Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da turo k'aramin bakinta ta ce

" Ba yanzu ka gama min masifa ba, kuma kaki tsayawa kaji abin da zan ce."

" Oh! Sorry my sister, faɗi inji mai kike so? "

Murmushi ta saki ta ce

" Dama so nake in ce maka laptop ɗina ya lalace, jiya da zan dawo daga school."

" Yanzu ya kike son a yi?"

" Abba nake jira ya dawo, sai in amshi kudi sai ka sayo min sabo, tunda wancen ya tashi aiki."

" Je ki ɗauko." ya yi maganar yana aje plet ɗin.

Ta mike da zumar tafiya, sai taji sallama a kofar falo, amsawa ta yi tare da tambayar "waye? Dai dai sanda ta isa kofar.

Ganin mai bawa fulawar gidan ruwa yasa ta ce

" Lafiya kuwa? "

" Lafiya lau Hajiya dama bak'one ya ce a kira ki."

" Bak'o?"

Tayi tambayar tana kallon wanda ke tsaye gabanta.

"Eh Hajiya."

"To ina zuwa."

Shi ne iyakar abin da Ameesha ta faɗa, mamaki sosai ya rufeta, ita ai bata yi magana da wani akan yazo gidan suba "to waye wannan" ta yiwa kanta tambayar da babu amsa.

Bedroom ɗin Ummi ta nufa, don ko takan Haidar bata yi ba, akan sallaya ta samu Ummin, zama tayi gabanta tare da rika hannunta ta ce

" Ummi kinji wai wani yazo nema na? "

Shafa Addu'an Ummi ta yi ta ce" To ya baki tafi ba?

" To ni ai Ummi ban San shi ba, kuma ai da nasan da zuwan shi zai kira wayata."

Ameesha ta yi maganar ranta a ɗan ba ce.

"Haba Ummin Abba ba'a haka, tashi ki ɗauko gyalen ki, kije kiga ko waye daga nan ki hada masa abin sha kin ji ko?"


Daga kai Meesha ta yi, badon ranta ya so ba, amma tunda Ummi ta bata dama bari taje, ji take kamar ba ita ba, tunda take bata taɓa zuwa harabar gidan su da sunanan tsayuwa da wani ba.

Amma yau gashi wani ya tako har gidan su, tana jinjinawa ko waye wannan da kokari. Ko ruwa bata ɗauka ba, ta nufi wajen dama jikinta fes yake, fuskar ta shafe yake da powder.


Cikin nutsuwa ta ke tafiyar, jikinta ko ina iska ke kada ta, tunda nesa ta soma shakar daddar turaren sa, tsaye yake ya jingina bayan sa jikin motar, waya ce a hannunsa da alama waya yake, can nesa da shi ta tsaya, tana kallon sa.

Bai san ta iso ba har sai da yaji kamshin turarenta ya cika wajen, a hankali cikin nutsuwa ya juyo da fuskar sa zuwa gareta, fuskar nan tashi ɗauke da murmushi

" Barka da zuwa Gimbiya sarautar mata."

Shi ne abin da ya faɗa, yana kallon Ameesha, dan tabe baki tayi cikin jin kai ta ce

" bawan Allah ban gane ka ba, daga ina kuma wajen wa kazo? "

Murmushin dai ya kuma yi ya ce

" Haba Ameesha baki dai gane niba, da farko dai sunana *Najeeb Mansur* dan Alhaji Mansur abokin Abban ki."

Zaro ido tayi cike da mamaki ta ce

" oh! Sannu da zuwa Najeeb ya Alhaji da Momi? "

Ameesha ta tambaya fuskar ta ba yabo ba fallasa.

" Lafiya lau Ameesha, zakiyi mamakin gani na a gidan ku ko? To wannan ba'a bin mamaki bane domin kuwa mai son ɗan tsuntsu shi ke binsa da jifa, gaskiyar magana dai nazo maki da wata magana ne mai muhimmanci, sai dai tunda baki san da zuwa na ba, ina son ki bani lokacin da zan dawo mu tattauna."

Kallon sa take tunda ya soma magana, Najeeb dai kyakkyawa ne son kowa kin wanda ya rasa, da ganin sa kasan da nutsuwa a tattare da shi, sannan kalaman da ya yi amfani da su wajen yi mata magana sunyi mata dadi. Amma sai ta basar tace

" No nikam bani da wani time, don kullum ina school yau ma kayi sa'a ne ka iskoni a gidan."

" Haba princess Meesha ki taimaka, matukar baki bani dama na fayyace maki abin da ke raina ba, tom zan iya shiga wani hali, kiyi hak'uri ki bani dama? "

Da muryan tausayi ya k'arasa maganar.

Yadda ya yi maganar har ya kusan bata dariya ya yi, amma sai tayi saurin fuskewa ta ce

" kana iya dawowa nan da two weeks."

Zaro ido ya yi a ɗan firgice ya ce

" Haba princess ina laifin two days, wallahi two weeks ya min yawa."

Ta gaji da jin maganar, tana son ko mawa cikin gida don haka ta ce

" to one week ya yi? Don ina da test a school, a cikin week din nan."

"Allah ya kaimu amma ba haka naso ba, sai dai kuma tunda princess ce ta zaba bani da yadda zanyi."

Har ta kama hanya zata tafi ya ce

" princess baki bani phone number ɗin ki ba please ki bani? "

Wayarsa ta amsa tasa masa numbers ɗinta sannan ta wuce. Shi kuma a nashi ɓangaren wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, da ya gama da wannan, don yasan tunda ya samu number ɗinta ya yi mai wuya.

Maimakon ya yi farin ciki da ya samu ta ɗan Amince da shi, sai takaici ya rufe shi, don yasan abin da zai aikata ba abin kirki bane, tunda yaudara ce zaiyi, takaici sosai da tausayin ta suka rufe shi.


A gefe ɗaya kuma yana yaba kyaunta da nutsuwarta, tabbas da a ce bashi da Rufaidat tofa zai iya auren ta, sai dai shi yanzu Rufaida kawai yake kallo a matsayin mace.

Ko da yake jan motar haka ya yi ta tunanin abin da zai aikata, Allah ya sani umurni zai cika ba yin kansa bane.

*********************************

Zama ya yi kusa da Nanne ya ce (o jod'i haa kombii Nanne! owi

"Nannena da alama yau dai kina tare da farin ciki?" ("Nanne aam ko fe'i hande banta ad'on seyi? ")

" Sosai kuwa Asmad tunda burina ya kusa cika." ( "sosai mid'on seye gam heje aam badake hubugo Asmad." )

Dariya ya yi wanda ya kuma fito da asalin kyaun shi ya ce ( o jali ha wad'ega mako beddi wartugo dendenta owi)

" Nannena kenan, hala saudiyya zaki kuma zuwa? " (" Nannena aam d'oo kaam makka na alorata? ")

" A'a ba saudiyya bane mafarkina na son Asmad dina yayi aure shi yake shirin tabbata." (' a'a na maka sam miyahata koid'ol aam on badake wartugo gonga Asmad aam badake bangugo. ")

" Kai Nannena yo nida ko budurwa bani da ita kike maganar aure?" ("Kai Nanne aam min mowala ko berajo awolwinta hala banga?")

" Ai uba nagari tuni ya samar maka da mata yar kirki."( "ai dottijo gonga hebani maa debbo jabdubo")

" Nanne kina nufin Bobbo ya samar min mata? Oh! Shet." ( "Tani wiaam bobbo aam subani aam debbo? Or toskiyam")

Asmad ya yi maganar cikin wani irin yanayi. (Asmad wi'ika der mettam beram)

" Eh ya zabar maka kuma mata yar kirki, wacce kai kanka zakayi Alfahari." (" E of subani Maa debbo kand'o bema to'o larima ko an alarima saito a mani moo")

Nanne ta yi maganar cikin kwantar da hankali. (Nanne wii banjin don wallina moo hakkilo.)

" wacce mai sa'ar Bobbo ya zaba mata ni a matsayin mijin aure? " (" mard'o sa'a to be bobbo subani aam?")

" Aneesa."

Nanne ta faɗa babu shamaki. (Nanne not moo)

Wani irin zabura Asmad ya yi bakin sa na rawa ya ce "What........?" (Asmad haftii hunduko mako don wama owi "d'ume........?")



_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:02 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

``` Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah```

*8*
Kallon Asmad din Nanne ta yi don ganin irin zaburar da ya yi ta ce

" lafiya kuwa Asmad? Ko zaɓin ne bayyi maka ba? "

Saurin dai dai ta nutsuwar sa ya yi, da ya tuna fa a gaban Nanne yake. Yace

" Haba Nannena ta ya zan ce zaɓin ku bayyi miba? Kawai dai gani nayi kamar Aneesar bazata yadda da hadin ba. "

Murmushi Nanne ta yi cikin jin daɗi, da samun Asmad ɗin matsayin da don bai taɓa jayayya da duk wani umurnin su ba, Koda hakan bayyi masa ba amsa ya ke ba tare da ya nuna ɓacin ransa ba.

" Haba karka damu ai Aneesa 'Yar'uwar ka ce, kuma da amincewar mahaifin ta hakan zata faru, don haka kayi hak'uri da zaɓin insha Allah zakayi Alfahari da shi."

Gyada kai kawai ya iya yi "ya mike ransa a dan bace" don bai so wannan zaɓin ba, to amma tunda Bobbo sa ya masa ya zama dole ya yi biyayya.


Kai tsaye yana fita daga falon Nanne, ɓangaren sa ya shiga kan kujeran dake falonsa ya faɗa yana ambaton Allah, da ya kawo masa ɗauki cikin wannan bak'on lamarin da ya kunno masa kai, abin da ko Mafarki bai taɓa tunanin gani ba. Amma yau sai gashi ido buɗe yaji kuma ya gani, da sauri ya mik'e tunawar da ya yi yana da shiga *CS* a dai dai wannan lokacin.

Bedroom ɗin sa ya shiga, ruwa ya watsawa jikinsa, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya riga da wando, bai koma falon Nanne ba sai ya nufi motarsa, ba kuma don wannan maganar ce ta hana shi komawar ba, a'a ganin da ya yi lokacin ya kusa, har ya buɗe mota zai shiga sai kawai ya fasa, ya zama dole yaje yawa Nannen sa sallama, ba haka ya saba yi ba.

Asmad kenan yaro mai neman Albarkan iyayen sa.

***********************************

Ameesha na shiga cikin falo, bedroom ɗin Ummi ta zame, wannan karon Ummin ta idar da abin da takeyi

"Ummi na dawo "

Cewar Ameesha tana zama abakin gadon ɗakin Ummi.

" Madallah! sannu da dawowa, har ya tafi ne? "

" Eh Ummi."

Ta bata amsa a takaice.

Dan juyo wa Ummin ta yi ta kalli Ameesha, ganin ta kwanta sai Ummin ta girgiza kai, a ranta ta ce

" Allah ya shirya min ke Ameesha, Yarinya kullum ciki zurfin ciki. Da Abban tane da yanzu ta soma bashi duk labarin abin da ya faru, amma ji yanzu ko ta sanar min yadda su ka yi. "

" Ummi wai kinsan waye yazo wajena? "

Ameesha ta yi maganar tana ci gaba da latsa wayarta.

" Ta ina zan sani Ameesha, nida ko falo ban lek'a ba har kika dawo. "

" Najeeb Yaron Alhaji Mansur abokin Abba."

Ameesha ta yi maganar ba tare da ta ɗago kai ba.
Dan ware ido Ummi ta yi cikin mamakin jin abin da Ameesha ta faɗa

"Najeeb kuma? To mai ya ce maki? "

" Ya ce zai dawo na bashi rana, shi ne na bashi."

" Allah ya tabbatar da Alhairi."

Shi ne kaɗai abin da Ummi ta iya faɗi, don zuwan Najeeb wajen Ameesha ya bata mamaki, sai dai kuma bata tashi hankalin ta ba, don tasan Najeeb yaro ne nutsatse bashi da wata matsala.

"Tashi muje kicin kin San yau Abban ki zai dawo."

Ummi tayi maganar tana kallon Ameesha, ɗan turo baki tayi tace

" Allah Ummi in mutum ya shiga kicin duk sai ya fito da gajiya."

" Allah ya shirya ki, ke kam ban san irin ki ba, amma in aka dafa kin iya bude baki ki ci? Zanga wanda zai rik'awa mijinki abinci."

" Ai Ummi na iya kawai shiga kicin din ne bana so a koda yaushe. "

" To kuma dai wannan ke kika sani, tunda baki zuwa ki gyara min bed ɗin akwai turaren wuta."

Ummi ta karasa maganar tana fita.

*********************************

Alhaji Mansur ne zaune tare da abokin sa Alhaji Kabiru, hira sukeyi hankali kwace, daga gani kasan abokan juna koma a kira su da aminan juna, Alhaji Kabiru ya muskuta tare da gyara zama ya ce

"Wai kuwa Alhaji ina maganar da mukeyi da kai waccen lokacin? "

" Tana nan koba ta Alhaji Taheer ba? Ai tuni har na soma aiwatar da k'udurina, kaima kasan bana wasa ta ɓangaren kuɗi, kasan Allah Alhaji sai nayiwa Taheer walak'anci, duk kuɗin da mutumin nan yake samu, amma don na ce ya bani contena ɗaya na shinkafar,da aka shigo masa da ita, shi ne ya ke neman wulak'antani, wallahi abin da zan masa sai ya fi wanda ya min. "

" Ai na tura Najeeb wajen 'yarsa kasan yafi sonta da kowa cikin ya'yansa? Da ita zanyi amfani.


Jinjina kai Alhaji Kabiru ya yi yana yabawa da karfin hali irin na abokin sa.

**********************************

Fitowar ta daga toilet kenan ta ji wayarta kirar Infinix dake kan drissing mirror tana riging don neman agaji, a hankali ta matsa wajen wayar ta zurawa number ɗin ido tana kallo, a zuwan ko zata gane mai numbers ɗin gani har yana shirin tsikewa bata gane lambar ba, yasa takai zara zaran yatsunta tare da ɗaukar wayar ta kara a kunne ba tare da tayi magana ba.

" Assalamu Alaikum."

Ya yi maganar cikin nutsuwa.

Shiru ta yi ba tare da ta amsa ba, sai ma tunanin mai muryan da ta faɗa yi.

" Hello." ya kuma faɗi a karo na biyu.

Cikin siririyar murya ta ce

"Hello wake magana please? "

Ajiyar zuciya ya sake a hankali, har yana lumshe ido ya ce

" Najeeb ne."

Dan murmushi Ameesha tayi tare da faɗin

" Oh! Sorry Najeeb wallahi ban ɗau muryan ka bane, ya Momi? "

" Tana lafiya." ya bata amsa.

"Kina gida ne in shigo yanzu? "

Girgiza kai ta yi kamar yana ganin ta da kyar ta buɗe baki ta ce

" A'a "

" Haba princess kiyi hakuri, wallahi ina son ganin ki a wannan lokacin."

Mtsssw taja tsaki ta ce

" Please wai Najeeb mai kake nufi ne? "

Wata mayaudarin dariya ya yi ya ce

" Ki bani dama nazo yanzu sai in fayyace maki abin da ke raina."

Kosawa da maganar tayi shine yasa ta ce masa "sai yazo." da haka su ka yi sallama.

Minti goma sha biyar ya kawo shi gidan, wayarta ya kira yana sanar mata da zuwan sa, tana zuwa kadai ta iya ce masa.

Waya ta ɗaga ta kira Mai ba fulawa ruwa, ce masa tayi ya kaishi falon baki, Allah ya yo Ameesha da son kwalliya koda yaushe cikin gayu take, matsalar dai tafi sa kananun kaya, Yau ma kamar ko da yaushe cikin gayunta take na doguwar riga wacce tayi mugun amsan jikinta, fuskar ta tasha kwalliya sosai tayi kyau, turare ta kuma fesawa sannan ta nufi fita.

Koda ta fita a bedroom din Ummi ta yada zango, kallonta Ummin tayi ta saki murmushi ta ce

" Autana sai ina haka? "

Dan ya mutsa baki ta yi ta ce

" Najeeb ne yazo yanzu."

" Ji sakarci shi ne kuma kika shigo nan? maimakon ki wuce babu kyau fa wulakanci Ameesha."

" Zuwa nayi kawai in gaya maki, amma yanzu zan tafi."

"Yawwa 'yar Albarka tashi ki tafi masa da ruwa."

"To." shi ne kaɗai abin da Ameesha ta faɗa ta mike.

Yau ɗin ma haka ta fita ba tare da ta ɗauko masa ruwan ba, shiga falon tayi da sallama ta samu waje ta zauna, ba tare da ta ce masa ta tafasa a sauke ba.

Kallon ta ya yi da murmushi ya ce

" princess da alama yau sarautar ta motsa."

Ko ɗaga kai bata yi ba balle ya samu arzikin magana. "

Shiru ya ɗan ratsa na mintuna, yana jiran ta yi magana, taki sai latsa wayarta da takeyi, ganin shirun ya yi yawa yasa ya ce

" Ameesha? "

Ɗago da kai tayi ta kalleshi bata ce komai ba.
" Kin san me ke tafe dani?"

Girgiza kai ta yi, alamar a'a.

" Karki yi mamaki in nace maki maganar soyayya ce ta kawo ni wajen ki."

" What.... " ta faɗa tare da ɗago kai ta watsa masa wani harara ta kuma bude baki ta ce.........


_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:02 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

``` Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah```

*9*
Girgiza kai ta yi tace

" Ayya Najeeb ai Ameesha bata soyayya, don bata iya wa da kayan takaicin da ke cikin soyayya."

Kasak'e ya yi yana kallonta, tare da mamakin furucin ta, in har hasashen da yake yi gaskiya ne, kenan Ameesha bata tab'a soyayya ba.

"Kayi hakuri Najeeb gaskiya ba zan iya amince maka ba, don ban son in jefa zuciya ta cikin halaka, shi yasa ko kadan bana ɓata wa kaina lokaci."

Tana gama faɗin haka ta yi waje.

Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, ganin ta tashi tafita, tabbas sai ya yi da gaske hak'an sa zai cimma ruwa, da wannan tunanin ya tashi jiki a sanyaye.

Ameesha na barin falon bak'in bedroom dinta ta shiga, hankalin ta ya tashi b'ata tab'a soyayya ba, haka kuma bata jin zata iya soyayya da wani, wayarta ta jawo ta dan nawa Meena kawarta kira.

Bayan sun gaisa ne Ameesha ke sanar mata da yadda sukayi da Najeeb din. Daga bangaren Meena ajiyar zuciya ta sauke ta ce

" Bai kamata kiyi saurin fada masa haka ba, kamata ya yi ki zauna kiyi dogon tunani akan maganar, musamman dai kin ga Najeeb ba wai mutumin banza ba ne."

" shi yasa na kira ki ai yanzu ya kike ganin za'a yi? "

" OK mu haɗu a school gobe. "

Daga haka sukayi sallama.

Bayan sunyi sallama ne, ta mike ta koma falo jin alamar shigowar Abbanta, ai ko shi ɗin ne yana zaune ga yayyenta suma a zaune kusa dashi, da sauri ta karasa tana fad'in
" oyo-yo Abbana welcome back."

Murmushin jin daɗi ya yi ya ce

" Thanks my daughter ya gida? "

" Lafiya lau Abba, gaskiya nayi kewarka fa."

Ta karasa maganar cikin shagwaba.

" Zo zauna uwata, ayi min Afuwa nima ina can tunanin rashin ki kusa dani ya dameni."

Sai da ta zauna kusa da Abbanta, sannan ta gaida yayyenta, wanda suke zaune cikin jin daɗin ganin Abban nasu, a tare suka amsa cikin kulawa don suna matukar son Ameesha sosai, kasancewar ta ita ɗaya ce mace cikin su.

"Wai Abba waye naga kun tsaya da shi ɗazun da ka shigo? "

Jaheed ne ya yi tambayar.

" Najeeb ɗin ne kuma yau baka sani ba? "

Alhaji Taheer ya yi tambayar fuskar sa cike da mamaki.

Dan rufe baki Jaheed ya yi cikin dan mamaki ya ce
" badai Najeeb din Alhaji Mansur ba? Allah Abba ban gane shi ba, naga ya canza."

" Aiko shi ɗin ne, nima nayi mamakin ganin sa a gidan."

"yo Alhaji wajen Ameesha yake zuwa, Yau shi ne zuwansa na biyu. "

Ummi dake zuwa falon ta yi maganar. Ai Ameesha tana jin maganar Ummin ta kwasa a guje tayi stair, bata zama ko ina ba Sai bedroom ɗinta.

Da kallo suka rakata, Jaheed ya dan kada kai take ya fahimci in da maganar Ummi ta dosa, Kai kusan dukkan su sun fahimta, amma shi Jaheed tuni ya fahimci zuwan Najeeb din, don yasan ba abin da zai kawo shi wajen Ameesha sai soyayya.

Mikewa su ka yi gaba daya jin an soma kiraye kirayen sallar magriba.

Bayan an idar da sallar ne suka dawo falon, don cin abinci wannan al'adar su ce, da safe da dare tare ake cin abinci a dining. Suna gama cin abinci duk suka mike zasu tafi

"Kai Jaheed da Abdul ku tsaya, ku kuma kuna iya tafiya."

Alhaji Taheer ya yi maganar ba tare da ya ɗago ba, Ameesha ta mike zata wuce
"A'a uwata ke zauna, ai yau hira zamuyi da ke wacce muka daɗe ba muyi ba."

Zama tayi tare da jingina jikinta da kujera, lumshe ido tayi "ba don Abbanta bane babu abinda zai hana ta wuce wa, don so take ta kebe waje ɗaya, don ta yi dogon tunani akan maganar ta da Najeeb."

"Wai ku kuwa sai yaushe zaku girma? Zuwa wannan lokacin yaci a ce kuna da mata, kai fa Jaheed shekaran ka talatin (30) kai Abdul kana da ashirin da takwas (28) shekarun ku kullum k'ara ja yake, me kuka nema kuka rasa? "

Shiru su ka yi suna sauraren mahaifin nasu, ci gaba da magana ya yi

" Duk kuna da aikin yin ku, kuna da karfin da zaku rike matan ku da ya'yan ku, to ku buɗe kunne kujini da kyau, na baku nan da sati biyu ku kawo min matan da zaku aura ko ya'yan waye ku tashi kuban waje."

Jaheed ya kuma sadda kansa k'asa ya ce

" Yi hakuri Abba wallahi dama tun satin da ya gabata, Abban Baderyeet yake ta ce min yana son ganin ka, to jira nayi zuwa da safe sai inyi maka bayani."

"Masha Allah kai amma naji daɗi da jin wannan furucin, insha Allah gobe zan tura su, Alhaji Isa da Alhaji Mansur don su tambayo."

"Kai fa? "

" Dan murmushi ya yi ya ce Abba nima mun dai dai ta, da Meena dama jira nake ka dawo sai in sanar maka."

Meena kawar Ameesha ita yake nufi.

To Alhamdulillah tunda hakane Allah ya sa Alhairi, duk gobe za'aje nema maku auren."

Farin ciki ne ya rufe Ummi da Ameesha, Ummi fatan Alhairi kawai takeyi a zuciyar ta, don sosai taji daɗin wannan maganar.

Da haka kowa ya wu ce, aka bar Ameesha da Abba da Ummi, wanda suke hira.


************************************
Bayan sati ɗaya komai ya dai dai ta, na maganar auren su Jaheed har an tsayar da ranar auren, wata biyu masu zuwa.

Kuma ya zuwa wannan lokacin, tuni an daɗe da sanya ranar auren Asmad da Aneesa, farin ciki wajen Aneesa ba'a magana, don wannan shi ne burinta ta mallaki Asmad a matsayin mijin aure, shi kuwa a nashi bangaren ba haushi ba haufi, wato kadaran kada han.

Ta fannin Ameesha kuwa, duk da dumbin shawarwarin da Aneesa ta bata, har yanzu bata yadda da Najeeb ɗin ba, sai ma garashi take kamar ball a fili, koda yaushe cikin zuwa gidan su yake, don Abban shi ya takura shi yana son jin gamsashshiyar amsa.

Yau ma kamar kullum, Najeeb din ne zaune a gaban Ameesha, yana ci gaba da jaddada mata irin son da yake mata.

" Zan yadda da buk'atar ka amma sai kayi min Alkawarin ba zaka ci amanata ba, ba zaka sa zuciya ta cikin damuwa ba, don kai kaɗai ta fara niyyar amincewa, sai dai ban baka wani babban waje ba, amma matukar kayi min Alkawari to ni kuma zan soma son da ban taɓa yiwa wani ba."


Kallon ta yayi gaban sa na dukan uku uku, da jin furucin ta lokaci ɗaya tunani kala uku ya yi cikin second goma, na farko ji ya yi zuciyar sa tana gargadin sa da karya cuci yar mutane, na biyu yana tunanin yadda zata kaya tsakanin sa da mahaifinsa, na uku kuwa shine take yaji zuciyar sa ta kamu da son Ameesha so na gaskiya ba irin wanda Abbansa ya turosa yi ba.

To kuma in haka ta faru tabbas akwai matsala babba.

Dago da kai ya yi ya dubi Ameesha dake ci gaba da matsa wayarta cikin sanyin murya ya ce

" ki yadda da ni princess, bada yaudara nazo gareki ba, da son gaskiya nazo wajen ki."

"Indai Alkawari ne nayi maki, ni Najeeb bazan ci amanar ki ba."

Gyada kai ta yi ta ce "Tom Allah ya sa haka, amma matukar dai ka yaudareni bazan taɓa yafe maka ba."

Wani farin ciki ya mamaye Najeeb don jin daɗin furucin Ameesha.

Soyayya suke gudanarwa, abin gwanin ban sha'awa hatta cikin gidan su Ameesha kowa yasan da maganar, Abba ya yi farin ciki sosai da jin wannan maganar, don yasan karfafa zumunci zaiyi da abokin nashi.

**********************************

Wata mahaukaciyar dariya Alhaji Mansur ya saki don jin Najeeb ɗin ya ce ai Ameesha ta

Please Login or Register in order to submit comment