Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi tambayar tana zama kusa da ita.

"Bari kawai, har da hakan ma wallahi, ina tunanin ya zaman yarinyar nan zai kasance, ita ba wata me koshin lafiya, wallahi naso ace magani aka fara neman mata fiye da maganar aure. Har yanzu mune muke kidanmu da kuma rawarmu, don gidan su Angon nan har yanzu tsinkensu bai shigo gidan nan da sunan maganar aure ba."

Ta karasa maganar tata hade mikewa zaune, cikin jimami tana kallon Aunty Saude.

A jiyar zuciya Aunty Saude ta sauke ta ce

"Ki bar tunanin nan kar ya haifar maki da wata matsala, tunda Alhaji ya yi niyyar auren nan na tabbata ko da ba zasu kawo komai ba tofa sai anyi shi, ita dai Ameesha addu'o kawai zaki rika yi mata."

"Insha Allahu zan yi.

"Amma anya kuwa Aunty gidan mazan nan suna son auren kuwa...?


_Ku yi hakuri da wannan Please._

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*23*

"To ni ina zan sani masu, abu daya dai na sani shi ne sun bata min rai." Cikin takaici Ummi ta k'arasa maganar.

"A dai kara hakuri Aunty."

"Yo ai hak'uri ya zama dole, tashi ki je wajen autar kila tana bukatar wani abun."

"To Aunty" shi ne abin da Aunty Saude ta faɗa tana mik'ewa.

***********

Asmad ne kwance a daki sai juye juye ya ke yi, tunda garin Allah ya waye sallah kawai ya yi, sam baya jin dadin jikinsa tunanin rabuwa da abar sonsa Ameesha shi ya haddasa masa wannan zazzafar zazzaɓin, duk da ya sha magani amma babu wani sauki.

"Sannu Hamma ya jikin?" Aneesa ce ta yi maganar tana zama a bakin gadon.

"Da sauki." Asmad ya yi maganar cikin karamar murya.

"Allah ya kara sauki, ko za'a sanarwa su Nenne ne?"

"No! Ba sai kin sanar masu ba, kar hankalinsu ya tashi, ai na samu sauki zuwa anjima zan fita."

"Allah ya kara lafiya."

"Amin! Haɗa min ruwan wanka kila ko na kara samun kwarin jikin." Ya dire maganar yana tashi zaune.

Cikin kankanin lokaci har ta gama haɗa masa ruwan, sannan ta fito tana faɗin

"Hamma na gama!"

"Na gode, ɗan taimaka min."

Da taimakon Aneesa ya yi wankan, har ya shirya babu laifi ya ɗan samu kwarin jikin, tunda har falo ya fito ya kunna t.v .


*Yau saura kwana daya biki*

Zaune a falo Ameesha ce da Meena, Meena ke gyara mata gashinta wanda suka je aka wanke, shi ne kaɗai abin da Ummi ta yadda akawa Meesha don ta ce yarta bata da lafiya abarta har zuwa lokacin da zata sami sauki sai a yi shagalin auren.

Meena ta kalli Meesha ta ce

"Meesha gobe iwar haka kin zama amaryar Najeeb."

"Amaryar Najeeb?" Meesha ta tambaya.

"Eh! Gobe zaki tafi ki barmu, zan yi kewa."

Wannan karon Meesha shiru ta yi kamar mai tunanin wani abu, haka Meena ta ci gaba da mata hira amma taki amsawa.

"Alhaji wai kuwa kana ga yaron nan na son Auta?"

"Wannan wacce irin tambaya ce?"

"Allah ya baka hak'uri, amma ni sam tsarin auren nan bai min ba."

"To ni kuma ya min." Abba ya kai karshen maganar yana barin wajen.

"Allah ya kyauta, amma wannan abin ban taɓa ganin ko jin irinsa ba."

**

Yau kam jikin Dr ya yi sauki don har fita ya yi asbitin su, sai da ya kammala da duba marasa lafiya tunkun ya koma office, duk da yau din ta kasance Lahadi ne, babu aiki amma shi Asmad ya saba ya je don duba marasa lafiya.

Office ya koma, ya zauna tare da janyo laptop dinsa, wani bincike yake yi akan wata ciwon, wayarsa dake gefe ta soma kara, ɗan tsaki ya ja don bai so a katse masa aikin da yake, sunan Hafiz ya gani .

Hannu yakai tare da ɗaukar wayar ya kara a kunne

"Hello Dr kana jina?"

"Eh! Dr ya amsa a takaice.

"Dama zan ce maka ne zaka samu zuwa wajen daurin auran kuwa?"

"Daurin auran wa?" Ya yi tambayar.

"Auren Ameesha mana."

"Oh! Wai yau ne auren?"

"Eh! Mana hala baka duba katin da Jaheed ya kawo mana ba?"

"Gaskiya dai ban duba ba, kuma yanzu ina wani aiki ne, bani ma a gida ina office don haka ba zan samu zuwa ba, amma ko zuwa gobe zan je na yi masa Allah sanya Alhairi."

"To ai shi kenan, nima ɗin da kashe aikin zan yi muje tunda haka ne to mu bari sai goben."

"Allah ya kaimu." Dr ya faɗa yana kashe wayarsa.

Ko da ya gama wayar, tagumi ya zuba idonsa taf da kwallah, zuciyarsa wani mugun zafi take, musamman da ya ji yau auren farin cikinsa, a fili ya furta

*"Shi kenan ni kuma na rasa farin cikina daga yau har zuwa ranar da zan koma ga mahaliccina."*

A dole barin aikin ya yi don wani sabon zazzaɓin ne ya kuma saukar masa. Da taimakon addu'a ya isa gidansu. Ko kyakkyawan fakin ba yi ba, ya fita daga motar.

Ko sallama kasawa ya yi sai zubewa da ya yi akan kujera, dage da kansa Nenne dake zaune a falon ganin shigowar Asmad ɗin a wannan yanayin yasata saurin mik'ewa tana ambaton sunan Allah.

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Asmad lafiya?"

Da kyar ya iya furta "Nenne bani da lafiya ne."

"Subhanallah me ya same ka? Daga ina kake?" A hargitse Nenne kewa Asmad ɗin tambaya.

Cije leɓe ya yi ya ce

"Daga office nake, wayyo Nenne kaina ciwo ya ke."

Hankalin Nenne ya mugun tashi da ciwon Asmad ɗin, wayarta ta dauka ta kira Bobbo tana sanar masa da halin da ake ciki. Ai cikin sauri Bobbo ya iso gidan yana, shi ma ya tsorata da yadda Asmad ɗin ya ke.

Wayarsa yasa ya kira wani Dr abokin Asmad ɗin, cikin kankanin lokaci ya iso, duba shi ya yi sosai sannan ya masa allura ya bashi magani, babu jimawa bacci ya kwashe shi.

Kallon su Bobbo ya yi ya ce

"Ku kwantar da hankalinku damuwa ce ta haifar masa da zazzaɓin, amma insha Allah sanda zai farka zai ji sauki ."

Godiya sosai suka masa sannan ya tafi. (To Asmad Allah ya baka lafiya da sauran musulmai baki daya.)


*Wajen daurin auran*

Jama'a ne dankam a kofar gidan Alhaji Taheer, duk inda ka duba motocine ga sunan birjik manya na Alfarma, kallo ɗaya zakawa Abba kasan yana cikin farin ciki da wannan rana.

Su ya Jaheed ma sun hallara, fuskokinsu cike da farin ciki, dangin Ango kawai ake jira a daura auren. Tun 12 aka sa lokacin auren gashi har 12:30 da yawan mutane har sun fara kosawa, shi kansa Abba mamakin rashin zuwan su Alhajin yake.

Wani mutum dake gefe ya buɗe baki sosai tare da fadin

"Kai wallahi mukam mun gaji da wannan jiran, zamu wuce don muna da aikin yi..."

Tun kafin ya gama rufe baki sai ga wani mutum, da gani kasan dan jagaliya ne don yadda ya burgago mashing ɗinsa cikin mutane mai cikakken hankali ba zai iya yin haka ba.

Kai tsaye wajen da su ya Jaheed suke ya nufa tare da mika masu zungureriyar takadda mai cike da rubutu, da rashin sani ya Jaheed ya kalli mutumin ya ce

"Kai wannan fa daga ina?"

"Kai ma ba kazo daurin auran ba ne?" Ya yi maganar cikin muryar su irin ta yan dabar.

"Eh! Ya Jaheed ya bashi amsa.

"To ka bawa uban amaryan, don ni ba sanin sa na yi ba." Yana gama faɗin haka ya ja mashin dinsa ya bar wajen. Da kallo suka raka shi, juya takaddan ya Jaheed yake sannan ya nufi inda su Abba suke, zuwa wannan lokacin jikin Abba ya jike sharkaf da zufa.

Zuwa lokaci Alhaji Taheer da abokinsa Alhaji Usman sun yanke shawarar a daura auren, har an soma gabatar da yadda ake auren.

Maganar Jaheed ce ta dawo da shi

"Abba gashi wani ya kawo wai abaka." Jaheed ya yi maganar yana mik'a masa takaddan.

Hannu Abba ya mika cikin faduwar gaba, ya ce

"Daga ina kuma ina mutumin?" Ya yi maganar yana juya takaddan.

"Yana bani ya wu ce."

"To aje wajenka har a gama daurin auran."

"A'a Alhaji ya kamata abude wannan takarda don sanin me ta kunsa, mu je daga waje." Alhaji Usman ya yi maganar.

Babu musu Abba ya yadda, sai da suka fita can nesa da jama'a suka tsaya, sannan Abba ya bama ya Jaheed umarnin ya karanta, take ko ya buɗe ya karanta masu.

Hankalin Abba ba karamin tashi ya yi da jin abin da takardar ta kunsa ba, nazari ya yi kamar na minti biyu da ya ce

"Mu je kawai Alhaji a daura auren, ka zama wakilin amarya ni zan zama wakilin ango."

Aiko haka aka yi cikin karamin lokaci aka daura auren, ana gama ɗaura auren Abba ya saki ajiyar zuciya take wata ni'ima ta saukar masa, hankalinsa ya kwanta.

Sai dai kuma a waje mutane duk sun cika da mamakin yadda aka canza akalar daurin auran kamar yadda suka gani a kati, haka dai suka gama haɗa hadar su

Abba kam yana gama sallamar manyan bakin da ya gayyata cikin gida ya shiga, falonsa ya shiga tare da cire babbar rigarsa wayarsa ya ɗauka ya kira Ummi lokacin tana cikin jama'a babu wayar a kusa da ita sai Aunty Saude ta kawo mata.

Tana duba Number din ta yi saurin ɗauka

"Ki sameni a falona." Shi ne kaɗai abin da Abba ya faɗa ya kashe wayar, ya soma sintiri cikin dakin, yana jan tsaki. A haka Ummi ta isa falon bakinta dauke da sallama.

"Lafiya Alhaji?" ta faɗa bayan ta kammala karantar halin da ya ke ciki.

"Babu lafiya Halima." Ya bata amsa a takaice.

"Me ya faru? Ta kuma masa tambayar hankali tashe.

"Babu lafiya."

"Ba'a daura auren ba ne?"

"An daura sai dai an samu canji."

"Wani irin canji kuma Alhaji?"

"Canjin ango aka samu."

"Ango kuma? To dawa aka ɗaura auren?"

"Da ..."

_Ku biyo ni don jin dawa aka daura auren, ni ce dai_

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*24*

Zama ya yi akan kujera, don duk wannan maganar da suke yi a tsaye ya ke ya ce

"Wato Halima da mutuncina da komai aka so tozartani, babu komai domin Allah ya kawo canji mafi Alhairi."

"Alhaji ka fara maganar kuma yanzu ka dauko wata, wacce ban fahimci komai daga ciki ba."

"Haba menene abin saurin tambaya kuma? Ai gani gaki dole ne kisan komai da ke faruwa, Alhaji Mansur ya bani mamaki matuka ya dasa min bakin ciki a zuciyata."

Tagumi Ummi ta yi tare da zuba masa ido tana kallonsa,har zuwa wannan lokacin bata gane inda maganarsa tasa gaba ba. Ganin ta kosa ta san komai sai Abba ya mika mata takaddan ya ce karanta wannan.

Cikin sauri tasa hannu ta amsa tare da buɗewa ga abinda sakon ya kunsa.

*Malam Alhaji Taheer kenan, nasan ya zuwa yanzu kun riga da kun hallara wajen daurin aure ko? To kar kayi mamakin rashin ganina da jama'ata, don tuni aka daura auren Najeeb da matarsa lafiyayya, na faɗa maka maganar gaskiya shi ne ka nema wa mahaukaciyar yarka miji dai dai ita, amma fa ba dai Najeeb nawa ba, don shi lafiyayye ne kuma lafiyayyen mata zai aura.*

*Wato tun lokacin da ya kamata ka yi maganar zaka hada su aure ba ka yi ba sai da yarka ta haukace tukun ka ɓullo da maganar don kana son rabuwa da ita, sai ni kuma ka kwaso ka kawo min gida to ba zai yuwu ba, nima bani haɗa zuri'a da mara hankali, don haka ka sama mata miji dai dai da rashin hankalinta, in yaso sai su yi ta haifo maka jikoki marasa hankali sako daga ni ALHAJI MANSUR.*

"inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Shi ne kalmar da Ummi ke maimaitawa a fili.

"Ai dama wallahi jikina ya bani, an so shirya mana walak'anci baccin haka ta ya za'a ki kawo kayan da gidan ango suke kawowa? Tun farko abin da na guda kenan sai gashi ya afku yanzu Alhaji ya kenan za'a yi?"

Ta ci gaba "amma wallahi Alhaji Mansur ya bani kunya ban yi tunanin haka daga gareshi ba."

"Sosai kuwa, domin ko ni lokacin da wasikar ta same ni, gaskiya na yi mamaki don har kiran wayarsa na yi ya kuma tabbatar min da shi ya aikota."

"To ai shi kenan, tunda haka ne yanzu ya za'a yi kenan?"

"Kamar ya fa?" Abba ya tambaya.

"Game da ɗaurin auren mana. Ummi ta bashi amsa.

Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, tare da muskutawa ya ce

"Bayan Jaheed ya gama karantawa kuma na kira Mansur ya kuma tabbatar min da shi ya aiko da takadan."

"Shi ne Alhaji Usman ya ce sam haka ba zai yiwu ba, in samu wani ko da a cikin ya'yan yan'uwana ne a daura da shi, nan ma naga ba wata mafita kada a samu cin mutuncin da yafi na Mansur, sai ga wani mutum ya nufo inda muke tsaye, shi ne fa ya tambaya me yake faruwa take muka sanar sa, sai ya ce n ba damuwa a daura ɗansa duk da a farko na so bijirewa amma sai Alhaji Usman ya hana, nan take na amince amma fa can kasan zuciyata ina tunanin abin da zai je ya dawo."

"Take mahaifinsa ya biya kudin sadaki dubu hamsin kawai na amsa, don irin halarci da ya min duk da ban san kalar ɗan nasa ba, sai dai ina fatan ya kasance mutumin kwarai.

"Ɗazun aka daura auren *ASMAD ABUBAKAR DA MARYAM TAHEER*

"Masha Allah Alhaji Allah ya tabbatar da Alhairi, Ubangiji yasa haka shi ne mafi Alhairi a garemu da ita baki daya."

"Amin." Abba ya amsa

"Yanzu dai ki tashi ki je ki ci gaba da sallamar baki zuwa anjima sai mu kara shawartawa, ni ɗimma da sauran mutanen da zan sallama."

Da to Ummi ta amsa tana fita daga falon, a zuciyarta tana Allah wadai da halin Alhaji Mansur.

A daya bangaren kuma tana addu'a Allah yasa wanda Ameesha ya zame mata bango wajen jin gina. Haka dai a kai ta gudanar da biki har zuwa lokacin da bakin kusa suka tafi sai wanda suka zo daga nesa.


******

"Najeeb ne zaune a wata farfajiya duk da iskar dake kadawa amma shi Najeeb, jin iskar ya ke kamar hucin wuta, kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin muguwar damuwa." Tsaki ya ja mai karfi tare da jawo wayarsa, a gogon wayar ya kalla karfe 2:01a gogon kasar Faransa dai dai da agogo Nigeria karfe goma sha biyu.

Wani murmushi ya saki a fili ya furta "Alhamdulillah! Yau Ameesha ta zama tawa."

"Ya so da Abbansa bai turo shi garin nan ba, musamman da yau ne ranar da ta kasance ranar farin ciki a rayuwarsa, amma sai Abbansa ya turo shi akan wasu kaya wanda shi bai ga wani amfanin su ba." Mtsss ya ja tsaki.

Hankalin Alhaji Mansur kwance yana zaune akan kujerar falonsa, waya kawai yake amsawa daga abokan arzikinsa suna masa murnar daurin auran, Mummy ce ta k'araso falon cikin farin ciki bayan ta zauna ne ta ce

"Sannu Alhaji an daura aure lafiya?"

"Yawwa Hajiya lafiya lau."

"To yanzu Alhaji ina za'a kai yarinyar kasantuwarta mara lafiya, kaga dole tana bukatar masu kula da ita, inda zai yiwu kawai a kawo ta nan har ta samu lafiya."

"Wa ki ke nufi ne?"

"Matar Najeeb mana Ameesha."

"A'a gyara magana dai, ai matar Najeeb sunanta *RUFAIDA*."

Wani zabura Mummy ta yi ta ce

"Ban gane Rufaida ba, ina ce Ameesha ce yar gidan Alhaji Taheer?"

"Haba Hajiya ya ki ke son maida hannun agogo baya? kin san tuni na ce bana son auren nan ke da ɗan ki kuka na ce sai an yi, to da naga na rasa hanyar da zan bi don hanawa shi ne ai na tura Najeeb ɗin kasar Faransa da sunan ya kular min da wasu kaya, na yi haka ne don in samu in cika burina, to kuma Alhamdulillah don buri ya cika..."

"Alhaji an ya kana cikin hankalinka kuwa? Wai kasan abin da kake faɗa ma kuwa?"

"Ras na sani, ce wa na yi da Rufaida aka daura auren ba da wannan mara hankalin yar Taheer ba, don ina son ake haifa min jikoki masu hankali ba mahaukata ba." Ya ida maganar cikin izzah.


"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Amma kam wallahil azeem Alhaji baka da imani, dama saboda ka tauye hakkin yaron nan ne ka tura shi can kasar? Allah sai ya maku hisabi da shi."

Harara kawai ya ke ta aika mata da shi sannan ya ce

"Kin gama zagina? To wallahi bari ki ji, ke kin yi kaɗan in zartar da hukunci ki ce zaki bijire min, ai tun farko sai da na ce bana son auren kuka na ce, don haka sai na bullo maku ta yadda baku tunani."

"Hmmmm! Wannan kuma matsalar ka ce, amma sam baka wa Najeeb da Alhaji Taheer adalci ba, kuma insha Allahu zaka ga abin da ka aikata masu."

"Ke wallahi ki yi a hankali akan wannan auren kina iya rasa na ki aurn." Yana gama faɗin haka ya tashi tare da barin mata wajen. Kuka Mummy ta fashe da shi domin kuwa abin ya ɓata ranta sosai, addu'a take Allah ya sawa Najeeb dangana akan Ameesha.

*******

Dr dai har yanzu sam jikin babu daɗi domin dai ya kasa cire tunanin Ameesha a zuciyarsa, Nenne ce ta shigo bedroom ɗin hannunta rike da cup, kallon Asmad ɗin ta yi ta ce

"Tashi kasha wannan shayin kana ciwo babu cin abinci!"

Girgiza za kai ya yi ya ce

"A'a Nenne bana jin dadin bakina ne, ki bar shi zuwa anjima zan sha."

"Ka daure dai ko kaɗan ne ka sha ka ji ko?"

Sam Asmad baya k'aunar yiwa Nennensa musu don haka sai ya tashi zaune tare da karbar cup din, kurba biyu ya yi ya ce ya koshi ya aje cup din.
"Ka kira Aneesa ka sanar mata baka da lafiya?"

"A'a Nenne."

"Tom ya kamata dai ka sanar mata, don karta ji shiru."

"To." ya amsa yana gyara kwanciya.

Girgiza kai Nenne ta yi kawai, wayar Asmad dake kan dressing mirror ta dauki kara, Nenne ce ta dauko wayar tare da mika masa.

Ganin Number din Bobbo ne yasa shi ɗauka tare da yin sallama.

"Assalamu Alaikum! Bobbo an wuni lafiya?"

Daga ɗaya bangaren Bobbo ya amsa

"Lafiya lau Asmad ya jikin naka?"

"Da sauki ." Asmad ya bashi amsa.


"Allah ya kara lafiya."

"Amin." Ina ji Asmad.

"Ka daure ka shirya zaka rakani wani waje."

Gaban Dr ya yi muguwar faduwa da sauri ya ce

"To Bobbo gani nan zuwa."

"Eh! Yanzu bari na shirya."

"Kai dawa kake magana? Har na ji kana ce wa kuna zuwa, kai da baka da lafiya?" Nenne ta yi tambayar tare da tsare Dr da ido.

"Nenne inji Bobbo wai in shirya zamu fita."

"A haka zaka fita kai da ba daɗi kake ji ba?"

"Ai zan iya tafiya." Dr ya yi maganar cikin karfin hali.

"Ok" kawai Nenne ta iya fada, cikin zuciyarta kuwa cike da mamaki ta ke fadi "oh! Dama don budurwarka tana aure shi ne har da yin ciwo? Lallai ba karamin so Asmad kewa wannan budurwar ba, da a ce tun-tuni tasan kallar son da Asmad kewa wannan budurwa kenan, to da tasan yadda ta yi har Asmad ɗin ya sameta, to an baro shiri tun rani, yanzu kam addu'a zata ke masa Allah ya daura masa hakuri da dangana." Domin dai ɗazun da Hafiz ya zo Ne ta ji hiranmu.

Shi ma Dr Nenne tana fita ya tashi ya shiga toilet, bai wani jima ba ya fito sam jikinsa babu kwari a haka ya fita falon ya samu Bobbo da Nenne

"Ya jikin naka? Bobbo ya kuma tambaya.

"Da sauki."

"Zaka iya tafiyar ma kuwa?"

"Eh! Zan iya." Asmad ya baya Bobbo amsa.

"To shi kenan mu tafi ko?"

"Eh! Kawai Asmad ɗin ya faɗa yana soma tafiya.

Cikin motar Bobbo suka shiga, Dr yasa hannu zai buɗe kenan sai ga Hafiz ya shigo, Bobbo ya yi murmushi ya ce

"Dama dai yanzu nake shirin kiranka ina ce ma mu haɗu a can."

"A'a kuma sai gani tanan."

"Ka kyauta, shiga mu je kawai." Shi Hafiz ya yi kamar yadda Bobbo ya bukata, sannan direba ya soma jan su.

Mamaki sosai ya kama Dr ganin sun nufi unguwar su Ameesha, bai gama yin mamakin ba sai da ya ga sun shiga cikin gidan. "To wai mai Bobbo da Hafiz suke nufi, sun dauko shi zuwa gidan su Ameesha bayan yau aka daura aurenta da wani, ko dai basu san sanadin ta ne ɗazun ciwo ya kama shi ba?" Ya yi wa kansa tambayar da babu amsa. A parking space direba ya faka sannan suka fita dai dai lokacin da ya Jaheed ke fitowa ganin Dr a da sauri ya k'arasa wajen, "a'a Dr Barka da zuwa ku zo lafiya?"

"Lafiya lau, an daura auren lafiya? Please ka yi hakuri wallahi yau ban wuni da lafiya ba ne." Dr ya yi maganar cikin sanyin murya.

"Haba Dr wallahi karka damu ai ciwo ya fi gaban wasa."

" Yi mana iso wajen Alhaji mana! Bobbo ya katse masu jiran da su ke yi.

Babu jimawa ya Jaheed ya dawo yana sanar masu da Abba ya ce su shiga, babban falo aka yi masu masauki zallar farin ciki ne ke tattare da Abba, duk sun zazzauna sannan Bobbo suka kara gaisawa da Bobbo.

Mamaki ya kama Abba ganin Dr tare Allhaji Abubakar ɗin

"A'a Dr yau kaine a gidan namu?"

"Eh! Abba." Dr ya amsa masa cikin girmamawa.

"Ashe kun ma san juna! To ai shi ne ɗan nawa."

"Eh! Mun san juna don shi yake kula da lafiyar yartawa." Domin dai Abba ya yi masa bayanin ciwon Ameesha ɗin.

"To ai shi kenan ma faduwa tazo dai dai da zama."

"Kai madallah! Wallahi wannan abu ya yi sai fatan Allah ya sama abin albarka,domin dai Dr mutumin kirki ne."

Duk wannan maganar suna yin tane bayan fitar su Asmad.

"Alhaji kun zo tafiya da ita ɗin?" Abba ya tambaya.

Murmushi kwance a fuskar Bobbo ya ce a'a ya zo dai ya gaidaka ne, har yanzu bai san abin da ke faruwa ba."

"To ai shi kenan."

"Yanzu abin da za'a yi kawai shi ne, Hafiz zai ɗauki ita Ameesha don shi Asmad gida zai tafi in ya so sai dai ya zo gida ya ganta ina ganin haka zai fi ko?"

"To ni ai bani da wani zaɓi da ya wuce yadda ka ce, fatan alheri zan yi masu da nasara, zuwa karshen sati za su tafi Egypt inda za'a duba Ameesha din."

"Allah ya kaimu, muna godiya da karamci Allah ya saka da Alhairi."

Haka su Bobbo da Abba suka yi ta hiransu.

Bangaren Asmad kuwa can lambun gidan suka koma shi da Hafiz da ya Jaheed hira suke, amma shi Dr daga eh sai a'a kawai ya ke faɗa, so yake ya tambayi ankai Ameesha ko ba'a kai ta ba amma ya kasa. Da ya gaji sai ya mik'e yana faɗin

"Ni kam na gaji da zaman nan, bari na tafi gida insha magani."

"Ayya to sannu Allah ya kara sauki." Suka hada baki wajen faɗa.

"Mu je sai na sauke ka a gidan." Ya Jaheed ya yi maganar yana tashi.

"Hafiz kai ba yanzu zaka tafi ba?"

"Eh! Zan jira Bobbo sai mu tafi." Hafiz ya bashi amsa.

"Ok." Dr ya faɗa yana tafiya.

"Allah ya kara sauki *angon Amee...*

Wani irin juyowa Dr ya yi cikin wani irin yanayi ya ce....


*YAR MUTAN RANO*
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*Na baki kyautar wannan shafin ki yi yadda za ki yi da shi, UMMYN YUSRAH ke ɗin ta daban ce, Ubangiji ya bar k'auna Allah ya raya mana su Yusrah bisa sunna.*

```Ina miko godiya a gareku masoya wannan buk ɗin hakika ina jin dadin yadda kuke gwada min k'aunar da kikewa wannan buk Rabbi ya barmu tare, ina sonku masoya```😍😍😍😍

*LAIFIN WA? & SANGARTA FANS* Ina

Please Login or Register in order to submit comment