Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saki tare da safa gefen fuskarta ya ce

"Karki damu my Anee zan kokarta yau din nan in baki ajiya, ina son yara ko nawa kika haifa ina sonsu, su Nenne ma zasu sosu kema kin san irin son da Nennena kewa yara, Please Aneesa ki haifa min yara." Cikin sanyin murya ya gama maganar.

"To Hamman Allah ya bamu masu albarka, amma ina tsoron haihuwa akwai wahala."

"Babu wani wahala fa, kuma zan yi maki addu'a Allah ya baki mai sauki My Anee." Cikin kwarin gwiwa ya yi mata maganar.

Daga kai ta yi alamar "to" fuskarta ɗauke da murmushi. Shi kuma Dr ya nufi kicin ɗin ransa fes yana addu'a Allah ya ba Aneesar sa ciki, burinsa bai wuce ganin Aneesa ta dauke da cikinsa ba.

Bangaren Aneesa kuwa, wani farin ciki ne ya rufe ta, musamman yadda Dr ke lallaɓata tabbas ko yanzu tasan tana da wani matsayi a wajen sa, sai dai da wuya ta iya yadda ta zauna da cikinsa domin dai ita fa bata jin zata iya yadda da ciki har ta haihu don bata son ta tsufa da wuri. Duk da ta yadda da halayyar sa da tausayin sa, da wani ne da ko sauraron ta ba zai tsaya ya yi ba, amma Dr mai kyawun hali bai ko duba rashin mutuncin da ta masa ba sai lallashinta yake yi.

Ko minti biyar ɗin bai cika ba ya dawo hannunsa dauke da cup din tea da bread, da kansa ya bata har sai da ta koshi, da kasan ya gyara komai na kicin ɗin da falo sannan suka nufi bedroom ɗinsa, wannan rana dai Aneesa a jikin Dr ta kwana, duk da dai yaso ya kwana wajen bincike asbitin da za'a kai Ameesha, amma ganin yadda Aneesa ta rukungume shi yasa ya hakura.

Washe gari karfe bakwai Dr ya gama kammala shirin sa, har a lokacin Yar Mulkin tana ta sheka bacci, tunda yasan dama akwai sauran dramar jiya sai kawai ya fita da nufi zai biya gidan Nenne ya yi break.

*******

Ko da Dr ya isa asbitin bai samu zama ba don wata mata aka kawo haihuwa ranga ranga don haka cs ya shiga yi mata domin ceto ranta da na abin da ke cikinta. Ya yi nasarar ciro mata yarta lafiyayya katuwa itama matar ta samu lafiya.

Ko da ya fito haka ya ci gaba da kula da sauran mutanen da zai duba, bai samu kansa ba sai karfe biyu. Sallah ya yi sannan ya jawo laptop ɗinsa akan ya soma binciken da yake son yi. Yana son ya samu cikakkiyar information akan asbitin da zai kai domin duba lafiyar Ameesha.

*AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL* shi ne sunan asbitin da Abban Ameesha ya faɗa masa sunan, binciken ya soma cikin nutsuwa, sai ga wayar Hafiz ya shigo, ɗauka ya yi cikin sauri magana suka yi sannan ya katse kiran.

Sosai ya duk'ufa neman abin da yake son sani, domin kuwa gaba daya tafiyar tasu bata wuce satin sama. Hamdala ya yi tare da sauke nannauyan ajiyar zuciya alokacin da ya soma karo da abin da yake muradin gani, dan haka sai kawai ya tattara kayansa don zuwa gida domin dai ya gaji kuma yana son ya yi komai a nutse.

Gidan Nenne ya nufa domin ɗazun da safe bai wani zauna suka yi hira ba, sai da ya biya sahad store, lokacin da ya yi karo da inda suka soma haɗuwa da Ameesha wani irin yanayi ya tsinci kansa, sai yaga kamar alokacin abin ke faruwa, tausayin Ameesha na halin da ta samu kanta a ciki ya kuma baibaye shi.
Jiki a sanyaye ya yo masu shopping ɗin sannan ya ɗauki hanya, mintina ƙalilan ya isa gidan, parking ya yi a parking space sannan ya kwashi ledojin da ya saya guda biyu ya yi ciki da su, ya yin da ya bar wanda zai kai wa Aneesa a mota. Cikin falon ya shiga bakinsa dauke da sallama, Nenne dake zaune a falon ta amsa masa.

Dan waro ido ya yi ganin wacce ke zaune kusa da ita, kafin ya gama mamaki har ta iso inda yake, jikinsa ta faɗa kamar kullum tare da ɗago kai tana kallonsa bakinta na faɗin

"Sweety Asmad!

Yar yaji tsigar jikinsa ya tashi, jin Ameesha a jikinsa a yan kwanakin nan yana sashi shiga wani hali, da kyar ya iya dai dai ta nutsuwarsa sannan ya ce

"Princess yaushe kika zo?" Yana maganar ne yana dan janye ta daga jikinsa, don kunyar Nenne ya ji.

Da ido ta bishi har suka dan gana ga kujera, zama ya yi ya zaunar ta gefen sa.

"Ina yini Nenne!"
Asmad ya soma gaidata.

"Lafiya lau ya aiki?"

"Alhamdulillah! Ya bata amsa yana lumshe ido alamar gajiya.

"Nenne wa ya kawo Ameesha?"

"Ni ce naje gidan sai ta ce zata biyoni, sai na taho da ita."

"Ameesha rigima bata yadda da kowa sai ni, yau kuma ta yadda da Nennena." Ya yi maganar cikin farin ciki.


"Aikuwa da ka ganta tun da muka iso take bacci yanzu ba'a daɗe ba ta tashi."

"Eh! Ai dama tunda wannan matsalar ta samu a gare ta yawan bacci ne da ita, fatan ta ci abinci?"

"Eh! Amma fa da kyar da alama bata son cin abinci kam."

"Shi kenan tunda ta ci, dama biyowa na yi mu gaisa daga office nake."

"Madallah! Ai ka kyauta, bari a haɗa maka abinci kamar kana tare da yunwa." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa.

Ameesha kam tana ma'kale jikinsa ko k'wak'waran motsi taki yi, lumshe ido kawai ta yi, a hankali ya juyo da fuskarsa gareta ya ce

"Princess!

Shiru ta masa sai dan buɗe ido da ta yi. "Tashi kije ki kwanta kamar baki gama bacci ba ko?"

Ma'kale kafada ta yi ma'ana bazata jeba. Hannu ya kai saman goshinta don yaga kamar batta jin dadi, aiko sai ya ji zafi zauu da sauri ya janye hannunsa yana furta

"Ya ilahi! Meesha baki da lafiya ne? A rude ya ke maganar, dai dai da zuwan Nenne.

"Lafiya kuwa?" Nenne ta tambaya.

"Zazzaɓi ne ya kama Meesha." Ya bata amsa.

"Subhanallah! Zazzaɓi kuma? Sannu Ameesha Allah ya sauwaka, bari na kawo mata magani." Nenne ta dire maganar tana nufa bedroom ɗinta.

Dr da kansa ya bata maganin zazzaɓin, tana gama sha ta soma rufe ido zata kwanta, amma Dr ya hanata sai ta yi minti goma bayan dasha sannan ta zame ta kwanta, kallonta ya yi cikin tausayi ya ce

"Sorry Meesha insha Allahu cikin kwanakin nan zaki warke ki koma kamar yadda kuke a da." Karshen maganar tasa sai da ta shi faduwar gaba, domin tuni Ameesha a watannin baya.

Girgiza kai Nenne ta yi ta ce

"Allah ya bada nasara Ubangiji ya sa a yi cikin nasara, hakika tana cikin yanayi a ce mutum ko ciwo yake yi bai san yadda zai faɗa ba! Kai Allah ya bata lafiya."

"Ameen." Ya amsa yana jawo ture ɗin abinci.


Sosai ya ci abinci ya koshi, yana kammalawa ya, ya zame Ameesha tare da gyara mata kwanciya, yana addu'ar Allah ya bata lafiya cikin zuciyarsa.

"Nenne zan wuce gida."

"To Allah ya kiyaye hanya, Ubangiji ya yi albarka ka gaida Aneesa."

"Amin Nenne zata ji." Ya amsa yana tafiya.

Ko da ya isa gida wanka ya faɗa sannan ya sanya kananun kaya, don kamar yanayin na zafi zafi ne, falo ya koma inda Aneesa ke zaune, kusa da ita ya zauna yana fadin

"Na shigo banji motsin ki ba?"

"Na dan kwanta ne, motsin ka yasa na fito."

"Ki daina kwanciyar yamma babu kyau."

"Na daina." ta bashi amsa tana shigewa jikinsa.

Remort ɗin TV ya dauka yana canza tasha, alokacin shida da minti goma "oh my Anee na manta akwai kayan za'kin da na shigo maki da su suna mota."

Gyara kwanciya ta yi ta ce
"Anjima ka dauko, ina son Jin dumin mijina."

Murmushi mai sauti Dr ya yi yana shafa gashin kanta Sannan ya ce

"Da gaskiyar ki yammata." Shi dai Dr biye mata kawai yake amma tunanin sa yana ga Ameesha musamman yadda ya barota yana son ya kira waya amma baya son ɓata ran Aneesa. Haka dai ya biye mata suka yi ta hiransu har aka kira yi magriba sannan Dr ya nufi masallaci, ita ma ta nufi bedroom ɗinta. Da dare suna zaune hira suke cikin kwanciyar hankali wayar Dr ta soma ruri da sauri ya dauka

Banji mai aka ce masa ba, kawai cewa ya yi "gani nan zuwa." Daga haka ya kashe wayar.

"Bari inje gidan Nenne bazan jima ba zan dawo." Yana maganar ne yana tafiya. Cikin mintina ƙalilan ya isa gidan ko kyakkyawan parking bai yi ba ya kutsa falon.

A tsaye ya samu Nenne "Lafiya kuwa?" Ya tambaya.

"Da sauki amma dai jikin nata sai a hankali yanzu zazzabin ya dawo sabo." Bai gama jin maganar da take faɗa masa ba ya kutsa bedroom din Nenne, kusan a tare suka shiga shi da Nennen.

Can a kan gado ya ga Ameesha kwance rufe da bargo, da sauri ya matsa yana yaye mata bargon, tare da ɗago ta yama manta da wata Nenne rungu...


```don Allah Fans KU yi hakuri da rashin ganin post kullum hakan yana faruwa dalilin bana samun isasshen lokaci, yanzu bana jin dadi ina barar addu'ar ku ```

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:08 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

``` Wannan page din kyauta na baki RUFAIDA OMAR fatan Alhairi a gareki da zuri'arki baki daya, Zulayheart Rano tana yinki sosai Allah ya kara maki basira da kaifin k'wak'walwa na fasihiyar marubuciya mai baiwar fikira da Nagarta```

*30*

Tsam ya rungume ta cikin jikinsa, yana kallon yadda take fusgar numfashi da kyar! Duk tausayinta ya cika shi. ɗago da kai ya yi ya ce

"Nenne bani ruwa da towel a goge mata jiki zafin zai ragu." Yana maganar ne yana kuma tallabar ta.

"To." Nenne ta amsa tare da fita. Cikin sakan ashirin har ta kawo masa ruwan, koda ta ba shi fita ta yi don ta ba shi waje. Yana ganin Nenne ta fita sai ya yi saurin kwantar da ita, ya zame rigar ta cikin nutsuwa yake bin jikinta da jikakken towel din yana manna mata, jikin dai har lokacin da zafi amma numfashi ya daidai ta.

Rasa yadda zai yi da ita ya yi, domin shi a wannan lokaci ya manta shi fa Dr ne, sai zuwa can wata basira ta fado masa cikin sauri ya kuma rungumota ya cusata a jikinsa ya soma murza mata baya ahankali, ya yi kusan minti sha biyar kafin ya ji zafin jikin ya koma daidai.

A lokacin kuwa har bacci ya yi gaba da Ameesha, a hankali ya zame jikinsa ya gyara mata kwanciya. Fita ya yi ya dauko first aid kit ɗinsa, allura ya haɗa ya yi mata. Ya zauna a gefenta yana kallonta fuskarsa ɗauke da damuwa, sosai yake jin Ameesha a zuciyarsa baya k'aunar koda 'kuda ne ya sauka jikinta balle aje ga batun ciwo.

"Sannu Asmad har ta samu bacci kenan?" Muryar Nenne ya ji.

"Eh! Ta samu yanzu." Dr ya bata amsa.

"To ya kamata dai ka tafi gida, domin dare yana kara yi fa, yanzu tara harda rabi." Ta dire maganar tana kallonsa.

Jikinsa sam babu kwari ya mike yana faɗin,

"To Nenne sai da safe duk yadda ake ciki da safe sai ki sanar min, duk da nayi mata allurar saukar da zazzabi." Cikin sanyin murya ya yi maganar.

"Allah ya kaimu, insha Allahu za ta samu sauki zuwa safen ma." Cikin karfafa masa gwiwa ta yi maganar.

Fita Dr. ya yi badan ya so tafiyar ba. Da tunanin Ameesha ya isa gida, ko da ya shiga cikin falon babu kowa don haka bai tsaya ba sai ya nufi bedroom ɗinta. Kwance ya same ta kallo ɗaya zaka mata kasan ba bacci take ba, zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"Madam har kin kwanta?"

Wani mugun kallo ta aika masa da shi tare da juya masa baya, mamaki ya kama Dr. ganin dai lafiya lau suka rabu ɗazun amma yanzu har ta ɗauki fushi

"Wai lafiyar ki kuwa?" Ya kuma mata magana.

Tsaki ta ja mai karfi ta ce,

"Ina ruwan ka da lafiyata? Ba wajen amaryarka ka je ba? Ita wato ka damu da damuwarta? Amma ni da yake baka kaunata baka damu da halin da zan shiga ba, ai shi yasa ka yi tafiyar ka sai yanzu kake dawowa anya ma kuwa Hamman kana tsoron Allah?"

Murmushi mai ciwo ya yi ya ce, "Ki yi hakuri duk yadda kike tunani ba haka bane, amma ki yi hakuri." Daga haka yasa kai ya fita.

Domin dai zafin karshen maganar Aneesa basu da maraba da saukar tafasasshen ruwa a jikinsa, ya barta mata dakin ne don karda zuciya ta sashi aikata mummunan aiki. Amma tabbas maganar ta ta bata ransa, duk iya kokarin da yake akanta bata gani, yana lallaɓata ne ba dan komai ba sai su Nenne amma yau har ta iya bude baki tana fada mishi *Yana tsoron Allah kuwa*. Ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta, "Aneesa kenan kinci daraja ɗaya amma karki bari laifin ki ya kara girma, domin dai akwai babban laifin da kika aikata min mafi muni amma na barki ne har zuwa lokacin da zan baki mamaki.

Dafe kai ya yi da ya tuna lokacin da ya yi arba da Aneesa ta zubar masa da cikinsa, tsab! Yasan tana da ciki amma sai bai nuna mata ba, shi ne da ta tashi ta zubar da shi zai nuna mata bata da wayyo rakata kawai ya ke.

Tashi ya yi zuciyarsa sam babu daɗi ya nufi toilet, ruwan sanyi ya sakarwa kansa, ya yi kusan minti sha biyar kafin ya fito, sallaya ya shimfiɗa domin dai ya dauro alwalarsa.

Tada sallah ya yi, sai da ya gabatar da ishsha a ya yi shafa'i da wuturi, addu'oi sosai ya yi na nemarwa Ameesha lafiya kafin daga bisani ya tashi tare da cire jallabiyar jikinsa ya jawo laptop ɗinsa don ya ci gaba da binciken da ya soma.

Bar mu waiwayi NAJEEB da amaryar sa.

Kasancewar yau week end, Najeeb ne zaune a k'aton falon gidansa, daga shi sai singileti da gajeren wando, hannunsa cup din fresh milk ne yake kurba. Rufaida ce ta fito cikin kyakkyawar shirinta na atamfa riga da siket sosai kayan suka mata kyau, fuskarta ta sha kwalliya, jikinta sai fitar da sansanyar kamshi yake.

Fuskarta ɗauke da murmushi mai birgewa ta nufi Najeeb ɗin rankwafawa ta yi dai dai fuskarsa ta ce"Ranka ya dade barka da hutawa." Cikin sanyin murya ta yi maganar.

Ɗago kansa ya yi cikin nashi murmushi ya ce

"Barkammu dai gimbiya, kin yi kyau"

"Na gode! Ta faɗa tana zama a kasan carfet tare da lankwashe ƙafafunta.

"Kamar kina son yin magana ko?" Ya dire maganar idonsa a kanta

Murmushi dai ta kuma yi tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta ce komai ba.

"Rufaida! Ya ambaci sunanta cikin wata irin murya. Saurin ɗago da kai ta yi jin yadda ya kira sunan.

"Na'am." Shi ne abin da ta iya faɗa.

"Me yasa kike min haka bayan kinsan mun zama daya Ni mijinki ne, ke matata ce, ki daina ɓoye min komai duk abin da kike bukata ki sanar min insha Allahu zan yi kokarin yi maki."

Gyada kai ta yi ta ce

"Babu komai fa Ranka ya daɗe."

"No! Rufaida tell me your problem."

"Sadda kai ta yi ta ce dama cewa zan yi ka kaini gidanmu ina son ganin Mamana." Cikin kunya ta k'arasa maganar, don sosai take son ganin family ɗinta tunda aka kawota babu wanda ya zo.

"Oh! Baby dama don wannan ne kika kasa faɗa min? To bari na yi wanka sai mu je har gidan Mummy." Cikin sakin fuska ya ke maganar.
Wani farin ciki ne ya rufe Rufaida har bata san time ɗin da ta rungume Najeeb ba, tana zuba masa godiya cikin tsantsan jin dadi.

"Na gode *hubby*." Ta faɗa tana kara hugging ɗinsa.

"You are welcome my baby, Amma fa sunan can da kina ambata ya min daɗi ki rika kirana da shi ina son sunan."

Kunya ce ta kama Rufaida, da sauri ta sake shi ta na nemar hanyar guduwa, har ta kusa shiga koriɗo wanda zai sadaka da ɗakunan baccinsu ya ce

"Baby ki haɗa min ruwan wanka gani nan zuwa."

"To." Ta amsa tare da shigewa.

Murmushi ya yi tare da girgiza kai, cikin farin ciki da samun Rufaida matsayin mata sam ita bata fushi, yana alfahari samun ta matsayin mata, shi yasa tun da Mummy ta yi masa bayanin aurensa da Rufaida, komai bai ji ba na takaici ko da nasani, domin dai Rufaida ma masoyiyar sa ce, yasan ya so Ameesha so na gaskiya amma tunda Allah baiyi nufin ita matarsa ba ce ya yadda da kaddara, ya kuma rungumi matarsa yana addu'ar dorewar zaman lafiya a aurensa.

Da taimakon Rufaida ya kammala shiryawa, cikin wasu riga da wando wanda suka amshi jikinsa, sansanyar kamshi turare ke fita daga ko wane lungu na jikinsa, keys ɗin mota ya ɗauka yana faɗin

"Madam mu je ko?"

Murmushi ta saki tare da daga kai alamar "to."

"Ka yi kyau hubby." Cikin muryarta mai sanyi ta yi maganar.

"Na gode." Shi ne abin da Najeeb ya faɗa yana ci gaba da tafiya.

Sai da suka biya wani babban kanti ya sayawa iyayen Rufaida tsaraba wacce zata kai masu, domin ko ya basu kuɗi ba amsa zasu yi ba, shi yasa ya sai masu kawai, tare suka shiga bayan ya gaida da Mamanta sai ya koma mota inda zai jirata, sai Maman ta yi farin ciki da ganin yartata don da gani hankalinta a kwance yake duba da irin kyaun da ta yi.

Bata wani jima sosai ba ta yi masu sallama, zata ta fi

"Hajiya ki yiwa mijinki godiya, mun gode Allah ya saka da Alhairi, don Allah Hajiya ki kula da auranki duk abin da zaki gani ki rika hakuri kin ji ko?"Maman Rufaida ke mata nusiha, da yake bata faɗan sunan Rufaida sai dai ta ce mata Hajiya, don sunan k'anwar mahaifiyar ta aka sanya mata.

"Insha Allahu Mama zan yi yadda kika ce, mu dai a ci gaba da yi mana addu'a."

"Addu'a kam ana yi sai dai a kara kaimi, Allah ya kai ku gida lafiya."

Da haka suka yi sallama, ji ta yi kamar kar ta tafi, a mota ta same shi yana zaune yana latsa wayarsa kamshin turare ta ya sanar shi isowarta.

Ɗago da kai ya yi tare da aje wayar ya ce

"Har kin fito?" Ya yi tambayar idonsa a kan ta.

"Eh! Ta bashi amsa tana bude kofar motar.

"Mama ta ce ayi maka godiya." A hankali ta yi furucin.

"No ba sai sun gode min ba domin suma iyayena ne." Cikin kulawa ya bata amsa.

Murmushi ta yi don ta ji dadin furucin sa, da haka suka isa gidan Mummy, sosai Mummy ta ji dadin zuwan Rufaida sai nan nan take da ita, tana son Rufaida har cikin ranta domin Allah ya yota da nutsuwa ga hankali uwa uba kuma kunya.

Nan Najeeb ya barta akan bayan magriba zai zo ya dauketa su koma gida.

***

Tashi ya yi cikin sauri tare da kallon agogon da ke manne jikin bangon daki "subhanallah! Ya furta a fili ganin har bakwai da minti sha biyar, ya makara sosai sakamakon kwanan da ya yi wajen binciken asbitin da zai kai Ameesha, tun tun sha biyu yake aikin bai samu kansa ba sai karfe huɗu, bayan ya kammala alwala ya dauro ya soma gabatar da sallah sai da ya yi asbah kafin bacci ya dauke shi, da azama ya isa toilet din shaf shaf ya yi wankan ya fito ya soma shiryawa.

Bai jima ba ya kammala shirinsa, falon ya fita hannunsa dauke da wayoyinsa, babu kowa a falon da alama ma dai matar gidan bata tashi ba, don haka sai ya nufi bedroom ɗinta yana tura kofar ta buɗe can ya hangota cikin bargo tana sharar bacci ta, takawa ya yi har bakin gadon ya zauna tare da ambaton sunan ta

"Aneesa! Ya yi maganar yana dana buga kafadarta ta, ido ta buɗe cike da mayen bacci ta ba ta ce komai ba sai kallonsa da ta yi.

"Kin yi sallah kuwa?" Ya tambaye ta tare da tsare ta da ido.

Doguwar Hamma ta yi tare da girgiza kai alamar a'a, "ok tashi ki yi gari ya waye ras har bakwai da rabi, zuwa yanzu ya kamata ki gyara halinki ki daina wasa da ibadanki."

Harara ta bi shi da ita don haushi yake bata, sam ta tsani ko da ganinsa tashi ta yi bata ko ce masa komai ba, yana zaune har ta fito sannan ya tashi tsaye yana faɗin

"To nikam na tafi office sai na dawo." Bata ce masa kala ba ta tayar da sallar ta.

Girgiza kai ya yi tare da fita, cikin zuciyarsa yana mamakin halin Aneesa.

Duk da yasan ya yi latti amma hakan bai hana shi biyawa gidan Nenne ba, domin duba lafiyar Ameesha da jiki, sallama ya yi cikin falon ya ji shiru, a zuciyarsa yana tunanin kila suna ɗakin Nenne don haka sai ya nufi haryar motsin da ya ji a dining ne ya sashi lekawa zaune ya ganta a dining din tana juya cokali cikin cup

Murmushi ya saki yana faɗin " *Heartbeat* kina nan ke kaɗai?" Ya ida maganar yana zama a daya daga kujeran dining din.

Itama murmushi ta yi ta ce

"Sweety Asmad! Shi ne kaɗai kalmar da Ameesha ke iya faɗa.

Siririn dariya ya yi yana kallonta cikin wani yanayi mai wuyar fassara ya buɗe baki zai yi magana kenan ya ji muryar Nenne

"Maganar wa nakeji kamar ta Asmad?" Nenne ta yi maganar tana zama a dining din.

"Wallahi ni ne Nennena, na biyo duba jikin Ameesha ne."

"Ah! Ai jiki ya yi sauki ka ganta nan." Ta dire maganar tana kallon Ameesha da har yanzu take juya tea din. Mamaki ya kama Nenne ta ce

"A'a Ameesha wa ya haɗa maki tea din?"

"Au bake kika haɗa mata ba? Nima nazo naga tana juya abinda, madallah! Ashe Heartbeat ta Fara hada shayi da kanta." Cikin murmushi ya ida maganar.

"A'a bani na haɗa mata ba don na shiga ciki, ai haka ake so sauki ya rika samuwa." Nenne tana maganar ne tana haɗawa Dr tea, a lokacin kuma Ameesha ta daga kofin tea din tare da kaiwa bakinta da sauri ta furzo shi tare da bata rai, da kallo suka bita da mamaki, ba su gama mamakin ba sai suka ga ta mika hannu tare da dauko cup din da Nenne ta haɗawa Dr tea ta kai...



_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:14 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

``` wannan page din kyauta na baki ZEETY MUM HANAN ki yi yadda zaki da shi domin jin dadin ki, ki daɗe ki yi karko uwargida sarautar mata, Allah ya kara maki lafiya da basira Ubangiji ya raya mana su Hanan rayuwa mai inganci ```

_*Hazika kuma Hamshaqiya fasihiya duk ke kaɗai kika amsa wannan sunan BESTYNA Khadija s Muhammad ke ɗin ta daban ce, fadan matsayin a wajena ba zai yiwu ba, sai ina kara tabbatar maki da Ina jinki har cikin jinina, Allah ya k'ara tsare min ke a duk inda kike amin ina jin dadin littafin LAFIN WA? Wannan Nagartacciyar marubuciya kina ɓarar da ilimi a cikin sa Allah ya kara basira*_


*31*
Bakinta da ta kurba sai ta saki murmushi tana kallon Dr, su dai mamaki kawai suke na Ameesha sai zuwa can Dr ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Heartbeat bani tea na in sha sauri nake yi." Ko kallonsa bata yi ba sai ci gaba da shan kayanta ta yi.

Murmushi Nenne ta yi ta ce "kai ka dauki nata kasha tunda ta dauki naka."

Ɗauka ya yi yana

Please Login or Register in order to submit comment