Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amince, har ma Alhaji Taheer ɗin.

" Wayyo Taheer na kusa tarwatsa maka farin cikin ka, na kusa sanya maka takaici."

Girgiza kai Najeeb ya yi cikin takaici da dana sanin biye wa mahaifin nashi buɗe baki ya yi yace "Abba............"



_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:02 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*

*10*
"Abba gaskiya abin da kake son aikatawa bashi da kyau, ka dubi girman amintar dake tsakanin ku da Abban Ameesha, amma Abba yau har kai kake son yin amfani da ɗiyar sa don cimma wani buri na..."

Wata muguwar tsawa ya daka masa, ransa a matuk'ar ɓace ya katse Najeeb cikin sauri.

"Kai Najeeb har ka kai matsayin da zaka zauna kana min wa'azi? To bari ka ji Allah yasa Masallaci ne kai ,ba malami ba tashi kabani waje tun ban tsinka maka mari ba."

Tashi Najeeb ɗin ya yi yana faɗin

" Allah ya huci zuciyar ka Abbana."

Dogon tsaki Alhaji Mansur ya ja tare da shigewa bedroom ɗinsa.

Najeeb na fita bangaren Mominsa ya shiga, zama ya yi a falon tare da dafe kai, don kwata kwata tunanin sa ya kulle ,da yana da yadda zai yi tofa lallai da ya hana mahaifinsa aiwatar da wannan mummunan aikin.

Sai dai bashi da wannan damar don mahaifinsa ya kasance mutum ne mai mugun ra'ayi, duk abin da ya yi niyya tofa sai ya cimma biyan buk'atar sa.

Haka Najeeb ya kasance cikin tunane tunanen yadda zata kaya, shi dai yasan a wannan gaɓar tabbas ya kamu da don Ameesha so kuma na gaskiya, bawai na yaudara ba.

**************************************

(" Asmad noi haa jotta minanai ad'on wolwa hala yahugo Adamawa da yald'e bangal d'on badita lutti burai sati tatii.") " Asmad har yanzu ban ji kana maganar zuwa Adamawa ba, ga lokaci nata gabatowa yaufa kwata kwata bai fi sati uku bikin ba amma, baka ko maganar zuwa."

(Nanne wii Asmad binni.) ce kewa Asmad maganar.

(O wo'ini jode mako dendenta o lorni hakkilo mako do Nenne owii.) Gyara zama ya yi tare da maida hankalinsa kacokan kan Nanne yace

(" To Nenne jotta saito miyahi Adamawa? Minna mi anda tomi andino da miyahino miwarti.") Yo Nanne wai a haka har Adamawa zanje, ni ai ban yi wannan tunanin ba, da tuni naje ai."

(Nenne d'oiliti moo) Harara ta yi masa cikin wasa,ta ce

( "Nananam 6ingel, jotta ad'on numa na saito a yahi ha Aneesa maan? To dei on narrata be mako?" )" Kuji min yaro , yanzu kai kana tunanin ba sai kaje wajen Aneesa ba? To kenan ta ya zaku fahimci juna?"

(" Allah Nenne sina gam awolwi mii tammai saito miyahi, amma jotta de a hirliti aam der satii do miyahan.") " Allah Nanne ban da yanzu da kika yi maganar ban san sai naje ba, amma tunda haka ne insha Allah cikin satin nan zan yi k'ok'arin shiga."

(" Yawwa barkantejo yahu Allah wanne barka.") Yawwa ɗan kirki ka k'ok'arta ka shiga ɗin Allah ya yi albarka."

("Amin") "Amin Nanne."

(Asmad noti d'on lara agogo jungo mako.) ya amsa yana kallon agogon hannunsa.

("Nanne hami yaha Asibiti gammi d'on momi wanni *CS* o badeke fintugo.") "Nanne bari na tafi asibiti don akwai wacce nayi wa *CS* to ta kusa farkawa."

("Allah wallu Nenne wii.") "Allah ya taimaka."

Nanne ta faɗa.

Mintina goma suka kai shi asibitin, a parking space ya paka motar sa, wasu takaddu ya kai hannu zai ɗauko kamar ance ya ɗago kai, sai kuwa idon sa ya sauka akan su.

Kara buɗe ido ya yi sosai, tabbas itan ce suke hira da saurayi da alama tana jin daɗin hiran musamman yadda take ta sakin murmushi, kana kallon su zaka gane su ɗin masoya ne, shi duk gani ganin da yake mata bai taɓa koda ganin tayi murmushi ba, amma gashi yau har dariya take, ji ya yi ransa ya sosu da ganin da ya mata haka.

_*( A'a ikon Allah, kuji shiga uku takabar suruki, inji Kamala Minna, in ba shiga uku ba ina ruwan Asmad da Ameesha? To ko dai ko dai..... bari nayi shiru don ban tabbatar ba.)*_

A fusace ya fita daga motar cikin zuciyarsa yana dana sanin zuwan sa asibiti a dai dai wannan lokacin, tabbas da yasan irin wannan gamon zai yi gaskiya babu abin da zai kawo shi.

Office ɗin sa ya shiga, sam bai samu sukuni ba a wannan rana, don hoton su kawai yake gani kota ina, tsaki kam har ya yi babu adadi.

Haka dai ya yi ta duba majinyatan nashi, duk don ya manta dasu amma ina kamar ma yanzu suke zaunen haka yake gani.

Su kam bama su san ya na yi ba, don hiran su suke sha irin ta masoya, Najeeb ne ya kawowa Ameesha ziyara har asibitin, karkashin wata bishiya suka zauna sai hira suke zubawa, sosai Ameesha ta kamu da yawa, bata k'aunar abin da zai raba ta da Najeeb don tana masa wani irin so ne.

Sun daɗe suna hiran kafin su ka yi sallama, shi ma badon sun so rabuwa da juna ba, Najeeb ya soma wucewa ita kuma ta kuma shiga ciki inda Meena ke jiranta

"Kai Meesha hala da ba zaku rabu da juna ba ne ? Kin shanyani Bros Abdul sai kirana yake."

"Ki bari kawai Meena wallahi in Ina tare da Najeeb bana k'aunar abin da zai gifta da sunan katse mana jin daɗin mu."

" Yana da kyau haka, yanzu dai tashi muje lokaci kan ya tafi sosai."

Meena ta k'arasa maganar tana ɗaukar jakarta, Meesha ma jakarta ta ɗauka sannan suka nufi inda motar Ameesha ya ke, suna zuwa shima Asmad na zuwa don shi ɗin ma gida zashi ya gaji da takaicin da yake tunawa

" Dr sai gobe."

Meena ce mai maganar,ita Madam ko kallon sa bata yi ba tayi shigewarta mota.

Murmushi ya yi ya ce

" Allah ya kaimu."

Tsaki taja tare da bama motar wuta ta juyo ta kalli Meena ta ce

"Ke kam kin fiye cusa kai ba k'warjini, wannan miskilin kikewa magana?"

" Babu wani cusa kai, yanzu ke fisbilillah ya da ce mu wuce ba tare da munyi sallama da shi ba?"

" Yo Ina ruwan biri da gada?"

Tayi maganar tana watsa hannu irin ko a jikina

Gyada kai Meena tayi cikin zuciyarta ta ce

"Allah ya shirya min ke."

Meesha kam bata kuma magana ba,don wayarta ta ɗauko ta kunna wak'a ,ita ma shiru ta yi har suka iso kofar gidan su Meena , buɗe kofa Meena ta yi ta ce

" To ta Najeeb! jikam sai gobe in Allah ya kaimu."

" Allah ya kaimu, don Allah ki zomin da han out ɗin nan na Chemistry, don gobe school zamu shiga kuma test jibi."

" Ok zan fito maki da shi ɗin."

Meena ta kai karshen maganar tana nufa get ɗin gidan su.

Meena tana wu ce wa, sai ta soma duba wasu takaddun ta ,duk ta duba motar babu ,da sauri ta kira Meena ta ce bata gansu ba, fitowa Meena ta yi ta ce "ki koma asibiti, muje ina raka ki."


"No Meena koma gida kawai bari na koma asibitin."

Ta ida maganar tana juya kan motar ,gudu take yi kai tsaye asibitin ta shiga don babu tantama a cen ta zubar, addu'a takeyi Allah yasa ta gani.

Tana shiga ta faka motar cikin sauri sauri ta fita , cikin ta shiga ta dudduba amma bata gani ba, bayan ta gama duba duk inda take saran ganin takaddun amma bata gani ba. Sai kawai ta dawo gurin motar jiki a mace, ji take kamar ta kwanta ta yi ta birgima da ƙafafuwanta kamar dai yadda yara suke yi idan abu ya ɓata masu rai sosai. Ta kai hannu jiki a mace da niyyar buɗe motar sai ta ji magana kamar daga sama.

" Lafiya ki ka dawo?"

Ta juyo kamar ta k'wala ihu, rasa abin da zata ce ta yi,sai ta zuba ma sa ido game da langaɓar da kai gefe hawayen da ta ke ɓoyewa , suka ziraro.

Mamaki ya kama Asmad,duk irin tsiwarta,yau kuma ita ce ta koma haka. Sai kawai ya yi murmushin da yake k'arawa fuskarsa kyau , buɗe wani file ya yi ya zaro takardun tare da mik'a mata.


_*Yar Mutan Rano*_
[10/8, 8:05 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

``` ina matukar taya ki murna my sweet sister BILKISU BILYAMIN Ubangiji Allah yasa kifi haka Allah ya kara baiwar fasaha da kaifin brain```

*Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*

*11*

A hankali cikin mutuwar jiki ta kai hannu ta amsa.

" Na gode"

Ameesha ta yi maganar cikin wani irin voice.

Murmushin nan ne dai kwance a fuskar sa

" no need "

Ya bata amsa, yana juya kai, bai wani bata lokaci ba ya tada motarsa don dama jiranta ya tsaya yi, kuma tunda ta dawo har ta amshi abin ta mai zai tsaya yi.

Fuskar nan tata yake gani kota ina, yanayin da ta shiga dazun yake mamaki, da wannan tunanin ya kama hanyar gidan su.

Ameesha kuwa bayan wucewar sa, da kallo ta raka motar har sai da ya kulewa ganin ta sannan ta saki wani sansanyan ajiyar zuciya a fili ta furta

" Allah na gode maka."

Motarta ta koma, zuciyar ta cike da tunanin Dr dan fullo, da irin taimakon da ya mata a wannan rana, da wannan tunanin ta isa gida.

Parking ta yi tare da zaro hand back din ta, cikin rashin kwarin jiki ta nufi hanyar shiga falo, dan juyowar da zata yi sai ko idonta ya sauka kan motar Najeeb dake aje a parking space, siririn tsaki taja ranta ya dan sosu da ganin motar.

Falo ta shiga ko sallama bata samu ikon yi ba sai ma zubewa da ta yi a kujeran falon ta furta

" Wash! "

Ummi dake fitowa daga kicin ta zubawa Ameesha ido, da mamaki ta ke kallonta don duk wanda ya ga Ameesha yasan ba a cikin nutsuwa take ba.

" Lafiya kuwa Auta? "

Ummi ta karasa tambayar tana nufa inda Ameesha ta ke.

Wani murmushi ta k'ak'alo wanda iya karsa lebe, don tun kallon da Asmad ya mata Jikinta ke mace.

" Ummi lafiya lau fa, kawai gajiya ce."

Ta bata amsa tare da maida hankali kan Ummi.

Zama Hajiya Halima tayi tare da riko hannun Ameesha, don ko kadan bata kaunar damuwar Ameesha.

" Anya kuwa Ameesha? Jifa yadda kika koma kodai baki da lafiya ne? "

Girgiza kai tayi alamar a'a.
" Are your sure?"

"Sure Ummi."

" OK tashi kije kiyi wanka, sai ki ci abinci, ga Najeeb can yana jiran ki."

"To " kawai ta amsa tana mikewa.

A toilet ma dai da Ameesha ta shiga, duk tunanin Asmad din ne a zuciyar ta, ruwa ta watsa tana fitowa ta shirya, Yau simple dress tayi, don riga da siket ta sanya na atamfa, powder ta mursa sai lipstick da ta shafa, ya zuwa wannan lokacin miss call a wayarta sun haurawa ashirin, a fusace ta dauki wayar

" Hello." ta fada bayan ta Kara wayar a kunne.

Banji mai aka ce mata ba Sai ce wa ta yi, ai nasan da zuwan ka amma yau sai dai ka daga min Kafa don ina da bukatar in samu nutsuwa."


Fadin haka keda wuya ta yanke kiran, tare da jifa da wayar rai a bace, tafiya ta soma yi don sauka falo, domin tasan matukar bata sauka falon ba to Ummi sai ta daga hankalin ta.

Najeeb kuwa tunda ya ga Ameesha ta datse kiran, yasan da matsala, shi kuma baya son tambaya don haka sai ya fito daga falon bakin da yake, jikin sa a sanyaye yana Addu'a Allah yasa ba shi ya bata mata rai ba.


Koda ta kammala da cin abinci sama ta koma, tana shiga taji karar wayarta, da sauri ta karasa tare da d'auka, suna nan Meena ta gani akan screen din.

" Ya Meesha wai kuwa kinga takardun? "

Ajiyar zuciya ta ja ta ce

" Eh Meena na gani a asbiti."

" Masha Allah, wallahi tun dazun tunani kawai nake yi fa."

" Ki bari kawai Meena zamu hadu a school akwai labari."

" Allah k'awata? "

" Allah kuwa."

" Dan fara bani labari mana kin san ni da son jin labari."

" No maganar bata yuwuwa a waya, ki dai bari har mu hadu din zai fi."

"To ai shi kenan." Meena ta fada.

Daga haka sukayi sallama.

*************************
Koda Asmad ya shiga gidan, bangaren sa ya soma shiga ruwa ya watsa sannan ya nufi babban falo, da sallama ya shiga.

Nenne da wata ne kadai suke zaune a falo, amsa masa sallamar su ka yi, ya ida shiga yana fadin

"Nenne barka da yammaci, Adda sannu da zuwa. "

" Yawwa Asmad an dawo? Ya aikin ya kuma masu jiki? "

" Aiki Alhamdulillah! Masu jiki da sauki. "

Zamewa kasa ya yi tare da gaida Addan, cikin sakin fuska ta amsa, bakuwa ce tazo daga adamawa matar Yayar Nennen Asmad, ta zo ne kan maganar bikin Asmad din.

Amsawa ta yi cikin farin ciki ta ce

" Asmad ango ya shirye shirye? "

Dukar da kai kasa ya yi cikin kunya bai ce komai ba, sai ma tashi da ya yi ya nufi kicin don yana jin yunwa, koda ya dibi abincin bai zauna a falo ba sai bangaren sa da ya nufa, don gaba d'aya kunyar Nenne da Adda ya ke ji.

Bayan ya kammala cin abinci ne ya koma cikin bedroom din sa, zama ya yi a bakin gadon sa, hannun sa ya kai saman sumarsa ya na shafawa a hankali, a hankali ya furzar da wani irin iska mai zafi, dai dai da soma ringing din wayarsa, juyo da kai ya yi ya dubi wayar sunan da ya gani ne yasa shi dan jan tsaki.

Bai dauki wayar ba sai ci gaba da tunanin sa kawai ya yi, fuskar Ameesha ce ke masa gizo, ya rasa fahimtar yadda ya ke ji game da ita.

****************************

Zaune suke a karkashin wata bashiya, saurin dago da kai Meena ta yi bayan ta gama jin labarin da Meesha ta ba, baki bude don tsananin mamaki ta ce

"Meesha Dr dan fullo fa kika ce? yaushe kuka dai dai ta da shi? "

" ki bari kawai amma wallahi jiya nayi matukar mamaki, da ya bani takardun nan, kinsan Allah daga jiya zuwa yau sai naji cikin kashi dari na haushin da nake ji nashi, ashirin da biyar sun fita."

Murmushi Meena ta yi cikin dai mamakin maganar nata ta ce

" Kuma ina maganar rama Mari aka barta? "

" Tana nan sai na rama komai dadewa. "

Taba Meena amsa tare da gyara zama.

" Amma nifa gani nake kamar gaba kadan zaku zama masoya, musamman yadda kuke hakan alamar soyayya ce."

Harara Meesha ta watsa wa Meena ta ce

" Allah ya kyauta waye zai yi soyayya da wannan mutumin, kema kin san na wu ce da ajinsa."

Dariyar rainin hankali ta yi ta ce

" Lallai Meesha ke Wai kina ganin kin fi Dr dan fullo aji ne? To wallahi bari kiji duk fa inda kike tunanin sa ya fi haka. "

Tsaki kawai ta yi tare da tashi tsaye.

Itama Meena ganin haka sai ta mike, suka kama hanyar su da yake daman sun riga da sun gama laccan ranar.

Yau dai sauran kwana bakwai bikin su Yaya Jaheed da Yaya Abdul Malik, shirye shiryen bikin ake ta yi kota ina, tuni gidan Alhaji Taheer ya cika da mutane domin wannan shine karon farko da zai fara auraswa, su Ameesha kam babu zama, sai kai komo ake musamman da Ya Abdul din Meena zai aura.

Kudin da Abban ta ya bata kawai don shagalin biki, dubu dari uku ne, a ce warsa baya son ta nemi komai ta rasa har a gama bikin.

Suna kwance a dakin Meena, bayan sun dawo daga shopping don a gajiye suke likis, wayar Ameesha ce ta soma ruri alamar neman agaji dan dago da kai tayi a hankali ta dubi fuskar wayar, Sunan da ta gani ne yasa ta sakin murmushi. Cikin sauri ta dauki wayar

" Hello."

Ta fada cikin sansanyar murya.

Daga bangaren Najeeb din lumshe ido ya yi, cikin jin dadin muryar da ya ratsa masa kunnuwa.

" Baby son ki na neman hallaka ni fa."

Murmushi mai sauti ta yi ta ce

" Kamar yadda naka ke wahalar dani."

"Kina ina ne haka? "

" Gani gidan su Meena."

" OK bari na zo don ina son ganin beauty face naki."

" Allah ya kawo ka lafiya." ta fada tana gyara kwanciya.

"Please Meesha ga number din Dr ki tura masa da text din bikin."

Maganar da Meena ta fada kenan wanda yasa Meesha saurin tashi zaune wani harara ta watsawa ta ta ce..."

_*Yar Mutan Rano*
[10/8, 8:06 PM] Zulayheart Rano: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
*12*

Ta ce " A haba dai Meena kema kinsan haka ba zai yuwu ba, sai dai ki kawo wayar ki in yi masa da naki."

Murmushi Meena taja ta ce

" To ai ga wayar nan kusa da ke ki yi masa, nidai burina Allah ya sa ya zo, don shima satin sama ne bikin sa."

Wani mummunan faduwar gaba ya zuyarci Ameesha lokaci guda, tare da wani irin sarawa da kanta ya yi, ji taji kamar Meena ta watsa mata ruwan zafi

" Da gaske auren sa ya kusa? "

Tayi tambayar hankali a dan tashe.

Mamaki ya kama Meena ganin yadda ta tashi hankalin ta lokaci daya, tabbas tasan wacece Ameesha ta kuma san halinta tsaf, a wannan karon ma akwai tunanin da take a kan Ameesha da Dr dan fullo.

Saurin kawar da tunanin ta yi tace
" Allah kuwa lokacin da ake maganar a asbiti kina ina? "

Da sauri ta wayan ce don kar Meena ta gane ta ce

" Oh! Wallahi kam na manta, Allah ya sanya Alhairi."

" To ai yanzu na tuna maki don haka sai ki shirya masa abin gudummawa."

Tsaki kawai Meesha ta ja tare da gyara kwanciya,bayan ta tura masa text din, zuciyar ta na wani irin zafi da maganar da Meena ta fada mata, har tana mamakin kanta na jin faduwar gaba da taji maganar auren sa.

Haka akayi ta shagalin bikin, anyi lafiya kuma an tashi lafiya, Meena gidan su Ameesha aka kaita bangaren da Yaya Abdul ya gina, ya yin da ita kuma matar Yaya Jaheed take gidan da ya gina a sabuwar gwandu, Dr dan fullo ya yi kokari wajen halartan bikin.

Tun kafin a gama bikin Ameesha ke Fama da wani zazzafan jiwon kai, da zazzabi daurewa ta tayi har aka gama bikin, Yau dai abin yana nema ya yi yawa don har ta kai ga ta kwanta jikinta ko ina rawa yake hakoran ta sai haduwa suke da juna.

Hajiya Halima ce ta haura saman Ameesha, ganin har rana tayi sosai bata fito ba gashi suna da school, don haka sai ta ce bari ta leka ta ga ko lafiya

" Inna Lillahi wa Inna ilaihin Raju'un! Shine abin da ta fada tare da saurin karasawa bakin gadon da take kwance.

" Auta lafiya meke damunki? "

Da kyar ta iya faɗin

" Zazzabi"

Hankali tashe ta dauki wayar Ameesha dake kusa da ita ta soma kiran layin Yaya Abdul.

Minti uku kacal sai gashi sun iso tare da Meena, suma hankalin su ya tashi da ganin jikin Ameesha

"Kira Dr don jikin nata sam babu dadi."

" Ummi asbiti ya kamata muje fa, kalli yadda ta ke? "
" Eh ina ga zuwa asbitin zai fi."

" Gaskiya kam Ummi."

" Je ka fitar da mota, bari mu fito da ita. "

Ita dai Ameesha bata ma San abin da su ke yi ba, don yadda take jin jikin nata.

Ummi da Meena suka taimaka mata har zuwa wajen mota.

*******************************

Asmad ne zaune shi da abokan su, suna ta tsara yadda bakin zai kasance, shi dai shiru ya masu ko ta tafasa a sauke bai ce ba, tunanin sa na kan Ameesha wacce yau kusan kwana uku bai ganta ba.

A takaice dai tun ranar daurin auren Meena da ya ganta, kuma yasan itan bata gan shi ba, don a lokacin tana tare da wasu ne sun ɗibo kayan da zasuyi amfani da shi a wajen walima.

Ba karamin kyau ta yi masa ba, kyau na gaske har yake ganin kaf matan duniya babu kamar ta, take ya hasaso kyau Aneesa don ita ma fa ba baya ba wajen kyau, amma sai ya ga Meesha ta fita sau dubu, matsala daya gareta shi ne jin kai, koda ya ke wannan jin kan da takeyi shi yake kara mata kwarjini.

" Ango lafiya kuwa irin wannan dogon tunani? In ka kwantar da hankalin ka kwana nawa ya rage? "

Wani daga cikin abokan sa ne yake magana.

Girgiza kai ya yi tare da bude baki da niyyar magana sai ringing na wayar sa ya hana shi, dan tsaki yaja tare da ciro wayar ya danna tare da karawa a kunne muryan da ya ji ne ya sa shi saurin tashi tsaye.

" bata da lafiya kuna ina yanzu? "

" Inna Lillahi! " ya kuma fada a rude.

" Ina zakaje kuma? "

" Sorry Hafiz nemana ake, wata ce bata da lafiya an kaita asbitin mu, kuma tunda suka nemeni abin ya dan girma, don haka zan wuce in na gama komai zan dawo. "

Yana gama faɗin haka ya fita daga falon.

" Allah ya bata lafiya." suka hada baki wajen faɗa

Kai tsaye asbiti ya nufa, cikin sauri sauri ya faɗa motarsa, emergency room ya nufa da sassarfa, don nan aka shiga da ita ko office bai nufa ba, haka kuma bai tsaya duba jama'ar da ke waje ba, nurse ya samu a kanta sun ɗaura mata dirif na ruwa.

Kallon ta ya yi cikin mamaki ganin yadda ta koma, daga ganin da ya mata zuwa yau.


Koda ya kai hannu jikinta ya yaji mugun zafi, take yasa wata daga cikin nurse din ta hada masa allura, wacce ke saurin saukar da zazzabi, hankali sa a tashe yake da ganin Ameesha a matsayin mara lafiya.

Cikin ikon Allah ba'afi minti goma ba sai zafin jikin ya ragu, sai a sannan ya samu dan nutsuwa har ya fita, yana fita Ummi ta yi saurin ta sowa tana tambayar sa jikin Ameesha.

Kallon Ummi ya yi take ya gane ita din ce mahaifiyar Ameesha, don muguwar kamar da su ka yi. Murmushi ya saki mai kwantar wa da mutum hankali ya ce

" Karki damu Hajiya ta samu sauki don yanzu ma bacci takeyi, Kuma zazzabin ya sauka, insha Allah sanda zata farka zata koma normal, gajiyar da tayi na aikace aikace ne wanda bata sababa shi ya haifar mata da zazzabin . "

(Hmmm abin mamaki su Ameesha *SANGARTA* na damunki, daga aikin biki sai ciwo? Kodai kodai damuwar wani akasa a zuciya?

Please Login or Register in order to submit comment