Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin dai ba zai fita office da wuri ba, nannauyan bacci ya kwashe shi, bai farka ba sai 9:30 shi din ma wata mahaukaciyar yunwa ta tayar da shi.

Wanka ya yi ya yi shirin fita, falo ya fita babu kowa ya duba dining babu komai akan dining din, sai ya nufi bedroom a kwance ya hango ta ta yi dai dai tana ci gaba da sharar bacci.

Cikin takaici ya girgiza kai tare da fita daga gidan gaba daya, gidan Nenne ya nufa don yasan can suna da komai, bayan sun gaisa ne ya ce

"Nenne yunwa ta biyo dani nan gidan fa."

"Yunwa ina Aneesar?" Nenne ta tambaya cike da mamaki.

"Wallahi Nenne bacci take yi kamar dai bata jin dadin jikinta ne." Ya ɓoye don kar Nenne ta fahimci wani abu.

"Allah ya bata lafiya." Shi ne abin da Nenne ta faɗa tana nufa dining, mintina ƙalilan

Nenne ta kawo masa break, yana ci suna hira har suka sauka kan na Ameesha gyara zama Nenne ta yi tana fuskantar Dr ta ce

"Wai kuwa Asmad ka koma gidansu Ameesha?"

"Ban koma ba Nenne." Kai tsaye ya bata amsa.

"Menene dalili?"

"Bana son ta kuma bata min rai."

"Kai bana son shashanci, ko ka manta matarka ce Ameesha, dole sai kana mantawa da wasu abubuwan kuma ai ɗan Adam ajazi ne, tana da hakki akan ka, don haka ya zama wajibi ka kula da hakkin ta."

"To Nenne in sha Allah, yau zan biya idan na dawo." Yana maganar ne bayan ya mik'e tsaye.

"Allah ya yi albarka."

Daga haka Dr ya bar gidan, ko da ya isa office bai wani jima ba, domin babu wani aiki tunda ranar ta ƙkasance asabar ne, da ya bar asbiti, wani mall ya biya ya yiwa Ameesha shopping don yasan ta da shan kayan zaki, yana fita diret gidan Alhaji Taheer ya nufa, ya yi hon maigadi ya buɗe masa, ya faka motar sannan ya daga waya ya kira number ɗinta.

Lokacin tana zaune ta yi nisa cikin tunaninsa, sai yanzu take dana sanin abin da ta masa ga shi rabon ta da shi tun ranar da ya bar gidan cikin zuciya babu mamaki ma fushi ya yi da ita.

Wayar ta ce dake kusa da ita ta fara ruri, a zabura ta kalli wayar, har murza ido ta yi don son ta gasgata abin da ta gani tabbas Number Dr Asmad ne, cikin sanyin jiki ta ɗauki wayar tare da karawa a kunne

"Assalamu Alaikum." Ta furta cikin siririyar murya.

Daga ɓangaren Dr sai da ya saki ajiyar zuciya jin muryar Ameesha

"Wa'alaikumus salam, ki fito ina jiran ki domin sauri nake." Abin da ya faɗa kenan ya kashe wayar.

Jiki a sanyaye ta mik'e ta kudirta sai ta ba Dr haushi tunda haka yake faɗa mata, sai da ta gyara fuskarta, ta nufi bedroom din Ummi, sanar mata ta yi da zuwan Dr ya ce

"Yana jirana."

"To ki shigo da shi falo mana, ke kamar wata mara wayau ki ke." Ummi ta faɗa cikin takaici.

"To." Ta amsa tana nufa waje.

Jingine yake jikin motarsa, ya zubawa hanyar da Ameesha zata fito ido, can yaga ta nufo wajensa cikin takunta mai daukar hankali, sosai ta tafi da hankalinsa har bai san time da ta iso wajen ba, sai jin sansanyar kamshi turarenta da ya gauraye wajen, dogo da kai ya yi tare da zuba mata ido.

"Sannu da zuwa." Ta faɗa tana kauda kai gefe.

"Yawwa."

Ya amsa a dakile, shiru ne ya ratsa na yan dakiku, sannan yasa hannu cikin mota ya dauko mata ledar da ya shigo mata da shi, yana tambayarta

"Ga wannan ki yi amfani da shi, baki jin komai a jikinki ko?"

"Eh!" Ta bashi amsa. Bata da niyyar amsan ledar.

"Princess ke fa nake mik'awa?"

"No! Dr ka barshi kawai na gode."

Da mamaki ya kalleta, cikin zuciyarsa ya ce "lallai yarinyar nan, Ni kikawa laifi amma kuma ke kike jin haushi na, aikam sai kin gane kuranki.

A fili kam sai ya ce "amsa ki kaiwa Meena, tunda ke baki buk'ata."

Babu musu ta amsa, Dr dai kuma kallonta ya yi ya ce

"Dama nazo dubaki ne tunda babu matsala zan wuce." Ya ida maganar yana buɗe kofar motar

"Ina son zuwa gidan Nenne."

"Allah ya dawo da ke lafiya, amma ki sani karki kuskura ki tuka mota da kanki." Yana maganar ne yana kunna motar, ko kafin Ameesha ta yi magana sai ganin motar Abba suka yi.

Cikin sauri Dr ya fito yana gaida Abba cikin yanayi me nuna alamar jin kunya, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana tambayarsa su Bobbo

"Duk suna lafiya." Dr ya bashi amsa, kanshi a kasa.

"Naji daɗin zuwanka domin tun jiya naso kiranka, akan ka fara shiri uwata ta tare a ɗakinta, zamanta haka babu amfani, kamar yaushe kake ganin zata tare ɗin?"


Shiru Dr ya yi, har yanzu kanshi a kasa, bai nuna alamar zai yi magana ba. Duk dai a zuciyarshi
Sosai ya ji dadin maganar Abba, don dama haka yake so kuma ga damar ta samu.

"Ko akwai matsala ne?" Abba ya tambaya gani shirun ya yi yawa


Har yanzu kanshi a kasa yake, yayin da ya kai hannunshi yana shafo kanshi

"To Abba, amma akwai wasu yan gyare-gyaren da zan yiwa bangaren ta, nan da sati biyu zafi kyau." Cikin ladabi ya yi maganar.

"Allah ya kaimu." Daga haka suka yi sallama.


_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*


*39*

Gida kai tsaye Dr ya nufa, bayan ya kira Hafiz ya sanar masa, yadda suka yi da Abba, cikin kwanakin sam Dr baya samun zama domin aikin da akewa sashin Ameesha, suma a bangaren Nenne da Ummi abin haka yake, Ameesha tana ta shan gyara, wata mata aka dauko mata musamman domin ta gyara ta.

Shirye-shiryen biki ya kankama yau saura kwana biyu tarewa, duka gidajen biyu cike yake da mutane wanda suka zo domin taya su murna, sosai Dr ya yi bajinta wajen haɗa mata akwatina. Aneesa kam idan hankalinta ya yi dubu to fa a tashe yake, musamman da taga irin kuɗin da Dr ya kashe wa Ameesha, duk sai ta ji ta raina kanta. Cikin tashin hankali ta dauki waya ta danna Number din Rukky ringing biyu ta dauka

"Hello Rukky! Aneesa ta faɗa cike da tashin hankali.

"K'awata lafiya kuwa na ji muryar ki a haka?"

"Babu lafiya kam domin jibi matar Hamman zata tare, kin ga irin kuɗin da yake kashe mata kuwa?"

"Ina zan sani ina Adamawa kina Kano?" Rukky ta faɗa.

"Wallahi kuwa Rukky, wallahi ina cikin tashin hankali, Please ki bani shawara."

"Kin ga Aneesa kwantar da hankalinki, ki bari ta tare sai asan yadda za'a yi, amma ki fito fili ki nuna masa fushinki."

"Hmmmm! Rukky kenan wai kina ganin Hamman yana wani damuwa ne idan yaga ina fushi?"

"Ko baya damuwa ki nuna masa."

"To shi kenan zan jaraba, zaki ji komai." Daga haka suka yi sallama, ita kam Aneesa ta ci gaba da kai komo tana neman mafita.

Wow gaskiya bangaren da za'a sanya Ameesha ya haɗu sosai, tuni aka kawo kanya daki an daka komai sai jiran zuwan amarya, Dr kam cike yake da farin ciki, ko yaushe fuskarsa ɗauke da murmushi.

Dinner kawai suka shirya, wanda za'a yi ranar tarewar, Dr ya yi gayyata sosai musamman abokansa da abokan aikinsa na kasashe daban daban, ciki har da Dr Ansar wanda ya taso takanas don hidimar bikin Dr Asmad, ya samu tarba mai kyau daga Hafiz domin shi ne ma masaukin baki, kuma babban abokin ango.

Abba, Bobbo da Dr, sai Hafiz angon wata dakakkiyar shadda suka yi, zanenta iri ɗaya da ta su ya Jaheed sai dai kalar ya bambanta, karfe uku aka tashi daga walimar da Bobbo ya haɗa don farin cikin Auren Asmad

Nenne da Bobbo suka zaunar da Dr suna masa nasiha akan ya riki matansa cikin amana da adalci

"Kana jina ko Asmad? Ina so ka sanya hakuri da juriya da kai zuciya nesa a cikin zamantakewar ku, ka kasance mai adalci tsakanin matanka, ka zama tsayayye namiji mai mulkar da adalci."

"In sha Allah Babbo zan yi amfani da duk abin da ka faɗa min."

"Allah ya maka albarka, Ubangiji ya baka zuri'a dayyaba."

"Amin." Dr ya amsa.

Ita ma Nenne haka ta yi masa nasiha mai tsuma zuciya, kafin suka sallame shi. Komawa cikin abokansa ya yi inda aka ci gaba da harkoki.

Ameesha da Dr Asmad yau ranar ta kasance ranar farin ciki ne a gare su, kallon fuskarsu kawai zai baka tabbacin haka, sanye take ciki wani rantsattsen lacce mara nauyi, wanda ya yi mugun amsar jikinta fuskar nan ta sha meka'up har wani kyalli take, duk inda ta gifta sai kamshin turarenta ke tashi, kawaye ta duk sun halarci taron tarewar ta, ciki har da Ni'eema sosai Ameesha ta yi farin cikin ganin ta.

Liyafa sosai aka hada, an ci kuma an sha, an dauki hotuna domin tarihi kai abin dai gwanin sha'awa cikin lafiya da salama aka gudanar da taron, karfe biyar Abba da kansa ya kai Ameesha gida Dr bayan tarin nasihar da tasha a wajen Ummi da Abba, kuka sosai ta yi har idonta ya yi jawur.

Ko time da Abba yasata cikin ɗakinta sai da ya kuma mata nasiha, mai sanyaya zuciya, kafin ya yi mata sallama, shiru ta yi zaune cikin dakin ita ɗaya hawaye suna zubowa daga cikin idonta, maganar Abba ta karshe ita ta kuma sanyaya mata jiki

*"Uwata ki sani ni da kaina na kawoki gidan aurenki, duk ranar da kika fita daga gidan nan da sunan ya ji karki kuskura ki nufo gidana, domin nan shi ne gidanki marufar asirin ki, mutuwa kaɗai nake fatan ta rabaki da gidan nan, Allah ya maki albarka."* Cikin murya mai kamar ta kuka ya gama maganar, don taga lokacin da yasa hannu ya share hawaye.

A fili ta furta "In sha Allah Abba zan yi maka biyayya." Ta yi maganar tana share wasu hawaye da suka zubo. Sai kuma ta tuno nasihar Ummi, kamar yanzu take mata maganar

"Ameesha ki kula da jinsa, ganinsa, da kuma dandanon mijinki,

*1 karki bari ya ji wani abu da daga hankalinsa, ko ta tsaftar jikinki, jikinki ya kasance ko yaushe cikin kamshi na turaruka, haka falonki da ɗakunan baccinku, bakinki da duk wani lungu da sako na jikinki*

*2 ma'ana karki bari yaga wani abu da zai bata ransa akanki, musamman ta bangaren gidanki ko jikinki*


*1 karki kasance kullum cikin girka masa abinci kala ɗaya, a'a ko wacce rana ki yi masa kaloli daban-daban kuma ba guda ɗaya ya ba ki yi hakuri da biyayya, karki kuskura ki bijirewa umarninsa domin aljannarki tana karkashin kafarsa, duk maganar da zaki yi masa ta zama cikin tsusasa murya da nutsuwa, in sha Allah matukar kika lazumci yin haka zaki ci ribar zaman aure.*

Tana cikin wannan tunanin ne ta jiyo motsin mutane kamar a falo, ko kafin ta yi wani kwaukwarar motsi har sun shigo bedroom din, muryar Aunty Saude k'anwar Ummi ta ji, ai da sauri ta daga gyalen ta sauka a gadon tana faɗin

"Sannu Aunty dama yanzu nake tunanin ni kadai a gidan har tsoro ya fara kamani."

"Nima Aunty Halima ta sanyamu zuwa, don ta ce bata son abarki ke ɗaya, nan da wasu awanni idan zaku je dinner zamu koma."

"Ai kam na gode wa Ummina." Hira suka shiga yi da Aunty Saude har lokacin da Dr ya bugo mata waya akan ta shirya, mai mata kwalliya zata shigo don yi mata

"To." Ta amsa tana gyara kwanciya.

Mintina ƙalilan ta ji sallama, lokacin Meena da wasu daga cikin kawayenta sun iso gidan, wanka Meesha ta sake sannan tare da dauro alwala, tana cikin sallah mai mata kwalliya ta iso, bayan ta isar Aunty Teena ta tsantsara mata kwalliya sosai Meesha ta yi kyau, gama kwalliyar babu dadewa motocin su Dr ya iso, cikin rakiyar Meena ta isa wajen motar da Dr ke ciki, cikin sanyin murya ta yi sallama tare da shiga, amsawa ya yi cikin kasalalliyar murya yana lumshe ido, domin kamashin turaren ta ya kashe masa jiki, Meesha kam kasa ta yi da kanta don ji ta yi a takure take.

A haka suka isa wajen, lokacin wajen ya cika sosai da dan adam, suna zuwa aka soma gudanar da shagalin.

Sosai dinner ta yi kyau, anci an sha, Aneesa ma an halarci wajen dinner, sosai ta yi kokarin danne kishinta har aka tashi, karfe goma aka tashi gida Dr da Ameesha kawai suka nufi gidan

Rike da hannunta Dr yake har cikin bedroom ɗinta, akan gadon ta ya yi mata masauki, yana faɗin


"Heartbeat ki zauna ki huta ina zuwa." Ya yi maganar yana buɗe gyalen ta.

Saurin rintse ido ta yi, domin yadda yake mata wani irin kallo, da kyar ta iya daga kai ta amsa, domin gaba daya jinta take kamar a daure, murmushi ya saki sannan ya bar dakin.

Mota ya dauka bai dade da fita ba ya dawo, hannunsa dauke da manyan ledoji, falon Ameesha ya shiga ya aje, sannan ya nufi bangaren Aneesa, a falo ya iskota ta zuba uban tagumi, zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"My Anne baki kwanta ba?"

"Yanzu nake son kwanciyar." Ta bashi amsa tana mik'ewa.

"Ok ga wannan bari." Ya yi maganar yana mik'a mata."

Ko kallonsa bata tsaya yi ba, ta yi shigewarta idonta taf da hawaye, tsaye Dr ya yi cikin mamaki halin Aneesa, sai kuma ya nufi bedroom ɗinta tunawa da ya yi da Ameesha ita ɗaya.

A kan gado ya ga ta zube tana aikin kuka, da kyar ya lallasheta ya nufi bangaren Ameesha, tana ganin ya fita ta kuma sakin wani kukan, Dr kam ko da ya koma bed din Ameesha a kwance ya sameta.

"Heartbeat ba dai har kin yi bacci ba?"

"Zan yi dai." Ta bashi amsa.

"Oya tashi ba zaki kwanta da yunwa ba."

"Dr nifa na koshi."

"No! Maryam tashi ki ci."

Tashi ta yi tana turo baki, falo ya koma ya dauko plet, juye masu lafiyayyen kasashen kaji ya yi, ya tsiyaya masu fresh milk a glass cup, lallaɓata ya yi ta ci kadan ta ce ta koshi

"Je ki yi brosh sai ki kwanta nasan kin gaji da yawa."

"To." Ta amsa tana mik'ewa, bata jima ba ta fito kwanciya ta yi tana addu'ar bacci, bata daɗe da kwanciya ba bacci ya kwashe ta.

Murmushi Dr ya yi ganin har bacci ya kwashe Ameesha, lallai bata da wuyar bacci, sai a lokacin ya soma ci, sai da ya koshi sannan ya tattara kayan ya kai kicin, dawowa ya yi yana tofe ta da addu'a ya rufe ta da bargo tare da kara mata gudun AC sannan ya fita.


*YAR MUTAN RANO*
[10/8, 8:17 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*


*40*

Bedroom ɗinsa ya nufa, sai da ya soma rage kayan jikinsa sannan ya faɗa toilet ruwa ya watsawa jikinsa, bayan ya fito ya gabatar da sallah, jikinsa ya shafe da mai tare da feshe ko ina da turarr, kayan bacci ya sanya sai ya bi lafin gado bakin sa dauke da addu'a, bai wani dade ba bacci ya yi a won gaba da shi, mai cike da mafarkin Ameesha. Kiran sallar asuba ya farkar da shi, mika ya yi tare da addu'a kana ya nufi toilet ya dauro alwala, bai ta yar da sallah ba sai da ya je dakin Ameesha wacce ke sharar bacci, a hankali ya matsa inda take tare da kai lallausan hannunsa fuskarta yana mata waiwayi.

Buɗe idonta ta yi mai cike da bacci, ta zuba su bisa fuskar Dr.

"Lokacin sallah ya yi tashi ki yi."

Mika ta yi tare da hamma alamar dai bacci bai isheta ba, ta amsa da

"To."

Yana zaune har ta shiga ta fito, sannan ya jasu sallah suna idarwa Ameesha ta sanyaya murya ta ce

"Ina kwana Dr!"

"Lafiya lau Heartbeat fatan kin tashi lafiya ya sabon waje?"

Murmushi ta yi kanta a kasa ta ce "Alhamdulillah!"

"Madallah! Yanzu dai nasan kina da buk'atar hutu, je ki kwanta ki huta zuwa anjima."

Mik'ewa ta yi ta nufi gadon, shima Dr gadon ya nufa ya kwanta cikin hikima ya jawota jikinsa tare da rungumota, kamar zai mai da ta ciki duk da son jiki irin na Ameesha amma ganin yadda Dr ya cusata jikinsa sai ta fara k'ok'ari janye jikinta, shi kuma ya ki barinta, gajiya ta yi ta barshi a haka bacci ya kwashe su.

Basu farka ba sai karfe tara, Dr ne ya soma tashi sannan Ameesha bed ɗinsa ya nufa don yin wanka, shaf shaf Dr ya yi wanka ya fita, kai tsaye bangaren Aneesa ya nufa.

A hakimce ya ganta zaune kan kujera, ko sallamar da ya yi kin amsa masa ta yi

"Kin tashi lafiya?"

Banza ta kuma masa, bai yi zuciya ba ya kuma faɗin

"Kin yi break ne?"

Mtsss ta ja tsaki ta ce

"Ina ruwanka da break ɗin na? Kai dai ba kana can tare da matarka ba, kaga kenan rashin yin break na ba matsalar ka ba ce." Tana dire maganar ta yi shigewarta bedroom.

Tsayawa kawai Dr ya yi yana kallon Aneesa, tun yana mamakin halinta zuwa yanzu har ya daina, nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da kaɗa kai ya fita.

Mota ya ɗauka ya fita, don nemo masu abin da za su ci, bai ta de ba ya dawo, wannan karon ma falonta ya shiga, mika mata tek away din ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fita, yana jin lokacin da ja tsaki.

A bangaren Ameesha bayan Dr ya fita itama toilet ta shiga wanka ta sillo daure da towel gaban madubi ta yi masauki, duk ilahirin jikinta ta shafe da mai kafin ta nufi wordrop da niyyar dauko kayanta, sai jin sallamar Dr ta yi take wani irin kunya ta kamata, motsi ma kasawa ta yi don kunya.

"Heartbeat baki gama shiryawa ba?" Shiru ta yi ta kasa ko da ɗago kai.

Ganin taki magana yasa ya karasa inda take yana faɗin

"Kinga Wallahi yunwa nake ji fa kuma nasan kema haka Please bari na shirya ki." Ya yi maganar yana sa hannu cikin wordrop ɗin, kaya ya dauko mata riga da siket da pant and bra, aje su ya yi kan gado tare da riko hannunta.

"Please Dr ka barni zan iya sawa fa." A hankali ta yi maganar.

"No! Bana so ki wahala bari na shirya ki kawai."

"Please.. "

Ko sauraron maganar ta bai yi ba, sai ma fara sanya mata pant da bra, tsaf ya shirya ta har yana shafa mata hoda, ita kam sai turo baki take har da kukan sangarta, hannunta ya ja sai falo a dining ya yi mata masauki, don ya yi masu tek away, tsaf ya shirya masu komai a kan dining.

Da kansa ya zuba mata komai sannan ya soma bata shi ma yana ci, suna ci suna soyayyar su har suka gama, tashi Ameesha ta yi tare da kwashe duk wani kaya da suka bata ta yi kicin da su, bata fito ba sai da ta wanke tare da gyara kicin ɗin. Dr na zaune shi kadai a falon yana jiran ta fito amma ya ji shiru sai kawai ya bita kicin ɗin, zaro ido ya yi cikin mamaki ya ce

"Heartbeat aikin me kike yi kuma?"

Murmushi ta saki ta ce

"Dr gyara kicin nake yi."

"Me yasa baki kirani ba?"

"In kiraka ka yi min me?" Da mamaki ta yi tambayar.

"Aikin mana." ya bata amsa.

"Hmmm! Dr kenan ai wannan ba irin aikinka bane nawa ne don haka na hutace ka." Yadda take maganar kawai abin birgewa ce. Domin har kasala ta saukarwa Dr.

"Ni dai ban yadda da wayonki ba, Heartbeat kullum nafi so ki rika hutawa kinji ko?" Ya yi maganar yana jan hancinta.

Dariya suka yi gaba daya, ta ce

"Na daina Dr."

"Yawwa autar Ummi mu je mu gaida Aneesa."

"To." Ta amsa tana tafiya.

Yana rike da hannunta suka yi sallama a falon Aneesa, Aneesa wacce ke zaune ta buga uban tagumi saurin ɗago da kai ta yi, tana amsawa cikin murmushin karfin hali ganin Dr da Ameesha. Ji ta yi kamar ta tashi ta shake Ameesha, wani irin kishin Dr ke a zalzalar ta, da kyar ta yi control ɗin kanta ta tattaro nutsuwarta ta furta masu

"Sannun ku da zuwa."

"Yawwa." Yawwa Dr ya amsa .

Yana zama a kan kujera Ameesha kuwa a kasa kusa da kafar Dr.

"Hamman ina kwana?"

"Lafiya lau My Anee ya kika tashi?"

"Lafiya lau."

"Ina kwana?" Ameesha ta faɗa cikin sanyin murya.

"Lafiya." Shi ne amsar da Aneesar ta bata, bayan ta dauki kusan minti biyar kafin ta amsa tana aika mata harara.

Gyaran murya Dr ya yi, wanda yasa duk suka nutsu tare da maida hankali kansa, godiya ya soma yi ga Allah da ya nuna masa wannan rana, sannan ya soma masu nusiha cikin kwantar da murya akan su zauna lafiya da junansu baya son tashin hankali. Shiru suka masa har ya gama sannan ya tambaye su ko da mai wata matsala

"Babu." Ameesha ta ba shi amsa.

Aneesa kam banza ta masa sai jijjiga kai da hura hanci take yi, ko kallon inda suke bata yi ba.

"Don Allah ku zauna lafiya, matuk'ar kuka zauna lafiya to kwanciyar hankalina ne, haka in akasin zaman lafiya ta samu wallahi tashin hankalina ne, ku rika kai zuciya nesa ku yi koyi da kishin matan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama."

"Allah ya bamu iko." Cikin siririyar murya ta yi maganar.

Aneesa kam ka sa cewa komai ta yi domin, ji ta yi wani kuka yana shirin zuwa mata, tana son Dr son da batawa kanta tana matukar kishinsa wanda har take jin kamar ba zata iya takwara zuciyarta ba, don haka ganin ya gama sai ta mik'e kamar dai wata kububuwa ta yi shigewarta bedroom

Ameesha kam hamma ta saki, don ta gaji da zaman, kallonta Dr ya yi ya ce

"Ya dai autar Ummi bacci ko?"

Kai ta gyaɗa alamar "eh."

"Ok tashi mu je ki kwanta." Ya yi maganar yana k'ok'arin tashi tsaye.

" *Wai Auta*! Aneesa ta maimaita sunan, wato ma ita ce Auta, sai wani narkewa ta ke masa, hmmmm! Zan yi maganin ku daga ke har shi, ganin yana niyyar tafiya yasa Aneesa ta ce

"Hamman ina son zuwa gidan Nenne, domin yau yan Adamawa zasu koma zan je masu sallama." Ta yi maganar ne tana maida kwallar da suke niyyar zubowa.

"Allah ya kiyaye hanya." Ya yi maganar yana mik'ewa tsaye rike da hannun Ameesha.

Kallonsa ta yi cikin wani irin yanayi, hankalinta ya tashi ganin yadda Dr ya mata, don haka suna fita ta saki wani irin kuka mai cin rai, tana bakin ciki da Auren Dr ta kula son da Dr kewa Ameesha ko kwansa baya mata, lallai sai ta mik'e tsaye domin ta samowa kanta yanci.

Dr kam suna fita daga falon ɗaga Ameesha ya yi sama tare da rungumeta, ita kuma sai ciccila kafa take alamar ya sauketa, bai sauketa ba sai ma ci gaba da tafiya da ya yi har suka shiga falonta, a nan ma bai sauketa ba sai juyata da yake kamar wata yar baby.

Kukan sangarta ta fashe masa da shi, ko hawaye babu tana ta bubbuga masa kirji

"Lalala autar Ummi an ya kuwa kina cin abinci?"

"Ni dai ka saukeni gaskiya Dr."

"Allah ba zan saukeki ba, tambayarki nake kina cin abinci kuwa?"

"Ina ci sosai ma, amma m e ka gani Dr?"

"Sam baki da

Please Login or Register in order to submit comment