Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kin taɓa ganin dangina sun zo maula gidan nan ko sun tako ƙafansu haka kawai babu dalili?"

Yatsina fuska tayi tace, "ban taɓa gani ba, amma ga shi nan sun turo min ɗaya ta zo tana cin arziki tunda su basu da arzikin riƙe ta, suna ganin kamar dukiyar Ubana dukiyar su ne..."

Tsawa ya daka mata yana cewa, "da Ni kike yi kenan ba da ita ba? Yau Ni kike yi wa gori Sharhabila? Ni Yunus kike gaya wa wannan maganar don kawai Mahaifinki ya taimaka min a rayuwa? But duk da taimakon da yayi min yanzu shi yake ciyar da Ni Ko Ni nake ciyar da gidana? Ki faɗa min?"

Tsaki ta ja tana sakin bulalan da ya riƙe, tare da juya wa zata fita tana cewa, "oho dai, koma dai mene ne shine silan arzikin ka, duk wani abun da zaka zama shi ya taimaka maka, don haka baka da bakin da zaka iya ɗaga min murya don nayi magana a kan waɗancan banzayen mutanen."
Tana faɗan haka ta saka kai ta ficewarta

Yayinda ran Yaya Yunus sosai ya sake ɓaci da jin kalamanta, lallai kuwa zai nuna mata kuskuren ta tunda har zata iya gaigaya masa magana irin haka, yau shi Sharhabila take yi wa gori don yana ƙyale ta? Hmm
Numfashi ya ja yana janye Sadam da ya ƙanƙame sa yana kuka da kiran sunansa a kan, "ya taimaka wa Aunty Madina zata mutu, jini na zuba a jikinta."
Sai lokacin shima ya kula da jinin da yake zuba ta ƙafafuna, sai da gabansa ya faɗi sabida ganin jinin, da sauri ya duƙa a gabana yana mai kware skirt  jikina tare da duba wurin, sai kuma ya sanya hannu ya ɗage rigana, sai da jikinsa yayi sanyi sabida ganin yanda Sharhabila tayi min ruɗu-ruɗu da jiki, abun ka da mai farar fata tuni zanen bulalan ya fito yayi jazur ya tara jini,
Janye Sadam ya kuma yi a gabansa sabida ƙanƙameshin da ya sake yi yana kukan, ya rasa ma abun yi don ganin halin da nake ciki, yana ganin kamar idan ya bar Ni a haka zan iya mutuwan musu a gida, kuma ƙarshe shi Iyayensa zasu tuhuma, a karon farko ya soma jin tausayina yana ganin abun da yayi bai dace ba, idan da ace yana hana Sharhabila dukana baza tayi min irin wannan dukan mutuwan ba,
Haka nan ya sanya hannu ya ɗago Ni kamar wata ƙaramar yarinya, don ji yayi tamkar ya ɗauki Mubashir sabida rashin nauyi da ƙanƙanta,
Da sauri ya fitar da Ni daga ɗakin ya nufi hanyar waje

Sharhabila na zaune a falon ta ganshi ya ɗauko Ni a hannunsa yana shirin fice wa da Ni, sai ta miƙe da sauri ta nufe sa cike da zallan kishi da baƙin cikin ganin ya dauko Ni rungume a jikinsa.
[04/08, 1:27 PM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 25*
_____"Wai ina zaka je da ita ne kake shirin fita da ita har da iya ɗaukan ta?"
Sharhabila ta furta hakan har tana cin tuntuɓe wurin zuwa wajen sa

Shi kuma sai ya narka mata wani shegen kallo tamkar idanunsa zasu faɗo ƙasa,
Ko ƙala bai ce mata ba ya wuce ta zuwa waje yana kiran sunan Mubashir, yace, "ya ɗauko masa key din mota."

Ita kuma kallon da yayi mata ne yasa ta kasa cewa komai, sabida bata taɓa ganin irin wannan kallon a wurin sa ba; wanda ke nuni da gargaɗi ne a gare ta, ta san halin Mijinta bai iya saurin fushi ba, amma idan yayi ba ya yi mata da kyau, tunda ta ga yanayin fuskarsa ta san ransa a ɓace yake shiyasa ta ja jikinta bata sake furta komai ba,
Sai ta koma kan kujera fuuuu kamar kububuwa tana cika tana batse wa, ranta itama a ɓace ƙafa ɗaya a sama tana karkaɗa su, lallai yau watan cin uwar yarinyar nan ta kama, domin dole ne tabar mata gidan su, zamanta ya ƙare daga yau, su je duk inda zasu je su dawo zasu zo su tarar da ita

Yayinda Yunus tuni ya saka Ni a cikin mota a baya, ya rufe ya shiga Motan, haka yabar wurin batare da ya bi takan Yaran da suke kukan zasu bi shi ba, kai tsaye wurin gate yayi yana danna horn, mai gadi yana buɗe masa ya fice ya nufi asibitin da suke zuwa, tunda private hospital ne babu nisa sosai, kai tsaye can ya nufa dayake akwai likitan da suka saba a can ɗin, koda ya isa shi da kansa ya ɗauke Ni ya wuce dani Office ɗin sa batare da ya bi takan mutanen da ke faman kallonsa ba,
Ai kuwa ya ci Sa'a Doctorn yana ciki, don haka tun kafin ma yayi masa bayanin abin da ya zo yi, yana ganin sa ya ɗauko Ni a hannu ya miƙe da hanzari ya amshe Ni, sai ya ɗaura Ni a kan gadon office ɗin yana mai kokarin duba Ni, a lokaci ɗaya kuma yake tambayar Yaya Yunus abun da ke damuna?
Babu ɓata lokaci ya sanar mishi da komai tunda babu ɓoye - ɓoye a tsakanin su, bazai iya ɓoye mishi Matarsa bane ta dake Ni ba, kasancewar Abokai ne

Shi kansa Likitan ya matuƙar tausaya min musamman yanda ya ga jikina ya farfashe, amma ganin jinin da ke fita a ƙasana sai ya mayar da hankali wajen duba wurin, don abun ya ba shi mamaki ganin jinin da nake zubar wa

Duk a gaban Yaya Yunus ake yin komai, don ya kasa ya tsare yana kallon abun da ake min

Bayan Likitan ya gano kamar period ɗina ne shiyasa ya koma yin min wata allura wacce zata tsayar da jinin, tare da kawo min sauƙi batare da na sha wahala ba, sai da ya gama kuma ya duba inda duk shatin bulalan yake yayi treatment inda ya fashe, sannan ya mayar da hankali kan Yaya Yunus yana faɗa masa dalilin zubar da jinin, yace, "maybe ta ji wahala ne thats the reason da take zubar da jini, amma ba damuwa bane period ɗin ta ne ya zo."

Sai lokacin Yaya Yunus ya sauke wani Gwauron numfashi yana godiya a zuciyarsa, but a ransa yana mamakin ya aka yi har na fara Al'ada ƴar ƙanƙanuwa da Ni haka? Don shi kallon da yake min ban fi ten years ba, koda na girmi Mubashir da kaɗan ne, bai taɓa kawo wa a yanzu haka nayi 13years ba, amma sai daga baya sai ya taɓe bakin sa tuna saurin auren da ake mana a ƙauye, a ransa yace, "meye ma baza a gani ba, tunda suna haihuwa koda an kaisu gidan Mijin."
Zama yayi bayan da Doctor yace masa, "su koma su zauna, yabar Ni kamar two or three hours, ina tashi jikin zai yi sauki sosai, inyaso sai mu tafi."
Kallon Doctorn yayi tare da cewa, "amma gaskiya a gyara mata jikinta don bazan iya koma wa da ita gida a haka ba, inyaso ka haɗa ta da wata Nurse ta ƙara mata bayanin wannan jinin, don I'm sure bata san komai a kai ba."

Dariya ne ya so suɓuce wa Doctorn, but sai ya kanne yana mai zaro idanunsa alamun mamaki yana cewa, "Y. Abubakar wai kana nufin yarinyar bata taɓa yi bane sai yanzu, i thought shekarunta zai kai like a 14 or 15years, duk da kamar tana da ƙaramin jiki ne?"

Jinjina kansa yayi yace, "lallai ka kai da nisa, wannan bata wuce goma ba wlh, yarinya ce."

Dariya yayi a yanzu yana cewa, "ok, but ƙanwarka ce kenan? Don na ga kamar ta ɓaci? Alamu daga rugar ku ta fito?"

Kansa ya gyaɗa masa don ba ya jin daɗin zancen,
But sai Doctorn ya ci gaba da masa zancen nata har yana cewa, "ko dai zai ba shi ita ne? Ya ganta fine and innocent girl? Yarinyar kyakkyawa da ita har ta fi shi kyau."
Wani irin kallo ya watsa mishi yana cewa, "kaifa idonka idon Mata ne wlh, ban san zancen nan mu barta kawai."

"A'a wlh, ba maganar wasa bane, da gaske nake Allah, in har zaka bani sai in ƙara ta biyu don na ganta kyakkyawa, dama ina son Mace mai sajen nan akwai su da kyau ne."
Ya ƙare maganar yana sake kai kallonsa gare Ni yana kallon yanda nake ta numfashi mai ɗan sauti alamun barcin yayi nisa

Yayinda Yunus ya ja tsaki yana cewa, "to an riga ka, ka san ƙauyenmu kamar wannan tana ɗakin Miji, to yanzu haka ma da Mijinta."

"Haba don Allah? Kamar wannan ɗin?"

Yaya Yunus dai banza dashi yayi yana mai jan wayansa ya soma latsa wa tare da bijiro masa da wani zancen,
Kamar wasa sai ga shi ya zauna jiran har in farka batare da gundura ba, don shi kansa yayi mamakin zaman da yayi da kuma kulawan da ya bani, don ba ƙaramin tausayi na ba shi ba,
A haka har lokacin sallan la'asar yayi suka fita tare da Doctorn suka je suka gabatar, sannan suka dawo a tare kuma har time ɗin ban farka ba,
Sake zama suka yi suka buɗe shafin hira

Sai kusan shida saura sannan na farka,
Dalilin da yasa Doctorn ya tashi kenan ya nufi inda nake; ganin yanda na farka a jigace a kuma tsorace kamar firgicin dukan da Sharhabila tayi min bai sake Ni ba,
Saurin riko Ni yayi yana cewa, "sannu baby, kwantar da hankalinki nan asibiti kike ba a gida ba, babu wacce zata sake dukan ki a nan, natsu ko?"

A nan take kuwa nayi shiru sabida ganin Yaya Yunus a gabana yana kallona, sai na bi Likitan da idanu ina mai sauke numfashin tsoro, daga kallon yanayi na duk na matuƙar tsorata musamman ganin wannan Likitan mai fararen kaya jibgege dashi a gabana, amma ganin har da Yaya Yunus shiyasa na kasa motsi bare in nuna irin tsoratan da nake ciki,
Amma su kansu koda daga kallon yanayina sun san a halin da nake ciki,
Likitan ne ya soma tambayana yanda nake jin jikin nawa?
Da sauri kuwa na amsa mishi da, "babu abin da ke min ciwo." Don a yanda nake jina kamar in tashi in zura a guje tsaban tsoro, Allah yayi Ni mai shegen tsoro da rashin ƙaunar mutane, bare tun abun da ya faru da Ni a baya; ba kowanne namiji bane nake yarda dashi, in har zan ga ƙaton namiji a gabana sai gabana ya faɗi jikina ya fara kerma sabida tsoron sa, har yanzu ruɗanin da na shiga yana tare da Ni bai sake Ni ba, tamkar abun ya taɓa min ƙwaƙwalwata ne; kwata-kwata sai in rasa natsuwata bazan taɓa samun sukuni ba har sai idan na kaɗaice ko kuma akwai Ummana da Yaya Haula

Yaya Yunus ne yace mishi, "don Allah Doctor kira wacce zata gyara ta sauri nake yi, ka ga dare ya soma yi."

"Ok to ba damuwa, tunda tace jikin da sauƙi ai ba wani damuwar kuma. Amma fa akwai magana a bakina friend."
Ya ƙare maganar yana mai nuna masa inda nake da ido alamun a kaina ne

Sai Yaya Yunus yayi kicin-kicin da fuska yana cewa, "dan Allah kar ka ja min raini a nan, ka san ba na son haka fa."


Dariya ya kwashe dashi yana mai sauya harshe saboda a tunanin sa ya san bazan ji kalman turancin ba, sai yace, "don Allah ba maganar wasa ba, wlh yarinyar tana da kyau, musamman yanzu da na ga ta tashi a barcin nan; baka ga yanda kyawunta ya ƙara bayyana ba, kuma tsoron nan da ya nuna a fuskarta ba ƙaramin kyau yayi mata ba, idan har zaka bani wlh na yarda zan aure ta don irin waɗannan yaran su ake kira da tsuntsu daga sama gasashshe; gam-da-Katar."

Shi kansa Yaya Yunus a yanda Doctorn yayi maganar, sai da ya mayar da ido a kaina yana bi na da kallo ya ga ta inda zahirin maganar sa yake,
Wanda hakan ne ya ƙara tsoratar dani gaba ɗaya idanuna suka bayyana a waje ina bin su da ido kamar za a ce ƙyas na zura a guje, shi kansa yanda nayi da fuska ba ƙaramin dariya abun ya so ba shi ba, yayinda sosai ya ga kyawun nawa da Doctorn yake son nuna masa, musamman yadda na dame fuskar kamar zan yi kuka, wanda hakan ne yasa ƙasan gemuna ya ɗan lotsa kaɗan ƙwayan idanuna suna yawo a kansu kamar wadda ake kaɗa su; sai wani karkaɗa su nake yi a kansu in kalli wannan in kalli wancan sai juya wa suke yi, hakan ba ƙaramin kyawu ya ƙara min ba,
Shi kansa mamakin yanda ya ga ainihin kamanmu da shi yake yi, zuciyarsa har buga wa take yi wanda lokaci guda ya ji wani yanayi wanda bai san na meye ba, hakan ne yasa da sauri ya janye idanunsa yana juya wa ya nufi wurin zaman sa na ɗazu tare da cewa, "wai don Allah Bilal ba na son fa wasting time, I have something to do."

Juyo wa yayi shima ya nufi wurin zaman sa yana cewa, "to baka ce komai ba?"
Banza dashi yayi; wanda hakan ne yasa ya ɗauki waya yana mai kiran wata Nurse,
Babu jima wa kuwa sai ga ta cikin office ɗin, ya dube ta yace, "Sister ku je da yarinyar nan ta gyara jikinta, and ki mata bayani a kan wannan al'adar naku na mata, sai ki bata Pad ɗin; ki bata package ɗin."

"Ok Sir."
Ta amsa mishi tana mai nufan inda nake zaune a saman gadon duk na takure kaina,
Ce min tayi, "in sauko." Ta kama hannuna ta taimaka min

Babu yadda na iya haka na sauka ina jin jikina a jiƙe kamar zan nutse don kunya, sabida na san meye ya jiƙa Ni haka, ga shi nan ma har a ƙasan kafafuna ya bi min skirt, kaina a ƙasa haka na bi bayanta muka bar office ɗin

Yayinda doctorn ya mayar da hankali kan Yaya Yunus yana ce mishi, "don Allah muyi maganar gaske Yunus, wai da gaske an bada ita ko zolayana kake yi?"

Ɗaure fuska yayi yana cewa, "I'm serious an bada ita nace maka, bazan maka ƙarya ba."

Kansa ya rausayar alamun bai ji dad'i ba, sai kuma ya ɗage kafaɗa tare da cewa, "well, dama nayi tunanin in nema ne, amma tunda ka ce haka..."
Sai bai ƙarisa maganar nasa ba ya ja numfashi yana taɓe baki

Yayinda Yunus ya harare shi yana cewa, "kai dai ban san inda zaka saka kanka da shegen son Mata ba, ka yi wa kanka faɗa wlh, maganar da ake faɗi a kanku yana son zama gaskiya, ko Matan mutane suka shigo haka kuke kalle su kuna musu maganar banza."

Wata iriyar shegiyar dariya ya fasa har da tafa hannu yana cewa, "oh! Wlh ƙarya ne, duk wanda yace maka kawai dai faɗa yake yi amma ba gaskiya bane."

"Ba gaskiya bane ga shi na gani da idanuna? Hmm kaima ka san na san halin ka Dacta kawai a yi sha'ani."

Shi dai dariyan kawai yake yi yana ƙaryata wa, har da cewa, "wai har da Matan aure ka ce fa? To wa ya fi mu sanin Matan mutane? Wlh ba abun da zamu yi da su, Ni ka ganni nan in ba na ga shila kamar wannan ba Allah yanzu Mata ba sa burge Ni, ai sun yi min hankali, ko zan tashi aure wacce bata san komai ba ita zan aura, Mata hmmm."

Sai kuma abun ya koma basu dariya gaba ɗaya,
Da haka dai suka ci gaba da hiran su wanda suna tuna baya duk a kan abun da ya faru da Doctor Bilal ɗin ne

Ni da Nurse ɗin muka dawo cikin office ɗin, tana gaba ina bayanta, ta bani wani zani wanda ban san na waye ba na saka, skirt ɗina da kuma abun da ta koya min saka wa shi kuma yana cikin ledan da na riƙe a hannuna, har lokacin kaina a ƙasa yake don ba ƙaramin matsananciyar kunya nake ji ba, musamman da nake tunanin su Yaya Yunus sun san halin da nake ciki, kenan shima ya san ina wannan jinin? Kunya duk ya rufe Ni wanda yasa na kasa magana koda Doctorn yake min wasa cikin raha,
Shiru nayi na kasa ɗago kaina ma,
Sai da Yaya Yunus yace, "mu tafi." Sannan na bi bayansa da sauri muka fice,
Kamar jela haka nake bin sa har zuwa wajen motansa,
Ina kallon sanda ya buɗe bayan motan ya ga kamar kujerar ta ɓaci da jini, sai ya buɗe gaba kuma yace, "in shiga."
Babu musu na shige da sauri na,
Shima sai ya shiga ya ja Motan muka bar asibitin,
Babu abun da ya ƙara ce min har sanda muka isa cikin gidan,
Wanda Ni kuma kaina yana ƙasa jikina sai rawa yake yi, ga tarin kunyarsa na kasa ɗagowa


Shi kuwa kamar ya manta da Ni, har sanda muka isa yace min, "za ki iya fita ai ko?"
Yayi maganar da sigan tambaya yana mai kallona

Ni kuma ban yi gigin kallon inda yake ba, tunda na ɗago kaina na ga inda muke, sai nayi sauri na saka hannu na tura ƙofan ina son buɗe wa,
Ganin ya ƙi buɗe wa kuma ban fasa tura wa ba

Shi kuwa tsaya wa yayi yana bi na da kallo cike da mamakina, kuma da ya tuna aifa ban iya bane sai ya matso ya saka hannu zai buɗe yana mai bi na da ido, a hankali ya furta, "haka ake bude ƙofan a garin ku? Ke wato ƴar ƙauye ba ki iya koman ki ba ko?"

Yadda na ji maganar nasa ne da saukar numfashin sa kusa da Ni, dole na ɗago ido ina kallonsa; yayinda na waro idanun waje kamar zasu faɗo ƙasa, lokaci ɗaya numfashina ya sauya bugu yana barazanar ɗauke wa,
Da sauri na janye idanun saboda yanda ya tsare Ni da nashi idanun, wani irin matsanancin faɗuwar gaba ya riske Ni wanda ban taɓa jin makamancin sa ba, bazan ce ga yanayin ba amma tsoro ne ya bayyana a gaba ɗaya zahirin jikina, wanda tuni jikina ya ƙara kerma; nayi saurin runtse ido ina mai sake duƙar da kai sosai

Bakin sa ya taɓe yana mai yamutsa fuska kamar mai jin wari, sai kuma bai ce komai ba ya buɗe min ƙofan batare da ya ƙara bi ta kaina ba

Haka na fice da sauri riƙe da ledan hannuna na nufi cikin gidan kamar zan faɗi ƙasa, ban tsaya a ko'ina ba sai a ɗakina tunda na ga babu kowa a falon,
Wani irin numfashi na sauke ina mai zame wa a ƙasa ina jin yanda jikina ke kaf-kaf-kaf tsaban zullumi da tsananin tsoron da ke tattare da Ni ya haifar min da hakan, na kasa ma wani tunani sabida halin da nake ciki, so nake yi nayi tunanin dalilin da yasa na farka na ganni a asibiti tare da Yaya Yunus? so nake yi na gane mene ne ainihin dalilin abun da ya faru da har ya taimaka min?
Amma ban gano komai ba, wanda tuni na ƙara takure jikina na zauna nayi shiru ina tunani da zullumi; ga zafin ciwo da ke ratsa Ni

Shi kuwa koda ya shigo gidan ganin babu kowa, sai ya nufi ɗakin Sharhabila yana yin sallama ya shiga,
Da gudu Sadam ya taso; wanda suna kwance a saman gadonta ne shi da Mubashir suna wasa, ita kuma tana toilet da alamun wanka take yi,
Zuwa yayi wurin sa yana cewa, "Dady sannu da dawowa."

"Yauwa my son." Yayi maganar yana shafa kansa tare da ƙoƙarin wuce wa bakin gadon ya zauna

"Dady ina Aunty Madina take? Ta ji sauƙi ko? Asibiti ku ka je Dady?"
Duk ya jero masa waɗannan tambayoyin batare da ya shaƙi numfashi ba

Shi kuma ya amsa mishi a takaice, tare da furta, "ina Mamyn naku?"

Mubashir ne yace, "Dady tana wanka, yanzu ta shiga toilet."

While Sadam ya miƙe ya nufi waje batare da ya sake tambayar Dadyn nasu ba, sai ya nufi ɗakin da nake

Shima Yaya Yunus jin shiru bata fito ba har yanzu, ga shi har lokacin sallan Magriba ya kusa, kuma shima yana son yin wankan, shiyasa ya tashi ya koma ɗakinsa yayi wankan sannan ya ɗaura alwala, ya saka manyan kaya yadi masu kalan ruwan madara, lokacin da ya fito Falo yayi daidai da fitowar Sharhabila ta ci ado cikin lace mara nauyi mai ja da design ɗin orange, tayi ɗauri mai kyau a saman kanta ya zauna ɗas, hips ɗin nan na juya wa a cikin zanin lace ɗin da ya zauna mata shima,
Kallonta yake yi but ita babu fara'a a kan face ɗin ta, sai wani turɓune fuska take yi,
Shi kuwa tuni ya saki fuska kasancewar ba mai saurin fushi ba, kuma bai da riƙo musamman yanayin yanda yake matukar ƙaunar Matarsa, shiyasa ya soma mata magana yana cewa, "Wifey, wannan kwalliya haka? Kin yi kyau."
Wani kallo ta watsa mishi tana sake kicin-kicin da fuska, yayinda cike da zallan kishi tace, "Allah yasa dai baka dawo min da yarinyar nan cikin gidan nan ba? Don wlh sai ta bar min gida tunda ba gidan Ubanta bane."

Ɗan waro ido yayi ya tsaya yana kallonta da ɗan mamaki

Ita kuma sai ta sake turɓune fuska tana mai juya wa zuwa ɗakin da nake; batare da ta sake bi ta kansa ba

A lokacin ina zaune ina biye wa surutun Sadam da ya saka Ni dole yin sa, don tunda na zauna na kasa tashi ina zaune a wurin, sai kawai na ji an bugo ƙofan an shigo, a firgice na ɗago ina kallon Aunty Sharhabila da ta shigo min fuskarta babu ɗigon imani,
Tace, "keee! Dan uwarki ki yi maza ki haɗa kan kayanki ki zo ki bar min gida, ko in ci miki mutunci in kakkarya ki a gidan nan."

Daga inda yake yana jin muryan Sharhabilan, shine dalilin da yasa ya kasa wuce wa ya taho da sauri shima ya shigo ɗakin,
A lokacin na kiɗime na ruɗe tuni na tashi na nufi kan kayana ina ƙoƙarin haɗa wa,
Kallona yayi sannan ya mayar da kallonsa kan Sharhabila, yau ya san rigima take ji don ya san halin ta ƙwarai da gaske, shiyasa yace, "a kan me zata tafi tabar gidan Wifey? Ke kika kawo ta ko Ni? Zamanki take yi ko nawa? Shin ko kin manta ita ƙanwata ce ina da ikon da zan kawo ta gidana?"

Wani mugun kallo ta sauke mishi, cikin ɗagawa da fariya tace, "gidan ka ko gidan Dadyna? Oh! Yaushe ka siya gidan da ban sani ba? Na gani dai tun sanda muka yi aure Dadyna ya baka gidan nan; kuma har yanzu a cikin ta muke bamu sauya gida ba. Da yaushe aka yi yarjejeniyar da ya danƙa maka bani da labari iyee?".
[05/08, 9:59 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












______________ *EPISODE 26*
_____Tsaye yayi kawai yana bin ta da kallo ya kasa cewa komai, ba wai don ransa bai ɓaci ba; a'a, don tsananin mamakin irin gorin da take mishi,
Ganin ta ci gaba da cin min mutunci tana zagina a kan, "in zo in bar musu gida."
Sai ya kalle Ni ransa a mugun ɓace wanda har a muryansa ya nuna yace, "ki mayar da kayan nan, idan kika bar gidan nan za ki ga abun da zan miki... Ke kuma."
Ya nuna ta da yatsa tare da cewa, "wlh idan har kika kore ta sai dai ku bar gidan tare, bazan tsawaita magana ba amma kina son ki ga ɓacin raina ne Sharhabila, kuma bazan ce komai a kan gorin da kika yi min ba cus Ni na ja har kika samu wannan damar..."
Daga haka

Please Login or Register in order to submit comment