Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mace ba d'aya ba... Lokaci guda ya cimmata..


Duk k'ok'arin k'watan kanta da take ta kasa, da k'arfi take fincika tana kuka sosai take fad'in "Let go of me, you monster, let me go..." Ta k'arashe tana mai kwad'a masa jakkan hannunta, saidai inaa Nasaar bai saketa ba ya jefata a mota had'i da saka ma motar key yana fad'in "You shut up, bakisan danger d'in da kike neman jefa rayuwarki ciki ba..."

Cikin kuka take fad'in "Babu ruwanka dani koma mutuwa nayi, you've no idea how much I hate you..." Ta k'arashe tana kuka sosai..







Koda suka iso gida ma da kansa ya sureta ya jefata a d'aki suka kulleta shida Junaid...

Kuka Azeeza take daga cikin d'akin tana rok'on Yayanta Junaid ya bud'eta...


Cikin b'acin rai yake fad'in "This is the consequences of your actions Azeeza, a cikin d'akin nan zaki zauna har sai na gama d'aukan fansata kan Siraj, na tabbata rashinki zai jefasa cikin musiba da k'unci yanzu zai d'and'ani zafin ka rasa masoyi kafin ya bak'unci lahira...

Cikin Kuka Azeeza take fad'in "Yaya Junaid don't hurt him please, I beg you kar ka cutar dashi, hurt me instead, dan Allah kar ka cutar da Siraj...."

Duk kalaman da take a kunnen Nasaar ji yake kaman yaje ya shak'e Siraj Azeeza ta daina tunaninsa... Cikin sauri ya fice daga parlorn don bazai iya ci gaba da sauraron kukan da take akan Siraj ba....

Haka suka kulle Azeeza saidai su dinga mik'a mata abinci babu fita


A haka aka kuma kwashe sati biyu, a dai-dai wannan lokaci Sabi'u yayi shirin tunk'aran iyayen Ahidjo domin ya sanar dasu mutuwar d'ansu....

Gidan Mai unguwa Sabi'u ya soma zuwa ya kuma sanar da abinda ya kawosa cewa sak'o yazo badawa ga mahaifan Aliyu, Mai Unguwa ya buk'aci a kirawo Malam Sanda saidai Sabi'u ya nuna yafiso idan da hali a kaisa can gidan Malam Sandan ya fad'i masu sak'om domin kaman hakan zaifi...

Mai Unguwa ya jinjina kai kana ya kirawo d'aya daga cikin 'yan fadansa yace suyiwa bak'om rakiya zuwa gidan Malam Sanda...

Tafiyace mai d'an rata kad'an dashike gidan ba'a cikin gari yake ba kafin suka isa....

Sank'ira yayi sallama k'ofar gidan Malam Sanda, baki na biyu aka amsa daga ciki kafin Malam Sanda ya fito suna gaisawa da Sankira... Nan Sankira yake masa nuni da bak'on da yazo nemansa daga can birnin tarayya


Malam Sanda ya maido da dubansa ga Sabi'u kafin ya mik'a masa hannu sukayi masabaha, cikeda rusunawa Sabi'u ke gaida Malam Sanda kafin Sankira ya masu sallama yace ya barsu lafiya...


Malam Sanda ya dubi Sabi'u kana yace "Toh bawan Allah gashi ban wayeka ba, lafiya dai koh...?"

Sabi'u ya d'an gyara tsayuwarsa kana yace "Toh wato Baba wani Al'amari ke tafe dani, kuma akan D'anka Ahidjo ne, amma idan bazaka damu ba zanso mu shiga daga ciki sai na sanar dakai komai gaban sauran iyalan naka domin Ahidjo ya sanar dani yanada iyali a nan gida..."

Baffah ya jinjina kai kana yace "Haka ne, amma abinda ban gane ba shine wani sak'o ne zai baka dashi bazai iya zuwa ba, wato abin nasa har ya kai ya daina zuwa saidai yayo aike, toh idanma wani abin ya baka ka kawo mana ka maida masa kayansa don dagani har iyalaina bamuda buk'ata...."

Shiru Sabi'u yayi yana duban Malam sanda had'i da karantarsa kana ya d'anyi gyaran murya yace "Baba wato wannan Al'amari da zan sanar daku Al'amari ne mai girma, kayi hak'uri mu shiga daga ciki, ka zauna kaima domin sak'o na magana zan sanar daku ba ta dukiya ko na wani abu makamancin haka ba... Dan Allah Baba..." Ya k'arashe cikin k'ank'an dakai...


Shiru tamkar Malam Sanda bazaice komai ba sai kuma yace "Shikenan mu shiga daga ciki...

Baffah da kansa yayiwa Sabi'u shimfid'a kafin ya kirawo Innah, ganin Baffah da bak'o matashi ya sanya jikin Innah yin sanyi don ba kowa ya fad'o mata ba face tilon d'anta, gaisawa Innah sukayi da Sabi'u kafin Baffah ya buk'aci ta kirawo Deejoh su taho tare...

Nan Innah ke sanar da Baffan Deejohn bataji dad'i ba tun safe zazzab'i ya rufeta, bata gane jikin ba....


Baffah yace "Subhanallah yaya baki sanar dani ba...?".


Naga zazzab'in ya d'an sauk'a ne shiyasa ban sanar dakai ba amma yanzu haka ma bacci take..."

Baffah ya jinjina kai kana yace "Ki zauna toh wannan bawan Allah sak'o yaron nan ya basa ya kawo mana..."

Jin haka yasa k'irjin Innah bugawa da k'arfin gaske domin kuwa tabbas tasan Ahidjo Baffah ke nufi, lokaci guda ta nemi waje ta zauna k'irjinta naci gaba da bugu, don haka kurum ta tsinci kanta da tsoron jin sak'on da za'a isar masun


***

*A garin Damaturu*


Yau yake cika sati biyu cif a asibitin, a hankali ya soma motsa d'an yatsansa, yana mai k'ok'arin bud'e idanunsa da suka masa nauyi tamkar an d'aura masa manyan duwatsu, da kad'an kad'an idanun nasa suka bud'e gaba d'aya... Nurse dake k'ok'arin d'aura drip mamakine ya cikata taga abinda batayi zato ba.... A guje ta fice kiran Dr Sahal hakan yayi dai-dai da shigowarsu Baba Malam da kuma Hafiz, ganin Nurse d'in ta fito daga d'akin a guje ya sanyasu nufan d'akin cikin sauri...


*Toh fah mai karatu wasan zai soma... Just stay tuned guys*


*SameenaAleeyou📚**FUSKA UKU*🏮




*45*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*




Sabi'u yayi gyaran murya kafin yaci gaba da fad'in "Nidai sunana Detective Sabi'u Lawan, kuma ni abokin aikin Ahidjo ne, munsan juna sama da shekara biyar sannan mu aminan juna ne domin mun wuce abokai wannan dalili yasa ya sanar dani labarinku don ko matarsa batasan daku ba...." Fasali ya d'an ja kafin yaci gaba da fad'in "Baba, Iya wato gaskiya kuyi hak'uri da batun da zakuji daga bakina..."

Inna da tuni hawaye ya soma fitowa daga idanunta cikin tsananin tashin hankali ta tari Sabi'u da fad'in "Bawan Allah dan Allah ka sanar damu mai ya sami d'anmu ka rik'e bayananka sai ka sanar damu halin da yake ciki na rok'i aezikinka..." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya... Baffah kam bai ma iya furta komai ba sai k'uri da yayiwa Sabi'u...

Sabi'u ya kuma muskutawa kafin yaci gaba da fad'in "Haka ne, a kwanakin baya yau kimanin wata guda cif an tura wasu 'yansanda daga cikin mu zuwa jihar Borno domin kwantar da tarzoma... Toh Ahidjo yana cikin wad'anda aka tura...."

Kukan da Innah ke dannewa ya fito mata gaba d'aya, lokaci guda take girgiza kai tana k'unshe bakinta zuciyarta bata daina yankewa ba sanda Sabi'u yaci gaba da fad'in "Sak'o ya riske mu cewa 'yan ta'addan sunyi nasaran kashe wasu daga cikin 'yansanda sannan cikin wad'anda tsautsayin ya ritsa dasu harda aminina Aliyu... Allah ya masa rasuwa tun wancan lokacin....!" Ya k'arashe yana matsan k'walla sai ka rantse har cikin zuciyarsa ne...

Jiri ne ya soma d'iban Innah daga zaunen da take, tama kasa yin kukan sai tara-tara da take gani, ta kasa gasgata kalamun wannan mutumi, Aliyunta tilon d'an nata wai shine babu sannan babun na har abada bama babun da za'ace wataran zai dawo ba.... Lokaci guda taji k'irjinta na mata zafi tamkar an d'aura mata gingimen dutse yayinda bakin Baffah bai daina karanto innalillahi wa inna'ilaihi raji'un ba...

Ganin Innah zata zube yasa Baffah saurin rik'ota murya na rawa sosai yake fad'in "Bilkisu ba kuka zakiyi ba, kiyita karanto innalillahi wa inna'ilaihi raji'un....!" Girgiza masa kai kurum Innah take hawaye masu tsananin d'umi suna ci gaba da gangaro mata, shi kansa Baffah da zai samu kuka ya fita masa tabbas da zaiyi sabida tsananin rauni da zuciyarsa tayi...

Girgiza kai Innah keyi tana rik'e da Baffah k'am take fad'in "Malam... Malam kace min ba haka bane, badai Ahidjo na ba, Malam nasan bai mutu ba, Malam ban tab'a ji a jikina ya mace ba... D'ana yana nan, d'ana bai mutu ba.. Dan Allah kuce min yana raye, ku fad'a min... !" Ta k'arashe cikin tsananin kuka mai ban tausayi

"Bilkisu ba'a k'aryan mutuwa, muyi hak'uri haka Allah ya k'addaro mana... Allah sarki Baba Wuro ashe dawowan da bazai mana ba kenan... Ashe rabuwa dashi zamuyi na har abada... Kaico ban bashi daman ya mana sallama ba.. Bilkisu zan dad'e inajin zafin wannan abu cikin zuciyata....!" Ya k'arashe yana fitar da hawaye don jarumtakarsa ta gaza, gudan jini ba wasa ba...

Sabi'u kuwa yanda kasan ya sami TV haka ya maida wad'annan bayin Allah, ya dubi wannan ya dubi wancan, ganin hawaye idanun Baffan Ahidjo da kuma yanda mahaifiyarsa ke fitar da nata kukan ya sanya jikin Sabi'u yin sanyi, sun basa tausayi matuk'a Allah sarki da alama basuda wani d'an sai shi....

Deejoh da k'arasowarta wajen kenan domin cikin baccin nata k'irjinta yayi wani irin yankewa ya fad'i, ba komai yazo bakinta ba sai Yaya Ahidjo, cikin sauri ta fito waje nan kuwa tajiyo kukan Innah daga sashen Baffah, k'afafunta na rawa ta k'arasa ga uban juwa dake d'ibanta, a dai-dai lokacin da Deejoh ke k'arasowa wajen ta jiyo muryar Sabi'u na fad'iwasu Baffah "Kuyi hak'uri ku masa addu'a Ahidjo mutumin arziki ne kuma yayi zaman amana da kowa, ubangiji ya gafarta masa.."

Idanuwan Deejoh shafe mata sukayi, wani irin bugu taji k'irjinta na mata tamkar ana sauk'e mata guduma.... Kalmar Allah yayi masa rahama ne kurum ke yawo a dodon kummuwarta da kwanyarta... Wani irin k'ara ta saki had'i da zubewa a wajen gaba d'aya hankulansu yayi wajenta....

Sabon tashin hankali daga Innah har Baffah suka nufeta cikin sauri domin ceto nata rayuwar....

***

Dr Sahal ya buk'aci su basu waje don ya gana da patient d'in nasa ya fahimci wani hali yake ciki.... Gaba d'aya Baba Malam da Hafiz suka fice suka bar Dr Sahal da wannan majiyanci...

K'uri Dr Sahal ya masa yana karantarsa yanda yayiwa Dr Sahal k'uri babu um balle um-um, da fari saida ya karkad'a hannunsa saman idanunsa ya tabbatar ganinsa bai gushe ba kafin daga bisani ya matso dab dashi kana yace "Sannu bawan Allah.. Zaka iya fad'a min sunan ka....?"

Shiru majinyacin bai amsa sa ba sai kauda kai gefe da yayi, Dr ya kuma komawa b'angaren da ya juya kansa kana ya maimaita masa tambayar da ya masa... K'uri majinyacin ya masa ba tareda ya furta komai ba... Dr Sahal ya soma tunanin k'ila ya rasa jinsa ne... Maimaita masa tambayar yayi a karo na uku sai sannan majinyacin ya d'an girgiza masa kai alamun a'a cikin murya da bai fita sosai irinta majinyanci mai tsananin jin jiki yace "Ina ne nan, meye nakeyi a nan...?"

Saida Dr Sahal ya masto da kunnensa dab da bakin majinyacin kafin yaji maganganun da yakeyi.... Murmushi Dr yayi don an haye wani sirad'in, rank'wafowa ya kumayi yana duban patient d'in kana yace "I'm Dr Sahal and nan da kake gani asibiti kake, you went through a serious accident... Zaka iya fad'a min menene sunanka ko kuma menene ya sameka...?" Ya k'arashe yanai masa k'uri

Patient d'in ya d'ibi dak'ik'ai yana duban Dr Sahal kafin ya d'an kuma girgiza kai a karo na biyu kana yace "I don't know, ban sani ba, I don't remember anything...." Daga haka kauda kansa gefe yayi ba tareda ya kuma amsa sa ba....

Mik'ewa Dr Sahal yayi had'ida d'an fuzar da iska kafin ya janyo file d'insa dake bisa table d'in gefen gadon yayi wasu rubutu kana ya fito ya taddasu Hafiz da Baba Malam....

Dr Sahal bai b'oye masu komai gameda patient d'in nasu ba don dama ya sanar dasu irin haka ka iya faruwa, shi baima zaci zai tsaya a haka ba, yayi zaton zai iya rasa ganinsa ko jinsa koma hankalinsa gaba d'aya amma Allah cikin ikonsa sai tunaninsa ya shafe kawai, tabbas abin a godewa Allah ne...



Dr Sahal ya sanar dasu nan da sati biyu za'a iya sallamansa amma yanzu suna iya shiga su gansa domin ya sanar da majinyacin cewa sune mutanen da suka tsincesa suka kuma kawo sa asibiti...


***

Abu kaman wasa Deejoh bata farfad'o ba duk irin ruwan da aka yayyafa mata, cikin sauri Sabi'u ya mik'e yana fad'in "Baba asibiti ya kamata mu kaita, kar a kuma...."

Baffah cikin tsananin tashin hankali yake fad'in "D'an nan babur d'ina yau kwananta guda wajen gyara, asibiti ba nan kusa ba sai mun shiga gari...."

Sabi'u bai jira wata-wata ba ya sunkuci Deejoh da Innah ke rungume da ita tana fad'in kar ta tafi itama ta barta, hanyar waje Sabi'u ya nufa yana fad'in "Baba muje akwai motata a waje..."

Cikin tsananin tashin hankali Baffah ya rik'o Innah suka fice domin gaba d'aya itama taimakon take buk'ata

Suna isa health center aka karb'i Deejoh, Sabi'u ko zama baiyi ba saida ya tabbata likita ne ya amshe ta, gaba d'aya sai rawar k'afa yake yana nuna tsananin damuwarsa..

Daga can reception ya samawa su Baffah wajen zama yana mai ci gaba da basu baki yana sanar dasu Deejoh zata sami lafiya...

Baffah tallafo matarsa sosai yayi hawaye na gangaro masa yake ci gaba da fad'in "Aliyu na yafeka duniya da lahira, wllhi na yafeka, ka yafeni d'ana ni kaina nasan ban kyautawa rayuwarka ba koda ka kasance mai laifi... Kaico wannan rayuwa mai cikeda tarin dana sani...!" Kukansa ya k'aru

Innah ce ke k'ok'arin basa baki tana fad'in "Malam addu'a zamuyi ba dawo da abubuwan da suka wuce ba, amma Malam zuciyata ta kasa aminta Ahidjo ya rasu saidai kaman yanda kace ba'a wasa da mutuwa, amma nikam jikina yana bani d'ana na raye kuma idaniyata tana jin zata sake ganinsa. Na yafesa duniya da lahira, saidai idan har da gaske ya mutu wajen yak'i sun cutar damu da basu sanar damu da wuri ba.... Sun cutar damu cuta mafi muni...."

Sai lokacin Sabi'u dake satan kallonsu ya k'araso a hankali, daga gefe ya d'an durk'usa kai a k'asa ya soma fad'in "Baba kuyi hak'uri, wllhi ni tun lokacin da abun ya faru naso na sanar daku saidai marigayi bai sanar dani ainihin garinsa ba kawai dai ya sanar dani mahaifansa na raye kuma yanada iyali a gida wacce mahaifansa suka aura masa, tun bayan rasuwarsa nake neman garin da kuke sai kwanan Allah yasa na dace kuma ban huta ba har saida na iso na sanar daku, kuyi hak'uri da ace nasan garinku tuntuni da nazo na sanar daku... Kuyi hak'uri Baba tabbas da zafi ace d'anka ya rasu baka sani ba balle ka masa addu'a.."

Lokaci guda Baffah ya sami kansa da k'uncin irin abubuwan da yayiwa Ahidjo a baya, wannan itace rayuwar duniya, wannan itace misalin rayuwar duniya, tabbas duk sonka da ita duk k'ink'a da ita wata rana dole a wayi gari babu kai, hak'i ka zauna da kowa da alkhairi shine ribar zaman duniya, ina amfanin d'aukan gaba da d'an uwanka, ina amfanin rashin yafiya, hak'ika shi d'an Adam ajizi ne mai kuskure ne mahaliccinmu ma muna masa laifi kuma ya yafe mana, idan da ace babu yafiya tabbas da duniyar tuni an kifite... Mu zama masu yawan yafiya a tsakanin Al'umma....

Wasu hawaye masu d'umi suka zubo wa Baffah, inama zaiga Ahidjo a idanunsa a halin yanzu, da ya sanar dashi cewa ya yafesa duniya da lahira, Allah sarki saidai hakan bazai samu ba, Ahidjo ya tafi, ya tafi ya barsu tafiya ta har abada..... A hankali Baffah ya furta "Ubangiji ya sadaka da rahamarsa Aliyu....."

Lokaci guda Innah ta kuma kamo bakin mayafinta tana share idanunta da tuni suka mata wani irin nauyi, tabbas Allah shi ya halicci mutuwa a tsakanin bayinsa, kuma sai ya sanya wa zuciya dangana da mantuwa bacin haka batajin rashin tilon d'anta zai tab'a gushewa daga cikin zuciyarta, yau koda Aliyu na gabansu bazai wuce kwanakin da mahaliccinsa ya d'ibar masa ba, wannan itace rayuwar duniya ba komai bace face wata tafiya ce da mukeyi gaba d'aya wanda duk runtsi duk daren dad'ewa zamu isa destination guda d'aya wato kabarinka, Allah kasa muyi k'arshe mai kyau.... Ameen..!


Sabi'u sai ka rantse iyakacin gaskiyarsa kenan, gaba d'aya ya kasa zaune ya kasa tsaye jiran likita yake ya fito ya sanar dasu condition d'in Deejoh, haka nan tunda yayi tozali da Deejoh yaji bai tab'a son wata mace a duniya irinta ba, bazaiso Nana H tasan da matar Ahidjo ba balle tayi tunanin cutar da ita, yayi ma kansa sha'awar yarinya kuma yaci burin mallakanta da zaran ta gama takaban Ahidjo, kuma idan yayi haka shine ya rik'i amanar Ahidjo tinda yasan yanda Ahidjo ke son inganta rayuwar Deejoh, shi kad'ai ne zai iya bata rayuwa mai inganci a wannan k'ank'anin shekaru da take dashi.... Lokaci guda ya fuzar da iska had'i da gyara tsayuwarsa a dai-dai nan likita ya fito yana tambayar wad'anda suka kawo Deejoh...

Cikin sauri Sabi'u ya k'arasa yana fad'in "Dr ta farfad'o...."

Kallonsa da kyau likita yayi kana yace "Kaine ka kawo yarinyar nan...?"

Kafin ya sami zarafin amsawa Baffah da Innah suka k'araso suna fad'in "Mune iyayenta likita..."

Jinjina kai Dr yayi yana mai kai dubansa garesu kana yace "Kuna iya biyoni ofishi na...." Ya k'arashe yana mai tunk'aran ofishin nasa yayinda su Baffah suka take masa baya cikin sauri...

Badon Sabi'u yaso ba ya dakata daga waje yana addu'an Allah yasa lafiya take....

Likita ya dubi Innah da Baffah kana yace "Kune iyayenta...?"


Jinjina kai Baffah ya kumayi a karo na biyu kana yace "Mune iyayenta likita ka sanar damu meke faruwa da ita..." Cikeda k'arfin hali yayi maganar domin Innah kam ta gaza cewa komai har lokacin hawaye basu daina bin k'uncinta ba


Dr ya d'an gyara zamansa yana tunanin yanda iyayen wannan yarinya zasu d'auki batun da zai sanar dasu, amma sanar dasu d'in ya zama dole....

"Likita ka sanar damu idan ita d'inma mutuwar tayi..." Tayi maganar tsananin tashin hankali na kuma wanzuwa a fuskarta

Girgiza kai likita yayi kana yace "Bata mutu ba hasalima zuwa wannan lokacin ina tunanin ta farka... Amma yaya akayi kukayi sakaci da rayuwar d'iyarku haka, na tabbata d'iyarku bazata haura shekaru goma shabiyar ba.... Shin ku wasu irin iyaye ne masu sakaci... Da yawan iyaye son abin duniya kansa su kasa saka idanu a rayuwar d'iyoyinsu musamman 'yan mata irin haka wanda nasan shakka babu wasu a irin tallata tallacen nan suke had'uwa da tsautsayi irin wannan, sai kaga yara k'anana amma tuni an lalatasu iyayen basu sani ba, sam a kamanninku bakuyi kama da mutanen banza ba..."

Baffah ne ya dakatar dashi da fad'in "Kaga likita kar ka nemi kaci mana zarafi, da ace kasan tashin hankalin da muke ciki sam da baka zauna mana wad'annan maganganun ba.. Ka sanar damu yaya lafiyar d'iyarmu idan kuma bakayi ka bamu ita mu tafi..."

Girgiza kai Dr yayi kana yace "Ai kaga irin halin taku, toh abinda zan sanar daku a yanzu sai yafi jefaku cikin tashin hankali, ko kunsan cewa d'iyarku juna biyu ke gareta.... Toh idan baku sani ba Yarinyar ku tana d'auke da juna biyu na tsawon satittika biyar......"

Daga Innah har Baffah kallo sukabi likitan dashi kafin Innah ta furta "Juna biyu likita...." Dr ya jinjina kai..


Wani sabon tausayin Deejoh ne ya sauk'ar masu, ga kuma rashin Ahidjo, Allah sarki ashe rabo ne yasa aka masa wannan auren, tabbas wannan shi ake kira rabo....

Kukan Innah ya k'aru Baffah ma cikin k'arfin hali yake lallashinta...

Dr ya girgiza kai kurum kana yace "Ba kuka zakuyi ba abinda ya faru ya riga ya faru, yanzu abinda zakuyi shine kuyi k'ok'arin kamo wanda ya mata wannan aika-aika ku maka sa a kotu kuma kada kuyi yunk'urin kashe....."

Baikai aya ba Innah cikin tsananin fad'a hawaye basu daina fita daga idanunta ba ta katse sa da fad'in "Kada ka kuskura ka sheganta min jika, abinda ke cikin Deejoh D'ah ne na halak, da ubansa dukda zai rayu baisan mahaifinsa ba amma d'an sunnah ne kar ka sake cewa za'a kashe shi.. Insha Allahu sai ya rayu a doron k'asa...." Ta k'arashe cikin tsananin kuka tana nunawa Likitan yatsa...


Baki sake likita ke dubansu yayinda Baffah yaci gaba da fad'in "Bilkisu muyi hak'uri haka Allah ya k'addaro mana...."

Innah cikin kuka take ci gaba da fad'in "Malam Ahidjo ya tafi ashe ya bar mana ajiya jikin matarsa,..." Ta juyo tana watsa wa likitan mugun kallo take fad'in "Bazan bar wannan mutumin ya sheganta min jika mai cikakken asali ba, wanda k'ila ma ya fisa asali...."

Baffah yayi saurin rik'ota yana fad'in " Kiyi hak'uri Bilkisu.... Kiyiwa Aliyu addu'a shine kawai yake buk'ata daga garemu a halin yanzu..."

Sai sannan likitan ya gane meke faruwa, take nauyinsu Baffah ya kamasu, cikin sauri ya shiga basu baki yana fad'in baisan haka abin yake ba suyi masa hak'uri, lokaci guda ya buk'aci ya rakasu d'akin da Deejoh take, suna isa kuwa suka tadda ta farka amma bata daina kuka tana ambaton Yaya Ahidjonta ba...

Innah na hangota taji wasu sabbin hawaye suna ziyartan idanunta cikin sauri ta k'arasa ta rungumeta....

Cikin kuka Deejoh ke fad'in "Innah wllhi Allah k'arya ne wllhi Yaya Ahidjo yana nan da rai, yace kuma zaizo ya d'aukeni mu tafi... Innah ni nasan bai mutu ba... Kawai k'arya mutumin nan keyi... Baffah da Allah kar ku yarda dashi wllhi k'arya ne Yaya Ahidjo bai mutu ba..." Ta k'arashe cikin tsananin kuka tana mai kai dubanta ga Baffan wanda ke rakub'e daga gefe tausayin yarinyar da abinda ke cikinta ya hanasa tab'uka komai sai karaya da zuciyarsa ta kuma yi... .

Cikeda tausayawa Baffah ke dubanta kana yace "Khadija kiyi hak'uri mai rai duk mamaci ne, shi kuma Aliyu haka Allah ya k'addara irin mutuwar da zaiyi kenan bazamuga gawarsa ba balle mu sallata, kiyi hak'uri kiyi masa addu'a Ubangijinmu yafimu k'aunarsa ya d'aukesa daga garemu, kiyi hak'uri kinga a halin yanzu bakida ishesshen lafiya..."

Girgiza kai take tana duban Baffah take fad'in "Baffah kaima ka yarda.. Baffah fah Allah wllhi wllhi k'arya ne, idan gaskiya ne ai da sun kawo mana gawarsa, nidai Allah Baffah nasan mijina na raye, zai dawo kaman yanda ya min alk'awari..." Ta k'arashe tana mai fad'awa jikin Innah...

Innah ma kasa juriyar tayi dole ta rungume Deejoh sukayita kukan su mai tsananin ban tausayi...


Sabi'u dake rakub'e daga bakin k'ofa sai binsu data mujiya yake, idanunsa kan Deejoh dake kuka wanda yake ji kaman ya rungumeta ya bata kafad'unsa tayi kuka bisa....

Likita ya sanar dasu tana buk'atan hutu sabida jaririn cikin dake jikinta sannan idan son samu a daina barinta tana shiga damuwa sabida kada yayi affecting cikin... Sabi'u shi yayi komai na asibitin ya kuma maidasu gida cikin motar sa, sosai Baffah yayita masa godiya yana tambayarsa yaushe zai tafi..


Sabi'u ya d'an gyara tsugunonsa kana yace "Baba dama zanso mu tafi can Abuja taredaku sabida ayi maganar rabon gadon Aliyu tinda nada wata iyali acan... Amma duba da yanayi na rashin lafiya da iyalinsa na nan gida ke ciki sai nakega bai kamata ta tunk'ari wancan matar tasa ba sabida mace ce mai tsananin kishi, a gaskiya Baba ina tsoron zata iya yiwa Deejoh wani abin musamman duba da yanda auren ya kasance bata san da ita ba...."

Bai kai aya ba Baffah ya girgiza kai kana yace "Allah shi yace a raba gado koma nace ya riga ya raba abundantly amma bacin haka sai na ce maka mu bamu buk'atan wani abu ya had'amu da wad'ancan mutanen balle har mu kuma jefa Deejoh da abinda ke cikinta cikin had'ari, mu wllhi dukiya sam bata gabanmu, mu mutane ne masu wadatan zuci, Alhamdulillahi... Sannan a halin yanzu babu zancen rabon gado sai an jira Khadijatu ta haife abinda ke cikinta an gani mace ne ko kuwa namiji ne kaman yanda shari'a ya tanadar... A bar wannan maganar a halin yanzu domin kuwa sam babu shi...."

Sabi'u da zufa ta shiga k'eto masa jinjina kai na dole ya shiga yi don bai

Please Login or Register in order to submit comment