Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauya bane, kuma a haka za ki saba ai tunda zaman aure ne bamu da yanda zamu yi. Kinji don Allah ki dena kukan nan ba na son ina ganin ki cikin damuwa, Ihsan ma tana gaishe ki, ita ta bani saƙo da kanta da nace wurin ki zan je."

Murmushi nayi kawai na kasa cewa komai ina mai share hawayena, sai kuma na gyaɗa kaina ina kuma dariya ina kallon cikin Yaya Haulan da ya ɗan tasa alamun ciki take dashi, amma Ni ban fahimci komai ba

Hira muka soma yi duk yawanci tambayoyi ne Umma take ta min cike da kula wa da son gane abun da ke damuna, Ni kuma ina bata amsa cike da ɓoye halin da nake ciki don kar ta gane, don bazan so ta gane wanne irin zama nake yi a gidan ba, sabida ban shirya zaman aure ba, zamana a haka ya fi min alheri gwara in dauwama ina musu bauta,
Koda ta nemi in kaita ɗakina su gani; ban wani ji ɗar ba tuni na ja su zuwa ɗakin tunda na manta da tunanin zaman aure nake yi a gidan

Basu ga aibun ɗakin ba kuma hakan bai saka musu wani zargi ba, duk da bai da wani girma sosai, kuma babu komai sai kayan gado da sif, Umma dai bata ce komai ba har suka shiga bayin suka yi alwala suka yi sallah ina zaune tare da su, nima tuni nayi alwalan na gabatar da sallan,
Sai lokacin take tamabayana inda mutanen gidan suka je?
Ina bata amsa kuma sai na tuna ai fa girki nake yi,
Jikina na rawa na miƙe ina salati na fita da gudu,
Umma na kirana amma ban tsaya ba,
Hakan ne yasa Yaya Haula ta bi Ni da saurin ta tana sake kiran suna na, inda ta ga na bi nan ta bi muka shiga kitchen ɗin kusan a tare,
Koda na buɗe tukunyar har ruwan da nayi sanwa ya kusa ƙare wa,
Ganin yanda na ruɗe sosai sai Yaya Haula tace min, "wai mene ne kika ruɗe haka? Dama girki kike yi kika bar shi haka nan?"
"To Yaya Haula farin cikin ganin ku ne ya mantar da Ni fa, yau na shiga Ukuna idan Aunty Sharhabila ta dawo ban gama ba, tace min karfe biyu zasu shigo."


Ganin dai kamar hankalina ba ya jikina ne duk na bi na ruɗe, abun da ya ɗan bata mamaki, amma bata tsaya tamabayana ba sai ta hau taimaka min, tunda dafa-dukan shinkafa zan yi shiyasa nan da nan ta taimaka min muka yi a tare, lokacin ƙarfe ɗaya da ƙwata ne kafin biyun har ya kusa tsotse wa,
Muna a kitchen ɗin na ji ƙaran buɗe gate, da sauri na ɗauki cooler ina cewa, "Yaya Haula wlh ga su nan sun dawo, bari in kwashe haka nan kar tace ban gama da wuri ba."

Ganin yanda jikina ke rawa sai ita ta amsa ta kwashe sabida kar in zubar in ƙona kaina,
Bayan ta kwashe ta bani na fita dashi, ita kuma ta tsaya kashe risho ɗin

Lokacin da na isa falon har sun shigo Yaran suna ta tsalle-tsalle

Itama Umma jin motsin su ne yasa ta fito daga ɗakin da nake kwana zuwa falon don su gaisa; tunda ta ji kamar mutanen gidan ne suka dawo.
[30/07, 8:00 AM] نفيسة OumƊahira: 💎💎💎💎💎💎💎💎
    *RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.












______________ *EPISODE 24*
_____Dukkansu kallon Umma suka hau yi suna mai mamakin ganin ta a cikin Falon; batare da sun amsa sallaman da tayi ba,
Dayake ita Sharhabila bata san ta ba shiyasa take mata kallon mamaki da tsoron ganin ta a cikin gidan su, ko kafin tayi magana Yaya Yunus yayi magana yana mai amsa gaisuwar Umman da take mishi cike da fara'a,
Sai shima ya saki fuskar sabida ya gane wace ce bazai taɓa manta fuskarta ba, yace, "Umma Asiya ke ce a gidan namu yau?"

"Wlh kuwa, yau Ni ce a gidan naku." Tayi maganar tana isowa ciki sosai tare da zama a saman Kujeran,
Shima sai ya zauna suka soma gaisa wa cikin mutunta juna, duk da a hasashen shi bai kawo tunanin Mahaifiyata ba ce sabida sam ya manta cewan an ce mishi ƴar wajen Babansu Sule aka aura mishi

Sharhabila ganin haka itama sai ta zauna tana kallon Umman tare da amsa gaisuwar nata, kasancewar a lokacin Umman ta mayar da kallonta gare ta tana gaishe ta itama

Ni kuma tuni na nufi saman dining na ajiye coolern ina gyara wa kamar yadda na ga Aunty Sharhabila tana yi, yayinda Sadam ya biyo NI yana tsalle-tsalle da min surutun sa yana bani labari,
Ni dai ban bi ta kanshi ba don hankalina yana a kan su Umma, har na gama na nufi hanyar kitchen don kwaso plates

Lokacin tuni itama Yaya Haula ta fito falon; ta nufi inda suke ta duƙa har ƙasa tana gaishe su,
Shi dai Yaya Yunus amsa ta kawai yayi amma bai gane wace ce ba, but da ya ga kamar muna kama shiyasa ya bi Ni da kallo yana sake kallon Yaya Haulan, a nan take mamakin ganin Umman a gidansa ya gushe sabida ya gano dalilin zuwan nasu

Ita kuma Sharhabila sai cika take yi tana batsewa tana faman taɓe baki ganin baƙin wanda ta gama tabbatarwa dole ƴan uwansa ne, tunda ga kama nan a fuskar Yaya Haula itama, shiyasa ta tashi tsam tana shige wa ɗakinta tare da kiran sunan Mubashir da Sadam suka bi bayanta

Yaya Yunus ɗan sakin fuskarsa kaɗan yayi yana cewa, "tun ɗazu ku ka zo ko yanzu ne Umma?"

"A'a mun ɗan jima, shi ne Madina tace min kun fita tun safe, amma yanzu ma zamu tafi."

Bai ce komai ba kuma bai yi tunanin tsayar da su ba balle yayi musu tayin abinci, kawai kuɗi ya ciro cikin aljihun sa har naira 3k ya miƙa wa Haula yace, "ke amsa, Umma sai ku ƙara kudin mota, mun gode da ziyara."

Murmushi Umma tayi tare da masa godiya har ya miƙe yabar wurin, kana ta kalli Yaya Haula tare da mayar da idanunta a kaina, don nima tuni na zo na gurfana a kusa da Yaya Haulan, tace, "to Madina zamu wuce, sai wani lokacin kuma, tunda mun ga gida insha Allahu za ki riƙa ganin mu a kai- a kai, sai ki kula ki ci gaba da haƙuri, Allah ya baku zaman lafiya."

Tuni hawaye sun soma cika min ido jin abun da take cewa, kamar zan fashe da kuka sabida yanda nayi da fuskata, cikin rauni na furta, "Umma tun yanzu don Allah? Don Allah kar ku tafi ku barni zan bi ku."

"Bin mu kuma Madina? Ko kin manta aure kike yi a nan? Ki yi hakuri kin ji ko ai zamu riƙa zuwa muna duba ki, Haula tashi mu je kar lokaci ya ƙure mana; tunda ke gida za ki wuce yau."

A haka ina ji ina gani su Umma suka bar gidan, har bakin gate na raka su har da share hawayena, domin ji nake yi tamkar na bi su amma babu hali, haka ina gani suka tafi dole na dawo ciki,
A lokacin mutanen gidan duk sun fito suna saman dining suna cin abinci,
Lokacin Sharhabila tana tambayar Yaya Yunus ɗin mutanen da suka fita ne? Shi kuma yana bata amsa, shiyasa tayi kicin-kicin da fuska tana bala'i tana zage-zage tare da cewa, "gaskiya bazai saɓu a riƙa kwaso mana kare da dogi cikin gida ba, idan yarinyar baza ta yi aiki ita kaɗai ba to babu dole tabar musu gida, don ba an kawo ta don dangi su riƙa biyo ta suna ganin abun da suke ci bane, haka kawai a riƙa saka mata ido?"
Tunda na ji waɗannan kalaman nata sai na tsargu na gane da Ni take yi, a hankali na taka na yi saurin shige wa ɗaki ban tsaya jin abun da Yaya Yunus yake faɗa mata ba,
Yayinda na zauna gefen gadona na fashe da kuka sabida tsaban kewan su Umma da nake ji, sai da nayi kukana ma'ishi sannan na share hawayena na shiga bayi na ɗaura alwala, ko sallan ma ban yi ba na ji kiran Aunty Sharhabila a kunnena, da sauri na saka hijabin jikina na fita da gudu don amsa kiran nata..**

To a wannan yanayin rayuwata ta ci gaba da gudana cikin daɗi da akasin sa, to ba dai zan ce ina shan wahala sosai ba; duba da rayuwar da nayi a baya, wannan zan iya cewa mai sauƙi ne sosai a kan rayuwata ta baya, tunda a kan ayyukan da nake gani masu wahala ba komai bane a kan ayyukan da nake fama da su a gidanmu, rayuwar tawa ta sauya fiye da baya, don baza a haɗa ba ma; kawai dai farin ciki ne yayi min ƙaura wanda na kasa samu daga Matar gidan, don gaba ɗaya yanda take azazzala min da irin muguntan ta sam ba na samun farin ciki, har sai idan nayi mata abu daidai nake tsallake wa daga hukuncin ta, don har takai ta kawo wani lokacin dukana take yi da igiyar wayar wuta, abun da tun tasowa ta ba a taɓa min ba; domin kasancewata mai biyayya da rashin ƙyuya, amma duk ƙoƙarina Aunty Sharhabila ba ta gani, kuma Yaya Yunus bai taɓa ɗaga kai ya kalle mu don ya hana ta hukunta Ni ba, tamkar ma bai san abun da ke faruwa ba, babu ruwansa da Ni balle yace don me take duka na? Gaskiya ina iya ƙoƙarina wajen yin mata biyayya, da haka rayuwar ta ci gaba da tafiya ga shi har na share kusan watanni uku da zuwana gidan,
Sai a lokacin Ummanmu ta sake zuwa ta duba Ni, sabida lokacin da ta zo ma ba sa nan mutanen gidan suna wurin aiki, yaran kuma suna makaranta, Ni kaɗai ta samu, kuma mai gadi bai hana ta shiga ciki ba sabida ganin wancan lokacin ma sun shiga lafiya mutanen gidan basu kawo mishi ƙorafin kar ya sake barin su ba, shiyasa ya barta ta shiga,
Kuma bata bari ma mutanen gidan sun dawo ba tayi min sallama ta tafi, duk da wannan lokacin ma ji nayi tamkar na bi ta, amma babu hali, nasiha kawai da ban baki ta dinga yin min, wannan karon ma ta kawo min tsaraba kamar wancan lokacin, duk da a waɗancan ma ban yi amfani da kayan miyan da ta siyo min ba, sai ɓoye wa da nayi ban ƙara bi ta kansu ba, a wannan karon ta tambaye Ni, "shin nayi amfani da su na kar'ar?" Nace mata, "eh." Kawai tunda bazan iya faɗa mata zaman da nake yi a gidan ba,
Koda ta faɗa min waɗanda suka bata kuɗin nayi mamaki matuƙa, yayinda a raina sai na ji daɗi matuƙa sabida soyayyar da Hajiya Ummee take nuna min, barin ma yau da ta kawo min dambun nama tace min, "Hajiyan tace a haɗa min musamman a kawo min."
Sosai nayi godiya ina ta murna da jin daɗi,
A haka Umma ta tafi tabar Ni, yayinda na ɓoye duk abubuwan da ta bani,
Dama ban da matsala da Aunty Sharhabila a kan duk abubuwan da ta ga ina saka wa, musamman suturu domin bata taɓa tambayana ba; bare ta damu da ganin kalolin kayan da nake saka wa, tunda itama Aunty Sharhabila tana son tsabta ba ta son ƙazanta, ganin ina kiyaye wa tunda ta ja min kunne shiyasa bata damu ta bincike Ni ba tunda ta san da abuna na zo, ba Mijinta ya siyan min ba.

Haka dai na ci gaba da musu bauta tun ban saba da rayuwar gidan ba har dai yanzu na saba, na kuma saba da wahala da muguntan Aunty Sharhabila, don in ya motsa mata babu kalan cin ubana da bata yi, ta dinga zagina kenan tana ƙare min tanadi ko a gaban Yaya Yunus ne bazai taɓa tanka wa ba, tunda aka kawo Ni kuma babu wanda ya taɓa zuwa ya leƙo ni a ƙauyen mu idan aka cire Yaya Haula da Umma, babu wanda ya taɓa zuwa, wani lokacin dai sau ɗaya Baban Sasa ya kira Yaya Yunus ya bani wayansa muka gaisa, ya sake jan min kunne yana tambayar halin da nake ciki? Na faɗa masa babu komai tunda a lokacin akwai Yaya Yunus ɗin ya tsare Ni a gabansa yana sauraron abun da nake ce wa, a lokacin har sai da ya tambaye Ni, "ko Yaya Yunus ɗin ya siyan min kayan ɗaki kamar yanda ya ba shi umarni? Kuma yayi min kayan akwati da komai? Don ya fi so ya tabbatar a bakina ne?"
Ko jingirta wa ban yi ba na amsa mishi da eh don ban ga fuskar da zan iya ƙin amsa wa ba, kar in ja ma kaina ya ci ubana ina zaune ƙalau haka kawai

Shi kuwa Yaya Yunus ganin ban ɓallo mishi ruwa ba har sauke numfashi yayi, yana ganin na gama wayan sai ya amsa ya juya ya tafi dakin sa, Ni kuma dama ina kitchen ne ina aiki ya zo ya miƙa min wayan, sai na ci gaba da aikin nawa ina tunanin tambayoyin da Baban Sasa yake min, a raina nace, "tab wanne kayan ɗaki zai yi min Ni da ba Matarsa ba? Nima wlh ba na buƙata ya riƙe kayansa, zamana a haka ya fi min alkhairi."
Sai kuma na koma tunanin duk sanda Matarsa ta san cewa akwai auren Mijinta a kaina na tabbata kashe Ni zata yi, baza ta taɓa barina da rai ba a yadda dai na santa da mugunta.
A haka dai na ci gaba da ayyukan nawa har na gama na wuce ɗakin Yaran na gyara musu nayi musu wankin kayan su a cikin ban-ɗakin su, sannan na gyara Falon kasancewar babu kowa tunda ana hutu Yaran an kaisu gidan su Aunty Sharhabila, kuma yanzu safe ne yanzu haka Aunty Sharhabila bata tashi ba, don akwaita da shegen barci yanzu tunda ta soma aiki, da zaran sati da Lahadi sun yi ranan Hutu ne a kwance zata wuni, komi Ni zan yi duk da dama Ni nake yin komai yanzu, babu abun da ban iya ba na daga cikin gidan, a takaice ma har kayan Yaya Yunus yanzu Ni nake wanke mishi, tare zan haɗa da kayanta da nashi in wanke tass sannan in goge, haka ma na yaran, yanzu har takai ta kawo ta sakar min ɗakin shi Ni nake shiga na gyara idan sun fita,
Kuma duk wadannan abubuwan da nake mata wani lokacin sai ta ci gyara na ko ta wawwanka min mari wai ban yi mata dai-dai ba, ko kuma ta bani abu ban yi a kan kari ba, shiyasa yanzu har na saba da zafin nama, komai nawa ina yin sa ne cikin sauri da zafin nama gudun samun matsala, kafin ka ce me na gama, ko kusa wahalhalun gidan ba ya bani wahala, domin idan da sabo ya ci a ce na saba, kawai dukan da take min ne yake cin min rai,
Tun zuwana gidan ban taɓa saka ƙafafuna a waje na fita wajen gidan ba, kullum ina cikin gidan Ni nake musu komai, yanzu ga shi kusan watanni takwas da kawo Ni gidan, tun ma ina ƙirga kwanaki zuwa watanni har yanzu ya ɓace min,
Ummanmu sau uku kenan ta taɓa zuwa duba Ni, Yaya Haula kuma sau ɗaya, duk da ta so zuwa amma babu hali Mijinta bai barta ba

A zuwan da Umma tayi wannan karon ne muka samu matsala da Aunty Sharhabila, tunda a lokacin da Umma ta zo shab na manta ta bani aikin gyaran kayan sif ɗin ta, don cewa tayi, "kaf in ciro kayan in sake goge mata su sannan in mayar in shirya."
Sai ta ware min masu datti waɗanda zan wanke,
To a lokacin tunda suka tafi na fara aikin gidan har na share falon tsab na gyara ɗakin Yaya Yunus dana su Mubashir, sai na je kitchen na fara ɗaura girkin shinkafa da miya da tace shi zan yi, sannan sai in haɗa musu da ferfesun kayan ciki da ta bar min, na je ɗaura wa kafin in je in gyara mata ɗakin, ga shi lokacin na tashi ba na wani jin daɗi, sabida ciwon da ya kunno min na mara da na saba yi, duk da zuwana gidan sai daga baya na fara yi yanzu kusan sau uku nayi, amma da ya ɗauke gaba ɗaya ba na yi, sai watanni ukun baya ya dawo min ba ƙaramin wahala na sha ba a waɗannan ranakun, kuma babu damar in faɗa musu tunda ban ga fuska ba, a haka nake daure wa in ta shan kuka a ɗaki ina ɓoye halin da nake ciki, tunda yawanci ma da dare yake tashi min, kafin safe sai ya lafa min, sai wani lokacin kuma ya sake tashi min har sai na ga jini ya fito, to wannan ranan tunda na ji marata tana karta wa na tabbatar shi zai zo, don abu ne mai wuya in yi ciwo haka kawai sabida ban saba yawan ciwo ba, tunda na ji haka na san shi ne,
Har na ɗaura farar shinkafan sai kuma cikina ya fara ciwo sosai, dole na nufi falo na kwanta a ƙasa ina birgima da yarfe hannu, sai kuka nake yi kamar zan mutu, don a halin da na shiga na manta wace ce Ni bare in tuna abun da nake yi, sai da can kamar zan mutu sannan can ya lafa min na soma dawowa daidai, duk na haɗa gumi nayi wujiga-wujiga idanuna sun yi ja, ganin bai ƙara murɗa min bane sai na mike a daddafe na koma kitchen ɗin, lokacin abincin har ya caɓe ya sha ruwa sosai ya dafu ya tafke ma kamar za a yi tuwo, da sauri jikina na kerma na sauke hawaye na bin fuskata sabida ganin yadda shinkafan tayi, na san na kaɗe a hannun Aunty Sharhabila tunda bata san kuskure ba, tabbas sai ta hukunta Ni a kan wannan abun da nayi mata, jikina babu ƙwari haka na fara gyara kayan miyan har na jajjaga na ɗaura miyan

A wannan lokacin ne kuma Ummana ta zo, nayi murnan ganin ta wanda yasa na manta da halin da nake ciki, farin ciki da ɗoki ya hana Ni wani tunani, tuni na maƙale mata ina murna

Ita kuma kallo ɗaya da tayi min ta gane kamar akwai abun da ke damuna, don yadda ta ga idanuna sun yi ja sai tahau tambayata tana sake taɓa min jiki ganin da ɗan zafi, sai tace, "Madina ba ki da lafiya ne; na ji jikin ki da zafi haka?"

Saurin girgiza mata kaina nayi ina mai mayar da kaina saman kafaɗanta na kwantar da shi,
Sai ta sake ɗago Ni tare da cewa, "a'a ban yarda ba, da alamu ba ki da lafiya, kinji yanda jikinki yayi kuwa? Ga idanunki nan fa har sun sauya; mene ne me ke damunki?"
Cike da son ɓoye halin da nake ciki sai nace mata, "Umma wlh babu komai, kaina ne dai yake ɗan min ciwo shiyasa kika ga jikina ya ɗauki zafi."

"Ai ba kawai bane Madina, ciwo kowanne iri ne ciwo sunansa, kin sha magani ne?"

Sai nayi ƙarya nace mata, "na sha." Don dai ba na son ta ci gaba da min wasu tambayoyin, don ban san me zan ce mata ba

Sai ta ja numfashi tace, "nima ba daɗe wa zan yi ba kinga yanzu zan tafi, dama nace ne bari in leƙo in duba ki tunda na dade ban zo ba."

Cike da shagwaba don ba ƙaramin taɓara nake dashi ba muddin na ganni a gaban Ummana, don jina nake yi kamar wata ƙaramar yarinya, kwata-kwata ba na girma in dai a gabanta ne, haka ma Yaya Haula, su kaɗai ne nake iya sakin jikina da su in ji kamar in koma cikinsu don taɓara, don ji nake yi bani da wata sauran gata in har ba ina gabansu bane, shiyasa da na sanya ta a gaba dole sai da ta ƙara lokaci kafin ta tafi,
Ni kuma sai na koma kichen na ƙarisa sauran aikina,
Kamar jira ake yi na gama sai marata da cikina ya hau karta, aikin da ban ƙarisa ba kenan ban tuna da sauran gyaran ɗakin Aunty Sharhabila da tabar min ba, kuma tabbas da na tuna koda zan mutu ne sai nayi sa, amma halin ciwo yasa na manta gani nake yi kamar na gama komai, ɗakina na shige na dinga kuka ina murkususu a ƙasa kamar zan mutu, ban san iya adadin lokutan da na ɗauka a wannan yanayin ba sabida azaban ciwo, sai can ya ɗan lafa min barci ya ɗauke Ni batare da na motsa daga inda na kwanta a ƙasan ɗakin ba, kaina a kife a saman hannuna fuskata tayi sharkaf da hawaye

Barcin da ya ɗauke Ni ne ban san lokacin da suka dawo ba mutanen gidan,
Sai can kamar a mafarki na ji wani irin zugin azaba ya tsarga min a bayana, ko kafin in tantance abun da ke faruwa da Ni; tuni muryan Aunty Sharhabila ya doki kunnena, da sauri na yunƙura zan tashi, amma ina wani irin azaban ciwo da kuma bulalan da ta zula min ya haɗe min a lokaci guda, wani irin uban ihu na tsandara ina mai gantsare bayana,
Ita kuma sai ta ci gaba da narka min wayan wutan da ke hannunta cikin fushi da ɗaga murya tana cewa, "dan kutmar uban ki har Ni zan saka ki aiki ki zo ki kwanta kina barci? Sannan kika ɓata min abinci kika mayar min dashi tuwo? Halan ubanki ya siyan mana shiyasa kika wulaƙanta mana tunda ba ki da asara? Ƴar matsiyata ƙauye basu saba ci ba, yau sai nayi miki dukan da baza ki sake yunkurin kamanta min irin wannan ba, har in sa ki abu ki ƙi yi ko? Wuyanki ya isa yanka kenan?"

Tun Yaya Yunus yana jin muryata daga ɗakinsa yadda nake ɓarka kukan kamar zan tsaga gidan, tun yana jure wa sai kuma ya kasa sabida jin ihun nawa ba na hankali bane, Yaransa tuni sun bar ɗakin sun nufi inda suke jin kukan nawa, don haka shima ya mike ya fita da sauri don kar a yi kisan kai a gidan sa, don ya ji abun ba na hankali bane,
A lokacin da ya shiga ɗakin tuni azaban ciwo da na dukan da take min yasa na sume gau,
Amma ita bata gane hakan ba sai lafta na take yi tana zagina ta uwa da Uba

Da sauri Yaya Yunus ya kama bulalan yana cewa, "wai kanki ɗaya kuwa Sharhabila? Kina ganin yarinya ta sume ba ta motsi kuma kike ci gaba da dukan ta? Kashe musu ƴa za ki yi?"

"Bar Ni in kashe ta mana ai ba asarana bane, don wlh ban ga ƴar iskan yarinyar da zata zo ta ci arzikina sannan ta ƙi min biyayya ba, ba a haife ta ba, ƴar iska shegiya matsiyaciya, dama ƙauyawa basu iya cin arziki ba, to Ni bazan lamunta ba gwara su zo su ɗauke ta tunda baza ta ci banza a nan ba, tunda ba wani shege daga can yayi mana wahala ba, dama tun yaushe ake faɗa min son banzan mutanen ƙauye amma ban ji ba, ga shi yanzu na soma gani an fara kawo min ɗaya gida, nan gaba ma sai su zo su tare gaba ɗaya mu ci da su, ai Ubana ba kuɗin banza ne da shi ba."

Gaba ɗaya ta soma tunzura Yaya Yunus bata sani ba, don bai taɓa jin haushin abubuwan da Sharhabila take yi ba irin na yau da take faman zagin masa asali, sai ya ga kamar har da shi take yi ga kuma iyayensa da take haɗa wa, ransa ya soma ɓaci dalilin da yasa ya tsawatar mata kenan yana cewa, "wai me kike son fada ne Sharhabila? A gabana kike zagin asalina ko an ce miki iyayen nawa basu da abun yi ne da kudin Dadyn ki suka dogara?

Please Login or Register in order to submit comment