Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaga amarya, kai tsaye wajen sa ta nufa da zuwa bata jira komai ba tasa hannu tare da zare laptop din, ta wani narke fuska kamar za ta yi kuka ta ce

" Haba Hamma aikin me kake ta yi ne har yanzu, ya ci fa a ce kana samun hutu"

Kallon ta ya yi tare da ɗan sakin murmushi ya ce

"Ban da abin ki ina hutu a wajen Dr? Ke dai kawai kin rasa abin korafi, yanzu ma tashi zan yi in shiga asibiti don duba petient ɗina."

Saurin ɓata rai ta yi ta ce

"Haba dai tun yanzu zaka soma fita, ina laifin ka yi one week a gida?"

"Ba zai yiwu ba ne Anee da na yi hakan, yanzu dai tashi muje ki haɗa min ruwan wanka,in yi shaf shaf."

Ba don ranta ya so ba ta mik'e, shi kuma ya saki murmushi kawai ya kashe laptop din.cikin sauri sauri ya kammala da shiryawa, sam Aneesa ta ki saki rai ita a dole kar ya fita.

A haka ta rako shi wajen motarsa

" Please Hamma kar ka daɗe."

" Ba zan daɗe ba My Anee."
Ya faɗa cikin tabbatar da abin da ke ransa.

" Allah ya tsare hanya ya dawo da kai lafiya."

Ta faɗa tana rufe masa kofar motar

"Allah ya sa" shi ma ya faɗa yana ba motar wuta.


**********************************

"Najeeb! Alhaji Taheer ya kira sunan sa cikin murya ta nutsuwa.

Najeeb da ke zaune gaban Abban Ameesha ya amsa cikin ladabi.

"Kasan abin da yasa na kira ka?"

Alhaji Taheer ya tambaya.

Girgiza kai ya yi ta re da faɗin

"a'a Abba."

" Yawwa to akan maganar ka da Auta ne, shin da gaske ka ke sonta ko kuwa?"

Dukar da kai ya yi , cikin sanyin murya ya ce

" Eh Abba."

Murmushi ya saki ya ce

"Allah ya yi maka albarka, na gode sosai, insha Allah zamu zauna da Mahaifin ka domin tattauna maganar, saboda bani son aja maganar."

"To Abba na gode."
Najeeb ya faɗa.

"Dama shi ne dalilin kiran tashi ka ta fi."

********* ******** ******* ******

Ko da Asmad ya fita kai tsaye gidan su Nenne ya nufa, don ya kwashi gaisuwa a babban falo ya same su, sallama ya yi su, su ka amsa masa cikin kulawa.

("Nenne a nyalli jam? Bobbo a nyalli jam?) "Nenne ina yini? Bobbo an yini lafiya? "

("Jam kolon Asmad noi Aneesa?")" Lafiya lau Asmad ya Aneesa? "

("O jamo kolon,owi mi hofnna mon.") " Tana lafiya, har ta ce a gaida ku. "

(" Min notii Allah wadbarka.") " Muna amsawa Allah ya yi Albarka. "

("Ameen Asmad noti.") " Amin." Asmad ya amsa

(" Wala damuwa fere Kam?) "Babu dai wata matsalar ko? "

(" Wala ko d'ume Bobbo,minastan noo asibiti on miwi hami yalta mihofna on") " Babu komai Bobbo, dama zan shiga asbiti ne na ce bari na biyo don na gaida ku. "

("To usoko Allah barkid'in ummu dillu de jam kam da alari kanko fere mako a accimo ha sare useni jogumo amana ta awada ko a wasmititta Yesu.") " To masha Allah tunda lafiya, ka tashi ka tafi kaga dai ita d'aya ka bari a gida, abin da dai nake kara jaddada maka shi ne ka rike amanar Yarinyar nan, kar ka yadda wani abu ya shiga tsakanin ku na sabani, har ya sa ka aikata dana sani. "

("Insha Allah mi mi hakkilan Bobbo.") " Insha Allah Bobbo zan kiyaye. "

("To Allah wallu") " To Allah ya taimaka. "

(O lari agogo jungo mako dendenta o ummii.) Agogon hannun sa ya kalla tare da mikewa.

(" Nenne minkam mi salan.")" Nenne nikam na ta fi. "

("Allah hoinu lawol a yaltan naa to ad'on qarya?") " Allah ya tsare hanya, zaka biyo ne in ka dawo? "

("Kai gonga miyaltata Nenne mi salan sare on.") " Kai gaskiya Nenne da kamar wuya, don ina tunanin gida zan wu ce. "

"(To Allah karu.") " To Allah ya tsare. "

("Nonnon Asmad wurti sare man odon der seyo.") Da haka Asmad ya fita a gidan cikin farin ciki da annashuwa.


Yana parking motarsa a parking space, ya fito nurse na Asibitin sai masa barka da zuwa suke tare da ta ya shi murnar aure, fuska a sake ya ke amsa masu har ya isa kusa da ofishin sa.

Yasa hannu zai buɗe kofar kenan ya hango ta, zuba mata ido ya yi cikin wani irin yanayi, sai ya ga ta rame ta ɗan kara tsawo, da yaga suna shirin haɗa ido sai ya yi saurin fuskewa

Wani irin daɗi ya ziyarci zuciyar Ameesha, ganin Dr yau a asibiti, ji ta yi duk wata damuwar ta ta ragu. Amma a zahiri sai ta kuma haɗa rai kamar zata ce wayyo Allah.

" Da gani ansan ango ka ke musamman yadda goshi ke kyalli."

Tayi maganar cikin zuciyarta, tare da saurin maida kwallar ta don kar ya gane .

"Barka da zuwa Dr."

Ameesha ta yi maganar a hankali, cikin nutsuwa.

Dan juyo da kai ya yi ya kalleta ya ce

" Yawwa ."

Bata ce komai ba sai ci gaba da tafiyar ta ta yi, har ta ɗan gota shi ya ce

" Ke ina son magana da ke?"

Juyowa ta yi tare da murguɗa baki ta ce

" Ba sunana ke ba Maryam Taheer sunana."

"Nice name." ya faɗa a zuciyar sa, amma a fili sai ya ce

"Oh! Ai ban ma san sunan ki ba, to Maryam ina neman ki."

Ya ida maganar ya na shiga ofis ɗin, ita ma Ameesha binsa ta yi, kujera ya nuna mata ya ce

"Zauna."

Ba musu ta zauna tare da duk'ar da kai k'asa.

Shi kuwa wasu file ya dauka yana dubawa, tsawon minti biyar babu wanda ya yi magana, ita Ameesha ci gaba da wasa da zoben hannun ta ta yi.

"Wai Maryam baki da labarin na yi aure ne?

Asmad ya yi maganar ya na ci gaba da abin da yake yi.

Wani mummunan faduwar gaba ya ziyarci Ameesha, da jin maganar sa duk da ta sani amma sai ta ji na yanzu ya fi ranar da ta soma jin maganar ta da hankali.

Amma sai ta yi saurin da kewa ta ce

"To kuma me hadina da auran ka?"

Ta yi maganar tana hararan sa.

"Oh! Ashe fa ba ruwan ki da aurena? Amma ai yana da kyau ko murna ki ta ya ni."

Wani kallo ta watsa masa wanda ya kasa fahimtar ma'anar sa.

Yau dai yana son ya ga shin Ameesha ta na sonsa, in tana sonsa zai tabbatar ,don haka sai ya tashi daga kujerarsa ya matsa inda ta ke, hannun ta ya rik'o ya ce

"Maryam me yasa ki ke min rashin kunya baki ganin girma na, kullum kallon tsana ki ke min?"

Juyar da kai ta yi murya na rawa ta ce

"Please Dr ka sakar min hannu, sauri na keyi fa Ummi na jirana."

"Zan barki amma sai kin bani amsar tambayar da na yi maki."

"Babu komai."

Ameesha ta ba shi amsa, dai dai da zubowar hawayen da ta e ɓoyewa, hankalinsa ya tashi da ganin hawayen Ameesha, don haka cikin sauri ya ce

" Iya sani na na taɓa marin ki a Sahad store, kuma shi ɗin ma wallahi ke ki ka jawo, domin kuwa in da ban mareki ba, to fa babu shakka ni zaki mara, amma ki yi hakuri ga fuska ta ki rama marin."

Maimakon hawayen su tsagaita sai k'ara tsiyaya suke, a kan fuskar ta tama kasa furta komai, don abin da ta ke son ji daga gare shi bai furta mata ba, duk da tasan da kamar wuya ta samu wannan tsadadden kalmar daga gare shi.

Asmad kuwa zuba mata ido ya yi yana kallon ikon Allah, zuwa can yasa hannu cikin aljihu ya cire hankacif na shi ta re da mika mata.

"Sorry Maryam ki bar kuka, ga shi ki share hawayen ki."

Ya kai karshen maganar yana mik'a mata.

Amsa tayi tare da goge hawayen da hankerchief ɗin da ya mika mata, sai ya kuma jan hannunta kamar dai wata karamar yarinya, zuwa kan doguwar kujerar da ke office din, ya zaunar da ita sannan shi ma ya zama .

Sanyaya murya ya yi ya ce...

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*

*Alhamdulillah Ina godiya da Allah ya kawo mu wannan lokaci, ina son in dakata da typing wannan littafin har sai Allah ya kaimu bayan sallah lafiya, ina wa ɗauka cin musulmai murnar zuwan wannan wata mai alfarma Allah ya sada mu da Alhairin da ke ciki Ubangiji ka bamu rabauta da falalar da ke wannan wata na Ramadan*

_*Har lau dai korafi baya karewa? To duk kuyi hakuri Yar Mutan Rano tana kara ce wa kuyi hakuri ku kara akan na da, insha Allah bayan sallah ba za ku yi korafin rashin typing ba*_ i heart you irin totallyn ɗin nan😍😍


*16*
Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, tare da zubawa Ameesha ido cikin wani irin yanayin da shi kaɗai ke gane wa, cikin taushin murya ya ce

"Magana ta tasa ki kuka?"

Girgiza kai ta yi , ba tare da ta ce komai ba.

"No Maryam in muna magana ki rika buɗe baki Please."

"Ni fa Dr ba maganar ka ta sani kuka ba." A shagwaɓe ta karasa maganar.

Ji ya yi ta bala'in burgeshi,yana ɗaya daga cikin abin da yasa yake sonta kenan.

"To me ya saki kuka in ba maganar ba, na ce baki min Allah ya sanya Alhairin Aure na ba, sai na ga kin fara kuka ko?"

Harara ta watsa masa ta ce

"Ni fa kaina ke ciwo shi ne kawai."

"Hmm Maryam kenan kina da saurin daukar zafi, nifa banga abin tada hankali ba cikin abin nan, in ki ka bi a hankali to komai zai ta fi yadda ki ke mafarkin samu."

Ya yi maganar ta re da kashe mata ido ɗaya.

Saurin ɗago da kai ta yi tana kallon sa, tare da mamakin maganar da ya faɗa "kenan ya san tana sonsa?" Ta yi saurin kawar da tunanin don ta san ba haka ya ke nufi ba.

Mik'ewa ta yi tare da ɗaukar jakarta, ta kuma kallon kyakkyawar fuskasa ta ce

"Dr ni kam zan wu ce don yamma na yi."

Wani tsadadden murmushi ya bata, wanda ya kara wa fuskarsa kyau ya ce

"To Princess sai yaushe kenan?"

"Gobe school zan shiga zuwa sai jibi."

"Ok Allah ya kaimu, mu je na saukeki ko kin zo da mota ne?"

Wani irin daɗi ya ziyarci zuciyar ta , amma sai ta fuske ta ce

"A'a Dr ka barni kawai na hau nafef."

Ta ida maganar tana tafiya.

"Maryam." Ya kira sunan ta da wani irin murya.

Cak Meesha ta tsaya ba tare da ta juyo ba, don yadda ya ambaci sunan sai ta ji kamar duniya babu wanda ya iya fadar sunan kamar shi.

"Mu je na ce maki ko?"

Ya yi maganar yana daukan key.

"Dr ai baka duba petient na ka ba?"

"Dama ba su nazo gani ba, da abin da ya kawo ni, kuma na gani hankalina ya kwanta."


Yana bata amsa ne yana rufe kofar, a tare suke jerawa sun yi mugun da ce wa da juna, don duk wanda ya gansu sai ya yi tunanin miji da mata ne a haka har zuwa inda motarsa ya ke , buɗe mata kofa ya yi ta shiga sannan shima ya zaga.

Yana shiga wayar sa ta soma ringing, da sauri ya dauko don ganin me kiran ɗan murmushi ya saki tare da karawa a kunne

"Hello My Anee ya aka yi?"

Ameesha na jin haka tasan tabbas da matarsa ya ke waya, nan take sai ta ji hankalin ta ya tashi.

Maganar shi ta kuma tsinkaya ya na faɗin

"Haba Anee gani nan a hanyar dawowa, bani minti talatin."

Ya faɗa tare da kashe wayar. Juyo da fuska ya yi yana kallon Ameesha ya ce

"Kinji matata tana kirana wai na daɗe?"

Karamin tsaki ta ja ,ba ta ce masa komai ba, don gaba daya haushin shi da kishin sa suka rufe ta.

Shi ma shiru ya mata ya ci gaba da tukin sa, Ameesha tana nuna masa hanya har suka isa unguwar, a dai dai get din gidan ya faka, kallon sa ta yi ta ce

"Na gode Dr sai da safe."

Harara ya mata ya ce

"Kuma shi kenan iya sallamar da za mu yi?"

Dan ware ido ta yi cikin mamaki ta ce

"Dr wani irin sallama za mu yi wacce ta fi wannan?"

Har yanzu fuskarta ɗauke da mamaki.

Dan sosa keya ya yi ya ce " To ai naga har kin fita ne, ko fa Number din ki bani da?"

"Hmmmm! ta furta da da dai wannan yanayin mamaki ta ce "bani wayar ka nasa ma kafin Abba ya zo ya same ni."

Mik'a mata ya yi ta amsa cikin sauri sauri ta sanya masa, sannan ta nufi get din Asmad na kallonta har ta shige cikin gidan sannan ya saki ajiyar zuciya a fili ya furta

"Allah ka mallaka min Maryam matsayin mata amin." Ya kai karshen maganar yana ta yar da motarsa.

******** ********** *******

Ko da Ameesha ta shiga gidansu da ɗoki ta k'arasa falon, ganin motar Yaya Jaheed ta san shi ɗin ne ya zo, sallama ta doka tare da shiga, wani murmushi ta saki ganin sa zaune a falon da matarsa. Ai da sauri ta isa inda suke tana faɗin "barka da zuwa Yaya" murmushi ya saki cikin jin daɗi ya amsa mata maganar ta.

"A'a Ameesha autar Ummi sai yanzu aka shigo?"

Matar Ya Jaheed ne ta yi maganar. Matsawa kusa da ita ta yi ta ce

"Aunty ina yini?"

"Lafiya ya makarantar?"

"Alhamdulillah." Ameesha ta bata amsa tana nufa hanyar stair. Har ta soma taka matakalar ta tuna bata wa Ummi sannu da gida ba don haka sai ta sauka, bedroom din Ummi ta shiga bakin ta ɗauke da sallama.

Hajiya Halima da ke buɗe k'ofar toilet ta amsa mata cike da kulawa.

"Auta kin dawo?"

"Eh na dawo Ummi."

"To sannu da dawowa,je kiyi wanka abinci yana jiran ki."

"Ummi nifa a koshe na ke, wanka kawai zan yi."

"Ke abin da na ce kenan je ki yi, naga yanzu kwata kwata baki k'aunar cin abinci ko?"

Ummi ta k'arasa maganar tana hararan Ameesha.

Shagwaɓe fuska ta yi ta ce

"Allah Ummi ina ci fa, kawai yau na koshi ne."

"To je ki yi wankan."

"Yawwa Ummina." Ameesha ta faɗa tana fita daga bedroom din.

Bayan ta yi wanka ne ta koma falo inda su Ya Jaheed da matarsa suke, tana zama Meena ta shigo hira suka ci gaba da yi.

*******

"Alhaji wato kasan abin da yasa na nemeka a wannan rana?"

Alhaji Taheer ya yi maganar yana aje cup din da ya sha ruwa.

"Sai ka faɗa Alhaji."

Alhaji Mansur ya yi maganar cikin ɗan murmushi irin na ya ke.

"Dama kan maganar Najeeb ne da Ameesha, na ga soyayyar ta su kullum kara gaba ta ke , shi ne na ce gara asan matsaya."

Wani mummunan faduwar gaba ya ziyarci Alhaji Mansur ya ce "Na shiga uku ni Mansur, kenan burina ba zai cika ba? To wallahi ba zai yiwu ba dole sai na cika abin da na yi niyya, Taheer ba ka isa ba ba zai yiwu."

Amma a fili sai ya kakalo ya ke ya ce

"Yo Alhaji ban da abin ka ai kana iya zartar da hukuncin auren su gaba ɗaya, babu abin da zance sai fatan alheri."

Sosai Alhaji Taheer ya yi farin ciki da jin furucin Alhaji Mansur ɗin, don haka sai ya ce

"To zamu zauna nan da kwana kaɗan don asa rana."

"Allah ya kaimu."

Da wannan hirar suka ci gaba da hirar duniya, sun daɗe sosai ka ɗin su ka yi sallama ko wa ya kama hanyar gidan sa.


Lokacin da Meesha da Najeeb suka samu wannan labarin ba karamin daɗi su ka ji ba, babu kamar Meesha da ta ke murna zata huta da tunanin Dr ɗan fullo, tunda zata auri wanda ta ke so.

*******

"Um um Abba yau fa kai zaka kaini school." Meesha ta yi maganar tana zama kusa da Alhaji Taheer ɗin.

Murmushi ya saki tare da shafa kanta ya ce

"Duk yadda ki ka ce haka za'a yi uwata, dama muna da meeting da su Alhaji Mansur, in na sauke ki sai na wu ce."

"Yawwa Abbana! Shi yasa na ke kara sonka." Ta kai karshen maganar tana kiss ɗinsa a kumatu. Murmushi ya yi cike da farin cikin yadda Ameesha ta yi.

Ummi da ke gefe ta ce

"Alhaji kenan kullum dai kai ke kara shagwaɓa yarinyar nan."

" Haba Hajiya dole na shagwaɓa yarinyar nan, ita fa kaɗai gareni gata da sunan Mamana."

"To Allah ya k'ara taimakawa."

Tana faɗan maganar dai dai da zuwan Ameesha "Ummi sai mun dawo."

"Allah ya dawo da ku lafiya."

Rike da hannun Abba su ka fita inda motar ta ke, har ta buɗe sai kuma ta rufe ta soma tafiya

"Auta ina zaki kuma?"

"Abba zan yi sallama da Ummi ne."

Ta bashi amsa tana tafiya, kafin Alhaji Taheer ya yi yunkurin yin magana har ta yi nisa.

Ita kanta ta rasa me yasa ta ji tana son k'ara ganin ummin, shi yasa kawai ta fasa shiga har sai ta gano Ummi ɗin.


Ummi da ke zaune ta yi mamakin ganin Ameesha ta dawo

"A'a ya kika dawo kuma?"

"Ummi ganin ki na dawo yi."

Ta bata amsa tana zama, kallo ɗaya zaka mata kasan jikin ta ya yi sanyi. "Anya kuwa Auta lafiyar ki?"

"Lafiya lau na ke Ummi."
Ta bata amsa tana kwanciya a jikin Ummin.

"To kuma na ga kin dawo?"

"Eh zan tafi ban son rabuwa da ke ne fa?"

"To fasa zuwa kawai."

"A'a Ummi zan tafi." Ta faɗa tana mik'ewa. Tana tafiya tana ɗagawa Ummi hannu har ta fita, a motar ta samu Abba yana waya, shiga ta yi ta zauna. Sai da ya kammala da wayar sannan ya juyo inda Ameesha ta ke

"Uwata sai yanzu ki ka fito?"

"Abba ina fa wajen Ummi ne." Kamar zata yi kuka ta ida maganar.

Bai ce komai ba ya ja motar. Suka tafi a kofar makarantar ya ajeta shi kuma ya wuce.

********

Zaune da wayarsa a hannu,sai juya wayar ya ke Number din ta ya ke son kira sai dai kuma yana tunanin abin da zai ce mata, da kyar ya yi shahada ya danna kira.

Ameesha da ke tafiya har ta kusa shiga class ta ji wayarta na ringing, cirowa ta yi daga cikin jakarta ta duba Number din, sai taga bata sani ba har zata maida jaka sai dai ta ɗauka.

Wani irin faduwar gaba ya ziyarce su lokaci ɗaya, Ameesha shiru ta yi bayan ta yi sallama, shi ma a nashi ɓangaren haka ya yi bayan amsa mata sallamar.

Kusan minti biyar sannan ta yi k'arfin halin ce wa " Hello wa ke magana?"

Sai da ya dai dai ta nutsuwar sa kafin ya ce

"Haba Princess nine fa?"

Murmushi ta saki mai kyau, amma sai ta yi kamar bata gane shi ba ta ce

"Ban gane ka ba ai..."

Tun kan ta ida maganar har ya katse, ɗan dariya ta yi da ganin ya kashe wayar. Shi kam tsaki ya ja da maganar da Meesha ta faɗa masa "wai wa ye?" Wannan abu ya bashi haushi.

Ita kam ko a jikinta class ta shiga, bar fito lacca ba sai karfe uku, yau Meena bata shigo ba haka kuma kawarta Ni'eema bata zo ba.

Don haka sai kawai ta kama hanyar fita don ta hau nafef, a hankali cikin nutsuwa take tafiya har ta fita wajen makarantar ta hau titi da niyyar tsallakawa sai ji ka ke kiii. Mota ta banke ta sai da ta daga ta sama sannan ta faɗi k'asa.

Kafin mutane su yi yunkurin ceto ranta har mai motar ya gudu, da sauri mutanen suka ɗauke ta zuwa asibiti don wajen basu da nisa da police station, da taimakon yan sandan aka amshe ta a asibitin Malam Aminu Accident and emergency room aka nufa da ita don ceto ranta, Allah yasa cikin wanda su ka kaita asibitin akwai wanda ya ɗauki wayarta, duba contact ɗinta ya yi yaga Number din Abbanta da sauri ya kira, lokacin Abba suna zaune da Alhaji Mansur sai hira su ke yi , ya ji karan wayarsa yana dubawa ya ga Number ɗin Ameesha murmushi ya yi ya kara a kunne yana faɗin

"Auta sai yanzu kuka fit...?

Bai gama rufe baki ba sai jin, mai kiran ya ce "kaine Abbanta ko to tana asibiti ta samu haɗarin mota, tana asibitin Malam Aminu Kano."

A kiɗime Alhaji Taheer ya mika hankalinsa ya yi mugun tashi, su Alhaji Mansur har suna haɗa baki wajen tambayar me ya faru?

"Ameesha ce wai mota ta bige ta tana asibitin Malam Aminu Kano."

Yana basu amsar ne yana tafiya.

Ko da Abba ya isa asibitin kasa nutsuwa ya yi, da ba'a barsu ganin ta ba, sosai ya yi wa wanda suka kai Ameesha asibitin sannan ya kira Ummi yana sanar mata, kuka ta fara ta na cewa "Allah sarki Auta dama shi yasa ɗazun ta kasa tafiya? Wayyo Allah ka tashi kafadar Auta."

Kan ka ce me har asibitin ya cika da mutane, sai dai duk wani taimako da ake wa Ameesha bata farka ba, kusan awa uku kenan manyan likitoci suka duk'ufa akan ta, kowa aiki yake abin mamaki babu wani ciwo da yake jikinta sai wani kusa da kanta, amma yadda numfashin ya ɗauke shi ne abin tsoro.

Asmad na zaune sai hira suke shi da Aneesa cikin farin ciki, sai jin wayarsa ya yi yana ringing, Dan tsaki yaja tare da kara wayar a kunne. Jin abin da ake faɗa masa a wayarta sa shi saurin mik'ewa

"Please Aneesa bari na je asibiti akwai babban matsala." Bai ko tsaya jiran me zata ce ba kawai ya yi gaba. Cikin sauri ya auri motarsa, ko parking me kyau bai tsaya yi ba ya tunkari emergency room din.

Haka kawai ya ji hankalinsa ya tashi, da taimakon addu'a ya isa gaban gadon "inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un". Shi ne abin da Asmad ya faɗa ya yin da ya yi arba da Ameesha.

"Princess me ya faru da ke? Dazun fa mu ka yi waya da ke?" A rude ya ke maganar jikinsa har rawa ya ke. Da sauri cikin kwarewa ya soma bata nashi taimakon, duk sauran likitocin gefe suka koma suna kallon sa, ya dai ki manin awa ɗaya kafin ya samu numfashin ya dawo dai dai, wani dogon ajiyar zuciya ya ja tare da hamdala ga Allah.

Suma sauran likitocin sun yi farin ciki sosai,kuma sun yaba da aikin Asmad ɗin. Da kansa ya gungura ta zuwa ɗakin hutu. Su Abba ma har hankalinsu ya ɗan kwanta da jin an samu numfashin ya dawo.

Sai da ta yi awa uku tana bacci kafin ta farka, lokacin ɗakin daga Ummi sai Meena da Abba. Meena ce ta kulla da Ameesha ta farka

"Ummi kalli bestyna ta farka."

Meena ta yi maganar cike da jin dadi, tare da nufa waje ɗin kiran Dr domin ya ce in ta farka a yi saurin sanar masa, murmushin farin ciki ne ya mamaye su Abba, har suna rufe rigen matsawa inda ta ke

"sannu Auta ya jikin?"

Da wani Irin kallo Ameesha ta bisu ina rashin sani, sun yi mamakin irin kallon sannan kuma bata yi magana da Kowa ba. Dai dai da zuwan Dr ɗan fullo.

Kallon Ameesha ya yi ya ce

"Princess kin tashi ina ke maki ciwo?"

Abin mamaki sai suka ji ta ce

"Princess kin tashi ina ke maki ciwo?"

Dan Zaria ido ya yi tare da murmushi ya ce

"Haba Princess kuma da tsokana ki ka tashi?"

Itama ma ta ce

"Haba Princess da tsokana ki ka tashi?"

Mamaki ya kama su da yadda Ameesha ta ke, don zuwa yanzu sun fahimci Ameesha fa ba wasa ta ke ba. "To me hakan ke nufi?"

Dr Asmad ya wa kansa tambayar da babu amsa.

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad my Besty*

_*Ina taya dukkan Musulmai murnar sallah, Allah ya amsa ibadunmu Ubangiji ya sa muna cikin yantattu da wadinda aka yiwa gafara Allahumma amin*_

_ina cigiyar Baseera Sabo Nadabo! Please baiwar Allah ina kika shiga haka?_

*My Besty ke kam dama ta dabance, a lokuta da dama har rasa kalmar da zanyi amfani da ita yayin nuna maki zallar farin ciki da kulawar da kike min nake yi, amma duk da

Please Login or Register in order to submit comment