Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka ina maki fatan alheri, Allah ya baki miji na gari Ubangiji ya nuna min auran ki muzo mu kwashi shokiiii*

``` Happy sallah Uncle HASSAN ATK & Uncle HUSSAIN ATK``` inji Sweet *SAFWAN* fatan kunyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana na baɗinbaɗaɗa

*17*
Zuru Ameesha ta yi tana kallon sa.

Shima Asmad ɗin zuba mata ido ya yi cikin wani irin yanayi.

A hankali ya girgiza kai, a zuciyar sa yace " *Lossing memory?* " Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Ashe maganar a bayyane ya yi ta sai jin muryar Meena ya yi ta ce

"What Dr Meesha tayi lossing memory? Hasbinallahu wani'imal walkil, Inna lillahi!

Haɗa rai ya yi yace " Please Meena kiyi shiru domin ban tabbatar ba."


Faɗin haka ke da wuya, sai ya nufi kofa da niyyar fita, zuciyar sa cike da tausayin halin da ta tsinci kanta a cikin.

Bai ko kalli su Abba ba, ya ce

" Alhaji bari na ɗauko wani abu a office."

Ita ma Ameesha maimaitawa ta yi, tana mik'ewa tsaye da sauri ta isa inda Asmad yake tayi saurin rik'o hannunsa ta kankame, sai kuma ta bata fuska.

"Cike da mamaki, haɗe da mutuwar jiki, Alhaji ya bi Ameesha da kallo, saboda yadda yaga ta kamkame hannayen likitan. Wannan bakon al'amari ne a rayuwar."

A hankali Dr ɗan fullo ya zame hannayen sa daga rikon da ta yi masa, ya zaunar da ita bisa gadon ya kalleta zuciyar sa a karye kamar zai zubar mata da hawaye "Zauna ina zuwa kin ji ko? Ya faɗa a hankali cikin dakin fuka. Ita dai kallon da ta yi wannan karon bata yi magana ba.

Wani murmushi ya saki, aiko sai ita dinma ta yi murmushin, kallon su Abba ya yi ya kuma maida kallon sa kanta, in har ya fahimta dai dai to Ameesha yunwa take ji, don haka sai ya ce

"Meena taimaka mana da tea please! Dr Asmad ya faɗa.

To kawai Meena ta amsa sannan ta soma haɗawa, cikin kankanin lokaci ta mika masa, shi kuma ya mikawa Meesha, ita dai Ameesha zubawa cup din ido tayi tana kallo don bata san ya zata yi da shi ba. Kamo hannunta ya yi yasa mata cup din ya ce

"Princess sha tea kina jin yunwa ko?

Cup din ta rike sannan ta maimaita abin da ya faɗa ɗin. Ita bata sha ba kuma bata aje ba.

Wani tunanin ya yi sai ya ce "Meena haɗa wani tea din ki zauna kusa da ita, sannan ki fara sha."

Yadda ya ce kuwa haka ta yi tana sanya cup din sai itama Ameesha ta kai baki, ta kurba sai ta aje shi a baki ta kasa haɗiyewa, don bata masan haɗiyewar ake yi ba.

"Meena ki kuma kurba sai ki hadiye ta gani." Dr ɗan fullo ya yi maganar.

Cikin ikon Allah kuwa sai Ameesha ta yi yadda Meena ta yi har saida ta shanye tas ta saki gyatsa. Sai ga zufa ya soma keto mata.

Murmushi ya yi irin mai nuna farin ciki.


Ji yowa ya yi ga su Ummi wanda suka yi jugum, suna kallon ikon Allah.

"Alhaji ku sameni a office yanzu."

"To" suka amsa, shi kuma ya nufi fita, ai kuwa sai Meesha ta mike ita a dole binsa zata yi, ita fa a nata tunanin duk inda Dr ɗan fullo ya yi shi zata yi.

"Jira ni yanzu zan dawo."

Still dai ta maimaita yadda ya ce, ganin tana don bata lokacin sa ga Aneesa tana ta kiransa sai kawai ya yi tunanin yin mata allurar bacci.


Wani dogon ajiyar zuciya ya sauke, tare da kuma duban Ameesha wacce ta zuba masa ido. Bai ɓata lokaci ba ya haɗa allura kawai ya yi mata, cikin zuciyar sa yana addu'ar Allah yasa ta farka lafiya ba tare da wannan lalura ba.

"Lafiya kuwa Dr me hakan ke nufi?" Muryar Alhaji Taheer kenan.

"No Abba kayi hak'uri ku dai sameni a office dina, nayi mata allurar ne don tana bukatar hutu."

"Tom Allah ya bata lafiya! Amma Please Dr ka taimaka kar wani abu ya sameta wallahi ita ɗaya ke gareni."

"Ku kwantar da hankalin ku insha Allah komai zai zo da sauki." Yana gama faɗin haka ya yi waje domin shi kansa yana da buk'atar ya samu nutsuwa har ya yi tunanin matsalar Ameesha.

Yana fita Ummi ta matsa inda Abba yake, sam bata cikin nutsuwa don gaba daya ta canza sosai hankalinta ya tashi da ganin yadda Ameesha ta koma, musamman maimaita maganar da ta yi a ɗazun abin ya tsaya mata a rai.

"Alhaji wallahi ina tsoron kar wani ciwon ya samu Ameesha, gani nake fa kamar hauka take yi fa!

"Inna lillahi! Ya yi saurin faɗa a zuciyar sa, don shi ɗin ma ya yi tunanin haka, domin kuwa yaji Dr ɗazun ya ce lossing memory, kenan ta manta komai? Kai ina hakan ba zai faru ba. Amma a fili sai ya ce "karki damu kiyi addu'a Hajiya babu wani abu da zai faru face da sanin Allah, don haka kawai kiyi hakuri ki barwa Allah."

"Na bar masa, amma gaskiya dai na firgita da wannan lamarin.

Alhaji Mansur dake gefe yana sauraron su, in ka kalli fuskarsa sai ka yi tunanin zallar tausayin Ameesha ya ke, amma ina a cikin zuciyar sa sai cewa ya yi "Allah na gode maka da haka ta faru, na samu hanyar raba ta da ɗana kenan, kai kuma Taheer sai a yi ta fama da biyan kudin magani tunda yartaka ta haukace." Ya karasa maganar tare da sakin wani mugun murmushi.

********************

A office Abba ne da Ummi zaune suna sauraron bayanin Dr, gyara zama ya yi cikin nutsuwa ya soma yi masu bayani yadda ciwon Ameesha ya ke.

*"Wato Alhaji gaskiya dai Ameesha ta samu matsala sakamakon bigewar mota, kuma dai gaskiya matsalar ta babba ce don ta samu ciwon nan da ake kira da mantau a turance kuma lossing memory amma asalin sunan ciwon (AMNESIA), shi wannan cuta ana samun ta ne musamman ga hatsarin mota, in kan mutum ya bugu cuta dai ta jikin k'wak'walwa.*

*Sannan kuma ita wannan cuta kala biyu ce, 1- akwai wanda in mutum ya kamu da ita zai manta komai na baya sannan kuma ko magana ka gama faɗa masa ba zai taɓa rikewa ba, kai ko hotonsa ya gani ba zay iya shaida ko shi ne ajiki ba, ko ya sha ruwa ko abinci zai iya mantawa yaga kamar bai ci ba.*

*2- shi na biyun yafi sauki, shi ne wanda zaka ga mutum ya manta komai na rayuwar sa na baya, amma kuma duk abin da aka faɗa masa ko aka koya masa zai fahimta har ya aiwatar, kamar dai yadda ita Ameesha ta keyi a halin yanzu.*

Dr ɗan fullo ya dire maganar sa cikin jimami, musamman yadda Ummi ke tsiyayar da hawaye, shi kansa Alhaji karfin hali kawai yake, amma ko kadan bashi a nutsuwar sa, jin irin ciwon dake damun yar tasa ba karamin daga hankalin sa ya yi ba.

"Babu komai Dr mun yadda da kaddara! Allah ya bata lafiya shi ne kawai addu'ar mu, amma Dr ita cutar bata da magani ne? In tana da kuma taya ake maganceta?"

"Tana da magani sai dai gaskiya bamu da kayan aikin ta anan Nigeria, amma dai in har mai lalurar ya ga irin abin da ya haddasa masa shiga tashi musamman in ya firgita to yana iya dawowa dai dai, sai kuma a rika tunawa mutum irin abin da yake aikatawa a rayuwarsa ta baya shi ɗin ma zai taimaka wajen dawo da tunanin mai lalurar ."

"Tom yanzu Dr ya kake ganin zamu yi?" Ummi ta yi tambayar hawaye na zuba.

"Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, kar da wannan ciwon yasa ki a damuwa insha Allah zata dawo dai dai, don zamu ci gaba da bincike tare da addu'a har Allah ya bata lafiya."

"Allah ya bata lafiya." Iya abin da Alhaji Taheer ya iya fadi kenan ya mik'e.

"Zan baku sallama gobe don allurar bacci nayi mata, sai cikin dare zata farka daga bacci, zuwa safe kuma sai ku tafi gida, domin dai bata da wani ciwo sai matsalar nan, sai ku tafi gida a ci gaba da addu'a da yawan ziyartar asibitin k'wak'walwa ko za'a da ce."

Daga haka suka fita daga ofis ɗin. Shi ma Dr tattara kayan sa ya yi ya tafi gida domin dai Aneesa ta addabe shi da kira.

Ko da suka koma dakin kowa zama ya yi, tare da buga uban tagumi suka yi jugum kowa da kallar tunanin sa.

Ameesha kam bacci take sosai bata farka ba sai kusan huɗu da rabi na dare, har a lokacin suna zaune babu wanda ya rintsa, ita ɗaya suke jira su ga farkawar ta ko da ta bude ido bata kalli inda su Ummi suke ba, sai ma lumshe ido ta kuma yi.

A wannan dare babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, tunda sassafe Dr ɗan fullo ya diro Asibiti don ganin yadda Ameesha ta kwana, sanda ya shiga bata farka ba don haka sai ya koma ofis.

Bata farka ba sai takwas, batawa kowa magana ba amma idonta a buɗe ya ke. ganin ta farka sai Abba da kansa ya je ya kira Dr.

Tare suka shigo da Abban, ya yi wa Ummi sannu tun kan ya gama rufe baki har Ameesha ta diro daga gadon ta rungu...


_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*


_*Gaskiya dai bani da bakin da zan ce wani abu domin kuwa masoya wannan littafin kun gama min komai, ko da yaushe ina samun sakonnin ku masu text message da masu kirana ta waya, fatan alheri nake maku ina jin dadin addu'oin ku, masu korafi kuyi hakuri wannan Nobel fa yanzu aka fara matukar dai kuna bina a hankali zaku fahimci komai, AMEESHA ma tana godiya da addu'ar ku.*_

*18*
Rike masa hannu ta yi gam, sai zarrare ido take kamar wacce taga wani abin tsora. Dr ɗan fullo kuwa kunya ce ta kamashi da sauri ya ja hannunta zuwa bakin gadon yana faɗin "Princess kin tashi? Barka da safiya!

Shiru ta yi ta dai zuba masa ido tana kallon bakin sa, murmushi ya saki don ya fuskanci halin da take ciki.

Mai da duban sa kan su Ummi ya yi ya ce
"Hajiya Princess fa yunwa take ji, matukar kuka ga ta natsu bata maimaita magana abu biyu ne ko dai yunwa ko kuma bata jin dadi."

"Insha Allah zamu kula, bari a bata shayi tunda babu abinci mai ɗan nauyi." Ummi ta yi maganar tana kokarin jawo flask. Sai ko ga sallamar yayyinta gaba daya, Ya Jaheed ne a gaba sauran suna binsa a baya. Kallo ɗaya ya yi masu ya shaida su ɗin yan'uwan tane musamman muguwar kamar da suke yi. Ita kuwa da kallo Ameesha ta bisu kamar idon zai fado, zuwa can kuma sai ta lumshe ido.

"Autar Ummi sannu ya jikin?" Abdul ya yi tambayar yana matsawa kusa da gadon.

Bata buɗe ido ba, amma ta maimaita abin da ya faɗa.

Hawaye ne yake tsiyaya daga idanuwansu, suna matukar tausaya yar'uwar tasu wai Ameesha autar Ummi ce cikin wannan halin, lallai ikon Allah ya fi gaban wasa. Kuka sosai Abdul ya yi domin dai dama shi ne abokin kaftawarta to kuma yanzu ga yadda Ubangiji ya maidata.

"Kunga bafa kuka za ku yi ba, ku yi mata addu'a ne." Ummi ta kai karshen maganar cikin kulawa ci gaba da fifitawa Ameesha shayi. Share hawayen su su ka yi sannan suka soma gaida iyayen nasu, Ya Jaheed ya mikawa Dr ɗan fullo hannu suka gaisa "Dr ya mai jiki?"

"To jiki Alhamdulillah sai godiyar Allah."

"Allah ya bata lafiya!"

"Amin." Dr ya amsa yana mikawa Ummi takardar sallama domin Abba ya fita daga dakin ya ce zuciyarsa zata iya bugawa matukar dai yana kallon Ameesha a irin wannan yanayin, ko a jiya da kyar ya kawo safe don yadda zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Ummi kam amsa ta yi tana masa godiya, lokacin shayi ya ɗan huce.

"Auta amsa ki sha! Tayi maganar tana mika mata cup din amma fir taki amsa, juyin duniya amma ta ki, Abdul ne ya je ya kira Dr. Tare suka dawo da shi, yana zuwa ya amsa ya kai bakin sa sannan ya mika mata yana faɗin
.
"Amsa Princess ki sha kin ji?" Babu musu ta amsa tare da kaiwa baki kamar yadda Asmad ɗin ya ce.

Kafin ta gama sha har sun gama kwashe kayan su daga ɗakin.

Wajen tafiya gida ma da kyar aka lallaɓa ta, don tirjewa ta yi ita fa adole babu inda zata je sai tare da Asmad, to shi dinma yana alhinin rabuwa da ita, sai dai bai nuna ba don karda su yi tunanin wani abun.

"Please Dr ko zaka taimaka mana ne ka kasance gida?" Muryar ya Jaheed kenan.

"No babu damuwa, domin ni ma gida zan ta fi." Dr ya ba shi amsa.

"Mun gode sosai Allah ya bar zumunci." Ya ida maganar yana nufa inda su Ummi su ke.

"Ummi Dr ya ce zai kai ta gidan tunda kinga fa bata yadda da kowa sai shi."

"Kar ka damu mudai mu yi fatan Allah ya bata lafiya." Ummi ta ida maganar tana kamo hannunta. Fisge hannun ta yi. Ganin haka sai Dr ya iso wajen ya kamo hannunta a hankali suka nufi inda motarsa ya ke.

Suma su Ya Jaheed suka nufi mota, babu wani bata lokaci suka isa gida har falo ya kaita, lokacin Meena ta gama haɗa break ɗin da za'a kai Asibiti, tana ganin Ameesha ta yi saurin aje flask ɗin hannunta tana faɗin

" A'a Meesha har kun dawo? Dr ina kwana"

Murmushi ya yi itama Meesha ta yi murmushin ya ce

" Kin san da yake bata da wani ciwo shi yasa."

"To sannu Dr da k'ok'ari mun gode sosai." Dai dai da shigowar su Abba.

Kallon agogon hannun sa ya yi ya ce " Ni kam bari na tafi gida, Ummi kusata ta yi wanka don ta ji daɗin jikinta. Amma sai dai a sami wanda zai koya mata"

Da sauri Ameesha ta fadi yadda ya ce. Dan murmushi Ummi ta yi tana kara godiya ga Dr sannan taja hannunta zuwa bedroom ɗinta tana faɗin


"Mu je kiyi wanka yana jiran ki a falo." Kamar ta san abin Ummi ta ke nufi sai ko ta ci gaba da tafiya.

Yana ganin sun tafi ya yi sallama da su Ya Jaheed sannan ya nufi fita. Ko da ya shiga lokacin goma saura don haka gidansu ya nufa, domin dai yasan Aneesa bata tashi ba don haka gara kawai ya tafi can ɗin, dama jiya bai samu zuwa ba.

*************************


Da sallama ya shiga falon Nenne da Bobbo ne suke zaune a falon suna hira, da alama yau Bobbo ba zai fita da wuri ba.

(Ha leddi o rongini o hofni saro mako.) Har kasa ya tsuguna yana gaida iyayensa.

(Der fertare be notani moo.) Cikin sakin fuska suka amsa masa.

(" Nanne nyami mo noi Aneesa waldi.") "Ya Aneesa ta kwana?" Nenne ta yi tambayar.

("O jamo kolon. Kenya minani odon wi'a o waran hamon.") "Lafiya lau ta kwana, jiya na ji tana faɗin zata zo nan gidan."

(Usoko! Allah waddu mo jam.") "Madallah! Allah ya kawo ta lafiya."

("Ameen" o noti Nenne welo minanta fa!) "Ameen ya amsa. " Ummi yunwa nake ji fa!

("To hami hauta ne nyamdu man gam minin maa jotta min hasiti.") "To bari na hada maka, muma da yake yanzu muka gama yin break ɗin.


("Haba Asmad noi a wurtata sare a hasiti? Bobbo wolwi der mettam beram.") "Haba Asmad ya zaka fito gida ba tare da ka tsaya ka yi break?" Bobbo ya yi maganar cikin ɗan faɗa faɗa.

("A'a Bobbo daga jamdi jego mi wurti sare gam mid'o mari nyoudo, mi yahi milari noi o waldi, den mi yalti en hofni dira wali didi mi warai.") "A'a Bobbo ai tun shida na fita don ina da wata mara lafiya, na je duba jikin ne shi ne na biyo nan mu gaisa tunda jiya ban leko ba."

("Towo jotta minanai hala, mi tamma daga sare a wani a darai a hasiti, Allah wasu barka.") "Aiho yanzu na ji magana, ai nayi tunanin daga gida kake shi ne baka tsaya ka karya ba, Allah ya yi albarka."

( Hokkilo don wali Asmad nyamata kasitari mako ha o timmini, o warti falo ha Nenne en wonii.) Cike da kwanciyar hankali Asmad ya ke yin break ɗinsa har saida ya kammala, falon ya dawo inda su Nenne suke

(" Nenne mi hiran sare.") "Nennezan na k'arasa gida!

("Allah hore jam, hofnu Aneesa.") "To Allah ya kaika lafiya ka gaida Aneesa."

("O nanan insha Allah." Asmad jabi moo.) "Za ta ji insha Allah." Asmad ya bata amsa yana fita.

Lokacin da ya je gida a falo ya iske Aneesa da sauri ta tashi tana faɗin

"Hamma daga ina kake?

"Daga Asibiti nake don akwai mara lafiyar da na je dubawa." Ya bata amsa yana zama a kujerar da ke kusa da ita.

Gyada kai kawai ta yi, haka kawai ta ji sam bata so ya fita ɗin ba, domin ita har ga Allah tana tsoron ganin sa da yammata balle kuma ya ce zai kara aure, bata k'aunar ganin wannan lokacin.

"Aneesa tashi ki haɗa min ruwan wanka, kin yi break?"

Da kai ta amsa masa don dai jinta ya yi sanyi.

"Ok mu je in yi wanka, kema ki yi ko kin fasa zuwa gidan su Nenne ɗin?

"Lah! Hamma zan je, naga baka yi min maganar ba ne."

"Ok to ai yanzu na yi maki sai ki shirya har na faɗawa Nenne zuwanki."

Daɗi ya rufe Aneesa da jin zata je gidan Nenne, aiko cikin saura ta shirya, shi ma a lokacin Asmad ya gama shirin sa jerawa suka yi har mota.

*Gidan Alhaji Mansur*

"Kai Najeeb kana jina? Bai jira amsar da Najeeb ɗin zai bashi ba sai ya daura a maganarsa.

"Kana jina ko! Kai aiwatar da abu daya da nake so, sai abu na biyu, ina tunanin baka manta da maganar babu aure tsakanin ka da wancen mahaukaciyar yariyar ba?"

"Abba wacece mahaukaciya?"

"Kai bana son shashanci Wancen yarinyar da bata da wani aiki sai SANGARTA. Uban wa ya sani ko haɗa baki suka yi da likitan har ya ce ta samu ciwon mantuwa, don nasan halin Taheer tsaf ba zai bari a ce Yar shi ta haukace ba nikam nasan hauka take yi sam bata aikin masu hankali."

"Abba yanzu baka tausayin halin da Ameesha ta samu kanta? Wallahi duk wani mai imani in har yaga yadda Ameesha ta koma zai tausa..."

Tun kun kafin ya gama rufe baki Alhaji Mansur ya sauke masa wasu mahaukatan mari har biyu, wanda suka yi mugun shigan Najeeb.


_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*Saboda yadda ki ke son wannan Nobel din yasa na baki kyautar wannan page din na yau, MARYAM BINTU hakika kin cancanci fiye da haka, amma ki yi haquri da wannan, fatana Allah albarkaci rayuwarki Ubangiji ya rabani da sharrin makiya, YAR MUTAN RANO tana k'aunar ki har cikin ranta.*

```Masu korafin in bude groups, don Allah ku yi hakuri ba sai na buɗe group daban ba, a kawai groups na yan'uwana da yawa, irin su UMMYN YUSRAH NOVEL, MARYAM MUKHTAR FAN GROUP, da dai sauransu duk ina post a ciki, ba sai na buɗe ba, ina godiya da shawarwari Allah ya barmu da k'aunar juna.```

*19*
Sadda kai k'asa Najeeb ya yi, cikin zuciyarsa yana mai tsantsan jin takaici da halin mahaifinsa. Muryar Alhaji Mansur ya ji yana faɗin "tashi ka bani waje shashashan banza kawai, kuma dole ka yi yadda na ke so , ko kuma wallahi ranka ya yi mummunan ɓaci."

Jiki a sanyaye ya mike bai nufi inda sashin sa yake ba, sai ya nufi wajen motarsa ya ɗauka, cikin nutsuwa ya tashi motar bai zame ko ina ba sai gidan Alhaji Taheer. Ya yi parking sannan ya k'arasa cikin gidan.

A babban falo ya samu su Abba zaune suna hira da Ummi, gefe guda kuma Ameesha ce ke kwance akan three sitter. Cikin sakin fuska Abba ya amsa masa sallamar da ya yi.

Tsugunawa ya yi har kasa ya ce

"Ina kwana Abba ya mai jiki?"

"Lafiya lau Najeeb mai jiki ta ji sauki, ya su Alhajin?"

"Yana lafiya ya ce a gaida ku!

"Muna amsawa."

Kansa ya kuma saddawa da alama magana ya ke son yi. Abba ya fahimci haka

"Kamar kana son yin magana ko?" Alhaji Taheer ya tambaya.

"Eh! Abba. Ya bashi amsa

"Ok ina jinka." Ya ida maganar yana maida hankalinsa shi.

"Ehm uum! Dama kan maganar Ameesha ne, Abba don Allah karka fasa bani ita, wallahi zan iya aurenta a ko wane hali take."

Murmushi Abba ya yi cikin jin daɗi da maganar Najeeb ɗin, don har cikin zuciyarsa yana tunanin yadda lamarin zai kasance, musamman daga halin da Ameesha ta samu kanta a ci, amma yanzu Alhamdulillah tunda ga Najeeb yana jaddada masa son da ya kewa Ameesha ɗin.

"Haba karka damu da wannan insha Allah Ameesha taka ce, bata da wani miji da ya wuce kai."

"Na gode Abba." Ya yi furucin cike da jin dadi.

Kallon agogon hannunsa ya yi tare da mik'ewa, don tuni Ummi ta bar falon

"Najeeb zan fita! In ka koma ka gaida su Hajiyar." Ya kai karshen maganar yana fita.

Shi kuma matsawa kusa da ita ya yi ya ce

"Meesha ya jikin?"

Idonta biyu amma in ba ka duba da kyau ba sai ka ce bacci ta ke yi, ko da ya yi maganar tana jinsa amma da yake yan maimaita maganar basu kusa ko ɗago kai ta kalleshi bata yi ba, domin dai wannan muryar bata saba jin taba, ita kuma so take ta ji irin wanda ta saba ji. Haka ya gaji da magana ya tafi.

Yana fita Meena ta shigo falon, ganin ta ita ɗaya a kwance sai ta matsa tana faɗin

"Meesha ke ce kawai a falon?"

Bata yi magana ba sai buɗe dara daran idonta da ta yi tana kallon Meena ɗin. Gyara zama Meena ta yi tare da sanya game a wayar Ameesha, kuma shi ne game din da Ameesha ta fi so akan ko wanne. Zuba wa wayar ido ta yi tana kallon yadda Meena ke buga game ɗin, har wani murmushi ta ke yi alamar abin ya mata daɗi, ganin haka sai itama Meena ta ji dadi.

"In baki kema ki buga?"

Bata fahimci me Meena ta ke nufi ba, don haka sai ta ci gaba da kallon wayar, mika mata wayar ta yi , amma sai ta bata rai, cikin sauri ta kamo hannun Meena ta daura akan wayar alamar dai ta ci gaba da bugawa .

Da ta fahimci nufin ta sai kawai ta ci gaba da bugawar, haka suka kasance cikin farin ciki, domin dai a duniya Meena tana son farin cikin Meesha.


*************************

Aneesa ce zaune a can kuryar gado, ta zabga uban tagumi kai da gani kasan cikin tunani take, can dai ta sauke tagumin tare da jawo wayarta dake dan nesa da ita. Number ta lalubo sannan ta danna kira ringing biyu aka daga wayar.

"Hello k'awata gaskiya fa ina cikin wani mawuyacin hali." Ta yi maganar ciki rashin nutsuwa.

Daga ɗaya bangaren ta amsa

"Anee mai ya sameki?"

"Ki bari kawai wallahi ina cikin matsala."

"Ke nifa bani son wannan abin na, ki yi min magana sak bana don kwana kwana."

Ajiyar zuciya Aneesa ta sauke ta ce

"Kinga wai fa ciki ne da ni, kuma ke kinsan bana son haihuwa a irin wannan lokacin."

Mtsss Rukky ta ja tsaki, ta ce

"Amma wallahi Aneesa har kin bani haushi, yanzu don Allah saboda cikin ne ki ka tada hankalin ki?"

"Dole in tada hankalina duka yaushe aka

Please Login or Register in order to submit comment