Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riga kalar blau da ratsin golden, sosai rigar ta k'arbi jikinta, gyale ta yawa fari, sannan ta ɗauki key na motarta, a hankali cikin ta kunta ta soma taka stair ɗin.

Har ta sauka babban falon, Abba da Ummi ne kaɗai a falon suna zaune, hira suke yi, ganin Ameesha ta fito sai Abba ya washe baki yana fad'in
"uwata an tashi?"

"Na tashi Abba Asbiti zan shiga, ina kwana? "

" Lafiya Lau Uwata fatan kin tashi lafiya? "

" Lafiya lau. "

" Ummi ina kwana? "

" Lafiya Ameesha, kin tashi lafiya? "

" Lafiya lau. "ta yi maganar ta na tafiya.

" a'a uwata ba zakiyi break bane? "

" Abba sauri nake yi, zanyi in na shiga."

"OK Allah ya bada sa'a."

"Ameen." ta amsa tana cigaba da tafiya.

Tana fita daga falon kai tsaye inda motocin gidan suke ta nufa, wata zafafaffiyar mota ta dauka, cikin kwarewa taba motar wuta, duk wanda yaga Ameesha cikin motar sai ya kalleta, don motar ta mugun da cewa da ita.

Kai tsaye Asbitin ta nufa, don suna practical ne a Asbitin Malam Aminu dake kano, Ameesha tana karantar Accident prevention and safety,Yau ce ranar da zasu fara practical d'in kuma da alama Dr da zai yi masu practical ɗin bashi da sauki, musamman in mutum ya yi duba da yadda Meena take mata magana.


Tana shiga daret ta nufi inda aka tana da don aje motoci, anan ta faka tata hand bag ɗinta ta ɗauka tare da ciro wayar ta, layin Meena ta soma kira, ringing biyu ta Meena ta dauka.

"Hello Meesha ya kin iso kuwa? "

" Eh gani cikin Asbitin kina ta wajen ina? "

" Please kiyi sauri ina wajen lab yanzu mutumin nan zai shiga, kuma yace koda minti biyu ya riga shiga bazai bar kowa ya shiga ba."

Kashe wayar kawai Ameesha tayi tare da nufa inda Meena take, Meena tana ganin Ameesha tace

"Wallahi Meesha kin kwafsa, yanzu ya shiga muje Allah yasa ya barmu."

Tsaki kawai tayi suka nufi hanyar shiga lab ɗin, gaban Ameesha ne ya faɗi ganin wasu yan class ɗin su a tsaye, suna isa wajen Ameesha ta cusa kai cikin lab ɗinn cikin dakewar zuciya.

Yana tsaye yana masu bayanin kansa sai ganin Ameesha ya yi ta shigo lab ɗin, k'ara bude ido ya yi da kyau ya tabbatar da ita ce dai wacce suka hadu jiya ta masa rashin kunya. Haɗa rai ya yi kamar bai taɓa dariya ba, dama fa shi ɗin ba gwanin dariyar bane, ko da yaushe fuskar sa a haɗe kamar ta sa............."


*Tofa ke Ameeshan Abba da wa Allah ya haɗa ki? Sai kun biyoni don jin ko waye.*



_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*


*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*5*
"Heeee." ya daka mata wata irin tsawa, da yasa Meena rugawa waje, don Meena fa akwai tsoro.

"Get out side."

"Sorry sir! Wallahi makara dai ko mukayi."

Ameesha ta yi maganar ta na ci gaba da tafiya.

"Baki ba ki ji abinda na ceba ne? ki fita min a lab, tun kafin na shigo ai na faɗa maku doka ta, don haka yi waje ba karatun kike so ba, da har zaki ce Wai makara ku ka yi noises nonsense kawai."

Cikin daure fuska ya ke maganar, in ba kana cikin lab ɗin ba, sai ka rantse da Allah ka ce ba shi ya ke maganar ba, don ko kallon inda take bai yi ba.

Cikin sauri Ameesha ta d'ago da kai, jin yadda ya zageta karaf suka had'a ido da shi, don dama duk maganar da su ke yi ba ta kalle , Shi ba tana ganin shi, sai ta saki wani malalacin tsaki tare da juyawa. Gaba d'aya yan lab ɗin sakin baki suka yi tare da bin ta da kallo.

Dai dai lokacin da za ta fita taji ya na faɗa masu sunan sa.

Wato *Asmad Abubakar ɗan Fullo*

Yace amma anfi sanin sa da *Dr ɗan Fullo*

Maimaita sunan Ameesha ta yi a zuciyar ta wato *"Asmad Abubakar ɗan Fullo* lallai zaka gane kuranka."

Ta k'arasa maganar tana fita daga lab ɗin.

In da Meena ke zaune ta nufa ranta a matukar ɓace, kallon ta Meena tayi tare da fashewa da dariya tace

"Kai Meesha wannan irin abu haka, kinga yadda kika yi kuwa kamar fulawar da ta samu yis da rana? " Meena ta kai Karshen maganar tana ci gaba da dariyar ta.

Wani malalacin kallo Meesha ta watsawa Meena ta ce

" Ke fa Meena baki da kirki me nayi da har kike cewa wata fulawa da ta sami yis da rana? Ke bama wannan ba wai tsoron mutumin can kikaji ne?"

"Sosai ma kina jin irin tsawar da ya zabga mana, kamar an busa algaita taf ai wallahi ya firgita ni, amma ke naga ko a Jikinki ?"

"Kwarai kuwa ko a jikina, dama ina neman sa, kuma ga shi yau Allah ya haɗa ni da shi, don haka wallahi sai na rama marin da yamin jiya." ta kai K'arshen maganar tana huci.

Cikin rashin fahimta Meena ta ce "ban gane ba Meesha dama kin san shi ne?"

Sweet ta ɗauko cikin jakarta tare da jefawa cikin baki ta ce

"Jiya muka haɗu a Sahad naje yin shopping, shi ne fa ya yi min crossing hanya don nayi masa magana sai ya mareni."

Mamaki ya kama Meena, don haka sai kawai ta zubawa Ameesha ido tana kallon ta, zuwa can tace

"Amma Meesha da zaki yadda in na baki shawara, wallahi ki bar mutumin nan, don baki da yadda za ki yi ki rama........."

Hararar da Ameesha ta jefeta da ita, shi ne ya hanata k'arasa maganar da take yi.

"Meena kenan kin manta halina ne hala?"

"A'a shawara dai na ke baki."

"To bani son shawarar rik'e kayan ki, amma ramuwa kuwa babu fashi."

Meena ta buɗe baki da niyyar magana, Ameesha ta yi saurin katse ta tace

"Please karki ce min komai, tashi muje nayi break don ban yi ba na fito, wallahi da nasan wannan nonsense ɗin mutumin ne, to ba zan fito ba sai na yi break d'ina."

Tashi Meena ta yi suka kama hanyar inda Rastaurants d'in da Ameesha ke cin abinci. Dai dai lokacin da suka dawo shi kuma ya ke fitowa daga lab ɗin, harara Ameesha ta cilla masa, sai ko akayi sa'a ya gani, girgiza kai kawai ya yi ya nufi inda motarsa take, hannunsa rike da bag d'in laptop ɗin sa.

Don tsakanin lab ɗin da office ɗinsa da tazara, don haka cikin motarsa ya d'auki hanyar da zata sada shi ga office nashi.

Waje su Ameesha suka samu suka zauna "ta ciro hand out ɗin tana dubawa, don suna da test idan sun koma school, ita ma Meena karatun take yi."


Karfe ɗaya da rabi suka bar Asibitin ,daga nan school suka nufa don suna da test,ba su fito ba sai biyu da arba'in da biyar, lokacin da suka fito a gaji suke bama kamar Ameesha da gaba d'aya bacci takeji, don haka suna fitowa bata tsaya komai ba ta nufi motarta, Allah yasa ma sun gama da laccan yau, burin Ameesha ta isa gida, sai da ta sauke Meena sannan ta wuce.

************************************

Zaune yake cikin kayataccen office d'in sa, iya had'uwa ofis d'in ya yi komai na ciki kalar brown ne da milk, katon table ne a gabansa mai d'auka da file na mutanen da zai duba. gefen dama wani dan gadone irin na duba marasa lafiya, gefen haggu kuma, karamin firij ne mai kyau, ga wani lallausan kafet da ke shimfide a tsakiyar ofis d'in, kai masha Allah komai na ofis d'in abin sha'awa ne.

Kallo d'aya zaki yi masa kasan yana cikin damuwa, don kuwa hannunsa ne cushe cikin tsakiyar kyakkyawan sumar sa dake kwance luf da shi, don yana samun gyara sosai, tsaki kawai yake jerowa a fili, duk motsin da zaiyi sai fuskar Yarinyar can ta bayyana ya rasa dalili.

Dan murmushi ya saki wanda iya karsa leb'e, da ya tuno yadda take magana d'azun, bai tab'a ganin Yarinyar ba sai jiya, amma kuma tunda suka had'u sai matsala ake samu, kamar wasu dai wanda suke jin haushin juna, shifa Yarinyar burgeshi take, musamman in tana rashin kunya.

Wayarsa ya jawo, wacce ke kusa da shi ya soma dialing number

"Hello ku turo su yanzu in duba su, don ina son fita."

Iya abin da ya fad'a kenan ya datse kiran.


Mintina k'alilan ya kammala da duba jama'ar da zai duba, gajiya ya yi sosai ya k'osa ya dan gana da gida, kila in ya sakarwa kansa ruwa zai samu sauki


Motarsa ya ɗauka kai tsaye gida ya nufa, a babban falo ya iske Nanne da Bobbo, duk'awa ya yi tare da gaisar da iyayen nasa, baki Alhaji Abubakar ya washe cikin jin dadin ganin ɗan nasa, shima Asmad din farin cikin ganin mahaifin nasa ya rufe shi. Cikin ladabi yace


"Baffa awarti jam! noi kugal?" ("Bobbo ka lafiya ya aiki?")

"Jam kolon asmad, noi kugal ma ambo?" ("lafiya lau Asmad, kai ma ya naka aikin?")

“Yettore jaumirawo Bobbo, wallahi hande kam mi somi siutare tan mi mari haje hande". ("Alhamdulillah Bobbo wallahi yau kam a gajiye nake hutu kawai nake bukata.")


" Na alari naa jotta to ad'onno mari debbo ni nanon non noo, alari jotta no awarti d'oo o hakkan noo ma diyam yiwugo be yamdu jamun" ("Kaji ba ka gaji ai da kana da mata duk da haka bata faru ba, kaga yanzu yadda ka dawo d'in nan zata baka ruwan wanka da lafiyyen abinci.")

Murmushi Asmad ya yi don yasan dama dole ne Bobbo ya masa maganar aure, burin sa kenan har kullum.

"Asmad mosii tan, nane maa o andino ko baffa wi'ata hala bangal tan haje mako"

A'a a bangal kam ai wakkati on ,bo ammi aam d'on wad'ana amm komi yid'i fuu, gamman na saito mi banyi. ("Kai Babbo shi fa aure lokaci ne, kuma Bobbo na tana yi min komai da nake so, don haka ba zanyi wani aure ba.")

Aa bangal kam dole a bangan, mid'o rufini maa gite taan dikka a fudda taskugo. ('a'a aure kam yinsa zakayi ina dai rakakane, amma tun yanzu gara ka soma shiri.")

Tab minkam bangal na jotta gam milarai momi yid'i, amma mid'o d'abbita be hakkilo harmi heba momi yid'i. ("taf ni kam Bobbo har yanzu ban ga matar da tayi min ba, zan dai ci gaba da bincika har na samu.")

denden ammi wad'i hunduko der hala man.("in ma baka samu ba ni zan zaba maka wacce ta dace da kai, kuma nasan zakayi farin ciki da zab'ina.")


Owii!


Sai a nan Nanne ta sa baki tace.


Allah subune ko lati hairu, ummu ayaha ayama yamdu maa ta fewa

"Allah ya kawo tagari Asmad, tashi kaje kayi wanka abinci na jiran ka."

Yana tashi ko bangaren sa bai kai ba, Bobbo ya dubi Nanne ya ce "na yanke wani shawara game da auren yaron nan, don banga yana da niyyar yin auren ba, amma zan tuntub'i Alhaji Bashir don inji ko ya Amince."

"Kai Alhaji wa zaka had'a da Asmad d'in? Nifa bani son azo rayuwaka suna b'aci fa?"

"Kar dai ki damu insha Allah Alhairi nake hangowa don haka ki taya mu da Addu'a, kuma had'in da zanyi kema zakiyi farin ciki."

"Allah ya taimaka, nasan Asmad bashi da matsala, zanyi masu Addu'an fatan Alhairi."

*******************
Alhaji Mansur ne tsaye a falon shi, cikin wani irin yanayi, me wuyar fassarawa. Da alama, ya kai karshen tunani ne amma bai samo mafita ba.

Ya yi amfani da hannunshi na hagu wajen kwankwasar kanshi, sai kuma ya nufi window ( taga) falon ya yaye labulen ya leka tare da kwada ma Najeeb kira iya karfin shi. Sai da yaga fitowar Najeeb ɗin, sannan ya sake labulen ya koma ya tsaya kamar ya hadiyi tabarya.

"Ka san Ameesha?" Alhaji Mansur ya faɗa bayan Najeeb ya zauna.

Ido da baki Najeeb ya bude sannan ya ce...

_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*


*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

``` Gaba ɗaya littafin nan naki ne my Cittah wato KHADIJAH A MUHAMMAD Allah ya bar k'auna ,inajinki har a zuciyata Kema kisa a ranki Zulayheart taki ce.```

*6*
" Bayan Najeeb ya rufe budadden bakin shi tun sa'adda ya ji sunan Ameesha a bakin mahaifinshi. Sai ya ce

" Na san ta. Akwai wani abu ne? Ko ba yar gidan Alhaji Taheer ba?" Shi ma Najeeb ya rufe maganar ta shi da tambayar mahaifin na shi.

"Eh itaa, to ka bude kunne ka jini da kyau."

Gyara zama Najeeb ya yi, tare da mai da hankalin sa kan Abban nashi. Sannan Alhaji Mansur ya ci gaba da maganar sa

"Kana jina ko Najeeb? so nake daga yau zuwa satin sama masu zuwa ka tabbatar ka cusa kanka gareta,so nakeyi nayi amfani da wannan damar don cimma burina."

Najeeb da kallo ya bi mahaifin nasa, don kwata kwata bai gane inda yasa gaba ba, kamar Alhaji Mansur yasan tunanin da Najeeb ya fad'a, don haka sai ya ce

"So nake kaje wajen ta da batun soyayya, ka san yadda zaka yi har ta soka wannan shi ne abin da nake umurtanka."

Zaro ido ya yi baki na rawa ya ce

"Abba kasan fa Yarinyar nan ba wata kunya ce da ita ba, kuma dai da kyar zata amince min don ba mutunci ne da ita ba."

Tun kafin ya kai karshen maganar Alhaji ke aika masa da wani mugun harara, wanda har ya firgita Najeeb din, cikin fushi ya soma magana

"Kai kam Najeeb anyi shashasha, yanzu kai a matsayin ka ka ce baka iya tsara wannan 'yar Yarinyar? To bari kaji dole sai kayi abin da na sanya ka."

Girgiza kai kawai ya yi, yana mamakin halin mahaifin nasa sosai.

"To naji Abba amma in ta amince ya zanyi da Rufaidat, kasan dai ita nake so."

Mtsww Alhaji Mansur ya ja wata doguwar tsaki, don takaici

"Kai fa Najeeb da alama kana son raina min hankali, ina ruwana da maganar Rufaida indai bukata ta zata biya, daga baya kasan yadda za'ayi da ita."

"Amma Abba baka tunanin a samu matsala, Yarinyar nan fa da wuya ta soni, kuma nima dai ba wani sonta nake yi ba. "

" Bani son rashin ta ido, kana jina koh? Maganar da ma fada maka dole ne kayi amafini da ita don abin da nake son yi kai zakayi Alfahari da shi ba ni ba."

" Yi hakuri Abba zan yi yadda kake so insha Allah."

Cikin ladabi Najeeb ya k'arasa maganar.

"Yawwa d'an Albarka haka nake so." Alhaji Mansur ya yi maganar cikin farin ciki.
Mik'ewa Najeeb ya yi yana mamakin halin mahaifin na shi.

Bayan fitar Najeeb, sai Alhaji Mansur ya manna bayan shi da kujera haka ya sauke wani numfashi me kauri.

Ya kai hannunshi yana shafa goshin shi, wannan ita ce hanya daya tilo da yake ganin zai yi amfani da ita don cikar wani buri na shi da ya dade a zuciyarshi.

Idan har wannan buri na shi ya cika, bai san irin kalar munan da zai yi ba.


Zumbur!Kamar Wanda ya tuna wani abu haka ya tashi, ya dauki key din motar shi ya nufi waje.

*****************
Nanne ce zaune a bedroom din Bobbo, magana yake fad'a mata kuma ga dukkan alamu maganar nada muhimmanci, cikin nutsuwa ta ce

"Amma kana ganin bamu shiga hakkin Yarinyar ba?"

"Maganar shiga hakki bata taso ba, tun da asalin maganar ba daga wajen mu take ba, abin da nake so kawai shi ne in samu Asmad din ya yadda."

"Kai ma Alhaji kasan bashi da matsala kuma yana kokarin yin biyayya, kar kayi tunanin haka, Ubangiji Allah ya sa haka shi ne Alhairi."

"Amin." Bobbo ya yi maganar cikin jin dadi.

" Yawwa da na manta Aneesa fa sun kusa komawa makaranta, don haka zata koma gida."

" Yaushe zata koma din?"

" Ranar Asabar zata koma."

"To Allah ya kaimu."

"Bobbo ya mike tare da fadin bari na leka wajen masu aikin gidan can."

A tare suka fita zuwa falon, suna shiga Shima Asmad na fitowa daga bedroom din sa, sauri yake yi don dama har ya fita mantawa ya yi shi ne ya dawo.

"Bobbo barka da rana. "

Asmad ya fada cike da ladabi.

" Lafiya lau Asmad har ka dawo ne?"

Bobbo ya amsa cike da kulawa.

"Eh amma yanzu zan koma, dama na danyi mantuwa ne."

Asmad ya karasa maganar yana nufa hanyar waje.

Najeeb ne a bangaren sa, ya na faman aikin kai kawo gaba daya kansa ya kulle ya rasa tunani d'aya da zaiyi. " shi damuwar sa Rufaida shin taya zata dauki maganar in har ta samu labari?"

Ya yiwa kansa tambayar da bashi da amsa, zuciyar sa tace " kawai kayiwa mahaifin ka biyayya tunda umurni ya baka."

Najeeb dai ya kasance d'ane mai biyayya sam baya tsallake maganar mahaifansa, don haka da sauri ya nufi toilet, wanka ya yo kana ya shirya cikin kananan kaya wanda suka amshi jikinsa, ya fashe jikinsa da turare mai sanyi kamshi, key na motarsa ya d'auka sannan ya yi waje."

Sai da ya isa bangaren mahaifiyar sa, bayan ya gaida ta sannan ya nufi parking space.


Tunda ya tada motar ya ke tunanin ta ina zai fara ne? Shi dai bai tab'a zuwa wajen wata budurwa da sunan soyayya ba Sai Rufaida, to yau gashi da rana tsaka Abban sa ya daura masa aiki, babban matsalar ma ita ce bashi ya ga Yarinyar yana so ba, da a ce shi ya ganta yana so to da da sauki, amma wannan umurnin da wuya in za'a ci nasara.

Rasa inda zai nufa yayi don haka kawai sai ya tsayar da shawarar zuwa makarantar su.

Bai zame ko ina ba sai makarantar su Ameesha, don yana tunanin tana school din, tunda yanzu sha d'aya ne na safe, parking ya yi a kusa da kofar makarantar yana jiran ganin fitowar Ameesha.

Najeeb na zaman jiran ganin Ameesha, ita kuwa tana Asbitin da take practical, suna zaune a karkashin wata itaciyar mangwaro hira suke ta sha da kawayenta.

Hira sukeyi hankali kwance, ita da Meena ce sai wasu 'yan class d'in su biyu, d'aya daga cikin wacce suke zaune ta kalle su gaba d'aya ta ce kunsan me?" ta ci gaba nifa wallahi Dr dan fullo burgeni da zai soni wallahi da na more..... "


Tun kan takai karshen maganar ta yi saurin katseta.

" Kina da aiki wannan mara mutunci ne zaki wani ce kina son sa? Taf lallai da babban aiki a gaban ki."

"Kai Meesha ke dai naga alamar ba zaku sha inuwa d'aya da Dr dan fullo ba, ko da yaushe akayi maganar sa sai ki soma wani hakikance wa."

Salmah ce ta yi maganar, a dan hasale, d'aya daga cikin wacce suke zaune a wajen.

" Allah ya baku Hak'uri, ni fa bani da matsala, amma na fada maki gaskiya tun wuri ki cire shi a ranki Kar ya zame maki wata wahalar, ni shi yasa nake Alfahari da kaina domin kuwa Allah bai doro min san maza ba ko kadan."

Hango Dr dan fullo tayi yana parking motarsa, taja wani dogon tsaki wanda yasa duk suka maida hankalin su kanta

"Meesha lafiya kike tsaki?"

" wancen dan rainin hankali ne kalleshi fa, yadda yake wani tafiya yana tak'ama, gaskiya Dr bai hadu ba."

Dariyar rainin hankali kawai Meena tayi, don tasan Meesha fad'a kawai ta yi, ko mara ido ya shafa Dr dan fullo yasan, hadadden guy ne, balle kuma masu ido matashi mai jini ajika, gashi kuma billion naira.

" Tashi muje kawai tunda yau bamu da lacca, muje gida daga nan ma zan biya na gaida Ummi."

Meena ta k'arasa maganar tana mik'ewa, su dai sauran shiru sukayi suna mamakin yadda Ameesha take raina Dr dan fullo.

Najeeb dai na zaune a kofar school har sha biyu da rabi, baiga alamar wata Ameesha zata fito ba, don haka sai kawai yaja motarsa da niyyar anjima zai kai mata ziyara gidan su.

************************************

Bobbo ya gyara zama tare da maida hankalin sa kan Nanne dake zaune kusa da shi.

"Yawwa kina jina ko mun gama komai da Alhaji Bashir, sannan su Baffa ma sun shiga maganar, komai anyi na yadda auren zai tafi babu gargada."

Nanne ta dubi mai gidan nata, cikin sakin fuska da kulawa tace

" Masha Allah Ubangiji ya tabbatar da Alhairi, sai dai har yanzu baka sanar dani wa ka zab'awa Asmad din matsayin matar aure ba."

Duk da taji ya ambaci Sunan Alhaji Bashir, amma tana son gasgata hasashen ta.

" yanzu zaki sani kuma zakiyi farin ciki da zabina ba kowa ba ce illa.......... "


_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:01 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*


*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

``` sadaukarwa ga KHADIJA S MUHAMMAD my Cittah```

*7*

Nanne ɗan murmushi ta saki, tana mamakin yadda mai gidan nata yake farin cikin sanar mata da maganar, ita ma nan take taji ta kosa ya sanar mata zabin da akayi wa Asmad din ta.

"Aneesa na masa zaɓi, don nasan ita ce kadai zata iya zama da shi cikin mutunci."

Kara gyara zama Nanne tayi, da jin zaɓin da aka yiwa Asmad, wani kyakkyawan murmushi ta saki, wannan shi ne burin da ta jima da shi a ranta, sai dai tayi shiru ne don kar ta shiga hakkin su, sai ga shi mijinta mai dogon tunani, shima ya yi irin nata nazarin."

Murmushi ta kuma sakewa a karo na biyu, wannan karon bakinta yak'i rufuwa, cikin jin dadi tace

" Allah ya sa Albarka cikin wannan haɗin, Ubangiji ya kade fitina, Allah ya basu zama lafiya da zuri'a tagari."

" Allahumma amin, Hajiyar Asmad ga dukkan alamun dai wannan maganar ta yau tayi maki daɗi?"

" Sosai kuwa Alhaji, ai wannan abin farin ciki ne, Allah ya tabbatar da Alhairin sa."

Haka suka ci gaba da hiran su, cikin jin daɗi.

*************************

Ameesha ce zaune cikin falon su, waya ce a hannunta da alama game takeyi ko chat, Haidar ne wato Yayanta wanda take bi mawa ya shigo falon da sallama.

Tayi saurin ɗago da kai ta ce

"Yawwa Ya Haidar, wallahi tun ɗazun zaman jiran ka nake."

Harara ya banka mata cikin daure fuska, Allah ya yo Haidar da iya haɗa fuska, baya k'aunar raini ko kaɗan, balle kuma Ameesha da ta rawan kai.
" Kai Ya Haidar daga magana sai ka soma min harara to na fasa."

Zama ya yi yana faɗin
" Kin yiwa kanki, tashi ki kawo min abinci."

"Kai don Allah nifa game nakeyi, kuma ina tashi zasu cinye ni."

A shagwabe Ameesha ta k'arasa maganar.

"Ba zaki tashi ba kenan?"

Ganin mugun kallon da yake watsa mata yasa ta mike, komai sai da ta haɗo masa sannan ta aje masa a gaba, komawa tayi kan kujera ta lafe, cike da jin takaicin yadda Haidar din ya mata.

" Yawwa k'anwata kin san me? Zo kiji? "

Haidar ne ya yi maganar, wannan karon fuskar sa a sake, kamar ba shi ba.

Banza ta masa tare da ci gaba da buga game ɗin.

" Meesha my lovely sister zo kiji please? "

Kallon inda yake ta yi tare

Please Login or Register in order to submit comment