Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi har bai samu kansa ba sai biyun rana.

****

"Sannu My Ruffy har yanzu amai ɗin bai tsaya ba?"

"Eh! Ta bashi amsa tana mai da numfashi, domin dai sosai ta galabaita, da kansa ya gyara wajen ya canza mata kaya, yana rike da ita har suka isa wajen motarsa, taimaka mata ya yi ta shiga, sannun da yake jero mata tunda ga bedroom ɗinta har nan sun kai hamsin.

Tsabar tausayin ta ke damunsa sosai, ba su yi wata tafiya mai nisa ba suka shiga wani karamin asbiti mai kyau, parking ya yi tare da riketa har cikin office din Dr, domin ya yi masa waya tun kafin su taho.

Dr Auyo sosai ya tausayawa Rufaida ganin halin da take ciki, tambayoyi ya fara mata tana bashi amsa, inda daga karshe ya kira Nurse tare da umurtanta da ta dibi jinin Rufaida da fitsarinta domin a yi test, ba'a wani dade ba ta dawo da result ɗin.

Gama karanta result ɗin ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi, hannu ya mik'awa Najeeb yana faɗin

"Congratulations! Sir Allah ya inganta, Madam na dauke da juna biyu na sati biyar."

Wani irin farin ciki ne ya kama Najeeb, wanda har bai san lokacin da ya rungume Rufaida ba, ita kam kasa ta yi da kai cike da kunya, Najeeb fa ya manta a gaban Dr yake, da Dr Auyo da yaga haka sai ya fita ya bar masu office din.

Najeeb kuwa rungume Rufaida ya yi a jikinsa, yana gwada mata tsantsan farin ciki da murna na cikin dake jikinta, lokacin da ya ɗago bai ga Dr Auyo ba murmushi ya yi don yasan shi da kunya.

Mik'ewa ya yi ya leka waje inda ya ga Dr na magana da wasu, Nurse ya sanya ta yi masa magana, bai jima ba ya shigo, bakin Najeeb sam yaki rufuwa ya ce

"Dr da alama cikin zai bata wahala musamman ta yawan aman dake damunta, ko akwai maganin da za'a bata?"

"Eh! Akwai wani magani da mai ciki take amfani da shi sunan sa *Ancloxine tablet* sosai yake tsayar ma masu ciki amai matukar dai ya amshe ta, kasan laulayi ne kowa da irin yadda ya ke yi." Dr Auyo ya yi masa bayanin cikin kwantar da hankali.

"To Dr muna godiya sosai Allah ya bar zumunci."

"Amin." Dr ya amsa ya na mika masa takaddan da ya rubuta sunan maganin. Daga haka suka yi sallama, ko da suka fita ba su nufi gidan su ba sai kawai ya nufi gidan Mummy da ita.

A falo suka samu Mummy tana ganin Rufaida ta mik'e cikin sauri tare da kulawa tana kamo hannunta fadi take

'yata Barka da zuwa, kune a wannan lokacin?" Rufaida dai da kyar ta iya gaida Mummy sai wani sinne kai take ala dole tana kunya.

Shi kam uban tafiyar sai washe baki yake kamar gonar audiga

"Daga ina kuke?" Mummy ta tsinka shirun da falon ya yi na yan sakonni.

"Asbiti na kaita bata jin dadi."

"Ayya sannu'yata, ashe shi yasa na ganki a haka sannu Allah ya baki lafiya, mai yake damunta?" ta yi maganar tana kallon Najeeb.

Mika mata takaddan ya yi yana murmushi, "Alhamdulillah! Ta furta murya a bayyane, zuciyarta cike da farin ciki.

Sosai Mummy ta nuna farin cikinta, sai ririta Rufaida take sam bata son wani abu ya daga hankalinta, Najeeb dai gidan Mummy ya bar Rufaida da niyyar bayan magriba zai dawo ya dauketa.

****
Zaune suke cikin bedroom na Ameesha, Meena da Meesha ne suke hira, sannu a hankali har suka iso kan Dr, Meena sai fadan Alhairin sa da kirkinsa take yi.

Meesha tana sauraron.

Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗaura idonta a fuskar Meena ta ce

"Wai wa ya bama Dr Asmad damar shigowa gidan nan har cikin falo ne, ranar da zamu fita zaga gari a CAIRO wai Abba har da cewa in tambayi Dr na dade ina mamakin maganar fa?"

"Meesha kenan Dr ai yana da matsayin da kike da shi a gidan nan, ke kusan ya fiki ma."

Zaro ido ta yi jin maganar Meena ta ce

"Haba dai duka yaushe yasan nan gidan da har zai taka matsayin da nake ? Kema wallahi faɗa kawai kike yi."

"Allah da gaske Dr yana da matsayin da na sanar maki, wallahi da zaki san irin taimakon da ya yi wa rayuwar ki tabbas da sai kin ninka akan son da kike masa a da, Dr Asmad wani jigo ne a rayuwar ki."

"Hmmmm! Bana fahimtar bayanin ki fa, yi min dalla-dalla don nafi ganewa."

"Zan yi maki bayani amma ba yanzu ba." Meena tana gama fadin haka ta mik'e tare da fita daga bedroom din.

Cikin zallar jin dadi ya dauki hanyar gidan su Ameesha burinsa kawai ya ganta ko hankalinsa zai kwanta, lokacin da ya isa kofar gidan hon ya yiwa maigadin gidan da sauri ya wangale masa get, ciki ya cusa hancin motar a parking space ya yi parking, wayarsa ya kwasa sannan ya fita daga motar cikin kwanciyar hankali yake takusa mai firgita yan mata, hannunsa na juya keys din motarsa, kamar an ce ya dubi gefen haggunsa sai ko idon sa ya sauka kanta, cike da mamaki ya kara bude ido yana kallonta tabbas ita din ce, tsaye da wani mutum idan har ba gizo idonsa ke masa har murmushi ya hango kwance a kan kyakkyawar fuskanta.

Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi, kishinta da sonta suka rufe masa ido har bai san lokacin da ya isa inda take ba, bai jira komai ba ya finciki hannunta, a firgice take kallonsa ganin kamar ba a hayyacinsa ya ke ba yasa ta yi shiru, shi kam bai zame ko ina da ita ba sai cikin falo jefata kan kujera ya yi sai huci ya ke yi.

"Baki da hankali ne zaki je ki tsaya gaban wani kato har kina masa murmushi?" A kausashe yake maganar.

Harara ta jefa masa ta ce "ikon Allah kai a suwa kuma *kare da gudun layya*? Ina ruwan ka sani? Bana son shishshigi ban shiga rayuwar ka ba, don haka kaima karka shiga rayuwata, baka isa ka rabani da samarina ba." Cikin karaji ta dire maganar.

Murmushin takaici ya yi ya ce

"Ni kike tambaya matsayina a gareki? Tabbas kuwa nike da matsayi da iko dake."

Dariyar rainin hankali ta masa ta ce, "kenan kaine Abba? Don nasan babu mai iko dani kamar Abba, idan ko kai ba Abbana bane waye kai?"

"Mijinki ne ni." Ya bata amsa kai tsaye.

Wani irin ihu Meesha ta yi cike da tashin hankali ta ce"..."


_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

```Wannan page din Sadaukarwa ne ga KHADIJA BEE BEEN MASOYA uwar Ilham mata a wajen Hafiz, uwargida kike kinfi amarya 😉 Hajiya ki daɗe ki karko ki yi shekaru irin na dabino, Allah ya ja zamanin ta Masoya mai Masoya da yawa, wannan kirarin duk domin ki ne ke ɗaya Հմʆαίհզ ɾզησ tαηα ψίηKi ιяσи ѕσѕαι ∂ιи иαи😍😍😍```

*37*

"Miji? Mijin wa kenan?"

"Mijin Maryerm Taheer Ameesha, don haka ina kara gargadin ki da ki shiga hankalinki wallahi idan ba haka sai kin gane kuranki." Yana gama faɗa mata haka ya juya fuuu ya bar gidan ma gaba ɗaya domin ransa ya ɓaci da kallon Ameesha da wani.

Ita kam Meesha duniyar mamaki ta shi da jin furucin Dr "Wai mijina! To ta ya har ya zama mijina da har yake ikirari?" A bayyane take wannan tambayar da sauri ganin bata da amsa, sai ta nufi bedroom din Ummi domin samun amsoshin tambayoyin ta.

Ko sallama bata yi ba ta shige cikin dakin, Ummi dake zaune tana linke kayan da aka gogo mata sai ganin Ameesha ta yi a yam a kanta kamar wacce aka jeho.

"Oh! Ni Halima ke kam Auta zanga ranar da zaki yi hankali, lafiya kika shigo min daki a wannan yanayin?"

Kukan shagwaɓa ta fashe da shi ta zube a wajen

"Ke nifa bana son rashin hankali, daga tambaya sai ki kama kuka, naga alamar ke kullum SANGARTAR ki gaba take, idan ba zaki bani amsa ba tashi ki fita."

Mik'ewa ta yi tare da ficewa, a cewar ta Ummi ta kara bata mata rai, girgiza kai Ummi ta yi tare da fadin

"Allah ya shirya min ke Ameesha." Ta gama maganar tana ci gaba da abin da take yi.

Ameesha kam bedroom ɗinta ta shige inda ta ci gaba da kukanta, wani tunani ta yi wanda yasa ta yi saurin mik'ewa sai alokacin maganganun Meena ke dawo mata

*"Meesha kenan Dr ai yana da matsayin da kike da shi a gidan nan, ke kusan ya fiki ma."*

*"Allah da gaske Dr yana da matsayin da na sanar maki, wallahi da zaki san irin taimakon da ya yi wa rayuwar ki to tabbas da babu raini har abada tsakanin ku, kuma sai soyayyar da kike masa ta karu, Asmad wani jigo ne a rayuwar ki*

"JIGO? ta yi tambayar a bayyane, "kenan jigo na nufin mijina ne? Ta ya ya zama mijina? Me yasa daga ranar da na tuna komai zuwa yau ban fahimta ba?" Wa zan tara da wandinnan tarin tambayoyin?

"Abba." Shi ne amsa da wata zuciyar ta bata amsa.

Wani sabon kuka ta fashe da shi, wata zuciyar tana farin cikin samun Dr matsayin miji, wata zuciyar kuma tana alhini, a haka bacci ya yi awon gaba da ita.

Dr kan ransa a matukar ɓace ya bar gidan, zuciyarsa wani irin zafi take masa, bai san son da yake wa Ameesha ya zarta har haka ba, ji yake kamar zuciyarsa zata faso, kasa zuwa gidansa ya yi sai ya dauki hanyar gidan Nenne, idonsa jawur kamar garwashin.

Ko parking Mai kyau bai tsaya ya yi ba, ya fita daga motar cikin kai tsaye falo ya shi da wani irin sauri, sallama ma kasawa ya yi sai zubewa da ya yi akan kujera.

Bobbo da Nenne a tare suka ɗago da kai suna kallon Asmad wanda yake dafe kansa da hannu bibbiyu

"Lafiya?" Nenne ta yi masa tambaya.

"Babu komai." Ya basu amsa yana a yadda yake.

"Kai karka faɗa min zancen banza, ya ana tambayarka kana faɗa mana babu komai bayan ga a yanayin da ka shigo? A fusace Bobbo ya dire maganar.

"So nake Maryerm ta tare cikin satin nan." Jikinsa ko alamar motsi baiyi ba ya yi maganar.

"Maryerm ta tare anya kana cikin nutsuwarka kuwa Asmad?"

"Eh! Nenne ina cikin hankalina."

"To bazata tare a satin nan ba ka ji na faɗa maka, tashi ka bamu waje shashasha kawai." Cikin faɗa Bobbo yake maganar.

Sai a lokacin ya dago kansa tare da bude ido sa, wanda suke masa nauyi, hankalinsu ya tashi da ganin yadda Asmad ya koma.

Dafa kansa Nenne ta yi tana faɗin

"Asmad ka riƙa hakuri da duniya saurin fushi yana kawo dana sani, riƙa maimaita inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, zaka samu sassauci."

Gyada kai ya yi cikin zuciyarsa yana maimaita inna lillahi, a hankali ya ji zafin zuciyarsa yana ragu wa, su kam kallonsa kawai su ke yi, ganin an kira magriba sai Bobbo ya fita Masallaci, Nenne dai bata matsa ko ina ba har sai da ta ji abin da yasa ɗanta ɗaya tillo damuwa.

"Ina jinka Asmad ɗina mai ya sameka haka?"

"Nenne wai na je gidan su Ameesha shi ne na ganta da wani a tsaye, wallahil azeem Nenne raina ya mugun ɓaci har dai na kasa danne kishina na yi mata magana Allah Nenne baki ji amsar da ta bani ba." Cikin takaici ya gama maganar.

"To ka yi hakuri, Ameesha dai matarka ce, komai dadewa zata tare gidan ka, da kanka zaka koya mata yadda zata soka kuma bana tunanin tasan kai miji ne a gare ta, na tabbatar da saurayi ne yazo wajen ta Hajiya Halima ba zata barta ba, babu mamaki cikin masu zuwa dubata ne. saurin fushi yanzu ba naka bane kaji ko?"

"To amma Nenne sai ta saka shi gaba har tana masa murmushi?"

"Ka dai yi hakuri na ce, tashi ka je ka yi sallah lokaci na tafiya."

Kai ya gyada alamar ya gamsu da bayanin Nenne

******
A gajiye Alhaji Taheer ya shiga gida, yau ko bedroom ɗinsa bai nufa ba, a babban falo ya yada zango, yana furta

"Wash!

"Sannu da dawowa Alhaji ya aikin?" Ummi ta yi maganar tana mika masa sassanyan ruwa.

"Aikin Alhamdulillah! Wallahi na gaji sosai, duk na kosa in dawo." Abba ya yi maganar bayan ya gama shan ruwan.

"Ai gaka ka dawo hankali ya kwanta." Cikin murmushi ta fada.

"Lallai kuwa Halima tunda na yi tozali da ke hankalina ya kwanta."

"Hmmm! Alhaji kenan." Ummi ta, ka yi wanka lokacin sallah ya gabato go."

"Mu je uwargida kuma amarya." Cike da farin ciki Abba ya fita Masallaci, ko da ya dawo a falo ya yada zango, Ummi ce ta fito cikin kwalliyar ta, kusa da Alhaji Taheer ta zauna tana faɗin

"Alhaji an dawo?".

"Eh! Na dawo." Ya bata amsa.

"Abinci na jiranka."

"Ok wai ina yaran gidan ne? Uwata fa tunda na dawo ban ji motsinta ba?"

"Rigimammiya Ameesha ɗazun ta shigo wai zata tambayeni, na ce akan me shi ne ta fara kukan sangarta bata ce min komai ba ta fita, to nidai daga haka ban kuma ganin ta ba."

"Kuka?" Abba ya tambaya cikin mamaki.

"Eh! Alhaji Ummi ta tabbatar masa.

Wayarsa ya jawo Number Ameesha ya kira ringing biyu ta dauka muryar irin ta mai bacci.

"Subhanallah! Uwata lafiya kuwa?"

Shagwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce

"Abba Dr ne."

"Dr kuma me ya faru da Dr?" A rude yake mata tambayar.

Wannan karan bata yi magana ba sai kuka da ta fashe da shi mai tsuma zuciya, hankalin Abba ba karamin tashi ya yi ba da jin kukan Ameesha don haka cikin sauri ya ce

"Sauko ina falo kin jiko ki daina kuka haka nan."

Ummi dai zubawa sarautar Allah ido ta yi har zuwa lokacin da Meesha ta sauko, kusa da Abba ta zauna tare da ɗaura kanta a kafadar Abban, har a time ɗin idonta na hawaye, saurin sa hannu ya yi yana share mata.

"Sorry uwata ki bar kuka me ya samu Dr?"

"Abba da gaske wai Dr Asmad mijina ne?"

"Wa ya faɗa maki?" Abba ya yi tambayar yana dan bubbuga kafadar ta.

"Shi da kansa ya faɗa min."

"To kuma shi ne abin tada hankali uwata?" Cin kwanta da hankali Abba ke Magana.

Wasu hawaye ne suka kuma zubowa ta ce

"Abba ta ya har ya zama mijina bayan Bama son junanmu?"

Murmushi Abba ya yi cikin nutsuwar da lallama ya warware mata komai, babu abin da Abba ya boye mata, kuka sosai Meesha ta yi domin jin yadda Alhaji Mansur ya kirata mahaukaciya sannan ya yiwa Abban ta walak'anci, sosai ta yaba da mutuncin Dr da na Bobbo domin sune silar samun nutsuwar mahaifinta, sai dai bata so yadda auren ya zama kamar na hadi ba, taso taji labarin Dr da kansa ya ce yana sonta ba wai mahaifinsa ya nemi a ɗaura ba kamar yadda ta ji Abba ya fada

Wani irin zabura ta yi ta ce

"Abba Dr Asmad shi ne mijina? Abba shi ne fa wanda ya mareni a sahad."

Wani irin zabura Alhaji Taheer ya yi cikin tashin hankali ya ce what..?"


_Nima Yar mutan Rano tsawar da Abba ya yi ce tasani jifa da wayata, Ni kam har na firgita da yanayin Abban Ameesha🤔 wai to mai yake shiri cewa ne? Kardai ku manta Abba ya dau alkawarin duk ranar da ya yi ido hudu da wanda ya mari Ameesha sai ya hukunta shi._

_To kuma yanzu wane hukunci zaiwa Dr Asmad? ku biyoni don jin yadda zata kaya_

*Allah ya baki lafiya bestyna Khadija s Muhammad please kusa min ita a addu'a👏*

_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*


*38*

"Au dama Dr Asmad ne ya yi maki wannan walak'ancin?"

"Eh! Abbana." Meesha ta bashi tabbaci.

"Ai ko sai na nuna masa kurakuransa tunda ya taɓa min uwata."

"Yawwa Abba wallahi ka nuna masa kurakuransa, har yau idan na tuna marin raina yakan ɓaci, kuma fa shi ne sanadin da na daina zuwa sahad yanzu."

"Yi hakuri 'yar Abbanta tabbas Dr bai kyauta ba, don haka zan dau mataki, tashi ki ci abinci."

"Bari na je na yi wanka tashina daga bacci kenan ko wanke baki ban yi ba."

"A fito lafiya, amma don Allah Mamina a daina baccin yamma."

Dariya sosai Ameesha ta yi jin yadda Abba ya yi maganar, kamar wani marayan yaro

"Na daina in sha Allah."

"Allah ya yi albarka, je ki fito ina nan tare za mu yi dinner."

Amsawa ta yi tana tattaka matakalar benen. A jiyar zuciya Ummi ta saki, domin tun ɗazun ta suma da jin maganganun Abba da 'yarsa, gyara zama ta yi tare da maida hankali kan Alhaji Taheer ta ce

"Alhaji da gaske mataki zaka ɗauka kan Dr Asmad?"

"Me kika gani?"

"Na ji kana tabbatarwa da Auta ne, to wallahi Allah tun wuri ka sake tunani, wannan SANGARTAR da kake nunawa Auta sam ba abin arziki ba, kai yanzu ko shawara aka baka sai ka ɗauka Alhaji?" Cikin sanyi take maganar.

Murmushi ya yi irin tasu ta manya ya ce

"Haba Halima! Ai karen hauka bai cijeni ba, da har zan ce zan ɗauki mataki akan Dr Asmad, ba Dr ba wallahi ko wanine babu abin da zan masa, kin san menene hikimar amsa mata zan dau mataki?"

Girgiza kai Ummi ta yi idonta na kan fuskar Alhaji Taheer.

"Saboda yanzu uwata ta zama hukuma sai da lallashi, yanzu da ace ba haka na ce mata sanin kanki ne da yanzu bata bar kuka ba, to kin ji dalilin amsa mata, ai kaf duniya uwata bata da wani miji sama da Dr Asmad."

Murmushin nasara Ummi ta yi ta ce

"Madallah! Da maigidana abin alfahari na, tunanin ka abin sone ga kowa, Allah ya tabbatar da Alhairi."

"Hhhhhhhhh! Tunanina? Ko tunaninki? Ai yanzu duk wani abu da nake aiwatarwa ke ce SILAH, a da bana gane karatun da ki ke min amma yanzu Alhamdulillah! Allah ya maki albarka."

"Amin." Ummi ta amsa sannan suka ci gaba da hira, a haka Meesha ta same su, kai tsaye dining suka nufa domin yin dinner, sai a time ɗin Haydar ya dawo gida.

Bayan sun gama cin abinci, Ameesha suka ci gaba da hira ita da Abba rabi duk nusiha ne, ta yadda zata kula da Dr, domin cikin hikima da basira Abba ya tabbatar mata da aurenta da Dr babu fashi, domin dai Dr Alhairi ne a gare su.

Bayan duk ta gama jin bayanin Abba, sai ta mik'e cikin zallar SANGARTAR ta fashe da kuka, harda bubbuga kafa kamar dai wata karamar yarinya, da gudu ta kwasa ta yi sama cikin fushi.

Duk yadda Abba yaso ya shawo kanta abin ya gagara sai kawai ya barta.

Da niyyar da safe zai lallasheta

****

Yanzu dai zaman Dr da Aneesa sai madallah, domin tana kokarin yi masa duk wani biyayya, wannan duk aikin Rukky ne, a cewar ta ta haka ne zata samu Dr a hannu kafin Ameesha tazo.

Dr kansa ya ji dadin haka, domin ranar suna zaune bayan sun gama love dinsu, Aneesa tana jikinsa sai shagwaɓa take zuba masa, sai ya ɗago da fuskarta ya manna mata kiss ya ce

"My Anne don Allah Yanzu baki jin dadin zaman da muke yi?"

Wani murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ta ce

"Ni kam ke ji, yanzu ko da yaushe ina tare da mijina mu yi bacci tare mu ci abinci tare, kana nuna min soyayya komai duk wani hakki nawa kana kokarin saukewa, nikam a duniya mai ta kai min wannan daɗi? Wallahi Hamman ba bi shi."

"To kinga wallahi kaf duniya zaman lafiya ya fi komai, don haka Please mu zauna lafiya da juna ko da abokiyar zamanki ta zo a daure a rika kai zuciya nesa."

Wani irin faduwar gaba ta ji da ya ambato abokiyar zama, ita da har ta manta da wata matarsa, sai yanzu da ya tuna mata, da kyar ta iya tattaro nutsuwarta ta ce


"Karka damu Hamman baza'a samu matsala ba da yaddar Allah."

"Allah ya maki albarka matata."

"Amin." Ta amsa tana sauka daga jikinsa, toilet ta faɗa sai da ta sha kukanta kafin ta yi wanka ta fito, tana fitowa ya shiga ko kafin ya fito, har ta gama shafe-shafenta ta kwanta kamar mai bacci, alhalin kan ba bacci take ba kishi ne ya motsa.

Magana ya yi mata, tunda ya ji ta yi shiru sai kawai ya kwanta a bayanta, tare da rungumota jikinsa a haka bacci ya yi awon gaba da shi.

Ta daɗe tana takaici kafin bacci ya kwashe ta.

Da asbah kusan a tare suka farka, Dr toilet ya shiga ya dauro alwala sannan ya wuce masallaci, Aneesa kam bedroom ɗinta ta koma, sallah ta gabatar sannan ta koma bacci, sam ta ji bazata iya haɗa masa abin break ba, domin da takaicin sa ta kwana.

Bayan ya dawo masallaci, karatun Alkur'ani ya yi, ko da ya kammala sai ya dan kwanta

Please Login or Register in order to submit comment