Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauke da murmushi mai nuna zallar farin ciki da jin dadi Dr ya dire maganar.

Ameesha kam kasa cewa komai ta yi sai kallon Dr da take yi.



Mu je zuwa dai an zo final in sha Allah.

*YAR MUTAN RANO*
[10/27, 8:07 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


®
_*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*50*


Haka ta wuni sukuku har su Aneesa suka dawo, a falo suka sameta kwance Miemie da sauri ta faɗa kanta tana faɗin "Mami min dawo." "Sannu da dawowa 'yar Momma ya Nenne?" "Lafiya lau tana gaidaki." Aneesa ta bata amsa. "Ina amsawa." Ta amsa a takaice "Wai har yanzu ciwon kan ne?" "A'a me kika gani?" "Babu komai kawai na ga kamar ba ki cikin nutsuwa?" "Ki bar kawai wallahi ɗazun bayan fitar ku Dr ya tabbatar min ina da ciki har tsawon wata biyu." "Shi ne abin tashin hankalin?" "Eh mana duka shekarar Miemie daya fa gaskiya ba haka na so ba." "Hmmm! Yar'uwa kenan wallahi wannan ba abin damuwa ba ne ki bar tada hankali ki yi addu'a Allah ya sauke ki lafiya, idan ta Miemie ne ba abin damuwa ba ne saboda Miemie tana cin komai tana tafiya kuma bata damu da nono ba."

"To ya zan yi dole ai na hakura Allah ya bamu masu albarka, Miemie kuma yanzu zan hado mata sauran kayanta dake dakina ku karata can, dama kun saba Allah ya raya maki ita." "Yar'uwa kina nufin kin yaye Miemie kenan?" "Eh, ta koma dakin Momman ta dama tun da ta zo duniya take ɗiyar Momma to yau Allah to yau Allah ya tabbatar." Ameesha ta gama maganar tana mik'ewa tsaye. Rasa abin da zata faɗa Aneesa ta yi don sosai abin ya bata mamaki, wato kyautar da Ameesha ta yi mata na Miemie tun ranar da ta fado duniya gaske ne? Lallai ta jinjina da karamci irin nata da zallar farin ciki da murna ta ce "Na gode sosai Ameesha Ubangiji Allah ya baki abin da kike nema duniya da lahira, wallahi da ana samun kishiya irin ki da ko wacce mace zata so a yi mata kishiya hakika ke kin bambanta da sauran mata, na cutar da ke Ameesha na mugunawa rayuwar ki amma duk da haka ke kullum da Alhairi kike nufina, a zatona tun da kin kasance shagwaɓaɓɓa idan kika auri Hamman za ki iya raba ni da shi ko dan salon SANGARTAR ki ashe abin ba haka ba ne, ki yafe min don Allah." "Na yafe maki Allah ya yafe mana baki daya." Ameesha ta faɗa fuska sake.

"Na gode Allah ya saka da mafificin Alhairi, Ubangiji ya biya maki buk'atar ki ya sauke ki lafiya." Murmushi kawai Ameesha ta yi ta amsa amin "Allah ya ci gaba da bamu hak'urin zama da juna da zuciya daya." "Amin" suka amsa tare. Sannan ta nufi bedroom kaf kayan Miemie ta kwashe ta kai bangaren Aneesa, farin cikin da Aneesa ta shiga a ranar baya misaltuwa. Ko da Dr ya dawo ya samu labari dariya kawai ya yi ya ce "Allah ya taya ta riko, Ameesha na lura dama kamar baki damu da Miemie ba?" "Haba beby wannan wacce irin magana ce? Miemie fa 'yata ce bana jin duk duniya akwai wanda ya kaini sonta, amma ka duba hidimar da Aneesa ke yi wa Miemie wallahi ta cancanci kyautar Miemie, na bata da zuciya daya Allah ya kara haɗe kanmu."

Rungumota jikinsa ya yi yana jin wani sabon soyayyar ta a zuciyarsa, bai taɓa ganin mai sanyin hali irin ta Ameesha ba, wallahi a time ɗin da suka fara haɗuwa da Ameesha a sahad bai taɓa tunanin tana da sanyin hali da tunani ba sai da ya mallaketa, kara matseta ya yi jikinsa ya ce "ina sonki matata so irin wanda bazai misaltu ba Allah ya yi maki albarka." "Nima ina sonka Dr Asmad Abubakar My fullo, Ina jinka har cikin zuciyata uban 'yayana, kullum fatana shi ne in faranta maka." Daɗi sosai ya rufe Dr jin kalaman da take faɗa masa, shi sai ya ji a duniya ya fi kowa sa'a. Sun daɗe a haka rungume da juna kafin Ameesha ta lankwashe murya tana faɗin "Beby wankan fa kalli time ga yi baka lek'a Aneesa da Miemie ba." "Oh! Wallahi har na manta, idan ina tare da ke manta kowa nake yi mu je ki yi min My wife." "An gama mijin mace biyu." Ta gama maganar da dariya. "Baki karya na autar Ummi ni ne mijin mace biyu Aneesa da Ameesha Baban Fatimah (Miemie)." Dariya sosai maganar Dr ya ba Ameesha don haka har suka shiga toilet din tana dariya.

Sun ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har Allah ya sanya Ameesha ta shiga watan haihuwar ta, ranar wata Alhamis ta tashi da nakuda ga shi Dr baya gida, Aneesa ce ke ta taimaka mata amma fa sosai ta sha wahala fiye ma  da haihuwar Miemie sannan  ta haifi lafiyayyun yaranta biyu mace da namiji, tsaf Aneesa ta wanke yaran tare da shirya su cikin kayan sanyi masu taushi da kyau.

Lokacin da Dr ya ya dawo Ameesha tana toilet, ido ya daura akan gadon ya ci karo da jarirai har biyu kwance akan gadon, matsawa ya yi fuska ɗauke da mamakin yadda Ameesha har ta haihu bai sani ba, karan buɗe kofar da ya ji ya sanya ya juya wayam ya ga cikinta baki buɗe yake kallonta, ita kam murmushi kawai take aika mas, doguwar a jiyar zuciya ya sauke yana faɗin "Cutie haihuwa kika yi shi ne ko ki sanar min in tari baby's ɗina da kaina?" "Sorry baby bayan fitarka babu jimawa sai nakuda, ni na hana Aneesa kiranka don can dinma aiki ka ke yi, kuma ka ga da sauki sosai tun da na sauka lafiya." "Madallah amma ban so yarana suka fito duniya bana kusa ba." Ya dire maganar yana isa bakin gadon. "Ai k'anwar ka ta amsheka domin ta yi aiki sosai Allah ya saka mata da Alhairi." "Amin.*" Dr ya amsa sosai ya cika da farin ciki kamar wannan ne karon farko da aka taba masa haihuwa, daukar yaran ya yi cikin zallar soyayyar su da kaunarsu, sai kiss yake masu take yama yaransa huduba da sunan Ummi da Abba.

Wannan abu ya yi wa Ameesha daɗi, mutane sai tururuwar zuwa barka suke har ranar suna, an yi lafiya an gama lafiya, yara suna amsa HIBBAN DA HIBBA, Ameesha zaune tana shayar da Hibba ya yin da Hibban ke kwance  Miemie ta shigo da gudu ta k'arasa bakin gadon tare da kaima Hibban raruma a dole daukarsa za ta yi, da sauri Ameesha ta janye Hibban ɗin tare da kaima Miemie duka ba na wasa ba. Kuka ta saki aiko cikin sauri Aneesa ta shigo tana faɗin "Subhanallah Miemie me ya faru? Yar'uwa me ya sameta?" Harara Ameesha ta banka masu ta ce "Allah Yar'uwa ki faɗawa yarki ta kiyayi min yara yanzu fa Babana yana kwance shi ne ta zo zata daukar min shi bige mata hannu na yi."

"Sorry yarinyata kin ji rabu da Mami kawai don zata ɗauki Hibban mu tafi unguwa  shi ne ki ta dokeki? Babu komai in kika kwantar da hankalin ki yanzu zamu bar maki gidan kuma ba bu inda zamu da Hibban ɗin." Ta karasa maganar tana daukar Miemie. "Hhh! Ku gaida su duk inda ku ka je za ku dawo ku samemu, Allah wannan yarinyar taki tana fama da sangarta." "Hmm! Yar'uwa yanzu duk SANGARTAR Miemie ta kai ki?" "Ta ma fini ki tambayi Ummi ki ji." "Umm ki faɗawa wasu amma mukam mun sa ni don haka sai mun dawo." "A dawo lafiya." Ameesha ta faɗa tana kwantar da Hibban ɗin.

Fitar su Aneesa gidan Nenne suka fara zuwa sun daɗe a can bayan la'asar suka fita dan zuwa gida, suna cikin mota Miemie ta ce "Mommana ice-cream." "Ok mu je gida akwai." "A'a Mommana ni dai ice-cream ki ciya min yanju." "Kai Miemie kin fiye rigima mu je." Kwana ta yi ta shiga wani super market ice-cream din ta saya mata robobi biyar sannan suka nufi wajen biyan kudi Aneesa tana biyan kudin Miemie ta fice ba tare da ta sa ni ba, ta gama biyan kudin ta duba bata ga yarinya ba cikin sauri ta fita wajen mota, sai dai me babu Miemie take hankalinta ya tashi ta koma ciki tana sanar da ma'aikatan wajen ba taga yarinya ba, su ma nan suka fara duba wa amma duban duniya babu Miemie babu alamar ta, tuni Aneesa ta barke da sabon kuka dama tuni ta fara, zaman dir shan ta yi a wajen ita sai an nemo mata yarta, duk lallashin da suka mata ta ki yadda.

Da kyar ta yadda ta nufi tafiya wanda sam ta kasa yin direban da kanta ga uban jiri idonta ya kumbura sun tun saboda kuka har bata iya buɗe su, babban tunaninta ta yadda zata tun kari Ameesha da Dr ita kuwa mai zata ce masu, sai sabon kuka a haka suka isa gidan da kyar ta shiga bangaren Ameesha hawaye na shatata, Ameesha tana jijjiga Hibba ta koma bacci sai ganin Aneesa ta yi sosai hankalinta ya tashi musamman yadda idonta suka koma, da sauri ta kwantar da Hibba ta nufi wajen Aneesa tana tambayarta menene.

"Yar'uwa Miemie! Miemie Yar'uwa." Shi ne kawai abin da take faɗa. " Miemie! Me ya sameta?" Wasu sabbin hawaye suka zubo daga idonta ta ce "a wajen sayan ice-cream ban ganta ba." "Baki ganta ba? Miemie ɗin?" A dan firgice ta yi maganar. " Eh, ta faɗa murya a dashe, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un shi ne kalmar da Ameesha ke maimaitawa har ta ɗan samu nutsuwa waya ta dauko ta soma kiran layin Dr lokacin har ya shigo cikin gida, ɗauka ya yi ya ce "To gani nan har za a fara min waya." Cikin dariya ya gama maganar. Ba iya cewa komai ba sai kashe wayar ta yi har ya isa shigowa.

"What! Dr ya fada da ya gama jin labarin da Ameesha ke ba shi tashin hankali sosai Dr ya shiga da jin ba a ga Miemie ba, a fusace ya nufi Aneesa tare da shako wuyarta tare da sakar mata wasu lafiyayyun maruka biyu wanda suka yi sanadin daukewar numfashin ta ya daura da faɗin "wallahi matuk'ar baki nemo min yarinya ba duk abin da na yi maki ke kika ja, tun farko irin haka na guda amma Ameesha kika na ce sai an bata dama mata da ba imani ne da ita ba ta ya zata iya kula da yar wata, da kanki Ameesha kika zubar min da ciki sannan kika ci gaba da shan magunguna har kika yi wa kanki illa, wannan ba matsala ba ce domin ko yanzu Allah ya nuna maki ishara ni, ki fito min da yarinya tun ban yi maki lahani ba."

Da kyar Ameesha ta samu Dr ya saki Aneesa sai huci yake, Aneesa kam sam shakan da Dr ya yi mata bai dameta ba sai ciwon rashin Miemie, tana zaune a wajen hatta motsi kasawa ta yi sai kallinsu ita kadai ta san halin da take ciki, cikin lokaci kadan har maganar batan Miemie ya karede jama'a, Abba tuni ya kai sanarwa gidajen rediyo da talabijin har cikin jaridu, Dr kam sam ya rasa nutsuwa duk cikin su Ameesha ce kawai mai dauriya amma Aneesa kam bata da aiki sai kuka da sambatu, bata taɓa damuwa da bakaken maganganun Dr ba bata da wani buri sai na ganin Miemie kusa da ita, har aka kwana shiru babu labari. Nan fa hankula ya kara tashi aka duk'ufa addu'oi.

****
"Hahaha." Dariya Alhaji Mansur kenan lokacin da su mugu suka kawo masa Miemie, kallon yarinyar ya yi ya ce "tabbas wannan jinin Alhaji Taheer ne, don haka da ita zan yi amfani wajen cimma burina." "Kai Alhajina gaskiya kasan kan tsiya yanzu wannan yar yarinyar ka sanya aka dauko maka na san dole hankalinsu ya tashi, kuma ko nawa ake bukata za su kawo." "Sosai kuwa ai na yi bincike ne akan son da suke mata, kuma idan muka dauko Alhaji Taheer akwai matsala amma kaga wannan bata sammu ba mu dinma bamu santa ba. "Ka yi farar dabara" tafawa suka yi cikin jin dadi.

Number din Alhaji Taheer ya ba mugu ya ce maza ya kira shi ya faɗa masa ga jikarsa sun kama sai ya bada miliyan ashirin za su bada ita "yau kwanan ta nawa ma." "Eh Alheji kwanan ta uku, gaskiya a yi ayi domin gaba daya ta damemu da sangarta kuma ka ce mu rika bata komai, haka jiya ta ishemu da surutun tsiya sai da bobo ya kai ma bakinta duka." "Du me? Waye  ya baku izinin duka? To kar ku kara." "An gama oga." Ya fadi maganar yana dan nawa Alhaji Taheer kira.

Lokacin yana zaune a cikin gida abin duniya ya dameshi sam ya rasa tunani daya sai jin kar'ar wayarsa ya yi, da sauri ya dauka ganin sabuwar Number Yana Addu'a Allah yasa sun ga Miemie ne, maganar da ya ji ya firgita shi amma cikin dakiya ya ce "Ku fadi in da za a kawo kuɗin nan da awa daya zan turo amma don Allah karku yi mata komai." Faɗa masa suka yi kafin ya yi wata maganar har sun katse layin. Dr ya kira yana faɗa masa yadda suka ce "Abba karka yi saurin tura masa kuɗin nan fa ka bari a yi bincike." "A'a zan tura Asmad zan iya kashe ko nawa in dai  Fatima zata fito mu ci gaba da addu'a." Cikin kankanin lokaci har su Nenne da Bobbo sun isa gidan Asmad su Ummi da Abba ma haka har da Meena.

Kudi Alhaji Mansur ya mika ma su mugu ya sayo masu abin sha, aiko ya sayo har da kayan maye sun sha sun yi ta tutul, Miemie sai wasa take yi abin ta bata damu ba da ta gaji da zaman falon ta fita, suna kallonta don sun san babu mai shigowa gidan tunda akwai mai gadi kuma ba zai barta ta fita ba, kuma ma dai ai Miemie bata da wayan da zata gudu fitarta ya yi  daidai da zuwan Najeeb tare da Littel Ameesha sun zo gaida Abbansa domin kwana uku kenan yana zuwa gidan baya samunsa shi ne ya yake shawarar zuwa nan gidan domin duba shi, ido hudu suka yi da Miemie duk da bai taɓa ganin yarinyar ba sai jiya a Arewa 24 ana cigiyar sa sunanta makale da sunan Dr Asmad ya shaidata, da sauri ya rikota yana dube-dube don kar wasu su ganshi a hankali ya ce "ke ce Miemie?" Kai ta gyaɗa ta ce "ka kaini wajen Mommana..."


*YAR MUTAN RANO*
[10/27, 8:08 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*

              
                     ©
    _*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*LAST*

_*Masha Allah! Alhamdulillah Ina matuk'ar godiya ga Allah da ya nuna min wannan rana da na kammala wannan littafi, ina cikin farin ciki mara misaltuwa*_

GODIYA

*GODIYA MAI TARIN YAWA GA*
*My Besty Khadija S Muhammad, hakika ina alfaharin samun ki a matsayin amintacciya, domin kuwa duk wani abu da aka gani cikin wannan labari ke ce silar shigarsa banza gaji da gode maki ba, Allah ta'ala ya saka maki da mafificin Alhairi ya bar mana zumunci har ya'ya da jikoki Allahumma amin.*

```JINJINA GA
Ummyn Yusrah fan's group
Bilkisu Bilyamin Novel's
3 Star Hausa Novel's
Surbajo Hausa Novel's group
Láifin wa? And sangarta fan's
Khalisat Haydar Hausa Novel's
Zama na amana 2
Hassan ATK
Hussain ATK
Umar Dalhat
Kamala Minna
Khadijah S Muhammad
Fa'eeza S Muhammad
Ummu Sayyid
Ummyn Yusrah
Amrah Auwal mashi (Princess Amrah)
Ramlat Ar Manga (My me Dambu)
Nafeesa Musa Ankerh```

Da sauran wanda ban lissafo ba.

```I hearttttt you my daughter Badeeyar Adam (beauty queen)```

     
*51*

Daukarta ya yi ba tare da ya ce komai ba ya nufi motarsa, ciki ya sanya su suna ci gaba da wasa da Littel Ameesha kai tsaye gidan su ya kaita, Rufaida kanta ta yi mamakin ganin Miemie har ta kasa hak'uri ta ce "Honey wannan kamar yarinyar da ake cigiya ko?" "Eh! Ya amsa mata a takaice. "Please ki yi mata wanka ki canza mata kaya sai mu kaita gidan su." "Gidan su honey baka tsoro ace kai ka saceta?" "Ai Gara ace ni ne na saceta akan akama wanda ya saceta ɗin, amma duk da haka ya zama dole iyayenta su san wanda ya saceta." Ya gama magana tana dage kai wanda ke tsananin yi masa ciwo, tir yake da halin mahaifinsa na son abin duniya, wato ashe Abba zai iya hada kai a yi kidnapped din jikar amininsa? Lallai duniya tazo karshe Allah ya rabamu da son zuciya.

Cikin kananun lokaci har Rufaida ta tsaftace Miemie ta shiryata cikin wata kyakkyawan doguwar riga mai kyau da tsada sosai yarinyar ta yi kyau da yake har kitson kanta ta canza mata sai ta fito fes, suna rike da hannun juna ita da Littel suka shiga mota, sai da suka biya suka ɗauki mommy sannan suka dauki hanya a tsanaki yake tuki har  suka isa unguwar. Horn ya yi a kofar gidan mai gadi ya buɗe masa  parking ya yi yana hamdala da ganin motar Abban Ameesha a gidan, hakan ya nuna cewa yana cikin gidan kenan, bayan ya faka motar bai fita ba sai ya ce "Littel da Miemie su fita, sai da yaga sun yi nisa har sun kai kofar falon Aneesa sannan suka fito daga cikin motar, kowa ya ga fuskar Najeeb yasan akwai damuwa "Ka ga Najeeb ka cire wannan damuwar kar wani cutar ta shigeka." Mommy ta yi maganar cikin sigar lallashi. "To mommy ya amsa yana kalkalo murmushi iri wanda iyakar sa laɓɓa. Suna kallon yaran suka fito daga ɗaya bangaren suka nufi ɗayan.

Duk suna zaune sai ganin Miemie ta shigo rike da hannun Littel, da mamaki suke kallonta sun kasa motsi, kallo ɗaya zaka masu ka tabbatar sun cikin farin cikin ganinta, babu ma kamar Aneesa har rige rigen zuwa daukarta ake wani irin mik'ewa Aneesa ta yi da gudu ta nufi Miemie wacce ta saki hannun Littel ta nufi Aneesa tana faɗin "oyo-yo Momma." "Oyo-yo 2 My baby I miss you, daga ina kike? Wa Ye suka dauke ki Miemie?" Aneesa ta jero mata tambayoyin cikin sauri. "Watu mutane tuka ta ni a motarsu wai za su kaini wajen Daddy shi kenan na tena ka nin ku." Cikin maganarta ta yi maganar. Kafin ta yi wata magana sai jin sallamar su Najeeb suka yi. Gaba daya suka ɗago da mamaki suna amsawa.

Ciki suka shiga aka gaisa Ameesha cike da ɓacin rai tana shirin yi wa Najeeb rashin mutunci, wato shi ya ɗauki mata yarinya ya barsu cikin matsala da tashin hankali, shima a bangaren Dr haka abin yake hanya yake nema da zai nuna wa Najeeb kurensa, sai yanzu ya tuna shi wannan saurayin Ameesha ne na da wanda suka yi zaman asbiti lokacin, maganar Najeeb ce ta dawo da su hsnkalinsu"Abba a yi hakuri ga Miemie nan ɗazun Allah ya sanya muka ganta, bana son kowa ya ce komai sai kun je gidan da muka samu Miemie daga nan sai ku san matakin da za ku dauka, amma ina rokon alfarma Abba kar ka ji kunyar wanda ya aikata hakan.

Duk sun yi na'am da maganarsa don haka gaba daya suka ɗauki mota don zuwa gidan motoci uku suka nufi gidan Aneesa rungume da Miemie kamar wani ya ce zai raba su.

Can bangaren kuwa ba su tashi farga babu Miemie ba sai da suka ga ta yi kusan awa bata shigo, nan fa hankalin su ya tashi duk gidan an duba babu Miemie sun tambayi mai gadi ya ce babu wanda ya shigo, domin Najeeb ya bashi kuɗi masu yawa ya ce kar ya faɗawa Alhaji Mansur ya shigo, ai ko ya ce babu wanda ya shigo, ya sanya su mugu su daure shi kenan aka fara horn, da sauri ya je ya bude don a tunaninsa Najeeb ne ya dawo, su mugu sun yi tunanin Yan sanda ne don haka da gudu suka biya. Mamaki matuka ya kama su gaba daya, Alhaji Taheer cikin fara'a ya fito yana faɗin "a'a Alhaji har kun riga mu isowa kenan? Lallai na yadda da soyayyar ka a gareni." Dabur cewa Alhaji Mansur ya yi zai fara kame kame Najeeb ya yi saurin cewa

"Ina mai bakin cikin sanar maku da mahaifina Alhaji Mansur ya sanya a dauke Miemie domin kwadayin abin duniya." Doguwar salati jama'ar wajen suka dauka "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." "Kai Najeeb bana son shashanci Yanzu ka rasa wanda za ka yi wa sharri sai mahaifinka?? Wannan wacce irin rayuwa ce Allah ya kawo mu da 'ya'ya basa kaunar iyayensu??"" "ABBA ya yi maganar cikin tashin hankali. "Sam Alhaji a zamanin yanzu kafin ka samu yaro mai biyayya wa iyayen sa kamar Najeeb da wahala wallahi duk abin da ya faɗa maka gaskiya ne, wannan kadan kenan daga cikin halin Mansur inda har baka ji tsoro ba wallahi shi ya sanya wasu marasa imani suka bige Ameesha har ta samu wannan lalurar." Wannan karon har kusan faduwa Abba ya yi don firgici, mutumin da ka yadda da shi shi ke ha'intar ka? Lallai mutum ba abin yadda ba ne, kallon Alhaji Mansur ya yi wanda ya yi tsiru-tsiru kunyar duniya ta rufe shi bai taba tunanin yana da kunya irin ta yau ba ji ya yi uwa kasa ta nitse ya faɗa ciki ko ya huta da kunya da nadama, yau kaɗai na ya ji ya tsani irin halinsa.

"Babu komai Alhaji duk abin da ka yi ka yi wa kanka, Allah ya sani da zuciya daya na daukeka amma tun da haka ne babu komai, har cikin zuciyata na yafe ma duk abin da ka yi min, kuma ina rokonku da ku yafe masa kunshi? Kai Jaheed ɗauko jakar kuɗin nan ka bashi miliyan biyar a ciki yi tun da domin kuɗi ya yi." Cikin sauri Jaheed ya cika umurnin Abba nusiha sosai Abba ya yi wa Najeeb wanda ya sanyaya masa jiki sannan suka juya, su ma su Najeeb motarsu suka shiga sai dai ya kasa jan motar sai Rufaida ta ja.

Su Abba na fita su mugu suka fito, Alhaji Mansur har zai fara kaso suka kwace kudin babu tausayi babu tsoro yana kallo suka wuce da shi, kuka sosai ya yi ya rasa aboki mai taimakonsa sannan kudin da aka bashi sun kwace wayyo tarin nadama da dana sani suka masa yawa take kansa ya fara wani irin sarawa. Da kyar ya iya jan motarsa zuwa gida, kwana biyu ciwo ya kwantar da shi, da kyar da lallashi Mummy ta samu Najeeb ya kai shi asbiti. Gwajin farko aka ce ciwon zuciya da hawan jini wanda suka masa mummunan kama, domin zuciyarsa kumbura ta yi haka jikinsa ya fara kumburi.

Allah ka bamu ikon aikat kyakkyawa, ba irin halin Alhaji Mansur ba na zallar cin amana da bakin ciki tare da hassada, ga dai yadda ya kare nan

Bangaren su Ameesha ma Alhamdulillah komai ya wuce, ta ci gaba da shayar da su Hibban da Hibba yara masu kyau da wayau sun yi tula-tula gwanin sha'awa

*BAYAN SHEKARA GOMA*
Alhamdulillah! Gidan Dr arziki ya ci uban na da don yanzu ya zama katafaren mai kuɗi k'aton gida ya gina masu, haka ya mallaki asbitoci har uku wanda ya sanya masu suna *A'A specal hospital* (Asmad Abubakar) duk a cikin garin Kano, duk inda ka zaga maganar sa ake Dr Asmad, ya yi suna fiye da tunani, yanzu yaransa biyar duk da su twins
*Fatimah (Miemie), sai su Hibban da Hibba, sai mai sunan Meena wacce suke

Please Login or Register in order to submit comment