Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni ban sallama dukiyarsa wa k'adangarun bariki ba ehe, banda sakarci da dolanci kun wani zauna a nan kun k'yale dukiyar wa matarsa ta bariki taci itada iyalanta ni kuma tawa d'iyan fah taci mene, yanda wancan take matarsa haka Deejoh take matarsa, kaso guda za'a basu domin yanda wancan zatayi takabansa haka Deejoh ma zatayi, ki fad'i min a banza zatayi takaba ko k'ak'a inyi... Ke Deejoh zo nan mu tafi wllhi baki takabansa sai an baki kason ki na gado...." Ta k'arashe tana k'ok'arin janyo Deejoh da kukanta ya k'aru....

Sai sannan Innah tayi hobb'asa ta fincike hannun Deejoh daga rik'on da Gaje tai mata, cikin tsananin b'acin rai take fad'in "Koda wasa kada ki kuskura ki kuma kai hannunki jikin Deejoh, anya kinada zuciya a k'irjinki Gaje wani irin bak'in zuciya ne wannan idanma kinada shi, shin ko tausayin Deejoh bakiji har kina bud'e baki kina maganar gado, sanar dani nawa ne kasonki a cik...." Bata kai aya ba Gaje ta shiga gud'a tana tafe hannaye take fad'in "Da aka aurar wa d'an naku Deejoh ai ba sayar masa akayi ba balle kice Deejoh ta shiga gado sai yanda kukayi da ita... Kuma na fad'i na sake fad'i idan kinga Deejoh tayi takaban sallamemmen bariki toh kuwa shakka babu an damk'a min gadon Deejoh ne ehe...." Ta k'arashe tana kuma kai damk'awa Deejoh dake k'ok'arin b'oyewa bayan Innah, cikin tsananin kuka Deejoh ke fad'in "Innah Gaje dan Allah kiyi hak'uri kar ki tafi dani, wllhi mijina bai mutu ba, dan Allah kiyi hak'uri Allah zai dawo...."

Baki Gaje ta kame tana salallami take fad'in "Inyi lallai Deejoh wato har kinsan dad'in miji kike fad'in bai mutu ba zai dawo koh, toh ki bud'e kunnuwanki da kyau kijini, ya mutu a yawon bariki bazaki sake ganinsa ba 'yancinki da hakkinki nake nema maki dana ce bazakiyi takabansa ba sai an baki kasonki na gado...."

Cikin kuka Deejoh ke fad'in "Nidai bani son gadon dan Allah ki k'yaleni, Innah dan Allah kar ki bari ta tafi dani..." Ta k'arashe cikin shesshek'a tana mai kuma kamo hannayen Innar...

Tsananin mamakin hali irin na Gaje ya hana Innah furta koda kalma sai kallon mamaki kurum da take binta dashi.... Bata ida mamaki ba saida taga Gaje ta kwab'e mayafinta tana kokawan sunkutan Deejoh... Innah ta soma kiciniyar hanata inaaa Gaje ingarmiya ce bata wasa ba...

Deejoh kuwa tsamin hammatan Gaje shi ya d'ago mata aman da take ji na taso mata tun shigowar Gajen..

Kokawar d'aga Deejohn take a dai-dai sanda amai yazo ma Deejoh gadan-gadan, aiko kan kace mai sai a fuskar Gaje.... Ihu ta saki tana shafa fuskarta tana jin tsantsi-tsantin aman... "Wayyo na shiga uku, Deejoh ki rasa yanda zakiyi amai sai fuskata dan ubanki, fuskar da ta raineki tun kina ficika ita zaki wanke da amai.. Mai hanani cin uwarki yau babu shi..." Ta k'arashe tana goge fuskar nata cikin gaggawa...

Innah kuwa fad'i take "Wllhi kika tab'a lafiyar Deejoh yau saidai ayi jini biri, yau ne zan nuna maki ba'a dandali kurum ake buga wasan shad'i ba a gida ma anayi..."

Deejoh dai tsugune tayi tana k'arasa sauran amai d'in dai-dai sanda Malam yayi sallama ya hangi Innah na kokawan hana Gaje d'aukan Deejoh...

"Subhanallahi, Bilkisu lafiya? Meke faruwa a gidan...? Ki saketa nace Bilki..." Ya k'arashe yana mai ida shigowa cikin gidan...

Sakinta Innah tayi tana mai ci gaba da huci take fad'in "Malam wannan matar mahaukaciya ce sai an mata na mahaukata tukuna a zauna lafiya da ita..."

Ganin Baffah ya shigo ya sanya Deejoh guduwa bayansa cikin sauri tana mai ci gaba da kukanta take fad'in "Baffah kace ma iya Gaje Yaya Ahidjo bai mutu ba zai dawo ya d'aukeni, Baffah kar ka bari ta tafi dani kaji dan Allah..."

Mamaki ya cika Baffah yama rasa meke faruwa har saida Gaje ta ci gaba da balbala ruwan bala'i kafin ya fahimci ina ta dosa....

Cikeda b'acin rai ya katseta da fad'in "A ina kika tab'a jin mace mai takaba ta baro d'akin mijinta muddin tanada masu kula da ita da kuma lafiyarta, babu yanda zaki d'auketa ki tafi da ita, kuma ki fice min a gida kafin na kira maki hukuma su rabamu tinda ke kin raina kowa...."

Gaje tayi shewa tana mai ci gaba da watsa bak'ak'en maganganu tana fad'in bazata bar Deejoh gidan ba sai an bada kasonta na gado.... Ana cikin wannan drama Sabi'u yayi sallama gidan don yanzu ya zamto tamkar d'an gida kullum k'afafunsa na Misau, aka kuwa yi sa'a yau d'in kakinsa ne a jikinsa....

Baffah yayi hamdala kana yace "D'ansanda gwara da Allah ya kawo ka na tabbata kai zaka rabamu da wannan matar...."

Gaje cikinta ya d'uri ruwa, ita kad'ai ta soma reverse tana nufan k'ofa mayafi a hannu.... Tsaban tsoro ta kasa furta koda kalma ga Sabi'u ya tsareta da ta mujiya.... Saida ta zo kusansa zata wuce ya tare hanya yana fad'in "Ina kuma zakije...?"

Gaje baki na rawa take fad'in "Yallab'ai wasan tashe nake, kaga ma rawar 'yan tashe...." Ta shiga juyi tana wani wak'e mai kama da sunbatu.... Shikam Sabi'u dariya taso basa saidai kafin ya ankare Gaje ta wawashe takalmanta da sunan rawan tashe ta arta a guje....

Sabi'u ya nufi waje zaibi bayanta Baffah ya kirasa yace ya k'yaleta bazata sake dawowa ba...

Sabi'u ya dawo cikeda risinawa yana mai gaida Baffah, Deejoh kuwa tinda ta hangesa taji wani k'atutun bak'in ciki na taso mata, bata san dalili ba amma haka kurum taji ta tsani mutumin tun ranar da yazo ya kawo masu sak'on mutuwar Yaya Ahidjo, shiko Sabi'u sosai yake kyautatawa su Baffah duk a cewarsa sabida zaman amanan da sukayi da Ahidjo ne, wani hidiman idan Baffah ya hanesa sam bai dainawa saidai yace iyakacin abinda zaiyiwa Ahidjo kenan yanzu da babu shi ya kula da iyalansa da iyayensa....

Sam Deejoh ko gaisawa bata tsaya sunyi ba ta shige d'aki abinta, tana jinsa suna gaisawa da Innah harda tambayan yaya jikinta, haushi tamkar ya kasheta, itakam sosai ta tsani wannan mutumi dukda kyautata masu da yake, ta danganta tsanar data masa sabida shine ya kawo masu sak'on mutuwar mijinta, bazata tab'a mance wannan kalamai da suka fita daga bakin wannan mutumi ba... (Deejoh kenan mai ji da k'uruciya da yarinta bata yarda mijinta ya mutu ba...)

***


*Abuja*


Yau d'in bata fice aiki ba sabida rashin jin dad'in jiki da take fama dashi, gaba d'aya foundation din sai bai masa dad'i ba, bai zaci ya shak'u da Asma'u har haka ba, mai yasa gaba d'aya ya kasa samun sukuni, shi kad'ai sai hangen k'ofan ofishinta yake yaga ko zata iso, wata zuciya tace mai yasa ka damu da ita har haka bacin kurum amfani da ita kake ka cimma burinka? Take b'angare na zuciyarsa ta basa amsa da sabo ne kurum ba wani abu ba, da zaran ka gama biyan buk'atarka ka breaking heart d'inta dana Uncle d'inta zaka cireta daga rayuwarka and that's all, tabbas babu macen da zata maye gurbin Zeenah cikin zuciyarka...

A hankali ya sauk'e ajiyan zuciya had'i da fuzar da iska.... K'ok'arin yakice tunanin cikin zuciyarsa yake amma ya kasa, koda ya kira layinta ba'a d'aga ba, hankalin Junaid ya kuma tashi, ji yayi bazai iya zaman foundation d'in ba, ji yayi yana son sanin halin da take ciki.... Tamkar wanda aka zabura ya shiga tura wheelchair d'insa ya fice, b'angare na zuciyarsa tana kuma k'arfafa masa gwiwa kan yaje ya dubata ta haka ne kurum zata kuma aminta cewa shid'in masoyinta ne, sannan ya tabbata a dai-dai wannan lokacin Siraj bai gida yana wajen aiki..Yana ficewa ya hango mai tasi kana ya saka masa hannu...


***


Wajajen k'arfe 11:00am ya shigo gidan, kana ganinsa zaka fahimci sam babu nutsuwa a tattaredashi ga wani uwar rama da yayi sai idanunsa da dogon hanci kurum kake hangowa a farar fuskar tasa....

Cikin sauri ya nufi sashen sa ya fad'a d'akinsa, kai tsaye closet ya k'arasa ya d'auki wata 'yar k'aramar jaka mai cin kaya a k'alla kala uku, cikin sauri ya shiga tura kayan ciki, waya mak'ale a kunnensa yake fad'in "Sameer I need the private jet ready right away..." Bai jira amsar Sameer d'in ba yaci gaba da abinda yake...


Tamkar ba Siraj ba haka ya fito, Shirt d'in Mango ne jikinsa mai ruwan toka sai wando black chinos, jakkar rataye a kafad'ansa ya isa parking space ya bud'e motarsa k'irar BMW ya jefa jakan cikin motar kana ya zagayo gefen matuk'i...

Kamar wacce akace ta lek'a waje tashinta kenan daga baccin asara ta hangi Uncle Siraj na jefa jakan kaya cikin mota, ta tabbata wannan tafiya ce zaiyi ta sirri wanda baiso su sani... A guje ta isa jikin window d'in ta wangale tapka-tapkan murafen window tana mai ambato sunansa take k'ok'arin fashewa da kuka tana fad'in kada ya tafi don dama ko jiya saida yasha artabo da ita da kuma Ammah, sam sun hanasa tafiyar da sunan nemo Azeeza....


A hankali ya shafi goshinsa don yasan yanzu zata taso masa Ammah.. A dole ya nufi cikin gidan kafin ta fito waje ta taddasa...


Ayiya ya tarar a k'asa ta fito kitchen hannunta rik'eda magungunan Nana A da ruwa saman k'aramar plate cikin glass cup...

Saida ta firgita da ganin yanayin Siraj... Wani irin wawan rama yayi lokaci guda... Baki bud'e take fad'in "Kai kuwa lafiya kaman wanda ya mik'e daga jinya..?"

Shafa goshinsa yayi yana duban maganin dake bisa parantin a hannunta kana yace "Badai sai yanzu Ammah zata sha maganinta ba..."

"Maganin Asma'u ce..." Ayiya ta basa amsa tana mai k'ok'arin saka kai..


"Nana A ce bata da lafiya... Since when, yaya ban sani ba...?" Ya tambaya yana mai duban Ayiyan...

"Yo ina kuwa zaka sani tunda ba 'yar gaban goshinka bace...." Ta kuma fad'i tana taka bene..


Dafe kansa yayi domin kuwa tabbas baisan batada lafiya ba, shi kansa bai zauna bane ga Al'amran da suka sha gabansa a 'yan kwanakin... Cikin sauri ya nufi upstairs aiko sukayi kicib'is da Nana H cikin kayan baccinta take ko d'aura falmaran saman batayi ba ta fad'a jikin Siraj tana kuka sosai take k'wallawa Ammah kira tana fad'in "Ammah kizo Uncle zai tafi garin yak'i ya barmu..."

Babu shiri Ammah ta fito tana fad'in "Siraj babu yanda zakaje, ince yarinyar nan ita tace bata sonka ko ana soyayya dole ne, ka k'yaleta tayi tafiyarta, ina kasan zaka sameta salon mu rasaka ko mai sanin kanka ne duniya babu yarda a yanzu....

K'ok'arin tsame jikinsa yayi daga rik'on da Nana H ta masa ya k'araso ga Ammah wacce tsananin tashin hankali ya nuna sosai a fuskarta...

Hannayenta ya kamo yake fad'in "Ammah dan Allah ki k'yaleni na nemo farin cikin rayuwata Azeeza, Ammah babu wanda yasan yanda ta tafi... Bazan iya zama bansan halin da take ciki ba, dan Allah Ammah kimin izini na tafi na rok'i arzikin ki...."

Kalamansa tamkar garwashin wuta haka Nana H take jiyosu, batasan Uncle ya kamu da soyayyar Azeeza har haka ba, ko mutuwar Zeenat Uncle bai shiga tashin hankali irin wanda yake ciki a yanzu ba.... Saurin k'arasowa tayi tana mai ci gaba da kuka take fad'in "Ammah wllhi asiri ta masa, kinga gashi wai zai bita.... Ammah shikenan ta raba...."

Tsawan da Siraj ya darara mata ne ya sanyata had'iye sauran maganarta lokaci guda kuma Ayiya da Nana A suka fito

Huci Siraj yake yana nuna Nana H da yatsa sanda yaci gaba da fad'in "You stay out of this okay... You've no right to decide for me.... Ina son Azeeza kuma zan nemota duk yanda ta shiga ta fita...." Maido da dubansa ga Ammah yayi wacce itama kallon mamakin take masa tamkar ba Siraj d'inta ba, gaba d'aya mace ta maidasa wani iri lokaci guda...

Ayiya kuwa tamkar ta taka rawa ganin Siraj ya dasa birki wa Nana H gaban kowa abinda bai tab'a yi ba duk munin kaifin da zatayi....


Siraj yaci gaba da fad'in "Ammah I'm sorry, but I really need to do this... Please understand me, Ammah zan iya kula da kaina dan Allah ki k'yalenk na nemo Azeeza..."

Ammah dake kallon wani gefen rai b'ace ta furta "Ban amince ba Siraj, ban amince maka ka fita neman yarinyar da ta sanar dakai bata k'aunarka ba..."

"Ammah please....!"

Dakatar dashi tayi ta hanyar d'aga hannu kana tace "Banson jin komai... Ka zab'a ko ni ko ita...."


Cak ya tsaya yana duban Ammah yayinda Nana H ta shiga murmusawa a hankali tana mai taune labbanta na k'asa alamun hukuncin Ammah yayi mata...

Wani irin bugawa k'irjin Siraj yayi, bai zaci Ammah zata yanke masa hukunci mai tsauri irin haka ba, shiyasa yaso ya tafi ba tareda saninsu ba... Yana nan tsaye a wajen sai ganin Nana A yayi ta k'araso cikin tafiyarta da yafi kama d'ingishi, hannayen Ammah ta kamo tana hawaye take fad'in "Ammah dan Allah ki k'yale Uncle yaje ya nemo Azeeza, Ammah Azeeza itace farin cikin Uncle kiga yanda ya rame a dalilin rashinta, Ammah dan Allah ki masa izini yaje bamu san wani hali take ciki ba.... Please...." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya...

Ganin Amman batace komai Nana A bata daina jijjiga hannunta ba alamun rok'o yasa Siraj k'arasowa ya rik'e hannun Nana A nan yaji zafin zazzab'in dake jikinta, a hankali ya soma furta "Kar ki damu sweetheart, Azeeza na cikin k'oshin lafiya a duk yanda take insha Allah, ki kwantar da hankalinki kinji I'll be fine...." Hannunta ya rik'e ya maidata d'aki, da kansa ya b'alla mata magani tasha tausayinsu ya kama Ayiya lokaci guda, for the first time da taji tausayin Siraj..

Nana H kuwa uwar harara ta raka Nana A dashi kafin ta takewa Ammah baya tana mai furta "Bak'ar munafuka a haka zaki k'are...."

Saida ya baiwa Nana A duka magungunanta kafin ya nufo downstairs zuciyarsa naci gaba da masa zafi, cikin sassarfa yake tafiyar har ya iso farfajiyan gidan....

Dai-dai sanda securities masu tsaron gate suka bud'ewa Junaid k'ofa...

Hango mutum saman wheelchair ya sanya Siraj tsayawa cak ba tareda ya kuma k'ara koda step guda bane....

Shima Junaid d'in hango Siraj da yayi tsaye a gabansa ya sanyasa daina motsa tayun wheelchair d'insa... A dai-dai kuma lokacin wayar Siraj ta soma ruri... Ga tsananin mamakin sa Sunan Lamid'o ne b'aro-b'aro ya bayyana masa saman screen d'in....




*Toh fah masu karatu ga Siraj ga kuma Junaid sun had'e, shin yaya zata kaya masu....?*

*Zuwan Junaid yayi dai-dai da bayyanar Lamid'o shin yaya wasan zata kaya.....?*



*Ku biyo alk'alman Sameena domin jin yanda wannan labari mai cikeda sarkakiya zata kaya👌🏽*





*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮



*48*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*






Maida dubansa ga wayar dake hannunsa yayi k'irjinsa na tsananin bugu, gaba d'aya ya kasa d'aga wayar sai duban screen d'in da yake yi cikin rashin yarda da abinda yake gani, sunan Lamid'o b'aro-b'aro, mutumin da ya b'ace sama da wata guda a halin yanzu.... Har wayar ta yanke Siraj bai daina kallon wayar ba, lokaci guda ya tuna da mutumin dake gabansa, cikin sauri ya d'aga kai saidai wani ikon Allah bai gansa ba, baiga wannan fuskar ba, fuskar da ya gaza tantancewa itace ko ba ita bace, kardai gizo abubuwa suka soma masa...

Cikin sauri Siraj ya nufi gate ba tareda ya sami zarafin magana wa securities ba... Ga tsananin mamakin sa babu mutumin nan, babu ko k'yallinsa, zuciyarsa taci gaba da bugawa, bai mutu ba.... Kai bashi bane, bashi bane mutumin da sukayi tarayya wajen ganin bayan rayuwarsa shida abokansa... Ya tabbata gizo abubuwa suka soma masa... Cikin sauri ya shiga shafa wayarsa yana ganin kiran Lamid'o na kuma shigowa... Jikinsa a mace ya d'aga wayar ba tareda ya iya furta koda kalma ba...

"Kana Company ko gida, ina zan sameka....?" Abinda Lamid'o kenan ya fad'i daga d'aya b'angaren....

Siraj ya zama lost gaba d'aya, wai meke faruwa ne...? Cikin sanyin murya yake fad'in "Lamid'o meke faruwa ne dan Allah... Ka sanar dani dan Allah....."

Katsesa Lamid'o yayi da fad'in "That's precisely why I called.... And if possible ka koma gida ka had'a 'yan gidanku gaba d'aya domin maganar ta shafesu suma..."

Jikin Siraj ya kuma yin sanyi... Girgiza kai yake cikin rashin gane ina kalaman na Lamid'o suka dosa kana yace "I don't get you, family na kuma.... Meye had'insu da b'acewar da kayi kuma...."

"Siraj kayi yanda nace domin babban Al'amari ke tafe dani...."

Jinjina masa kai yake tamkar yana ganinsa kafin yace "Shikenan, ina gida sai kazo....." Bai ko jira cewar Lamid'o ba ya katse kiran ya k'arasa saman wasu kujeru ya zauna yana tunanin yanda Al'amra suke tafiya masu, Fuskar da ya gani d'azu-d'azu a gabansa ta kasa b'ace masa, sannan zuciyarsa ta kasa aminta cewa shid'in ne... A hankali ya kifa kansa a wajen ga tunanin Azeeza na neman zautar dashi....

Kardai wannan shine Junaid... Yes Junaid, junaid sunansa, kardai shine saurayin da suka had'uda Nana A a foundation.... K'irjinsa tai wani irin bugawa... Tabbas sai yanzu abubuwa suka shiga dawo masa, yaron nan fansa yazo d'auka akansa tabbas bai mutu ba, wato yazo yayi amfani da Nana A ya d'auki fansar sa akansa.... Cikin sauri ya nufi cikin gidan kaman zai kifa da k'asa zuciyarsa na masa zogi....

"Nana A! Nana A!! Asma'uuuu....!!!" Ya k'arashe cikin tsananin d'aga murya...

Ba Nana A kurum ba gabaki d'aya d'okacin gidan a d'ari suka nufo downstairs yanda suka tarar da Siraj na faman huci, bai tab'a kasancewa irin hakan ba musamman kan nieces d'in nasa...

Jikin Nana A na rawa ta k'arasa garesa Ayiya na biye da ita tsoron kada ta kifa...

Baki har na rawa Nana A ke fad'in "Uncle... La... Lafiya.. Meke faruwa, wani abu ne ya faru....?"

Bai daina huci ba yake fad'in "Asma'u wanene Junaid, waye shi mai ya kawosa rayuwarki....?"

Gaba d'aya parlorn da mamaki suke dubansa, babu kaman Ayiya da Ammah,

"Tambayarki nake...!!!!" Ya kuma fad'i cikin daka tsawa...

Lokaci guda idanunta suka shiga fidda ruwa tana mai girgiza kai don batama san mai zata ce masa ba....

Ayiya kuwa juyawa kurum tayi tana watsa wa Nana H dake tsaye jikin staircase mugun kallo don tasan wannan bazai wuce aikin Nana H ba, ita dai tak'i jinin taga 'yar uwar cikin farin ciki, tasan bazai wuce d'aya daga cikin tuggunta ba....

Cikeda fad'a Ayiya ta maido da dubanta ga Siraj dake tsaye yana faman huci kana taci gaba da fad'in "Toh idan bai sota ba kaine zaka aureta ko me, kaji min tsiyan hali.. Ka wani zo kana kumfan baki... Toh Junaid shine mijinta yaron arziki kuma shi zata aura da yardar Allah ba mayaudari irin wancan gantalellen abokin naka ba...."

A hasale yake watsawa Ayiya mugun kallo kana yace "Idan ina magana da Asma'u ki daina saka min baki, ke baki san komai ba... Sannan duk duniyar nan ni ne mutumin da zai bada auren Asma'u kuma na gama magana bazata auri wannan yaron ba har abada...."

Kukan da Nana A ke rik'ewa ya kufce mata, cikin sauri ta fad'a jikin Ayiya tana mai fitar da sautin kukanta ...

Ammah da ranta ya gama b'aci dama bata huce da fushin da take da Siraj d'in ba ga wani tashin hankali ya kunno kai a hasale ta k'araso gaban Siraj dukda numfashinta dake seizing asthma d'inta naso ya tashi...

Cikin tsananin fad'a take fad'in "Siraj wai lafiyarka, ko shaye-shaye ne ka soma abinda bakayi a k'uruciya ba... Tun shekaran jiya ake d'aga hankalin kowa a gidan nan... What's gotten into you.... Meke damunka, don kai taka budurwar ta tafi tace bata sonka sai kace kowa ma bazaiyi aure ba, idan zakayi adalci wa Asma'u ince yanzu yanzun nan ko awa guda ba'ayiba ta ida kareka tana bin bayanka... Toh ka bud'e kunnuwarka da kyau kaji, idan a baya na zuba maka idanu ka banbance tsakanin Asma'u da Hafsat yanzu bazanyi ba, sanda Hafsat tace tana son marigayi abokin ka ince jikin ka har na rawa ka bada aurenta sai yanzu da Asma'u ta sami mijin aure zakace bazaka bada ita ba... Kai waye ya matsa maka, dukda lalura irin taka bamu tab'a fasa nema maka aure ba.... Toh bari kaji na fad'a maka.. Idan wannan yaro Junaid shine zai zamto farin cikin jikata then I'll give her my unconditional support.. Kai baka isa ka hana ba....."

Jikinsa ya d'anyi sanyi ganin yanda numfashin Ammahn ke fita da k'yar, dole ya bita a sannu sabida health condition d'inta... A hankali ya soma furta

"Ammah please understand me, bamuyi bincike kan yaron nan ba, haka kurum bazamu d'auki aure mu basa b....."

Katse sa tayi da fad'in "Banson jin komai, baki da baki muka jima muna hira dashi a nan, kuma da dabara na tambayesa komai gameda shi kuma ya sanar dani.... Nasan abinda nake Siraj, idan kai baka bada aurenta ba dangi basu k'are ba, wllhi kasa tsiya can Bulkacuwa zamu tafi a d'aura aure.."

Kansa a k'asa yayinda kukan Nana A ya sassauta, shiru ya d'an ratsa parlorn....

Dai dai nan Nana H ta k'arashi sauk'owarta daga bene tana mai tafe hannaye had'i da yin dariya mai d'an sauti kad'an take fad'in "Bravo Ammah, my Grandmother is now acting like the head of the family already.... Ammah kar ki hada soyayyata da Ahidjo da wannan gurgun saurayin Nana A d'in... Kar ki mance Ahidjo ya bani jini sanda nayi ciwo kaman zan mutu, sannan a lokacin bakuda abinda zaku biyasa dashi da ya wuce ku mallaka masa ni tinda ya nuna yana sona, idan ban mance ba da bai bani jininsa a wancan lokacin ba da zaiyi wuya idan baku rasani ba, so bakuda zab'i da ya wuce ku d'auki aurena ku baiwa Heedj dukda cewa baku san iyayensa ba baku tab'a ganinsu ba..."

Ta k'arashe tana mai k'arasawa kusan Siraj dake binta da kallon mamaki domin lamarin Nana H ya soma basa tsoro, duk duniya babu wanda take gani da gashin ido.... Hannayensa ta kamo had'i da saka fuskar tausayi kana ta soma fad'in "Uncle this isn't the first time da aka soma aure ba tareda sanin dangi ba a wannan gidan, idan baka mance ba anyi akaina da late DT Ahidjo, Uncle my Sister loves that crippled so much, dan Allah ka aura mata shi kaji Uncle, Nana A tana buk'atan aure ni na sani, kaga tayi k'ok'arin tsare kanta tsawon shekarunta, yanzu data sami mai k'aunarta tsakani da Allah ba irin Lamid'o ba ya kamata ka aura mata shi kafin hak'urinta da juriyarta su gaza ta soma bin maza...." Ta k'arashe tana wani juya idanu kana ta k'arada "Shawari ce..."

Gabaki d'aya parlorn babu wanda ya iya tofa mata yayinda Nana A ta bita da kallo idanunta na ci gaba da fitar da ruwa, tabbas bata san meye 'yar uwar tata ta d'auketa ba...

Siraj kam duk bayanin da zai masu yasan bazasu fahimcesa ba hasalima baiso k'wai ta fashe suji sirrinsa da ya jima yana b'oye masu... Cikin sauri ya fice daga parlorn kaman zai kifa da k'asa....

***

Waje ya kuma dawowa ya zauna saman wasu kujeru had'i da kwantar da kansa saman table d'in gabansa... Gaba d'aya ya tukwikuye kan nasa ya damk'e


Har bak'ar jeep d'in k'irar Prado ta ida shigowa haraban cikin gidan Siraj bai sani ba, tin daga cikin mota Lamid'o ke hangosa, tausayin Siraj ya rufe zuciyarsa, tsanar Bulama da bak'in ak'idarsa ta d'aukar fansa ya kuma cika zuciyar Lamid'o, dunuya a yau anyi watsi da hak'uri sai k'alilan Ubangiji ka sanyamu cikin k'alilan d'in...

K'arar rufe mota ne ya sanya Siraj d'ago da kansa daga kifen da yake...

Hango Lamid'o ya tuno masa abubuwa da

Please Login or Register in order to submit comment