Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi Sallama ta shiga. Hajiya Halima dake zaune ta amsa. "Ummi ki ban kudi inji Abba" Ameesha ta fada.

Girgiza kai Ummi ta yi tace "Allah ya shirya min ke Ameesha, wai yaushe zaki hankali ne?" Ta karasa maganar tana mika mata kudin.

Amsa tayi tare da yin waje. tana zuwa ta aje masa kudin a kusa da shi. Cikin muryar kuka ta ce " Abba ba na son kudin nan"

Hankalin sa ya tashi da ganin hawayen tilon diyarsa mace, yace "Uwata me ya faru?"

Jikinsa har wani rawa yake. "Ba Ummi bace bayan ta ban kudin tace Wai Allah ya shirya ni.........."



*_Yawan Comment dinku zai sa ni cigaba..._*



*_Yar Mutan Rano._*
[10/8, 8:00 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)*


*SANGARTA*


©
*ZULAIHEART RANO*



*2*



Zaro ido ya yi yace "Me Hajiya take nufi da wannan kalmar? Tana nufin ke ba shiryayya bace?" a zafafe yake maganar.

"To Nima fa Abba abin da ya ban haushi kenan, ita Ummi kullum bata son taga ina farin ciki, sai tayi dalilin sani cikin damuwa"

Ameesha tayi maganar tana cigaba da matsar kwalla. "Yi hakuri yar Abba tashi kije zan sami Hajiyar yanzu, sai ta fada min dalilin ce maki hakan, oya je ki wanke fuskarki"

Ummi ce ta fito daga bedroom dinta, ganin Ameesha na kuka yasa ta mamaki tace "ke lafiyar ki kuwa?"

"Wani irin tambaya ce haka Hajiya, kefa kika sa Yarinyar nan kuka, amma yanzu kina tambayar ta" cikin fad'a ya kara sa maganar.

Dan murmushi Ummi tayi tace "Haba Alhaji ka daina saurin daukar fushi a kan lamarin Ameesha, in banda kaima kana biye mata, har yaushe zata ce na sata kuka ka yadda? Ko da yake tunda *Sangarta* na damunta, dole tayi kuka don nace Allah ya shirya min ita"

"Yawwa kinji ba, me kalmar Allah ya shirya ta yake nufi?Gaskiya ni ban son haka, duk mai son zaman lafiya to karya tab'a min uwata."ya yi maganar cikin fushi.

Jinjina kai Ummi tayi tace"Allah ya baka hakuri Alhaji, amma maganar neman shirin Ameesha wajen Allah yanzu na fara fada" tana gama fadi haka ta yi kicin.

"'Yar Abba tashi kije ki wanke fuskarki, sai kizo ki tafi ko?"

"Nifa Abba kamar na fasa zuwa"

Ameesha tayi maganar tana cigaba da latsa wayar ta. Don dama duk maganar da Abbanta da Umminta suke tana jin su, ko kallon su bata yi ba har suka gama.

"Haba yar'lele mai zaisa ki fasa, tashi maza kije ko kina son na kaiki da kaina ne?"

"A'a Abba da kaina zanje."

"Ok wane motar zaki fita da shi?"

"Abba sabuwar motar ka zan hau yau, wannan wanda aka kawo last week, *Bugatti vogron* dinka" ta bashi amsa tana hawa down step.

Fada da fara'ar sa ya yi yace "To maza ki fito kizo ki dauko key, sai ki tafi yar Abbanta." ya karasa maganar yana girgiza kai.

Da sallama ya shigo falon tare da tsugunawa, ya soma gaida mahaifin nashi. Fuska sake ya amsa da "Lafiya Lau Jaheed ya ka tashi"

dukar da kai kasa ya yi yana amsawa. Hajiya Halima ce ta fito daga kicin fuska dauke da fara'a tace"Lallai Jaheed yau Kayi nannauyan bacci, har sha daya kafin ka fito?"

Dan murmushi ya yi yace "Wallahi Ummi jiya da zazzabi na Kwana yanzu ma da kyar na tashi"

"ayya Sannu Allah ya kawo sauki, tashi kayi break sai kasha magani, shi yasa banga ka fito da wuri ba, gashi yau kuna da aiki." cikin tausayawa dan nata take maganar.

"Abba na dauko key din Sai na dawo." muryan Ameesha ya cika falon.

"OK yar Abba a dawo lafiya"

"Ke ina zaki yanzu a wannan lokacin har da daukan mota?"

Jaheed ya tambaya ransa a b'ace"Yaya saloon zanje fa daga nan zan biya nayi shopping"

cikin shagwaba ta yi maganar. Harara Alhaji Tahir ya zabga masa yace"Kai nikam ban son fi'ili ina ruwan ka da inda zata je, kawai ka sawa Yarinya ido sai faman tambayar ta kakeyi"

"Yi hakuri Abba bada wani manufa nayi Mata tambayar ba."

"Kudai kuka sani kuma, amma uwata da shen Allah ne."

Ummi ta jinjina kai cikin ranta tace"Lallai lamarin Alhaji kara gaba yake"

Ameesha ta matsa inda Abban ta yake ta manna masa kiss a kumatu tace"Abbana ina sonka sosai, sai na dawo."

murmushi ya saki yace "A dawo lafiya uwata Allah ya tsare, ki rika kula don kin San akwai Wanda suka sa maki ido."

"Insha Allah Abba." ta yi maganar tana fita daga falon.

Mamaki sosai ya rufe Ummi, da irin maganar Alhaji Tahir din, jaheed ya bude baki zayyi magana suka hada ido da Ummi, yana ganin kallon da Ummin tayi masa ya gane nufinta, don haka sai ya yi shiru. Ameesha kam tayi tafiyar ta.



*ASALIN LABARIN*



AMEESHA diya ce wajen Alhaji Tahir da Hajiya Halima,Yarinya ce yar gata wajen mahaifinta, Alhaji Tahir haifaffan garin kano ne, cikin karamar hukumar bicci, yana da matar aure d'aya da ya'yan sa biyar,Hajiya Halima itace matar sa, Kuma ita ce ta haifa masa duk ya'yan sa, suna zaune cikin garin kano a unguwar Tudun Yola dan kasuwa ne babba Allah ya bashi tarin dukiya. Don yana da manya manya shaguna a kantin Kwari da singa duk dake garin kano,Babban dansa shine Muh'd Mujahideen, wanda suke kira Jaheed, sai AbdulMalik, Umar Faruk, sai Aliyu Haidar, sai Auta Maryam Wacce suke kira Ameesha, Allah ya daurawa Alhaji Tahir son Ameesha, yana kaunar ta sosai don tace Sunan mahaifiyar sa, Kuma ta kasance ita daya ce ya mace da Allah ya azurta shi da ita, Baya kaunar bacin ranta, lokacin da take karama duk rashin kunyar da tayi maka, baka isa ko kallon banza Kayi mata ba, balle akai ga maganar duka ko zagi, to a ranar ba zaman lafiya don an tab'a masa 'yar lelensa, haka yasha zuwa makarantar akan an daketa ya zabgawa malaman rashin Mutunci, Ameesha tun tana karama abin da tayi niyya shi takeyi, babu daman wani ya yi magana sai Alhaji Tahir ya soma, yana cewa an sawa yarsa ido, Koda kuwa Ummi ce da yayyin ta sukai magana Kan abin da take haka yake rufe ido ya yi ta ruwan masifa, *Sangarta* kala kala Ameesha keyi, babu mai magana. wannan Abu yana bawa Hajiya Halima haushi, sai dai bata da yadda zatayi da ya wuce Addu'a. Har zuwa lokacin da ta girman ta bata rage ko Abu daya daga Halayyar ta ba, sai ma rashin Mutuncin ta dake karuwa a kullu yaumin.

***

Fitowar ta kenan daga cikin Shahad store, inda tayo shopping din duk wani Abu da take so, idonta sanye da wani kwamemen glass, Kallo daya zaka yi mata kasan babu mutunci a tattare da ita. Musamman yadda take wani irin taku cikin isa da tak'ama. Hannu tasa tare da zame glass din idonta, tana kallon motar da aka faka kusa da ta ta motar. Jinjina kai ta yi tana mamakin wanda ya faka motar don ya tare mata hanyar fita, tsayawa ta yi jikin motar tana jiran ganin fitowar ko ma waye mai motar, don ta nuna masa ba'a mata haka, Yau zata nuna ma duk Wanda ya yi mata wannan aikin rashin Mutunci. Tafiya yake cikin nutsuwa, wayar sa makale a kunnen sa, da gani kasan waya yake yi, isa ya yi wajen motar sa tare da budewa, zai shiga ciki kenan maganarta ta hana shi shiga.

"Kai Malam me kake ji dashi da har zakayi min crossing din hanya, sannan kazo ka wuce ba tare da ka ban hakuri ba?"

Dago da kyakykyawan fuskar sa ya yi, ya sauke idon sa Kan fuskar ta, take ya ji wani yanayi ya shige sa wanda bai tab'a jin sa ba. Kallon beauty face din ta yake babu kakkautawa. Ran Ameesha ya baci matukar da irin kallon da yake mata, sannan ta yi magana bai amsa mata ba, don haka sai ta daga hannunta tare da kaiwa fuskarsa mari. Saurin gocewa ya yi bata same shiba, ransa ne ya baci har Shima bai San Sanda ya daga hannu tare da gwaura mata wani lafiyayyen mari. cikin sanyanyar murya yace" Ke dabba, mahaukaciyar ina ce da har zaki daga hannu da sunan marina?"

Bude ido ta yi cike da mamakin marin da ya mata, a iya saninta rabon da wani ya mareta tun tana primary 3, Shima malamin Sanadin dukan da ya mata ya bar koyarwa a school din, cikin sauri ta zaro wayar ta tare da dailing number din Abbanta cikin kuka ta soma zayyane masa abin da ya faru...... "


*_Yar mutan rano_*
[10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*3*

"Wa ye shi a Nigeria da har zai daga hannu ya mareki?"

Alhaji Taheer ya yi tambayar a zafafe.
Hawaye suka kuma zubo wa a idon Ameesha, don ba karamin shigar ta marin ya yi ba. Murya a sanyaye tace

"Abba badan ko wa bane hasalima wani kaskantaccen mutum ne, wanda ba shi da ko sisi, motar da yake hawa ko kyauta aka bani bazan iya hawanta ba."

"Maza dauko min number din motarsa, zanyi maganin kowaye."

Dago kan da Ameesha ta yi sai taga wayam babu motar mutumin, wani karin takaici ya rufeta, a zafafe tace

"Abba ya wuce ban san ma lokacin da ya wuce ba."

"Maza ki dawo gida, ko nazo na dauke ki ne? "

" No Abba ba sai kazo ba yanzu zan taho."
Ameesha ta yi maganar tana shiga motar, a ranta ta kudurta bata kuma zuwa *Sahad store* ba domin wajen ya zama mata wajen jin kunya.

Cikin gida kuwa Abba sai kai komo yake, yana ta jan tsaki, don hankalin sa ya tashi da jin maganar marin Ameesha, Hajiya Halima ta fito daga kicin tare da kallon mai gidan nata, cikin kulawa tace

"Alhaji lafiya kuwa?"

Tsaki yaja tare da hararan Hajiyar yace

"Yo ina fa lafiya, an samu wani dan iskan ya maran min yarinya a banza."

Mamaki ya kama Hajiyar tace

"Alhaji mari Ameesha aka mara kowa? "

" Inada wata 'yar ce bayan Uwata? Ya cigaba kinga Hajiya karki kuma 'bata min rai, dama fa na kula tun farko baki so fitan yarinyar nan ba, don haka burin ki ya cika tunda an wulakanta min ita a waje."

Girgiza kai Ummi ta yi tace

"Amma Alhaji kana bani mamaki, in ka fad'i wata maganar, ta ya zakace wai ina son a wulakanta Ameesha?kar fa ka mata ni na haifeta, kuma banki ace Ameesha tafi ko wace ya mace nutsuwa ba, na tabbata Ameesha rashin kunya ta yi wa duk wanda ya mareta, amma kai ba ka yi bincike ba, sai ka yanke hukunci ka daura laifi akan mutum, gaskiya haka ba kyau.

Daga mata hannu ya yi alamar ta yi masa shiru, dai dai da shigowar Ameesha, jikin Abba ta fad'a tare da sakin wani sabon kukan.

Bubbuga bayanta Abba ya soma alamar rarrashi "Yi hakuri uwata karki bar wannan ya dame ki, insha Allah zan dau mummunan mataki akan koma waye, shi duk randa Allah ya had'a mu."

"Da dai kabi komai a hankali zaifi, amma wannan maganar da kake ba shine dai dai ba."

Hajiya Halima ta yi maganar tana zama kan kujera.

"ke Ummi kinga kuwa irin wulakacin da ya min?kike cewa a bi komai a hankali, wallahi Abba karka bi a hankali."

"To uwar rashin kunya, duk wannan abin da kuke yi wata rana sai kunyi nadama kuma ma mara amfani."

"Nifa wallahi Hajiya ban son irin maganar da kike yi, ke kullum baki mana fatan Alhairi sai mugun baki, to ta Allah ba ta kiba."

"Gaskiya ce baku so ni kuma dole sai na fad'a."

"Ki rike gaskiyar ki bamu so din"

"Yawwa Abba ina son duk lokacin da kuka had'ui, karka saurara masa ka nuna masa ni din yar gatan ka ce."

"An gama Uwata maza jeki daki ki dan watsa ruwa ko zakiji sanyi."

"To Abba sai nayi sallah zan fito, don a hanyata ta dawowa naji an kira."

"A fito lafiya diyar Abba."

Murmushi Ummin Ameesha ta yi, don wannan halin na Ameesha kadai ke burgeta, duk abin da take da zaran taji an kira sallah, bata bari lokaci ya wuce.

Kusa da Ummin ta matsa tace

"Ummi yau me kika dafa ne?"

"Tuwon shinkafa ne miyar wake."

"Wow Ummi kinyi abin da nake son ci."

Da fa kanta Ummin ta yi tace

"To ga yacan a dining komai is ready."

"Ok bari na fito." Ameesha tayi maganar yayin da take taka matakalar benan don hayewa sama.

Farin ciki ne ya kama Alhaji Taheer mahaifin Ameesha ganin yadda suka yi magana cikin walwala da farin ciki.

Shigarta bedroom din ke da wuya sai ta wurgar da Jakarta dake hannunta (hand bag) tare da cire gyalen da ta yafa, Kai tsaye toilet ta nufa ta sakarwa kanta ruwan sanyi, kila ko ta samu sassaucin abin da take ji a zuciyar ta, ta jima sosai sannan ta fito bayan ta dauro alwala, zanen da take sallah ta dauko tare da hijjab dinta sannan ta tayar da sallar.

Bayan ta idar da sallar, ta shirya cikin wani wando da riga wanda suka mata matukar kyau, wandon pencil ne kalar pink, rigar kuma body top ne kalar white, sun amshi jikinta, ta yi pakin kanta da ribbon kalar wandon ta, tsaf ta feshe jikin ta da turaruka masu kamshi.

Masha Allah, Gaskiya Allah ya yi halitta don Ameesha kam babu inda Allah ya rage ta, ta fannin halatta kyakkyawa ce wato (First Class) a jin farko, gata doguwa, bata da Kiba ko kadan, amma fa akwai ta da hips and braest, komai cif.

********************************

Cikin kwarewa yake driven motar, fuskar sa dauke da wani special smile, haka kawai in ya tuna Ameesha yake jin zuciyar sa fes, sai dai wani bangare na zuciyar sa tana fama da rad'ad'i tare da dana sanin marin da ya mata. A fili ya furta

"Shi is very beautiful girl, duk wanda ya samu wannan matsayin mata lallai ya more."

Wayarsa ce ta soma ruri a lamar tana neman agaji, da sauri ya dauki wayar ganin mai kiran yasa shi sakin murmushi, picking ya yi tare da karawa a kunne

"Hello Allah hokke sabbugo Nannena, mid'o a nyalli jam, noi sare? " (" Allah ya baki tsawon rai Nannena, fatan kina lafiya ya gida?)

" Jamni tawon Asmad mid'o yela wala billare fere kam.... " (" lafiya Lau Asmad fatan kaima baka da matsala?)

" A'a Nanne wala ko d'ume, jottama mid'o lawol Wartugo sare." ("a'a Nanne babu matsalar komai, yanzu haka ina hanyata ta dawowa gida")

"Allah wadde jam amma a hakkilina lawol anani naa barkantejo.... " (" Allah ya dawo min da kai lafiya Amma ka kula da kyau kaji dan Albarka.")

Murmushi ya yi lokacin da ya kammala waya da mahaifiyar nasa,yana jin farin cikin yadda Nannen shi ke bashi kula, cikin mintina k'alilan ya isa unguwar su, bakin wani makeken get naga ya nufa, hon ya yi cikin sauri mai gadin ya wangale masa get din, wow masha Allah wannan rantsatsen gida haka, gida ne babba ginin zamani, Kai da ganin gidan kasan an kashi kudi, da ka shigo gidan da dakin maigadi zaka soma karo, gefen dama kuma, wani dan dakine aka gina da alama na generator ne, sai wasu flowers da aka daddasa masu kyau, su suka kuma sa gidan ya had'u, gefe guda kuma parking space ne, motoci jere a ciki masu dan banzan kyau.

Sai mutum yayi dan tafiya kafin yasa da kansa da ainahin cikin gidan.

A parking space ya faka motar sa, sannan ya fito tare da d'aukan laidar da ya yi sayayya a Shahad din, kofar babban falon gidan ya shiga bakin sa dauke da sallama, wata kyakkyawan macece wacce bazata wuce shekaru 40 zuwa 42 zaune cikin hadadden falon, babban falo ne wanda aka kawata sa da wasu manya manyan kujeru na alfarma, ga wani carpet mai shegen kyau wanda ya fito da ainahin kyaun falon, kalarsa da kujerun d'aya, wato brown color, haka ma labulen, babban plasma TV ne manne a bangon falon.

Kallo daya zakiyi wa matar kasan bafulatana ce, fara ce fuskar ta kunshe da annuri, macece mai riko da Addini don hannunta rike yake da wani littafin Addu'oi tana karantawa, jin sallamar dan nata yasa tayi saurin d'agowa fuska d'auke da murmushi ta amsa masa sallamar.

Inda take zaune ya 'karasa, zama ya yi kusa da kafarta tare da lank'washe 'kafarsa, ya soma gaidata, shafa kansa tayi tace

"Ja66ama Asmad, awartii Jam... " (barka da zuwa Asmad ka dawo lafiya?)

" Jamni tawon Nanne, sai welo minanata... " (lafiya Lau Nanne sai dai ina jin matukar yunwa).

" Ta damu mitimmini nyamdu.... "(karka damu akwai abinci, ban dade da gamawa ba.)

" Yawwa Nanne 6ewaddina aam sudu aam, hiddeko mi wurta yiwugo..." (Yawwa Nanne a kawo min bedroom dina yanzu, kafin na fito wanka.)

"To ha ladidi waddine.... " (bari ladidi ta kawo maka.)

" A'a Nanne miyid'a 6ingel d'o nastimi sudu aam, toi aneesa ko'o huwata, hokku moo ne o wadda..." ( "a'a Nanne ban son wannan Yarinyar tana shigar min bedroom, ki dai Ba Aneesa ita aikin me takeyi?)

" To yahu hami hokka aneesa man waddine..." ("To jeka Aneesa zata kawo maka.")

"Yawwa Nanne hanju wad'i miyid'i Ma..." ("Yawwa Nanne shi yasa nake Kara sonki."

Asmad ya yi maganar yana Mika mata, d'aya daga cikin ledar da ya shigo da shi, amsa ta yi tare da sanya masa Albarka, shi kuma ya fita tare da nufa 'bangaren sa.


_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: [4/15, 4:00 PM] Zulaiha Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* *(NWA)*


*SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*

*Please fans kuyi hakuri anyi mistake a pagen ɗin jiya amma gashi yanzu na gyara da fatan zakuyi min afuwa,ku cigaba da bibiyar littafi*


*Nice dai Zulayheart Rano*

*4*

Asmad na wucewa Nanne ta soma 'kwalawa Aneesa kira, cikin sanyin murya ta amsa da

"Na' am Nanne ga ni"

Aneesa ta fada lokacin da ta isa wajen Nannen.

"Yawwa yi sauri ki hada wa Hammanki Asmad abinci, ki kai masa bangaren sa."

Murmushi ta saki jin Nanne ta ambaci Asmad.

"To Nanne."

Ta yi maganar tana nufa hanyar kicin din, cikin kankanin lokaci har ta shirya masa duk wani abu da suka dafa ta nufi, bangaren da shi, a k'ofar falon ta tsaya tana sallama, Asmad dake fitowa daga toilet ya amsa, tare da buɗe mata ya dan matsa ta ida shiga bedroom ɗin.

Kallon sa ta yi cikin wani irin shauki, bayan ta aje tire ɗin tace

"Hamman Asmad Sannu da dawowa"

"Yawwa." ya amsa yana goge kanshi da karamin towel.

Tsayawa ta yi tana kallon sa, a rayuwarta tana mugun son Asmad sai dai tasan, ta makaro don bata cikin irin matan da Asmad yake so, domin duk wani hanya da zata bi don shawo hankalinsa ta yi amma a banza.

"Ke tunanin me kike yi da bazaki wuce ba, kin wani sani gaba kina kallo kamar na zamar maki bak'o?"

Dan murmushi ta yi ta ce
"Lah yi hakuri Hamman, dama so nake nace maka ina son zuwa wajen saloon."

"Anjima ki amsa kudi a wajen Nanne, jeki ina son gama shiryawa."

Jiki a sanyaye Aneesa ta bar ɗakin, ba don ranta ya so ba. Aneesa 'yar k'anwar Nanne ce ta zo daga Adamawa, da yake dama duk sanda ta samu hutun school to anan kano gidan su Asmad take yin hutun ta. Kamar ko yaushe wannan karon ma hutu ta samu, Aneesa budurwa ce kyakkyawar gaske, tana da dan jiki sai dai bata da tsawo, shekarun ta Ashirin da haihuwa, a fuska mutumiyar kirki ce sak, amma akwai ɓoyayyen hali a tattare da ita, tun tasowanta take son Asmad din, sai dai shi bata tata yake ba.


Falon Nanne ta koma, a inda ta barta na ta sameta, kasa tayi da murya tace

"Nanne inji Hamman wai ki bani kudi anjima zani saloon."

"Ba dai yau ba, sai gobe don yanzu kam yamma ta soma yi."

"To Nanne." Aneesa ta yi maganar cikin sanyi.

cikin kwanciyar hankali, Asmad ya gama shirin sa, sosai ya yi kyau, domin Asmad kyakkyawan bafulatanin garin Adamawa ne.

*Asmad Abubakar ɗan Fullo* shi ne cikakken sunan sa, mahaifinsa Alhaji Abubakar da mahaiyarsa Hajiya Binta duk haifaffun garin Adamawa ne, kasuwan ci ya kawo mahaifinsa kano.

Allah ya ba Alhaji Abubakar dukiya, sosai ɗa ɗaya Allah ya basu shine Asmad, ya taso cikin gata ta ko wane fanni, sai dai ya samu ingantaciyar tarbiya, duk da kasancewar sa shi ɗaya Allah ya ba iyayen sa, akwai shi da nutsuwa da hankali, shekaran sa ashirin da takwas da haihuwa,

Nanne takasance mece ce mai hankali da tunani, ko da yaushe fuskar ta a sake take, mace ce masaniyar Alkur'ani mai girma, Kuma mai aiki da shi, shi yasa sam bata yadda aka ɓata Asmad da wasu munanan d'abi'u ba, amma fa dai-dai da minti ɗaya in ka zauna da su zaka fahimci tsananin son da Nanne ke masa, don bata iya ɓoye son Asmad a gaban kowa, duk da kasance warta bafulatana.

Asmad Abubakar ɗan Fullo, babban likita ne wanda duk faɗin garin kano aka san da shi, kawarrene a kan aikin sa, yana aiki a babban asbitin kano.

**********************************
Juyi tayi akan makaɗeɗan gadon ta, tare da kai hannu ta dauki wayar ta dake neman a gaji, idonta fal da bacci ta dubi screen din sunan wacce ta gani ne yasata ɗaukar wayar tare karawa a kunne

"Hello k'awata." Ameesha ta yi maganar tana lumshe ido

Daga ɗaya ɓangaren a ka amsa

"Meesha kina ina ne haka? gani a hospital, tun dazun kin san Dr ɗin da aka ce mana zai zo yi mana practical 8:30 zai shigo lab gashi yanzu 8:20."

Ya mutsa baki Ameesha tayi, kamar wacce ke mata maganar tana kusa da ita tace

"Kinsan Allah Meena na manta da maganar zuwan wani asbiti, yanzu haka da kikeji da gani cikin blanket nake, wayar ki ta tasheni daga bacci."

"Haba Meesha please ki tashi yanzu kiyi sauri ki shirya, kinsan fa irin mutanen nan basa tsayawa jira, kina gani hatta manyan malaman makarantar suna mugun bashi girma."

Tsaki taja tace "to uwar tsugudidi gani nan zuwa, tunda naga kina son takura ni."

Ta karasa maganar tana tashi zaune, Meena kam murmushi tayi, tana mamakin halin Meesha.

Toilet ta faɗa saida ta salle jikinta sannan ta fito, Kai tsaye gaban dress mirror ta nufa, inda kayan kwalliyar ta suke, zama ta yi ta tsantsara kwalliyar ta mai kyau, ta feshe jikinta da turaruka, shiryawa tayi cikin wani doguwar

Please Login or Register in order to submit comment