Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

✍

👨‍⚕️ Doctor Shazim👨‍⚕️
     
Daga alƙalamin

KHADIJA ( M ) ABDULWAHAB

KAINAAT... ✍ 

*_KING AND QUEEN WRITING CHAMBER_*

Proud to my first novel

Ina alfahari da  kasan cewar wannan littafi na farko agareni 📚 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma ɗaukakin sarki mai kowa mai komi da ya bani ikwan rubuta wannan littafi.
Ya ubangiji al'arshe kabani ikwan rubuta abin da zai amfani muslinci da muslmai, ka bani ikwan rubuta abun da zai amfaneni duniya da lahira 🙏

✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️

Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na littafin   nan ba ta kowace hanya, ba tare da an nemi izni a wurina ba.
idan kunne ya ji jiki ya tsira!

Wannan labari ƙagegen ne ,sannan ban rubuta shi ba da niyyar muzanta wani ko cin mutuncin wani ba,  duk   wanda ya ga wani abu yayi shige da halayyar shi arashi ne. 

Season one
Free

Episode 1_2

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ_

12 June 2003

_Ƙarfe 12:30 Am

Yanayin sanyin da gari yayi, da iskar da ke kaɗawa wanda ya haddasa ganyayyakin bishiyu yin rangaji, tare da ba da wata sassanyar iska.
Yadda sauran ruwan saman da ƙasa bata gama shanyewa ba, da wanda yake gudu acikin kwalbatoci zai tabattar maka da lallai damuna ta kama.

Shiru anguwar take sai kace ba kowa a cikin ta saboda yanayi na dare haɗi da damuna, duk da daman ba'a cika samun mutane na kai kawo a cikin irin waɗannan anguwannin ba ko da kuwa da rana ne, sai hasken bulbs daya haske anguwar haɗe dana street lamps  kaɗai ake gani.

Anguwace irin ta masu faɗa aji a cikin ƙasa, domin kuwa daga shahararrun yan kasuwa sai manya a gwamnati ke a cikin ta.

Motace ta shararo da gudu daga kwanar dake hannun dama a cikin anguwar, yayin da wasu ba ƙaƙen motoci guda huɗu ke biye da ita.

Gudu motar take sosai har ta fita daga cikin anguwar ta hau babban titi, still wa ɗannan moticin na biye da ita a baya
Daga irin gudun da mamallakin motar ke yi zaka san cewa yana gudu ne tsakanin rayuwa da mutuwa.
ta mirror ɗin motar yake hangen fitilar motocin da ke binsa,
yana gudu motocin na bin sa har suka hau kan titin da zai fitar da kai daga garin, gudu suke har suka fita daga garin,
in ban da salati da neman ɗauki daga ubangiji babu abun da mai motar nan ke yi.
domun shi a yau ya san tashi taƙare, saboda ya galabaita a dalilin dukan daya sha, tukin neman ga garar sa yake, ƙarfinsa ya kusa ƙarewa, dubawa yayi ta cikin mirror motar amma bai ga alamun waɗannan motocin ba, tunani ya fara to ko ya tsre masu ne, amma duk da haka bai fasa gudun da yake ba, wani mummunan Bugun da yaji an kaima ma motar shi ne yasa shi fahimtar ce wa kenan wata hanyar suka bi amma suna biye da shi mirror ɗin motar ya kalla, amma sai yaga ba waɗan cen motocin ba ne, wata ƙatuwa truck ce ke binsa yanzu saɓanin waɗancen motocin, ba shiri ya karya kwana ya faɗa cikin daji, gudu kawai yake amma ba wai ya san inda yake dosa ba ne, tsintar kansa kawai yayi a bakin wani ƙaton rami mai zurfin gaske, dole tasa shi taka birki ba dan ya shirya ma hakan ba sai dan baya da wani zaɓi, kawai ya sadakat kwanan shi a yau sun ƙare.
bai gama wannan tunanin ba yaji me truck ɗin ya kaima motar shi wani mumunan bugu wanda ya haddasa mashi buguwar kai nan take ya suma.
Sake ja da baya me truck ɗin yayi ya kaima motar wani bugun wanda yafi na ɗazun, nan take motar tayi cikin ramin, ko karar faɗawar ta ba'a ji saboda tsananin zurfi irin na ramin .
parking me truck ɗin yayi a bakin ramin tare da leƙa ramin ta hanyar hasken motarshi daya bari a kunne.
wani irin ramine me zurfin gaske, wanda tsananin zurfin shi zai sa ka kasa ganin abunda ke ƙasan ramin.

dariya yayi me sauti da amo tare da cewa yanzu kam nasan zan samu cikwan kuɗina domin wannan sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba.
komawa yayi cikin motar shi, anan yasamu wayar shi na ringing  ɗaukar wayar yayi
boss  shine sunan daya bayyana a jikin screen ɗin wayar,  picking call ɗin yayi tare da sa wayar a handspree  tun kafin yace wani abu me kiran nashi yace " Ina fatan kagama dashi? "
answer ya bama boss  ɗin da cewa " ai wannan tashi ta ƙare sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba,  dan a yanzu yana can ya gana da magabatan sa"
"amma naji daɗin jin haka" boss   ɗin ya faɗa .
"amma boss ya kake ganin za'ayi da matar shi da yaran shi ?" me truck ɗin ya tambaya.
"Kar ka damu da wannan big boss.   zaiji da komai , yanzu dai katuraman da account number ka domin natura maka Sauran kuɗin aikin ka "
"thank you so much boss" me truck ɗin ya faɗa. boss ɗin ya ce
"don mind" Kit ya kashe wayar
account number ya turama boss tare da yima motar key ya bar wajen

WANNAN KENNAN.

🌹~ _Kainaat_ ~ 🌹

Gida ne matsa kaici shi ba ƙarami ba shi kuma ba babba ba chan sosai ɗan dai dai.
gida ne namasu rufin a siri kuma yan boko naji da faɗa.
Painting ɗin gidan ya kasance white and blue color ne, haka ma get ɗin gidan blue and white ne.
daka shiga compound ɗin gidan zaka fara cin karo da ɗakin mai gadi daga hannun hagu Sai parking lot daga hannun dama wanda ke ɗauke da rides masu kyen gaske da tsada na fashion a ƙallah za su kai guda 5 a parking lot ɗin.
Sai garden mai kyen gaske ga suke suke masu ɗaukar hankali.
Sai boys quarters dake bayan part ɗin masu gidan.
Masha Allah na furta a ya yin da nayi arba da parlorn gidan wanda aka ƙawata shi da furniture's masu kyen gaske da tsada, komai na cikin parlor onion and pitch color ne, daga gefen daman parlor twin up stairs ne me kyau
Sai kitchen dake gefan hagu wanda yake haɗe da store kusa da shi kuma dining area ne mai ɗauke da chairs guda 7,Sai wani ɗan corridor daga gabas ɗin parlor mai ɗauke da 4 bedrooms, daga chan kuma up stairs ɗin ya kasu kashi 3,part ɗin matar gidan dake haɗe dana yaranta ke hannun hagu Sai na me gidan dake hannun dama sai chan gaba na yaron gidan ne namiji. daga part ɗin dake hannun hagu naji anata kwala Kiran Aaimah! Aairah!! Aairah!!!.
Wata kyakyawar mace ce tafito daga ɗaya daga cikin  bedroom ɗin  ta nufi wanda ke kallon nata ta na cigaba da Kiran
" Aaimah " da "Aairah".
Fara ce sosai tana da jiki ba sosai ba ita ba rammama ba Ita ba mai ƙiba ba a kalla zata kai kimanin shekara 50 . jikin ta sanye yake da sleeping dress riga da wando masu santsi yana yi da Pakistan dress pink color. ba ƙaramin kyau suka yima surar jikinta ba.
"Kun kuwa san ƙarfe nawa" ta faɗa yayin da take tura ƙufar bedroom ɗin ta shiga.
Masha Allah na faɗa domin kuwa bedroom ne me kyan gaske, komai na cikin sa ya kasan ce pink and white color ne , yaji kaya masu kyan gaske bawai cike yake da kaya ba.
bed ne sai bed side drawers, sai dressing mirror gefen shi kuwa wardrobe ne wanda clothes set ne ciki sai jikin ƙofar shigowa kuma jere suke da ƙofar bathroom sai wani ɗan corridor inda ya kasan ce laundry basket ne da shoe rag ne sai bag hanger , bags ne masu kyau na gayu dana school kowace bag set biyu ce kuma color ɗaya.
turus ta tsaya ganin ta kwance har yanzu akan bed, " Aairah lafiya kike kuwa da baki tashi ba ina Aaimah take Ita ma, ko yau baku zuwah school ne iye. "
Ƙarar buɗe ƙofar bathroom taji juyawa tayi, wata kyakyawar budurwa ce ke tsaye jikinta ɗaure da towel iya gwiwarta jikin ta sai raɓar ruwa yake, alamar wanka tayi,  fara ce Ita ma kamar mahaifiyar ta tana da dogon gashi har ƙugunta, ga matsakai tan idanu masu ɗauke da brown eyeball da zara zaran eyelashes, hancinta ma ɗan dai dai dogon bamai yawa ba sosai, ga small mouth me ɗauke da pink lips, tana da shape mai ɗaukar hankali sannan tana da tsayi amma ba sosai ba chan. masha Allah kawai zamuce, akalla zatai kimanin shekara 18 a duniya.
"Ok kintashi kenan Aaimah ce kenan bata tashiba."
"Wallahi mom  tunɗazu nake tashin ta amma taki tashi wai Ita batagaji da bacci ba."
"Tafi ke ki shirya, rabu da Ita yanzu ai zata tashi ba dan halinta ba " mom ta faɗa a lokacin da ta ƙarasa jikin bed ɗin , "Aaimah! Aaimah!! wake up, its time for school , ko kina sone kuyi late ne iye autar mom . "
"Uhm uhm uhm haba mom wai miyasa kike cema Aaimah auta nifa" Aairah tafaɗa yayin da take buga ƙafa tan turo baki haɗe da rike ƙugu.
ai kuwa nan Aaimah ta tashi tana ma Aairah dariya harda gwalo, dama duk abunda mom ke faɗa tana ji, tashi ne kawai bata yi ba
"mom  kinganta ko dariya take man harda gwalo"Aairah ta faɗa sai wani turo baki take da hura hanci. "Ke da'alla  rabu da Ita, ai kema autah ce"
mom ta faɗa  tana dariya ganin yarda Aairah kema Aaimah dariya harda tsalle, "oho dai ai ni aka fara cemawa" mom ta katse ta da cewa
" To ya isa haka maza kushirya
ABIE na nan yayi shirin tafiya , kunsan dai yau zai koma wurin aiki abuja."
"to shikenan mom gamu nan zuwa" har suna haɗa baki wurin faɗin haka.
fita Mom tayi daga bedroom ɗin haɗe da jawo masu ƙofa, ta shi Aaimah ta yi ta nufi bathroom tana faɗin my twin sister dan Allah kifito man da uniform ɗina kafin na fito"Aairah ta ce " to sannu mom kinji koh"
"haba twin sister dan Allah fa nace" Aaimah ta faɗa tana lan gwabar da kai , Aairah ta ce " hmmm sai shegen daɗin baki kamar ta Allah"
" Pls twinee" Aaimah tasake faɗa
"shikenan ba dan halinki ba"Aairah ta faɗa tana ya tsine fuska,murmushi Aaimah tayi tana faɗin "yawwa twenny Ni na san nafi kowa Sa'ar Yar uwa a duniya shiyyasa nake alfahari dake baki sani ba fah irin daɗin da nake ji Idan naganki kusa dani ba" , baki kawai Aairah ta saki tana sauraron ƙar yar da Aaimah ke shirga mata. "wallahi Aaimah kin bani ki rinƙa jin tsoron Allah , ko kunyar ƙarya ba kyaji " gwalo Aaimah tayi hadi da jawo ƙofar bathroom ta shige, dariya kawai Aairah tayi haɗi da girgiza kai tana faɗin " Allah ya shirya ki Aaimah da karya"
wurin dressing mirror ta wuce Vaseline ɗin dove ta shafa tare da farar powder kaɗan ta shafa a fuskar ta sai kwalli da tasa ma eye's ɗin ta, wurin wardrobe ɗin su ta wuce buɗewa tayi , kaya ne masu yawan gaske komai set biyune, wurinda hijaban su suke daban haka ma sleeping dress ɗinsu da ban suma dogayen riguna da atamfofi wurinsu suma da ban haka ma uniform ɗin su na school dana Islamiyya,
uniform ɗin school ta ɗako masu set biyu itada Aaimah wurin bed ɗin su ta koma da kayan a hannun ta domin ta shirya.
shaf shaf ta shirya cikin uniform ɗin ta masu ɗan karan kyau, riga ce da skirt, rigar white color ce, skirt ɗin wanda ya kasance iyakarsa gwiwarta pink color sai sock's fara me ratsin pink daga sama sai top wacce itama ta kasan ce pink color sai Yar baby hijab it kuma white color ce, wurin corridor ɗin su ta nufa shoe da school bags ɗin su ta ɗauko masu, white color ne takalman snikers sai school bag pink color.
"Sis kin ɗauko man nima uniform ɗin" Aaimah ta faɗa wacce fitowar ta kenan daga bathroom. amsa Aairah ta bata da "Eh Amma fa kiyi sauri ki shirya kona tafi wurin Abie na barki" wurin dressing mirror Aaimah ta nufa tana faɗin" sorry karki damu yanzu zan shirya ki bani 5 minute insha Allah " shaf shaf itama ta shirya cikin nata uniform ɗin Masha Allah
Itama ba ƙaramin kyau tayi ba saboda itama Aaimah kykyawa ce sosai a bun da kawai Aairah zata nuna mata tsayine shima ba wani finta tayi ba sosai ka mannin su ɗaya da Aairah tsayinne dai kawai banbancin su shima sai insun jera zaka fahimci hakan.
Snickers ɗin ta itama ta saka tare da amsar bag ɗinta dake hannun Aairah
a tare suka fita daga bedroom ɗin direct part ɗin Abie suka nufa, hannun su cikin na juna suka shiga parlor  ne mai matuƙar kyau,  dan yafi na down stairs kyau da haɗuwa domin ya ƙawatu da expensive furniture's, komai na cikin parlorn sky blue ne da fari.
wani kykyawan matshin tsohone wanda Akallah zaikai ki manin shekara 60 a duniya, yana da haske shima sosai, zaune yake akan 2 siter
" abie " kenan
tea yake sha wanda mom  ta haɗa mashi, sallama sukayi tare da ƙarasawa ciki suna faɗin "abie  ina Kwana antashi Lafiya "suka faɗa yayin da suke samun wuri kusa da abie suka zauna,
"lafiya lau alhmdllh my daughters ina fatan kuma kuntashi lafiya" "Alhmdllh abie " suka faɗa, Abie ya ce
"to Masha Allah haka ake so"
"amma Abie zaka tafi yau shine baza ka yi breakfast damu ba" Aaimah ta faɗa tana turo baki
"Sorry my daughters duk da ma laifin kune tunda tun ɗazu ya kama ta ace kuntashi amma kuka yita bacci gashi ni kuma sauri nake, ai daya ke bajima wa zanyiba wannan time ɗin, zandawo very soon kunji koh."
"shikenan abie Allah ya dawo da kai lafiya"da ameen abie ya amsa tare da kai cup ɗin tea bakin sa.
"to uwayen surutu atashi aje ayi breakfast time na kurewa, abar shima abie ya samu ya gama nashi breakfast ɗin karya makara "mom  ce ke magana wacce fitowar ta kenan daga bedroom ɗin abie hannun ta riƙe da jakar kayan shi da zaiyi tafiya da Ita
"Uhmmmmm haba mom dan Allah kibari muƙara sa yin ban kwana mana" Aairah ta faɗa tana turo baki, dariya kawai Abie ke masu
"Kinci gidan ku nace kutashi kuyi breakfast yana chan baba larai tashirya maku,  nima abarni nayi ban kwana da mijina"
"ah mom sai kice mutashi soyayya ta motsa, to bari muyi ta kanmu," Aairah ta faɗa tareda yin dariya
"Kunci gidan ku jairan banza marasa kunya kawai "abie ne ya faɗa tare da yi masu daƙƙu wa
dariya suka kwashe da Ita, " abari muga soyayya tukunnan sai mu tafi" Aaimah ta faɗa hadi da gyara zaman ta, wurin su mom  ta nufo ai bashiri suka mike da gudu suka fita daga part ɗin suna dariya.......
"Kaga man jairan yara marasa kunya"mom ta faɗa yayin da take zama kan hannun sofa da abie  ke zaune, dariya abie  yayi tare da cewa "Allah ya shirya, dan inkika biye ma su Aairah sai su samaki ciwan kai" "wallahi  kuwa ai abdallah  ne kawai maganin su, yama shigo kuwa" mom ta faɗa.

Aa ina jin baigama shirin zuwa hospital nasan daya gama zai shigo muyi sallama, haka ne kuma mom ta faɗa  tare da cewa" yanzu dai ba wannan ba yaushe zaka dawo? "
"2 week's kawai fa zanyi "
"ashe kuwa kashirya zuwa dani abuja kenan Indai 2 week's zakayi ƙafata ƙafarka,  murmushi  abie  yayi haɗi dacewa "to su fa yaran ki kibarma wa su iye"
" dan Allah kabar ma maganr yara Sai kace wasu yan goye saunawa Nake zuwa abujar batare da su ba"

Assalamu Alaikum sukaji an faɗa  katse labarin dasuke sukayi haɗi  da amsa sallamar, wani matashin saurayi ne kyakyawan gaske wanda ko ba'a faɗa maka waye shi ba kamanin sa da abie zaitabbatar maka da cewa ɗan sane, DR. ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM  kenan matashi maiji da waye wa ga ilimi both side boko da Islama, farine shi ma sosai yana da tsayi dai dai misali gashi irin mazannan ne masu motsajiki dan yana da kirar jiki mai kyan gaske ga  ƙasumba irin ta yan gayu domin kuwa daga ganin ta kasan tana shan gyara, jikin sa sanye yake da uniform ɗin  sa na  aiki hannun sa riƙe da  briefcase  ɗin  shi,  ƙarasawa ciki yayi wuri ya samu ya zauna,yana faɗin " inakwana abie mom ina kwana",  lafiya lau alhmdllh suka amsa mashi abie  ya ɗaura da cewa "har anyi shirin fita aiki kenan? "
" eh abie  dayake ina da shiga thearter   ƙarfe 10:00," 
"masha Allah , Allah ya taimaka," "ameen ya rabbi , abie dawuri zaka wuce ne yau? "

"eh dawuri zan wuce saboda gobe tunda safe ina da shiga court ‍,  amma insha Allah bazan jima ba zan dawo ina ma tuna nin two days zanyi na dawo"
"to shikenan abie  Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya" da ameen suka amsa mom na faɗin
"breakfast ɗinka nachan dining,  sannan su Aairah na nan kawuce dasu school in baza kayi late ba, 
"amma mom mi ya hanasu bin school bus yau? "
" uhm kai dai bari,  shegiyar shiririta ce irin tasu , kasan halin su yanzu haka idan akace maka suna can basu kammala breakfast ɗin  su ba ba'a gardama,  narasa gane shiririta irin tasu Aaimah wallahi yara sai kace ba masu jini ba ajiki suyita abu kamar basu sanyi, Allah dai ya shirya su, ameen abdallah  ya faɗa  tare da cewa "bari naje nayi breakfast ɗin  sai na dubasu"
"ok muma ga mu nan sakkowa"tashi yayi ya fice ya nufi  dining,  tunkafin ya isa yake jin hayaniyar Aaimah da Aairah sunata zagaye dining Aairah ta ɓatama Aaimah baby jiba da tea itakuma Aaimar nacewa saita rama shine fa suke ta zagaye dining baaba larai sai cewa take su bari amma ina kamar ƙara zugasu take.

Tsawa abdallah  ya daka masu tare da cewa "ashe ku shasha shune ban sani ba,  zaku dawo ku zauna ko sai ranku ya baci sakarkarun banza da wofi,  wallahi kushiga hankalin ku kullum girma kuke amma ɗabi'un ku sak na yara. bashiri kowace cikin su ta nemi wurin zama, baaba larai ce ta matso zatayi serving ɗin ya abdallah tana faɗin " abdallah  an tashi lafiya"
"lafiya lau baaba,  ina kwana," Alhmdllh tace "mizan zuba maka"
"a'a kibarshi kawai baaba Aairah ta zuba man,"
"to shikenan ni bari nawuce kitchen"
Aairah yace ma tayi serving ɗin sa ita kuma Aaimah tayi sauri ta chanzo hijab ɗin  ta tunda sungama breakfast ɗin su , to tace haɗi da tashi ta nufi  bedroom ɗin su.

Abie  ne ke saukowa shi da mom hannun ta riƙe da  jakar kayan sa  ,  "abie  kafito " ya abdallah  ya faɗa  ayayin da yake kar ɓar jakar kayan a hannun mom,yana faɗin "abie muje koh" yayin da yake fita daga parlorn , bayansa suka bi har da Aaimah wacce sakowarta kenan daga bedroom ɗin  su dataje chanzo hijab,"adawo lafiya,  alhaji Allah ya kiyaye hanya yakai ka lafiya ya dawo da kai lafiya" "ameen ya rabbi baaba larai" abie  ya bata amsa, fita sukayi compound ɗin  gidan wurin motar abie suka wuce wacce baka driver  ya daɗe  da fito da ita dan har ya abdallah ya saka ma abie  kayan shi a booth ɗin  motar bankwana suka shigayi su Aairah har da hawaye abie  sai lallashin su yake.

abdallah ne yace" dan Allah abie  ka kyale  yarannan  sai sun sa kayi late", "kuyi hakuri bazan jimaba zan dawo may be na dawo nan da 2 days kunji" "to abie  Allah yatsare hanya"
ameen abie yace
abdallah ne yace "to kuwuce ciki ku ɗauko school bag ɗin  ku na ajiye ku a school,  abie  Allah ya tsare"  ya faɗa   haɗi da tasa keyar su Aaimah zuwa ciki, mom ce ta matso kusa da abie  tana cewa "wallahi barrister kamar kar ka tafi nake ji"
" tofah yara shagwaɓa  uwa shagwaɓa  toni wazan kama" ya faɗa  yana dariya "uhmm kaima kasan wanda zaka Kama" ta faɗa tana ɓata rai,  "yau naji shiyyasa kenan kika ƙi magana sai da yaran ki suka shige ciki zakiyi man adawo lafiya , ashe shagwaɓa  za'ayiman ban sani ba ", mom tace "ok hakama zakace "ta faɗa haɗi da juyawa zata nufi ciki ,  hannun ta abie  ya riƙo yana faɗin  "Sorry kubrah,  kema kinsan wasa nake , karki damu bazan jima ba zan dawo insha Allah"

"to shikenan Allah ya dawo man da kai lafiya" ameen abie  ya faɗa  yayin da yake shiga cikin mota sit ɗin  baya ya zauna  bala driver na  gaba key yayima motar, hanu mom ke ɗaga ma abie  shima yana ɗaga mata,suka nufi gate,buɗe masu gate baba mai gadi yayi yana faɗin a dawo lafiya " mom na nan tsaye har sai da motar tafita daga gidan sannan ta juya tashiga ciki , dasu Aairah tacikaro suma sun fito a dawo lafiya tayi masu tawuce ciki abdallah  ne ya sauko daga upstairs part din sa  
Yana ce masu ku wuce mu Tafi.

  🌹~KAINAAT~🌹

Fita sukayi wajen mota suka shiga abdallah  ya jasu gate suka nufa wanda tun fitar abie  baba megadi yabar masu shi buɗe  gaishe dashi suka

Please Login or Register in order to submit comment