Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗin "wai Nenne Ameesha ta haɗa tea da kanta amma sai ta dauke wanda kika haɗa min, bayan nawa bai kai kaurin nata ba." Ya ida maganar ya kai cup bakinsa, da sauri ya zubar da wanda ya kurba tare da aje cup din.

Kallonsa Nenne ta yi ta ce

" Lafiya kuwa menene ka zubo da shi?

"Nenne tea din fa ɗaci yake saboda tsabar sugar da ta cika." Cikin dariya da mamakin yadda Ameesha ta iya wayon haka ya ida maganar.

"Au ho! Wato shi yasa ta kasa sha kenan? Ikon Allah wannan abu da mamaki fa."

"Yo ai bazai sha wu ba kam, hakan da ta yi ba karamin daɗi ya yi ba, domin in sha Allahu da alamar nasara."

"To Allah ya taimaka, bari na hada maka wani yaushe ne tafiyar taku?"

"Jibi ne zamu tafi, kawai Nenne ki bar shi idan na tsaya sha zan yi latti."

"Allah ya kaimu, fatan ka sanar da Aneesa?"

"A'a ban sanar mata ba."

"Sam haka bai kamata ba, idan ka koma ka sanar mata, Asmad ka kasance mai adalci tsakanin matanka fa."

"In sha Allahu zan kasance Nenne, walllahi abin ne ya ɗan shige min, amma yau da na koma zan sanar da ita." Ya dire maganar yana k'ok'arin tafiya.

"Allah ya baka iko amma ka dai daure ka sha sai ka ji dadin tafiyar."

Sam Dr ba ya son musu da Nennensa shi yasa ya zauna. Zuwa wannan lokacin tuni har Ameesha ta shanye tea din Dr har ta dire cup.

Nenne tana gama haɗa masa ta mike zata bar dining Dr ya ce

"Nenne inaga kamar fa gara ki sanarwa da Aneesa maganar tafiyar mu zai fi." Ya kai karshen maganar yana kurɓar tea.

Komawa Nenne ta yi ta zauna tare da zubawa Asmad ido, kamar tana son gano wani abu, zuwa can kuma sai ta girgiza kai ta ce

"Me ya sa ni zan sanar mata, kai ba zaka iya bane?"

"No! Ba wai bazan iya faɗa mata bane, kawai ina ga idan kika sanar mata zaifi."

"To shi kenan, zuwa anjima zan sa direba ya daukota sai in sanar mata, amma anya kuwa kuna zaman lafiya da Aneesa?"

"Me kika gani Nenne? lafiya lau muke zaman mu fa." Dr ya bata amsa.

"To ai shi kenan." Ta yi maganar tana mik'ewa, ta fita daga dining room din.

Shi kuma Dr yana ganin Nenne ta basu waje, sai ya kai duban sa kan Ameesha ya ce

"Allah ke Heartbeat ko wato kin iya mugunta, shi ne kika dauke nawa bayan kin cikawa naki sugar ko?"

Dan murmushi ta yi tare da kallonsa, zuwa can kuma sai ta fara hamma alamar bacci

"Oh! Lallai ma Heartbeat wato bacci ma za ki yi ko?"

Ita dai Ameesha bata ce masa komai ba, duk maganar da yake, sai ma k'ok'arin tashi don taje ta kwanta take yi, dakatar da ita ya yi ta hanyar rike mata hannu daya, bai sakar mata ba har sai da ya kammala break kafin ya mike

Yana rike da hannunta har cikin bed room din Nenne, kwantar da ita ya yi yana faɗin

"A tashi lafiya Yar Ummi." Lumshe ido ta yi batare da ta yi magana ba. Yana fita falo ya samu Nenne zaune tana karatun littattafin hisnul-muslim, dubanta ta kai ga Asmad ta ce

"A'a Asmad dama baka tafi ba?"

"Eh! Dama Ameesha ce take jin bacci shi ne na kai ta bedroom, na barta har ta fara baccin." Ya bata amsa yana sosa kai.

Harara ta zabga masa ta ce

"Ya yi kyau, amma bana son wannan shashancin."

"Yi hakuri Nennena." Dr ya yi magana cikin shagwaɓa. Murmushi ta yi ta ce

"To na hak'ura Allah ya taimaka."

"Amin." Dr ya amsa daga haka ya fita zuciyarsa fes, ko da ya isa office aiki sosai ya yi, da zai koma gida bai biya gidan Nenne ba domin dai yasan matukar ya je ba zai je wajen Aneesa a kan lokaci ba. Don haka sai kawai ya wuce gida.

A falo ya samu Gimbiyar kwance da waya a hannunta, ko sallamar da ya yi bata amsa ba, bai nuna ya ji haushi ba domin so yake su yi magana ta fahimta, don haka sai ya isa inda take kwanciya ya zauna yana faɗin

"Wai Aneesa har yanzu fushin ne?"

Ko ɗago kai ta kalleshi ba ta yi, sai ma ɗan matsar da jikinta da ta yi, tana taɓe baki, murmushi ya yi tare da jawota jikinsa yana fadin

"Gaskiya na gaji da fushin nan zuwa yanzu ya kamata a sarara min."

"Wa yake fushi da kai?" Ta yi tambayar kamar bata fahimci inda ya dosa ba

" Ke ce kike fushi da ni Aneesa."

"A kan me zan yi fushi da kai?" Ta yi maganar cike da rainin hankali.
"Ok shi kenan tunda baki fushi da ni, yanzu dai tashi mu yi wata magana dake mai muhimmanci."

"Kunne ke jin magana don haka ina jinka."

"A'a kinga ki tashi kawai kamar yadda na bukata, don ba maganar wasa za mu yi ba." Cikin daure fuska ya yi maganar.

"Mtsss" taja ƙaramin tsaki a zuciyarta tare da tashi ta zauna "ina jinka." Ta faɗa cikin karamin murya.

Ya bude baku zai yi magana ta yi saurin katse shi

"Dazun Nenne take sanar min da tafiyar ka Egypt, da gaske tafiyar zaka yi ka barni?" Ta kai karshen maganar tana gyara zama, sam fuska babu walwala.

"Eh! In sha Allah jibi ne tafiyar."

"Ni kuma a ina za'a barni kenan? Ko tare zamu tafi? Tsare shi ta yi da idanunta.

"A'a ita ɗaya zamu tafi, ita ma ɗin don lalura ce, in sha Allah zan rika dawowa ganinki har lokacin da zata samu sauki.

"Asmad kenan! Allah ya bata lafiya, amma dai a rika yin adalci." Zuciyarta wani irin zafi da raɗaɗi take yi.

"Kar ki damu my Anee zan rika yi." Cikin farin cikin yadda abin ya tsaya a haka yake yi, tabbas yasan badan Nenne ta faɗa mata maganar da kanta ba, lallai da ba karamin daru Aneesa zata masa ba.


"Sai ki yi min list ɗin duk wani abu da zaki buk'ata."

"Hmm! Sai anjima zan yi, ina godiya." A takaice ta bashi amsa.

"Ok ari na ɗan watsa ruwa zafi nake ji, sai na fita na samo mana abin da zamu ci nasan yanzu hutu kike yi babu ruwan ki da girki." Cikin zolaya ya karasa maganar yana tafiya.

"Hmmmm! Shi ne kaɗai abin da Aneesa ta iya faɗa, lokacin da taga Dr ya shige dakinsa, wani irin takaici ne ya rufe ta.

"Lallai Asmad kenan zai kai matarsa Egypt! Duk da dai rashin lafiya ne, amma ai sam bai kyauta min ba, har yaushe ni da ya fara aura ko Abuja bai taɓa zuwa da ni ba, amma ita zai tafi har Egypt Wai don neman lafiyar ta, ko wane irin ciwo ke damunta oho! To koma dai hutun amarci zasu je, no! Ta ba kanta amsa dai dai da zubowar hawayen da suka cika idonta.

Kuka sosai take yi, a haka har Dr ya fito ya sameta, bai yi mamakin yadda yaga tana hawaye ba, don sa rai ya san ta da bakin kishi, babu mamaki akan maganar tafiyarsa take kuka.

Lallashinta ya yi da kyar ta yi shiru, sannan ya shiga kicin da kansa ya dafa masu indomie, ya juyo a plet sannan ya fito falon, ko da ya kawo cewa ta yi bata ci sai da kyar ya rarrasheta ta yadda zata ci, a baki ya rika bata har ta koshi.

"Madam har kin koshi kenan?"

"Eh! Ta bashi amsa a takaice.

"Ok sai bacci ko?"

"Uhmmm." Ta ce
tana mik'ewa

"To Allah ya bamu Alhairi."

Cikin kosawa da maganar ta ce "Amin" tare da tafiya.

Da kallo ya bi bayanta har ta shige,, sannan ya sauke nannauyan ajiyar zuciya, plet ya dauka yafara cin abincin don sosai ya ke jin yunwa, tas ya cinye ya kora da fresh milk, kallo ya kunna don yana son kallon news, karfe goma ya kashe komai na falon sannan ya nufi makwancinsa, sai da ya leka Aneesa ya ga ta yi bacci kafin ya wuce.

Yana shiga dakin ya yi shirin kwanciya, yana addu'an samun nasarar tafiyar su.

A bangaren Aneesa kuwa tana kallon lokacin da Dr ya shiga ɗakinta, kuka take yi amma jin shigowar sa , sai ta yi kamar tana bacci, don bata bukatar ganinsa so take ta yi kuka sosai don ta samu sassauci a zuciyarta, tana jin fitarsa ta kuma sakin wani sabon kukan kwana ta yi tana tsiyayar da hawaye, da ta tuno da maganar tafiyarsa sai hankalinta ya kara tashi, bata taɓa sanin tana wa Dr mahaukacin so ba sai yau, kishinsa ta ke fiye da tunani.

Tunda ya dawo sallar asuba bacci ya koma bai farka ba sai bakwai saura, sai da ya gama shiryawa ya fita falo bai samu Madam a falo sai ya shiga bedroom, kwance ya sameta jikinta rufe ruf da bargo bacci take yi, kallo ɗaya zaka mata kasan ba baccin jin dadi bane. Girgiza kai ya yi tare da soma tashin ta a hankali har ta bude ido.

"Tashi ki yi sallah Please."

Sai da ta yi doguwar mik'a kana ta sauka cikin daure fuska kamar wacce bata taɓa dariya, alwala ta yo sannan ta tayar da sallar har ta kammala yana zaune, tana idarwa ta koma kan gado tare da jan blanket.

"Barka da safiya Madam, tunda ni dai bani da matsayin da za'a gaisar da ni."

"Sorry wallahi bacci ne a idona, ina kwana an tashi lafiya?" Ta ida maganar tata tana lumshe ido, domin dai sosai take jin bacci don sai kusan karfe huɗu da rabi kafin bacci ɓarawo ya dauketa.

"Lafiya lau." Shi abin da ya iya faɗa, cikin takaici sosai yake mamakin halin Aneesa, wani time sai ta zama kamar mai tambotsai, haka dai ya fita jiki a saɓule ga wata irin yunwa da yake ji shi yanzu har kunyar zuwa gidan Nenne ya ke tunda har ta soma zargin basu zaman lafiya da Aneesa.

Badon ransa ya so ba ya dafa shayi zalla da bread da shi ya yi break ya fita, office ya wuce kai tsaye, bayan ya kammala da duba marasa lafiya sai ya jawo wayarsa ya kira Hafiz bai fi minti goma ba sai ga shi ya iso asbitin.

Bayan sun gaisa Dr ya gyara zama ya ce

"Gobe ne fa tafiya."

"Eh! Ai jiya bayan na tashi aiki sai da na biya gidan Nenne ita ke sanar min, ina maku addu'ar samun nasara da lafiya."


"Muna godiya da addu'a, ai gaskiya ina gano nasara domin Dr Ansar ya yi matukar k'ok'ari, tun daga information na asbitin da ya bani na ji na yadda, sannan na kuma bincike sosai asbitin *AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL* ya kware wajen iya kula da masu ciwo."

"Ai wannan asbitin ya fi haka Allah dai ya bada nasara, yanzu gobe ku kaɗai zaku tafi kenan?"

"Eh! Sai su Nenne da su Abba su biyo bayanmu."

"Hakan zai fi kyau, nima in sha Allah idan aka dan kwana biyu zan zo."

"Allah ya kawo ka lafiya"

Hira sosai suka yi har wajen karfe uku kana suka bar office don zuwa gidan Abban Ameesha. Bayan sun gaisa ne Abba ke kara tambayarsa yadda tafiyar zata kasance, nan dai suka tattauna da Abban yana ta masu fatan alheri da samun nasara daga karshe ya yi sallama da Abba akan sai gobe.

Yau ta kasance ranar asabar kuma ranar ne da su Dr zasu tafi Egypt tun wuri ya tashi domin dai jirgin karfe takwas zasu bi ya yi wanka tsab ya shirya cikin wasu kananan kaya wanda suka matukar amshi jikinsa, sai baza kamshin turare ya ke yi falo ya fita hannunsa dauke da karamin jakar da ya shirya kayansa kai tsaye bed in Aneesa ya nufa da sallama.

A zaune ya sameta ta zuba uban tagumi, cikin sauri ya matsa inda take ya na faɗin

"Lafiya kuwa?"

"Lafiya lau mai ka gani?"

"Naga kin haɗa kai da gwiwa ne alamar damuwa zalla."

Murmushi ta kakalo ta ce "Babu komai fa Hamman, har ka shirya kenan?"

"Eh! Na shirya ki yi mana addu'a." Cikin murmushi ya yi maganar.

"Allah ya tsare hanya."

"Amin ya amsa yana kallon agogonsa tare da tafiya.

"Hamman..." Sai kuma ta yi shiru.

Dawowa ya yi ya zauna kusa da ita yana faɗin

"Menene Aneesa fadi maganar ki ina ji."

"Don Allah ka barni in tafi Adamawa." Murya na rawa ta dire maganar.

Girgiza kai ya yi ya ce

"Ba zai kije Adamawa ba, amma dauko gyalen ki in kaiki gidan Nenne."

"Please Hamman."

"Bana son musu ki yi yadda na ce kawai."

Haka nan ta tashi badon ranta ya so ba, gyale ta dauka suka fita.




_*YAR MUTAN RANO*_
[10/8, 8:15 PM] Zulayheart Rano: *SANGARTA*


©
*ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

```Sadaukarwa ga AMRAH AUWAL MASHI (Princess Amrah) na sadaukar maki da wannan page din kyauta domin jin dadin ki, Allah ya kara basira da kaifin k'wak'walwa, ki ci gaba da suburbuɗo mana AMRAH NAKE SO muna jin dadin buk ɗin sosai, ina gaida RAZ```


_*I hearttttt You My Besty irin har abada dinnan.*_💞
*32*

Tsayuwar motarsu ta yi dai dai da zuwan motarsu Abban Ameesha, cikin sauri Dr ya faka motar ya fito, kai tsaye wajen su Abba ya nufa, cikin fara'a Abba ya fito tare da mikawa Dr hannu sukai musabaha, ya yi da Dr ya tsuguna yana gaida Ummi da Abba cikin kunya.

Wasu motar ce suka kuma shigowa, yaya Jaheed ne da matarsa sai ta ya Abdul da Meena, duk fitowa suka yi suka nufi inda Alhaji Taheer ya ke.

Sai a lokacin Haydar ya fito daga cikin motar su Abba, gaisuwar mutunci suka yi da Dr sannan suka kama hanyar falon, wanda tuni Aneesa ta shiga tana zaune a falon tare da Nenne suna dan taɓa hira.

Sallamar Dr ce ta katse masu hiran "Nenne ga su Abban Ameesha sun iso fa." Dr ya yi maganar bayan sun gama gaisawa.

"Je ka dakin Bobbo ka sanar masa, bari na shigo da su Hajiya Halimar." Nenne ta ida maganar tana mik'ewa.

Daret Dr bed room na Bobbo ya shiga ya sanar masa da zuwan su Alhajin, a tare suka fito fara'a sosai Bobbo ya saki suka gaggaisa da Alhaji Taheer, don tuni sun shiga falon.

"Nenne ina Meesha ne?" Meena ce ta yi tambayar don tun shigowar ta bata ganta ba.

"Twin's din Ummi har kin gaza hakuri kenan? To tashi tana cikin bedroom." Cikin dariya Nenne ta yi maganar.

Ai tun kafin Nenne ta rufe baki har Meena ta nufi bedroom din.
Su dinma dariya suka yi, suna jin dadin yadda Meena da Meesha suke rayuwa, sam babu hassada balle bakin ciki.

Dr kallon agogon hannunsa ya yi yana faɗin

"Abba time yana tafiya fa, 7:45 AM yanzu kuma 8:15 AM jirgin zai tashi."

"To mai muke jira? Ya ci gaba "ai inaga gara mu tashi mu tafi kar mu makara." Abba ya gama maganar dai dai da fitowar Meena da Meesha. Murmushi Abba ya saki ganin Ameesha.

Ita kam wajen Nenne ta nufa ta zauna, sai kallon su Ummi take yi, ido Aneesa ta zubawa Ameesha tana kallon kyau irin na Ameesha sai yau ta yi mata kollon sosai. Sanye take da wani hadaddiyar doguwar riga kalar pink da white, fuskarta ta sha kwalliya daga inda Aneesa ke zaune tana jiyo sansanyar kamshi turaren da ke jikin Ameesha a jiyar zuciya ta sauke a ranta ta ce "Dole Hamman ka riƙa yin rawan kai."

Shi kuwa Dr tunda yaga Ameesha ta fito sai ya maida hankalinsa kacokan kan Ameesha yana kallon irin kyau da ta yi, yana jinjina k'ok'ari irin na Meena don yasan aikinta ne wannan. Sosai ya shagala har ya manta a wajen da yake sai da ya ji muryar Alhaji Taheer yana faɗin

"Dr ka tashi mana lokaci fa yana tafiya."

"To." Dr ya faɗa yana mik'ewa.

Gaba daya suma suka mik'e, daret wajen motoci suka nufa kusan duk bakin su dauke da addu'ar samun nasara, kai tsaye babban filin saukar jirgin saman suka ɗauki hanya, cikin mintina ƙalilan suka isa airport.

Ba su wani daɗe ba, suka gama duk wani shiga da fita har komai ya kammala, sai jiran a fara kiran fasinjoji Dr ne ya dubi Abba ya ce

"Abba zamu tafi a yi mana addu'an samun nasara." Cikin ladabi ya yi maganar.

"Allah ya taimaka Dr in sha Allah za'a samu nasara, nan da kwana huɗu zamu zo, Allah dai yasa a yi cikin a." Cikin kwantar da hankali Abba ya yi maganar.

"Allah ya kawo ku lafiya Abba." Dr ya yi maganar dai dai lokacin da aka fara kiran fasinjoji. Addu'a kawai su Ummi suke yi har da hawaye, musamman yadda ita Ameesha bata wani damu da abin da ake ba, ita dai tunda taga da Dr zasu tafi sai ko tada hankali bata yi ba, Dr yana daga masu hannu har suka shiga cikin jirgin.

Meena wani sabon kukan ta fashe da shi a fili take faɗin

"Allah kaba Ameesha lafiya, Ubangiji ka yaye mata wannan lalura." Ta ida maganar wasu hawaye suna zubowa.

"Amin." Su Ummi suka amsa, suna wajen har sai da jirgin ya tashi tukun suka dauki hanyar gida. Dr kuwa ko da suka shiga jirgin zama suka yi, ya dauko wani littafi yana karantawa, jingine Ameesha take da jikinsa har bacci ya kwashe ta, ko da yaga haka sai ya gyara mata kwanciyar, yana shafa sumar kanta wanda yasha gyara sosai Meena ta gyara mata sumar sai kyalli take, tafiya ce mai tsawo suka yi kafin suka isa Egypt.

Lokacin da jirgin ya sauka a *INTERNATIONAL AIRPORT CAIRO* Dr Asmad kallon agogon hannunsa ya yi yaga karfe biyu saura mintina goma sha biyar, akalla sunyi awa biyar da minti ashirin da biyu suna tafiya, yana rike da hannunta suka fito daga jirgin motar da zata ɗauke su a wajen suka sameta, da yake Dr sun yi musayar pic da Dr Ansar basu yi wahalar gane juna ba.

Gaisawa suka yi cikin farin ciki kamar sun daɗe da sanin juna sannan Dr Ansar ya umurce su da su hau mota, suna shiga direba ya ja bai zame da su ko ina ba sai *Steigenberger Hotel El-Tahrir* dake cikin birnin CAIRO, sosai hotel din ya yiwa Dr kyau repretion suka shiga inda aka basu makilin dakin, Dr Ansar har dakin ya raka su

"Dr ku zauna anan idan ku ka huta ku ka ci abinci zuwa 6:30 direba zai zo daukar ku." Cikin turanci yake maganar.

Gyada kai Dr Asmad ya yi tare da cewa "To muna godiya Dr." Murmushi kawai Dr Ansar ya yi ya ja masu kofar ya wuce. Ciki Dr ya shiga inda ya samu Ameesha kwance akan kujera three sitter, idonta lumshe kamar mai jin bacci zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"Heartbeat kina Jin yunwa ko? Sorry yanzu za'a kawo mana abinci, tashi ki yi wanka." Ya ida maganar yana latsa wayarsa lambar Nenne ya kira.

"Hello Nennena fatan kina lafiya?"

"Lafiya lau Asmad kun sauka lafiya?"

"Alhamdulillah lafiya muka sauka, gamu a hotel ma."

" Masha Allah! Na ji dadin jin haka, Allah yasa ayi wannan aiki a sa'a ina autar Ummi?"

"Ga ta nan tana jinki Nenne."

"To ai shi kenan Allah ya taimaka."

"Amin." Dr ya amsa sannan suka yi sallama.


Number Abba ya Kira, nan ma sun daɗe suna hira

Please Login or Register in order to submit comment