Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bugu sosai. Lokacin da mutum zai dawo hankalinshi sai ya manta dukkan wasu abubuwa da suka faru da shi. Wannan ita ce ake kira Amnesia."

Ya tsahirta hade da kallon su Abba kafin ya ci gaba.

"Cutar ta kasu kashi - kashi, amma kashin da ya fi shahara shi ne: *Anterograde* da *Retrograde*

Antrograde: ita mutum baya iya tuna abinda ya faru da shi nan take, yanzu zai yi abu, yanzu kuma zai manta ya yi."

"Subhanallah! Abba ya fad'a cikin jimami

Likitan ya ci gaba " Retrograde kuwa, mutum ya kan manta komai ne na baya, sai dai ya dora sabon tunani."

"Allah mai iko" Abbah ya kuma fad'a.

"Cutar ba ta da magani da ake sha don a warke, sai dai ko a magance wani ciwo da aka ji a lokacin da tsautsayin ya faru. Kuma ba a yi mata aiki, ma'ana a yanka mutum don kwashe cutar. Dabaru kawai ake amfani dasu wajen magance ta, shi ne tunawa mutum duk abu muhimmi da ya faru da shi, yin wani abu a gabanshi wanda ya saba yi, ci ko shan wani favourite food na shi, sanya kida ko amfani da wani abu me kamshi da ya sani."

Ya dan tsahirta yana duban Asmad da ya yi shiru kamar bai taba jin bayanin cutar ba sai yau.

" Don haka da ma na fada maku, koda kun kawo ta zamu yi amfani da wasu hanyoyi ne don jaraba sa'armu, wanda ba lallai ne kuma ayi nasara ba. Kuma yanzu haka da su din muka yi amfani, inda muka yi nasara Kwakwalwarta ta cafki sauti guda daya, a yanayin yadda ta tashi, muna da tabbacin dawowar tunaninta, amma dai sai a hankali za ta rika tuna wasu abubuwan, abu d'aya zaku yi shi ne, tuna mata duk wani da kuka san tana yi lokacin da take da lafiya, ko kawo abinda kuka san tana so lokacin da take da lafiya....

"To in sha Allah zamu yi kokari Allah ya saka da Alhairi." Abba ne ya yi maganar cikin dakiyar zuciya.

Daga wannan bayanin suka yi sallama da Dr Ansar, cikin mutunci.


Sai da suka leka dakin da Ameesha take, ganin tana bacci yasa suka fita don komawa masaukinsu don su huta, tunanin Abba shi ne da me za'a fara tuni ga Ameesha.

DR bai tsaya jira su Abba ba, ya koma hotel zuciyarsa tana takaicin rashin sa bo da Ameesha kafin ta samu ciwon, domin da ace ya saba da ita da kansa zai rika tuna mata har ta koma dai dai, tunanin Meena ce ta fado masa a fili ya furta

"Dole ana bukatar Meena a wannan lokacin, domin tafi kowa sanin abin da Ameesha ke aikatawa da wanda ta fi so, matsalar bata a kusa da daga yau ta fara..." Da sauri ya juyo, ganin Abba ne ya dafa shi sai ya saki murmushi.

"Tunanin me kake yi haka sai sambatu kake yi?" Abba ya yi tambayar yana rike da kafadar Dr Asmad.

"Babu komai fa Abba."

"Ka kwantar da hankalinka ka ji ko? Mu je ciki ka samu ko abinci ka ci, dubi yadda ka koma lokaci ɗaya?"

"Bana jin yunwa Abba." Dr ya bashi amsa.

"No! Mu je dai ban yadda da kai ba." Cikin murmushi Abba ya dire maganar.

Babu yadda Dr ya iya haka nan ya bi su Abba ciki.

Shigar su dakin ba jimawa wayar Abba ya soma ruri, daukowa ya yi yana mamakin ganin Number Jaheed kuma da Number kasar CAIRO

"Ikon Allah." Ya furta yana kara wayar a kunnensa.

"Kuna airport fa ka ce? To sai ku dauko mota ta kawo ku, Steigenberger Hotel El-Tahrir muna ciki yanzu haka." Daga haka ya kashe wayar.

Ummi ta bishi da kallo ta ce

"Su waye ke airport?"

"Su Jaheed mana, wai sun kasa jure rashin ganin Ameesha, shi ne suka biyo mu."

Murmushi Ummi ta yi a zuciyarta ta ce "ikon Allah soyayyar yan'uwa jini daya ba wasa ba." Amma a fili sai ta ce

"To ai shi kenan tunda sun iso sun kyauta."

"Sun kyauta kuwa, amma da sun yi shawara baza su taho yanzu." Cikin faɗa Abba ya dire maganar yana shiga toilet.

Mintina ƙalilan suka kira Ummi suna sanar mata ga su cikin hotel ɗin, kusan a tare suka fita harabar hotel ɗin, Dr ma da yake ya ji wayar da suke har ya ri ga su zuwa, rungume juna sukai da Jaheed yana tambayarsa jikin Ameesha.

"Alhamdulillah! Dr ya bashi amsa, tare da kai dubansa ga Meena ya ce


"Madallah dake kawarmu wallahi kamar dai kin san muna da buk'atar ki a dai dai wannan lokacin."

Murmushi Meena ta yi ta ce

"Kuma sai gani, na kasa jure rashin ganin Ameesha na kwana biyu."

"Kamar yadda ita dinma yanzu taimakon ki take buk'ata, yanzu dai mu shiga ku samu ku ci abinci ku dan huta sai mu je wajen ta."

"Ina ai babu maganar hutu kawai a kaimu muga autar Ummi." Ya Jaheed ya yi maganar.

"To ai sai ku je mu kam zamu huta dawowar mu kenan." Abba ne ya yi masu maganar cikin fara'a.

To Abba suka amsa suna shiga cikin mota.


"Ke Meena da kin zauna ki huta, don yanayin jikinki fa."

"A'a Ummi zan iya zuwa, ina son ganin Meesha sosai ne nayi missing ɗin ta."

"To ai shi kenan a dawo lafiya."

Har a lokacin da suka isa asibitin Ameesha bacci take yi, don haka zama suka yi bayan sun gaisa da Nenne, tare da tambayar ta mai jiki.

"Da sauki tun ɗazun da ta farka ta koma bacci har yanzu bata tashi ba."

"Allah yasa ta tashi cikin nasara." Ya Jaheed ya faɗa.

"Amin." Nenne ta amsa tana faɗin

"Oh! Ni yarsu, sannu Meena da k'ok'ari ko nauyin jikinki baki ji?"

Murmushi ta yi ta ce

"Allah Nenne akan Meesha har mantawa nakeyi da wani nauyin jiki."

"Ai naga alama, Allah ya bar kaunar juna kin cika kawa ta gari, samun irin ki sai an tona."

Meena dai murmushi ta yi , tana zaune a ɗakin burinta bai wuce ganin Meesha ta farka, a lokacin kuwa su ya Jaheed da matarsa Badiyyah da mijin Meena Abdul hotel suka koma Meena da Dr sai Nenne kadai ke asibitin.

Sai da Meesha ta share awanni uku tana bacci kafin ta tashi, idonta kyar akan Meena tana kallonta, murmushi Meena ta yi ta ce

"Yes Meena ce Besty friend dinki a gaban ki, ya jikin?"

Ameesha shiru ta yi tana kallon Meena kamar mai son tuno wani, amma ta kasa, ita kam Meena buɗe jaka ta yi ta ciro kwalbar turare wani Meesha tafi kauna da so sunan turaren *Obsessed* a duniya shi ne turaren Meena.

Mik'awa Meesha ta yi cikin murmushi ta ce

"Ga tsaraba na kawo maki, nasan zaki yi farin ciki."

Amsa Meesha ta yi tana jijjuya...




_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:16 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*


*35*

So take ta tuna wani abu, sai dai sam k'wak'walwa ta ta kasa tunowa, Meena ta kula da haka sai kawai cikin sauri ta ce

"Kin manta ranar da muka je sahad, kika ga turaren har ki ka ɗauka! Duba sunan ki gani Obsessed sunansa."

"Meena Obsessed! Ameesha ta maimaita sunan da wata irin murya.

"Yes! Shi fatan kin tuna?"

A hankali lokacin da ta saya turaren ya fara dawo mata, sai dai ta kasa tuna wani abu bayan shi, kanta ne ya yi wani irin sarawa

"Wash! Ta furta a fili

"Mu je ki yi wanka kafin Abba ya zo."

"Abbana? Ina Abba yake Ummi fa?"

"Duk za ki gansu, yanzu dai ta shi ki yi wanka."

Da kanta ta yi wanka, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, sosai kayan sun yi mata kyau, Nenne ta haɗa mata shayi domin babu abinci cikin dakin, Dr Asmad ya tafi kawowa.

"Na gode! Ta faɗa tana kai cup bakinta, tas ta shanye tana aje cup din ta furta

"Alhamdulillah!"

Murmushin nasara Nenne ta yi, domin kuwa tabbas ta yadda Ameesha ta fara samun lafiya, tunda gashi har tana abubuwa da kanta.

"Ga wayar ki Ummi zata yi magana da ke." Meena ce ta yi maganar tana mik'awa Meesha wayar.

Amsar wayar ta yi tana kallon ta, sai kuma ta ɗago kai ta zubawa Meena ido, kafin ta yi magana sai jin sallamar su Abba suka yi, cikin masu amsawa har da Ameesha, wacce ta yi saurin tashi tsaye tana faɗin

"Abbana ina Ummi?" Ta kai karshen maganar tana fadawa jikinsa, don sam bata kula da Ummi ba balle su ya Jaheed.

"Kai masha Allah autar Ummi ta samu sauki, ga Ummin ki da su Jaheed." Abba ya faɗa yana dagota.

Kallon su ta yi tana ganin Ummi da sauri ta nufeta ta rungume ta cikin zallar farin ciki

Duk sun ji dadin ganin yadda ta koma, hira suka shiga yi ita dai Ameesha tana jin su, bata furta komai ba domin bata fahimtar inda hiran tasa gaba, a haka Dr Asmad ya yi sallama lokacin idonta a lumshe yake, jin sallamar sa yasa ta yi saurin bude ido domin dai take ta dauki muryar sa.

Fes ta sauke idonta akan fuskarsa, wani kallo suka wa junansu mai cike da ma'anoni daban daban, murmushi Dr ya saki tare da fadin

"Princess kin tashi?" Wani kasala ta saukar mata jin muryar sa, bata iya bashi amsa ba sai lumshe ido da tayi tare da buɗewa.

Kana kallon Dr zaka iya fahimtar yana cikin zallar farin ciki, da kansa ya zuba mata abincin ya mika mata, amsa ta yi har a time ɗin bata daina kallonsa ba.

Haka dai a hankali sauki ke samuwa ga Ameesha har aka yi kwana uku, a lokacin Dr Ansar ya ce zai sallame su, tunda zuwa yanzu ta fara tuna wasu abubuwan a hankali zata tuna komai.

Suna zaune dukan su, kanta yana saman cinyar Nenne ta yi kamar tana bacci, su kam dama hira suke zumbur kamar an tsikare ta ta mik'e tana waige-waige

"Ummi Ina Najeeb?"

"Najeeb kuma? Wanne Najeeb ɗin?"

"Ummi Najeeb mana yaron Alhaji Mansur abokin Abba?" Ameesha ta fada tana gyara zama.

"Autar Ummi Najeeb yana Nigeria fa, nan muna CAIRO ne."

"Cairo kuma? To mai ya kawo mu?"

"Baki da lafiya ne aka kawo ki."

"Bani da lafiya? To mai ya sameni? To amma Ummi ai ko a ina nake ya kamata yazo, ya zama shi zan fara gani, tunda har Abba ya soma maganar aurenmu da shi."

Shiru suka yi suna sauraron maganar ta, cike da mamaki Meena ce ta yi karfin halin yin magana

"Meesha ya sunana?"

"Haba wannan wane irin tambaya ne? Meena mai kika mai dani?"

"Yi hakuri k'awata zaki iya lissafo min duk mutanen dake dakin nan?"

Harara ta watsawa Meena ta ce

"Eh! Duk na sansu *Ummina, Meena k'awata, ga Abbana* ke duk na sanku na tuna komai.

"Kin tuna komai fa kika ce?"

"Eh! Ta bata amsa kai tsaye.

"A ranar da Abba ya kai ki school, bayan kin fito lacca zaki koma me ya faru da ke a hanya?" Meena ta yi saurin jefa mata tambaya.

"Na fito daga school na je tsallaka titi naji karan wani abu, to nidai daga haka ban kuma sanin komai ba sai yanzu."

"Gud k'awata ta koma normal Alhamdulillah!

"Amma wadinnnan ne ban san ko su waye ba.

Ta nuna su Nenne da Bobbo

"Karki damu suma kin sansu domin su ɗin suna da matukar muhimmanci a rayuwar ki, a hankali zaki san matsayin su a gareki." Ummi ta bata amsa.

Shafa kanta Nenne ta yi ta ce

" karki damu 'yata, ki kwantar da hankalinki."

Gyada kai ta yi tana gyara kwanciya, sallamar Dr ne yasa ta buɗe ido, da mamaki take kallonsa bakinta har yana rawa ta ce

"Dr!

"Na'am Princess ya jikin naki?"

Harara ta aika masa tare da fadin

"Ni kam lafiyata lau."

"Au to yi hakuri lafiyar ki lau, Allah ya kara mana lafiya." Ko kafin ta yi magana ya riga ta

"Abba Dr Ansar fa ya bamu sallama, ko yanzu zamu iya barin asibitin tunda an samu nasara."

"Kai madallah! Yanzu to sai mu hada kayanmu, mu koma hotel zuwa gobe sai mu koma Nigeria."

Duk sun yi na'am da maganar Abba, don haka cikin sauri suka haɗa kayan su, hotel suka koma Ameesha sai zubawa Abba shagwaɓa take a hanya, shi kam biye mata yake domin dai yana cikin farin cikin dawowar ta dai dai.

Suna isa kowa ya shiga dakinsa, Ameesha kam cewa ta yi inda Nenne take nan zata zauna, domin kuwa lokaci ɗaya Allah ya daura mata son Nenne saboda ta kula Nenne tana da kyawun hali.

Suna shiga akan kujera ta zube tana furta

"Wash! Kallonta Nenne ta yi ta ce

"Lafiya?"

"Lafiya lau Nennena."

Da sauri Dr ya kalleta jin yadda ta ce wai Nennenta.

"To ai shi kenan yanzu dai bari na yi wanka, sai mu fita harabar hotel mu dan sha iska, wallahi na gaji da zaman waje daya." Nenne ce mai maganar tana shiga bedroom.

"A fito lafiya Nennena." Meesha ta faɗa tana gyara kwanciya, wayarta ta jawo dan kallon wayar ta yi, cikin phone ta shiga tana duba kiran da kai mata a hankali take sauke Number har ta isa kan wanda take tunanin lambar Dr ne.

Ta ɗan yi mamaki ganin 23 /june /2018, kenan a yadda Meena ta faɗa mata ta yi wata kusan uku tare da ciwon tunda yau dai 7/ August /2018, ikon Allah lallai Allah yana kaunata. Cikin zuciyarta take maganar.

Fita ta yi ta shiga contact, number din Ni'eema ta gani, murmushi ta yi tare da danna mata ki, ringing biyu ta dauka

"Meena ko Meesha?" Shi ne farkon tambayar da ta yi.

Murmushi Meesha ta yi ta ce "Meesha ce fatan kina lafiya?"

Cike da mamaki Ni'eema ta amsa

"Lafiya lau ya jikin?" Da yake Meena ta sanar mata da ciwon Meesha ɗin, kuma lokaci zuwa lokaci takan kira ta tambayi jikin Ameesha, shi yasa yanzu ta cika da mamakin ganin kiran Meesha.

"Na warke fa nikam, ina Fasmir da Yumna?"

"Duk suna lafiya, in sha Allah gobe zamu zo gaida ki."

"Bamu dawo ba, muna Egypt yanzu haka, amma gobe zamu dawo da yaddar Allah."

"Allah ya dawo da ku lafiya." Hira suka ci gaba da yi, ya yin da Dr ya zubawa Ameesha ido, shi dai a duniya tana matukar burgeshi, duk wani abu da zata yi kyau yake mata, yana jin sonta kota ina babu ma kamar yanzu da ya yi wani irin sabo da dumin jikinta.

Muryar Nenne ce ta dawo da shi daga tunanin da ya lula

"Wayar ce dai har yanzu bata kare ba?"

"Eh! Nenne da wata k'awata muke yi, wai gobe zata zo gaidani shi ne na ce mata bamu dawo ba."

"Ayya gaskiya tana da kirki."

"Sosai kam Ni'eema keda kirki, yawwa Nenne tunda kin fito bari na cewa Abba mu zaga gari tunda gobe zamu tafi."

"Babu inda zaki." Dr ne ya yi maganar yana ci gaba da danna wayarsa.

Wani irin juyowa Ameesha ta yi ta ce

"Kai kuma a suwa da zaka hana ni fita *Ji shiga uku takabar suruki*,To sai naje ɗin. Meesha ta faɗa tana fita daga dakin.

Nenne kam harara ta aika masa da shi ta ce

"Ina ruwan ko? Kana ganin yarinyar an samu da kyar Allah ya taimaka shi ne zaka ɓullo da wata maganar?

"Allah ya baku hakuri ne..."



Wai typing da wahala Yaseen.



_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:16 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

Dedicated to _*RAHEENAT MAMOUDOU (HEENART)*_

```Betsy Allah ya baki lafiya, jin ciwon ki nake kamar a jikina yake 😭😭 sosai na yi missing ɗin ki, Allah yasa kaffara ne```👏
*36*


Nenne bata ce masa komai ba, sai ma zama da ta yi tana jiran zuwan Ameesha, bata fi minti biyar ba ta dawo da ganin yadda ta turo baki zaka san da magana, kusa da Nenne ta zauna cikin zallar SANGARTAR da ta saba.

" 'Yata lafiya kuwa?"

"Ba Abba bane wai inzo in tambayi Dr, idan ya bari sai mu tafi." Cike da shagwaɓa har da dira kafa kamar wata karamar yarinya ta ida maganar.

Wani irin murmushi Dr ya saki don tabbas ya ji dadin maganar Abba, ya kuma bashi wani matsayin na musamman, domin ya cika suruki na gaske.

Sosai ta cika da mamakin furucin Abba da ya ce sai da izinin Dr zata fita, to wani matsayi Dr ke da shi a wajenta da har Abba zai fadi wannan maganar?" Tambayar ta yiwa kanta wanda bata da amsar sa, ko kafin ta lalubo amsa sai jin maganar Nenne ta yi.

"To kai ka ji abin da ta ce ko?" Babu alamar dariya Nenne ta masa tambaya.

"Eh! Na ji Nenne a dawo lafiya, mu je nima ina son k'ara ganin garin."

Kusan a tare suka fito, domin su Meena ma yawon zaga garin zasu je, haka suka fita suna hira Ummi da Nenne suna taɓa hira, Meena da Meesha ma haka, sai su Jaheed da Dr, sun zaga gari sosai har sayayya suka yi, Dr ma ya sayawa Aneesa tsaraba domin ya faranta mata, washe gari jirjin karfe takwas suka bi.

*NIGERIA*

ko da jirgin su ya sauka kowa gidan sa ya nufa, Dr dai kin bin su Nenne ya yi domin cewa ya yi sai ya kai Ameesha har gida, Allah ya sani baya son rabuwa da ita don dai ya zama dole ne.

Yana cikin gidan sai wajen karfe shida ya fita, a lokacin tuni Aneesa ta shirya masa lafiyayyen girki, shi kadai take jira ganin har shida ta yi sai ranta ya soma ɓaci domin ta yi amanna yana tare da Ameesha shi yasa ya manta da ita.

Sallama ya yi tare da shiga cikin falon, Aneesa dake zaune ta watsa masa wani irin kallo tare da dauke kai

"My Anne mai nayi kuma daga dawowata?" Ya yi maganar tare da hugging ɗinta.

Bata fuska ta yi ta turo baki, tana mutsu-mutsu so take ta zame jikinta daga rikon da ya mata

"Sorry na yi laifi ko? Amma fa ba laifi na yi ba, kinsa tare da mara lafiya nake dole tana da buk'atar kulawa."

Kuka ta fashe masa da shi tana faɗin.

"Ai Ni bana buk'atar kulawa tunda har ka tafi kusan kwana goma." Da shashsheka take maganar.

Gyara rikonta ya yi ya ce

"Please ki yi hakuri bazan kuma ba, kin ji matata farin cikina?"

"Babu komai ya wuce."

"Da gaske?"

"Eh! Mu je ka yi wanka sai ka ci abinci."

"Yawwa matata yar albarka."

Aneesa ta taimaka masa ya yi wanka, jallabiya ya zira lokacin ana kiran sallar magriba, masallacin kofar gidan ya je lokacin da ya dawo bai taras da ita a falo ba, don haka sai ya nufi bedroom ɗinta, zaune ya ganta gaban dressing mirror tana fesa turare, shakar kamshin ya yi yana rungume ta jikinsa.

"My Anne kin yi kyau."

"Na gode." Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.

"Ranka ya daɗe mu je ka ci abinci."

"No! Barni in gama shakar kamshin matata."

"Please." Ta faɗa kamar zata yi kuka.

Sakinta ya yi ya riƙe hannunta, a haka suka isa dining room din. Da kanta take ciyar da shi har ya koshi, falo suka koma, ranar dai sosai Dr ya cika da mamakin canzawar Aneesa.

Washe gari tun wuri Dr ya shirya domin ziyartar asbiti, bai biya ko ina ba, domin baya son ya yi latti ya dai turawa Ameesha text message na barka da safiya, karfe takwas a asbiti ta yi masa da yake sun san ya dawo komai a gyare ya taras, aiki sosai Dr ya

Please Login or Register in order to submit comment