Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin su kai sallama. Ya kira Hafiz Yana sanar masa sun sauka, ya dai yi waya da mutane da yawa.

Ameesha dai buɗe ido ta yi tana kallon sa, bata da alamar tashi, murmushi ya sakar mata tare da sa hannu ya dagota ta faɗa jikinsa, tsam ya rungume ta yana sunsunar wuyar ta, wata duniya Dr ya shiga mai cike da nishaɗi, kwankwasa kofar da ake ne yasa shi dawowa nutsuwarsa, kwantar da ita ya yi sannan ya nufi kofar tare da buɗewa. Abinci ne aka kawo masu, amsa ya yi ya shiga da shi, ajewa ya yi kan dining din dake falon ya matsa inda take kwance cak ya dauketa kamar wata baby bai zame ko ina da ita ba sai toilet, d kansa ya cire mata kayan jikinta ya mata wanka sannan ya fito da ita, shirya ta ya yi, kafin shi ma ya shiga.

Ko da ya fito shiryawa ya yi cikin kaya marasa nauyi, kamar yadda ya sawa Ameesha itama, sallar azahar suka gabatar, rike da hannunta suka nufi falon ya zaunar da ita, abinci ya soma bata sai shagwaɓe masa take a haka har ta koshi bayan ta koshi ya fara ci shima, ko da suka gama toilet ya kaita ya wanke mata baki da suka fito basu zame ko ina ba sai kan gado.

Rungume Ameesha Dr ya yi kamar wani ya ce zai raba su, a haka bacci ya dauketa mai dadi farin ciki ne ya mamaye Dr ganin yau gashi ga Ameesha a gado ɗaya yana rungume da ita, hamdala ya yiwa Allah yana fatan Allah ya nuna masa ranar da zasu kasance tare tana cikin hankalinta, kara manna ta da jikinsa ya yi kafin shima bacci ya kwashe shi.

Ba su farka ba sai shida saura minti goma, da sauri ya sauka a gadon, tashin ta ya fara yi, da kyar ta iya bude ido don har a time ɗin bacci ne a idonta.

Alwala ya yi ya taimaka mata ta yi sannan suka gabatar da la'asar, falo suka koma ya kunna masu t.v suna kallo, karfe shida da minti sha biyar Dr Ansar ya kira wayar Dr yana sanar masa da su sauka kasa motar asibiti tana zuwa, tashi ya yi ya canza kayan dake jikinsu kafin ya ja hannunta suka sauka.

Ko zaman minti biyar basu yiba sai ga motar ta iso, shiga motar suka yi sai asbitin *AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL*, cikin mintina ƙalilan suka shiga asbitin babba ne sosai iya haɗawa ya hadu, duk da girman asbitin amma babu wasu mutane dai ɗai ɗaiku, domin dokar asbitin mutane basa zama, ana yin parking kafin su fito har Dr Ansar da wasu likitoci sun iso wajen motar.

Cikin girmamawa da mutunta juna suka tarbe su, cikin asbitin suka shiga, bayan kara gaisawa ne Dr Ansar ya bukaci Dr Asmad ya yi masa bayanin ciwon Ameesha, take ya fito masa da duk wani fayal da ya shafi ciwon, amsa ya yi ya duba, sannan ya dubi Dr Asmad ya ce

"Wannan ciwon yana da saukin warkewa a wajen mu amma da yaddar Allah, yanzu zamu fara mata gwaje gwaje sai musan matsayin da zamu taka."

"Allah ya taimaka ya bamu sa'a."

Dr ya faɗa yana ji cikin zuciyarsa kamar Ameesha ta samu lafiya, Dr Ansar yana gaba su na binsa a baya tare da wasu Nurse har wani daki mai cike da na'urori wani riga aka ba Ameesha ta sanya, da taimakon Dr ta sanya wajen shiga da ita ciki sam taki yadda a dole sai da Dr aka shiga, abin da yasa aka bar Asmad shiga don shima ya kasance likita ne kuma Dr Ansar yasan matsayin Ameesha a wajen Dr Asmad shi ne dalilin barinsa shiga ciki, wasu na'urori aka sanya mata akai ya yin da Dr Ansar ya koma wajen computer dake nuna cikin kan Ameesha. Dr Asmad da wasu manyan likitoci suna kallon computer.

Dai dai kan wani abu, wani ɗan alama ya tsaya sai mutum ya zuba ido da kyau zai iya fahimtar menene a wajen, juyowa Dr Ansar ya yi yana kallon sauran likitocin ya tsaida kansa a kan Dr Asmad.

Ya ce

*Wai wallahi na gaji ku yi hakuri da wannan i hearttttt you all SANGARTA FANS*




_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:15 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*


*33*

"Dr ka kula da menene a wajen ca." Ya yi tambayar idon akan Asmad.

Dr Asmad bai kalli Dr Ansar ba idonsa yana kan computer yana nazarin abin dake k'wak'walwar Ameesha, kusan minti biyu tukun ya sauke a jiyar zuciya ya ce

"Dr duk iya nazari na ban gane ko menene ba." Har a lokacin yana kallon computer.

Murmushi kawai Dr Ansar ya yi yana zomming na pic na photo, sai ga wajen ya fito fes, zaro ido Dr Asmad ya yi cike da mamaki ya ce

"Da fatan yanzu ka ga komai?" Ya yi maganar yana ci gaba da daddana wa.

"Yes! Dr na ga komai har na gane abin da ke wajen."

"Me ka gani kenan?"

"Jini ne kwance a wajen, ga shi nan." Dr ya yi maganar yana nuna cikin computer.

"Tabbas jini ne ka duba da kyau yana motsa wa daf yake da gangarawa cikin k'wak'walwar ta, kuma da zarar ya ida shiga babu tantama haukace wa zata yi."

"What! Dr ya faɗa da karfi.

"Yes! Abin da na faɗa ma gaskiya ne, domin wannan ciwon da kake gani ba karamin illa garshi ba, AMNESIA babban cuta kenan sosai yake mai da mutane mahaukata amma ita nata da sauki kawai manta baya ta yi sakamakon wannan jinin dake cikin k'wak'walwar ta, amma da zarar an cire shi tunaninta zai dawo, sai na yi mamaki da duk fayal din da ka kawo babu mai makamancin irin wannan, mu kuma a binciken farko mun gano asalin inda matsalar ta ɓullo."

Jinjina kai Dr ya yi yana kara yadda da kudurar Ubangiji, ya yadda da ci gaban kasashen duniya wanda har zuwa yanzu Nigeria bata da kashi biyu bisa uku cikin masu ci gaba ba, cikin lokaci ƙalilan har an gano ciwon da aka yi kusan wata uku ana fama, ya tabbata da kudi na sayan lafiya da Abban Ameesha ko nawa zai iya sawa ya saya mata, sai dai shi lafiya wani kyauta ne daga Allah madaukakin sarki, yau ga shi cikin karfin ikonsa ya kawo su idan zata samu waraka _(Allah ka kara mana imani da tsoronka, Ubangiji kara mana son Annabi Muhammad.)_

"To Dr yanzu yaushe za'a shiga da ita don wanke jinin, bana son ya gangara gaskiya."

"Kar ka damu bari mu shiga office sai mu tattauna maganar, yanzu bari mu ci gaba da bincike ko zamu gano wani abun." Yana maganar ne yana bubbuga kafadar Dr Asmad.


Dr Asmad bai kuma magana ba, sai ci gaba da kallon computer,
Sun dauki time cikin wajen kafin Dr Ansar yasa suka koma office don ba suga komai ba, wani daki yasa a kai Ameesha allura ya umurci nuser su kuma suka fita.

Dr ne zaune shi da Dr Ansar wanda keta rubuce rubuce, kusan minti biyar sannan ya ɗago da kai yana kallon Dr Asmad

"Tunda an yi saurin gano matsalar zuwa gobe sai a yi mata aiki ma'ana a wanke jinin dake cikin k'wak'walwar ta."

"Eh! Haka ma ya yi don burina da na iyayenta bai wuce ganin ta dawo normal ba."

"In sha Allah zata koma dai dai duk da aikin babban ne, dole sai an hada da addu'a." Cikin karfafa masa gwiwa Dr Ansar ya dire maganar.

"Kullum addu'a ana yin sa sai dai akara."

"Nan zata zauna gobe da karfe biyar na yamma za'a shiga da ita tiyata."

"To! Shi ne abin da Dr ya iya faɗa, zuciyarsa cike da tunanin samun nasara ko akasinta, sun daɗe shi da Dr Ansar kafin suka nufi dakin da Ameesha take, tana kwance kamar tana bacci sai dai ba bacci take yi ba allurar da aka mata ne ke aiki a jikinta.

Wajenta Dr ya nufa zama ya yi tare da ɗaura hannunsa a kan fuskarta yana shafa wa a hankali

"Kar ka damu fa Dr in sha Allah sauki zai zo." Maganar Dr Ansar kenan da ya yiwa Dr Asmad.

Murmushi ya yi ya ce

"Babu komai Dr a wannan shi ne burinmu, saboda zan yi kewarta ta ne daga yanzu har ranar da za'a fito da ita." A ɗan raunane ya dire maganar.

"True love kenan kada ka damu da wannan, domin kana da matsayi a wajena zaka iya ganinta duk time da kaso."

"Na gode da karamci, amma da gaske Dr ba zan dawo sai bayan an yi mata aiki, domin nasan zata samu kulawa yadda ya kamata." Ya kai karshen maganar yana mik'ewa tsaye.

Sosai Dr Ansar ya ji dadin irin yabon da ya samu daga Dr Asmad, wata nuser yasa ta zauna da Ameesha su kuma suka fita, Dr Ansar da kansa ya kai Dr Asmad hotel ɗin da ya sauka, sai da ya ga shigarsa dakin kafin ya yi masa sallama.

Ko da ya shiga falon zubawa ya yi akan kujera yana sauke numfashi, ya yi farin ciki sosai da zuwan sa garin, domin yadda yake ta ganin nasara a kan komai, rigar jikinsa ya cire tare da dauko wayarsa sam ya manta da wata aba wai ita waya Number Bobbo ya Soma kira suka gaisa yana tambayarsa yadda jikin nata yake

"Da sauki Bobbo na barta a asbiti."

"To madallah! Allah ya kara lafiya."

"Amin." Dr ya amsa sannan Bobbo ya mik'awa Nenne wayar, sun gaisa take tambayarsa jikin Ameesha.

"Ai Nenne Alhamdulillah! Nasara ta samu har an gano matsalar a gabana akai komai, nan yaba Nenne labarin komai da ya faru. Sosai ta ji dadi sai addu'a take zuba masu shi da Dr Ansar.

"Tun da ka ce gobe za'a mata aiki zuwa jibi zamu taho, ai bamu san abin haka yake ba."

"Allah ya kawo lafiya, da karfe biyar zasu shiga, kila har ku iso kafin ta farka."

"In sha Allah muna zuwa, yanzu dai ka sanar da mahaifin Ameesha domin ya samu kwanciyar hankali."

"Yanzu zan sanar masa, ina Aneesa?"

"Tana ɓangarena yanzu karfe biyu na dare ne, ka bari da asbah sai ka kirata, ko dama ba ku yi waya ba ne?" Cikin mintinan da ba su fi uku ba Nenne ta yi masa maganar.

"A'a Nenne mun yi waya da ita ɗazun." Ya ba Nenne amsa.

"To shi kenan Allah ya taimaka ya bada nasara."

"Amin." Ya amsa sannan suka yi sallama.

Wayar Alhaji Taheer ya kira, bayan sun gaisa yake masa bayanin komai, sosai Abba ya ji dadin wannan bayani, suna gama wayar ya tashi ya dauro alwalarsa kamar yadda Nenne da Bobbo suka suka yi duk addu'ar tasu akan samun nasara aikin da za'a yi mata ne.

Shi ma Dr toilet ya shiga sai da ya yi wanka ya dauro alwala jallabiya ya sa, kafin ya tayar da sallah, ya daɗe yana addu'a, sai kusan huɗu bacci ya kwashe shi.

Bacci sosai Dr ya yi bai farka ba sai karfe tara na safe, da sauri cikin takaicin irin baccin da ya yi har ya rasa sallah aka lokaci yake, toilet ya shiga ya sake wanka tare da alwala, sallah ya gabatar kafin ya kira yan hotel ɗin ya sanar masu abin da yake buk'ata, wayarsa ya dauka ya danna Number Aneesa, lokacin tana kwance cike da tunaninsa sai ta ji karan wayarta dauka ta yi tare da karawa a kunne

"Hello Assalamu Alaikum my Anee!" Dr ya yi maganar lokaci ɗaya.

Lumshe ido ta yi ta buɗe don jin muryar Dr ta yi ta kara daɗi, har wata kasala ta saukarwa Aneesa, shiru ta yi masa

"To me kuma na yi da aka ɗauki waya magana dani ya gagara?" Cikin sanyin murya ya mata tambayar.

Turo baki ta yi kamar yana ganin ta ta ce

"Babu komai fa gani na yi ka manta da ni!"

Dan wari ido ya yi waje ya ce "Ke kullum cikin korafi yanzu don Allah wa ya faɗa maki na manta da ke, Ni ban yi korafin kin kirana da ba ki yi ba amma ke ki ke min?"

"Babu." ta bashi amsa a takaice.

Ajiyar zuciya ya sauke, cikin ransa ya ce "ina jiran ganin ranar da Aneesa zata yi hankali." Amma a fili sai ya ce

"My Anee gaisuwa ma yau ya gagareki balle ki tambayeni mai jiki?"

Harara ta wurgawa wayar kamar dai Dr na kallonta ta ce

"To ina kwana ya mai jikin?" Daga jin yadda ta yi maganar yasan ta ji haushin maganar sa.

Dariya ya yi ya ce "Lafiya lau Aneesa mai jiki ta ji sauki." Hira suka shiga irin ta mata da miji har kusan sha daya sannan suka yi sallama, an kawo masa abinci tuni amma wayar da ya ke da Aneesa ya hana shi ci, har sai da suka gama ko da ya gama cin abincin zama ya yi yana kallo har bacci ya kwashe shi.

Ko da ya tashi wanka ya yi tare da sallah, bayan ya ci abinci ya shiga yawon zaga gari domin dai zaman ya ishe shi, bai koma masaukin sa ba sai karfe biyar, a dai dai lokacin kuma aka shiga da Ameesha dakin tiyata, inda suka kwashe kusan awa uku ana yi, basu fito ba sai takwas na dare.

Fuskar Dr Ansar kaɗai zaka kalla ka fahimci halin da yake ciki na farin ciki, domin dai ya ji a jikinsa aikin zai yi kyau, don ko kadan ba'a samu matsala a lokacin yin aikin ba, Dr na zaune akan sallaya don tun da ya shiga dakin dukufa ya yi addu'a da samun nasara, wayarsa ce ta fara ringing Yana dubawa yaga sunan Dr Ansar ai da sauri ya dauka.

"Alhamdulillah! Dr Asmad ya faɗa da murya mai cike da zallar farin ciki, domin albishir din Dr Ansar ya yi masa na har sun fito daga aikin, suna gamawa ya kira su Abba ya sanar masu, su ɗin ma sosai suka yi farin ciki.

Daga Dr har su Nenne su Ummi da Abba kwana salloli da addu'a suka yi, Dr kam bai rintsa ba sai da ya yi sallar asuba nannauyan bacci ya kwashe shi, karar wayarsa ce ta tashe shi daga bacci cikin baccin ya ɗauki wayar Muryar da ya ji ne ta shi saurin tashi.

"Assalamu Alaikum Abba har kun iso ne?"

"Eh! Gamu nan a airport muna jiranka."

"To Abba gani nan zuwa yanzu in sha Allah." Dr ya yi maganar yana tashi, mamaki sosai ya yina irin baccin da ya yi, sai a lokacin ya duba agogo yaga har karfe biyu na rana, shaf shaf ya yi wanka ya shirya daret airport ɗin ya nufa, cikin lokaci ƙalilan suka hadu Abba ne da Ummi sai Bobbo da Nenne, sosai Dr ya yi farin ciki da ganin su, bayan sun gaisa sai Nenne ke tambayarsa

"Ameesha ta farka kuwa?"

"A'a Nenne ya ce sai nan da awa biyu."

Gaba daya suka hada baki wajen faɗin "Allah ya tabbatar da Alhairi, yasa an yi a sa'a."

"Amin." Ya amsa sannan suka shiga mota zuwa hotel su dan huta kafin su je asbitin. Sosai suka huta don har abinci da salloli suka yi, sai suka dunguma zuwa asbitin.

Tun a farkon shiga Abba ya fara yabawa da tsarin asbitin don komai na ciki mai inganci ne da kyau

Fitowar su daga mota ta yi dai dai da zuwan Dr Ansar, yana ganin su Dr Asmad sai ya yi saurin k'arasawa, musabaha suka yi da Dr ya gaida su Abba, sannan suka shiga cikin asbitin daret dakin da Ameesha take suka nufa Dr Ansar yana kara faɗa masu yadda komai ya wakana, sun ji dadi burinsu su karasa inda Ameesha don su ga halin da take.

Wani daki ne mai kyau sosai kamar ba dakin asbiti ba suka shiga, Dr Ansar da Dr Asmad ne a gaba sai Abba da Bobbo dake biye da su a baya, wajen gadon suka yi burki tana kwance kamar gawa don babu inda ke motsi a jikinta addu'oi suka fara tofa mata suna addu'ar Allah ya bata lafiya

"Dr zuwa yaushe zata farka?" Dr ya yi tambayar.

"Nan da minti talatin zuwa awa daya." Dr Ansar ya bashi amsa yana kallon agogonsa.

"Ok Allah ya kaimu." Duk suka faɗa.

Sannan suka fita daga dakin aka bar Nenne da Ummi, Nenne ce ta matsa tare da riko hannun Meesha tana mata addu'a, Ummi kam kasa matsawa ta yi sai dai ita dinma addu'a take yi mata daga inda take zaune.

Dr Asmad ne tare da su Abba, yana tsugune gaban su kansa a kasa magana yake son yi amma ya kasa.

"Asmad kamar kana son yin magana ko?" Abba ya tambaya.

Dan sosa kai ya yi ya ce

"Amm dama Abba cewa zan yi ko da Ameesha ta farfaɗo karku sanar mata da matsayin ni mijinta ne."

"Me ya sa za yi haka? Kasan dai dole zata san da maganar ko?" Bobbo ya yi saurin jeho masa tambayar.

"Eh! Bobbo ina son sanar mata da kaina ne, ina rokon alfarma."

"To ai shi kenan tunda kai ka bukaci haka." Abba ya bashi amsa. Daga haka suka shiga hiransu da ciye ciyen.

Cikin dakin kuwa Nenne tana rike da hannun Meesha sai taga hannun ya soma motsi....


```Tofa jama'a ga dai Meesha nan ta fara motsi alamar ta farka shin a wane yanayi zata farfaɗo?

To wai idan ta farfaɗo ta ji maganar aurenta da Dr kuna ganin zata yadda?

Ya Dr zai kasance bayan farfaɗowar Ameesha?

Duk da wannan amsar yana ga Zulayheart Yar gidan Haruna, ku biyoni a hankali zan warware maku komai da yadda Allah, i hearttttt Your My fans```

_*Yar mutan Rano*_
[10/8, 8:15 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

```Har abada bazan manta da Alhairin ku a gareni ba, tabbas ba dan kuba wallahi da yanzu babu sauran maganar labarin SANGARTA, amma kasancewar ku a wajena yasa ku ku ka assasani har labarin ya kawo yanzu, ina kara godiya a gareku Allah ya saka maku da mafificin Alhairin sa ameen da ku nake

KHADIJAH S MUHAMMAD ( Bestyna)
&
BADEEYAR ADAM (Beauty Queen) Allah ya barmu da k'aunar juna```

*Dedicated to LAIFIN WA & SANGARTA FANS* ina son ki sosai😍😍😍

*34*

Da sauri Nenne ta kara damke hannun, cikin zuciyarta tana tasbihi ga Allah a haka duk jikin Ameesha suka fara motsi

"Alhamdulillah!" Nenne tafa murya a bayyane.

Ummi da sai a lokacin ta kula da sauri ta matso tana faɗin

"Kamar tana motsi ko?"

"Eh! Bari a kira Dr." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa.

"A'a zauna kawai bari na kira shi." Ummi ta dire maganar tana fita daga dakin ranta fes.

Lokacin da Ummi ta sanar masu duk sun ji dadi, suna addu'ar Allah yasa ta warke kenan, babu kamar Dr da ya ji maganar kamar anyi masa bushara da aljanna, sujada ya yiwa Allah don nuna jin dadin sa, ji ya yi kamar ya ri ga kowa ganin Ameeshar sa, sai dai yana kunyar su Ummi, lokacin da ya dawo tunaninsa wayam yaga wajen ma'ana har su Abba sun tafi ganin Ameesha kenan? Ya yi maganar shi ma yana nufa dakin.

Su kam su Abba kusan a tare suka shiga, kan gadon duk suka nufa tare da zuba mata ido,

"Dr ashe ta farka?" Abba ya tambaya.

"Eh! Ta farka yanzu, sai dai akwai buk'ata ta samu hutu."

"Ku yi hakuri ku dan bani waje." Dr ya yi maganar yana nufa wajen gadon, ya soma duba ta ganin numfashin ta ya dawo normal, sai dai bata buɗe ido ba, ganin haka da Dr Ansar ya yi sai ya ce

"Kin farka?"

A hankali ta soma buɗe ido har ta bude su duka, ta daura idonta akan na Dr Ansar tana masa wani irin kallo na mamaki, sam Dr bai damu da haka ba.

farin ciki ne ya kama Abba da su Nenne ai da sauri suka shiga ɗakin, ganin an turo kofar yasa Ameesha saurin daga kai tana kallon masu shigowa bata ce komai ba sai lumshe ido da ta yi

"Alhamdulillah! Autar Ummi." Ummi ta yi maganar cikin farin ciki.

A karo na biyu ta kuma buɗe ido ta zuba su kan fuskar Ummi, ko kadan bakinta bai motsa da sunan magana ba.

Gaba daya suka fita sai Nenne kawai aka bari a daki, Nenne bata yi musu ba domin babu mamaki Ameesha ta farka tana bukatar wani abu babu kowa.

A inda suke Dr ya same su "Abba ina son magana da ku a office." Dr Ansar ya yi maganar yana tafiya, bayan sa suka bi Ummi da Abba da Bobbo, sai Dr Asmad da ya bisu a baya.

A hankali likitan ya zare farin gilashin da ke fuskarshi, lokaci d'aya kuma ya tattara hankalinshi a kan Su Abba da suke zaune su ma hankalinsu a kanshi.

"Ita cutar Amnesia cuta ce da take samuwa ta hanyar duk wani abu da zai taba Kwakwalwa sannan a rasa hankali gabadaya, musamman idan kai

Please Login or Register in order to submit comment