Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

had'amu abinci plate guda ne toh sai anyi fad'a kafin a ida cin abincin, kuma da zaran anyi fad'an toh za'a shirya bayan an gama cin abincin... Barr na k'are maka nida Zeenatu rakiyar kura muke ma junanmu tamkar bazamu rabu ba... A haka rayuwa taci gaba da tafiya mana, har zuwa lokacin dasu Zeenatu suka bar inguwarmu amma bata daina zuwa yanda nake ba nima kuma ban daina zuwa yanda take ba, aminci tsakanin iyayenmu ya k'ara k'ulluwa, har takaiga sun k'ulla alk'awarin aure a tsakanin mu dukda cewa mu a lokacin bamu fahimci soyayya muke ba, a lokacin shekaruna bazasu wuce sha tara zuwa ashirin ba, Azeeza kuwa bata wuce Sha biyu ba.."

Shiru ya d'anyi idanunsa suka cika da ruwa....

A hankali yaci gaba da fad'in

"Wata rana mahaifanmu sun tafi ziyara k'asar Cameroon suka barmu ni da k'anwata hannun Mai taimakawa mahaifiyata da aikace-aikace na cikin gida mai suna Umma Marie... Iyayenmu sunso tafiya damu saidai lokacin muna tsaka da makaranta dagani har k'anwata....."

Hawaye suka soma zubowa daga idanunsa sanda yaci gaba da fad'in "Dawowar da basuyiba ta har abada, kallo na k'arshe da muka masu sanda muka rakasu airport.... A hanyarsu ta dawowa Nigeria sukayi had'arin jirgin sama wanda ko d'aya a cikinsu babu wanda ya rayu......" Kukan Junaid ya tsananta... Lokaci guda Barr yasa hannu yana k'ok'arin maida nasa k'wallan...

Bai tak'urawa Junaid yaci gaba da basa labari ba har saida Junaid d'in yayi kuka mai isarsa had'i da addu'o'i wa mahaifansa Barr na amsawa da ameen kafin ya daidaita kansa yaci gaba da fad'in

"Mun rasa mahaifanmu a wannnan lokacin, daga ni har Azeeza rasa mai k'arfin zuciya akayi cikinmu har saida Baba Datti mahaifin Zeenatu yayita nusar dani nine babba dole na koyi hak'uri ko don k'anwata Azeeza, haka Umma Marie wacce ta zamto tamkar uwa a garemu taci gaba da bamu baki.... A haka har abin ya soma barin jikinmu kullum Zeenatu tana gidanmu tana d'ebe mana kewa.... A lokacin ina jami'a Baba Datti ya buk'aci na soma aiki da DATTI INVESTMENT Companyn sa tinda yaga kalan k'wazona da himma na, sannan sunyi zama na amana da mahaifina marigayi Alhussain..... A haka na soma aiki da Datti Investment na maye gurbin mahaifina, ina karatuna ina aiki na soyayyarmu da Zeenatu na k'aruwa, kowa yasan muna soyayya I zuwa lokacin..... Wata rana Companyn mu ta soma samin barazanar fad'awa matsalan kariyar arziki wato bankruptcy, a lokacin Zeenat ta soma aiki itama da Comapanyn sai ya zamana mun hutar da Baba Datti nida Zeenat mune akan Compnayn muketa k'ok'arin shawo matsalar da muke k'ok'arin aukawa ciki... Kwatsam ana haka cikin k'ok'arin tallata hannun jari na kampaninmu da mukeyi Zeenatu ta had'u da SIRAJ LAUSHI President na LAUSHI GROUP.......







*SameenaAleeyou...📚*
[12/13, 5:14 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮



*06*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*






Junaid yaci gaba da fad'in "Siraj....!" Shiru ya d'an biyo baya..... Hannu yasa ya shafe fuskarsa gaba d'aya d'an sauran hawayen duk suka tafi kana yaci gaba da fad'in "Tun lokacin da ya d'aura idanunsa kan Zeenatu ya aukawa soyayyarta.... Bugu d'aya Laushi Group ta amince da had'akar kasuwanci da Datti Investment, nasan zaka iya sanin lokacin tunda kaima kana k'ark'ashin Companyn....?" Ya k'arashe yana duban Barr cikin idanu...

A hankali Barr ya girgiza masa kai kana yace "A lokacin ban fara aiki da Laushi Group ba domin lokacin da na soma aiki dasu lokacin auren Siraj ne....."

Junaid yayi shiru tamkar mai nazari kana ya gyara zamansa saman wheelchair d'insa...

"Baka sanar dani mai ya rabaka da matarka, meyasa kake zaune daga kai sai 'ya'yanka... Shin kaima iftila'i ce ta rayuwa ta auka maka....?"


Shiru Barr yayi yana dubansa kafin ya d'an murmusa ya d'an shafi nape d'insa kana yace "Bai kamata ana bada labari a katse a shiga wani ba idan da mai saurarenmu zai shiga rud'ani...." Ya k'arashe murmushi kwance saman fuskar sa.....

Junaid d'inma murmusawa yayi yana mai karantar Barr kana yaci gaba da fad'in "Kace wani abu.... A ina na tsaya maka ma?"

Tambayar saida yaso baiwa Barr dariya ya kuwa d'an murmusa kana yace "Had'uwar Siraj da Zeenatu..."

Junaid ya murmusa yace "Haka kuwa...." Saida ya kuma saita kansa kana yace "Murmushi ba d'abi'ata bace tun bayan rasa farin ciki na sai gashi yau ka sa sai yinta nake a arha... Da ace Umma Marie da Zeeza zasuga fuskata da murmushi da sai sun maka kyauta....."

Barr ya kuma murmusawa kana yace "Ni fatata ka dawamma cikin murmushi domin sosai take k'arawa fuskarka annuri da kamala...."

Junaid ya shafi k'asunbin sa wanda bai jima da tarawa ba kana yaci gaba da fad'in "Sabo sosai Siraj da Zeenatu sukayi duk a tunaninta sabida kasuwancin da ya had'asu ne sam bata kawo Siraj nada wata nufi na soyayyarta cikin zuciyarsa ba... Wasu lokutan haka kawai zai buk'aci suyi confidential meeting da Zeenat su biyunsu, su fita tare joints parks da sauransu duk akan ana tattauna business ne... A lokacin sai na fara zargin wani abu sam banason keb'ewanta da young tycoon d'in.... Toh sai na fara nuna mata rashin amincewata gashi lokacin Datti Investment ta soma hab'akowa da taimakon Laushi group, a lokacin Zeenat sai ta d'auki abun kishi ne kawai irin nawa, wani sa'in har ta nuna rashin jin dad'inta tunda gashi har mahaifinta na alfahari da ita, you know how business men are... Kasuwancinsu ya fiye masu komai... Ana haka abu ya soma bayyana da gaske dai Siraj soyayyar Zeenatu ne tam cikin zuciyarsa, ni kuma a lokacin sai na soma jin Zeenatu taci amanar soyayyar da nake mata, duk da banso zuciyata ta aminta da zarginta na cin amana amma na kasa... Wasu irin manyan kyauta Siraj yake mata wanda har ita kanta ta soma tsorata da lamarin nasa, koda tazo ta sameni ta sanar dani halin da ake ciki banza na mata, Mahaifiyarta kanta bataso saka Zeenatu da Alhaji Haruna Datti yayi kan hark'ok'in kasuwancinsa ba tinda ita mace ce gashi ita kad'ai Allah ya basu... Shiko Alh Datti ganin kasuwancinsa na hab'aka sai ya mance da komai, sai ya zamana Alh Siraj Laushi bashida wajen hira sai wajen mahaifin Zeenat, wanda shi kansa mahaifin Zeenat gani yake wannan babban nasara ce a gareshi tinda Alh Siraj ya tsallake k'anan Kamfanunuka da dama ya tunk'ari nasa... A haka Siraj ya soma sanar da mahaifin Zeenatu buk'atarsa..." Aya ya d'an saka ya d'ago yana duban Barr kana yaci gaba da fad'in "Kasan meye abin mamakin...?"

Nasaar ya girgiza kai alamun a'a bai sani ba...

Junaid yaci gaba da fad'in "Mahaifin Zeenat ya amince da buk'atan Siraj wanda bani kawai ba harta mahaifiyar Zeenatu da ita kanta Zeenatun saida muka shiga rud'ani.... Ranar wata alhamis Baba Datti ya kirani har parlornsa yake sanar dani _Junaid kayi hak'uri ka amshi soyayyarka da Zeenat a matsayin k'addarar rayuwarka, sannan ka nemo wata yarinyar ko a ina take ni zan tsaya maka a matsayin mahaifi har ka mallaketa, Junaid na riga na amshi kud'in auren 'yar uwarka Zeenatu nanda wani lokaci kad'an za'ayi auren...._ "A lokacin sumewane kawai banyi ba domin duniyar juyamin ta soma yi.. I was like.... Ta yaya Baba zaimin haka, bayan duk mafarkan da mukashayi wajen gina gidanmu da Zeenatu, tare muka girma tare muka gina rayuwarmu da mafarkanmu da komai da komai, bamusan soyayyar kowa ba sai na junanmu, rana d'aya tak ace na rabu da ita... How could that be possible....? Muryata tana rawa nake fad'in Baba lafiya wani abin nayi.. Baba ko baka aminta da tarbiyata bane... Baba dan Allah kar ka rabani da Zeenatu wllhi bansan yaya rayuwata zata kasance ba... Baba please don't do this na rok'eka... Baba ya kalle ni da idanun tausayi kana ya duk'ar da kansa yana girgizawa ya d'ago ya dubeni da k'yar yace _Junaid I'm sorry, ka yafe min d'ana wllhi banida zab'i kasan akan kasuwancina babu abinda bazanyi ba muddin inada halin yi d'in, rayuwata gaba d'aya nayisa ne cikin k'ok'arin gina kasuwanci na.. Kayi hak'uri Junaid kayi hak'uri d'ana..._ A lokacin bansan sanda na mik'e na soma tafiya hanya na hard'e min ba sai ganin Zeenatu nayi gabana cikin shesshek'ar kuka ta rik'eni tana fad'in _Junaid dan Allah kar ka bar Abbah yayi haka... Junaid dan Allah kace ya aura mana juna, please don't let him do this.... Junaid kar ka bari a aura min wanda banaso, ka manta mafarkanamu da burikanmu.... Junaid ka amsa min mai Abbah yace maka....._ Tamkar mutum mutumi haka Zeenat ke jijjigani ina kallon kyawawan idanunta masu zuban ruwa, kasa ganewa nayi zafin kukanta nakeji kokuwa zafin abinda Baba Datti yamin nakeji.... Ban iya ce mata komai ba sai b'anb'are hannayenta da nayi daga jikina... Ina jiyo sautin kukanta yanda na barta a durk'ushe tana rok'ona na dawo amma ban iya juyawaba sabida tsoron kar na zube a wajen nima..." Shiru yayi idanunsa suka kad'a sukayi jazir yayinda idanun Barr ya kawo ruwa sosai wani irin tausayin Junaid yakeji....

Junaid yaci gaba da fad'in "Da fari Siraj yayi kaman ya janye neman auren Zeenatu sabida sam bata sonsa dukda dukiya da kyau da Allah ya masa, amma abokansa guda biyu sukayita ingizasa don bana mancewa a k'ofar Datti Investment wani rana abokinsa Lamid'o yake fad'in _Yanzu duk dukiyar da ka kashe zai tashi a banza, shikenan kan wani k'aramin talaka saika zuba idanu wa macen da kake k'auna. Haba Siraj kada ka badamu, mai amfanin dukiya da Allah ya maka a d'an k'ank'anin shekarunka, ka taka wanda kake so kayi abinda kaga dama babu wanda ya isa ya had'a nema dakai amma fah idan kabi shawarina...._ Iyaka abinda na iya jiyowa kenan suka shige luxurious cars d'insu suka bar k'ofar kmfanin.... Bayan kaman sati guda da faruwan haka saiji nayi ana d'aura auren Zeenat da Siraj.... Na ga kira bila adadi da sak'onni da layinta ban d'aga ba ban mata reply ba,... A ranar auren kaman bazan d'agaba sai kuma na d'aga kiran cikin tsananin kuka naji muryarta tana magana k'asa-k'asa tana fad'in _Junaid zasu kasheni dan Allah kazo ka cecni ka cireni daga gidan nan... A toilet na kulle kaina amma wllhi ina jiyo muryarsa nemata suke zasu kasheni...._ Hankalina sosai ya tashi na mik'e tsaye ina tambayarta wani gida su waye zasu kasheta?... Cikin kuka da k'ank'an da murya taci gaba da fad'in _Junaid kasheni zasuyi dan Allah kazo kazo yanzun nan zanyi iya k'ok'arina yanda bazasu ganni ba har ka iso....._ Cikin tashin hankali nace ta min texting address cikin k'ank'anin mintuna kuwa adreshin gidan ya bayyana jikin screen d'in wayata... Umma Marie da Zeeza suna parlor suna kallo sai ganina sukayi na fice nida gaba d'aya ko aiki na daina zuwa ba tareda na sanar dasu daliliba amma sai ganina sukayi na fice cikin sauri.... Umma Marie ta mik'e tana fad'in _Junaidu lafiya ina zaka da mangariban nan....?_ Ina ko amsata banyi ba na fice a gigice, ina fita na sami mai babur na d'ale.... Ina isa gidan na fad'a cikin gidan kai tsaye saidai dai-dai sanda na isa na jiyo sautin k'aranta tana ambato sunana tana fad'in nazo na taimaketa.... Da k'arfin gaske na kira sunanta na shiga bud'e k'ofofin Mansion d'in ina neman ta ina take...... Kafin na ankara saijin k'aran harbi nayi tauuuu.... Daga wannan lokacin ban kuma jin ihunta ba.... Jikina ya d'auki rawa na fad'a cikin gidan sosai ina neman ta ina zan ganta..... A k'ofan bathroom d'in dake d'akin tsakiya na hangeta jini na b'ulb'ulowa daga k'irjinta yanda aka d'ana mata harsashi tana mik'o hannu tana yunk'urin yin magana amma ta kasa.... Da rarrafe na k'arasa gabanta cikin sark'ewar murya na shiga jijjigata ina tambayarta waye yayi mata haka, su waye suka mata haka.... A dai-dai lokacin Siraj, Ahidjo da kuma Lamid'o suka shigo a birkice bindiga rik'e hannun d'ansandan cikinsu wato Ahidjo... Cak suka tsaya suna kallonmu yanda na rungumeta ina kuka... Hannu take k'ok'arin d'agawa sama amma ta kasa lokaci guda Zeenatu ta daina motsi.... Na saki k'ara ina kuma k'ank'ameta.... Siraj da k'irjinsa bai daina bugu ba kukan kura yayi yayo kaina yana fad'in mai nayi wa matarsa wllhi shima sai ya kasheni.... Nima d'in damk'o shi nayi ina fad'in mai sukayi ma Zeenatu wllhi sai na kashesu gaba d'aya... Kafin na ankara saiji nayi sun had'u gaba d'aya su duka uku suna dukana kaman zasu aikani lahira, shi d'ansandan da boot d'insa ya dinga takani abokansa suna tayasa... K'afafuwana kuwa dandatsasu suka dinga yi wanda tun ina iya kallonsu har na daina.... K'arshe da sukayi tunanin na mutu suka sa securities d'insu suka kwasheni suka tafi dani can wajen gari suka watsar dani wajen gari, wani mutumi shi ya tsinceni gefen gonarsa bayan sunmin magani na gida har na soma magana sannan ne nake sanar dasu ga daga yanda nake ma'ana gidanmu.... Sosai Umma Marie da Azeeza sukayi kuka babu kaman Azeeza wacce takega tamkar ta kuma rasa wani jigo na rayuwarta... Ban sanar da Azeeza gaskiyar abinda ya faru ba sai Umma Marie wacce bayan na sanar da ita bata barmu garin Abuja ba tsoron daga su san cewa ban mutu ba su biyoni har gida su k'arasani... Tuni Umma Marie ta d'aukemu muka koma can garinsu Yobe cikin garin Damaturu, toh a nan ne aka soma jinyar k'afata har aka min aiki a babban asibitin Damaturu, saidai ba'ayu nasara a aikin ba likitoci sun tabbatar mana akwai jijiyoyi da suka daina aiki a k'afata..... Na wayi gari na bud'e idanu na tsinci kaina gurgu.... A cripple..... Bazan kuma tafiya ba for the rest of my life kaman yanda suka tabbatar mana.... Zan k'are rayuwata saman wannan keke da kake gani......." Sauk'e ajiyan zuciya yayi kana yace "Wannan shine labarin Junaid, wannan shine babban illa da FUSKA UKU sukayiwa rayuwar Junaid..." Ya k'arashe yana duban Barr wanda jikinsa ya gama yin sanyi gaba d'aya da rayuwar Duniya......


Barr ya zaro handkerchief daga suit pocket d'insa ya goge hawayen da yaji suna taruwa cikin idanunsa sabida tsananin tausayin Junaid da rayuwar da suka fuskanta kana yace "Tabbas kaga rayuwa sannan dole kayi tunanin d'aukan fansa, amma kanaga anya sune suka kashe Zeenatu kodai rashin sa'a akayi kuka isa wajen a tare...?"

Junaid ya d'ago ya dubesa kana ya girgiza yana mai fad'in "Kai kasan Siraj Laushi ka kuma san duk budurwar da ya nema da sunan aure mutuwa take, a matsayinka na lauya shin ka tab'a tunanin mai yasa matan suke mutuwa? Shin mai yasa babu mahaluk'in da ya tab'a tunk'arar Siraj Laushi...? Sabida yanada k'arfin dukiya, ko kuma meye dalili...? Idanma Siraj Laushi dukiyarsa na tsafi da mata ne toh bazai sha jinin Zeenatu ya zauna lafiya ba, wllhi wllhi jinin Zeenatu sai ya tsaya masa a mak'ogoronsa.... Banzo nan ba saida na shirya...."

Barr ya sauk'e ajiyan zuciya kana yace "Kenan shigar da k'ara zakayi... Ko menene shirinka...?"

Junaid yayi wata murmushi don sam baiji mamakin tambayoyin da Barr Nasaar ke masa ba tunda yasan fanninsa ne..

"Ka tab'ajin anyi defeating mai dukiya a shari'a a wannan duniyar tamu.... Ko kuwa ka tab'ajin anyi fad'a da hukuma.... Kasan abokinsa d'an sanda ne mai license na harbi... Toh koma ba wannan ba ta ina shaida d'aya tak zaifi shaidu uku.... Ba wahalar da kaina nazo yiba doka nazo d'auka da hannayena Barr dan haka kada ka soma tunanin irin taimakon da zaka min kenan..."

Barr yayi shiru yana dubansa, muryar Junaid ya katsesa da fad'in "Naji dad'i da ya kasance kanada babban alak'a da Laushi Group... Taimakon da nake so babba guda d'aya ka soma min shine ka samarwa Azeeza aiki a kamfaninku sannan aikin ya kasance ta zamto Sakatariya ga SIRAJ LAUSHI.....



Ba Azeeza dake bakin k'ofa ta gama jiyo komai ba hawaye na faman ambaliya a idanunta harta Barr Nasaar saida k'irjinsa yayi wani bugawa.....


****


Ta jima tana zaune saman kujeran tana faman fiffincike cotton wool dake cikin k'aton teddy bear d'in dake hannunta, sam bata zaci Nadiya bazata aminta da buk'atanta ba... Lokaci guda ta matse teddy bear d'in jikin kujera tana masa magana tamkar mai tab'in hankali...

"So tell me uncle why? Meyasa sai kayi aure? Meyasa bazaka zauna da family d'inka kawai ba sai ka auro wata... Uncle bakasan rabamu dakai zatayi ba? Bakaga yanda Ahidjo bai damu da nasa family d'inba sai na matarsa,... Uncle haka kaimafa zaka zama idan kayi aure... Haka zata rabamu dakai ka koma sai ita kad'ai da danginta.... Uncle bazan tab'a bari wata ta rabamu ba... Kaji wllhi bazan bari ba..." Ta k'arashe tana duban yanda ta lalata teddy d'in lokaci guda ta rungume teddy d'in tana fad'in "Oh I'm sorry... I'm sorry luv... I didn't mean to hurt you... I'm sorry kaji..." Ta k'arashe tana cuccusa cotton wool d'in cikin rigar teddy d'in.. lokaci guda ta mik'e ta kaisa ma'ajiyansa ta ajiye... Cikin sauri ta zari car keys d'inta daga gidan ta fice....

***

Wani map suke kan kalla suna tattaunawa akai shida abokin nasa suna ganin tsarin da ya kamata a maida kamfanin, k'aran da wayarsa tayi ne ya sanyasa excusing kansa ya fice saida ya sami keb'ebb'en waje kafin ya soma amsa wayar...

Daga d'aya b'angaren mutumin yace "Lamid'o wai shin mai ka tsayayi har yanzu, kwana biyu fah bana gane maka..."

Lamid'o ya shafi k'eyarsa kana yace "Sir k'ok'arin da nakeyi yanzu kenan insha Allah bazan baka kunya ba, komai zai tafi kaman yanda muka tsara is just a matter of time... Komai ya kusa zuwa k'arshe... I'm sorry sir muna tsaka da meeting zan kiraka in the next 15 minutes... I don't want him to be suspicious ...."

Daga d'aya b'angarwn mutumin ya amsa masa kafin ya katse kiran... Saida ya fuzar da iska had'i da shafa kansa kafin ya fito daga elevator d'in ya koma office d'in Siraj..





*SameenaAleeyou📚*
[12/13, 9:44 PM] ‪+234 810 044 6653‬: *FUSKA UKU*🏮




*07*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*





Girgiza kai kurum Barr Nasaar yake kana yace "Amma baka tsoro ka jefa k'anwarka cikin wannan tashin hankali.... Azeeza k'aramar yarinya drag her into this please...." Ya k'arashe tsananin damuwa ya nuna sosai a fuskarsa...

Junaid ya matso dabda Nasaar kana yace "Da taimakon Azeeza zan cimma wani b'angare na burina ka gane.... Kar ka damu bazanyi abinda zai cutar da ita ba nasan mai nakeyi...."

Barr ya jinjina kai kana yace "Ko baka tsare Azeeza ba wllhi zan tsareta kuma a shirye nake na tayaku d'aukan fansa.... Amma ina labarin mahaifan Zeenat su kuma mai ya faru dasu...?"

Junaid ya girgiza kai yana mai fad'in "I don't know ban sani ba... Ban k'arabi takansu ba, FUSKA UKUN nan ne kurum na maida hankalina akansu su nake karantar duk wani motsi nasu tsawon shekaru...."

Barr ya kuma jinjina kai yana mai duban agogon hannunsa sai jiyo muryar Junaid yayi yana fad'i "Nasaar na aminta dakai lokaci guda ba kasafai nakeyin hakan ba amma kai bansan dalilin da yasa na aminta da kai cikin k'ankanin lokaci ba.... If there's one thing I hate is betrayal.... Nasaar wllhi wllhi kayi tunanin cin amanata zan zame maka sanadin k'unci na biyu A DUNIYARKA bayan matarka.... Nasaar ka rik'e min amanata..."

Ganin yanda jijiyar goshinsa ta fito sosai ya sanya k'irjin Barr bugu, k'ak'aro murmushi yayi kana yace "Kana tareda yardata Junaid bazan ci amanarka ba da yardar Allah...."

Junaid ya jinjina masa kai dai-dai lokacin da Azeeza ta shigo hawaye na safara a fuskarta...

Kallo take kan faman binsu dashi yayinda Junaid ya soma k'ok'arin saita kansa donyima k'anwar tasa magana...

Girgiza masa kai ta soma tana fad'in "Yaya u don't have to explain..... I've heard everything, so that was the reason.... Yaya why? Meyasa... Haba Yaya Junaid shin Fansa ya kamace ka, shin A DUNIYARKA babu hak'uri.... Yaya I can't bazan iya ba... And I'm going back to Damaturu immediately.... Bana cikin burin Fansarka....." Tana kaiwa nan tasa kai zata juya cikin tsananin huci... Saidai kafin takai k'ofa Junaid ya isa ya rik'o hannunta...

Juyowa tayi suna kallon juna hawaye na ci gaba da ambaliya a fuskarta....

"Azeeza you must.... You must help me.... Babu komawa da baya sabida na riga na fara....."

Tsugunawa tayi suna fuskantar juna su duka biyun.... Kasa magana tayi sai wani sabon kukan da ya b'alle mata... Cikin sauri Junaid ya rungumeta cikin jikinsa shima hawayen na neman ciko idanunsa....

Barr ya bisu da kallo cikeda tausayawa....

****

*Tambuwal*


Kaman kullum suna zaune tsakar gidan suna sana'arsu ta sark'an beads itada Zaliha da k'awarsu Hanne yayinda Dadda ke bayi tana wanka da shike hantsi ta sako kai sanyi ya d'anyi sauk'i...Abinka da Dadda tana bayin tana wankan tana 'yan wak'e-wak'en ta.... Tun daga bayin taji ana bugun k'ofar gidan ana k'wantara sallama....

Uwar tsaki taja don tasan yanzu haka bazai wuce masu karb'an sark'an amarya bane gashi su Mairo sun sake kid'an Barmani Mai Choge a tsakar gidan tasan bazasu saurari bugun k'ofarba....

Tsaki taja tana goga soso take fad'in "Wai wayene mai bugun k'ofar nan ne....?" da shike bayin ba wani ratar kirki bane garu ne ya raba tsakaninsa da wajen gidan....

Daga yanda suke tsaye sai jiyo muryoyinsu tayi suna fad'in "Daga ofishin Hisbah ne...."

Ai a d'ari Dadda ta wanke sabulun dake idanunta tana fad'in "Na'am... His mene...?"

D'ayan ya k'ara cewa "Hizbah..."

Cikin sauri ta janyo zaninta saman garu ta d'aura a k'irjinta tana fad'in "Toh lafiya dai koh, ko kunyi zaton nan d'in gidan Magajiya ne...?"

"Ko mu shigo ne....?" d'ayan ya kuma tambaya...

"Kai gani nan zuwa ku jirani, ina tafe..." Ta k'arashe tana d'aukan kwandon wankarta.... A filin tsakar gidan ta tarar dasu Mairo an sha kallabi a gefen kai jai rangaji da kai ake ana zura beads jikin d'an robar tsark'ar da gani suna jin dad'in sana'ar tasu... Batabi takansu ba sai hijabinta data d'auka saman igiya ta nufi k'ofar gida...

Aiko tana bud'ewa taga mutum biyu da Uniform jikinsu da dorinai ga kuma Malam Balarabe a gefensu yana muzurai yana hura hanci....

"Toh lafiya dai ko...?" Ta tambaya tana yarfe sauran ruwan fuskarta...

"Hajiya kin gane wannan.? " Guda d'aya ya tambaya yana nuna mata Malam Balarabe da dorinar hannunsa..

Yatsina fuska kurum Dadda tayi kana tace "Yo na ganesa mana, ba yaron nan ba d'an gidan Tale d'an bana sauk'e kawai ya soma malamta ko ba shine ba....?"

"Hajiya toh a gidan nan naki munji labarin akwai karuwai kina tara 'yanmata da sunan kina koya masu sana'a ashe kawalci kike., kuma tabbas gashi muna jiyo sautin gurmi daga cikin gidanki na tashi don haka yanzu zamu shiga muyi kame..."

"Bantan uba...." Ta furta tana tattaro hijabinta, kafin ta ankara sai gani tayi sun shige gidan Malam Balarabe yana fad'in "Ku dai shiga suna ciki watsatsun amma ku rintse idanu...."

A d'ari Dadda ta take masu baya tana ruwan bala'i had'i da tafe hannaye....

Su Mairo kam zumbur suka mik'e ganin maza cikin gidansu rik'e da dorina...

Dadda fad'i take "Wata doka ce ta baku dama ku shigo min kan iyalai na 'yan mata... Toh wllhi sai munyi shari'a daku...."

Malam Balarabe suna had'a idanu da Mairo yayi bayan jami'in hizbah guda d'aya yana fad'in "Ka gansu nan suna asharalle dama na fad'a maku koda na masu wa'azi mutunci na sukaci harda cewa zasu bugeni...."

Jami'in Hizbah ya d'aga dorina yana fad'in " Ya subihanallah.. Ku wuce muje... Muje nace, baku iya komai ba sai bad'ala da cin mutuncin Malamai...."

Abinda ya basa mamaki shine babu wanda ya motsa daga Mairo har k'awayenta... Kallo d'aya kurum tayi wa k'awayen suka fahimci mai take

Please Login or Register in order to submit comment