba ya jiki na, jefi-jefi nake sharan hawaye zuciyata tana min zafi tare da ƙunci, tunanin kawai yadda rayuwata zata kasance a nan gaba nake yi

Da dare kowa ya watse ya tafi gida. A lokacin ne kuma su Baffa suka shigo shi da Alh. Badamasi wai zai duba jikina, har ɗakin mu aka kawo shi tunda ina ɗakin mu ne, su Fa'iza suka fita suka bar mu bayan sun gaishe shi

Baffa yace, "tashi zaune Madina zaku gaisa da Mijin naki."

Jikina ne ya soma yin rawa gaba ɗaya na kasa ɗago kai in kalle su tun shigowar su, a hankali na tashi na zauna ina takurewa a wuri ɗaya. Ina jin Baffa yana cewa, "to Alhaji bari in fita, idan ka fito ina ƙofar gida."

Murmushi Alh. Badamasi yayi yana amsa mishi. Bai tashi daga inda yake tsaye ba har lokacin da Baffa ya fita, sannan ya tako a hankali ya shigo ɗakin sosai, duk katifu ne a ɗakin tunda muna da yawa masu kwana a ciki, shiyasa bai zauna ba ya tsaya daga inda yake yana faman kallo na

Sai ga Binta ta shigo da kofin ruwa ta kawo mishi, tayi mishi sannu da zuwa sannan ta fita

Ni kuwa duk gaba ɗaya a rikice nake har yanzu na kasa ɗago kaina, har wani sabon zazzaɓin nake jin yana rufe Ni tsaban tsoron da ya cika Ni. Suna na ya kira, hakan ne yasa na ƙara takura jikina ina kerma

Ya fahimci kamar a tsorace nake shiyasa yayi murmushi yana ƙara gyara malun-malun ɗin jikinsa, tare da gyaran murya a hankali yace, "ya jikin naki Madina?"

Kasa magana nayi illa rufe idanuna da nayi ruf ina ƙara cusa kaina a tsakanin cinyoyina, yayinda gabana yake ƙara bugawa da ƙarfi ga tsananin tsoron da yake ƙara mamaye Ni har tsirga min ciki yake yi

Sake magana yayi ganin nayi mishi shiru, cikin lallami da tausasa murya yake cewa, "Amaryata baza ki ɗago kai ki kalle Ni ba ko? Ko nayi miki laifi ne?" Nan ma shiru nayi mishi kuma na kasa ɗago kan, hakan ne yasa yayi murmushi yana shafa farin gemun sa tare da jan numfashi yana sake cewa, "tom zan tafi, Allah ya ƙara sauƙi kinji ko? Gobe ma zan sake dawowa tunda kin ƙi magana."

Har ya fice ban tanka mishi ba, yana fita na sauke ajiyan zuciya mai karfin gaske ina kama ƙirjina, sosai nake sauke numfashi sabida yanda na ɗauke shi a lokacin da yake cikin ɗakin, ko ƙwaƙƙwaran motsi na gaza yi duk sabida tsoro da fargaban da ya cika Ni, kwanciya nayi da sauri na rufe idanuna ina ta jan numfashi ina ƙara ƙanƙame jikina, ina jin motsi na buɗe idona a firgice, a tunani na ko shi ne ya dawo ashe su Nafisa ne suka shigo, hakan ne yasa na sauke ɓoyayyiyar ajiyan zuciya ina ƙumshe bakina sabida kukan da ya taho min

Su kuwa wuri na suka iso suka zauna. Binta tace, "lallai Madina kin ciri tuta da kika samu Alh. Badamasi a matsayin mijinki, ga shi da kuɗi sosai, kuma da alamu za ki ji daɗi don naga yana yinki fa." Ta ƙare maganar tana dariya

"Wa ya ga Tsoho da soyayya, Allah ya kashe ya ba ki a sama." Inji Fa'izan itama tana dariya, sai suka kashe da Binta suna ci gaba da zolayana

Duk maganar nan ban tanka musu ba har suka gaji suka yi shiru

Nafisa ta ɗago Ni tana cewa, "wai don Allah Madina baza ki dena wannan damuwar da kike yi ba? Mene ne kuma ya rage bayan an ɗaura miki aure dashi? Haka nan za ki yi hakuri tunda shi ne Allah ya ƙaddara Mijin ki, ki saki jikinki ki riƙa walwala kamar da sam ba na jin daɗin ganin ki a haka, gaba ɗaya kin sakwarkwance sabida maganar auren nan bayan kin san baza a taɓa fasawa ba, mu nan gani muke yi kin fi mu Sa'a wlh tunda kin samu wanda yake sonki, shi da kanshi fa yace yana sonki ba tallanki aka yi ba, Allah ya bamu haƙuri mu da bamu samu wannan galihun ba."

Hannuna na sanya na rufe bakina ina duƙar da kaina saboda hawayen da suka taho min, sam baza su gane halin da nake ciki ba, Ni kaɗai na san azaban da nake ji sabida kwata-kwata ba na ƙaunar auren, tsoro ne ke ɗawainiya dani, ga kewar Ummana da nake jin tamkar in buɗe ido in ganni a gabanta, na kasa yin musu magana tunda ba daɗin jikina nake ji ba, zaman ma da nayi tamkar in mutu haka nake ji har numfarfashi nake sauke wa, haka na zame na kwanta ina juya musu baya

Shiyasa suka tashi suka fice tunda na ƙi kula su, suka share Ni suka ci gaba da harkokin gaban su. Sai da suka gama hira sannan suka dawo lokacin ma har nayi barci, tunda Inna Lami ta aiko Autan ta A'isha ta kawo min abinci, haka na tsakura na ci sannan na kwanta, cikin tunani barci ya sure Ni

Washe gari jikina da ɗan sauƙi don har fita nayi da kaina nayi wanka, lokacin da na dawo ne naga Yaya Haula ta zo gidan

Ina shiga ɗakin ta bi Ni da kallo, kana ta matso kusa dani tana cewa, "ya jikin ƙanwata?"

Kallonta nima nayi da kumburarrun idanuna, sai kawai na ji ƙwalla sun soma taruwan min a idanu

A hankali ta riƙe hannuna cike da tausayi ta zaunar dani, kana ta sauko Ihsan ta ajiye ta tana kallona da cewa, "ki dena kukan nan don Allah Madina, wlh kina ɗaga min hankali, ki bar komai ya wuce ki cire tunanin auren nan a ranki tunda komai ya wuce, ki dena tsoro babu abun da zai faru, kowa da haka ya fara fa."

Hannu nasa na share hawayena wasu suna zubo wa, a hankali cikin raunina nace, "Yaya.. Ummana, Ummana bata zo ba ko?"

Itama hannunta ta sanya tana share min hawayen tana faɗin, "na kira ta na sanar mata duk halin da kike ciki, kuma na faɗa mata an ɗaura miki aure, amma tace baza ta iya zuwa ta ganki a wannan halin ba, kinga idan ba ki kwantar da hankalin ki kin natsu ba Umma baza ta taɓa zuwa ba, ba ta son tashin hankalin ki, idan ta zo ta ganki a haka ranta bazai yi daɗi ba zata shiga damuwa, don haka ki mayar da komai ba komai ba Madina ki dena cutar da kanki, ke yarinya ce kar wani ciwon ya kama ki, ina jin tsoro matuƙa, idan hakan ta faru bazan yafe wa kaina ba, kin fi so nima na shiga wani hali ko?"

Girgiza kaina nayi ina shashsheƙa, sai kuma na buɗe baki zan yi magana amma na kasa sabida kuka, da sauri na rungume ta ina fashe wa da wani sabon kukan

Itama hawayen take yi tare da rarrashina cikin ƙarfin hali, ta zama kamar babba duk sabida ni, ita ce uwata kuma ubana a yanzu, bani da wanda nake gani naji daɗi sama da ita. A haka tayi ta rarrashina har nayi shiru, itama ta share nata hawayen tare da cewa, "kinga Ihsan ma kuka take yi na dungurar da ita a nan". Sai ta ɗauke ta ta soma bata nono tana cewa, "tashi ki sanya kayan ki."

Babu musu na tashi ba tare da na amsa mata ba, a hankali nake yin komai sabida rashin ƙarfin jiki, domin har yanzu ina jin ciwo a jikina; sai dai sauƙin da na samu kaina da ya dena ciwo, shiyasa nake iya yin wasu abubuwan yanzu, ina gama wa na zo na zauna a gefen ta na manne mata; tare da ɗaura kaina a kafaɗan ta

Sai ta ɗaura hannunta a kaina batare da tace dani komai ba, sannan tana ci gaba da ba wa Ihsan nonon

Sai da rana tayi kafin ta tafi gida ta bar Ni, kamar in bi ta nake ji don har na faɗa mata, "zan bi ta."

Amma sai Inna Lami tace, "babu inda zan je in koma ɗaki, Ni da bani da lafiya babu inda zan fita, sannan ma Baffa yace Alh. Badamasi yana nan zuwa gaishe Ni."

Hakan ne yasa na koma ɗaki ina zubar da hawaye. Nafisa ce ta zo ta zauna dani tana rarrashi na, don ita ta fi ƙaunata kuma mun fi shaƙuwa da ita sosai sabida kasancewar Inna Lami mahaifiyarta ce kuma ita ce mariƙiyata. Ita ta ɗauke min hankali har na manta da fargaban zuwan Alh. Badamasi, sai da ya zo ne sannan A'isha ƙanwar Nafisan ta shigo tana faɗa min, "inji Innarmu tace ki shirya ki je falon Baffa ana jiran ki." Hakan ne yasa jikina ya soma rawa duk na gama ruɗewa

"Wai tsoron me kike ji ne Madina?" Nafisa ta tambaye Ni tana riƙe min hannu

Cikin ƙwalƙwal da idanu nace, "yayi min girma Nafisa, ina zan kai mutumin nan a matsayin Mijina? Ganin sa nake yi kamar Babana."

Sai ta tuntsire da dariya tana cewa, "Baban ki kuma?"

Kamar sokuwa na ɗaga mata kai ina matse hawaye

Sai dai bata kai ga magana ba muka ji kiran da Inna Lami take min

Dole na tashi da sauri ina rawan jiki zan fita

Sai Nafisa ta tsayar da Ni tana ɗauko min humranta da ke cikin jaka a ɗan kwalba, ta shafa min a kayana sannan ta bani sabon gyalenta tace, "in yafa."

Jiki a sanyaye na yafa ina jan ajiyar zuciya, har yanzu idanuna hawaye suke zubar wa sun kaɗa sun yi jajir. Daƙyar ta lallaɓa Ni ta riƙe min hannu ina bin ta kamar sokuwa muka wuce har falon Baffa, a bakin ƙofa ta bar Ni ta tafi

Ni kuwa sai na tsaya a wurin ina ƙanƙame hannuna jikina a mace, tsananin tsoro da fargaba yana ƙara shiga na kamar in zura a guje. Daƙyar na daure na shiga sabida kar a zo a ganni a wajen ban san me zan ce ba, a hankali na shiga ko sallama na kasa yi, kaina a kasa tunda na shiga na tsaya a bakin ƙofan na kasa taka ƙafafuwana tsaban kakkarwan da jikina yake yi

Alh. Badamasi yana zaune a kan kujeran falon, ya sha fararen kaya na yadi wanda kana ganin kayan ka san akwai tsada, sai dai yanayin zubin nasa babu tsari ko kaɗan, kana kallonsa kaga bugun ɗan ƙauye sai washe baki yake yi; wanda haƙoran nasa duk sun dafe da cin goro, ga shi ya kwafa hula a saman goshin sa ƙeyansa kuma a buɗe ya sha talliyan mola. Ganin na tsaya ban ƙariso ba sai yace, "ƙariso mana Amaryata, me kike jira a wurin?"

Daƙyar na iya ɗaga ƙafana na iso wurin da yake, can nesa da shi na durƙushe a ƙasa ina sunkuyar da kaina, har yanzu rawan jiki nake yi shiyasa na kasa cewa komai don ban san me zan ce ɗin ba. Amma sai jinsa nayi yana cewa, "taso ki dawo nan kusa dani." Lokaci ɗaya na ɗago kaina a karon farko na kalle shi a tsorace, idanuna har sun yi ƙwalƙwal ganin inda yake nuna min, da sauri na duƙar da kaina ina sake ƙanƙame jikina

"Taso nace ki dawo nan kusa dani, Ni mijinki ne ba na so kina min gardama, ko ba ki san muhimmancin Miji bane? Idan ba kya son in faɗa ma Baffan ki taso ki dawo kusa da Ni."

Jiki na rawa na rarrafo kusa dashi jin abun da yace, ko ɗago kai ba na iya yi. Ina jin sanda yake dariya a hankali yana ce min, "Amaryata kenan!" Ni dai ban kula sa ba ina ta sussun da kai

Hannu yasa ya dafa min kafaɗa a firgice na ɗago, sai yayi dariya yace, "meyasa kike tsorata haka sai ka ce na zamar miki dodo? Duk da haka tsoron nan yana miki kyau matuƙa." Sai ya sa hannunsa ya kama ƙoƙarin ɗago Ni yana cewa, "dawo nan ki zauna a kan kujeran."

"A'a... A'a don Allah..." Na furta cikin rawan murya a rikice ina shirin yin kuka

"Mene ne haka wai? Ni fa Mijinki ne ki dena tsorata haka." Ya ɗago Ni batare da damuwa da yanda nake jan jiki ina kafewa ba, ya ɗaura ni a kan jikin shi

Kukan tsoro na saka mishi ina shirin tashi da sauri. Amma ya riƙe Ni sosai yana cewa, "ki natsu na ce." Yanda yayi maganar ne dole na natsu wuri ɗaya amma na kasa dena kukan da nake yi. Hannu ya ɗaura a saman fuskana yana shafa min; cikin murmusawa yace, "ba na son gardama kinji ko? Duk abun da nace kiyi ba na son kina min musu, Ni mijinki ne daga yanzu, kuma na biya sadaki har nera dubu ashirin, ki dena tsoro na bazan cutar da ke ba, yanzu ki share hawayen naki." Ya ƙare maganar yana share min

Amma wasu hawayen zubo min suke yi, sai shashsheƙa nake yi ina zazzare ido, don tsoro kamar in ruga aguje nake ji, amma ya riƙe Ni gam babu yanda zan yi in tashi

"shiyasa nake ƙara sonki sabida kyawun nan naki, ki dena tsorata dani Madina Ni mai ƙaunar ki ne bazan cutar da ke ba, za ki ji daɗi a gidana domin zan tarairaye ki sosai, babu abun da zai same ki kinji ko?"

Shiru nayi masa na kasa ɗago kaina bare na kalle shi; don jina nake yi kamar a ƙaya, sam ba na fahimtar abun da yake faɗa min; ga shi ƙaiƙayi ya dame Ni daga ƙasana na rasa yanda zan yi in sosa, ganin dai azaban ya ishe Ni haka na ɗaura hannuna da sauri ina sosa wurin

Hakan ne yasa ya tsaya yana kallona yana wani lashe baki kamar maye, sai ya ɗaura hannunsa a kan nawa yana cewa, "mene ne? Zafi yake miki wurin?"

Kaina na gyaɗa mishi ina shirin kuka tare da ƙoƙarin ƙwace hannuna zan ci gaba

Amma

Please Login or Register in order to submit comment